Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mirmishi kawai suke yi na farinciki.

"Ina ga nima zan yi auren nan."

Hamma Saddam ya faɗa yana kallon su yana mirmishi sai a lokacin kunya ta kama Umma Salma ganin yadda aka zura musu idanuwa sai ta sunne kanta a jikin kafafun Hamma Lamiɗo tana dariya.

"Auta da gulma sai yanzu ne kika san kina jin kunyar mu?
Received at 08:42Reactions: ❤ 8, 👍 2, 🥰 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Hamma Jibo ya faɗa yana dariya ai sai ta tashi da gudu ta bar falon ta bar Hamma Lamiɗo na faɗin ta bi a sannu.
Kallon shi kawai suke yi suna ganin sabon mutum

"Lamiɗo ka canza fa da gaske."

Hamma Jibo ya faɗa yana dariya

"Ƙanwar ka ce ta susuta shi fa."

Hamma Mustpha ya ba shi amsa suna ta dariya. Shi dai kawai mimishi yake yi bai yi magana ba shi kuma daman Hamma Abdulrahim tunda aka yi maganar Baɗɗo ya ɗauke wuta.

Ranar gidan ya yini cikin farinciki da yamma su Adda Suwaiba suka zo tare da kawo abinci. Ummu Salma ce kawai ta saka Harira ta dafa mata dankalin hausa da ta ga su Ammah na da shi ta ci gaya ya yi mata daɗi sosai.

Ranar gida Ummu Salma ta koma tunda a wajen ta Hamma Lamiɗo zai kwana ta yi ta yi ya barta ya ce Nahi da yaren indiyanci kuma babu abin da ya shiga tsakaninsu sun dai yi hiran su na ma'aurata sannan suka kwanta manne da juna.

Washegari su Hamma Jibo duk suka koma har Hamma Kabiru. Su Baffa Umaru sun koma tun safe tare da Umma A'i, Umma Balki za ta zauna har Umma A'i ta je gida ta dawo nan da sati biyu.
Mami kuma sai jibi za ta koma su Umma Salma kuma gobe da safe.

Ummu Salma ba ta yi ma Baɗɗo maganar Abdulrahim ba amma ta yi ƙudiri niyyar za ta yi ta yi ma Abdulrahim maganar har sai ya ji ya amince tunda ba dole Ammah ta yi masa ba.

Saboda shi ma ta zo gidan da wuri amma baya nan yana wajen aiki.
Sai yamma ya dawo ta bi shi har bangaren su tana sake yi masa maganar ya ce zai yi tunani akan haka.

"Wallahi Hamma Baɗɗo ba ta da matsala, mace ce mai alheri da sanin ya kamata sannan mace ta gari ce abar alfaharin kowa ni namiji."

Shi dai ya ce zai yi nazari sannan zai yi addu'an in zuciyarsa ta kwanta da ita zai amince amma ba wai ya ce Aisha ba ta cancanta ba ne kawai abin ne ya zo masa a baza ta bai taɓa tunanin haka ba. Tunda kuma ya ce zai yi addu'a sai ta ƙyale shi, itama za ta yi addu'an alheri, domin tana son Baɗɗo ta auri ɗaya daga cikin yayyenta saboda alherin Aisha ga rayuwarta.

Har Lamiɗo ta samu da maganar wai cikin hikima ya nuna ma Abdulrahim muhimmamcin wannan zaɓin na Ammah.
Tana kuma faɗa masa shi Abdulrahim ɗin ya ce zai yi nazari sannan zai yi addu'a amma tana ce masa wai ya je ya yi masa magana cikin hikima.

"Ki kwantar da hankalin ki, ba ya ce zai yi nazari da addu'a ba to mu ba shi lokaci."

"Aure fa ya wuce wasa Ummu Salama. Ki bari ya zaɓar ma kansa abin da zai dauwama da shi har abada."

Daƙyar ya lallasheta ta samu natsuwa ganin ta damu kanta.

"Ke ma ki yi addu'a. In Ubangiji ya so za a yi."

