Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a zauna lafiya.
Ya fahimci akan kishin Ummu Salama za ta iya kamuwa da wata cutar to a haka ma ya aka ƙare ballatana ta tabbatar da hasashenta na cewa ya fi son Ummu Salama ai ba zaman lafiya. Shima a bangaren sa ya yi tunanin zai dinga kiyayewa saboda gudun nuna bambamci ko kawo ɓaraka a rayuwar gidan shi da iyalansa, kuma daman fatan shi a koyaushe Ubangiji ya ba shi ikon ci gaba da yin adalci tsakanin Bilkisu da Ummu Salama.

Kawai ta zauna a yadda take Bilkisunta ba Bilkisun yanzu mai ƙorafi da yawan fushi ba.
Suka kwana cikin farinciki suka tashi cikin farinciki ya faɗa mata zuwan su Mami ta ce Allah ya kawo su lafiya ta fita da kanta ta ce Hidaya ta shiga bangaren Ummu Salma ta gyara Debora kuma ta ce ta shirya abinci.

Har da asuba nan sai da Lamiɗo ya sake yi mata sabon lallashi da alƙawarin in Ummu Salma ta haihu za su tafi duk ƙasar da take so shi da ita tunda karshen shekara ya zo. Ta dinga murna tunda ta ji ya ce daga shi sai  ita yara ma a gida za su bar su kanta ya fashe tana jin kanta kamar sarauniya. Tana so ta koma yadda take a baya amma kishin ne ke murƙusaan zuciyanta

Ta rasa yadda za ta yi, sai ta kira Umman Kano bayan sun gaisa take ce mata.

"Umma wani addu'a mutum zai yi Allah ya rage masa zafin kishi a zuciya?

Tunda dai har abada za ta cigaba da ganin Ummu Salma a kusa da mijinta. Gwara ta nemi hanyar da za ta samu sauƙi kar kishi ya yi ajalinta watarana.

Umman Kano ta yi dariyansu na manya kafin ta ce." Ni kika gado a kishi Bilkisu, amma kuma ba ki gado yadda za ki yi yaƙi da shi ba. Na sha faɗa miki wannan kishin na ki illa zai yi miki watarana ba ki sani ba."

"Umma ina son na samu sauƙi a zuciyata ya zan yi.?

Ta faɗa kamar ta yi kuka, ta gaji tana son zuciyanta ta samu hutawa

"Kishi halas ne Bilkisu ba ki yi laifin komai ba. Na fiki zafin kishi amma kika ga na zauna da kishiyoyi kuma na iya allona haƙuri ake yi kawai sannan ki dinga maimaita Hasbunallahi wa'imal wakel a cikin zuciyarki a duk lokacin da kika ganta. A sallolinki ki dinga faɗa ma Ubangiji ya sanya miki sassauci da salama ki dinga samun lokaci ki tashi cikin dare ki yi salla ko raka'a biyu ne ki roƙi Allah ya sanyaya miki zuciya ya ɗaga tauraruwarki a zuciyarki mijinki. Kar ki sake bari ya fahimci kina da kishi mai zafi.
Received at 08:43Reactions: ❤ 8, 👍 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ki iya kissa da kisssinan da za ki fi kowa a wajen mijinki in kika yi haka a hankali a hankali komai zai dinga raguwa har ma watarana in kin gansu tare ba za ki ji komai ba."

Umma ta daɗe tana ba ta shawarwari masu kyau, irin wanda Ya Hadiza take ba ta take ganin kamar su ba za su gane ba ne. Amma yanzu ta fahimci maganganunsu, tunda Ummu Salma ba za ta bar mata mijin ta ba, gwara ta koyi yadda za ta rayu tare da ita cikin salama ta gaji tana bujatar ta zauna da zuciyanta lafiya
Ita yanzu kawai mijinta za ta kama a hannunta yadda Ummu Salma za ta fahimci da sauran ta a jira.

