Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

za mu dinga kiran takwaran Mami Banafsha."

Baɗɗo ta amsa da yanzu kuwa sun rabu bayan ta ce Umma Salma ta ɗauki hoton Banafsha ta tura mata, tana hannun Mami ne, likitocin ma ba sa bari ana ɗaukanta sosai sun fi son ta a kwance a ɗan gadon ta.

Sai da Nurses suka shigo sannan Banafsha ta dawo gadon ta lokacin Ummu Salma ta ɗauke ta hoto an yi mata gayu da wasu fararen kayan sanyi. Nan take ta tura ma Baɗɗo itama a karo na farko ta yi status da hoton Fatima(Banafsha)

"Alhamdulillah it's a Baby girl. Today, we named her Fatima, Fatima Muhammad Nasiru(Banafsha.)"

Haka ta yi status, waɗanda suka gani suna ta Allah ya raya. Hamma Saddan ne yan gaba gaba tuni ya ɗauka shima ya yi status da shi.
Sannan Iklima da su Kaltume duk sun gani sun yi mata barka tana da lambar Hajiya Falmata itama ta gani ta ce haihuwar na su ne tunda takwaran Mami ce daman ta yi mata barka da suka yi magana ta wayar Mami.
Sai su Adda Suwaiba suna ta Allah ya raya tare da tambayan yaushe za su dawo ta ce an kusa.

Ta tura ma Hamma Lamiɗo hoton, ya tafi sai dai kafin ya duba ne aiki a baya ma ana fama ballatana yanzu. Ba ta yi wani mamaki da Bilkisu ba ta yi mata barka ba, ba su da lambar juna amma ai haihuwa ta wuce wasa.

Ranar ta kama bakwai da haihu itama ta sha kwalliyarta cikin leshi , kamar ba asibiti ba.
Sai ga Bilkisu ta yi ma Mami voice call sun gaisa.
Ta ce a ba ma Ummu Salma wayar, suka gaisa ta yi mata barka a status ɗin Adda Safina ta ga sunan jaririyar Fatima.

Da yake ba su saba waya ba, kawai dai ta yi mata barka ne kawai sai ta haɗa ta da yara Sultan da su Beena har da Hanan suna ta cewa suna son ganin jariri.
Received at 15:16Reactions: ❤ 19, 👏 2
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Sai Mami ta ce a kira video call, Mamin ta karɓi wayar ta kira yaran suka ga ƙanwarsu suna ta zillo a waya kamar za su faɗo ta cikin wayar lokacin sun yi shirin makaranta ne safiya ce a can Nigeria domin uniform ne ma a jikinsu. Har su Sabuwa sun leƙo sun gaishe da Ummu Salma da su Debora suna ta murna da suka ga yar jaririya fara sol da ita.

A cikin masu yi ma Ummu Salma murna da status ɗin da ta saka har da Shamsiya da yake ta yi saving ɗin lambarta. Ta gani ta yi mata magana da tambayan ta haihu ne? ta amsa mata da eh, ta yi mata barka da murna har tana cewa za ta zo barka tana ina ne?

"Ina Egpyt a can na haihu amma zan dawo Jimeta nan ba da daɗewa ba"

Jiya sun yi magana da Hamma in suka dawo Jimeta za ta zauna kafin komai ya kamkama su koma Daura gabaɗaya.

Shamsiya ta yi mata alƙawarin za ta zo, in ta dawo ta kira ta ta ce in sha Allahu.
Tausayin Shamsiya take ji, duk da ta tsane ta a baya amma yanzu tausayi take ba ta, Habib ne har abada bai taɓa ba ta tausayi ba.

Abin da ya aikata ne ya ga sakamakon sa. Hanan ɗin da ya so ya salwartar ita ce dai sanyin idaniyarsa. Ba shi da wani ƙwai a duniya Allah ne ya jarabce sa.
Kuma ya ga ishara ga rai ga lafiya amma haihuwar ce Ubangiji ya hana shi domin nuna masa ishara kan niyarsa ta baya.