Sai ta aminta da shawaransa ta miƙa ma Ubangiji lamarin.
A ranar aka dawo da Hanna ƙanin Habib Maharazu ne ya kawo ta da kayan ciye ciye sannan sun yi mata kayan salla wajen kala huɗu har da kuɗi. Sai murna take yi tana nuna ma su Sultan da yake sun zo gidan lokacin da aka dawo da ita. Sallama suka zo yi ma Ammah.
Washegari kuma suka bi jirgin zuwa Lagos.

Bayan Lamiɗo ya cika store ɗin gidan Ammah da kayan abinci sannan ya bar mata kuɗaɗe masu yawa.
Tana ta saka albarka har tana hawaye.

*

Tunda suka koma gida Ummu Salma take ta addu'an Allah ya sa alheri ne a tsakanin Abdulrahim da Baɗɗo ga shi har a lokacin bai kira ta ba ya ce bai gama nazarin shi ba.

Tana zuwa asibiti tunda har ta fara awo, sosai take kula da lafiyanta, tsakaninta da Bilkisu kuma ba ta canza zani ba. Gwara ma haka kowa ya yi harkan gaban shi tunda kowa da na bangaren shi. Amma dai in sun haɗu Ummu Salma na gaishe ta saboda haƙkin musulunci sun koma Lagos da sati Biyu Lamiɗo baya nan aka yi ma su Bilkisu rasuwa.

Matar Mai martaba ta uku ce Allah ya yi ma rasuwa. Ummu Salma ba ta sani ba a waya ta gani ana ta sawa shi ne ta shiga har bangaren Bilkisun ta yi mata gaisuwa.
Ashe kawai yayarsu dake aure a Turkiya ita ta jira a daran jirgi ya sauke ta a Lagos nan ta kwana Ummu Salma ta je itama har ɗaki ta yi mata sannu da zuwa da gaisuwa tana da fara'a ba kamar Bilkisu ba.
Da safe suka wuce Kano tare.
Ba ta je da yara ba tunda suna da makaranta da Sabuwa kuma kaɗai ta tafi sauran suna gida.
Received at 08:42Reactions: ❤ 9, 👍 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Kuma sai da aka yi bakwai ta dawo, shima har bangarenta Ummu Salma ta bi ta, ta sake yi mata gaisuwa ta amsa. Da Lamiɗo ya dawo ya shirye sun je gaisuwa shi da Bilkisu suka kwana ɗaya a kano suka wuce Daura suka kwana ɗaya sun sake duba Mai martaba tunda jikinsa na shi ya rikice a satin ma za su koma London in da yake ganin likita sauƙin ta ma Saleem ya gama karatu yana gida ne shi ke kula da wasu abubuwan. Ummu Salma ta so ta bi su Lamiɗo ya ce aa saboda yanayinta. Shi fa yanzu taka tsantsan yake yi ba ya so su sake yin wani rashin a karo na biyu.

Allah ya amshi roƙon Ummu Salma, kawai sai ga Baɗɗo ta kira ta tana faɗa mata cewa Hamma Abdulrahim ya zo wajenta da maganar aure.
Ummu Salma ta saka ihun murna.

"Wani amsa kika ba shi?

"Na ce zan yi shawara."

"Dilla banza wani shawara ki amince mu sha biki "

Baɗɗo na dariya ta ce sai ta ja ajinta.

"Ki tsaya garin jan aji, ajin na ki ya tsinke."

Baɗɗo ta ce in ya tsinke shike nan. Ita kanta tana cikin farinciki kuma nan da nan ta ba da kai bori ya hau Saddam ya fito group yana faɗa ma su Hamma Jibo suka ce shikenan suna gama daidaitawa sai maganar aure. A wannan maganar ba wanda yakai Umma Salma farinciki ta gama lissafin abubuwan da za ta yi da bikin Baɗɗo burinta kenan ta rama mata alherin da ta jima tana yi mata.

