Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

juna cikin idanuwansu.

"Ba ka yi ba."

"Who tell you! I miss you sosaai."

Ya faɗa yana sumbatar bakinta, ta yi masa mirmishi da fari, kafin ta koma ta kwanta a saman ƙirjinsa.

"Ina son Hamma na "

"I know."

"Nima kin san ina son ki ko?

Ta gyaɗa masa kai, sai ya gyara mata kwanciya a saman jikinsa.
Yana faɗin su yi barci, ta ce to wayarta dake gefe ta zura hannu ta jawo ta shafa haske ya kawo hoton hannunsu ne tare da Banafsha wanda suka ɗauka a Jimeta tun tana jaririya shi ne a fuskar a wayar in ta buɗe wayar hoton su ne ita da Hamma Lamiɗo ranar graduation ɗin su na catering school ɗin da ta yi a Lagos tana son hoton nan sosai.

Shi ya lumshe idanuwa kamar mai barci ita kuma tana duba wayarta, saƙonnni take dubawa sai ta ga Mami ta turo mata hoto tana shiga ta ga hoton Banafsha ne sun je park tare da Mami da Faruk, sai ta ɗago tana kallon shi lokaci ɗaya tana kara masawayar.

"Banafsha an zama yan kaduna."

Ya yi shuru bai yi mgana ba ya buɗe idanuwansa ya kalla ya koma sake ya lumshe idanuwansa

"Hamma "

"Uhm"

"Ko za mu bar ma Mami Banafsha ne?

Ya yi shuru kamar bai ji abin da ta ce ba.

"Ba ka ce komai ba?

Sai da ya ɗan muskuta sannan ya ce" Me kike so na ce? A' a in kina son ki ba ta ita go ahead daman ke ma a wajenta na gan ki."
Kai tsaye ya yi maganarsa amma sai da ta yi dariya

"Aa a ɗakin Ammah ka fara gani na dai."

"Ina zuwa Kaduna saboda ina son Mami sosai."

"To masu Mami ni ma dai ina da tawa Ammah."

Ta fara dariya tana faɗin ita ba ta ce ba shi da shi ba

"Kafin ki ce ne na faɗa miki."

Ta mike zaune daga kan jikinsa. Ta zauna a gefen shi ta yi kwanciyar ruf da ciki da sauri ya ce" Na hana ki ko? Ba ki ga kina da lalura ba ne?
Sai ta yi saurin mirginawa suna fuskantar juna.

"Na bari."

"Better."

Ya gama faɗa idanuwansa na sake lumshewa.
"Ya aiki? Akwai wahala ko Mulki?
Ta gama faɗa tana shafa sajen fuskarsa.

"Na fara sabawa, shekara ɗaya kenan ina matsayin Sarkin Daura."

"Haka ne Allah ya kara tsare mana kai ranka ya daɗe."
Ya amsa da Amin a fatar bakinsa ta fara masa tambayiyo daman aikinta kenan yana amsa mata, yau ma masarautar katsina zai je, akwai taron sarakuna na yankin katsina da zamfara da za a yi.

Ya gaji ya ce mata su kwanta ta kara shigewa jikinsa har ya fara barci ta tashe shi da kiran sunan shi.

"Hamma."

"Ummu Salama."

Ya kirata cikin ƙosawa, ya gaji yana so ya kwanta ba ya son hiran nan a yanzu.

"Na ce miki mu kwanta ko? Bana son magana."

Ya faɗa idanuwansa a lumshe muryansa ta yi laushi alamun da gaske barcin ya ke ji.
Received at 08:04
14 people reacted with ❤
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
"Hamma na tuna wani abu, saƙon da na yi maka na tafiyar Banafsha kaduna me ya sa ba ka amsa ni ba?

Ta gama faɗa tana kallon shi, yana jin ta ya yi kamar bai ji ba har tana buɗe masa idanuwana da hannunta.

"Ka faɗa mini sai mu yi barcin."

Ya takura sosai ba ya son magana a lokacin kuma tana sane ta takura masa.

"Ummu Salama."

Ya kira sunanta a kausashe sannan ya buɗe idanuwana yana kallonta.

"Kina so na yi miki faɗa ne?

"Dililin da ka share saƙo na za ka yi mini bayani."
Ta faɗa cikin shagwaba har tana murza idanuwana.

"Faɗa zan yi miki, shi ne dalilin."

Ta ware idanuwana a kan shi cikin mamaki.

"Me ya sa kika ce ma Mami sai kin tambaye ni?