An yi yanka raguna huɗu a can Adamawa Ammah ta yi taron suna an ci an sha, naman suna kuma an soye shi an yi rabo sai fatan Allah ya raya Fatima Banafsha.

Sakeena daga England ta yi ma Ummu Salma barka haka ma Badia'tu daga Nigeria sai Gimbiya Shahida da suka sake yin magana Hajiya Kilishi da Hajiya Zaliha ba ma sau ɗaya ta yi magana da su ba Saleem dai ba su yi magana ba ya dai yi mata saƙon ta ya murna da Allah ya raya ta chart.

Kwanan Hamma Kabiru uku da zuwa suma suka fara shirin tahowa gabaɗaya sun sake magana da Hamma sau ɗaya ya ce tunda likitocin sun ba da tabbacin ba wata matsala to ba amfanin zaman su taho kawai gida.
Sai da suka kwana ashirin cif da saukan su a ƙasar Egpyt a daran ranar Jirgi ya kwashe su zuwa Nigeria.
Ummu Salma da Banafsha sun sha hotuna da larabawan kasar Egypt kafin su baro kamar kar su dawo saboda yanayin kasar akwai daɗin zama.

Ta Abuja suka sauka da safe a gidan Hamma Jibo suka fara yada zango
Nan Mami ta fara gasa jikin Ummu Salma can fa ba sa bari ta yi amfani da ruwa mai zafi saboda BP ita kanta Banafsha da ruwa ɗumi kawai suke mata wanka wata rana ma goge jiki ne.

Nan suka kwana Adda Nauwara ta dama mata kunun tsamiya ga ferfesun ganda da na kayan ciki, shi Hamma Kabiru a jiya ya bi jirgi zuwa Taraba.
Ya ce za su dawo tare da Adda Safina da yara in sun koma gida.

Su kuma sai a washegarin bayan sun kwana sun hatse suka bi jirgin Yamma zuwa Adamawa Yola.
Hamma Saddam ya je da motar Hamma Lamiɗo ya ɗauko su zuwa gidan Ammah.

Tuni an gyare ɗakin Umma Salma nan ta sauka daman ta ce ma mijinta anan wajen Ammah za ta zauna ya ce yadda take so haka za a yi.

Gida ya cika da su Adda Suwaiba da su Ummi ikki ɗakin Umma Salma cike ana ta hira ana mayar da magana da labarin komawa Daura Adda Suwaiba na faɗin za su sha bikin naɗin Sarauta har tana cewa kowa ya tanadi kuɗi shigar manyan mata suma za su yi ana ta dariya.

Ummu Salma ta tura ma Lamido sakon sun sauka.

"Mun dawo gida Mai martaba na"

"Welcome back home Sarauniya ta"

Ta yi mamakin yadda ya samu sararin bata amsa shi da yake can yana fama da sha'anin mulki ga shi komai sabo zai gani tunda baƙo ne hakan a gare shi a matsayin shi na Sarki.

Kowa sai mamakin kiban Ummu Salma yake yi ana cewa ƙasar waje ta karɓeta. Banafsha ma ta yi ɓul, kuma suna dawowa Ammah ta fara mata kunu gero da na shinkafa sai ga ruwan nono, Ummin ikki ke yi mata wankan jego, Mami ta koma Kaduna ita da Barira ta duba gida tunda ta daɗe bata nan.

In Lamiɗo ya samu dama suna waya da Ummu Salma bayan kwana ɗaya haka watarana ma duk dare.
Received at 15:16Reactions: ❤ 19, 🔥 1, 🥰 1
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Yanzu a ƙarshen watan nan Mai martaba mai murabus za su yi ƙaura zuwa can gidan shi na cikin garin Daura an tsara za a yi shagalin naɗin sarautar Lamiɗo a farkon watan December su Hajiya kilishi sun haɗu sun tattauna da cewa za a haɗe shi da taron sunan Banafsha a Masarautar Daura gabaɗaya.