Abu kamar wasa sai ga magana ta miƙa. Kowa ya sani har can dangin Ummin ikki da dangin mahaifin Baɗɗo. Kowa ya ji sai ya ce tuwona maina. Soyayya ake sha tsakanin Baɗɗo da Hamma Abdulrahim ba sauƙi kamar daman can sun daɗe suna son juna. Sai aka tsayar da maganar cewa in su Hamma Jibo suka zo babbar salla za a yi maganar auren a saka rana a yi bikin cikin lokaci kowa ya huta.

Haka kuma ya faru kaf ɗin su tare da iyalansu a gida suka yi babban salla.
Su Umma Salma kuma kamar yadda aka saba a Daura suka yi salla. Wannan sallar da ta gayyaci Baɗɗo zuwa sai ta ce ba za ta je ba wai in ta tafi ta bar Sweety ɗinta shi kaɗai. Ummu Salma ta saki baki ta kasa magana saboda mamaki.
Baɗɗo kuma na ta dariya.
A wannan salla har Baffa an yi ma layya da fatan Allah ya kai masa ladan kabarinsa aka raba ma maƙota naman gabaɗaya.

Karshenta dai tare da Islam suka tafi Daura salla ta haɗe da su Amira. Hafsat ma ta fara karatu a jami'ar Abuja.
Lokacin cikinta na wattani shi shidda saura kaɗan ya faɗa wattaninsa bakwai an yi scan an ce mace za ta haifa wannan karon.

Da yake ta samu sauƙin laulayi yanzu har girki tana yi lafiya lau. Ta yi ma Mai martaba abinci da kanta ta kai masa har fadar shi na cikin gidaa. Ya zauna ya ci ya saka mata albarka.
Ranar har labarin Mami sai da ya ba ta Batula ikon Allah, yana ba ta labarin darun Mami Ummu Salma na dariya duk kuma abin da ya faɗa gaskiya ne Mami ba ta canza ba. Da za ta tafi ya ba ta kyautar doki ya ce duk ranar da ta shirya ta saka Lamiɗo ya ɗaurata saman doki tana ta masa godiya.

Sai da suka gama salla a Daura sannan suka je Adamawa. A lokacin aka sanya ranar bikin Baɗɗo cikin ikon Allah wata biyu ma su zuwa aka sanya saboda komai yayyensa sun ce za su yi komai su za su haɗa karfi su gyara gida a fitar masa da bangarensa ya fara zama kafin ya mallaki na shi.

Lefe kuma ango ya ce shi zai haɗa abin shi sai dai abin da za a ɗan taimaka masa. Hamma Lamiɗo ya ce zai shiga ciki. Baɗɗo za ta zama amarya nan da wata biyu. Farincikin Ummu Salma ya kasa ɓoyuwa, wannan zuwan ma na su Hanan ta je gidan su Habib ta kwana huɗu sannan suka dawo da ita. Tunda suka koma Umma Salma shirin biki kawai take yi ba ta taɓa kuɗin gadonta ba su akwai abin da za ta yi da su. Kuɗin hannunta dai take ta tanadin bikin Baɗɗo da su.

Kuɗaɗen dake bankinta ta lissafa za su isa ta siya ma Baɗɗo fridge da Tv sai ga shi ma Hamma Lamiɗo ya ba ta miliyan biyu ya ce ta ƙara farinciki kamar za ta suma, Bilkisu ko kamar za ta mutu domin lokacin da ya ce zai ba da guddumuwarsa suna cin abinci ne a saman dinning tana ji tana gani, Ummu Salma na juyi yadda take so Lamiɗo na take mata baya.
Received at 08:42
9 people reacted with ❤
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Miliyan biyun nan duka ta tura ma Baɗɗo ta ce su ƙara wajen siyayya. Ita kuma nata ta ce sai ta zo amma ta ce kar su siya fridge da Tv da gas sai ta zo.
Baɗɗo da iyayenta babu abin da za su ce ma Ammah da ahalinta sai godiya. Ammah ma miliyan ɗaya ta ba ma Ummin ikki, Mami ma 500k abincin da za a ci a duka gidajen kuma su Hamma Jibo suka ɗau nauyin komai.