"Ni zan ce a'a ne?

"Kina so ki haɗa ni da mamarki ta yi mini faɗa ne?

A jere ya yi maganar sai ta rasa ma abin da za ta ce masa.

"Kin sa Mami tana mini faɗa wai na zo na karɓe Hanan wannan ma me nake nufi?

Ummu Salma ta fara dariya tana danne bakinta.

"Ba abin dariya ba ne."

Ya faɗa ba wasa a fuskarsa sai da gimtse dariyarta

"Ni na isa na ce kar Mami ta tafi da Banafsha ne? Ko ke ta ce za ta tafi dake ba zan ce aa ba."

"Na faɗa maka ne saboda ya kama ta ka sani."

"No, ba ki kyauta ba. Ba haka za ki yi ba."

Sai ya ɗan miƙe zaune kaɗan yana kallonta.

"Ba cewa za ki yi Mami na son tafiya da Banafsha ba neman izinina za ki yi ba. "

"Cewa za ki yi Hamma Mami za ta tafi da Banafsha, a matsayin kin faɗa mini na sani ba neman amincewata ba."

Ta ƙura masa idanuwana tana kallon shi wani son shi na kara shiga zuciyarta da gangan jikinta.

"Mami ta ɗauka amincewata kika nema sai ba ta ji daɗi ba. Nima ban ji daɗi ba."

"Sorry ni ce ban saka mganar dakyau ba."

"Is Okay, shi ya sa kika ji ban miki mganar ba. Daman na ce zan miki gyara saboda next time."

"To ba za a ƙara ba."

"Da ni da ke da ya'yanmu duka Mami na da iko akanmu, ita ce za ta ba mu umarni ba mu ne za mu ba ta umarnin ba."

"Haka ne ba za a ƙara ba"

"Aa ni kawai na miki gyara ne, saboda ni ta ga laifina ba ke ba, ke ai tana son ki. Ba za ta ce ba ki kyauta ba."

"Kai ma haka Ammah ke yi, ba ka laifi."

"She's my Mother."

Ya faɗa cikin alfahari, har yana wani mirmishi.
Ta koma ta kwanta a saman kirjinsa shi kuma ya rumgumeta.
Tana so ta yi magana ya yi saurin hana ta.

"Ummu Salama."

"Bana son mgana, in ba za ki yi barci ba you can go back."

Ya furta a hankali tana jin abin da ya ce ta yi saurin kama bakinta tunda ta ji ya fara maganar ta koma bangarenta ta san ta dame shi, da har so ta yi ta ɗauko masa maganar haɗuwarta da Barrister Salamatu Doma amma dole ta yi shuru.

Kamar yadda ya ce ranar Masarautar Katsina ya tafi sai yamma ya dawo, kuma ranar ba a wajensa ta kwana ba Bilkisu ce, sai da kwana ya zagayo kanta sannan suka yi maganar ya ce ba matsala ta fara shi dai ya ce duk abin da take buƙata yana nan yana jiran ta.

Ta kira Barrister Salamatu sun yi mgana abu na farko sunan Foundation sai kuma register da Corporate Affairs Commission CAC.
A katsina ta je ta yi register ɗin CAC Mai martaba ya haɗa ta da dogarai da masu kakin masarauta ita kuma sai ta tafi tare da Harira da Asabe ta shigar da sunan ta a ƙarkashin Foundation ɗin.
Ummu Salma Muhammad Lamiɗo ta yi amfani da shi, daman ko asibiti da wannan sunan take amfani.

Bayan an yi register kungiya ta kafu da kanta ta je ta faɗa ma toshon Sarki ya saka albarka nan take ya ce ya ba da gudummuwar miliyan goma, Fulani ta saka miliyan biyar, Gimbiya Shahida miliyan uku Gimbiya Amratu miliyan biyu, daɗi ya kama Ummu Salma nan da ta fara ƙokarin buɗe ma gidauniyarta asusun banki, guda uku ta buɗe first bank, Gt bank da Zenith bank, da kuma sunan gidauniya Sarauniya Daurama's Foundation, tuni har kuɗaɗen da aka ba su gudummuwa sun samu matsugunni a cikin ɗaya daga cikin bankunan gidanuniya. Ta saka lambarta da lambar Mami tare da Baɗɗo a duka bankunan da ta buɗe ma gidauniyar.
Received at 08:04
13 people reacted with ❤
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Mai martaba Lamiɗo ya ba da na shi gudummuwar shi ya ce tunda akwai tsarin za a raba kayan abinci na tallafi da azumi shi zai ji da komai, sannan ta ɗau masu mataimaka mata ga Baɗɗo daga can Jimeta kamar P.A ɗin ta sannan anan Daura akwai Salima matar Hafiz sai kuma wata Mardiya wazirin Daura kakanta ne, tana aure a gidan wani attajiri a katsina.

