Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ku je?

"Ni kaɗai, Harira za ta raka ni."

"Baɗɗo fa ko kuma Umma Balki ta raka ki."

Mami ta faɗa tana kallonta.

"To."

Kawai ta ce tana kauda kanta.
Ba haushin Mami take ji ba kawai itama ta san tana bayan masu cewa ba ta kyauta ba. E ta san maganganun da ta faɗa ma Ammah ba ta kyauta ba, wannan ta yarda ta kuma karɓi kuskuranta amma a kan maganar Lamiɗo tana da ja akan masu cewa ita ce ta yi masa laifi.

"Ummu Salma."

Mami ta kira sunan ta lokaci ɗaya tana matsawa kusa da ita har tana riƙo hannuwanta.

"Ɗago ki kalle ni nan."

Ta ɗago idanuwanta tana mai kallon Mami.

"Ki yi haƙuri ki daina damuwa. Baffa addu'a za mu yi ta masa, maganar Hanan kuma ki kwantar da hankali babu wanda ya isa ya karɓe ta daga hannun ki."

Idanuwan Umma Salma suka kawo ƙwalla suka kece mata a saman kumatunta.

"Mami yau kwana huɗu amma ba su dawo da Hanan ba."

"Za su dawo da ita, in ma ba su dawo da ita za a je a ɗauko ta."

Mami ke share mata hawaye da tafin hannunta.

"Ke da za ku koma Lagos da zaran Muhammadu ya dawo, tare da ɗiyar ku za ku koma in sha Allahu.'"

Hankalinta ya ɗan kwanta ta tabbata koma me zai faru Mami tana tare da ita.

Ba za ta koma Lagos ba sai Hamma Lamiɗo ya janye kalamansa in kuma bai janye ba ta rantse da wanda ranta ke hannun shi ba za ta bi shi ta koma ba.
Mami ta sake lallashinta da cewa ta sake zuwa ta samu Ammah ta sake ba ta haƙuri.

"Ko ɗazu da safe ma na shiga na gaisheta dakyar ta amsa gaisuwa ta Mami."

"Ki sake zuwa ki ba ta haƙuri abin ne ya dame ta."

"Mami nima fa ba a kyauta mini ba."

"An ji ke ma ba a kyauta miki ba, amma ke ce ƙarama ke ce ba ki da gaskiya."

Sai kawai ta yi shuru.

"Uwa ce ita, duk wanda zai so ki da cigaban ki bayan ita ne."

"Haka ne."

"To ki sake zuwa ki same ta daga ke sai ita, ki sake ba ta haƙuri."
Ta amsa da to za ta je.

"Shi Lamiɗon kin kira shi?

"E bai ɗauka ba."

Ta yi ma Mamin ƙarya domin ita dai ba za ta kira ba.
Kawai sai Mami ta ɗau wayarta tana cewa bari ta kira shi.
Received at 11:37Reactions: ❤ 4, 👍 1, 🔥 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
*FJ littafin kuɗi ne 1k a manhajar Telegram tura kuɗin karatu ta wannan acct ɗin 9069067488 Opay Jamila Umar shaidar biya ko tuntuɓa ta waɗannan lambobin.*
08032773332
09069067488.

Tunda Hanan ta dawo ranar cikin salama da aminci Ummu Salma ta yi barci har da makara.
Tashin hankalinta daman a ce yau za a raba ta da Hanan amma tunda ta dawo gare ta, sai fargabanta ya ragu abin da ke gabanta kawai Hamma Lamiɗo ya dawo su yi ta ta ƙare.

Ba ta ma san a ranar za su dawo ba sai da suka yi waya da Fulani ta kira ta, domin ta gaisheta da jiki daman lokaci bayan lokaci tana kiran ta a waya. Ita ke faɗa mata Hamma Lamiɗon da Bilkisu suna tafe yau, bayan kuma sun gama wayar wajen bayan azahar Hamma Abdullahi ya zo ya karɓi key din bangaren Bilkisu a hannun Ammah ya ce Lamiɗo ya ce ya karɓi yana jin a gida za su fara sauka.

