Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yake yi ba ta yi kuka ba amma Allah kaɗai ya san suyan dake cikin zuciyarta.

"Rasuwar dare ce?

"Ƙarfe uku na dare da wani abu ya cika."

Ya jinjina kai cikin sanyin jiki da na zuciya.

"Allahu akbar Ubangiji ya karɓi bakuncin Baffa."

Ta amsa da Amin Amin

"Ka kira sauran yan'uwanka, sannan ku sanar da Baffa Umaru."

Ya miƙe yana amsa mata.
Ya kalli Abdullahi ganin yadda yake hawaye da kuka har yana sauti.
Ga su Saddam can a tsakar gida suna ta hawaye suma
Kamo Abdullahin ya yi ya miƙar da shi

"Haƙuri za mu yi Abdullahi. Lokacin Baffa ne ya yi ba mu da yadda za mu yi."

Ya faɗa yana dafa kafaɗan shi alamun lallashi.
Suka fita tsakar gida shima Abdullahi a yarin su Saddam ya bi ya yi zaman dirshan a tsakar gida yana dafe kansa lokaci ɗaya yana hawaye.

Ya rasa ma wanda zai fara kira wayarsa ya zaro a cikin aljihu ya ga Ummu Sulaim ta kira shi ganin yadda ya fita hankali tashe shi ya sa ta damu.

Bai kira ta ba, sai da ya kira wayar Baffa Umaru bai same shi ba sai ya kira na Baffa Salihu shi ya sama bayan sun gaisa tun kafin ma ya sanar da shi abin da ke faruwa ya ce ba lafiya tunda ya ga kiran shi da sassafe haka nan ya sanar da shi Baffa lokaci ya yi.

Baffa Salihu ya ja salati ya dire.

"Hadi ya rasu Abdulrrahaman?

"Wallahi Baffa sa'i ya yi."

"Allahu akbar., ciwo ya yi ne ba mu sani ba?

"Ba ciwo Lafiyan shi kalau jiya har sha biyun dare muna tare da shi. Lokaci ne kawai ya yi "

"Allahu akbar. Allah ya jikan Hadi Allah ya yi masa rahama."

Ya amsa da Amin yana faɗa masa ya kira wayar Baffa Umaru bai same shi ba ya sanar da su Baffa lokaci ya yi Baffa Salihu ya ce yanzu kuwa tunda kuma rasuwar ta dare ce sai yanzu kowa zai sani a sanya jana'izar zuwa sha ɗaya na safe haka kafin nan kowa ya iso Hamma Abdurrahama ya amsa masa da to.
Suna ma cikin wayar Ummu Sulain na ta sake kiran shi.

Sai da suka gama wayar ya kira ta tana tambayan shi me ya faru ya ce kawai ta rufe gida ta ɗauko yara su samu adaidaita su taho gida.

"Me ya faru?

"Baffa ne Allah ya yi ma rasuwa.'

Ta ja salati bai bari ta ƙarisa ba ya kashe wayarsa.
Ya juya yana yi ma su Abdullahi nasihan su daina kuka addu'a kawai Baffa ke bukata.

"Abdullahi ka yi haƙuri, yanzu mu tsara yadda za mu isar da Baffa gidansa na gaskiya."

Cewa ya yi Abdulrahim ya je ya faɗa ma limamin masallacin da su Baffa ke salla nan kusa da su ne, ya tashi yana goge hawayensa ya zura takalmin shi ya fita Saddam dai ko motsi.
Dakin Baffa suka koma dukkansu biyu suka durƙusa gaban Ammah.
Abdulrahaman na faɗa mata ya samu Baffa Salihu a waya ya faɗa musu ya ce suna tafe yanzu.

"Ku kira Fatima, kar ku faɗa mata kai tsaye ku yi magana da mijinta."

Hamma Abdullahi ya ce bari ya kira Daddy.

"Abdulrahaman ki kira su Balki ku faɗa musu, sannan ka kira Lamiɗo."

Ta yi shuru tana saukar da numfashi.