Da suka zo barka ne suka faɗa ma Umma Salma.
Hajiya kilishi, Hajiya Zaliha da Hajiya Binta sai Gimbiya Shahida da Gimbiya Amaratu da matar Waziri da Shamaki.
Sun kawo akwati guda goma biyar na mai jego, biyar na Banafsha, sai kuɗi a takarda miliyan biyu daga Fulanin Daura.

Sai kyautar mota sabuwa GLK daga Uban Lamiɗo kakan Banafsha tsohon Sarki mai murabus, Alhaji Dr Nasiru Muhammad Shitu mota na can masarauta tana jiran su.

Wani kaya sai amale, sun ce ranar tara ga watan December za a yi naɗin saboda haka Ummu Salma ta yi magana da Lamiɗo, su fara shirin komawa can Daura domin gabatar da shirye shirye, ga shi kuma za a haɗe shi da taron suna
Sannan sun ce duk waɗanda za su je akwai jirgin da Mai martaba zai ba da, sannan za a turo lafiyayuun motoci daga Masarauta ta ɗau mutane tare da wasu kaya.

Lokacin da suka zo Shamsiya na gidan tare da Habiba da Gwaggo sun zo barka tunda Shamsiyar da ta gaji jiran kiran Ummu Salma sai ta kira ta shi ne Ummu Salma ta sanar da ita ta dawo tana gida shi ne su ka zo zuwan su kenan ma sai ga baƙin Masarauta.

Sai suka koma gefe suna ganin arziƙi, Habiba a fili take faɗin Allah ya rabamu da talauci. Domin talauci bai yi ba Annabi ma Salallahu alaihi wasallam ya nemi tsari da talauci.
Sai da su Hajiya Kilishi suka tafi sannan aka ma tuna da su Shamsiya.

Da gayya Baɗɗo ta ce in za samu zuwa suna gayyatarsu Daura naɗin Sarauta da taron suna tun kafin Shamsiya ta amsa Habiba ta ce za su je. Domin za ta je ta ga kuɗi da masu kuɗi.
Shamsiya na faɗin sai sun tambayi Habib a zuciyar Habiba ta ce bai isa ya hana ta ba, duk da yanzu abubuwa sun ragu tunda yana koyarwa yana kuma aikin karfi kamar aikin gini sannan ga Shamsiya tunda ya aure ta ya samu wasu sauƙin abubuwa. Amma a rashin mutumcin Habiba ba wanda ya ragu ita sai Habib ya sake ta shi kuma ya ce da ita aka fara da ita kuma za a gama. Suna gidan har yamma sannan suka tafi.

A daran Ummu Salma ta kira Mai martaba mai murabua daman da suka dawo sun yi magana sau ɗaya ya yi mata barka da samun kai lafiya. Godiya ta yi masa ya ce bakomai kin iya haihu tunda kika haifi Batula. Ya ce yana jiran amaryan sa ta zo ta gaishe shi. Ummu Salma ta amsa da in sha Allahu cikin ladabi mai yawa.

Da suka yi waya da Lamiɗo ta faɗa masa zuwan su Hajiya kilishi duk da ya san da zuwan su amma bai gwalese labarin ba.

Faɗa mata yake yi an gama gyaran Masarauta Bilkisu za ta fara yo gaba ita da yara daga Lagos daga baya ita Ummu Salama sai ta taho daga nan Adamawa ta ce babu matsala hakan ma ya yi.



*Janafty*
Received at 15:16Reactions: ❤ 19, 🥰 1
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
*FJ littafin kuɗi ne 1k a manhajar Telegram tura kuɗin karatu ta wannan acct ɗin 9069067488 Opay Jamila Umar shaidar biya ko tuntuɓa ta waɗannan lambobin.*
08032773332
09069067488.

