Join Our WhatsApp Group

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

Login Register

tunda tana dawowa gidan Hamma Abdullahi ya kawo cefane kenan ya san da halin da take ciki kuma ya san a in da take.

Na cikin ne tana da tabbacin bai sani ba. Ammah ce za ta faɗa masa kuma kunyarta ba zai barta ta faɗa ba.
Mami kuma a tunanin ya sa ni shi ya sa ba za ta yi tunanin sanar da shi ba.
Su Hamma Abdullahi kuma wannan ba damuwar su ba ce

ita ta dai ta dage da kula da kanta. Wannan karon ba ta so ta rasa jaririnta. Tana cin abinci amma tana laulayi mai zafi komai ta ci sai amai, ga miyau. Amma duk da haka tana daurewa ta ci abincin ko da za ta yi aman ne.

Magungunar wajen Surayya Halin yau kuma tattarawa ta yi ta miƙa ma Baɗɗo ta ce ta ba ma su Iklima su yi amfani da shi, ita ai ta gama amfani da shi sai in Allah ya sauketa lafiya. Amma ba laifi ta fara mayar da jikinta wannan ramar ta ragu.
Ta fara kula da jikinta tumbin ma ya ragu yana ta bajewa a hankali a hankali.

*Janafty*
Received at 07:52Reactions: ❤ 10, 🥰 1, 🤩 1

[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
BAYAN WATA BIYU.
JIMETA.

Wattani biyu sun shuɗe kamar kiftawar idanuwana, a halin yanzu cikin Ummu Salma watannin shi biyu da wasu satittuka amma bai kai uku ba.

Ammah kuma takaba ya gangara Baffa na cikin wattani uku da rasuwa za ta fita Takaba cikin azumi tunda azumin ya kusa bai fi wata ɗaya da wasu kwanaki ba.

A cikin waɗanan wattani biyun Ummu Salma tana cikin laulayi ne mai zafin gaske irin laulayin da ba ta taɓa yin irin shi ba, ashe cikin mai sunan Baffa kamar kyauta ne ubangiji ya ba ta, ba ta san da haka ba sai da ta samu wannan cikin kuma da alamun haka za ta yi ta shan wahala har sai ta haife shi tunda tun cikin na sati biyu ta fara shan wahalan shi har kuma yanzu tana kan wahala ne.

Duk kuma wannan wahalan da take sha Lamiɗo bai sani ba, tun rabuwarsu bai neme ta ba, itama ba ta sake neman shi ba ta kudirta a zuciyarta ko wani tsawon lokaci ne za ta jira shi tana kuma da yaƙinin in zuciyarsa ta yi sanyi zai neme ta. Ko a chart ba ta masa magana sai dai ta yi ta kallon hoton su tare tana hawaye, adadin kwanakin da ya ƙaurace mata adadin lissafin kaifin maganar da ta faɗa masa tabbas maganar ta cancanci a yi mata wannan hukuncin maganar tana da zafi da kaifi. Addu'anta kullum in ta yi salla Allah ya sausauta zuciyarsa a kanta ya yi mata afuwa.

Ko da ba ya kiran ta a waya ta san yana neman lafiyanta a wajen makusanta ta. Su kuma daman ba su san wani abu ya faru ba kowa a tunaninsa tana zaune ne in Lamiɗo ya zo za su koma tare. Hamma Abdullahi na zuwa lokaci bayan lokaci yana duba ta, zai tambayeta in tana da matsala? sai ta ce babu. Laulayi ne kuma shi ba shi da magani.