Lefe kuma rabin shi Hamma Lamiɗo ya saki bakin aljihu Adda Suwaiba ta haɗa akwatina takws shake da kaya sanna tuni an fara gyaran gida An bige ɗakin Baffa an bige kitchen ɗin Ammah an sake sabon tsari.
Itama ɗakin na ta an kashe bedroon ɗinta zai shiga cikin bangaren Baɗdo ita kuma Ammah sai aka haɗe mata da wannan ɗayan ɗakin na waje.

Cikin lokaci aka fitar da flat ɗin Hamma Abdulrahaman mai falo da bedroom biyu da kitchen.
An sake yin wani kitchen a tsakar gida amma Ammah ma an yi mata wani kitchen ɗin a cikin bangarenta.
An sake sabon fenti gida ya dawo kamar sabo fes. Lokacin da bikin ya ƙarato cikin Umma Salma wattani takwas kaɗan ya rage bai shiga watannin tara ba Lamiɗo ma ya fara nema musu Visa, shi da ita da Mami tare da Harira za su tafi can Egypt ɗin tuni har asibitin da Ummu Salma za ta haihu a can Egypt ɗin mai suna EL NADA HOSPITAL CAIRO, EGYPT Lamiɗo ya nemi bayanan su ta goggle. Asibiti ne mai kyau na maternity in da ake bawa mata masu haihuwa kulawa da yaransu asibitin kuɗi ne mai kyau.

Hamma Lamiɗo ne ya yi musu email ya tura musu duka bayanan Ummu Salma da asibitin da take zuwa awo suka rubuta ya riga ya yi musu booking ɗin komai jiran su kawai ake yi.
Amma sai an gama bikin Baɗɗo sannan za su tafi.

Bai kyautu a ce a yi bikin Baɗɗo Ummu Salma ba ta nan ba duk tsaka tsantsan ɗin Hamma Lamiɗo shi kan shi ya sara ma wannan amintar dake tsakanin matarsa da Baɗɗo. Tun ana sauran sati ɗaya ta taho Adamawa tare da Harira. Bilkisu kuma sai ana gobe biki za ta taho tare da yara da Hamma Lamiɗo.

Tunda ta sauka garin ba su zauna ba ita ce babbar ƙawa komai ita ce akan gaba. A can gidansu Baɗɗo ma ta sauka ta ce a can za ta yi bikinta. Hamma Saddam ke ɗawainiya da su a mota a washegarin ranar da ta iso suka je kasuwa ta siya ma Baɗɗo Tv babba da gas cooker mai shidda da frige.
Baɗɗo ta yi hawaye ta rumgume Ummu Salma sai suka kama kukan a tare haka da suka dawo yan'uwan Ummin ikki da su iklima suna sake yaba karamcin Ammah da iyalanta. An yi ankon leshi da atamfa duk da ba biki za a yi sosai ba tunda Baffa ko shekara bai yi da rasuwa ba.

Su Adda Safina tun ana saura kwana huɗu suka iso. Da su ake ta shirye shirye. An kai lefe tun wuri saboda Amarya ta samu bayar da ɗinkuna.
Sun yi gayya amma daga maƙota sai yan'uwa kawai gidan Ammah ma cike da mutanen Mubi ango kuma abokansa sun zo har da waɗanda suka yi karatu daga kasar waje ya sauke su a hotel. Ummu Salma ta kira Shamsiya ta gayyaceta ta yi mata alƙawarin za su zo.

Ranar Jumma'a, da yamma Hamma Lamiɗo da Bilkisu da yara suka iso tare da su Sabuwa. Ummu Salma bata ma gidan suna wajen saloon ita da Baɗdo da su Kaltume.

Sai da suka dawo suka sauka a gidan Amarya kuma ta wuce gida.
Ummu Salma ta yi ƙunshi ja ta yi kyau ga cikinta da ya girma sai ya sakata ta wani fashewa ta yi kiba.
Lamiɗo in bai samu zuwa ɗaurin anan ba sai Ummu Salma sai yi fushi da shi, da ya ce ba zai samu zuwa ba ta fara rigima.