Tana falo ne a lokacin ta zo ɗaukan ruwa ta ji Hamma Abdullahin ya shigo suna magana da Ammah
Ɗaki ta koma abin ta, gwara ya dawo domin ta san matsayin ta.

Ko ya janye kalamanshi ko kuma ya cika abin da ya faɗa. Gidan shi suka wuce domin sai yamma suka zo gidan abin da ya kara baƙanta ma Ummu Salma zuciya bai neme ta ba tana jin shi a falo tare da su Ammah amma bai leƙo in da take ba. Itama ta yi kudirin ba za ta fita ta gaishe shi ba sannan ba za ta neme shi ba.

Sai Bilkisu ce ta shigo tare da su Sultan sai ta ga kamar ma Bilkisun dariya take yi mata lokacin da ta shigo ta ganta ta fito wanka ne ɗaure da towel tana yin wanka da safe da Yamma da ruwan zafi sosai Mami ta ce ta dinga yi har sai ta yi arba'in amma ba ruwan zafi sosai ba

Ta ga tana mata kallom sama da ƙasa tana dariyan fatan baki. Sai take tunanin me take yi ma dariya? Sai da ta fita ta kalli kanta a madubi ta fahimci abin da Bilkisu take yi ma dariya. Duk ta lalace fuskarta ta yi baƙi gashin kanta ya yi biji biji, ga tumbi da ta ga wannan haihuwar ya yi mata kumbiyu a jikinta. Hawaye suka cika kwarmin idanuwanta, duk a dalilin wa ta koma haka! A dalilin wanda ya ce zai iya sakinta bai damu da halin da take ciki ba. Dole kishiya ta zo tana yi mata dariya.

Baƙinciki da kishi suka rufe mata jin ta da ganinta sai da ta yi kuka ta samu salama.
Har kuma suka bar gidan bai neme ta ba Hanan ma bin su ta yi domin da ta fito ta ga ba ta gan ta ba Umma Balki ta ce ta bi babanta zuwa gida.

A tunaninnta in ya zo washegari zai neme ta amma ta ji shuru.
Ya zo gidan da yamma sannan suka fita da su Hamma Abdulrrahaman zuciyarta ba ta ƙara zafi ba sai da Umma Balki ta leƙo ɗakin da take tana ce mata ya ba ta ga tana shiri ba ne.

"Shirin me ne Umma Balki?

"Shirin tafiya mana, ko ba da ke za a koma Lagos ɗin a goben ba ne?

Kenan gobe za su tafi amma bai faɗa mata ba, kuma a tunanin shi ta shirya ta bisa bayan ya gama tozarta ta, ya ja mata dariyan kishiya.

Amsa ma Umma Balki ta yi da cewa kayanta a haɗe suke. Harira za ta haɗa mata sauran. Amma baƙincikin ya yi mata hawa hawa a zuciya.

Ba za ta bari sai goben ba a yau koma mai zai faru zai zo ƙarshe. Ƙarshen renin hankali ya gama yi mata.
Wato tunda shi yana da ya'ya ba zai damu don ta rasa jaririnta ba tuna haka kawai in ta yi kuka yake sakata yankata fa aka yi amma ba ta samu kulawa daga wajen wanda take tunanin ya fi kowa son ta ba.

Tana idar da salla ta jawo wayarta ta tura masa saƙo.
Tun wannan kiran da ya yi mata ba ta ɗauka ba, bai sake neman ta ba.
Shima kiran saboda Mami ne bai yi ra'ayi ba.

Kenan har gobe yana nan akan bakan shi ita ce mai laifi shi kalaman da ya faɗa daidai ya yi.

"Hamma ka ce za ka sake ni amma na ji shuru."

Sakon ya tafi da wajen mintina goma bai dawo mata da amsa ba.

"Abin da ka nuna na rashin damuwa da ni ya fayyace mini nufin ka a kaina. Kar ka damu ko ka sake ni ba zan tagyayara ba"

"Ina jiran ka, domin ba zan bi ka ko'ina ba."

