Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

har su Baffa Umaru Hamma Abdullahi ya ce tafiyar mota za su yi gabaɗaya su mazan a daran Jumma'a za su isa a yi taron naɗi ranar asabar, lahadi litini su dawo gida ba shikenan ba.

"Shike nan, kuwa amma ni ina gida ba zan je ba"

Gabaɗayansu suka kalli Ammah, sun ɗauka ta daina maganar cewa ba za ta je ba

"Ammah za ki je mana, Hamma Lamiɗo ba zai ji daɗi in ba ki je ba."

In ji Hamma Abdullahi, Hamma Saddam na ta faɗin Ammah sai fa kin je tana faɗin to ubana.

"Ammah Hamma ya ce da ke za a zo fa."

Ummu Salma ta faɗa tana kallon ta.

"To in ma ba ta je ba gida fa ba kowa."

In ji Baɗɗo.

"Za ta je ma in sha Allahu."

Hamma Abdulrraham ya faɗa yana danna wayarsa.
Received at 15:21Reactions: ❤ 14, 👏 2
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
"Me zan je na yi? Fatan alheri ne, na yi ma Lamiɗo a waya duk waɗanda ya kamata za su tafi ni ba sai na je ba."

Ammah ta gama ta faɗa tana jadaddawa amma ba ta rantse ba.

"Kowa fa zuwan shi na dabam, Ammah ke ce uwar Sarki ce kin ga ko zuwa Daura Dole "

In ji Hamma Saddam yana dariya.

"Mami fa a matsayin uwar Auta za ta je gwara ki je, ke ma ki yi capacity a matsayinki na wacce Sarki ya fi darajawa a duniya "

"Gaskiya Ammah sai kin je, haba ya ma za a yi ba ki je ba ai sai Hamma ya ce duk mu ba mu da amfani in har bai gan ki ba."

Hamma Saddam ya faɗa yana girgiza kai, har yana haɗa hannayensa yana riƙon Ammah ta je kar ta ce ba za ta je ba.

"Kai ba zan je ba, kar ka dame ni."

Ammah ta gwale shi, Baɗɗo ta saka baki Ammah ta ce ba za ta je ba ta ñaɗa Ummin ikki ga su Umma Balki ba sai ta je ba.

Kowa ya yi shuru ganin ta dake, Ummu Salma ta ce a zuciyanta Allah ya jiƙan Baffa da yana raye shi zai tankwasa Ammah sai ta je amma tunda ba shi Lamiɗo na raye shi ne kawai in ya yi magana da ita za ta amince.

"Ammah Hamma ya ce tare dake zamu taho "

"Shima zan faɗa masa dalilina."

Ammah ta faɗa alamun da gaske take yi, sai kowa ya yi shuru domin anan dai ba wanda zai tursasata ta amince, Ummu Salma ta kira wayar Lamiɗo ta shiga amma bai ɗauka ba sai ta tura masa saƙon text massages da cewa Ammah ta tubure ta ce ba za ta zo ba, ya kira waya ya yi magana da ita.

Daga baya ma sai aka bar maganar. Falon ya zama kowa da abokin hiran shi, ita Ummu Salma da Baɗɗo suke hira tana nuna mata irin ɗinkin da Mami ta turo mata ta ce a I.g ta gani ko a yi mata a leshinta ne Baɗɗo ta ce ɗinkin ya fita gaskiya a yi mata irin shi, itama ta ce shigen shi ta ba da a yi mata a wani ɗaya daga cikin leshinta na lefe suna ta kuskus ɗin su Hamma Saddam da Hamma Abdulrahima ma sun haɗa kai suna kallon wani abu a wayar Saddam ɗinm

Hamma Abdullahi ne da Hamma Abdulrrahaman suma suke hiran su, Ammah ta yi shuru kawai tana tunanin Allah ya taimaketa ma ba ta da hawan jini amma da a halin da ta shiga na damuwar rashin Baffa da tana da shi da yanzu ta faɗi, Allah kuma ya taimaka daman ita ɗin Jaruma ce.

Sun daɗe suna hira sai goma da rabi suka watse a bangaren Ammah.
Su Hamma Abdullahi suka yi sallama suka tafi gidajen su Baɗɗo ta wuce bangarenta ita da mijinta haka ma Hamma Saddam Ummu Salma ta karɓi Banafsha ta shiga ciki itama Ammah ciki ta shiga ta yi shirin kwanciya.

