Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

karɓi jinjirar ta rumgume tana yi ma Allah godiya. Bayan fitan Nurses ɗin ne ta samu damar kunna data, Lamiɗo ta so ta fara kira amma baya online sai kawai ta tura masa hoton jinjirar. Sannan kira Mami domin ta ga tana online.

Video call ne Mami na ɗauka sai ganin Ummu Salma ta yi da jinjira a hanunta baki ta saki.

"Me zan gani? Daughter kin haihu ne?

"Mami na haihu, abin mamaki Mami na haihu."

Ummu Salma ta faɗa tana washe baki idanuwanta sun cika da ƙwalla.
Mami ta yi kabbara tana jera Hamdala Ummu Salma na ji Mami na ƙwalama Harira kira sai kuma ta katse wayar.

Baɗɗo ta so ta kira sai ta ga ba ta online sai kawai ta tura mata hoton su da aka yi mata da jinjirar lokacin da ta haife ta.

"Alhamdulillah ɗiyarki ta zo duniya jiya da daddare"

Ta so ta tura a gidan Baffa da Ammah kunya ya sa ba ta tura ba.
Kafin ta kashe datar sai da ta koma ta kira lambar Hamma shuru ba ta same shi ba tana farikciki amma ya ɗan samu nakasu, tunda ba Hamma a kusa da ita. Ta haihu amma bai sani ba ta kira shi kuma ba ta same shi ba.

Hoton jinjirar ta tura ma Gimbiya Shahida sannan ba ta kashe datar ba ta koma ta kwanta ba kawai ta yi zaune tana ta kallon jaririyar tana ta barcinta hankalinta kwance.

Mami da Harira suka baro hotel suka hau Taxi zuwa cikin asibiti.
Suna cikin tafiya ne Mami ta shiga instagram saƙon da ta ci karo da shi yana yawo ne ya firgita ta.
Received at 18:55
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
BBC HAUSA suka fara fitar da sanarwan sannan sauran gidan jaridu suka fitar tare da sauran mutane suna ta sawa. Hannunta na rawa ta fita ta shiga goggle ta yi searching Masarautar Daura sai ga labarin ya fito, ta zaro ido cikin mamaki.

"Kai.."

Ta faɗa da ƙarfi har Harira na tambayanta ko lafiya ta kasa cewa komai da ta shiga wasop ta ga Hajiya Falmata ta turo mata.
Sannan Hamma Kabiru ma ya turo mata.

"Mami is this true?

"Na kira wayar Amini a kashe"

Itama abin da ta gani kenan amma ba ta da tabbacin domin ba ta san komai ba tunda kuma ga shi ana yawo da shi gaskiyan kenan.

Suna isa asibitin waya a hannunta ta shiga ɗakin da Ummu Salma take suka same ta ga jaririyar kwance gefenta ga kuma wayarta a hannunta.
Suna shigowa ta ɗago tana kallon su.

"Mami."

Ta kira ta da ƙarfi.

"Mami wai Hamma ya zama SARKI?

Ummu Salma ta faɗa cikin ƙarajin da muryanta cikin ruɗewa Mami ta ƙarisa kusa da ita Harira kuma ta sandare a tsaye.

"Mami da gaske ne?

"Nima haka na gani."

Mami ta amsa mata tana jin wani abu a ƙasan zuciyanta da ta rasa ko mene ne.

Hannu ta miƙa ta ɗauki jinjirar ta rumgume kawai ta yi tsaye.
Ummu Salma ta ce"Mami BBC suka sanar ga sauran gidan jaridu nan ma na fitar sanarwan Mami ga shi su Hamma Kabiru a group ma suna mganar"

Take faɗa cikin ruɗewa sannan ta fara karanta abin da BBC HAUSA suka fitar da hoton Mai martaba.

"SARKIN DAURA ALHAJI DR NASIRU MUHAMMAD SHITU, YA YI MURABUS DAGA KAN ƘARAGARSA A DARAN JIYA SANNAN YA ƊORA BABBAN ƊANSA MUHAMMAD NASIRU MUHAMMAD A MADADINSA."