Ta jira amsar shi shuru shuru har takwas ta gota sai ta tashi ta kabbarta sallar isha'i.

Tana cikin sallar wayarta ta yi haske tana idarwa gabanta na faɗuwa ta jawo wayar ta duba shi ne.

"Okay."

"Ki zo ki karɓa abin da kike so ɗin"

Abin da ya ce mata kenan da sauri ta tura masa tambaya.

"A ina?

"Bangaren su Saddam."
Received at 07:52Reactions: ❤ 6, 😁 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ko fita daga kan saƙon shi ba ta yi ta miƙe da Hijabin da ta yi salla ta fice.
Umma Balki ce kawai a falo tana salla Ammah na ciki, tana jin Umma Balki na uhm uhm da gyaran murya ta zura takalmin silafas ɗin dake ƙofar ɗakin Harira na kitchen tana wanke wanke sai da ta leƙo.

"Ranki ya daɗe ina za ki je?
Sai ta juya tana kallonta

"Hamma ke magana da ni a waje."

Sai ta jinjina mata kanta ko tsaya ma sauraranta ba ta yi ba ta wuce
Zuciya ce ke tura ta gwara ta san matsayinta.

A hanya ta haɗu da Saddam da Abdulrahim za su shiga cikin gida.
Ta tambaye su ina Hamma Lamiɗo?

"Yana bangaren mu."

Ba ta ma tsaya jin ƙarshen maganar ba ta wuce da sauri.
Suka bi ta da kallo ganin saurin da take yi cikin gida suka nufa ita kuma har tana haɗawa da gudu da gudu.

Akwai haske a bangaren tunda akwai nepa a lokacin.
Tana shiga falon shuru kamar ba kowa amma ta ji ƙamshin turaren shi tana ɗago idanuwa suka haɗu da na shi kallon mai kassara sauran kuzarinta.

Yana hakimce a saman kujera, sanye yake da ƙananun kaya wando baki rigar fara mai layi layin baki sannan tana da dogon hannu.
Kafa ɗaya kan ɗaya.

Ta daɗe ba ta gan shi ba, tun ranar da kalamansa suka ɓata komai.
Ta ga ya ƙara yi mata wani kyau da ƙwarjini ne

Cak ta tsaya ta kasa ƙarisawa domin mutuwar jiki ne ya same ta duk ƙarfin gwiwan da ta zo da shi ganinsa kawai da ta yi yana neman ya ruguza shirinta.

Saurin kauda kai ta yi idanuwanta na tara ƙwalla amma ba ta bari sun zu bo ba.
Shi kuma a hankali ya miƙe yana takun nan na sa na ƙasaita har zuwa gaban ta.
Ya tsaya lokaci ɗaya yana tusa hannuwansa a cikin aljihun wandon jikinsa.

Kafe ta da idanuwana ya yi yana kallonta kuma tana jin kallon a cikin jikinta.
Amma ta ƙi yarda su haɗa ido, kar ya yaudare ta da kallon shi ta ji kawai ta bar maganar ba tare da ta bi kadin wulakancin da ya yi mata ba.

Shi kuma Lamiɗo ƙura mata idanuwa yake yi sosai so yake yi ya fahimci ko tana da wata matsala ne! Domin abin da take yi ya yi kama da na wanda bai da lafiya

Abin da ta yi ma Ammah ya yi masa ciwo sosai, maganar da ya yi ɓacin rai ne da kishi amma har a zuciyansa ba haka ba ne ko giya ya sha ba zai iya sakin Ummu Salma ba. A lokacin dai ya ji in har ta fi son wani akan shi zai iya sakinta sai da ya tafi Daura tunaninta ya hana shi sakat daga nan ya gane ba zai iya rayuwa babu ita ba.

Ya fahimceta amma abin da ta yi ne ba ta kyauta ba amma ta kasa gane laifinta.
A zuciyarsa kawai in ya tuna da kalamanta sai ya ji yana fushi wai ita ke cewa ya sake ta ɗin mana sai me? Bai taɓa tunanin haka daga gare ta ba. Da farko ya yi fushi amma daga baya ya sauka ya yarda da maganar Mami tana bukatar kulawa saboda yanayin da take ciki.