Sai da asuba Ummu Salma ta ga saƙon Hamma Lamiɗo.

"Ammah za ta je Daura in sha Allahu."

Kuma ta duba ba ta ga kiran shi ba, ita kaɗai ta yi ta tura baki tana kunƙuni ta yi kewarsa, kewarsa na murƙukusan mata zuciya da gangan jiki haƙuri kawai take yi sama da kwana ashirin ba ta gan shi ba Banafsha ba ta ji ɗumin babanta ba tunda ta zo duniya.

Da gari ya waye ranar laraba kenan bayan ta yi wanka Ammah ta yi ma Banafsha wanka suka shirya. Breakfast Baɗɗo ta ba su ita ke girki tana ba ma Ammah yanzu Harira ce ke taya ta aikace aikace gida kamar shara ko wanke wanke.

Tare da Baɗɗon suka fita zuwa wajen Saloon Ummu Salma ta yi driving ɗin su a motar Lamiɗo.
Zuwa wani ƙaton shagon saloon suka je mai kyau booking Ummu Salma ta yi musu har da gyaran kafa za a yi musu Harira dai wanke mata gashin ta aka yi ta ce kitso za ta yi, ita ce ke renon Banafsha.

Suna can shagon har bayan azahar an gama musu gabaɗaya suna ma shirin tahowa ne ma sai ga wayar Lamiɗo.
Ta yi mamakin kiran shi da rana tsaka haka.
Yanzu ba H. lamiɗo ba ne tuni ta goge ta mayar da shi Hamma na.

Yanzu ma jikinta na rawa ta ɗaga kiran na shi cikin zumuɗi.

"Hamma na."

"Ranki ya daɗe."

Ya faɗa cikin kasaitar shi wanda da yanzu kamar ma ya fi na da.

Sai ta ji kunya, ita fa mantawa take yi da yanzu Hamma Sarki ne sai ta dinga ganin kamar komai bai sauyawa ba.

"Ayi mini afuwa ranka ya daɗe"

Ta faɗa tana mirmishi gefe ta koma tunda Baɗɗo ta ga tana dariya a fili ta furta mai Daura ne.

"Kina ina?
Received at 15:21Reactions: ❤ 14, 🥰 1
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Abin da ya faɗa kenan ta amsa masa da cewa suna shagon Saloon ita da Baɗɗo sai ya tambaya za su koma gida wuri ne? ta ce sun gama ma, ga su nan a hanya daga haka ya kashe wayar ta ɗauka ma za su yi magana ne jin ba ta gida shi ya sa ya kashe.

Nan ta ce su tashi su tafi ATM ta ba da aka cire kuɗin masu yawa tunda speacial booking suka yi sannan mai tsada ne Saloon ɗin da aka yi musu.
Sun taho ma suna hanya Ammah ta kira wayar Baɗɗo tana ta faɗan sun je sun zauna ta kira wayar Ummu Salma ba ta samu ba ahalin ta san ana jiran ta.

Da Baɗɗo ta faɗa mata abin da Ammah ta ce sai da ta yi mamaki.

"Ana jirana? Waye ke jirana?

Ta tambaya cikin mamaki, lokaci ɗaya tana mayar da hankalinta wajen tuƙi.

"Ban sani ba haka dai ta ce."

"Ko baƙi kika yi?

"To ƙila masu zuwa barka ne mu ƙarisa gidan"

Suna zuwa gidan a waje Ummu Salma ta yi parking ɗin motar in wani cikin su Hamma Saddam sun dawo sai su shigo da ita.
Suna shiga haraba suka ga wasu manyan jifa jifai baƙaƙen motoci guda biyu, ga dogari guda ɗaya da ɗan sanda sai wani mai suit.

Mamaki ya kama su, Ummu Salma na ganin kayan jikin dogarin Daura ta faɗo mata arai sai ta kalli Baɗɗo tana faɗa mata baƙi ne daga Masarauta
Suka rankwafa suna gaishe da Ummu Salma ta amsa sannan suka shiga cikin gida.

