Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dake."

Dole aka bar Islam da Baɗɗo.
A bangaren Ammah kuma mazan suna nan gabaɗaya ango ne kawai da Saddam ba su a wajen suna can tare da abokan ango lokacin da Ummu Salma ta shigo tana tura ciki a gaba sai da Umma Balki ta yi mata maganar kumburun kafafunta.

"Ki huta yar nan, nauyi ne a tare dake fa."

In ji Umma A'i Mami ta ce itama tun safe ta ga kafafun Ummu Salman sun ɗan kumbura Lamiɗo na gefen Hamma Kabiru yana kallon Umma Salma dake tsaye a gefen Mami shima ya ga kumburin kafafun nata.

"Zirga zirga ne fa ba wani abu."

Ummu Salma ta faɗa sannan ta ce za ta shiga ta yi wanka bayanta ma na ciwo.
Umma Balki ta ce ko tana kan gwiwa ne.
Mami ta amsa mata da cewa akwai saura EDD ɗin ta farkon watan November ne.

"To ina ruwan Allah da abin da bature ya ce? Ko yanzu Haihuwa ta zo ɗa zai fita fes."

Umma Balki ta faɗa har tana tafa hannu, Umma A'i na cewa ƙwarai kuma yadda cikin Ummu Salman ma ya yi ƙasa daga gani ya kusa fitowa duniya.
Mami ta karɓe da cewa da ikon Allah sai sun isa Egpyt sannan Ummu Salma za ta haihu a hannun ƙwararrun likitoci aka amsa da in sha Allahu.

Bilkisu ta na zaune ta ji maganar kamar daga sama.
Ta kalli Lamiɗo zuciyanta ta rufe saboda kishi ashe a Misra Ummu Salma za ta haihu bai faɗa mata ba.
Ta kalle shi amma shi hankalin shi ma ba ya kan kowa sai Ummu Salma, Hamma Kabiru ma na yi masa magana kunnensa ne kawai ke ji amma hankalin shi na kan Ummu Salma da suke magana da Mami.

Har duhu take gani saboda kishi da baƙin ciki. Ta daɗe tana tunanin Lamiɗo ya fi son Ummu Salma akanta sai yanzu take sake samun tabbacin haka. Ita duk haihuwanta a Nigeria take haihuwa na Sultan ma a wani babban asibitin kuɗi ta haihu a Abuja na Beena ta haihu a Lagos.
Kuma ita daman ba ta da ra'ayin fita kasar waje ta haihu tunda duka haihuwanta ba ta samu matsala ba, ko ƙaruwa da mata ke yi wajen haihuwa Allah ya ba ta da sauƙi ba ta taɓa samun wata matsalar ba.

Kallon kowa kawai take yi a falon cikin jin haushi. Domin ta fahinci ma da wannan bikin ko Ammah ba ta bi ta kanta ba. Kowa ya koma ma Ummu Salma, babban baƙin cikin Bilkisu a ce tana waje amma har tauraruwarta ta dishe sai Ummu Salma kaɗai ake gani, sannan har ana shirye-shiryen fita da ita kasar Cairo ta haihu amma Lamiɗo bai taba faɗa mata ba. Idanuwanta sun cika da ƙwalla ta yi ƙokarin ɓoyewa, ta jima tana fahimtar Lamido ya fi son Ummu Salma a kanta ko daga ganin yadda yarinyar nan ke juya shi, sai abin ta ce shi yake yi.
Wani turiri ne ke tasowa daga ƙasan zuciyanta so take yi ta samu kaɗaici ko za ta yi kuka ta ji sauki.
Received at 08:43Reactions: ❤ 7, 😁 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Kamar ta a ce Ummu Salma ta ƙere mata. Ita ta yi nasara ita kuma ta faɗi. Tun tana ƙarama ba ta taɓa yarda wata mace ta fita ba. Nadama take yi nadamar raina Ummu Salma tun farko ga shi ta raina ta, ta zo ta zame mata ciwon ido da damuwa kuncin dake zuciyanta Ummu Salma ce sila domin ta tsani ganinta kusa da mijinta. Jikinta ba in da ba ya rawa saboda damuwa da kishi.
Shi yasa ta tura ma Lamiɗo sako a waya da cewa tana son ta koma gida ta gaji za ta huta.