Ya ɗauka da gaske ta yi nadama za su daidaita kan su, Sai ga shi ita ba haka take so ba tun a ranar da Mami ta ba ta wayar ya son rigima take ji ta ƙi magana sannan ta kashe wayar, ya kira wayarta kuma ya san tana gani ba ta ɗauka ba.

Shi kuma ya ba ta lokaci ne ba ya so yadda take cikin ɓacin rai ya sake nemanta a tunanin shi in suka koma can gidansu sai su zauna su daidaita kan su, ya dawo idanuwansa na kewar ganinta amma ba ta fitowa, yana da dalilin da ya sa bai neme ta ba ai shine a gaba da ita. Ita ya kamata ta fara neman shi a matsayin shi na namiji kuma mijinta.

Duk da haka ya sauke komai na shi ya yi niyyar a daran nan zai bita ya lallasheta ya ɗauketa su koma gida da safe kuma su bi jirgi zuwa Lagos.

Amma sai ga saƙonnin ta masu rikitarwa.

"Why Ummu Salama"

Yake faɗa a zuciyarsa duk da ranshi ya ɓaci ba zai biye mata ba. Gaskiya Mami ta faɗa tana bukatar lallashi duba da yanayinta. Duk da har Ammah cewa suka yi ya fita batun ta, ba zai iya ba ne duk mulkinsa da komai na shi zai rusuna mata in dai za ta haƙura.

"Ina saƙon?

Ya ji ta faɗa kai tsaye, sai ya ɗaga idanuwana yana kallon ta.

Har tana miƙa masa hannu.
"A takarda ka rubuta ko a baki za ka faɗa mini?

Mirmishi ya yi ta kasa ma kallon fuskar shi ashe ƙaryan rashin kunya take yi.

"Ba anan zan ba ki ba."
Received at 07:52Reactions: ❤ 6, 😁 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ya fada yana ɗan lumshe idanuwana sannan ya sake buɗewa a kanta sai da ta ɗan yi baya ta daburce.
Matsota ya fara yi ta jingina da bango

"Hamma ka tsaya fa."

Take faɗa tana kare shi da hannayenta.

Ko kusa da ita ma bai yi ba.
Giransa ya sosa yana ɗan mirmishi.

"Ni ba taɓa ki zan yi ba."

"Mu je ciki ki karɓa saƙon na ki."

Ya faɗa yana wucewa, ɗakin farko na jerin ɗakunan ukun dake falon ya nufa ya shiga, kafafunta suka lamkwashe saƙon me? Sakin na ta ya yi da gaske?

Ƙirjinta ya buga wani hadari ya ruguzo mata a saman kanta.
Ta kasa gaba ballatana baya domin kafafunta har sun yi wani gara gara.

"Ki zo ki karɓa mana?

Ya leƙo yana kallonta.

"Ko ba ki so ne?

Ya faɗa yana shafa sumar kansa. Daƙyar ta ja kafafunta ta bi bayan shi. Ita ce ta ce ya yi abin da ya furta amma barazana ce ba ta taɓa tunanin zai iya sakinta da gaske ba.

Wata zuciyar ta ce to sai me in ya sake ki? Kamar ta farka daga barci sai ga ta bi shi cikin ɗakin tana shiga ashe yana ta baya wajen kofa ganin ba shi a ɗakin tana shirin juyowa ta ji ya rumgumeta ta baya ƙamƙam ya hana ta ma juyawa.

Ta fara mutsu mutsun ƙwacewa amma bai ba ta dama ba ya kanannayeta sosai ya sagalo hannayensa ta wajen cikinta ya nitsata a cikin jikinsa kansa na wajen wuyanta yana sake tusawa gabaɗaya duk ya kashe mata jiki, har jikinta ya fara rawa.

"Ina..ina saƙon?