Takalmin maza suka gani a ƙofar ɗakin Ammah takalmin mai kyau ne irin na masu Sarauta Ummu Salma ta kalli takalmi sannan ta juya tana kallon Baɗɗo.

"Hamma ne"

Ta faɗa da sauri kafin ta yi saurin faɗawa falon Mami har mayafin ta na yin ƙasa,
Zuciyanta na bugawa, wanda take tunanin ganin shi ne ta gani, yana zaune a saman kujera cikin alkeybba da rawani ga wata sanda a hannun shi irin ta masu mulki, rawanin shi fari ne har bakinsa da hancinsa ba a gani idanuwansa ne kawai a waje. Ammah na gefen shi itama a saman kujera ta sadda kai ƙasa kwarjininsa da ƙamshin turaren sun cika falon gabaɗaya.

Cak ta tsaya ta kasa gaba ballatana baya. Ba ta taɓa tunanin za ta ganshi a wannan lokacin ba.

Baɗɗo da Harira suka shigo ai ganin shi ya sa Harira ta yi ƙasa tana gaisuwa.
Baɗɗo ma ta rankwafa Sarki ne fa ba abun wasa ba ne. Allah ya sa Banafsha na bayan Harira a goye

"Kika tsaya ma mutane a kai kuma."

Ammah ta faɗa tana hararan Ummu Salma ganin ta tsaya kawai ta kafe Lamiɗo da idanuwana shima kallonta yake yi ta cikin rawaninsa yana jin zuciyarsa na yin ɗumi.

Daman ya ce ba zai faɗa mata ba, bai yi tunanin zuwan na shi zai tabbata ba ne. Sai ga shi kuma ya tabbata irin yadda kewar Ummu Salma ya yi masa rugu rugu in zai furta ma ba za a amince ba.

"Ki ƙariso ki gaishe shi, sun fi awa da zuwa kina can kun fita tun safe ba ku dawo ba."

Ammah ta sake faɗa tana sake hararan Ummu Salama.
Da ta kasa ma tafiya kafafunta na rawa itama ƙwarjini Hamma ya yi mata sosai sai ta ke jin sa kamar baƙo a gare ta.

Da ƙyar ta samu ƙarisawa gaban shi, sai kawai ta ji ƙafafunta sun rinjayeta ta zube a gaban shi.

"Hamma"

Sai kuma da ta faɗa ta tuna da sauri ta rufe bakinta tana kallon Ammah dake hararanta.

"Ranka ya daɗe."

"Sannu da zuwa."

Ta faɗa a rarrabe sai kuma ta sadda kanta ƙasa tana wasa da gefen mayafinta.
Yana kallonta yana jin wani iri a jikinsa Ummu Salma ta canza ya ji daɗin ganinta ta yi kiba.

"Mun same ku lafiya?

Ya faɗa a ginshiƙe muryansa a kausashe kamaar yadda ya saba amma wannan karon a ƙasaice.

Ta amsa da lafiya lau tana satar kallon shi.
Ammah ta mike ta isa ga Harira ta karɓo Banafsha.
Ta kai ma Lamiɗo har in da yake zaune ya karɓeta yana yi ma Ammah sannu tana ba shi ta bar bangaren daman Baɗɗo da Harira sun fice, suna bangaren Baɗɗo ita kuma Ammah sai ta shiga kitchen ɗin tsakar gida kamar za ta yi wani abu nan ko ba abin da za ta yi, ta ba su damar ganawa ne.

Bayan fitan Ammah Lamiɗo ya ajiye sandar hannunsa a gefe ya riƙe Banafsha dakyau a cikin jikinsa yana kallonta barci take yi amma kamar ta sani sai da ta farka tana ta cilla kafafu irin na jarirai ya saka ɗan yatsan shi na hannun dama a cikin na ta yatsan na hannun dama yana kallonta da wani irin soyayya ta ɗa da mahaifi.

Ummu Salma na zaune tana satar kallon shi tana mirmishi farinciki ya cika ta.
Received at 15:21Reactions: ❤ 12, 👏 2
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
"Hamma ka daɗe da zuwa ne?

"Shi ne ba ka faɗa mini ba?

Ta gama fada har tana zumbura masa baki ya kalleta sau ɗaya ya kawar dakai in tana masa wannan shagwaɓar da za ta saka ya kasa riƙe kansa.