BAYAN SATI ƊAYA.

Ta ko'ina shirye-shirye ya fara gudana. Ga shi yau har biyar ga watan December saura kwana huɗu bikin naɗin sarautar Lamiɗo tare da taron sunan Banafsha.

Tuni Mai martaba tsohon Sarki mai murabus da iyalansa sun bar cikin masarauta sun koma gidansa dake cikin garin Daura ɗan gaba kaɗan da masarautar, shi kenan fa haka rayuwa take ko mutuwa ne haka za a yi a gama suma ga shi kamar ba su zauna a cikin masarauta ba yau ga shi zamansu ya ƙare daman in yau kai ne gobe ba kai ba ne. Allah ya sa mu dace.

Lamiɗo ya so Fulani ta zauna tare da shi a Masarauta ta ce ba za ta zauna ba duk in da Nasiru yake tana tare da shi. Tare da ita aka koma wancan gidan shima kato ne mai kyau na alfarma da zanen gidan Sarauta a jikinsa. Masarauta kuma tuni ana ta gyara an sauya tsarin duka bangarorin gabaɗaya komai sabo ake saka kama daga furnitures da komai da fenti sabon Sarki sabon gyara.
Tuni tsarin katin gayyata har ya fara isa ga manyan kasa da za a gayyata. Masu Sarautu ma'aikatan Gwamnati, gwamnoni yan kasuwa yan majalisu da sauran su.

Daura za ta cika ba matsaka tsinke baƙi ne za su sauka a garin daga kowani yanki na Nigeria. A can Daura ma an kacame da shiri domin kaf iyalan Marigayi tsohon Sarki Muhammad Shitu za su hallaci wannan naɗin kama daga waɗanda ke gida Nigeria da mazauna kasashen waje, kaf ƙannen Lamiɗo za su taho gida ayi biki wannan naɗin da su tare da bikin sunan Fatima(Banafsha).

Ummu Salma ma anan Jimeta shiru kawai suke yi, suma daga bangarensu gayya guda ne ce za su tafi Daura. Kaf yayyenta maza da matayensu tare da yaransu za su je Daura wannan taron naɗin sannan akwai wasu daga Mubi irin su Baffa Umaru Umma Balki da Umma A'i ita Umma Salamatu tunda tana fama da ƙafa ya'yan ta mata ne guda biyu za su je, sannan har da Hafiz da matarsa Salima Ummu Salma ta gayyata tunda su suna ma cikin garin ne a can kawai za su haɗu. Ummin ikki har da Iklima da Kaltume Ammah na cewa ba za ta je ba kowa na ce ta je amma ta ki Ummu Salma ta faɗa ma Lamiɗo abin da Ammah ta ce ya ce za ta zo in sha Allahu zai yi magana da ita.

Har kuma yau bai zo ya ga Ummu Salma ba, ballatana Banafsha sai dai a hoto ko kuma a video call ta gaji da yi masa ƙorafin bai zo ya gansu ba ta ƙyale shi. Bilkisu gobe za su baro Lagos su sauka a garin Daura Hidaya ta faaɗa ma Harira da suka yi waya. Su za su fara sauka ita Ummu Salma tana tunanin sai ranar alhamis, wasu kuma dole a mota za su je saboda tafiya da wasu kayan.

Mami daga can Kaduna za ta dira a ranar Jumma'a tunda taron naɗin ranar asabar ne. Tare da Islam da Faruk da Hajiya Falmata za su je Daddy yana Abuja amma a ranar asabar ɗin zai isa can Daura. Shiri kawai kowa yake yi saboda za a je a baza kafacity Ummu Salma ta ba da ɗinkuna sama da kala talatin ta ɗiba cikin kayan da aka kawo mata daga Daura sannan ta sake ɗinka na cikin lefenta domin har lokacin ba su ƙare ba. Ga Lamiɗo ya tura mata 5M bayan ATM ɗin shi dake hannunta kuma akwai kuɗi a ciki duk ta haɗa ta yi siyayya ta yi duk abin da za ta yi in ma bai isa ba ta faɗa masa.