"Kar ku faɗa ma Auta tana da juna biyu, za ta iya shiga hatsari ku kira su Jibo su sanar da su, su taho da wuri a sallaci Baffa a sada shi da gidan shi na gaskiya"

Ya amsa mata da to, tsakar gida ya fita ya fara kiran Hamma Jibo.
Shi kuma Hamma Abdullahi ya kira Daddy ya sanar da shi ya ce yana Abuja amma zai kira Mami ya sa ta samu jirgin da za ta taho Adamawa cikin dubara ba tare da ta san abin da ya faru ba.
Received at 09:09Reactions:
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Cikin lokaci kaɗan labarin rasuwar Baba ta zagaya kunnuwan dangi na kusa da na nesa.
Ammah da kanta ta kira Ummin ikki ta faɗa mata Baffa lokaci ya yi.
Su Adda Suwaiba ne kaɗai suka riga ta zuwa sai liman sai gata tare da su Baɗɗo da babansu.

Ammah falonta ta koma aka bar ma mazan nan ɗakin Baffa. Su Hamma Jibo haka suka ji mutuwar Baffa kamar saukan aradu kowa ma sai ya ce wai ya yi ciwo ne.? A ce ba ciwo ajali ne ya yi kira.

Su Umma Balki suma hankalinsu a tashe suka ce yanzu za su kamo hanya.
Lamiɗo kuma Abdullahi ya kira shi bai same shi ba sai ya tura masa sako
Kafin ya ga sakon Hamma Kabiru da ya ji labari ya kira shi shidda da mintina Hamsin na safe ya faɗa masa
A lokacin ya dawo daga masallaci kenan ya kwanta gefen Ummu Salma da yake yau an yi wa'azi a masallacin ya tsaya ya saurara.
Lokacin da Hamma Kabiru ke faɗa masa Babu Baffa sai da ya ji jiri ya kwashe shi.
Tsam ya tashi daga kan gadon ya mike ya fita falo.

Mutuwan ta girgiza shi Baffan da suka yi magana da shi jiya lafiyan shi ƙalau. Ammah kawai yake tunawa daga ita sai Ummu Salama sai Mami waɗanan ukun ya za su ji yau in suka tabbatar da Babu Baffa.

Tashin hankalin shi yadda zai faɗa ma Ummu Salma babu Baffa. Ga ta da ciki tana da B.P.
Kansa ya dafe yana kiran sunan Allah.
Wayarsa ya shiga ya nema musu jirgi, har ya amince ma Ummu Salma za su fara biyawa ta Abuja kafin su sauka Adamawa.

Sai ga shi komai ya sauya daman bai nema musu ticket ba. Nan take ya shiga ya nema musu jirgi kuma an yi sa'a akwai wanda zai tashi zuwa Adamawa takwas na safe

Sai bayan ya yi booking sannan ya kira wayar Mai martaba bugu ɗaya ana biyu ya ɗauka bayan gaisuwa ya shaida masa halin da ake ciki.

"Allahu Akbar."

Mai martaba ya ja kabbara sau uku.

"Allah ya jiƙan Hadi. Ubangiji ya kyautata makwancinsa."

Tambaya ya yi ƙarfe nawa ne za a yi janaizar?

Ya ce sai ya kira ya tabbatar zai faɗa masa.
Mai martaba ya ce to ya kira shi ya faɗa masa yanzu zai sa a shirya tagawa za su taho in sha Allahu.

Mai martaba ne ya kira Fulani a waya ya sanar da ita tana ta salati nan ma Masarautar tuni labari ya kai ma kowa, Saleem kuma ya shiga group ɗinsu na iyalan Mai martaba ya sanar cewa kawun Yarima Yayar mahaifiyarsa kuma mariƙinsa sannan uban matarsa Allah ya yi masa rasuwa jiya da daddare.
Gimbiya Hadiza ta fara kiran Bilkisu ta faɗa mata rasuwan Baffa ta ji mutuwan nan sosai domin wani abu bai taba shiga tsakaninta da Baffa ba sai alherinsa.

Da ta kira Lamiɗo yana waya lokacin da Abdullahi yana jin lokacin da za a yi Jana'iza ya ce sun saka sha ɗaya na safe. Saboda yan nesa su ƙariso, ya ce Ummu Salma ta yi nesa da wayarta tunda duk sun fitar da sanarwan a kafafen sada zumunta Lamiɗo ya ba shi tabbacin zai hana ta ɗaukan wayarta har sai sun iso.