Sai ya ce okay, su shirya sai su tafi lokacin Ummu Salma ta shiga ciki. Ta miƙe tana yi ma Sabuwa magana da ta tattara yaran za su tafi.
Daidai Ango na shigowa tare da Saddam ba aboki ko ɗaya Saddam ya ce duk sun koma yau. Ammah ta yi nasiha su Hamma Jibo ma duk sun yi masa nasiha da sake tunasar da shi nauyin da ya hau kansa sai ya yi haƙuri a matsayinsa na namiji kuma shugaba. Lamiɗo ma ya ce yanzu ya zama babban mutum ya yi duk abin da zai yi ya daraja wannan auren da matarshi tare da iyayen shi gabaɗaya.

Ba wanda ya yi masa rakiya ɗakin Amarya sai Saddam dauke da ledojin Kaji da lemuka. Adda Safina na ta cewa Ummu Salma ta fito ta je ta yi siyan baki, ta ƙi fitowa ga gajiya sannan ga sallar mangariba da isha'i a kanta. Tana fitowa wanka ta fara yi sallar mangariba a zaune take yin sallar saboda bayanta ya riƙe kafafunta ma na ta ciwo suna tauna.

Tana zaune bayan ta idar da sallar isha'i ta miƙe kafar kenan ta ji an buɗe ƙofa an shigo ta ɗauka ma Mami ce tana juyawa sai ta ga Gogan ta ne

Ta sakar masa mirmishi ya mayar mata da martani.

"Hamma na."

Ta faɗa cikin shagwaɓa kamar za ta yi kuka tana ware masa hannuwanta daga zaune. Ya tako har gabanta ya duƙa suka rumgume juna.

"Na yi missing ɗin Hamma."

"Na yi missing ɗin ƙanwata"

Ya amsa mata kansa na tsakanin wuyanta da kafaɗanta, lokaci ɗaya hannunsa guda ɗaya na saman cikinta yana shafawa.

"How is my girl doing?

"Yau sai tokari na take yi"

Ummu Salma ta amsa masa cikin shagwaba
Tana cigaba da faɗa masa bayanta da kafafunta na ta ciwo.

Bai ce komai ba illa sakinta da ya yi ya koma yana matsa mata kafafun yana faɗin suna ciwo ne ta ce babu ciwo.

"Ɗan zirga zirgan da na yi ne kawai fa Hamma."

"To wa ya ce ki yi zirgan zirgan?

Ya faɗa ba tare da ya kalleta ba. Kanta ta miƙa masa, ya saka hannu ya cire mata hijabin jikinta. Daga ita sai wata yar shimi rabin cinyoyinta duk a waje ga cikinta da ya yi tsini.

"Hamma bikin Baɗɗo ne fa. Dole na yi zirga zirga."

"Baɗɗo ta wuce tunanin ka a wajena."

Duk yasan da wannan labarin kamar sake maimaita masa take yi, tana faɗa masa komai na ta Baɗɗo ce akan gaba. Duk abin da ya sameta na farinciki ko na baƙinciki ita ke tare da ita.
Shi dai matsa mata kafafunta yake yi bai yi magana ba. Domin sake tusa masa abin da ya sani kawai take yi.

Ya ɗan jima a wajenta yana yi mata maganar ya za a yi da maganar tafiyarsu
Shi yana tunanin za su koma Lagos tare da Bilkisu.
Ita kuma Umma Salma sai ta ce ya bar ta anan sai Visar su ta fito tukunnah.

Ya ce ba ta da matsala za ta iya zama. Bai bar ɗakin ba sai da Bilkisu ta kira shi awaya suna ta jiran shi ta shaƙa ta kusa fashewa daga cewa yana zuwa ya shanya su ta kuma san wajen Umma Salma ya je ya yi zamansa.
Ko da ya fito ya yi ma su Ammah sallama tuni Bilkisu da su Sabuwa suna haraba suna jiran shi a bakin mota.