Ƙarfe huɗu da wasu mintina Bilkisu da Lamiɗo suka je filin jirgi suka ɗauko Ummu Salma da Mami tare da Harira. An gyara gida ko'ina kal yana tashin ƙamshi karon farko da Mami ta taɓa taka gidan Lamiɗo a rayuwarta kenan.
Bilkisu ta yi ƙokarin sakin jikinta da fuskarta saboda Mami kuma Mamin ta yaba mata sosai.

A bangaren Ummu Salma ta sauka a tare da yaran gabaɗaya suka ci abinci a saman dinning gida ya yi daɗi ana ta hira.
Saboda Mami sai Umma Salma ta ce Lamiɗo ya je wajen Bilkisu kawai ya kwana ita yanzu ma ta kanta take yi.

Zuwa wayewan gari duk sun gama haɗa kayan tafiya. Kayan haihuwa kuma daman kaɗan suka ƙara siya wannan karon tunda akwai ma wancan da yake both boy and girl suka siya, jirgin dare za su bi Ummu Salma ta kira duka yayyenta sun yi sallama tare da yi mata fatan alheri. Baɗɗo ta ce tana nan ne amma gabaɗaya addu'anta na kan Ummu Salma in sha Allahu za ta haihu lafiya.

Ammah kuma da suka yi sallama ta ce duk safiya ta dinga karanta ayatul kurusiyu tana tofawa a ruwa tana sha komai zai zo da sauki. Bilkisu da yaran gabaɗaya suka raka su har filin jirgi misalin tara na dare James ya tuƙa su.

Harira na ta murna za a je kasar larabawa daman ta san da tafiyar tunda tun kafin su zo bikin Baɗɗo Lamiɗo ya sa aka yi mata international passport tunda karon farko kenan da za ta bar Nigeria itama Ummu Salma sabo ya sake yi mata, na ta na shekara biyar ne ya yi expire, Mami ne da shi suke da na shekaru goma-goma su ba su da matsala.

Ummu Salma na sanye da a baya baƙa. takalmin kafarta mai saukin tudu ne amma dakyar ta tura shi saboda kumburin kafarta.
Yaran ɗaya bayan ɗaya suka rumgumeta suna yi mata sallama wai suna jiran now baby tunda Papa ya ce Anty Umma tare da Baby za ta dawo. Har da su Sabuwa aka zo filin jirgi yin sallama, Anitha da Debora da aka bari gida kafin fitowarsu suna ta mata fatan dawowa lafiya tare da Baban Adila.

Bilkisu ta ba ma Ummu Salma hannu suka yi masabaha.

"Allah ya raba lafiya"

"Amin na gode."

Ummu Salma ta amsa tana mirmishi.

"Ki yafe mini in na yi miki laifi. Ban sani ba ko Allah zai sake haɗa fuskokin mu"

Ummu Salma ta faɗa idanuwanta sun cika da kwallan gani take yi kamar a wajen haihuwan nan za ta mutu duk a firgice take.

Bilkisu ta kalleta ta yi mata laifi mai girma ta aure mata miji. Ƙananun laifukan kuma daman kowa ya yi ma ɗan'uwansa.

"Bakomai nima ki yafe mini."

"Allah ya yafe mana gabaɗaya."

Bilkisu ta yi sallama da Mami ta amsa mata cikin yanayinta na koyaushe.
Sannan suka rumgume da Lamiɗo lokacin Mami ta juya baya tana magana da Daddy a waya. Yaran ma ɗaya bayan ɗaya ya rumgume su suka yi sallama.

A filin jirgin suka barsu suka koma gida. Jirgin na su sai ƙarfi sha ɗaya na dare ya ɗaga zuwa EGYPT babban birnin Cairo Ƙasar da Annabi Musa ya yi rayuwa wanda a wancan zamanin ake kiran ƙasar da ƙasar MISRA.