"Ga shi nan"

Ya faɗa yana sumbatar wuyanta.

"Ke a tunanin ki sai na iya sakin ki?

"Why Umma Salma?

Ya faɗa lokaci ɗaya yana sakinta sannan ya juyo ta suna kallon juna.

"Kin yi mini laifi amma ni kike horawa?

Ƙureta da idanuwansa ya yi, da ya sa ta kasa jurewan kallon shi.

"Kai ne ka ce za ka sake ni da bakin ka a gaban kowa da kowa."

Sai hawaye suka kece mata sharr.

"Menene laifina da za ka tozarta ni Hamma? Don kawai na ce kar a tafin mini da ƴa ta?

Sai kuka wiwi har da sauti ya yi shuru yana sauraranta.

"Na san na yi laifi maganganun da na faɗa ma Ammah ɓacin rai ne bana cikin yanayi mai daɗi amma kai abin da ka faɗa mini ya yi daidai?

"I'm sorry."

Ya faɗa a hankali yana riƙe hannuwanta duka biyun

"In kowa bai duba yanayina ba, kai fa? Ka manta Baffa fa na rasa sannan na rasa jaririna ko tausayina ba ka ji ba?

"Sorry."

Ya sake ba ta haƙuri, domin duk ya amsa laifinsa maganar ta wuce.

"Ka tafi ba ka sake nema na ba, ka manta da ni, ka manta da halin da nake ciki."

"Yiyiyiyi..."

Sautin kukanta, har da majina tana faɗa zafin abin na sake dawo mata sabo.

"Sorry, kina raina na kuma damu da halin da kike ciki."

"Ba ka damu ba, da ka damu da ka nuna kulawar ka a kaina."

"Haushi na ji, haushin maganganun da kika faɗa ma Ammah."

"Ai na ba ta hakuri."

Ta faɗa cikin kuka.

"Kuma nima ai ba a kyauta mini ba, ba a kyauta mini ba."

Kukan da take yi har ya yi yawa da sauri ya jawo ta jikinsa ya rumgumeta yana lallashinta da hannun rigarsa ya dinga share mata hawaye

"I'm sorry, ki yi mini afuwa."

"Sai ka janye kalaman ka na cewa za ka iya sakina."

"Na janye."

"A gaban kowa da kowa za ka faɗa."

"Done."

Ya faɗa yana sake shigar da ita jikinsa ya samu dai maganar ta wuce. Daga lallashi ya zarce da sumbata, ba ta wani ba shi haɗin kai ba sai ma ture shi da take yi amma ya nane mata sai ga su a saman katifar ɗakin Saddam sun baje, a nan komai ya wakana ba wani daɗewa tunda ba ta bada dama ba sosai.

Wanka ya shiga ya bar ta nan tana kuka, ya fito ya mayar da kayan jikinsa har lokacin ba ta daina kuka ba.
Ya ce ta tashi ta yi wanka cikin masifa ta ce ba za ta yi anan ba.
Sai ya ce to ta tashi ta saka kayanta sai ta je cikin gida ta yi wankan a can.

Ko a jikinsa da kukan da take yi. Sai ma wayarsa da ake kira ya ɗaga yanayin wayar kawai ta gane Bilkisu ce falo ma ya fita ya barta kishi ya tirniƙeta ta tashi ta mayar da kayan jikinta tana yi tana kuka ta zura hijabin ta kenan ya shigo ɗakin
Ganin yadda take yi ya sa dariya ta kama shi har tana sauti. Zuciya ta ciyo ta, ta kalle shi cikin hawaye tana faɗin

"Dole ka yi dariya mana dole na zama abin dariya."

Sai kuka wiwi, kamar ƙaramar yarinya.

"Na zama abin dariya haka ma matarka ta zo tana kallona tana dariya."
Received at 07:52Reactions: ❤ 7, 👍 1, 🥰 1, 😁 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Sai ya yi shuru kawai yana kallonta amma ya daina dariyan ganin da gaske take yi.