Bilkisu ta kasa ko da dariya.
Kishin ta ya kasa ɓoyuwa daman kuma ita abin da ke damunta ba ta iya ɓoye shi yana bayyana har a saman  fuskarta.

Har suka isa gida ba ta yi magana ba duk da ko Lamiɗon ya yi mata magana ta kalle shi kallon tara saura kwata zuciyanta na zafi ta kauda kai. Tunda ya ga haka sai ya ƙyaleta ba daga Bilkisun har Ummu Salama ba wacce bai san halinta ba ya san halin Ummu Salma ciki da waje ya san kuma halin Bilkisu. Kawai shi dai mutum ne da ba ya son yana takura ma mutane, yana nuna kamar bai san komai ba ne amma babu abin da bai ankara da shi ba.
Received at 08:43Reactions: ❤ 8, 🥰 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ya san Ummu Salma da Bilkisu ba sa shiri amma tunda ba faɗa suke yi ba no need ya shiga ciki. In dai za su daraja junan su to zaman su a haka bai zama illa a gare shi ba. Ya san Bilkisu tana da zafin kishi ba ta ɓoye kishin Ummu Salma saɓanin ita Umma Salma da ba ta taɓa nuna masa tana kishin Bilkisu ba, kuma ya san tana yi kawai ba ta nunawa ne. Yau ɗin ma abin da ta yi masa ya san kishi ne saboda ya tsaya wajen Ummu Salma. Ba ya son fitina ko kuma shi na shi ran ya ɓaci shi ya sa kawai ya ƙyaleta.
Da suka koma gidan ma ɗakinta ta shige ta rufe ƙofa shima sai bai neme ta.

Duk da ba aiki zai koma wannan satin ba amma yana buƙatar su koma gida ya huta sosai kafin visar su ta fito. Sai dai kafin su tafi zai je Daura. Shi yasa washegari da safe ya bi jirgi zuwa Katsina daga can aka zo aka ɗauke sa zuwa Daura.

Yana zuwa Daura akai akai saboda jikin Mai martaba duk ya sasaabe duk da ba kwantar da shi cutar ta yi ba amma ta jima a jikinsa kafin ta bayyana.
Amma yanzu likitocin dake duba sa a kasar London sun tabbatar da Lever ɗinsa ta taɓu 50% amma tunda ana kan magani akwai yuyuwar ba za ta cigaba ba.

Daman yana ta fargaban kar Mai martaba ya ɗauko masa wancan maganar. Sai kuma aka ci sa'a Mai martaba bai yi masa zencen ba. Sun dai jima suna hira suna tattaunawa game da sha'anin mulki da sarkaƙaƙiyar dake cikin ko wace masarauta.
Fulani ma ta ji sauƙi amma itama suna shiryen shiryen suwa Saudiya  itama a can take ganin likita tare da Hajiya Kilishi da Hajiya Zeenatu za su tafi.

Washegari da Safe ya dawo Adamawa. Ya nema musu ticket, a ranar da karfe shidda na yamma suka koma Lagos shi da Bilkisu da yaran gabaɗaya.
Sun zo gida sun yi ma su Ammah sallama Bilkisu ta yi kamar ta yi bindiga lokacin da Ummu Salma ta yi musu rakiya har tana riƙe hannun Lamiɗo kuma bai hana ta ba.
A masu rakiyar har da Amarya Baɗɗo Hamma Abdullahi ne ya kai su filin jirgi washegari suma su Hamma Jibo duk suka koma garuruwansu da ilyalansu gida ya rage daga Ammah sai Ummu Salma da Mami, Umma Balki da Umma A'i ma sun koma Mubi
Sai Amarya Baɗɗo da angonta sai Hamma Saddam.