*Janafty*
Received at 08:43
11 people reacted with ❤
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
*FJ littafin kuɗi ne 1k a manhajar Telegram tura kuɗin karatu ta wannan acct ɗin 9069067488 Opay Jamila Umar shaidar biya ko tuntuɓa ta waɗannan lambobin.*
08032773332
09069067488.

*CAIRO, EGYPT.*
EL NADA HOSPITAL.

A safiyar ranar talata suka sauka a ƙasar Egypt babbar birninta Cairo. Tun kafin su sauka motar asibitin da wasu daga cikin nurses ɗin asibitin suka zo tarban su.

Da yake yanzu zamani ya kawo mu komai ta waya ake yi, ta email Lamiɗo ya yi magana da asibitin tun bayan da ya yi bincike kan asibitin kuɗi mai kyau a ƙasar in da Ummu Salma za ta haihu da ikon Allah da kuma ƙwarewarsu. Ta Email ɗin ya tura musu duka bayanan Ummu Salma sannan suka ba shi lambar da zai dinga magana da su. hatta booking ɗin komai an gama jiran su kawai ake yi, shi ya tura musu sakon ticket ɗin su da lokacin da za su ta so da kintatan lokacin da za su sauka shi ne kafin su saukan ma suna filin jirgi suna jiran su.

Tun a filin jirgin Lamiɗo ya tabbatar da Ummu Salma za ta samu kulawa na musamman. Sun taho da gadon marasa lafiya ga wheelchair bayan an ɗaura ta daga bakin jirgi zuwa motar asibitin su kuma suka bi su a motar haya har zuwa asibitin.

Garin daman na larabawa ne asibitin ma yawaanci duk labarawan ne duk da akwai turawa asibitin ya haɗu haɗuwarsa ya wuce a zauna ana rubutawa
Harira baki kawai take saki tana yi ma Allah kirari.

Mami kuma daman ta saba zuwa ta san Egpyt sosai suna yawan zuwa da Daddy sannan lokacin da ta haifi Islam sai da ta yi kusan wattani biyu kafin ta koma Nigeria so Egypt ba baƙo ne ba ne a wajenta.
Lamiɗo ma da bai taɓa zuwa ƙasar ba shi dai daga ƙasar Malaysia sai Saudia Arabia ya taɓa zuwa haka na musamman Malaysia saboda can ya kwashe shekaru sama da huɗu yana karatu, Saudiya kuma ya je sauke farali da Umra bai san sau adadi ba. Sauran ƙasashen kuma aiki ke kai shi daga ruwa sai ruwa ba yawo suke yi a cikin gari ba amma duk da haka ba za ka gan shi ka ce masa baƙo a ƙasar ba saboda iliminsa da wayewa.

Ummu Salma ma wannan ne karon ta na farko. Ita daman Umra kawai ta taɓa zuwa sanadin Daddy da Mami tana da burin zuwa Saudia ta sauke farali tun a baya ballatana yanzu da take son ta je ta roƙa ma Baffa gafara da rahama a wajen Allah. Tabbas Hajji kiran Allah ne ba rashin kuɗi ba ne ya hana ta zuwa Allah ne bai kirata ba.

Suna zuwa asibitin wasu takardu ne kawai Lamiɗo ya cike maganar payment daman tun a Nigeria ya tura musu kuɗaɗen da suka caje su a ƙiyasi dai Ummu Salma za ta iya yin wata ɗaya ƙarƙashin kulawarsu tunda EDD ɗinta tara ga watan November ne sun kuma sauka a asibitin 31 ga watan actober.

A wani ƙayattacen ɗaki na musamman aka ware ma Ummu Salma ga girma ga shi abu abin da babu a cikin ɗakin nan kamar irin ta zo shaƙawata ba haihuwa ba. Babu abin da za ta nema ta rasa. Sannan kafin a shigar da ita sai da suka sanya mata kayan su na asibitin wani fari mai layi layin baƙi, riga da wando masu sakewa ba su kama ta ba, har da irin hulan su na asibitin da takalminsu ga blanket komai anan suka samu
Kuma ba su buƙatar masu jinya su kwana su za su dinga kula da majinyaci sai dai daga safiya zuwa yamma.