Ɗinkunan daman Kaduna ta aika da shi telan Mami na zaria ya iya ɗinki shi zai ɗinka mata, nan Jimeta ma ta bayar da wasu tare da na Harira sannan an yi ma Beena da Hanan wata atamfa gold mai kyau iri ɗaya.

Ba anko za a yi ba amma an ce kowa ya ɗinka leshi na fita kunya kowa ya siya kalan na shi daidai ruwa daidai kurji. Duk da akwai leshina masu tsada a ɗinkunan Ummu Salma sai Mami ta saka siyan wani na miliyan uku da rabi wanda za ta saka ranar naɗin a can Kaduna Mami ta siya ta ba da ɗinki bayan an tura ma Ummu Salma ta zaɓi kala sannan ta sake siyan gold na miliyan huɗu ta haɗa da kuɗin da Fulani ta ba ta, ta siya domin Mami ta ce ɗiyarta ta kai kuma itama ta isa ta yi shigar ke ce reni da alfarma Ammah ce ke cewa su rage kashe kuɗin nan sun yi yawa Mami ta ce kuɗi tunda akwai su za su yi ta kashewa kamar ba su san zafin su ba.
Received at 15:21Reactions: ❤ 14, 👏 1
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ita kanta Ammah miliyan uku Lamiɗo ya tura ya ce a yi mata siyayya kuma ya ce sai ta je Daura. Ba tare da ta sanin ta ba Adda Suwaiba ta siya mata rantattsun kaya masu tsada aka ba da ɗinki kowa fa zai je ai ba zai yuyu a barta ita kaɗai a gida ba.

Bangaren gyaran jiki kuma har skin care Ummu Salma ta je an yi mata sannan ga jego sai ta yi wani kyau da haske ga shi ta ɗan yi kiba kamar ba ita ba. Sannan har ƙunshi da gyaran kai anan Jimeta za ta yi kafin su tafi maganar kayan gyara majalisar ɗinki duniya ma wannan karon ba ta jira Mami ba da kanta ta yi ma Surayya Dee 080322773332
Bojuwa waya ta haɗo mata package ɗin mai jego har an aiko mata da shi ta fara sha tunda jinin haihuwar ya tsaya ta yi tsarki har ta fara salla. Banafsha ma acan Kaduna Mami ta yi mata siyayyan kayan alfarma da za ta ci taron suna da shi, domin itama ranar ai ranar ta ce.

Tunda December ta shiga kowa shiri yake yi in aka taru a falon Ammah ba a da magana sai na taron naɗin da za a yi ma Lamiɗo a Daura abu kamar wasa ƙaramar magana ta zama babba. Irin manyan baƙin da aka gayyata ma kawai abin birgewa ne.
Abin da ya danganci wannan daga can Masauratar Daura ake gudanar da duka shirin, su nan sai dai ƙarishe kawai amma can suke da shiri sosai.

Lamiɗo yanzu ya zama babban mutum nauyi ya hau kan shi ba a cika samunsa ma a waya ba. Ko Ummu Salma sai can dare suke magana yanzu ma da abin ya taso na taron naɗin nan sun kwana biyu ba su yi magana ba. A chart ma ta yi masa sako bai buɗe saƙon ta ba, rigima take yi masa da cewa in har ya bari ta zo Daura to sai ya biya kuɗin siyan baki zai gansu ita da Banafsha da ta yi fushi da shi, a tunanin Ummun Salma ko ma ya ya ne ai sai ya samu ko bai kwana ba ya zo ya gansu ya koma ita ba ruwanta da wani Sarki mijinta kawai take ji amma ya yi mata nisa tana tunanin ko can suka koma ba za ta samu ganinsa sosai kamar yadda take samun ganin shi a Lagos in yana gari ba. Yanzu abubuwa da dama sun canza, in kiɗa ya canza dole rawa ma ya canza.

