Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaji ko?

Nan ma bai amsa mata ba.

"Na yi kewar ka Hamma "

Ta faɗa cikin shagwaɓa, kuma da gaske ya ji kewar shi a muryanta da ya kalleta sai ya ga idanuwanta har sun fara tara kwalla yana kallon fuskarta yana mai nacin kallonta kamar ya daɗe bai ganta ba yana jin zuciyarsa na warwarewa a kanta.

"Da gaske na yi kewar ka."

Ta sake faɗa tana lamgwaɓe masa kamar wata karamar yarinya.

"Yanzu bana ganin ka sosai, ka zama na mutane ba na Ummu Salma ita kaɗai ba."

Ta gama fada tana masa fari, sai da ta kusa saka shi dariya ya yi maza ya kame Hattara dai Sarki ne fa.

Mug ɗin hannun shi ya ajiye a saman teburin dake gaban shi na tangaran.
Ta janyo jikinta zuwa wajen kafafunsa ta kama da duka hannuwanta ta rumgume a ƙirjinta

"Yaushe rabon da mu yi hira! Hammaaaaa"

Ta ja sautin sunan sai da ya ji a zuciyarsa jikinsa ya ɗau ɗumi ta saka kanta a tsakanin kafafunsa kamar wata yarinya.

"Har na fara rama saboda rashin ka."

Ta gama faɗa tana sake tusa kanta a tsakanin kafafunsa nenan ta birkita shi take yi, ya yi saurin matse kafafunsa ya saka hannu ya jawo kanta sai kawai ta ɗora kan a saman kafafunshi tana sauke masa ajiyar zuciya.

"Hamma."

Ya ƙi magana ta sake kiran shi.

"Hamma na."
Nan ma ya yi mata shuru kawai.

Ta ɗago tana kallon shi ya  ɗauke kansa sama yana wani ginshiƙa.

"Hammaaaaaaaaaa."

Ta ja sautin sosai sai da ya kalleta bai shirya ba.
Sai kawai ta tashi ta haye saman cinyarsa ta yi ɗare dare

"Hamma."

Ta sake kiran shi tana tallabo fuskar shi, suna kallon juna cikin idanuwansa.

"Hamma"

"Ummu Salama."

Ya kira sunanta cikin ƙosawa.

"Ni dai ka amsa."

"Me?

"Hamma na."

Sai da ya ɗan juya bakin shi yana so ya yi dariya cikin zuciyarsa ya na jin salama.

"Na'am"

"Shike nan?

Ya faɗa yana kafe ta da idanuwana, sai ta yi masa mirmishi ta sumbaci bakin shi.

"Ba ka yi kewata ba ne?

"A'a."

Ya bata amsa kai tsaye ta kalle shi ta yi masa narai narai kamar za ta yi kuka.

"Ni ko?

"Ba komai to."

Ta gama faɗa tana ƙokarin sauka daga kafafunsa ya sanya hannu ya jawo ta, ta faɗo saman ƙirjinsa ya rumgumeta da tattausan hannayensa zuwa faffaɗan kirjinsa a tare suka sauke numfashi, kowa na jin zuciyarsa na ɗaukan ɗumi na rashin ɗan uwansa sun jima a haka suna jin bugun zuciyoyin junan su.

"Hamma."

"Uhm."

"Ina son ka."

Sai ya yi shuru kafin ya ɗan gyara kafafunsa.
"Kin daina sona yanzu?

Da sauri ta kalle shi

"In ji waye?

"In ji ni."

Ya amsa mata kai tsaye.

"Tunda na zama Sarki. Kin fara guduna."

Ya faɗa yana kafeta da idanuwana ta zaro idanuwana tana kallon shi.

"Yes"

Ya faɗa yana kara haɗe rai, har yana wani ɗauke kansa

"Yaushe ne na guje ka?

"Ba ga shi nan ba kin taɓa zuwa kin kwana a waje na tunda kika zo?

Ya tambayeta yana kafe ta da idanuwansa masu sanyata kasala da mutuwar jiki.

"Au wai daman shi ne kake magana."