Har sun fara duba lafiyarta an yi ma gwaje gwaje domin a fahimci matakin da take har scan na cikin ta sun sake yi mata duk da an turo bayanan ta suna bukatar ganin komai da kansu sun yi tsarin cewa har abincinta su za su tsara da lokacin cin ta lokacin da za yi dinga barci saboda jininta ya yi sama akwai buƙatar ya sauka kafin haihuwar ta zo. Daga ganin wannan asibitin za ka san naira ce ta yi kuka naira mai suna naira miliyoyi da ba za su ƙirgi ba.

Lamiɗo da Mami har da Harira suna asibitin sai gabda azahar suka tafi Hotel ɗin dake kusa da asibitin mai suna NADA HOTEL 3star hotel ne mai kyau hadaɗɗe mai hawa hawa ba iyaka.

Lamiɗo ya yi musu booking ɗin ɗakuna nan za su zauna sai dai za su dinga zuwa lokacin da asibitin da tsara suna duba Ummu Salma shi yana gama abubuwan da zai yi yana so ya koma saboda ranar friday zai koma bakin aikin shi.
Received at 18:55
Rabi'atu reacted with ❤
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ko da suka baro sun ba ta abinci sun yi mata allura ta fara barci. Akwai wayarta a hannunta za ta dinga amfani da ita amma sun ce ba za su bari ana damunta da hayaniya ba a takaice dai tana under control ɗin su ne. Suma an kawo musu abinci mai rai da lafiya bayan sun yi wanka sun yi salla suka ci suka kwanta suna barcin da ba su samu damar yi a jirgi ba.

Lamiɗo ya so ya kama ma Mami ɗakin ta ita kaɗai amma ta ce ba ta son zama ita kaɗai ya kama musu ita da Harira shi kuma umarninta saman muradinsa ne sai ya yi mata yadda take so.

Mai martaba ya daɗe yana faɗa masa Mami ta fi kowa son shi ba ta dai nunawa ne sannan wani lokacin in suna hira da Ummu Salama in ya ce Mami ta fi son ta sai ta ce kara take yi maka. In ya ce Ammah ta fi son shi sai Ummu Salama ta ce kara take yi maka amma ba wacce za ta fi uwa son abin da ta haifa. Ya tabbatar da haka yanzu da suke samun kusanci ya ɗauka a baya duk wani abu da ya shafe sa ne ba ta so har da shi ma sai daga baya ya fahinci tabbas kara take yi ma Ammah da Baffa sai wata darajarta da ƙimarta suka ƙaru wajensa sannan kwanaki ya ji wani wa'azi malamin ya ce ko a bakin kura kake to wajibi ne ka yi ma mahaifiyarka biyayya sai ya zauna ya yi tunanin tun tasowar sa wani biyayya ya yi ma Mami a matsayinta na uwa a gare shi? Ya kasa tunawa shi ya sa yanzu ya gyara biyayya yake yi mata duk da ko a baya yana yi mata biyayya shaƙuwa ce dai a tsakanin su sannan ba sa shiga rayuwar juna amma dalilin Ummu Salma ya sa yanzu zai iya doguwar magana da Mami bai sani ba itama za ta zauna ta yi masa mganganu ba ta sani ba, a hankali dai tazaran rashin shaƙuwar dake tsakaninsu tana ta haɗewa ba tare da sani ba.

Ba za su koma asibiti ba sai da yamma. Yanzu ɗin ma Mami ce ta baro ɗakin su zuwa na shi ta ce ta gaji da kwanciya. Shi kuma daman bai iya barcin ba yana dai kwance yana hutawa bayan ya gama waya da Bilkisu ya sanar da ita sun sauka tunda suna sauka ƙasar ya siya sabon layi ya fara amfani da shi.