Amarya da ango suna ta cin amarcin su. Suna bangarensu amma ko wani safiya Baɗɗo za ta shigo ta gaishe da Ammah da Mami ba ta fara girki ba Adda Suwaiba na aiko mata da abinci. Haka ma Adda Ummu Suleim nan gida kuma Harira tare da Barira suke girkawa wani zubin kuma Mami ko Islam tunda ta iya girkin itama.
Sai Ummu Salma da kan shiga wajen Baɗɗo in Abdulrahim na bangaren Ammah su sha hira.

Washegari Daddy ya zo, bai samu zuwa ɗaurin auren ba domin ba ya ƙasar. Bai kwana ba a ranar ya koma tare da Islam da Faruk
Barira kuma za ta zauna tare da Ammah kafin su Mamin su dawo daga Cairo.

*

LAGOS.
BAYAN KWANA HUƊU.

Tunda suka dawo Bilkisu ta canza masa. Ba ta sakin masa fuska, ba ta zama da shi ko a dinning suka zauna cin abinci haka za su zauna su ta shi amma ba wani hira ko sakin jiki ya fahimci tun suna Adamawa ne ta canza masa. Ba ta kwana a bangaren shi ya ɗauka tana buƙatar lokaci ne sai da aka kwana huɗu sai ya fahimci sai sun zauna sun yi magana wata kila akwai rashin fahimta. Shi ya sa ya yanke shawaran zai yi magana da ita domin su fahimci juna.

Ba ta nan ta je asibiti, ya yi niyar cewa zai faɗa mata har maganar tafiyar su Egypt to da yamma ma kafin ta dawo ma aka tura masa sako Visar su ta yi ready, za su tashi nan da kwana uku. Tunda kamfanin da ya nemi Visa package ne gabaɗaya har da kuɗin jirgi da komai da komai.

Ya tura ma Ummu Salma saƙo tunda ya kira ta bai same ta a waya ba. Ya kamata zuwa gobe su taho Lagos tunda ta nan jirgin su zai ta shi. Ya samu Mami a waya sun daɗe suna tattaunawa. Sun rabu da cewa zai neme musu Ticket gobe su taho Lagos jibi sai wuce gabaɗaya.

Lamiɗo bai taɓa tunanin har da maganar tafiyar su Cairo a cikin abin da ya ɓata mata Bilkisu rai ba sai da ta dawo da daddare da kan shi  ya bita bangarenta.

Ya fara da tambayanta ko akwai wani abu dake damun ta ne?
Tana gaban madubi tana gyara gashin ta, ta yi shirin barci ma lokacin da ya shigo.
Received at 08:43Reactions: ❤ 8, 👍 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ta yi masa banza kamar ba ta ji shi ba. Haushin shi na sake kamata.
Kishi mai zafi na murkukusanta.
Tunda har ya fifita wata mace a sama da ita shima haushin shi take ji, ta nuna fushinta tunda suka dawo amma sai yau ne ya neme ta, ba ta da muhimmanci a wajensa shi ya sa bai damu da fushinta ba.

Ya sake maimaita tambayarsa sai a lokacin ta amsa shi da cewa bakomai.

Ya yi shuru kawai yana kallonta. Ya san da komai ɗin shi ya sa ya tambaya.

Dole shi ya ƙariso kusa da ita ya rakwafa fuskokinsu na bayyana a cikin madubin yana sanye da kayan barci ne masu taushi riga da wando ita ma rigar barcin ce a jikinta mai santsi rigar tana da leshi- leshi a saman wuya.

Ya daɗe yana kallonta ta cikin madubin ita kuma ta ƙi yarda su hada ido. Habarta ya ɗago yana kiran sunanta.

Ta goce habarta daga hannunsa ta miƙe har tana ture shi. Domin kuka ne ke son ƙwace mata, kwanaki nan kwana take yi kuka kishi na neman zautar da ita jininta har hawa ya yi, yau sai da aka yi mata gwaji.

Ta so ta je ta yi kwanciyarta ne sai ya tokare ta da jikinsa ta sake juyawa ya yi saurin riƙota ta baya ya rumgumeta. Ta fara mutsu-mutsun ƙwace kanta amma ya matse ta sosai a cikin jikinsa ba ta da yadda za ta yi kawai sai ta saki hannunta kukan da take riƙewa ya ƙwace mata ta kece da kuka mai sauti da ƙara.