Ta faɗa tana rufe baki, ya balla mata harara amma bai yi mgana ba ta kwashe masa da dariya sai ya yi fuska bai sake kallonta ba.
Ta rumgume shi tana faɗin" Hamma ma ina sonka abadan abadan har ƙarshen numfashina."

"Sweet mouth."

Ya faɗa yana ƙokarin cire ta daga jikinsa.

"Zo ki tafi,."

Ya faɗa a hankali ta maƙake masa yana so ya ɗago ta tana ƙara ƙamƙamesa.
Sai ya ƙyaleta sai don kanta ta sake shi tana shafa sajen shi.

"Ranka ya daɗe."

Ya ƙura mata idanuwana zaman ta a saman jikinsa har wani kasala ya sakar masa.
Ta kama hannuwansa ta damƙe a cikin na ta.

"Hamma."

"Saura kwana biyu na yi arba'in."

Bai tambaya ba amma yanayin kallon da yake yi mata na neman ƙarin bayani ne.

"Kasan in mace ta haihu a al'ada sai a ce sai ta yi arba'in sai ta koma ma miji, balle ni tunda ga Anty Balki shi ya sa ka ga ba na zuwa amma ba gudunka nake yi ba."

"To mene ne?

Ya tambaya yana kallonta.

"Ba ka gane ba?
Ta tambaye shi tana kallon shi.

"Ai ba umarnin Allah ba ne"

Ya ba ta amsa kai tsaye.

"Ke da al'ada kuke rayuwar aure ba addini ba?
Received at 19:42
12 people reacted with ❤
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
"Wa ya ce sai an yi kwana arba'in?

"Haka fa ake yi, ko su Ammah da Mami duk haka suka yi."

Ta ba shi amsa tana masa shagwaɓa.

"Ba dai Ammah na ba, da na zama ɗan gata da ace zan samu rabin abin da Ammah take yi ma Baffa."

Kai tsaye ya yi maganarsa ta saki baki tana kallon shi.

"Ammah is a good wife. Ba ta taɓa barin kusa da Baffa ba. Da a ce Ammah ce ta riga Baffa rasuwa da har abada ba zai samu kamarta ba."

"Hamma."

Ta kira sunan shi.

"Ba wani Hamma, ba haka Ammah ke yi ba sai dai in Mamin ki."

Ya gama faɗa yana wani daƙuna fuska, dariya ta so kamata ganin ba wasa ya sa ta danne dariyanta.

"To na ga ina jinin haihuwa ne fa ga kuma ga Banafsha"

"To me zan miki? Ummu Salma kawai na ganki a kusa da ni a feel safe "

Yadda ya yi maganar daga ƙarƙashin zuciyarsa ne sai da jikinta ya yi sanyi.

"Sorry."

"Ka yi haƙuri."

"Kuma ba ki faɗa mini ba, kawai ba kya zuwa wajena."

"Kin kyauta?

"Ban kyauta ba."

Ta yi saurin amsa mishi tana wani lamgwabe kanta.

"Ban kyauta ba, ba zan ƙara ba."

Ya yi mata shuru, yana kokarin cewa ta ɗaga shi, ta zo ta tafi dare ya yi.

"Anan zan kwana."

"A'a ni bana so."

Ya amsa mata ba wasa a maganarsa.

Ya miƙe tsaye tare da ita, ya juya ya ɗauko mata Banafsha, ya miƙa mata ta karɓa tana kallon shi.

"Hamma."

"Na ce fa ka yi haƙuri."

"Na haƙura"

"Ki bari sai kin yi arba'in."

Ya sake jadadda mata, kuma tunda ya furta ba zai sauya magana ba, sai kawai ta juya ta wuce ya bi bayanta har bakin bangaren shi sannan ya ba ma dogarawan dake gadin bangaren shi umarnin su yi mata rakiyar har sai ta shiga bangarenta suka amsa masa da girmamawa.