Mamin ce ma ta tuna masa ya kira su Ammah ya faɗa musu sun sauka sai ya kira har ya ba ma Mami suka yi magana tana faɗa mata asibitin suna da ƙwarewa da ikon Allah Ummu Salma wannan karon za ta haihu da kanta.

Bayan sun gama waya da Ammah sun jima suna hira da Mami tana faɗa masa yadda yanayin asibitin da ya nema sun birge ta kuma daga gani za a samu abin da ake so. Tana faɗa masa itama asibitin da ta haifi Islam mai kyau ne sosai sun kula da ita sosai nan take ta shiga nuna masa hotunan a wayan ta, ga lokacin da suka yi hotuna da likitocin larabawa ga Islam tana jaririya gwanin sha'awa Mami ba ruwanta duk hiran da ta zo bakin ta faɗa masa take yi, har tana ce masa ta sha wahala an har kusa yi mata C.S Allah ya taimaka ta haihu da kanta. Shekaru sama da ashirin kafin ta haifi Islam dole ta ji jiki.

Wani maganarta na ta ya yi ɗan mirmishi wani kuma ya jinjina kai. Shi dai ba hira yake yi mata ba domin bai iya ba ita ce ke hiranta yana amsa mata in buƙatar hakan ya ta so, to sanin halin shi itama ba ta damu ba. In hira ta yi mata daɗi har dafa kafaɗan shi take yi.
Akwai wani suna da take kiran shi yana yi masa daɗi sosai.

Muhammadu ta ke ce masa, ta kan jima ba ta kira shi da Lamiɗo ba. Ko ta ce Ɗan Ammah amma in ta kira shi Muhammadu sai zuciyarsa ta yi masa ɗumi.

Lokacin salla la'asar ne ya yi, ya sa hiran ta su ta katse. Ta koma ɗaki shi kuma ya shirya ya fita masallaci akwai masallaci a cikin hotel ɗin tunda duk musulmai ne.
Sai dare suka koma asibiti suka sake duba Ummu Salma ba su daɗe ba mintina talatin ne kawai suka ba su, suka ce za ta ci abinci ta kwanta.
Tana ji tana gani suka tafi suka barta har kuka sai da ta yi. Kewa duk ya ishe ta ga kaßaici ita kaɗai ba wanda ta sani sai baƙin fuskokin Nurses da likitoci larabawa.
Ga shi duk a tsorace take gani take yi kamar wannan karon ma haihuwa za ta zo da targaɗa kamar ta baya. Sannan ba ta so a sake yankata ta fi so ta haihu da kanta wannan karon yawan yin C.S ga mace na rage mata karfin jiki.
Received at 18:55
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
lokacin ma ya san Yariman ya zo garin ko shi Mai martaba bai yi zencen da shi ba Fulani ce kawai ta sani kuma ba ta faɗa ma kowa ba.

Sannan a daran ya sake haɗa musu wata ganawar ta sirri da malamai da masu iko a ɓoye ba tare da kowa ya sani ba. Suma tattaunawar ta su ta ɗau tsawon awanni huɗu kafin Mai martaba ya sallame su.

Washegari kuma Mai martaba ya karbi baƙuncin Baban Alkalin kotun musulunci na jihar Katsina Qadi, shima ɗin tattaunawa ce ta sirri, bayan tafiyar shi ya gana da Limamin jumma'a na masallacin cikin fada a daran kuma ya gana da sauran hakimai da dattawan fada.

Daga lokacin Masarautar aka fara yaɗa jita jitan magana duk da ba wanda ya san asalin abin da Mai martaba yake son aiwatarwa amma maganganun nata ta shi tunda ba a taɓa ganin Mai martaba ya yi irin waɗanan ganawar cikin sirri haka ba, ba kuma wanda ya sani waɗanda suka sani ɗin kuma ba su da ikon cewa komai.
Manyan majalisar zaɓen fada da suka yi ta shiga suna fita su ne su Waziri, Madaki, Galadima da Yarima Lamiɗo, sai Sallama musamman mai sharia da zuwansa fada wajen su uku.