"Tafiyar ce sai yau ta tabbata."

"Na fara sauka a fadar sarkin Adamawa ne, ba daɗewa zan yi ba yanzu za mu tafi amma zamu biya gidan Gwamna kafin mu tafi."

Ya gama faɗa yana sake wasa da hannun Banafsha dake hannunsa.

"Na zo ganin ku ne."

"Ke da takwaran Mami."

Ya furta cikin wani irin amo, amon da ya shiga jinin jikinta ya sakar mata wani kasala.

"Na gan ku."

"Na ji daɗi."

Ya gama faɗa ya ɗan kallon Ummu Salama.
Itama shi take kallo cikin wani yanayi.

"Come here."

Ya furta yana cigaba da kallonta, sannan lokaci ɗaya yana nuna mata gefen shi, kamar daman tana jiran ya furta ta tashi da sauri ta ƙarisa gare shi ta zauna a gefen shi, tana zama ta rinjayi jikinta zuwa gefen kafaɗan shi lokaci ɗaya tana kwantar da kanta a kafaɗar na shi a saman alkeybban jikinsa da rawaninsa.

"Na yi kewar ka."

Ta gama faɗa tana turo hannunta ta sagalen hannayen shi ta riƙe shi, ga shi gidan ba kowa su Hamma Saddam duk suna wajen aiki.

Kallonta ya yi ta cikin rawaninsa.

"I miss you too.'

A kalaman shi, ta ji gaskiyan abin da ya faɗa.
Ta yi masa mirmishi, ta kalli Banafsha, dake hannunsa itama sai ta miƙa yatsunta suka sarke yatsun yarinyar a tare sau uku.

"Ka ga takawaran Mami ko?

Ta furta tana kallon shi, ya ɗan gyara zaman shi kaɗan. Ya saka hannu ya kama hannun Ummu Salma, sannan suka kama hannun Banafsha a tare suka jimƙe.

"Na ganta. Kin iya haihuwa. Allah ya raya mana ita. Ubangiji ya yi mata albarka ita da sauran yan'uwanta gabaɗaya."

Ta amsa da Amin Amin. Ummu Salma ta ga hannuwansu ya yi kyau sai ta kalle shi.

"Hamma ina wayarka?

Kafin ma ya yi magana ta ji tudun waya a jikin rigar saƙin dake jikinsa nan ta zura hannu a cikin akeybban ta zura can ta ciki ta ɗauko wayar.
Ta ga akwai password kafin ta tambaya ya faɗa mata shekaran haihuwansa ne.

Ta buɗe wayar ta ɗauki hannayensu hotuna, sannan ta yi musu selfie.
Ta haɗe kanta tare da na Lamiɗo shi yana cikin rawani ta ɗauke su a tare.
Sannan ta tashi tsaye ta ɗauke shi yana rike da Banafsha sai da ya gaji ya ce mata ta zo ta zauna sun kusa tafiya sannan ta haƙura da hotunan ta dawo ta zauna

"Me kika za a dinga kiran ta?

"Banafsha."

Ya kalleta amma bai yi magana ba ta fara masa bayanin sunan mai kyau ne duk da ta faɗa masa ta chart wataƙila ma hankalin shi bai kai can ba. Tunda yanzu abubuwa sun ƙaru.

"Banafsha."

Ya maimaita sunan sai da gefe da gefen bakin shi ya motsa.

"Nice name."

"Sunan ya yi daɗi Baɗɗo ce ta zaɓa mata."

Ya jita amma bai yi magana ba

"Ba yau su Anty Bilkisu za su je Daura ba?

"Su na can ma"

Ta kalle shi cikin mamaki. Ta san dai a yau ɗin za su isa amma ta yi mamakin ashe sun isa da wuri.

"Jirgin safe suka biyo."

Ya sake amsa mata tambayarta tun kafin ma ta yi tambayar.

"Allah sarki muma gobe muna tafe."

Ya tambayeta tsarin tafiyar ta fara masa bayani.

"Akwai jirgin da za ku bi da ƙarfe goma na safe, mutane ashirin kawai sauran akwai mota."

Ta amsa mishi da cewa su Hamma Abdullahi sun ce a mota za su isa Daura ranar Jumma'a.