Sai da ta shiga bangarenta sannan suka koma, ta damu da fushin Hamman nata, da ta koma kafin ta kwanta sai da ta tura masa saƙon ban hakuri bai ba ta amsa ba a chart ma ta ga yana online ta yi masa saƙo bai buɗe ba sai ta ƙyale shi. Kuskurenta ɗaya da ba ta faɗa masa ba, ita ina ta san bai sani ba amma abin da ya ba ta mamaki Bilkisu ba ta zuwa ne? Ta so ta tambaye shi, sanin ba zai amsa mata ba shi yasa ba ta tambaya ba, sanin halin shi ba ya tattauna duk abin da ya shafi Bilkisu da ita, itama ba ta damu da ta sani ba, gwara haka kowa ya tsaya iya matsayinsa.

Washegari da wuri suka yi wanka tare da su Banafsha suka je masa gaisuwan safe kafin ma ya fita Fada yaran suna nan sai sabuwar shekara za a sanya su a makaranta. Ko a fuska bai nuna mata yana fushi da ita ba. Itama ba ta nuna masa komai ba ta so dai su keɓe amma yaran ne suka hana, kuma zai fita Fada ba su samu lokacin keɓewar ba.

Sai ta bar shi a tunda gobe za ta yi arba'in jibi sai ta shirya masa tarba yadda za ta wanke kanta. Duk da ya ce ba komai ta san yana fushi da ita fushin nan na shi mai shiga jiki yana illata mutum bai sani ba. Ranar da ta yi arba'in da kanta ta jagoranci girke girken da aka yi, tana so za ta je gaishe da Mai martaba da Fulani shi yasa ta yi abinci daman ta ce ita za ta dinga yi ma Mai martaba girki duk ranar girkinta da kanta a kitchen ɗin bangarenta.
Saƙo ta tura ma Mai martaba na fitan da za ta yi ya amsa mata da Allah ya tsare.

Su Beena ma suka ce za su je ta ce su je a shirya su, ita da Harira ne da Asabe sai wata Hadima Habi, motoci biyu suka yi amfani da su akwai sau dogarai guda biyu sai masu kaki guda biyu, duk da ba nisa za su yi ba umarnin Sarki ne su yi mata rakiya.

Abinci kala uku ta yi, tuwon shinkafa miyar agushi da naman ganda sai farar shinkafa da miyar kaza, sai dambun couscous, na zogale mai hanta sai lemun kankana da ayaba, sai zoɓo mai sanyi booth sai da ya cika da manyan kololin alfarma.

Sai dai suka gansu kwatsam tunda Ummu Salma ba ta sanar suna tafe ba.
Mai martaba mai murabus ya ji daɗin ganin su, sai Ummu Salma ta ga ya yi kiɓa ya samu hutu sosai sai dai farin gashi duk ya mamaye masa fuska. Ya ce ya ji daɗin ganinta ga shi ta zo da yaran gabaɗaya ta kawo masa Batula da ta yi kiba tana da wuntsila kafafunta ta samu ruwan nono sannan ga madaran yara. Fulani ma ta yi ta saka albarka, a gidan suka yini har yamma.
Received at 19:42Reactions: ❤ 13, 👍 1
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Gimbiya Shahida da Gimbiya Amaratu ne daman iyayen ɗakin Ummu Salma Gimbiya Hadiza da Maimanatu sama sama ne, Hafsat ta koma makaranta Amir ne kawai da Amira a gidan.

Da za su tafi haka Mai martaba ya ba ta farar takarda cike da kuɗi ita da Banafsha tare da yaran gabaɗaya haka ma Fulani Ummu Salma ta rasa ma ina za ta kai kuɗaɗe kamar ma sun yi mata yawa ga uban na sunan da ta samu ba ta ko kirga ba kuɗi ne ba kaɗan ba suna cikin kwandon da aka tara su a cikin bedroom ɗinta ba ta bi ta kansu ba ma.