Sai da suka gama waya ne ya kira Bilkisu
Ta tambaye shi ya tabbatar mata.
Nan take ta ce za ta nema musu ticket ita da yara itama za ta taho ya ce suma yanzu shiri za su yi jana'izar ƙarfe sha ɗaya na safe.

"Ciwo ya yi ne Ranka ya daɗe?

"Lafiyan ƙalau jiya ma mun yi magana da shi."

"Allah ya jiƙan shi."
Ya amsa da Amin suka yi shuru.

"Ummu Salma ta sani?

"Ban faɗa mata ba."

"Kar ka faɗa mata akwai hatsari."

Ya amsa da toh, ta na faɗa masa ya bari in sun je can kawai ya ce haka yake tunani.
Ba su daɗe suna wayar ba suka yi sallama da cewa sai sun haɗu a can duk da ba ta son Ummu Salma amma Baffa bai yi mata komai ba ta ji mutuwarsa sannan ta tausaya ma Umma Salma ta san yadda take son Baffan nan na ta sosai.

Mami kuma tana cikin barci wayar Daddy ya tashe ta.
Tunda ta ji ya fara cewa za ta je Adamawa a yau yau ɗin nan da safe nan ta watsake.
Ta san ba lafiya ta ce koma me ya faru kawai ya faɗa mata ita ba yarinya ba ce za ta iya kula da kanta.

Lokacin da ya faɗa mata Baffa ne ya rasu ya yi mamakin ƙarfin halinta Mami ta yi shuru kamar a mafarki.

"Allah ya jiƙan Baffa. Allah ya yi masa rahama."

Tausayinta ya kama shi ya ji takaicin ba ya kusa. Nan take ya ce ta nemi mota su taho Abuja ya duba babu jirgin da zai taho Abuja zai nema musu jirgin da za su tafi Adamawa daga can Abujan.
Ta ce shike nan bari su shirya.
Received
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Zama ta yi a ɗaki ta sha kukanta tun shekaranjiya take jin jikinta ba daɗi ashe maraniya za ta zama jiya ne kawai ba su yi magana da Baffa a waya ba. Lafiyan shi lau bai yi ciwo ba amma ajali ya kira shi.

Data ta buɗe tana ganin hotunan Baffa da R.I.P a jiki sai ta ji kawai ta sake fashewa da kuka.
Status ɗin Hamma Abdulrrahaman ya fi karya mata zuciya.

"Allah ya yi ma mahaifina Alhaji Hadi Baba Rasuwa a jiya da daddare za a yi jana'izar sa yau da misalin sha ɗaya na safiyar ranar talata a gidansa dake anguwan Zone3 a garin Jimeta Adamawa."

"Ku yi masa addu'a. Ku nema ma mahaifina gafara."

Ba hoto ya saka ba rubutu ne amma gabaɗaya jikinta ya saki. Tana kuka ta fita ta yi magana da Barira.
Tare za su tafi tunda ba ta san yaushe za su dawo ba lokacin da Barira ta ji Baffa ne ya rasu itama ta yi kuka sosai, Islaam ma kuka share shere Faruk har yana birgima ko wanka ba su tsaya sun yi ba, ballatana maganar abinci.
Mami ta kira Hajiya Falmata a waya ta faɗa mata.
Ta tausaya mata domin ta san a duniya Mami ba ta da kowa sama da Baffa nan ta yi mata gaisuwa ta ce kafin a yi uku za ta taho.

Rufe gidan suka yi karfe bakwai da wasu mintina Hamisu ya kwashe su a baƙar pradon ɗin Dadduy suka ɗau hanyar Abuja.
Mami tana idanuwanta sun tasa muryanta har ta dishe ta umarci Hamisu da ya yi gudu sosai shi yasa cikin awa biyu da wani abu suka isa Abuja.

Har suka isa Abuja Mami kuka take yi, a filin jirgin suka haɗu da Daddy ashe jirgi ɗaya za su hau zuwa Adamawa tare da Hamma Jibo da iyalansa.

Jirgin karfe goma ne, A Airport Daddy ya rumgume Mami tana ta kuka yana lallashinta Hamma Jibo bai yi kuka ba amma duk ya yi zururu.