Gimbiya Amratu ta haɗa su da Ummu Salma, tunda ita ma Hajiya Mardiyan a can katsina tana harkan gidauniya na ba da tallafi ga mata da ƙananun yara sannan a gefe ɗaya ga Mami ta ce ba za a barta a baya ba. Aikin alheri ne da ita za a yi komai cikin wattani biyu gidauniyar Sauraniyar Daurama Foudation ta zauna da kafafunta har sun buɗe karamin ofishi anan garin Daura Ummu Salma ce shugabar ta fara zama busy tunda suna ta tsare tsaren yadda za su fara fidda tallafinsu na farko na watan azumi dake gabatowa.

Kowa ya ji ƙudirin Ummu Salma sai ya saka albarka ya yi son barka Yayyenta suna ta yabawa da basiranta da ƙokarinta Hamma Kabiru ko da suka yi waya sai da ya ce da a ce ta yi karatu mai zurfi da komai zai zo mata da sauƙi sai dai kawai ta yi dariya ba ta ce komai ba shi dai ba zai daina yi mata maganar komawa makaranta ba.

Bilkisu ma sai da ta ji labari a bakin Sofia, suma a group ɗin su na iyalan Mai martaba Saleem ya faɗa Lamiɗo bai faɗa mata ba kuma da ta ji labari ba ta yi tambaya ba. Itama shiryen shiryen tafiya Canada take yi akwai wani course da za ta yi na shekara ɗaya amma ba yanzu take son tafiya ba sai karshen shekara kuma da suka haɗu da Ummu Salman a bangaren Lamiɗo ba ta nuna mata ta ji labari ba, ballatana ta yi mata fatan alheri, haushi take ji ganin Ummu Salma da wani cikin ita kuma shuru duk ta cire abin da ta saka na tsayar da haihuwar tunanin ta me ya sa za ta zo ta fita har yawan haihuwa?

Ita ko Umma Salma abubuwan dake gabanta ma sun isheta ga tafiyar da handels ɗinta na girke girke tuni Youtube har sun fara biyanta saboda ta gama tara musu abin da suke so amma ita ba wannan ne a gabanta ba, ta kai in da ta ke muradi da kuma fata. Kuɗi ba matsalanta ba ne, suna da kuɗi ita cimma nasara da fata ne kawai a gabanta.

An tsara yadda za a fara tallafin azumi, Mai martaba ya saka an kawo kayan abinci shinkafa na ƙananun buhu guda ɗari biyar ga taliya ga macaroni, ga manja da mangyaɗa ga rafar dubu goma na cefane, kuma a jikin duka kayan akwai sunan Sarauniyar Daurama's Foundation, an raba kayan gida uku ne, ɗaya anan Daura ɗaya katsina Hajiya Mardiya za ta raba ɗayan kuma aka aika da shi Adamawa wajen Baɗɗo a kuma rana ɗaya suka yi rabon bayan sun tattara sunaye, tunda an ta yawo da abin a kafafen sada zumunta bayan tantancewa aka cire adadin mutanen da za su samu tallafi.

Ana azimu saura kwana biyar aka raba kayan tallafin Ummu Salma da kanta a gaban ofoshin su dake gaba da Masarauta kaɗan aka yi rabon mutane dafi dafi kamar salla, ga kayan abinci sannan ga kuɗin cefane duk da mata sun fi yawa amma kuma har da maza, an ɗau hotuna ana ta yawo da shi a kafafen sada zumunta da cewa matar Sarkin Daura Ummu Salma Muhammad Lamiɗo Sarauniyar Daurama ta yi rabon kayan abinci tallafi ga marasa karfi ƙarkashin gidauniyarta na Sarauniyar Daurama Foundation a garuruwan Daura, Katsina da jiharta ta haihuwa Adamawa Yola.

Can ma Jimeta hakan ce ta faru a ƙofar gidan Baffa Baɗɗo ta tara na ta jama'ar tare da taimakon su Adda Suwaiba. A cikin waɗanda suka karɓi tallafin har da Shamsiya domin Ummu Salma ta ce a saka sunanta
Mutanen anguwa suna ta godiya, domin kowa ya ji tallafin daga Sarauniyar Daurama ne sai ya cika da farinciki, ana ta yabon kirkin Baffa da cewa Ummu Salma ta samu kyakyawan tarbiya daga gare shi ne.