Kuma ga shi ba wani magana da ta fito daga fada daga yawun Mai martaba amma mganganu na ta tashi. Gimbiya Shahida ta so tambayan Mai martaba abin da ke faruwa ba ta samu fuska ba, ba ma ita ba duka sauran mata ya ce su jira lokaci kawai.

Gimbiya Hadiza har ta kira Bilkisu ta faɗa mata wani abu zai faru Yarima ya zo Daura kuma Mai martaba na ta ganawar Sirri da Manyan wakilan fada. Ga shi daman Bilkisun ba ta samun shi a waya har ta shaƙa da kishin ya tafi can wajen Ummu Salma ya manta da ita ashe yana Daura, kuma bai faɗa mata zai zo Daura ba.

"Ya Hadiza me ke faruwa ne? Bana samun wayar Lamiɗo wajen kwana uku kenan?

"Ba za ki same shi ba, ba shi da lokaci ana ta tunanin ko sabon Sarauta Mai martaba zai yi masa"

"Akwai Sarautan da ta fi Yarima ne?

Gimbiya Hadiza ta ce" Ko Chiroma zai yi masa, kin san Sarautar Yarima ba dole sai wanda zai gaji Sarki ba ita kuma Sarautar Chiroma magajin Sarki ne kuma babban ɗan sarki ake ba ma wannan Sarautar na fi tunanin wataƙila tunda Mai martaba na son ya gaje shi bayan ba shi shi yasa ya yanke shawaran yi masa wannan sarautar yanzu."

Bilkisu ta gamsu kamar yadda itama Gimbiya Hadiza take tunani. Ba ma su ba kowa tunanin da yake yi kenan. Ba wanda ya yi tunanin Mai martaba zai iya tsallake gurbabe masu girma har ya kai matakin da ya yanke a yanzu.

*

Ummu Salma ma daga nan Egypt hankalinta duk a tashe tunda Lamiɗo ya tafi bai kira ta ba, itama ta kira shi ba ta same shi ba. Hankalinta ya ɗan kwanta ne da ta kira Fulani ta ba ta tabbacin yana lafiya har a lokacin yana Daura wasu azurori ne masu girma suka sha masa kai, shi ya sa ta ɗan kwantar da hankalinta.

Amma mamakinta kwana uku huɗu a ce Hamma bai kira ta ba, ko Daura ya je ba ya kwana bai neme ta ba in ma an kwana ba za a yini ba. Amma har kwana huɗu shuru babu wayarsa sannan abin da ya ba ta mamaki daɗewarsa a Daura ahalin ya ba ta tabbacin in ya daɗe ne ya yi kwana biyu. Ga shi Fulani ta ce wasu uzirori sun riƙe shi, da ta kasa gane wasu irin uzirori take magana, suma can Adamawa suna video call ko vioce call suke yi da su ko ta wayar Baɗɗo ko ta wayar Hamma Saddam suma ɗin sun ce ba su yi magana da Lamiɗon ba.

Har Ammah ta ce tun saukarsu da suka yi magana ta kira wayarsa a kashe a bakin Mami ma take jin Mai martaba ne ya kira shi yana can Daura. Babu wanda ya yi tunanin a halin da Lamiɗo yake ciki ba ya ma tunanin su, tunanin tarin wasu nauyin alummar dake ƙoƙarin rataya a wuyansa yake yi. Waya ma ya manta da ita. Barci sai dai ɓarawo kawai ke iya fizgan shi.
Yana cikin damuwar, kuma dole ne ya cika Umarnin Sarki ko yana ko ba ya so.