Adda Nauwara ma da su Saudat ɗin kukan suke yi
Allahu akbar rai baƙon duniya.
Sai da jirginsu ya ɗaga sannan Hamisu ya baro Airport ɗin ya kama hanyar komawa Kaduna.

*

Ƙarfe goma da mintina arba'in da takwas su Mami suka iso Adamawa.
Tashar Napep biyu suka yi zuwa gida.

Tun daga farkon layin motoci ne sun cika ga jama'a.
Mai martaba ya iso tun wajen goma tare da Tawagan wakilan Fada, da Saleem da Fulani tare kuma da Gimbiya Shahida da Gimbiya Amratu.

Bilkisu ma ta iso tare da su Sultan da su Sabuwa.
Hamma Mustpha ya iso haka ma Hamma Kabiru.
Mutanen Mubi motoci uku sun iso, daman su Mami ne sai su Lamiɗo ba su taho ba.
Tuni har an yi ma Baffa wanka an haɗa shi sannan an je makabarta an yi hakan kabari
Baffa Umaru ne da su Hamma Mustapha da Hamma Abdulrrahanman da Abudullahi suka yi masa wanka.

Cikin gida tun daga haraba har cikin ɗakuna cike yake da jama'a kama daga yan'uwa da mutanen anguwa. Ammah na zaune a falonta da Hijabi Ummin ikki na gefenta tare da su Umma Balki. Kowa da Hijabi a jikinsu masu kuka na yi masu share hawaye na yi.
Zuwan Mami ya rikita falon domin zubewa ta yi a jikin Ammah tana gunjin kuka su Umma Balki ne ke ba ta baki.

"Baffa ya tafi ya bar ni, ni ba marainiya ba ce a baya amma yanzu na zama marainiya."

Har tsakar gida ana jin ihunta. Mai Martaba na cikin ɗakin Baffa tare da su Baffa Umaru da su Hamma Mustapha.
Yau ga Mai martaba ga Batula sun haɗu bayan shafe shekaru sama da talatin amma haɗuwar ba ta zama mai daɗi ba. Yana kallonta cikin rawaninsa cikin tausayinta lokacin da ya yi mata gani na ƙarshe tana kuka yanzu ma da ya sake haɗuwa da ita cikin kuka ne
Ƙirjinsa ya dinga suya, yana so ya lallasheta amma kuma ba shi da wannan hurumin yana gani Daddy ya riƙe mata kafaɗu yana lallashinta wanda suka shigo ɗakin tare da su Hamma Jibo.

Gabaɗayansu sun zagaye gawan Baffa suna ta yi masa addu'a da fatan dacewa
Allahu akbar ga Baffa kwance ba ya motsi. Jiya fa lafiyan shi ƙalau amma yau ba ya raye. Duniya zencen banza Ubangiji ya sa mu gama lafiya.

Hamma Lamiɗo ake jira da Ummu Salma su kuma sun samu tsaikon jirgi ne sai ƙarfe goma sauran jirgin su ya tashi.
Duk da Umma Salma ba ta sani ba. Amma ta ji a jikinta wani abu mara daɗi na faruwa tun da tashi da safe take jin ta wani iri kamar mara lafiya sukuku ba ta da kuzari.
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Barcin da ta koma bayan sallar asuba ta yi wani mafarki ta ga gidansu cike da jama'a ta ga kowa da kowa har mutanen Mubi amma ba ta ga Baffa ba kuma ta kasa faɗa ma Lamiɗo mafarkin da ta yi amma tunda ta farka zuciyarta duk ba daɗi hankalinta duk ya koma gida.

Lamiɗo ya yi dubaran ya ɗauke wayarta ya kashe ba tare da ta sani ba, halin da take ciki ne ya sa ba ta ma nemi wayar ba, ba ta cikin yanayi mai daɗi
Ko karyawa ba su tsaya sun yi ba ya ce in suka isa can za su karya.

Da shi da Ummu Salma da Hanan da Harira.
James da Baban Adila ya sallame su, rufe gidan za su yi suma su tafi garuruwansu hutun kirisimeti da sabuwar shekara.