Bai hana ta ba, ya bar ta yi kukan ta ko ta samu sauƙi.
Juyowa da ita ya yi ya matse ta a saman ƙirjinsa yana bubbuga bayanta alamun lallashi ta yi kuka da sauti ta koma shessheƙa hawayenta duk ya ɓata masa gaban rigar barcin jikinsa

Kusan mintina goma suna tsaye kafin ya ja ta zuwa bakin gado ya zaunar da ita. Ya durƙusa a gabanta ya sanya hannayensa yana share mata hawauye

Ta yi masa zuru tana kallon shi. Ko alama ba ta ji son shi ya ragu a zuciyarta ba. Tana son shi kuma har abada tana son shi. Ba ta son ta yi sharing ɗin sa da kowa shi yasa zuciyanta ke ciwo.

Hannunsa ta riƙe tana kallon shi.

"I love you Lamiɗo. Ina son ka, bana son wata mace a kusa dakai. Ji nake yi kamar zan mutu."

Take faɗa hawaye na sake kece mata. Dole ya miƙe ya zauna a gefenta ya ɗagota  zuwa saman jikinsa
Ta sake rikice masa da kuka shi kuma ya na ta lallashinta da ƙyar ya samu ta daina kukan ta koma ta lafe a jikinsa tana sauke tagwayen  ajiyar zuciya.

Ya sake ɗago fuskarta yana share mata hawaye.

"Is okay! na ce ya isa."

"What wrong with you? Ni ne na yi miki laifi?

"Ki faɗa mini, zan ba ki hakuri bana son wannan shuru.'

"Shuru ba ya kawo mafita a relationship, ballantamu da muke Ma'aurata. Juzt in ma wani abu ne da na yi miki ba ki ji daɗi ba you can feel free ki yi mini magana mu tattauna mu samu fahimtar juna."

Ta yi shuru tana kallon shi kawai ta kasa magana yana nufin bai san laifin shi ba.
Laifin shi ɗaya me ya sa ya auri wata macen ya fifitata a sama da ita.

"Uhm tell me what happen?

"Why?

Ta tambaye shi muryanta a shaƙe.

Ya zura mata ido yana kallonta.

"Why? Me ya sa ka aureta?

"Me ya sa ka auri Ummu Salma.?

Daman ya san matsalan kenan ya ɗauka ta fahimci kaddara tun daga fari ashe tana buƙatar ƙarin bayani.

"Why me ya sa? Kasan yadda na ke ji a zuciyata in na ganta tare da kai?

"Ji nake yi kamar zan mutu kamar zan yi hauka."

"Ina sonka, ni kaɗai na ke so na mallake ka. Me ya sa ka aure ta?

Ya ɗan lumshe idanuwana ya buɗe a saman fuskarta yana kallonta.

"Kaddara."

Sai ya ɗan yi shuru kafin ya ɗan gyara mata zaman ta a saman cinyarsa.

"Tun a littafin zanen kaddarata. Ubangjina ya zana zan aure ki da farko ke Bilkisu daga baya zan auri Ummu Salma. Kuma ba wanda ya isa ya goge wannan zanen a cikin littafin kaddarata. Domin Ubangiji ne ya zana hakan kuma dole ya faru."

Ya dakata yana fahimtar yadda ta karɓi maganar.
Sai hawaye shar suka zubo mata a saman kumatunta.

"Amma hakan ba ya na nufin na yi hurting feeling ɗin ki ba ne. I'm sorry."

Sai kawai ta sake fashewa da kuka.
Cikin kukan take faɗin" Me ya sa to sai ita ba ka auri wata ba?

"Saboda ita Ubangiji ya rubuta mini."

"Kana son ta?

"Yes i do"

Ta runtse idanuwana wasu hawayen na sake kece mata.

"Ka fi sonta a kaina. Kafi son ta."