In ta zauna tana duba rayuwarta tun daga farko har matakin yau sai ta yi hawaye. Ba ta taɓa tunanin rayuwa za ta juya mata haka ba. Yau ita ce a matsayin matar sarkin a gidan Sarauta na Daura a matsayin Sarauniyar Daurama. Yau ita ce a matsayin matar Hamma kuma wai sun haihu tare sai ta yi ta mamaki, tana jinjina ma ikon Allah, ta juya ta ga irin daula da ni'imar da take ciki sai ta yi hamdala. Ta tuna da Baffa ta yi hawaye tana nema masa gafara Baffa ya sha faɗa mata ta kwantar da hankalinta Lamiɗo zai zame mata mjjin marainiya ga shi kuma ya zama amma Baffa ba shi da rai ballatana ya ga wannan daular da kuma cigaban rayuwar da ya same ta, har abada ba za ta manta da rashin Baffa ba.

A baya tana ganin kamar in tunda ta rasa Habib ta rasa komai tana ganin ba za ta samu madadinsa ba. Haka ma Shamsiya ta taɓa faɗa mata a wancan lokacin ta tabbata yanzu da ta zo ta ga yadda rayuwarta ta koma za ta karyata kanta da kanta. Ƙwata ƙwata ta ma manta ba ta kira ta yi musu bangajiya ba, a daran suka sake mgana da Baɗdo tana faɗa mata ta rasa ina za ta zuba kuɗaɗen nan da ta samu.

"Ki kai su a ɗura su a cikin banki ya fi sirri."

"To wa zai kai min! Kin san dai nan ba Jimeta ba ne, Hamma ba zai bar ni na je banki ba "

"Kuma haka ne, to ki yi mgana da shi dai ki ji."

Sai ta ce za ta faɗa masa, kuɗin akwai abubuwan da za ta yi da su za su yi mata amfani sosai.
Hamma Lamiɗo kuma sai washegari take so ta tarbe shi za ta yi masa mganar abin da ta yanke domin ta ji shawaransa.

Sai washegari ta kira Shamsiya a waya ta ba ta haƙuri tare da yi musu bangajiya da fatan sun koma gida lafiya

"Lafiya lau ranki ya daɗe, na so kiran ki sai kuma na ce ba lalle ki ɗauka ba kuna ta fama da jama'a"

Wani girma take ba ma Ummu Salma rayuwa kenan, Shamsiya ce ke godiya da irin tarban arzikin da aka yi musu da abubuwan alherin da suka samo a Daura Ummu Salma ta ce bakomai ba su jima suna yawa ba suka yi sallama ta tambayi Hanan Ummu Salma ta ce ba ta nan tana bangaren Bilkisu.

Lokacin da Ummu Salma kira Shamsiya suna tsakar gida ne tare da Gwaggo da ƙannen Habib maza da matan masu aure kuma hiran Daura take yi musu, tunda ta dawo kullum sai ta ba su labarin abin da ya faru a can, suna ta cewa lalle masu mulki da masu arziki sun huta duk sun zo da jakar da aka raba da calander da duka abubuwan da aka raba duk wanda ya ga hoton Lamiɗo sai ya sarara ya ce rabo ne kawai ya haɗa auren Habib da Ummu Salma tun farko amma ba tsaran juna ba ne.

Shi kan shi Habib ɗin duk Shamsiya ta faɗa masa duk abin da ya wakana a can Daura yana ji nadama na sake kama shi, ya yi sakaci ya yi wasa da damar shi, ga shi Ummu Salma ta yi masa nisa, shi dai ya rasa komai na shi, sai godiyar Ubangiji kawai Habiba ma haka ta je gidan su tana ta ba da labarin abin da ya faru a Daura ga abubuwan da suka dawo da shi, har jin daɗi take yi tana ba da labari, tana faɗin wata miyar sai a maƙota. Tana faɗin Habib ba shi da kuɗin da zai iya siyan takalmin da Hanan take sawa ba ma sutura da sauran bukatu ba, sai dai kawai ya yi hakuri a dinga ba shi aron ta amma Hanan ma ta fi ƙarfin shi ballatana Ummu Salama. Ga shi tana ta faɗin a jirgi suka dawo ita dai Habiba ta gama ganin duniya, faɗi take yi Habib ya cuceta da bai sake ta ba, ta tsani zama da shi, ba shi da komai sai haƙuri da rayuwa. Amma ta ga alamun ba zai sake ba kamar yadda ya faɗa ba yana so a sha wahala da ita, ta roki Baba Usman ya shiga mganar ya ce ba zai shiga ba sai dai ta yi haƙuri kawai dole ta haƙura amma tsakaninta da Habib ba rangwame ba tausasawa.