Sannan Baɗɗo ma zuwa lokaci bayan lokaci ta fara kasuwacin siyar da takalma mayafai turarukan wuta da na jiki. Gida kuma lokaci bayan lokaci za ta shirya ita da Harira su je can su yini har wani lokacin ma har su kwana kowa tausayinta yake ji har Ammah, saboda cikin mai amai ne komai ta ci sai ta yi amai haka nan za ta sake ci abin da ya tsaya shi ne rabon ta wanda ya fita kuma shike nan ga shi cikin rama yake sakata ko ta fara mayar da jikinta cikin lokaci sai ta koma ta bushe. Da Mami ta dawo ta je ta ganta ta ce cikinta mai laulayi ne sannan ba zai saka ta kiba ba, bushewa kawai za ta dinga yi sai kuma in ta haihu, sannan abu ɗaya take ci ya zauna a cikinta tuwo shima ɗin gaya, ko kuma in an shanya shi ya bushe sai a daka mata ta dinga cin sa da ƙulii, tuwo ko gaya yana kwana huɗu a firizanta tana cin sa, sannan ba ta son kamshin komai in ta shaƙa ko wani ƙamshi yini za ta yi amai ba zaman lafiya shi ya sa gidanta na nan dum Harira tuni ta daina saka turaran wuta itama Ummu Salmaan ta daina amfani da duk wani nau'in turare abu ɗaya ne ta ke son ƙamshin shi ƙamshin ƙasan anguwan su Ammah shi ake ɗibo mata a leda ta jiƙa shi da ruwa ƙamshin ƙasan take shinshina tana jin daɗi in kasar ta daina ƙamshi ta zubar ko Hamma Saddam ko Hamma Abdulrahim cikin su duk wanda ya samu dama shi ke diɓo mata ya kawo mata da yawa a baƙar leda ta zauna ta jiƙa shi da ruwa to yana gefen ta duk in da za ta zauna ko za ta kwanta tana shaƙa tana jin daɗi ta rage yawan yin miyau amma kuma yana taruwa a bakinta sai dai ba sosai ba.

Ta koma asibiti sau biyu saboda yanayin cikin da ya zo da laulauyi an auna BF ɗin ta sun ce ba matsala. Duk kuma lokacin da za ta je sai sun riƙeta sun ƙara mata ruwa saboda yanayin yaushin jikinta sannan da dokar ta dinga cin abinci tana shan ruwa akai akai, to gwara ruwan tana sha wannan cikin ma mai sanyi yake iya karɓa don sai ya yi ƙanƙara ma take iya sha in ya huce ba za ta iya shan shi ba. Gata nan dai ta tsuge sai hanci wuyanta sai kasusuwa kowa tunanin shi laulayi ne ba su san har da kewar mijinta ba.

Ta azabatu da kalaman bakinta, domin wannan horon ya yi mata nauyi sosai wataƙila yana tare da ita, da ba za ta wahala kamar haka ba. Ta yi magana da Hanan sau wajen uku bayan tafiyar su ta wayar Harira tana da Lambar Hidaya suna magana.
Received at 07:54Reactions: ❤ 9, 🥰 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Hanan ko a jikinta ba ta damu da rashin uwarta ba in dai suka yi magana sai dai ta ce Mahma yaushe za ki zo? A bakinta ta ji cewa Hamma Lamiɗo ya dawo har ya koma. Kenan da gaske yake yi har a yanzu bai gama hucewa da ita ba.
Ba ta damu da Hanan ba ta san za ta samu dukkan kulawa wajen su Anitha.
Bilkisu daman ba ita ke kula da yaran ba, ba su da lambar juna ba waya suke yi ba.

Amma tana da tabbacin Bilkisu murna take yi da rahin dawowarta domin ita daman ba za ta so ta koma ba tunda ba ta son ta da mijinta. Sai dai ta yi hakuri domin tunda ta shiga ba za ta fita ba.
Hidaya na turo ma Harira hotunan su Hanan ta WhatsApp tunda tana yi ga su nan duk sun kara mata girma a idanuwa a cikin wattanin da ba ta gan su ba, ga sabon gida nan fa sun manta sun tsufa a cikin shi.

Shamsiya ko sai da ta daina ɗaukan wayanta in Hanan ne ai ta faɗa mata ba sa tare, amma sai ta dinga damunta da waya. Wata alaja ce ba ta fatan ya sake haɗa su an yi na farko kuma ya zama na ƙarshe kenan har gaban abada. Shi ya sa tana ganin kiran ta ba ta ɗagawa lambar ma ba ta yi saving ba amma da yake tun a baya ta san lambarta shi yasa da ta kira take gane ita ce.

Kwanaki har saƙo ban hakuri ta turo mata wai ta yi hakuri tana damunta ne daman suna son tambayan lafiyan Hanan ne ko amsa Ummu Salma ba ta mayar mata ba ta goge saƙon ba su san da lafiyar Hanan ba sai yanzu? Lafiya ke sa a ji shuru in da ba lafiya da sun ji labari.