Take faɗa cikin gunjin kuka.
Received at 08:43Reactions: ❤ 7, 😁 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
"A'a ba gaskiya ba ne "

Ya yi saurin katse ta saboda shi dai ya san ba gaskiya ba ne.

"Gaskiya ne mana komai ita ce abubuwa da dama a tare da kai ta canza ka, me ya sa? Saboda kana son ta ne ka ba ta damar ta canza ka, amma ni ba ka bani damar haka ba."

"Na ba ki dukkan dama Bilkisu."

Ya faɗa yana kallomta lokaci ɗaya yana share mata hawaye.

"Ban taɓa takura miki ba, duk abin da kike so ina son shi. Saboda na ba ki damar samun auren ki cikin farinciki. Duk wani baƙon abin da kika ga ina yi Ummu Salma ke so, ta nuna tana so sai na yi mata ke kuma ba ki taɓa nuna kina son abu ban yi miki ba. Ni kuma ina gudun yin wani abun da ba ki so, bana so na ɓata miki rai bana so na ɓata ma duk wani wanda nake zaune da shi rai. Ina girmama ra'ayin duk wanda zama ya haɗa da ni da shi Bilkisu."

"Ai ko ban faɗa ba ka san na daɗe ina son mu dinga wanka tare amma ba ka taɓa ba ni damar haka ba?

"Ba ki ce kina so ba, kawai saboda ni bana so sai ba ki damu ba. Ita kuma tana so ta damu shi yasa na yi mata abin da take so."

Tana kallon shi zuciyanta na sake ɗaukan zafi da ɗumi.

"Am sorry."

Ya faɗa yana sake riƙeta a jikinsa.

"Ban taɓa hana ki abin da kike so ba. Kin sani."

"Ka fi son ta ne kawai ka yarda da magana."

Kukanta yaƙi tsayawa saboda kishi.

"Na ce miki ba gaskiya ba ne ."

"To mene gaskiyan? Yanzu ma ƙasar za ku bari ba ka faɗa mini ba. Ni yaushe na samu damar yin tafiya da kai!? Lokacin da na haifi Sultan ne kaɗai muka je Maroco shima ba mu daɗe ba muka dawo amma ita fa? Tare za ku tafi wataƙila ma sai ta haihu za ka dawo,  kana ji da ita a gaban kowa kake nuna tsananin kulawarka a kanta me ya sa ba zan ce ka fi son ta ba?

Sai ta bashi tausayi yadda take magana ya fahimci ya yi hurting ɗin ta.

"I'm sorry."

"I'm sorry ina ta so na faɗa miki ne ki yi haƙuri please."

Lamiɗo na birge ta ba shi da girman kai. Ko ya yi laifi ko bai yi ba zai ba da haƙuri domin a samu daidaito.

"Bilkisu."

Ya kira sunanta a kausashe.
Ta kalle shi tana fahimtar duk maganar da zai faɗa da gaske ne.

"Na gode sosai "

Ya faɗa yana yi mata mirmishi sannan ya sumbaci kumatunta har yana saka harshen shi ya lashi hawayenta.
Ta kankame shi jikinta na shaking kamar tana jin sanyi.

"Thank you. Thank you for marrying me, for giving birth to our childreen and for your love and everthing. I love you."

Ya faɗa yana sake ƙamƙameta itama tana ƙamkame da shi tana hawaye raɗaɗin dake cikin zuciyanta na raguwa

"Kana sona? Ni fa Fulani ce ta yi maka tayi na.? Ita fa cewa ka yi kana son ta."

Tana jikinsa take faɗin haka.
Ya yi shuru kawai yana sauraranta.

"Kana yi mata wasu abubuwan ko da ban yi niyar kishi ba sai na ji kishi. Sai nake tunanin kana fifita ta sama da ni saboda ka fi son ta."

"Na ce ba gaskiya ba ne ko?."

"Wallahi tallahi kinsan rantsuwa ko?

Sai ta ɗago tana kallon shi ba ta taɓa jin ya yi rantsuwa haka ba.