"Me ya sa?

"Sun ce suna son ganin gari."

Ya ɗan jinjina kai.

"Ba wata matsala?

"Babu komai Hamma."

"Are you sure?

Ya sake tambayata sai ta amsa masa da cewa komai suna da shi sun siya.

"Allah ya saka da alheri."

Ya amsa da Amin a saman labɓan sa.

"Ammah fa ta ce ba za ta je ba "

"Na yi magana da ita. Za ku taho tare in sha Allahu "

"Ta amince?

Ta tambaya tana ɗan ware idanuwana.
Ya lumshe idanuwana ya buɗe.

"Uwata ce fa, za ta je ta sanya mini albarka."

"Haka ne ɗan Ammah"
Ta faɗa tana dariya hakoranta sun bayyana a waje ya shagala da kallonta.
Itama shi take kallo zukatansu na fizgansu akan junan su.

Ummu Salma ta bi shawaran zuciyarta ta barta ta rinjayi gangar jikinta sai ga shi ta na sumbatar gefen fuskar Lamiɗo, ya juyo ya kalleta ta sumbaci bakinsa ta cikin rawani.

Ya kanƙance idanuwana yana kallonta.

"Kar ki taƙale ni."

"Ba anan ba."
Received at 15:21Reactions: ❤ 12, 😁 2
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ya furta a rarrabe, ba ta ƙyale shi ba sai ji kawai ya yi ta tallabo kan shi ta zare rawanin ta yi kasa da shi, yana mata gargaɗi da idanuwansa ta yi kamar ba ta gani ba ta fara sumbatar bakin shi, shima kamar yana jira ya tarbi harshenta ya kuma saka hannu ya riƙe kugunta da hannu ɗaya, dayan hannun kuma ya riƙe Banafsha kar ta faɗi.

Sai ga Mai Daura da Sarauniyar Daurama suna masu sumbatr juna cikin shauƙi da soyayya a falon Ammah, na sama da mintina biyar sannan Ummu Salma ta saurara ta lafe a ƙirjinsa tana mayar da numfashi. shima numfashin yake mayarwa a jere amma shi a saukaƙe yana so ya daidaita yanayinsa.

"Kin cire ma Sarki rawani ko?

Ya faɗa yana jin zuciyarsa na matsewa waje ɗaya.

Yar dariya ta yi amma ba ta yi magana ba.

"A gaban ɗiyata kike sumbata na Ummu Salama?

"Muke sumbatar juna dai?

"Kuma a falon Ammah na."

"Ni ba ruwana, har da kai."

"Sai da na ce kar ki yi. I warned you kafin ki fara."

"Da na fara ai ba ka ture ni ba."

"Kenan kana so?

Ta faɗa tana kallon fuskar shi.

"Ina so."

"Sosaii.. ."

Ya ja sosai ɗin yana jin wani iri, yana buƙatarta amma kuma ba lokacin hakan ba ne yanzu.

"Ai Anty Bilkisu na nan yau."

Ta faɗa tana ƙoƙarin danne yanayinta.

Sai ya yi kamar bai ji ba ya kawar da maganar da cewa ta gyara masa rawaninsa ta saka hannu ta ja sama ta rufe bakin da hancin.

"Ya yi? Kar Sarki ya ji kunya fa."

"Ba wani kunya ya yi kyau, har ya fi ma wanda ka zo da shi."

Ta gama faɗa tana danne dariyanta da gaske ya yi sakwa sakwa, tunda ya ga tana dariyan ya san bai yi kyau ba kawai ɗan girgiza kai ya yi bai yi magana ba.

Tambayan shi take yi za a tafin mishi da wasu kaya daga nan ya ce no Need.
Ita kam ta ce za ta tafi da wasu ya ce ta je da duk abin da take so.

"Ranka ya daɗe ina so Asabe ta dawo bangarena in mun koma."

"As you wish princess."

Ta sumbaci ƙuncinsa tana sake yi masa godiya.

"Mami sai jibi za ta taho daga Kaduna."

"Mun yi magana da ita."

"Mami ba ruwanta, ba irin Ammah ba ce. Na ce ga shi dai yau sila Mami za ta je Daura."

"Saboda ke ce."

Ya amsa mata kai tsaye.