*
Da daddare ne duk suna falon Ammah suna ta hira, hiran daman ba ya wuce hiran taron naɗin Sarautar da zai gudana a garin Daura.
Ammah ke zaune a ƙasan cafet tana rike da Banafsha da ta fara rigima ta karɓeta sai Hamma Saddam da Abdulrrahaman sai Hamma Abdullahi da Hamma Abdulrahim, suna zazzaune saman kujerun falon Ammah, Ummu Salma da Baɗɗo ma duk suna falon ana hira ana faɗin irin kafaciy ɗin da mutanen Jimeta za su baza a garin Daura.
Harira na ciki ta kwanta.

"Ina faɗa muku, irin shigar da zan yi zan fito asalin ƙanin Mai martaba Sarkin Daura Muhammad Lamiɗo."

Hamma Saddam ya faɗa, har yana miƙewa yana gwada irin tafiyar da zai yi ranar ana ta masa dariya
Ammah na faɗin ya yi addu'an Allah ya sa yana raye da rai da lafiya.

"Ammah ina raye da ikon Allah, da lafiyata in sha Allahu."

Ya amsa mata da sauri, kamar yana jira nan ma dariya aka sake saka masa.

"Ai in dai ba mutuwa Saddam ya yi ba, to ko yana gargada sai ya je Daura."

Hamma Abdullahi ya faɗa, Hamma Abdulrahim ya amsa da cewa ko yana tashi daƙyar ne sai ya je saboda yadda ya ci buri sosai.

Ya ce wallahi in bai samu zuwa Daura ba akwai matsala irin yadda yake saka katinan gayyata naɗin nan a duka paltform ɗin shi na Social media kowa kawai jira yake yi ya hango shi a kusa da Sarkin Daura a ranar.

"Ni fa ba wanda bai san Hamma Lamiɗo yayana ba ne, in ban je ba akwai matsala."

"Za ka je in sha Allahu."

In ji Hamma Abdulrahaman ganin Hamma Saddam ɗin ya fara karaya yana cewa su yi shiru don Allah baya son ma maganar suna ta yi masa dariya har da Baɗɗo.

Ummu Salma ce kafarta ba safa Ammah ta fara mata faɗa.

"Sanyi ake miki gudu ya kama jikin ki, tashi ki je ki saka safa sannan ki saka hijabi ki rufe jikin ki."

Tura baki take yi, ta gaji da wannan jegon zafi take ji ga shi Ammah ta hana ta amfani da fanka yanzu in ma a falo ne in dai tana zaune sai ta ce a kashe fanka ba ta da damar zama a ƙasan cafet sai Ammah ta yi magana in ta zauna ba safa ma haka sannan ba ta barinta saka wasu kaya haka, sai masu nauyi da za su rufe mata jiki ruf ta ji ɗumi, ga kunun da take dama mata duk safiya da maraice abinci ne
Received at 15:21Reactions: ❤ 15, 🥰 2, 👎 1
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
mai rai da lafiya Ammh ke matsa mata sai ta ci, ga shi wanka safe da rana ba da ganye ba ne, amma dai da towel ne, tunda Umma Balki ta koma sai ta koma tana yi da kanta Ammah dai ta ce in ta gasa jikinta ita ta sani in ma ba ta gasa ba, ita ce za ta ɗanye ce ita dai ba ruwanta. Dole Umma Salma ta dake tana kula da kanta kuma ta ga amfanin haka ɗaki ta koma ta saka safa doguwa domin Ammah ba ta barinta ta saka gajerun da take da su na gayu sai ta ce wai ba safa ba ne ta siya wasu dogaye masu kaurin tsiya ga su har gwiwar kafa in ba ta saka ba Ammah ta dinga masifa tana faɗin da ta bi uwarta can Kaduna ita ba za ta iya da wannan abin nata ba.