Ta kyaleta da damuwar dake damunta. Ga kewar miji ga kewar Baffa. Tana da tabbacin rashin Baffa sai an daɗe kafin ya zame mata jiki gani take yi kamar Baffa zai dawo ta kasa gasgata mutuwarsa, gani take yi kamar zai dawo wata yar tafiya ya yi. Duk da babu abin da ta nema ta rasa kayan abinci ne ga su nan tsibiri guda a store sai kuma cefane duk wata Hamma Abdullahi zai kawo, su kifi su nama duk da ba ta ci sai dai Harira ta ci ko ta saka ta soya ko ta yi ferfesu ta kai ma su Ammah, wacce yanzu karɓa karba suke yi Umma Balki ta koma yanzu Umma A'i ke zaune da ita, suma ɗin babu abin da ba su da shi naman ne kifin ne sai abin da suka ga dama za su ci.

Kuɗi kuma tun wanda Hamma Lamiɗo ya bar mata da zai tafi ko rabi ba ta taɓa ba, sai in Harira za ta je kasuwa ta ba ta sakon kayan marmari da su aya da goriba tana cin su, a asibiti ma likita ya ce ta yawaita shan kayan marmari saboda za su ƙara mata kuzari wani lokacin ta sha ta zauna lafiya wani lokacin kuma ta yini tana amai sai dai godiya kawai.

Kewar mijinta har ya bayyana a idanuwanta da jikinta daurewa kawai take yi. Amma tana buƙatarsa ga shi ya yi mata nisa amma tana ji a jikinta nisan na ɗan lokaci ne koma mene ne ya kusa dawowa zuwa gare ta. Za ta duƙa har kasa ta ba shi hakurin laifinta kuma bakinta ya yi limzami har abada ba za ta ƙara gangancin furta irin waɗanan kalaman ba, ta yi ganganci ta yi kuskure ta yi kuma nadama tun a lokacin sai dai kuma nadamar ne mara amfani.

*
LAGOS.
MARINE ROAD.
THURSDAY, 12:00PM.

Barcin sa ya yi nisa, hasken da ya dinga kashe masa idanuwa shi ya farkar da shi daga nannauyan barcin da ya kwashe shi tun bayan dawowarsa salla asuba.

Kare fuskar shi ya yi da hannun daman shi yana ɗan yamutsa fuska.
Dariyan ta ya ji, daman ya san ita ce.

"Ranka ya daɗe pass 12, ka tashi ka yi wanka mu yi breakfast."

Lumsssun idanuwansa da suka shige ciki saboda barci ya buɗe yana ɗan muskutawa sannan ya ɗan tashi zaune yana jinginar da kansa jikin masagalin gadon da yake kwance. Sannan lokaci ɗaya yana yaye bargon dake jikinsa.

Sanye yake da dogon wando baƙi, amma wandon bai rufe masagalin kafafunsa ba, ana iya ganin ƙaurin kafafunsa ga ƙananun gargasa nan kwance luf a zararan dogayen ƙafafunsa.

"Yara suna ta jiran ka, suma yau tare da Papa za su yi breakfast"

Bilkisu ta sake faɗa lokaci ɗaya tana zama a gefen shi.
Ta ci kwalliya cikin ado mai burgewa na riga da wando yan kanti ta naɗa wani mayafi mai santsi a saman kanta.

In da ta buɗe labulen ya kalla rana ta fito sosai, wajen wani glass ne wanda in ka fita za ka samu wajen shan iska ga kujeru a wajen.

"Good morning Papa."
Received at 07:54Reactions: ❤ 6, 🥰 1

Ta faɗa lokaci ɗaya tana rumgume shi.
Shima sai ya ɗan rumgumota yana amsawa.

"How was your night?

"Am fine."

Ta amsa shi tana masa mirmishi, goshinta ya sumbata ita kuma sai ta sumbaci leɓen shi suna kallon juna cikin mirmishi.
Wanka ya ce zai yi, suka miƙe a tare tana jikinsa tana faɗa masa ta yi kewarsa sosai.

"I'm with you."