"Ba saboda ni ba ne."

"A'a saboda ni da kai ne."

"Ummu Salama."

Ya kira sunanta ta amsa tana kallon shi.

"Mami ce surukata. Ammah is my mother that's the truth"

Ummu Salma ta fara dariya tana faɗin haka ka raba mana abin ya yi shuru ya ƙyale ta. kuma gaskiya ya faɗa Ita Mami a suriki ta ɗauke shi ba ɗa ba, Ammah ce uwarsa ba ta taɓa masa kallon suruki ba.

Biyu har ta gota ya ce za su wuce a gidan Gwamnati za su ci abinci su yi salla daga can za su wuce.

"Daga can Fadar Sarkin Adamawan aka tura aka ɗauke ku?

Ya amsa mata da gyaɗa kan shi, miƙa mata Banafsha ya yi, sannan ya miƙe yana gyara alkeybban jikinsa Ummu Salma ta taya shi sannan ta ɗauko masa sandar shi ta miƙa masa.

"Allah ya kara maka lafiya Hamma na "

"Amin Sarauniya ta."

Ya faɗa yana mai kallonta.
Sai ya ware mata hannu suka shige jikinsa ita da Banafsha da hannu ɗaya ya ɗan yi tapping ɗin bayanta sannan ya duka ya sumbaci Banafsha.

"Sai kun taho "

"Sai mun zo ranka ya daɗe."

Ta amsa masa suna mai sakin juna.
Ya yi gaba tabi bayan shi yana fita ya zura takalmin shi, lokacin da suka iso dogarin da suka zo tare da jami'ai sun babbake za su shigo har cikin gida ya hana su nan ɗin gidan su ne, ba ya buƙatar nuna shi sarki ne, tafiyar daman cikin sirri ya yi ta, shi ya sa bai taho da tawaga ba. Mai martaba mai murabus ya ce ya je tare da Jakadiya ya ce ba sai ta je ba. Saleem ya bari da fada kafin ya dawo. Ummu Salma za ta yi fushi da shi, in bai zo ba kuma ko ya yi bayani ba za ta gane ba. Sai kuma ga daman zai kai gaisuwa wajen Gwamna da fadar Adamawa yanzu alaƙa ta ƙullu tunda ya zama Sarki ya zama dole ya fara sanin mutane sosai.

Ammah na kitchen ɗin tsakar gida tun kafin Ummu Salma ta kira ta sai ga shi ta fito daman da hijabi a jikinta. Lamiɗo ya ce za su tafi yanzu.

"Allah ya tsare Allah ya kai ku lafiya."

"Amin Ammah sai kun zo."
Received at 15:21Reactions: ❤ 15, 🥰 1
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ta amsa da in sha Allahu
Ya yi gaba yana tafiya cikin ƙasaita Ummu Salma na bin bayan shi amma sai ta lulluɓe mayafinta a saman kanta tana rike da Banafsha suka fita haraba dogari na ganin su ya taso ya tare su da Baban rigan shi.

"Hattara dai, takawarka lafiya bajimi na al'ummar Daura. Barka da fitowar dogon sarki barka da fitowa farin Sarki ɗan Nasiru jikan Shitu Allah ya kara maka lafiya da tsawon kwana."

Haka ya kare su suna tafiya har wajen mota da tuni masu kaki suka buɗe masa jeep ɗin guda ɗaya.

"Hamma ba ka ga Saloon ɗin da na yi ba."

A lokacin Ummu Salma ke masa raɗa ya kalleta ya ɗan murmusa amma saboda yana cikin rawani ba ta gani ba

"In kin zo sai na gani "

Ya amsa a hankali wanda ita kaɗai za ta ji.
Ya kalleta ya ɗan rausayar dakai. Sannan ya shiga mota.

Sai lokacin dogarin nan ya saki rigar sa. Ta yi baya tana ɗaga masa hannu dogarin ya shiga gaban motar Lamiɗo da direba a ciki mai suit ya buɗe get suka fita shi ɗayan jeep ɗin daman ta masu kaki ce sai da suka fita ya dawo ya rufe get ɗin sannan ta koma cikin gida tana mai farinciki.

Wannan zuwan da ya yi ya gama wanke mata zuciya. Ko da bai zo ba, ba za ta yi fushi ba amma zuwan sa ya sa ta samu tabbacin Ummu Salama na da capacity.