Duk in da ka shiga labarin dake yawo kenan bisa laka'ari da cewa ba a cika samun Sarki ya yi murabus ya gadar ma wani ɗansa Sarauta ba an fi dai samun Sarki ya rasu a fafata a zaɓen majilisar fada har a samu wanda zai gaje shi sama da shekari hamsin a tarihin Masarautar Daura haka bai taɓa faruwa ba shi ya sa ya zama sabon abu.

Ummu Saalma sai hawayen farinciki daman shi ya sa aka ji Hamma Shuru shi kaɗai ya san halin da yake ciki.

"Allah sarki Hamma ba ya son sha'anin mulki. Daman abin da muke so ba shi Allah ke bamu ba, sai wanda ba mu saka rai da samun sa ba."

Sai hawaye shar sannan ta cigaba da faɗin.

"Ko ya zai ji a yanzu?

Shi kawai take tunani ga shi ba ta kusa da shi da ace tana kusa ma ba za ta samu ganin shi ba. Yanzu ba Yarima ba ne Sarkin Daura ne.

"Allah ya ta shi riƙo. Allah ya tsare shi."

Mami ta faɗa duk koƙarinta na kar ta yi hawaye sai da ta yi ta tuna maganar Baffa in tana cewa ta tsani abin da ya shafi Sarauta

"Ki kika sani ko ɗanki ya zama Sarki watarana Fatima? Ko ba na raye hakan ta faru ki yi masa fatan alheri Ubangiji ya kaddara haka ki daina jayayya da kaddara "

Ta fashe da kuka tana rumgume Jaririyar Hannunta.

"Allah ya gafarta maka Baffa."

"Kin zo duniyar a ranar da mahaifinki ya zama Sarki. Barka da zuwa SARAUNIYA DAURAMA."

"ALLAH ga bawan ka nan Muhammadu ya zama shugaban wasu al'umma a yau, Allah ka ta ya shi riƙo ka jiɓanci lamuran shi, ka kiyayesa ka taya shi kar ka barshi shi kaɗai Ubangiji ka taya sa riƙo."

Ummu Salma da Harira suna taya ta da amsawa da Amin a tare wayoyin su suka ɗau kara Video call ne ita Ummu Salma Baɗɗo ce ke kiranta ita kuma Mami Hamma Saddam.

Jaririyar Mami ta miƙa ma Harira ita kuma ta ɗauki wayar sai ga Ammah da Hamma Saddam da Hamma Abdulrahim, har da su Hamma Abdulrraham daga gani daga salla asuba suka zarto gida kowanne da Jallabiya.

"Fatima Lamiɗo ya zama Sarki."

Ammah ta faɗa cikin wani karaɗi a muryanta.
Mami ta ce haka ta gani Hamma Saddam ya yi jinjina.

'Sannu Fulanin Daura an gaishe ki."

Aka kwashe da dariya. Ammah na hawaye tana addua'n Allah ya ta ya Lamiɗo riko.
Su Hamma Saddam na ta murna da ihu sannan ga murnan Auta ta sauka an haskota tana videa call da Baɗɗo wacce ke ta murna da tsalle.

"Ranki ya daɗe da gaske dai kin zama Sarauniyar Daurama."

"Kin iya haihuwa tarihi ba zai manta da wannan haihuwar taki ba Sis na."

Ga murnan haihuwa ga ta Sarauta. Ummu Salma ta yi magana da su Ammah kowa sai da ya kira su video call har Hamma Kabiru ya ce bai samu Hamma Lamiɗo a waya ba.
Received at 18:55
Bilkisu reacted with ❤
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
"Mu ma nan ba mu same shi ba tun tafiyan shi. Yanzu ɗin ma ba lalle a same shi a yanzu ba mu jira ya neme mu."

Haka Mami ta faɗa, dole kam a jira jin ta bakinsa.
Yayyenta duk sun mata barka suna faɗin ta iya haihuwa.

Kafin ka ce me gabaɗaya social media da dukkan wani platform sun saka labarin abin da ya faru a Daura. Sannan hotunan Lamiɗo sun fara yawo tare da cikakken tarihinsa wasu hotunan da naɗi a jikinsa irin wanda ake yi masa da salla ne sai wasu hotunan kuma yana cikin Uniform ɗinsa na tukin jirgin ruwa.