Ummu Salma ko a cikin jirgi sukuku take har Lamiɗo ya ji tsoron ko ta sani ne? Sai dai daga baya ya fahimci yanayin. Yanayin da mutum zai ji a jikinsa in ya rasa wani abu mai muhimmanci ko da ba a faɗa masa a lokacin ba zai ji a jikinsa.

Da suka sauka a filin jirgi ta ga ba a zo ɗaukan su ba. Tun daga nan ta san wani abu na faruwa a gida. Hamma Lamiɗo shima wani iri take ganin shi ya ginsheƙe fuska ba ya son ma ta yi masa tambaya amma yana riƙe da hannunta kamar za ta gudun masa. Suma Napep ɗin suka yi tasha zuwa gida.

Ta tabbatar da zarginta da yanayinta tun lokacin da suka doso anguwan su ta ga layin su cike da motoci.
Tun daga lokacin ta san wani abu ya faru.

"Hamma "

Ta kira sunan shi cikin wani rauni tana mai kallon shi lokaci ɗaya tana rike hannuwansa.

"Me ya faru ne?

"Ya na ga mutane sun cika ƙofar gidanmu."

Mutuwa aka yi haka zuciyarta ke faɗa mata? Domin taron mutane dalili biyu ke kawo su lokacin farinciki ko lokacin baƙin ciki. Na baƙin cikin take zargi domin in na farinciki ne za ta ji labari.
Zuciyanta na rawa. Waye ya rasu?

Har ta fara hawaye, me ya faru? Wa ye ya rasu.
Ba ta son ta kawo lissafin ma waye ya rasu ɗin ji take yi kamar za ta haukace a lokacin saboda tashin hankali da fargaba.

Rumgumeta kawai ya yi yana lallashinta
Harira ma duk a firgice take tunda ta ga tarin mutane ta san ba lafiya suna sauka get ɗin a wangale yake haraban gidan ma ga mutane nan suna ta alwala.
Sannan ta ga dogarai da masu kaki sun taso suna yi ma yarima barka da zuwa.

Ta ga Hamma Saddam idanuwansa jajir shi da Hamma Abdulrahim.
Fuskokin mutane take dubawa tana neman Baffa amma ba ta gan shi ba.

Tana kokarin ƙwace hannunta Lamiɗo ya hana ta
Harira na ɗauke da Hanan, daman ba su ɗauko kaya ba akwati ɗaya ne da jaka.
Lamiɗo bai saki hannun Ummu Salma ba har cikin gida, Baɗɗo da su Adda Suwaiba duk suna tsakar gida zazzaune da Hijabai ita ce tana ganin su ta taso, ita ya miƙa ma Ummu Salma yana kallonta.

"Ki yi haƙuri "

"Allah ya jiƙan Baffa."

Ya faɗa yana yana runtse hannun Ummu Salma cikin na shi.
Sannan ya miƙa ma Baɗɗo hannun nata.

"Please take care of her."

Ko bai faɗa ma ta san Baffa ne ya rasu a cikin taron mutanen da ta gani tun daga waje ba ta ga Baffa, in kuma yana nan to da tabbas shi za ta fara gani a haraba tantama take yi shin da gaske Baffan ne ya rasu?

ƙafafunta suka fara rawa ta damƙe hannayen Baɗɗo hawaye na yi mata ambaliya.
Baffan ne ya rasu? To in ba Baffa ba waye zai rasun da kowa da kowa zai zo. Ina Ammah?
Zuciyanta ta harba, ta yi tsalle ji take yi kamar ta buɗe idanuwana ta ga komai mafarki ne.

Hamma Kabiru ne ya fito suka yi musabaha da Lamiɗo sannan suka nufi ɗakin da gawar Baffa ke ciki.
Ganin sun nufi ɗakin Baffa ga takalma nan masu yawa a ƙofar ɗakin daga nan ta ji kafafunta na rinjayanta.
Amma ta kasa bin unarninsu, ba ta ga Baffa ba sannan ba ta ga Ammah ba tabbas wani cikin su ne ya rasu yau.

Ummu Salma ta kasa zama tuni ta saki jakar hannunta haka ma takalmin kafarta Adda Suwaiba ta tattara mata su duka ta rumgume suma kuka suke yi ba mai ba ma wani hakuri, suna tuna jiya fa har da shi a masu yi musu rakiya.