Haka ma Katsina ya gudana da jagorancin Hajiya Mardiya Kaduna kuma Mami ita ce kamar ma'aji mai kula da kudaɗen gidauniya, komai ya tafi kamar yadda aka tsara, aka fara azumin ramadana cikin farinciki a lokacin kuma suka fara shirin tallafin kayan salla, shi ga mata ne da ƙananun yara sannan Ummu Salma ta yi Ramadan kitchen by Sarauniyar Dauramas Kitchen, har zuwa karshen azumi ta kuma yi giveaway ɗin dubi hamsin hamsin ga zakarun da suka fi ƙwarewa
Received at 08:04
14 people reacted with ❤
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
wannan abin ya sake jawo mata mabiya sosai kamar yadda suka tsara kafin sallar ma suka raba tallafin atamfofi da yadikan maza na yara, a garuruwa uku nan gaba Ummu Salma na fata tallafin gidanuniyarta ya zaga arewa gabaɗaya. Ga shi yaɗarwar da ake yi a social media ya sa gidauniyar ta yi suna sosai tunda Hajiya Mardiya na tafiyar musu da gidauniyar a zamanance, sannan Barrister Salamatu Doma na iya bakin ƙokarinta da shawara ko gyara, suna ta samun tallafin manyan kuɗaɗe daga manyan mutane da masu Gwamnati, kuma sai abin ya zo da ita matar Sarki ce har gidan Gwamnatin Katsina an kira Umma Salma ta je, ya ba da tallafin naira miliyan ashirin haka ma mai martaba Sarkin katsina ya ba da miliyan goma. Foundation ɗin kuma da yake na masu kuɗi da mulki ce sai ta fara da ƙarfinta ita kanta Ummu Salma mamaki take yi, amma dai tana yawan cewa bayan wannan nasaran nata akwai wani gwarzo, jarumi wato mijinta Mai martaba Sarkin Daura da bai amince ba da duk ba ta yi wannan ba, ga ciki a jikinta har ya turo Allah ya sa ba ta laulayi shi yasa ta samu damar aiwatar da ayyukanta shi kuma bai hana ta ba, sannan ta samu goyon bayan surukanta da mutanen dake zagaye da ita.

Ranar ana gobe salla ma shanaye biyar suka yanka a Daura aka raba ma magidanta da dubu ashirin ashirin na cefane a katsina ma an yi haka sai Jimeta, Baɗɗo ma yanzu ba ta samun lokacin kanta mata suna fita wasu na shiga a gidan Ammah, sauƙin ta ma Ammah na nan ita ke ɗawainiya da Junior, sannan ga Hamma Saddam na gida yana taimaka mata da rubuce rubuce, a bangaren Hamma Abdulrahim ma shima yana ba da na shi gudummuwar, haka ma su Adda Suwaiba suma suna ƙokarin ta ya ta tantance matan da za a raba ma tallafi.

Mami ma acan Kaduna ta yanka Sa itama ta raba shima Daddy ya jefa na shi gudummuwar ya ce ba za a bar shi a baya ba.
bayan na salla sai kuma suka fara tsarin raba ma mata ɗari uku tallafin jarin da za su kama sana'a domin dogaro da kansu, suna da kuɗi sosai a ƙasa ko Hajiya Zaliha miliyan goma ta saka ita da Hajiya Kilishi, har da Hajiya Binta da Hajiya Zannura tare da yaransu duk sun ba da ta su gummuwar, tuni garin Daura da kewaye ya ɗauka kowa Sarauniyar Daurama hatta sauran danginsu dake ƙauye Ummu Salma ba ta manta da su ba tallafin na zuwa musu, sannan kuma hadiman masarauta ma da sauran dogarai da ma'aikata suna cikin alheri domin Sarauniya Daurama alheri ce, da salla haka ta yi ma Mai martaba mgana suma suka samu tallafi su da yan'uwansu gabaɗaya.