"MUHAMMAD NASIRU MUHAMMAD LAMIƊO, SHI NE ƊA NA FARI GA MAI MARTABA SARKIN DAURA MAHAIFIYAR SA HAJIYA FATIMA BABA, BA YAR MASARAUTA BA CE SUN RABU TUN KAFIN TSOHON SARKI MAI MURABUS YA HAU KAN KARAGA. MUHAMMAD LAMIƊO MATASHI NE ƊAN KIMANIN SHEKARU ARBA'IN A DUNIYA YA YI KARATUNSA NA TUKIN JIRGIN RUWA A ƘASAR MALAYSIA YANZU HAKA MA'AIKACI NE A KAMFAMIN CHEVRON NIGERIA LIMITED A MATSAYIN ƊAYA DAGA CIKIN MARINE, MA'ANA CAPTAIN ƊIN SU MASU JIGILAN JIRAGENSU ZUWA ƘASASHEN WAJE YANA DA MATAR AURE GUDA BIYU DA YARA BIYU, MATARSA TA FARKO HAJIYA BILKISU USMAN BAYERO ƊIYAR SARKI KANO USMAN BAYERO."


Rubutun dake ta yawo kenan tare da hotunan Lamiɗo nan da nan yan'uwa suka fara status na ta ya murna ga Lamiɗo da kuma na samun ƙaruwa.
Gimbiya Shahida ta kira Ummu Salma a waya sun yi magana ta ce Fada ta cika saboda murabus ɗin mai Mai martaba a maganar da take yi ma tuni Lamiɗo na fada a matsayin Sarkin Daura.
Ta ce su kan su ba su san hukunci da Mai martaba ya yanke ba kenan.

Ana ta yawo da maganar ko wata Sarautar zai canza ma Yarima ashe Murabus zai yi suma tun jiya ba su gan shi ba murabus ɗin cikin dare aka yi shi a daran kuma aka naɗa Lamiɗo sai dai Kawai aka wayi gari da sanarwaan amma zuwa yamma Mai martaba zau gana da yan jaridu da gidajen talabijin zai yi bayani ga al'ummar Daura da sauran mutane.

Ta kwantar ma da Umma Salma hankali da cewa ta kwantar da hankalinta ta samu lafiya ta kula da kanta da jaririyarta. Har zuwa nan da kura ta lafa yanzu dai Lamiɗo ba zai samu kan shi ba gaskiya. Kuma gaskiya ta faɗa tabbas sai nan da lokaci kaɗan maganar haihuwa ma bai sani ba domin ba a faɗa masa ba waya ce kuma ba ta tare da shi.

Kamar yadda Ummu Salma ta ga abin daga sama haka Bilkisu ta ji, ita tana barci daga cikin ahalin gidansu aka samu wani yayanta ya kira ta ya faɗa mata tana hawa social media ta samu tabbaci jiki na rawa ta kira Gimbiya Hadiza ta ƙara samu tabbaci. Ta tabbatar mata da cewa da suma haka suka wayi gari amma kamar Fulani da duka yan'uwan Mai martaba mai murabus sun san da faruwar komai.

Bilkisu ta daka tsalle ta dira saman gado ta fita falo daga ita sai rigar barci ta dinga kiran Sabuwa sai ga su a rikice sun ɗauka wani abu ne ya faru sai ga shi tana faɗa musu Yarima ya zama Sarki bayan ta rumgume Sabuwa.

Su Debora da Anitha suka rumgume juna suna yi ma Bilkisu congratulations yara ma ihun murnanta ya tashe su ai sai ta shiga ɗaga su ɗayan bayan ɗaya tana juyi da su. Har da Hanan tana faɗa musu Papa is now a king of Daura duk da ba su wani gane ba suna ta murna. Bilkisu kai ya yi girma ta zama matar Sarki ta manta da batun wasu kishiya murna kawai take yi haka ta kira Umman kano tana murna ta ce suma sun samu labari.

Ta ce sai ta yi ta ma Allah godiya tare da addu'an Allah ya taya mijinta riƙo.
Sai bayan sun gama wayar ne ta lura da status ɗin Adda Safina da hoton jaririya ta fara cin karo.