Umnu Salma ba ta ma sanin in da take jefa kafafunta Baɗɗo na rike da ita, itama hawayen take yi.
Falon Ammah ta shiga, tunda ta ga Ammah zaune gefenta su Umma Balki da Hijabai
Ta kai kallonta kan yan'uwansu na Mubi matayen su Baffa Umaru suna ta kuka.
Received at 09:16Reactions: ❤ 12, 😭 2, 🔥 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ta hango Mami a jikin Umma Balki tana ta kuka.
Tabbas Baffa ya rasu ta yarda tunda ta ga Ammah ta ga kowa ban da Baffa.
Ba domin Baɗɗo ba da faɗi za ta yi ita ce ta tare ta sai ta kasa shiga ɗakin ta juya Baɗɗo na rike ta suka fito tsarkar gida ba ta gani ma sosai ɗan cikinta ya dunƙule waje ɗaya jiri ma take gani ta zame nan samar tabarma ta zauna tana saka fuskanta a cikin tafukan hannayenta ta saki wani marayan kuka.

Baɗɗo ta zauna a gefenta ta rumgumeta tana lallashinta itama kukan take yi.

"Baɗɗo Baffa."

"Baffa."

Take faɗa tana wani gunjin kuka.
Hankalin kowa ya koma kanta.

"Ki daina kuka ki yi masa addu'a."

"Jiya fa mu ka gama waya da shi."

"Wayyo Allah Baffa."

Kuka har da ƙaraji daidai lokacin da su Hamma Jibo suka fito shi ya shiga falon Ammah ya ce ita da Mami su taho su yi ma Baffa bankwana za a fita da shi a yi masa salla.
Ammah ta miƙe Ummin ikki na rike da ita tare da Gimbiya Shahida da su Fulani.

Umma Balki ta riƙe Mami tare da su Umma A'i.
Suka fito Ummu Salma kuma Hamma Jibo da kanshi ya riketa ta miƙe suka tafi ɗakin Baɗɗo ta rufa masa baya.
Su Baffa Umaru duk sun fito, wasu suna ta cewa za su shiga ana cewa in iyalansa sun gama sai su shiga su yi masa addu'a.

Duka ya'yan Baffa har da Lamiɗo da Mai martaba da su Fulani sai Hamma Jibo ya leƙa yace su Adda Suwaiba su shigo tare da su Saudat masu hankali.

Haka ya'ya da jikoki suka zagaye gawan Baffa.
An fara koke koke liman ya tsawarta. Ya ce a yi masa addu'a babu kyau ka tasa mamaci kana yi masa kuka.

Kowa kukan zucci wasu kukan na fidda sauti.
Mami kuka har da majina ta kamkame Baffa tana kuka.

"Baffa me ya sa ka tafi ka bar ni?

"Lokacin da na rasa su Gwaggo ban yi kukan maraici ba saboda ina dakai, me ya sa za ka tafi ka bar ni?

Duk wanda ke ɗakin nan ya tausaya ma Mami, da Umma Salma itama kamar za ta shiɗe sai da Lamiɗo ya riketa har Bilkisu tana ɗakin itama har hawaye sai dai ta yi ba mutuwar wani kake yi ma kuka ba, taka mutuwar kake yi ma kuka.

Ammah ce ta ba ma kowa mamaki ba ta yi kuka ba.
Amma har Hamma Jibo ya yi hawaye.
Su Saddam kamar mata kuka share share.

"Allah ya jiƙan ka Baffa. Tun zamana da kai ba ka taɓa mugunta mini ba. In ma ka yi a cikin kuskure na yafe maka, baƙin cikina ɗaya da ka koma ga Allah ban nemi gafaranka ba."

"Allah ya jikanka. Ubangiji ya sada ka da rahamarsa. Allah ya haskaka makwancinka ayyukan ka na alheri ya bi ka har kabarin ka. Na gode Na gode Alhamdulillah."

Daga nan kawai ta tashi ta fita, ta bar su Ummu Salma ta shesaheƙa.
Sha ɗaya har ta gota da mintina sha biyar mutane na ta jira a waje.