Dole ya samu lokaci, sai kuma ya ci sa'a a satin ya dawo yana da cikakken lokaci. Shi dai faɗan shi Umma Salma ta bi a hankali har a samu matsala ta ce masa tana kula da kanta.
Bilkisu tana gefe tana kallon kowa ɗaya ɗaya.
Amma takaici da kishi sun hanata farinciki ganin yadda Ummu Salma ta zama tauraruwa.

Mami ta iso tare da su Islam har da Barira. Hanan na ganinta ta maƙale mata.
Washegari Asabar 25 ga watan october aka ɗaura auran Aisha Salisu da Dr Abdulrahim Hadi Baba, Baffa Umaru shine waliyin ango kamar yadda aka saba Baɗɗo kuma kanin mahafinta ne.

Ɗaurin auren ya samu hallata mutane dabam dabam ciki har da Waziri da shamaki da suka wakilci Mai martaba. Mata kuma Gimbiya Shahida ce ta zo da Gimbiya Amratu sai Hajiya Zaliha
A ƙofar gidan su Baɗɗo aka ɗaura auren.
Received at 08:42Reactions: ❤ 7, 🔥 1, 🤗 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Bayan an ɗaura ango da abokansa suka shiga cikin gida aka yi hotuna da Amarya sannan suka tafi can gidan Ango.
Ummu Salma ma Hamma Saddam ne ya zo ya ɗauketa za su ɗau hoton tarihi gabaɗayan su.

Sun ɗauka gabaɗaya yaran har da Lamiɗo da Mami.
Ummu Salma kusa da mijinta har tana kwantar da kanta a saman kafaɗarsa.
Tana mirmishi Bilkisu ta kasa tsayawa a wajen saboda kishi. Ga shi Ummu Salma ta yi kyau ta saka wani farin leshi kamar ita ce amaryan.

Duk in ta bi ta zama abin kallo. Ga Harira na biye da ita kamar jela. Gidan su Baɗɗo ta koma domin ta ce ita can take bikinta sai sun kawo Amarya.
Shamsiya ta cika alƙawari ta zo tare da Habiba dake ta taunan cigham tana wani kallon kowa ɗaya bayan ɗaya. Shamsiya ta san gidansu Baɗɗo shi ya sa ba su wahala ba duk da an sami canje-canje amma gidan su Baɗɗo ba zai ɓace mata ba.


Baɗɗo ma duk da haushin Shamsiya da take ji ta sakar mata fuska. Ummu Salma ta karrama su an ba su abinci da abin sha da za su tafi an ba su abin raba wa sannan Shamsiyar ta ce ma Ummu Salma za su je su gaida Ammah a can gida daga nan suka yi sallama suna fita gidan Ammah suka je Shamsiya ta yi mata Allah ya sanya alheri.

Har suka ga Hanan ta sha gayu da leshi iri ɗaya da na Beena da Ummu Salma
Tana ganinta ta ganeta ta nufeta tana cewa Anty.
Habiba daman ba saninta ta yi amma ita kanta yarinyar sha'awa take bata to ba ta san talauci ba. Ta taso cikin gata yarinya ƙarama ga turanci ga larabci a bakinta.

Sun fito har haraba tare da Hanan tana ganin su Lamiɗo ta saki hannun Shamsiya ta nufe shi tana kiran Papa.
Da Shamsiya ta gan shi ko ba a faɗa mata ba ta san shi ne mijin Salma ballatana ta san shi a hoton tun a wancan lokacin da suke ƙawance da Ummu Salma.

Ƙwarjininsa ya sa har Habiba sai da ta gaishe shi ya amsa sau ɗaya domin Hanan ta faɗa masa Anty ne, kuma a kaf a danginsu bai san su ba shi ya sa ya fahimci ko su waye sau ɗaya ya amsa ya yi wucewarsa wajan su Hamma Kabiru dake zaune saman darduma a haraban gidan suna hira.

Sum sum Shamsiya da Habiba suka bar gida.
Shamsiya ta sake samun tabbacin Ummu Salma ta yi ma rayuwarsu nisa har abada. Haka ta je ta ba ma Habib labarin mijin Ummu Salma.