Ya amsa mata lokaci ɗaya yana sake sumbatar gefen kumatun ta.
Tambayata yake yi yau ba za ta je asibiti ne ta ce za ta je sai after 1 za ta fita

Sakin ta yi ya wuce tiolet ta bi shi da kallo kamar ta kamo shi ta lashe shi da gaske ta yi kewar sosai. Jiya da yamma ya dawo a gajiye yake shi ya sa daga ita har yaran bai wani zauna da su ba da wuri ma ya kwanta a bangaren shi ita kuma sai ta bar shi ya huta ta koma bangaren ta, ta kwana da safe ma daya ya dawo masallaci barcin ya koma.

Yanzu ma ganin sha biyu ta gota shi ya sa ta zo ta she shi. Ta san in har aka yi azahar zai yi mata faɗan me ya sa ba ta tashe shi ba. Lamido zai iya asaran komai bai damu ba amma ban da asaran salla a cikin jam'i.

Bargon ta ɗan janye tana gyaran gadon, baya so su Hidaya na shigar masa bangaren shi tun suna ma wancan gida ba wannan ba. Shi yasa in dai yana nan za ta ɗan gyara amma fa in baya nan Hidayar ke gyarawa ba za ta iya ba.
Bayan ta ɗan ninke bargo ta ajiyesa a gefen gado ita ta koma ta zauna wayarsa dake saman side drower ta ɗauka wayarsa babu tsaro shi ya sa ta samu damar duba abin da take nema.

Kwata'kwata babu sunan Umma Salma a call long ɗin shi. Ta duba bangaren sakonni ba ta ga wani sabon sako ba tun wanda ta gani ne wancan dawowar da ya yi ne anan ne ta tabbatar da zarginta wani laifi ne mai girma Ummu Salma ta aikata masa, zuciyarta ta yi mata tsalle lokacin da ta ga saƙon Ummu Salma na ya sake ta ranar dakyar ta iya barci saboda farinciki ta fara zargin ya yi sakin amma ba tare da kowa ya sani ba ko kuma an sani an rufe maganar ne saboda ba al'adar gidan Sarauta ba ne sakin mata.

Tun wancan dawowar ta bincike wayar nan tas, nan ta gano rikita shin Umma Salma ke yi a baya da hotuna da videos tare da chart na kalaman soyayya ai dole ya rikice akanta amma ta duba date wajen wata biyu kenan ba su ƙara magana da juna ba, ba waya ba saƙo kenan zarginta ya zama gaskiya.

Saurin ijiye masa wayar ta yi tana ɗan yarfa hannuwanta sama alamun murna, Allah ya ga zuciyarta ya kawo mata masalaha a cikin sauƙi, duk a wancan dawowar na shi ma ta yi ta dukan ruwan ciknsa ta ji wani magana game da Umma Salman bai faɗa mata ba daman ta san ba zai taɓa faɗa ba.

Miƙewa ta yi, tana juyi a cikin bedroom ɗinsa mai kama da ɗakin turawa komai cikn tsari. Wannan gidan ya fi wancan girma sai biyu ma.