Lokacin da suka bar gidan Gwamna ya kira ta ya ce suna filin jirgi bayan la'asar lokacin ma Balkisu mai ƙunshi ta zo gida za ta yi musu tunda da safiyar gobe za su wuce Daura.

Masu kunshi har biyu suka kira bayan Balki tunda su Adda Suwaiba sun taho gidan za a yi musu ga Maijidda za ta yi kitso har da Ammah za ta yi kitso ƙunshi ta ce ba ta so lallaɓe za ta yi su Adda Suwaiba na yi mata magiya. Kowa ya ji Hamma Lamiɗo ya zo sai ya yi ta mamaki haka ma su Hamma Saddan sun ciji yatsa da ba sa nan.

"To ya kika gan shi?

Hamma Saddam ya tambayam

"Ya zama babban mutun ya kara ƙwarjini da Haiba."

Ta ba shi amsa tana mirmishi.

"Ya yi kyau a cikin rawaninsa."

Ta faɗa tana wani lumshe idanuwana sai da Baɗɗo ta kai mata duka a baya.

"Muguwa Sarauniyar garin Dauran kike duka.?

"Gwara ta dake ki, kina neman suma saboda Lamiɗo"

Adda Suwaiba ta faɗa ana ta dariya. Hamma Saddam na faɗin shifa ya gama shirinsa gobe sai tafiya ana ta dariya.

Shi ya ɗauki Harira a mota ta je can gida ta kwaso ma Ummu Salma kayanta na masu amfani akwati biyu ta kawo mata, domin ta ce ba za ta bar kayan rikita maigida a Jimeta ba da shirinta za ta je Daura.

"Sarki ne ba Yarima ba kuma haramu ne ki rikita Sarki."

Baɗɗo ta faɗa tana dariya.

"Ni ba Sarki na sani ba mijina na sani. Kuma in Sarki ne a fada ni a cikin bangarena ni ce Sarkin."

"Capasicitated Autar Ammah"

Adda Ummu Sulaim ta faɗa tana dariya har suna tafawa da Ummu Salma.
A tsakar gida aka baza tabarmu ana ƙunshi Maijidda na ɗaki tana yi ma Ammah nata.

Ƙunshi nan har dare ba a gama ba. Su Maijidda sai sha ɗaya na dare suka bar gidan sun sha kuɗi har Ammah an yi ma jan ƙunshi, Ummu Salma ja da baƙi aka yi mata ta yi kyau har ta gaji da kyau.

Washegari da sassafe su Umma Balki da Umma A'i tare da ƴa'yan Umma Salamatu Adda Hauwa da Adda Khadija suka iso. Baffa Umaru sai da yamma za su taho tunda tafiyarsu sai safiyar Jumma'a.

Jirgin ƙarfe goma ne kafin goman kowa ya hallara.
Mutane ashirin ne daman za su bi jirgin. Tuni Ummu Salma ta tura ma Gimbiya sunayen masu tafiya a jirgi.
Ammah, Ummu Salama, ga mutanen mubi mutum huɗu, ga Baɗdo su bakwai.
Ga Adda Suwaiba da Adda Ummu Sulaim, ga Ummin ikki ga iklima ga Kaltume ga Harira su goma sha huɗu, ga Adda Aisha suma da safen suka iso sai Hamma Saddam sai sai yaran Hamma Mustpha, Babban mai sunan Mami sai kuma Zainab.
Su Adda Suwaiba a gidan iyayensu suka bar yaran su.

Hamma Abdulrahim da su Hamma Abdullahi ne suka kwashe su zuwa filin jirgi.
Kafin su tashi sai ga Shamsiya ta kira wayar Ummu Salma bayan sun gaisa ta ce Habib ya ba su izinin tahowa Daura.
Ummu Salma ta ce su yanzu ma suna filin jirgi za su tafi akwai mota bari ta yi magana ta ji yadda ake ciki za ta kira ta.

Baɗɗo ta ja gefe ta sanar da ita wayar su da Shamsiya.
Received at 15:21Reactions: ❤ 10, 👍 1
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
"Ai ni da gayya na ce su zo, akwai mota

Please Login or Register in order to submit comment