Lokacin da za a fita da gawar Baffa Mami ta ƙamƙame makaran har tsakar gida tana kuka.
Ummu Salma kuma Gimbiya Shahida ta karɓeta daga Hannun Lamiɗo ta hana ta fita ta zaunar da ita ga ciki a jikinta kar ta miƙe ta faɗi.

Dakyar aka samu aka ɓambare hannun Mami daga makara aka fita da Baffa daga gidan duk matan sun miƙe tsaye masu kuka na yi da masu hawaye.

"Allah ya jikan ka."

"Allah ya sada ka da mala'inkun rahama."

Hamma Jibo ya dawo yana faɗin a cikin mata waɗanda za su yi jana'iza su yi alwala su fito. Anan ƙofar gida za a yi masa salla.

Kowa ko ya tashi yana neman ruwa domin alwala wasu kuma daman da alwalansu.
Sai ga shi yau Fulani ce ke ta lallashin Mami tana ba ta baki.

Har ta daina kuka da murya sai hawaye.
Ta ce in za ta iya ta yi akwala ta sallaci gawan ɗan'uwanta ta ce za ta iya.
Ammah ko kowa mamakinta yake yi ta dake ta yi jarumta tuni har ta yi alwala ta fita tare da su Ummin ikki.

Ummu Salma ma ta ce za ta iya. A ɗakin Ammah ta je ta yi alwala ta saka hijabi a saman doguwar rigar jikinta su Adda Suwaiba daman da alwalan su.
Rabin matan dake gidan sun fita sun sallaci gawan Baffa.

Maza na gaba da tazaran taku goma haka matan suka kafa sahu a bayan su. Baffa ya yi jama'a Ubangiji ya bamu irin tashi.
Limamamin masallacin da Baffa ke salla me ya yi masa salla. Mutane maza da mata suka sallace shi, akwai Mai Martaba sarkin Daura tare da Waziri da Shamaki.
Akwai wakilan Gwamman jahar Adamawa tunda tawagan Gwamnan ne suka zo filin jirgi suka ɗauke su.
Ga zaratan yaran Baffa kaf ɗin su.
Received at 09:16
11 people reacted with ❤
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ga yan anguwa abokan kasuwanci da waɗanda ma ba a yi tunanin zuwan su ba. Cikin su kuwa har da Habib tsohon mijin Ummu Salma a cikin dubban mutanen da suka sallaci gawan Baffa.

Makabarta da ɗan tafiya amma a ƙasa aka ɗau hanya. Shike nan an yi an gama.
Mata suka koma cikin gida suna kuka
Mami a haraba ta faɗi a sume aka ciccibeta zuwa cikin gida aka watsa mata ruwa ta farfaɗo tana ta kuka gwanin ban tausayi.
Ammah na zaune kanta a sunkuye ta kasa kuka amma zuciyarta na ɗaci tana jin kamar itama za ta iya bin Baffa saboda halin da take ciii.

Ummu Salma kuma Gimbiya Shahida da Baɗɗo na kafa kafa da ita, suna riƙe da ita kar su saketa ta faɗi domin sai layi take yi kamar ma ba ta iya tsayuwa da kafafunta hawaye kawai ke fita babu sautin kuka.

Cikin gida suka koma a falon Ammah suka zaunar da ita.
Gida ya cika danƙam da jama'a ana ta koke koke.


Ubangiji ya sa mu yi kyakyawan ƙarshe.



*Janafty*
Received at 09:16Reactions: 😭 34, ❤ 8, 😢 7
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
*FJ littafin kuɗi ne 1k a manhajar Telegram tura kuɗin karatu ta wannan acct ɗin 9069067488 Opay Jamila Umar shaidar biya ko tuntuɓa ta waɗannan lambobin.*
08032773332
09069067488.

Lokacin da za a sanya gawar Baffa a cikin Kabari aka ce ƴa'ƴansa su haɗa hannu wajen saka shi Hamma Abdullahi ƙasawa ya yi saboda hawaye da majina haka suke zuba masa, Saddam da Abdulrahim ma sun kasa suna dai tsaye suna kukan zucci da hawaye.

Hamma Jibo ne da Hamma Mustapha sai Lamiɗo

Please Login or Register in order to submit comment