Mami ce dake tare da Ummu Salma ke kwantar mata da hankali. Domin ba a so kuma ta shiga damuwa har jininta ya ɗaga. Hankalinta ya kwanta tunda yana can Daura ta tabbatar yana lafiya amma nemanta ne da bai yi ba zuciyarta ba daɗi.
Received at 18:55
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ranar talata da suka cika sati ɗaya a kasar na Egypt, ya kama kwanan Lamiɗo biyar da tafiya kenan cikin dare 8 ga watan November misalin uku na dare Ummu Salma ta haihu, Alhamdulillah kawai za ta ce da godiya ga Allah.
Kamar wasa tana cikin barci naguda ya tashe ta daman akwai wata na'ura ta emergency dake gefenta an faɗa mata in wani abu ya taso ta danna wannan na'uran zai yi ja, ya yi ƙara domin a san tana buƙatar taimako.

Da ta ji ciwon baya ga maranta ya riƙe ta so ta miƙe ta kasa da wani ciwon maran ya tirniƙeta ba ta san lokacin da ta matsa abin nan ba ya yi ƙara cikin lokaci sai ga likitoci da Nurses sun cika ɗakin da take ana gwadata aka ce haihuwa ce ta zo gab. Ba ta taɓa tunanin za ta iya haihuwa da kanta cikin lokaci haka ba.

Da fara naƙudarta da haihuwarta mintina talatin ne ta haifi ɗiyarta mace kyakyawa ƙatuwa da ita kamar Lamiɗo ya yi kaki, kuma cikin ikon Allah ko ƙaruwa ba ta yi ba.
Cikin awa ɗaya nurses suka gyara ta, tare da Baby gabaɗaya ɗakin ya dawo fes kamar ba a haihu ba.

An yi ma jinjirar wanka an saka maka kayan sanyi masu kyau daman kayan haihuwan da suka taho da shi suna cikin drowers ɗin cikin ɗakin. Nan da aka kawo ƙaramin gado na jariri aka saka ta a ciki sai wuntsila kafafu take yi irin na yara amma kafin nan sai da aka ba ma Ummu Salma jaririyar ta rumgume ta ji ɗuminta tana hawayen farinciki.
Ta ba ma Nurses ɗin wayarta suka ɗauke su hotuna sannan suka yi ma jaririyar hotuna itama

Ko kafin Asuba har ta koma barci, kamar ba ta haihu ba.
Ummu Salma ta tabbatar wannan asibitin wajen kulawa da ba ta ki duk haihuwanta ta haihu anan ba, ga shi jininta bai hau ba sun ce 120 sannan su za su yi maka komai kamar kana ɗakin mahaifiyarka.
Ga abinci mai rai da lafiya da zai ingata lafiyarka.

Karfe shidda na safe ta tashi barci Nurses suka tashe ta, ta yi wanka ta gasa jikinta sosai suna faɗa mata kar ta yi amfani da ruwa mai zafi sosai saboda BP. ta ce musu to amma ba ta sauraresu ba, ba za ta biye musu ba gwara ta gasa jikinta. Da harshen turanci suke magana tana ji sai dai mayarwa ne take amsa musu da iya abin da ta iya kuma suna ganewa
A karo na farko Ummu Salma ta ji ra'ayin son komawa makaranta domin maganar Hamma Kabiru gaskiya ne ilimi ginshiƙi ne na rayuwa akwai in da za ka je ka ga ana yi babu kai.

In ta ga yadda Mami ke turanci sai ta ji ta burgeta har ta ji wataƙila ta sauya ra'ayi ta koma makaranta. Sun yi ma jinjirar wanka an sauya mata kaya ba su damu da nono ba har sun fara ba ta madara. Ita ma daman ruwan nonon bai zo ba har matsawa ta yi sai dai kaɗan kaɗan, Itama sun ba ta abin kari mai kyau ta karya sannan ta

Please Login or Register in order to submit comment