*
Received at 19:42
11 people reacted with ❤
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ranar da Ummu Salma za ta tarbi Lamiɗon da wuri ta yi aikace aikacenta tare da su Harira da sauran Hadimai masu kama mata girke girke ta yi masu rai da lafiya da yamma ta tura masa saƙon yau za ta kwana a bangaren shi bai ba ta amsa ba.

Abincin da ta yi duka a bangaren Mai marbaba aka je aka jera ba ta ci ba ta saka a zuciyarta tare da shi za su ci abincin dare yau. Kwalliya ta yi mai ƙayatarwa cikin wata atamfa ta san ya na son ya ga ta saka atamfa ya na yawan kallonta. Ba ta yi ƙunshi ba saboda wanda ta yi bai fita ba gashinta kuma ta gyara shi ta saka masa mai yana ta ƙyalli.

Da wuri ta tafi bangaren tare da Banafsha ta ɗaukan musu duk abin da za su buƙata kafin gobe da safe.
Bangaren Mai martaba ƙal yake a gyare yana tashin ƙamshi ga kalolin abinci na garari an jera a saman dinning ta dafa masa ruwan tee mai kayan ƙamshi irin wanda yake so, anan ta yi sallar isha'i daman da alwalanta daman haka take so in ya shigo daga Fada kawai ya fara tozali da ita.

Ta sha zama wajen karfe tara da rabi na dare wayar ta ce ta ɗebe mata kewa ta shiga youtube ta cigaba da sauraran labarin Turken gida na Janafty a tashar tsakar gida, ta gama ɗingishin kwaɗo, yanzu tunda kallo ya fita kanta ta koma jin Audio kuma yanzu ya zame mata jiki tana aikinta tana saurarawa, ko tana zaune yanzu ma Turken gidan tana gama ji za ta saurari buzu na Marubuciya Ayushercool.

Yanzu ma tana zaune a saman resting chair na bedroom ɗin Lamiɗo, Banafsha na gefenta tana da wassaninsu na yara, itama ta sha gayunta tana ta ƙamshin turare, ita kanta Ummu Salma wani irin ƙamshi ne ke tashi daga jikunta, turarakan Maryam suna da matukar kyau da kama jiki, in ta yi amfani da shi, Lamido na yabawa ballatana shi da ba ya son ƙamshi mai karfi duk sun cika ɗakin da ƙamshin su.
+234 812 195 7799

Hankalinta na can wajen jin diraman Sadiya da Yallaɓai, in da ya ce ta tafi gida saboda Gimbiya tana saurara tana kumduma ma Yallaɓai a shar a cikin zuciyarta tana kuma jin zafin lamarin sosai sai ga Bilkisu ta shigo itama ta ci gayunta masha Allah

Ganin Ummu Salma ya sa ta yi turus tana kallonta, itama ta ɗan ji wani iri da ta ganta amma ba ta nuna ba sai ta wayance ta gaishe ta Bilkisu ta amsa daƙyar fuskarta ba fara'a Ta juya za ta bar bedroom ɗin sai Ummu Salma ta miƙe bayan ta tsayar da karatun gwara ta yi mata bayani kar ta ce ta yi mata rashin adalci.

"Anty Bilkisu."

Ta kira sunanta sai ta juyo tana kallonta.
Ummu Salma ta tako har gabanta ta tsaya.

"In ba damuwa ina son magana dake."

Sai ta ɗan juya idanuwanta kafin ta ce" Uhm ina jin ki."

Sai ta ɗan yi shuru kafin ta ce" Ki yi haƙuri ban faɗa miki ba, na ɗauka kin sani tunda na dawo ban kwana a bangaren nan ba, tunda na haihu ban yi arba'in ba sai jiya ne muka yi kwana arba'in"

Bilkiisu ta kalleta tana nazarin maganarta.