"Welcome to the world Princess. Kin iya zuwa duniya. Ranar da muke murna Babanki ya zama Sarkin Daura."

Ko ba a fada ba wannan jaririyar ɗiyar Umma Salma ce ta haihu kenan? Ta san da Lamiɗo na cikin sukuni zai faɗa mata yanzu ko a duniya ta ji ta ce Allah y raya ba ta damu ba. Ita yanzu ba kishi ba ne a gabanta she is now Gimbiya Bilkisu Gimbiya Bilkisu matar Sarkin Daura.

Ta zauna ta saka hoton Lamiɗo ta yi dogon rubutu na murna ta yi status dangi da abokan arzuƙa ana ta taya ta murna da barka da arziki.
Received at 18:55
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ranar har busa ta yi connecting ta wayarta daga speaker ta fara juyi tana kaɗa kai ranar farinciki ce wayoyin ko da ta amsa na mutane ba ta san adadi ba har da su Sofia duk sun yi waya suna ta ya ta murna ko da hukuncin bai yi ma wasu daɗi ba hukuncin ya riga ya zartu ba yadda aka iya.

Da yamma misalin shidda na yammaci aka fitar da maganar da Mai martaba mai Murabus ya yi da manema labarai aka watsa a duniya.

"Ni Alhaji Dr Nasiru Muhammad Shitu, a jiya 8 ga watan November wanda ya yi daidai da shekara ta dubu biyu da ashirin da biyar. Na yi murabus daga kan ƙaragar mulkin garin Daura na gadar ma babban ɗana Muhammad Lamiɗo ɗan Nasiru jikan Shitu, a kuma jiyan ya fara zama wakilin ku sarkin ku. Dalilina shi ne ina cikin jinya ina buƙatar hutawa domin inganta lafiyata. Bayan zama da masu ruwa da tsaki na fada majalisar zaɓe tare da malamai, Hakimai masu Sarauta alƙalai tare da limaman mu, sai kuma dattawan da hikaman mu a karshe suka aminta da tsarina bayan duba da cancantar wanda na kawo a matsayin wanda zai gaje ni. Alhamdululillah Allah na gode maka ina bayar da haƙuri duka al'ummata na Garin Daura da kewayenta. Da wanda ya ji daɗi da wanda bai ji daɗi ba, ku sani nima na ji daɗin tsawon shekarun da na kwashe ina mulki tare da ku, da wannan damar nake neman afuwarku na san a shugabancina ba zai yuyu na faranta ma kowa ba, ku yi mini afuwa in da na kuskure ina fatan Ubangiji ya tsare Masarautar Daura. Allah ya kare Jihar Katsina da Al'ummarta gabaɗaya. Ina mai yi muku albishir ɗin cewa za ku ji daɗin mulki Sarkin ku na Yanzu Muhammad Lamiɗo fiye da mulkina. Ubangiji ya taimake mu ya taimaki kasarmu Nigeria gabaɗaya ya ɗaga darajar Masarautun gargarjiya da addinin musulunci gabaɗaya.."

Video ne ga Mai martaba zaune ya sha rawani, ana ta yawo da shi da fatan Allah ya ba sa lafiya wasu jama'ar Daura har da masu kuka domin sun san Tsohon Sarkin adali ne akwai masu cewa Saleem ne ya cancanta Hakimin Daura wasu kuma suna faɗin Yarima Lamiɗo ne ya fi cancanta kowa dai na faɗin ra'ayin shi.

Sai da aka kwana biyu wannan murabus ɗin na Sarkin Daura ke trending a social media.
Har kuma zuwa lokacin ba wanda ya ji daga wajen Sarki na yanzu wato Lamiɗo.
Sai ranar ta uku ne cikin dare misalin uku da wani abu Lamiɗo ko na ce Mai martaba Sarkin Daura na yanzu ya kunna wayarsa ya kira Aminin shi a waya.

Maganar haihuwar Ummu Salma sai jiya ya ji a bakin Fulani sarkaƙiyar da ya shiga ya sa ya manta da wata waya. Amma kuma duk damuwar da yake ciki bai manta da Ummu Salma dake can tsakanin rayuwa da mutuwa ba.