"Ai dalilinka ne na koma haka, kana gani ina kuka amma ka kasa lallashina sai ma fita ka yi kana waya da matarka ko ajikin ka."

Ta karishe faɗa hawaye na kece mata a saman kumatu.

"Ummu Salama."

"Na ce miki sorry, na lallashe ki da baki da aikace amma kin ƙi yin shuru"

"Me zan yi miki? Kin ce duk ni ne da laifi na amince. Kin ce na janye i do, kin ce a gaban mutane zan faɗa na ce done? Amma ba ki daina kuka ba."

"To ya kike so na yi miki?

Ya faɗa yana ɗan sassauta maganarsa
Ba ya son ranshi ya ɓaci amma kuma Ummu Salama na son sai ta ɓata masa rai.

"Haka za ka ce ko?

Ta ke faɗa tana nuna shi.

"Ai daman ba za ka san raɗaɗin dake zuciyata ba."

Cikin idanuwana ta kalle shi.

"Saboda ba ka yi rashin da na yi ba. Jaririn da muka rasa a wajenka rashin ba shi da ciwo tunda kana da wasu ya'yan da matar."

Ya yi mata ƙuri yana kallonta zuciyarsa na ɗaukan zafi yana ƙankance idanuwansa cikin mamakin kalamanta

"Sannan ba ka yi rashin mahaifi ba shi ya sa ba za ka san zafi da raɗaɗin dake zuciyata ba dole.."

"Ummu Salamaaa"

Ya kira sunanta a ƙausashe.
Cikin tsawa da sai da ta dakata da maganarta.
A irin kallon da yake yi mata ne ya sa ta dawo hayyacinta ta tuna abin da ta ce.

Sai ta koma ta rufe bakinta ba ta san maganar ta fito ba, ba ta san ma aka yi ta faɗi haka ba.

"Gori ki ke yi mini?

"Faɗa mini kike yi Baffa ba shi ne ya haife ni ba?

Ya faɗa yana kallonta kallon mamakin ke ce zaki ce mini haka.

Nan da nan ta gano ɓarnan da ta yi da sauri ta buɗe baki za ta yi magana.

"Get out"

Ya faɗa a tsawa ce.

"Hamma..."

"I said get out."

Ta tsaya kawai tana rawan jiki. Wallahi sheɗan ne ya tunzurata ta faɗi haka amma ba haka ta so faɗa ba.
Ganin ba za ta fita ba shi ya bar mata ɗakin yana banko mata ƙofa ta kwashi gudu ta bi shi har falo key ɗin motarsa ya ɗauka a saman kujera ya wuce ta ko kallonta bai yi ba.

Ta kwashi gudu ta bi shi tana faɗin.

"Hamma ka yi haƙuri don Allah."

Take faɗa tana kuka, ita ce ta ce yau za a yi ta ƙare ashe ita ce komai zai ƙare a kanta mai ya kai ta faɗin wannan maganar! Ɓacin rai ne da kishi wallahi tallahi ba ta san bakinta ya subuce ta furta waɗanan kalaman ba.

Tana bin shi tana kiran sunan shi ko waiwaye bai yi ba sai ga su a haraba.

Motarsa ya nufa ya buɗe ta ya shiga sai ta tsaya cak ta kasa ƙarisawa gare shi.
Me za ta faɗa masa?
Ba ta kuma da abin da za ta faɗa masa ita ce yau take yi masa gorin Baffa ba mahaifinsa ba ne.

Bakinta ta rufe da tafin hannunta hawaye na gangaro mata kunyar kanta na kamata, ita ce yau in ta ji wani na faɗin haka sai in da karfinta ya ƙare amma a ce yau da bakin ta take faɗin Hamma Lamiɗo bai san zafin rashin uba? Ta manta ko ita tasowa ta yi ta gan shi ƙarkashin tarbiyan Ammah da Baffa.

Me ya same ta! Kishi ne da takaicin dariyan da yake yi mata ko wauta ne duk ba ta san ma me ya shiga kanta ba. A lokacin da ta furta a lokacin kuma fargar jaji ya kamata. Amma ina magana ai zarar bunu ce ta riga ta fitar kuma ya ji ba ta kuma da sauran kalaman da za ta iya kare kanta da su.