Ga dai shashen Umma Salma can a rufe amma ba za ta dawo mata gida ba. Tunda suka dawo ta yi sallama da damuwa da tashin hankali ta mayar da jikinta kamar ba ita ba. Ganin Umma Salma kawai a gidan ta, tana giftawa barazana ne ga zaman lafiyanta amma yanzu ita shar, Hanan ce kawai ta rage kuma Ya Hadiza ta ce ta ƙyaleta kawai me yarinya ta sani? Ba ma haka ba Lamiɗo ba zai taɓa yarda ya mayar da Hanan ba duk da a surutun yarinyar ta ji tana faɗin Abba da Anty sai ta yi tunanin wataƙila yarinyar ta haɗu da ubanta na gaskiya ne sai ta kira Ammah daman tana kiran ta bayan ko wani kwana biyu suna gaisawa shi ne ta ɗan kawo mata zencen Hanan ɗin nan ko Ammah ta kwashe komai ta faɗa mata amma ba ta faɗa mata hatsaniyar da Umma Salma ta yi ba nan ta tabbatar da wataƙila nan gaba kaɗan Hanan ɗin ma za ta bar mata gidanta da mijinta da yaranta ta koma gidan su. Saboda son jin kwaf irin na Bilkisu har tambayan Ammah take yi ya wajen su Ummu Salma? Sai Ammah ta ce suna lafiya lau da yake Ammah na da kunyar fulani, ba ta faɗa mata zencen cikin Umma Salma ba, ballatana ta ji labarin cikin sai kawai ta cigaba da zama cikin yaƙinin ta cewa Lamiɗo ya saki Umma Salma ba, ko a can Masarauta Ya Hadiza ta ce ba ta ji wani labari ba kenan suna ɓoyewa ne aamma duka alamomin sun tabbatar da wani abu ya faru.
Received at 07:54Reactions: ❤ 6, 👍 1, 🤗 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Duk da ta fahimci su Sultan sun shaƙu da Hanan ɗin ba ma su har Lamiɗon da su Hidaya kowa Hanan saboda kazar kazar ɗinta kuma zamanta a tare da Beena ya sake saka ma Beena himma sosai, ba ita ke kula da yaran ba amma dai tana duba su lokaci bayan lokaci ta fahimci Hanan tana da ƙokari kuma sannan bayan dawowarsu an yi Parents day ta je musu anan ne headteacher ɗin su Hanan ta ke cewa yarinyar na da ƙokari suna tunanin yi mata jumping zuwa nursery 2 ajin su Beena ta ce a barta a in da take ba ta so daga zuwan yarinya ta zo ta fi yaranta ƙokari shi ya sa ta faɗa ma Anitha ta dake ma da Beena ta daina wasa da karatu ba ta son a fita sannan ba ta son a fi yaranta gwara ma Sultan shi ba ta jinsa. Amma Hanan irin masu kaifin kwaƙwalwar nan ne sau daya za a yi mata karatu ta ɗauke shi ko a Qur'ani duk ta iya ƙananun surorin nan ga shi ta iya salla ta iya azkar ta ce Mami ta koya mata daman ai Mami ba ta da wasa.

Har Safina matar Kabiru Bilkisu ta kira ta ji ko da gasken Lamiɗo ya saki Umma Salma amma ba ta ji wata magana ba. Ba saba waya suka yi ba shiya sa suna gama gaisawa da tambayan yara suka yi shuru Bilkisu kuma ego ɗin ta ya hana ta tambaya dole suka yi sallama.
Murna kawai take yi farinciki ya cikata.

Tana nan tsaye har ya fito daga tiolet sanye da rigar wanka.
Ta juya tana kallon shi cikin wani shauƙi, Ummu Salma ta zo ta yi mata aiki kuma ta tafi ta bar mata mijinta da gidanta. Ta yi mata aikin dawo da Lamiɗo irin yadda take so, Lamiɗon da ba zai sanya wani hijabi a tsakaninsu ba.

In a baya ne ba zai taɓa tsayawa a gabanta kirjinsa a buɗe ba sai ga shi yanzu komai ya sauya.
Har wanka suna yi tare su kwanta fatar jikinsu na gogan na juna.

Yanzu ɗin ma ita ta shafa masa lotion ta yi masa cumbing ɗin gashin kansa sannan ya shiga clotset ya zaɓo riga da wando, wando baki ne amma rigar milk colour ce duk ita ta siya masa, ganin yanzu ya daina zaɓan kalololi, itama ta zage in dai ta fita Shopping sai ta siya masa jin daɗin ta kuma yana saka kayan.

Tare suka fito daga bangaren na shi suna masu rike da hannun juna. Har zuwa main falon, wani babban falo mai ɗauke da saitin kujeru wajen uku a falon.
Sannan ga wata faskekiyar plasma mai kama da bango guda in kana kallo kamar mutane za su fito tsabar girma.

Duka bangaren suna jikin juna ne, falt ne suna haɗe ne a waje ɗaya. Saboda Lamiɗo ba ya so na wanda ke rabe, wani ma za ka ga sai an samu tazara tsakanin wannan shashen da wannan amma shi ya fi son mai gabaɗaya.

Bangaren Bilkisu ne a farko mai falo da bedroom uku da kitchen amma kafin bangarenta akwai korido da ƙofa da ya raba tsakanin bangarenta da na maigidan.
Sai na Lamiɗo mai falo da bedroom 2, shima kafin na Umma Salma akwai dogon korido da ƙofa mai falo da 3 bedroom sai kitchen

Please Login or Register in order to submit comment