Daga saukarsa a garin Daura zuwa yau ɗin nan rayuwarsa ta juya daga sama zuwa ƙasa nw. Juyin da bai taɓa tunani ba tun yana ganin wasa har sai ga shi ya tabbata amna yana gani kamar a mafarki ne, kamar in ya buɗe ido zai ga komai bai faru ba.

Tun a daran da aka masa naɗin Sarautar Sarkin Daura bai sake cikakken barci ba. Ɓata dare yake yi cikin tunani da fargaba, ba zai iya ba ya faɗa ma Mai martaba amma bai saurare shi ba. Yanzu ɗin ma kafin ya kira Kabiru sai da ya tura ma kamfanin su takardaan ajiye aiki ya fi mintina talatin yana juya saƙon kafin ya tura musu ta email ɗin su.

Shike nan yanzu ya yi sallama da mafarkinsa. Yana ji yana gani kaddara ta sake juya masa sabuwar rayuwa
Da gaske ne shi ne Sarkin Daura an yi masa naɗi Mai martaba da iyalansa ma suna shirin barin fada ne zuwa wani gidansa dake cikin garin Daura shiryen shiryen gyara Masarautar ake yi tare da saka lokacin bikin naɗi yanzu shi ne ke zama a kan karagar mulki a fada, shi ake yi ma biyayya shi ne umarninsa ke saman na kowa. Allah mai iko da gagara misali.
Shi ne ke shiga irin ta Sarki, alhalin Sarki na raye bai mutu ba.

Ba zai iya magana da kowa ba a lokacin ba sai Aminin shi, yana kiran shi kuma har ta kusa katsewa ya ɗaga saboda shima gani yake yi kamar wasa.

"Amini."

"Kai ne?

Sai kawai Lamiɗo ya yi gyaran murya Kabiru sai ya ji ya yi masa ƙwarjini duk da ba ganinsa yake yi ba.

"Allah ya taimake ka Allah ya ƙara lafiya. Allah ya taya ka riƙo."

"Amini."

"Na'am Ranka ya daɗe."
Received at 18:55
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
"Na zama Sarkin Daura amma kafin na zama haka ni ne dai Muhammad Lamiɗo aminin ka."
Sai ya ɗan ja fasali kafin ya cigaba da faɗin.

"So ka yi magana da ni kamar yadda muka saba."

"To."

Kabiru ya amsa domin yana ganin kamar a mafarki.
Aminin shi ya zama sarki falo ya fita kar ya tayar da Safina dake barci.
Duk da akwai yuyiwar faruwar haka amma komai ya faru a cikin lokacin da ba wanda ya yi tunanin faruwarsa.

"Ummu Salama ta haihu, ka nemi visa da sauri don Allah ka je ka duba mini su, ka yi ma yarinya huɗuba."

"In sha Allahu."

"Da wani suna?

"Ka tambayi Ummu Salama duk sunan da ta zaɓa ka yi mata huɗuba da shi."

"In sha Allahu."

Kabiru ya amsa masa kamar baƙin juna sai suka yi shuru.

"Kana dai lafiya ko? Muryanka ta yi kama da wanda ya daɗe bai sami barci ba"


"Lafiya lau."

Kawai ya iya cewa duk abin da zai faɗa ba za a gane ba, bai kuma san me zai ce ba domin bai iya bayani ba.

"In ka yi waya da Ammah ka ce ina gaisheta zan kirata in na samu sarari."

Kabiru ya amsa da zai faɗa mata daga nan suka yi sallama. Sarauta gaskiya ce a muryan Lamiɗo har ta canza yana magana cikin natsuwa da ƙasaita duk da daman halin shi ne amma yau na dabam ne.
Kafin ya kwanta ya fara neman visa ta online tunda yanzu komai a sauƙake ne ko wani kamfani suna da handel a social media xa ka iya samun su ko ta email.

A daran Lamiɗo ya kunna data sakonni wasu na ture wasu bai buɗe na kowa ba sai na Ummu Salma ta turo masa hoton jaririyar ya buɗe ya gani.
Sai da zuciyarsa ta yi haske daga wani shashe.