Kunyar ma haɗa ido take yi da shi, kunyar kanta da kanta na kamataa jikinta ya yi matukar sanyi da tana ji tana gani ya fice daga gidan da gudu a mota

Sai kawai ta duke kan kafafunta tana kiran sunan Allah kukanta yaƙi tsayawa.
Ta ɗora hannuwa bisa kai tana kiran sunan Allah.

"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un"

Take maimaitawa hawaye na kece mata wasu na zuba wasu na tunkuɗowa.
Ta jima a wajen kafin ta tashi tana jan kafafunta da suka yi sanyi zuwa cikin gida sai da ta tsaya a haraba ta goge hawayenta sannan ta karisa.

Amma da Umma Balki da su Saddam suna falon ta wuce su sum sum ba ta yi musu magana ba.
Umma Balki ce ma ta ke tambayanta Lamiɗon ya tafi ne ko juyowa ba ta yi ba ta ce ya wuce ɗakinta ta shiga har tana rufo ƙofa tare da Harita suke kwana yanzu har ta yi shimfiɗa ta kwanta ta fara barci.
Received at 07:52Reactions: ❤ 8, 👍 1, 👏 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Gefen gado ta zauna tana zabga tagumi da hannayenta biyu, in har wannan abin da ta faɗa ya je kunnen Ammah ba ta san me za ta yi mata ba, ba ma ita ba kowa ya ji sai ya tsine mata ita kanta tana jin haushin kanta sosai subul da baka ne ba ta san kalaman sun fito da zafi haka ba.
Zaman ne ta ga ba zai kawo mata mafita ba sai ta jawo wayarta ta buɗe ta daga key tana kan sakon shi ne ma ba ta fita ba, sai ta fita ta je bangaren kira ta lalubo lambarsa ta fara kiran shi.

Kiran da ta yi masa ya fi goma bai ɗauka ba.
Ta koma tana ta tura masa sakon ban hakuri sama da goma amma bai kira ba, bai kuma amsa saƙon ta ko ɗaya ba. Daga karshe ma da ta sake kira sai dai ta ji ɗi ɗi sai kiran ya yanke.

Kamar ma ya rufe ta ne kwata-kwata. Tana hawaye kace kace, har da majina ta dafe kanta cikin tashin hankali da nadama. Nadama mara amfani.

Me ya sa ma ta je ta same shi? Da ta san haka abubuwa za su lalace da ba za ta je ba. Haushi ta ji haushin yadda ya yi banza da ita ta je da nufin ta bi kadin abin da ya yi mata kuma ya bige da ribatanta har ta ba shi dama a kanta, dariyan da yake yi mata ne ya tunzarata. Ba ta ma san mganganun dake bakinta ba kenan ita dai a harzuƙe take a lokacin shi ya sa aka ce in rai ɓaci hankali ke neman shi magana kuma dafi ne kaifin dafin ta yafi kaifin takobi.

Ita dai maganganunta kaifin dafin sun soki Hamma Lamiɗo sokewar da bai taɓa tunani ba.

"Na shiga uku ni Ummu Salama."

Ita kaɗai take maganarta tana kuka, ta rasa wa za ta kira akan wannan matsalan duk in ta je ta faɗa to ita ce a kasa, ta yi tunanin kiran Baɗɗo sai ta tuna yadda suke ba daɗi ma, yanzu tana faɗa mata abin da ta yi abubuwa ne za su ƙara lalacewa.

Ta koma tana sake tura masa sakon ban hakuri.

"Ka yi hakuri Hamma suɓul da baka ne. Wallahi na yi nadama kuma na janye kalamai na"

"i'm Sorry ba zan ƙara ba."

Amma da alamun ma bai san tana yi ba, ta kasa barci ta yi kuka kamar me, daman a kwanaki nan ta ƙulla abota da kuka nadamar abin

Please Login or Register in order to submit comment