"In za ki yarda da ni, ban fi son wata akan wata ba."

"Ban fi son Umma Salama a sama da son da na ke yi miki ba."

Ta yi ƙuri tana kallon shi.
Ya ɗan sauke numfashi kaɗan yana kallonta itama shi take kallo, sai ya ɗan kauda kai, saboda abin da yake faɗa sabanin abin da ke zuciyarsa ne amma saboda samun daidato da zaman lafiya gwara ya faɗi saɓanin gaskiya.
ta sakalo hannayenta ta wuyansa  suna masu kallon juna.

"Ke na fara aure ke kika fara mayar da ni uba me ya sa zan fifita wata macen sama dake?

"Dukkan ku ina son ku i'm sorry ba ina nufin na ɓata miki rai ba. Ina son Umma Salma a yadda take, kema ina son ki a yadda kike. Bana son wannan canjin a tare dake. I love you do way you are. Itama haka nake son ta a yadda take."

Ya lumshe idanuwana ya buɗe sun ɗan rusuna sannan muryansa ta ɗan shige ciki.

"Ki daina damuwa da cewa ina son ta sama dake ba gaskiya ba ne. Sannan maganar ina ririta ta kuma kin san ba ta da lafiya ta rasa Baffa ta rasa jariri she is not fine, ina tare da ita domin kar ciwon damuwa ya kamata ga shi ta zo ta sake samun wani cikin, tana cikin hatsari tana da Bp komai kin san zai iya faruwa.
Received at 08:43Reactions: ❤ 5, 👏 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Maganar zuwa Egypt kuma tun wancan haihuwan a can na tsara za ta haihu sai kuma ga kaddaran da ya faru ba nufina na ɓoye miki ba i'm sorry da ban faɗa miki akan lokaci ba."

Ya yi shuru yana kallonta. Yana so ya ga yadda ta karɓi maganganunsa da alamu sun shigeta ta daina kuka fuskarta ta nuna tana fahimtarsa

"Ba kuma a can zan zauna ba, muna zuwa aka gama komai zan dawo na bar su a can tare da Mami na san she'll be okay with her."

"I'm sorry."

Ya sake ba ta haƙuri sai ta lumshe idanuwana ta buɗe sannan ta kalle shi.

"Do you love me?

"Yes i do."

"I love you so much."

Ya faɗa cikin sanyin murya.
Sai kawai ta sake ƙamƙame shi.

"In dai kana sona za ka cigaba da sona, sannan in dai ba ka fi son Ummu Salma sama da ni ba i'm okay."

Kanta yake shafawa zuwa bayanta alamun lallashi.

"In ba ki shawara?

Ya faɗa yana ɗago fuskarta sai ta gyaɗa masa kai

"Ki daina bari zuciyarki na jin zafi akan wani abu. Aure fa umarnin Allah ne, tunda haka ne bai kama ta ki bari kina damuwa ba. Please ki cire komai a zuciyarki ki sani ina tare dake har abada."

"I will."

Ta faɗa tana share hawayenta da bayan hannunta.

"Zuciyata ke zafi in na ganta a kusa da kai ban san yadda zan yi ba."

"Ki yi hakuri."

Hakuri ne kawai zai iya bata. Domin ba zai iya cire mata abin da ke zuciyanta ba.
Za ta cigaba da ganinsa da Ummu Salma har abada.
To gwara ta yi hakurin shine mafi alheri.

A daran kuma ya sake tabbatar mata da cewa Ummu Salma ba ta fita a wajensa ba. Koma mene ne ya bar ma zuciyarsa wannan amma shi ɗin banza ne ya isa ya iya daidaita soyayyar mata biyu a zuciyarsa? Dole akwai wacce ya fi so, sannan ko wacce akwai dalilin da ya sa yake son ta amma domin a zauna lafiya sai ya nuna ma Bilkisu ita ce tauraruwa tunda ya fahimci ita a komai ta fi son ta shiga gaba sai ya nuna mata ita ɗin ce a gaba domin

Please Login or Register in order to submit comment