"Ke wannan mijin miji ne, nima wataƙila rabon Hanan ne ya sa muka yi aure amma in ana maganar mazaje irin su Lamiɗo na layi mu ba mu isa ma mu zo wajen ba."

Habib ya ba ta amsa yana jinjina kai.
Har gobe yana son Umma Salma, amma yana ƙokarin cire ta daga zuciyarsa ya tabbata yau ko mutuwa Lamiɗo ya yi Ummu Salma tafi ƙarfin shi har gaban abada.








*Janafty*
Received at 08:42Reactions: ❤ 8, 😁 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
*FJ littafin kuɗi ne 1k a manhajar Telegram tura kuɗin karatu ta wannan acct ɗin 9069067488 Opay Jamila Umar shaidar biya ko tuntuɓa ta waɗannan lambobin.*
08032773332
09069067488.

Bayan sallar isha'i da misalin karfe takwas na dare abokan Hamma Abdulrahim suka zo ɗaukan Amarya.
Har da su Hamma Abdullahi da Hamma Abdulrrahaman a cikin su.

An kai Baɗɗo wajen dangin mahaifinta sun yi mata nasiha, sannan Ummin ikki ma ta yi mata.
Da cewa in da za ta je ba baƙon ta ba ne, Ammah ba uwar miji ba ce uwa ce a gare ta. Ta yi biyayya iya iyawarta domin bautar aure ne ya kaita. In ta ji ko da sau ɗaya ta yi ma Ammah wani kallo ba ta yafe mata ba.

Baɗɗo ta sha kukan rabuwa da gida, Ummu Salma na gefenta duk da ta gaji ciwon kai na damunta kafafunta suna ta ciwo amma ba ta bar gefen Baɗɗo a matsayin ta na babbar ƙawa kuma ƴar'uwa ba duk da akwai wasu ƙawayen ƴa'ƴan yan'uwan Ummin ikki daga Mubi da wasu yanmata a dangin babansu Baɗɗo.

Ga kuma maƙota har da mai yi ma Ummu Salma kitso Maijida da Bilkisu ke yi mata ƙunshi in tana gari.
Sannan akwai yan makarantar su Baɗɗo da suka yi karatu tare, duk sun zo kuma sun yi mata kara sosai.

An kawo motoci masu yawa shi ya sa kowa ya tafi. Ammah aka damƙa ma Amarya tare da cewa daman ɗiyar ta ce dawo mata da ita kawai suka yi. Ammah ta ce ta karɓa ta yi kuma alƙwarin zama da Baɗɗo ba a matsayin suruka ba, sai a matsayin ɗiya a gare ta. Aka yi addu'a da fatan alheri sun ba ma Ammah turmin atamfa na uwar miji da botikan cincin da dublan na Ammah da danginta daman kuma an riga an yi jere Ammah da kanta ta shigar da Amarya har kan gadonta bayan ta yi addu'an da ko wata amarya ke yi a lokacin da za ta shiga ɗakin auren ta.

Ɗaki ya yi kyau sosai sai fatan alheri kawai mutane ke yi da fatan zaman lafiya. Gado biyu aka yi mata kuma masu kyau da quality. Mutane suna gama ganin ɗaki bayan sun ci abinci tunda su Adda Suwaiba sun yi abinci mai rai da lafiya na tarban Amarya, suka yi fatan alheri duk aka mayar da su gida.

Baɗɗo kawai aka bari sai Umma Salma dake tare da ita, sai wata ɗiyar yayar Ummin ikki Mubeena sai Islam su kaɗai a tare da Baɗɗon. Nan suka kwana tare da ita tunda ba kowa a wajenta.
Ummu Salma ta yi waya da Hamma Lamiɗo shi gida suka kwana tare da Bilkisu da yara har da Hanan ita kuma sai ta tsaya a wajen Amarya.

Da safe kuma aka yi musu abin ƙaryawa mai rai da lafiya aikin su Adda Suwaiba ne. Suka kuma shigo dukkansu suna ta tsokanar Baɗɗo.
Sai dai ta sunkuyar da kanta ta kasa magana bakinta ya mutu Ummu Salma ce ke tare mata.