"Yau ne zan kwana da gobe, jibi kuma sai ki karɓa. Ko kuma na koma mu dawo daga farko tunda ke ce babba, ni jibin sai na karɓa.

Ta faɗa tana kallon Bilkisu, da ta yi shuru ba ta yi magana ba.

"No. Alright."

Ta amsa mata sannan ta juya za ta bar ɗakin sai ga Lamiɗo ya shigo, tun daga falo ya cire alkebban jikinsa da rawaninsa.
Ganinsu tsaye suna kallon shi sai ya ba shi mamaki amma bai bayyana haka a saman fuskar shi ba. Bilkisu ta fara masa barka da shigowa ranka ya daɗe.
Ummu Salma ta ce sannu Hamma, ita manta ma take yi da wani ranka ya daɗe ya amsa ba tare da ya kalle su ba, sai da ya zauna a saman kujera yana ajiye kayan hannun shi sannan ya kalle su amma bai yi magana ba.

Bilkisu ta yi musu sallama ta fice Ummu Salma ta bi ta da kallo, ta faɗa mata gaskiya ne kar ta ɗauka tana shiga hakkinta ne. Shi dai bai tambaya ba, kuma Ummu Salma ba ta faɗa masa ba, ta taya shi rage kayan jikinsa ya shiga wanka ita kuma ta hau ninke kayan tana kai su ma'adanan su. Bilkisu kuma ba ta yi mamaki ba sanin halin Lamiɗo, baya ƙarin bayani duk abinda kika gani kawai ki yi shuru, ta yarda da Ummu Salma domin ta sha zuwa bangaren da daddare ranar da ba ita ba ce sai ta ganshi shi kaɗai bai taba faɗa mata ba. Ba ma zai faɗa ba wataƙila ma tunanin hakan bai kawo masa ba.
Received at 19:42
8 people reacted with ❤
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ta ji kishin barin Ummu Salma da mijinta har ta kai bangarenta zuciyarta na zafi sai da ta dinga addu'a tana neman tsarin sheɗam sannan ta samu sauƙi.

A can bangaren Mai martaba kuma bayan ya fito wanka tuni Ummu Salma ta ɗauko masa saukaƙkun kaya ya saka, ta ce masa ga abinci daman daga baya ta tura masa saƙon za ta yi abinci.

Cewa ya yi ta kwaso abincin zuwa ciki ya gaji ba zai iya fita ba. Ta bi umarninsa anan suka ci abincin kuma ya ci sosai, ya sha ruwan zafin da ta dafa masa ita ma ruwan zafin kawai ta sha, Banafsha ke hannunta tana shayar da ita bayan ta gama ta ba shi ita ya riƙe ita kuma ta kwashe komai ta mayar saman dinning ta gyara wajen sannan ta zo ta yi shirin kwanciya ta sauya kayan jikinta zuwa na barci haka ma Banafsha ta rage mata kaya masu nauyi daga jikinta zuwa masu sauƙi.
Suka saka ɗiyarsu a tsakiya suna kallonta Lamiɗo na rike da Hananun Banafsha, sai Ummu Salma ta riƙe hannun shi tana kallon shi, ya kalleta amma bai yi magana ba

"Hamma "

"Uhm"

"Na yi arba'in."

"Congratulations"

Ya faɗa yana kallonta sai ta yi masa mirmishi, ya yi shuru yana wasa da hannun Banafsha, sai Ummu Salma ta tashi ta janye Banafsha gefe yana kallonta bai yi magana ba. Ta tsallako ta zo ta shige jikinsa tana sauke numfashi, ya ƙi riketa ta fara shafa fuskarsa tana kiran sunan shi.

"Uhm"

"Na ce na yi arba'in.".

Ta gama faɗa cikin shagwaɓa, kamar za ta yi kuka.

"Me zan miki?

Ya ƙura masa ido tana kallon shi.

"Hamma."