Hijabin ta saka har ƙasa ta rufe jikinta ta koma falo, aka cigaba da hira ana ta maganar Baffa ya kusa shekara a kasa Allahu akbar.

"Ranar mun kai wani maƙocin mu da ya rasu a can, na kasa gane kabarin Baffa alaman da muka sanya ya bace Ammah an zuba da yawa a cikin shekaran nan wallahi su Baffa suna can ciki ba ma zan iya gane wajen ba."

Hamma Abdullahi ya gama faɗa yana jinjina kai.

"Allahu Akbar. Allah ya gafarta maka Baffa Ubangiji ya sa kana cikin rahamar Ubangiji."

Ammah ta faɗa tana jin hawaye na cika kwarmin idanuwanta Banafsha na cikin jikinta ta rufeta ruf ta sake rumgumeta. Da a ce yau Baffa na raye ya zai ji in har ya ga jinin Ummu Salama da Lamiɗo ga shi yau Lamuɗo ya zama Sarki ga shi Baffa ba ya raye shi daman ya daɗe yana faɗin yana ji a jikinsa watarana Lamiɗo zai iya Shugabantar al'ummar Daura.

Kowa jikinsa ya yi sanyi da tuna Baffa.
Ummu Salma sai da ta share hawaye. Ta jima tana tunanin yadda radaɗin rasa mahaifi yake, sai da ta rasa nata ta san irin zafi da raɗaɗin da ake ji, ta kasa mantawa da Baffa rana ba za ta fito har ta faɗi ba ta tuna da shi ba, Allah ya gafarta masa amma mikin nan na rashin Baffa mai girma ne a zukatansu ba zai gushe ba har abada.

Suka taru suka yi ma Baffa addu'a sannan suka cigaba da hiran tafiya Daura.
Hamma Abdullahi na faɗin jirgin da za a ba da ma ai ba zai ɗauki duka mutanen ba.

"Ai wasu dole su bi mota. Ɗazu ma mun yi charting da Gimbiya Shahida ta ce mota za ta zo ranar alhamis ranar da za mu tafi kenan da yamma ta kwashi wasu da kaya a safiyar Jumma'a kenan za su isa Daura a daran ranar."

Ummu Salma ta faɗa tana cigaba da faɗin Mami ta tsara waɗanda za su rakata. Tunda Hamma Jibo daga can Abuja za su wuce Daura haka ma Hamma Kabiru ya ce ba za su biyo ta nan ba shima ranar alhamis za su isa Hamma Mustapha ne kawai za su biyo ta nan sannan su tafi tare da su Ummu Salama.

"Mami ta ce ni da Ammah da Ummin ikki da Ummu Balki da su Umma A'i, da su Baffa Umaru sai Baɗɗo da ku gabaɗaya ni ban ma san waɗanda za su bi motar ba"

"To ku matan ku bi jirgin ku, mu kuma mazan sai mu tsaya mu tafi a mota za a tafi da wasu kaya ne?

Hamma Abdullahi ya tambaya yana kallon Ummu Salama.

"E akwai kayana a can gida da wasu anan da zan tafi da su gaskiya."

"To ba matsala sai mu yi hakan ko?

Ya faɗa yana kallon Hamma Abdulrrahan da ya jinjina kai ya ce hakan ya yi.
Saddam ya tura baki ya ce jirgi zai bi, ba zai iya tafiyan mota ba.

Hamma Abdulrahim ya ce suma ai ba wai kuɗin jirgin ne ya gagaresu ba, gwara su yi tafiyar mota ko za su ga gari. Ammah ta amsa da cewa tafiya kuma mabuɗin ilimi ba.
Saddam tunda ya ce ba ya son tafiyar mota aka ce sai su tafi tare da su Ummu Salama amma

Please Login or Register in order to submit comment