A ranar lahadin ma an yi biki sosai a gidan Ammah tunda an kawo Amarya. Shagali sai ya dawo sabo gida ya sake cika aka ci aka sha' babu abin da babu nama da naman kaza ko har ana ragewa a saman abinci Alhamdulillah kawai Ammah za ta ce, daga Masarautar Daura ma kuɗi ne masu yawa daga Mai martaba da Fulani, a ranar su Gimbiya Shahida suka koma ba su kwana ba.
biki ne na yan gayu na masu kuɗi ba a yi wani shagali ba sosai saboda mutuwar Baffa amma dai an haɗu an yi zumunci an yi wasa an yi dariya.

A ranar ma sun  sake yin hoto gabaɗayansu har da surukai da jikoki Baffa ne kaɗai ba shi a cikin wannan hoton an yi na tarihi ne domin sai a daɗe ba a sake haɗuwa ba ballatana a yi hoton. Har da Bilkisu tunda itama ai surukar gidan ce.

Zuwa dare gida ya watse sai bakin nesa da ba su koma ba.
Adda Suwaiba da Adda Ummu Sulaim sun koma gidajensu da yaran su. Adda Nauwara ne da Adda Aisha sai Adda Safina ke gidan. Sai Ummu Salma da su Islam da su Mami tare da su Umma Balki har da Bilkisu da sauran yaran.

Ummu Salma da Islam tare da su Adda Safina suna bangaren Amarya suna ɗan yi mata gyare gyare tunda yau ango zai shigo ɗaki.
Su Mami ne ke can falon Ammah suna ta hiran su, da Bilkisu da ta hakimce cikin manya ana magana tana kallon bakin kowa ɗaya bayan ɗaya.

Ummu Salma na zaune saboda ba za ta iya wani aiki ba, jikinta ciwo yake yi ga bayanta. Sannan kafafunta sun tasa aikin ma su Harira ne, ita ke shara Hidaya na mopping Sabuwa na tare da Bilkisu. Daman su Anitha suna can Lagos aka bar su tare da su James suna tsaron gida.
Received at 08:43Reactions: ❤ 7, 👏 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Adda Safina na ta yi ma Baɗɗo shaƙiyanci da cewa Amarya ta ango yau dai Abdulrahim zai shiga ɗakin Amarya.

"Ko kunya haka zai wuce bangaren Ammah ya shigo nan ko?

In ji Adda Nauwara aka kwashe da dariya.
Adda Safina na faɗin ga Abdulrahim da kunya dama Saddam ne mai ido a tsakar ka, ita dai Baɗɗo ba ta magana sai dai mirmishi.
Ummu Salma na gefenta ita ce ke shigar mata.
Baɗɗo kafafun Ummun Salma ta kalla da ta miƙar da su a saman cafet ɗin dake falon. Ta ga yadda suka kumbura suna sheƙi.

"Kafafun ki sun kumbura fa Sisna?

Ta faɗa tana kallon Ummu Salma.

"Zirga zirga ne ya sa suka ɗan haye sosai"

"Ko jinin ki ya hau ne?

"E ya ɗan hau zuwa asibitin da na yi na ƙarshe likita ya ce jinina ya ɗan yi sama."

"Allah ya sauwake. Ubangiji ya raba lafiya, yaushe ne tafiyar ta ku?

"Visa muke jira, tana fitowa za mu tafi."

"Allah ya kai ku lafiya. Allah ya sa a rabu lafiya cikin Aminci."

Ummu Salma ta amsa da Amin Amin.
Sai da suka gyara mata ko'ina suka turara shi da turaran ƙamshi ko'ina ya yi ƙal gwanin sha'awa.
Sallama suka yi ma Baɗɗo suka koma bangaren Ammah tunda ga tashin muryoyin maza nan a can bangaren.
Baɗɗo ta roƙi Ummu Salma ta zauna da ita kafin Hamma Abdulrahim ya shigo.

"Na gaji Sisna, zan je na yi wanka  ga Islam ta zauna

Please Login or Register in order to submit comment