Ya rasa me zai ce ma Ummu Salma ya so ya kira ta sai kuma ya kasa.

"Thank you Ummu Salama. Thank you."

Haka kawai ya iya rubuta mata. Sai saƙon Bilkisu na gayyar sticker da emojin murna da dogon magana da turanci na ta ya shi murna.

"Bilkisu"

"I will call you later."

Abin da kawai ya ce mata kenan yana buƙatar natsuwa. Yana bukatar lokacin da zai karɓi wannan sabuwar rayuwar tashi tukunna kafin abubuwa su daidaita.



*Janafty*
Received at 18:55
Muhammad reacted with ❤
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
MASARAUTAR DAURA.

Har yau da kimanin kwana biyar kenan da tsohon Sarki Alhaji Dr Nasiru Muhammad Shitu ya yi murabus daga ƙaragan mulki ya ɗora ɗan shi Muhammad Lamiɗo Al'ummar garinn Daura ba su daina cece-kuce ba.

Wasu kuma suna ganin abin kamar a mafarki domin abu ne da ya faru ba tare da shiri ko barin wata alama ba. Wasu kuna suna tunanin rashin cancantar Lamiɗo wasu kuma tsohon Sarki suke so suna ganin a shekarunsa bai dace ya yi murabus ba, duk da ya faɗi dalilinsa ai suna ganin jinyar tunda ba ta kwantar da shi ba, bai kamata ya yi saurin yin murabus ba. Wasu kuma suna faɗin dama Hakiman Daura Saleem ya ɗaura a ganin su, shi ne ya fi kowa cancanta da wannan karagan tunda yawancin abubuwan fada da shi ake gudanarwa sannan ya sha wakiltan Mai martaba tsohon Sarki a wasu tarurruka masu muhimmanci an fi sanin shi tunda ana ganin shi saɓanin Lamiɗo da sai salla salla, amma in dai yana gari matasan garin Daura suna shaida zuwan shi saboda alherin shi.

Sauran kuma ko maganarsu ba a yi. Yazeed da Sagir gani ake yi ana babbakan giwa wa zai tuna da zomo amma duk da haka a cikin mutane ba za a rasa masu kawo su a matsayin suma waɗanda suka cancanta ba ko'ina dai ceceku ce yaƙi karewa amma kuma ba abin da zai sauya wannan kaddara tun a ranar da Sarki ya yi murabus Al'umma Daura suka bar ƙarƙashinsa suka koma ƙarƙashin jagorancin Lamiɗo Sarki na yanzu.

A cikin Masarauta ma kowa ka gani lamarin bai gama kama jikinsa ba. Nan ma mganganu suna ta tashi da cewa Sarki ya yi gaggawa ko na ce tsohon Sarki sannan ya yi shammata. Duk da duk wanda yake tare da Mai martaba tsohon Sarki kowa zai iya shaida Lamiɗo yake so ya gaje shi amma ba wanda ya taɓa tunanin da ran tsohon Sarki hakan zai faru masu hangen nesa ma gani suke yi Lamiɗo ba zai yi Sarauta ba, in Sarki ya rasu ba lalle ma ya fito neman karagar ba duba da ba ya son Sarauta ko da ma ya fito suna ganin majalisar zaɓe ba za ta zaɓe shi ba.

Sai ga shi komai ya faru a cikin dare ɗaya aka wayi gari da fashewar boom ɗin da kowa bai taɓa tunani ba sai ƙalilan mutanen da suke da alhakin sanin komai kafin zartarwa.

Kafin kowa da Fulani tsohon Sarki ya fara tattauna shawaransa da matsayarsa ta kuma ba shi goyon baya saboda itama a suffa da hallaya ba tun yanzu ba ta daɗe da ganin cancantar Lamiɗo a matsayin wanda zai gaji karagan mulkin Mai martaba. Kuma lokaci ya yi da zai dawo gida ya rumgumi rayuwarsa hannu biyu lokacin da ya ganawar sirri da sauran yan'uwansa mata ne wasu suka nuna ba su amince ba. Kamar Hajiya Kilishi a rashin nuna ba ta amince ba dalilinta shi ne ai ba jinya mai tsanani Mai martaba yake ciki ba, a ganinta bai kamata ya yi murabus ba.