Ta kira sunan shi tana dukan ƙirjinsa, haushi ta ji wai me zai yi mata sai kawai ta juya masa baya tana jin hawaye na taruwa a kwarmin idanuwanta.
Ya fa san abin da take magana amma yana yi mata wulakanci, ta ɗauka ba zai lallasheta ba ganin an fi mintina biyar bai riƙeta ba sai can ta ji shi a bayanta ya ɗora kansa a saman kanta yana rumgumeta.

"Sarauniya ta."

Ya faɗa a hankali yana shafa bayanta zuwa maranta, ta rike hannun shi amma ba ta yi magana ba

"Na yi kewar ki."

Ya faɗa yana yi mata raɗa.

"Ki taƙale ni, ina ina soo.."

Ya faɗa kamar wani yaro yadda ya yi maganar ne sai da ta ji motsi a cikinta duk yadda ta so ta ja aji ta kasa dole ta juyo da sauri ta kama kanshi, ya riƙe ta gam suka fara sumbatar juna kamar suna jira, da zafi zafi suna saman gado mai rumfa, da wasu labulaye masu kyau da yarari da suka rufe gadon gabaɗaya Banafsha na gefe iyayenta na gefe suna shan shagalinsu.

Ummu Salma ta kusa saka Mai martaba Sarkin Daura ihun sarari, duk kamewarsa sai da ya yi mata sambatu, wani irin salo ta dinga yi masa na salon da za ta rikita shi ita ta jagoranci komai shi dai kawai ɗan rakiya ne. Bayan sun gama tsarkake jikinsu suna ƙamƙame da juna, yana yi ma Ummu Salma raɗa a kunne tana masa dariya. Ta fara masa cakulkuli ya daure ya zille amma sai da ta saka shi dariya.

"Hattara dai Sarki ne ni."

Yake faɗa yana kallonta.

"A waje kake Sarki, a gaba na kai ba Sarki ba ne."

"I see."

Ya faɗa yana jan hancinta.

"Thank you,"

Ya faɗa yana sumbatar goshinta, ya rasa me zai ce mata! Amma ta saka shi farincikin da tunda ya zama Sarki bai yi irin shi ba. Hira suke yi a hankali, Ummu Salma ta juya kanta na saman hannun Lamiɗo yana ta bayanta ɗayan hannunsa ya zagaye cikinta zuwa Banafsha dake gefensu, kamar ba dare ba suna ta hira ƙasa ƙasa Umma Salma na ba shi labarin kudaɗen da ta samu masu yawa.

"Hamma ina so na cigaba da tafiyar da girke girkena a social media sannan ina so a ƙarƙashin haka na buɗe wata gidauniya domin taimaka ma marasa karfi."

Ya ce mata idea ne mai kyau, sannan ta cigaba da faɗa masa filayenta na Jimeta tana so ta ba da su a sadakatul jariya ga Baffa, tana so ta ba da su a gina islamiya da masallaci

Sai Lamiɗo ya tambayeta mene shawaranta ta ce babban filin za ta ba da shi kyauta a gina makarantar islamiya, ƙaramin kuma tana so ta gina masallaci da kanta domin Baffa.
Nan ya ba ta goyon baya ya ce abin da za ta yi tunani ne mai kyau sosai.

"Za ki samu duka support ɗina. A matsayin Miji da Yaya in sha Allahu, duk abin da kike bukata ki zo kai tsaye ina tare dake har abada."
Received at 19:42Reactions: ❤ 11, 👍 1
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ta sake shigewa jikinsa tana yi masa godiya.
Maganar girke girkenta kuma ya ce gidan abinci take so a buɗe mata? komai take so zai yi mata saboda ya yi supporting ɗinta sai ta ce tukunna dai ba ta da sha'awar gidan abinci ta fi bukatar buɗe wani training center domin koyar da matasan mata girke girken zamani da na gargajiya da kuma koyar da su yadda za su iya sarrafa fulawa domin samun sana'ar dogaro da kai. Ya ce hakan ma tunani ne mai kyau yanzu dai sun yi shawara za ta cigaba da ɗora video na girke girkenta sannan daga baya komai sai ya biyo baya.

Sai wajen

Please Login or Register in order to submit comment