Haka ma Hajiya Zaliha ta ce, sauran kuma irin su Hajiya Binta suna nuna cewa bai cancanta Lamiɗo ya yi gadon karaga ba. Me ya sani game da harkan mulki? sannan mahaifiyarsa ba yar sarki ba ce me ya sa zai mulke su! Mai martaba shi ne mahaifin Lamiɗo kuma ya cika duka sharaɗan zamowa Sarki saboda haka yana neman yardansu zai yi murabus sannan zai kai maganar wajen wakilan zaɓen Sarki, sun daɗe suna tattaunawa kafin a samu daidaito, kawai dai sun amince ne domin ba su da ta cewa tunda ba su cikin masu zartawa wannan alhakin majalisar zaɓe ne.

Ko da ya kira Lamiɗo ya taho Daura ya riga ya gama shirya komai. Ya san zai ce ba ya so shi ya sa ya ce umarni ne ba neman yarda ba, bai ma tsaya masa wani jawabi ba sai dai kawai ganin shi ya yi ya gayyato Kingmakers.
Majalisar zaɓe tunda ya ga haka ya san an zo bus stop, sannan ya saurari duk abin da suka tattauna suma ɗin dai wasu sun amince da tsarin Mai martaba wasu kuma ba su amince ba amma dai ya tattauna da su sannan ya kawo musu hujjojinsa masu ƙarfi ya kuma ce su je su zauna su sake nazarin komai a tsanake amma kar ya ɗau lokaci, Lamiɗo kuma ba a ba shi wata dama ba a wannan gabar jiran umarni ne kawai na shi ko ya yi magana a wannan gabar lokaci ya ƙure masa.
Received at 15:16
11 people reacted with ❤
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ba duka ne waɗanda ke da alhakin zaɓen Sarki suka amince da tsarin tsohon Sarki ba amma tunda majority sun amince sun ga kuma cancantar Lamiɗo.
Majalisar zaɓe da Mai martaba ya fara ganawa da su, a hukumance su ke da alhakin zabe ko tsige Sarki. Ko kuma rashin lafiya mai tsanani. Kuma majalisar zaɓe ta ƙunshi manyan Hakimai guda hudu zuwa biyar.
Mai sarautar Madaki, Waziri,Galadima da Chiroma ko Yarima babban yaron Sarki da sallama mai kula da ƙofar fada.

Aikin su daman taruwa ne a ɓoye domin nazarin lamarin. Suna yin shawarwari kan mutumin da ya dace bisa tsarin mulki na gadon Masarautar. Su ne kuma ke gabatar da dalilai ga majalisar Sarki ya yin sauke shi ko tsige shi.

Babban Alƙali kuma shi ne shugaban sharia' yawaancin shawararsa kan halascin sauke sarki ko zaɓen shi a addini ne bisa shari'ar musulunci.
Sai limamin Juma'a; wannan mutumin yana da mutumci a idanuwan talakawan gari, shawararsa kan zaɓen shugaba mai adalci yana da tasiri ga al'ummar garin gabaɗaya.
Sai sauran Hakimai da Dattawan suma wajibi ne a ji ta bakin su domin samun amincin talakawa.

Sannan akwai alhakin amincewar Gwamnati shi ya sa Mai martaba bayan duk ya gama samun amincewar Fada da sauran masu ruwa da tsaki a safiyar da murabus ɗinsa zai fito ya ɗauki Lamiɗo suka je har gidan Gwamnati suka gana da Gwamnan Jahar Katsina tattaunawa mai tsawo bai baro gidan Gwamnatin Katsina a daran ba sai da ya samu sahalewarsa sannan Gwamna da kan shi ya ce zai yi waya ya sanar da shugaban ƙasa.

Shi ya sa a daran ba tare da sanin kowa ba wakilan fada da hakimai tare da dattawan fada da majalisar Sarki haɗe da limamin fada a gaban su a ka yi komai Mai martaba tsohon Sarki ya yi murabus nan take aka maye gurbin shi da Muhammad Lamiɗo shi ya sa a wayewar gari labarin ya fita bayan

Please Login or Register in order to submit comment