Gimbiya Hadiza da yaranta na ta yi ma Bilkisu zugin tana zaune amma Ummu Salma na neman ta ƙwace komai, sunan ta kawai ake ji kamar ita kaɗai ce matar Sarki sannan ganin manyan mata na zuwa ganinta sai suke ganin Bilkisu ta yi sake, ita kuma ta saduda ne yau dai duk adawarta da nuna cewa Ummu Salma ba ta isa ba, sai ga shi a yau ta isa da ita ake damawa ita kuma ba ta son ta yi kwaikwayo ita likita ce ba ta da wannan lokacin shi yasa take son ta faɗaɗa bangarenta domin gobenta, duk abin da suke faɗi tana jin haushi amma kuma ba ta da yarda za ta yi, ba ta gasa amma ko su Fulani yanzu Ummu Salma ce gwana a wajen su, mutanen Daura kuma da kewayenta da sauran matan manya duk Ummu Salma suka sani a yanzu ba ita ba.
Ita a ganinta haka ne amma kuma su a wajen su duk ɗaya suka ɗauke su.

Ummu Salma ko da zuciya ɗaya ta fara wannan gidauniyar da kuma saka ran duk abin da take yi na lada ya kai kabarin Baffa ya samu salama, rana ba ta fitowa ta faɗi ba ta tuna da shi ba, albarkar da take samu na jama'a kuma addu'ar iyaye ce kawai dalilin wannan gidauniyar har waya ta yi da matar mataimakin shugaban kasa matan gwamnoni da matan Sarakai kaɗan ne yanzu ba ta waya da su, suna kawo mata ziyara saboda suna ganin kamar ta zo da wanii abu sabo da ba su sani ba. Ita ɗin da ake ganin ba kowa ba ne, ita yanzu wata ce.

Tunda aka yi sallar azumi babbar salla ta karato Mai martaba Lamiɗo da Bilkisu za su tafi Saudiya da tare da Ummu Salma ne to ciki ya hana ta zuwa. Mami ma za su tafi tare da Daddy da Islam, Faruk kuma wajen Ammah za a kawo shi Barira kuma za ta je gida, itama ta kusa komawa can gabaɗaya za a yi mata aure.
Received at 08:04
9 people reacted with ❤
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Sai a lokacin Mami ta dawo da Banafsha da ta yi wayau, sai ƙirniya kamar Hanan Lamiɗo har yana faɗin ko haka goyon Mami yake? Ummu Salma surutu Hanan surutu da ƙirniya ga Banafsha ma, Ummu Salma ta yi ta dariya da wuri suka tafi tunda Lamiɗo ne amirul hajji na jihar katsina a shekaran Bilkisu kuma na cikin liktocin da za su tafi daga Jahar ta katsina. Ummu Salma aka bari a gida tare da yara Masarauta kuma an barta hannun Waziri kafin Mai martaba ya dawo.

Da Babban sallar ma Foundation ɗin Sarauniya Daurama sun raba shinkafa da atamfofi sun raba ragunan layya ga mazan da ba su da karfi sun raba kayan salla ga mata da yara.
Kamar yadda tsarin ya gudana, Ummu Salma so ta ke yi sai Foundation ɗinta ya yi karfi sannan sai ta fara tunanin samar da wani reshe domin buɗe wajen da za ta dinga koyar da mata da y'an mata girke girken zamani da na gargajiya tare da iya sarrafa fulawa domin samun abin dogara da kai, ta tara mabiya a shafinta na tiktok mabiyanta sama da miliyan buyu, youtube kuma ta kai subcriver dubu dari da Hamsin, kuɗin da suke biyanta duk a gidauniyarta take sakawa tana fata nan gaba kamar yadda suka buɗe ofishi a garin Daura su samar a katsina da Jimeta tare da Kaduna kafin sauran jihohin.

Lokacin da su Mai martaba suka dawo cikinta na wattani takwas ne, duk da ya tsufa ba ya damunta sai dai ta fara fuskantar jiri da kumburin kafa daman kuma a General hospital Daura take awo asibitin da Bilkisu ke aiki sun faɗa mata stress ya saka jininta yana sama sosai sai ta fara jin tsoro, da ta faɗa ma Lamiɗo nan take ya ce zai nemi Visa ta koma Egpyt ta haihu kamar haihuwan Banafsha ba shawara ba ne umarni ne, haka kuma aka yi ya shirya musu tafiya kamar dai baya sai dai wannan karon tare da Ummin ikki ne Mami ba ta nan lokacin za a yi bikin Barira kuma ba zai yuyu ba ta nan ba ta Lagos suka ta shi amma sai da suka kwana uku a gidan su dake Lagos su James nan na ta kula da shi Bilkisu dai na yawan zuwa ita, tunda suna yawan zuwa Lagos hallatar Seminar na su na likitoci, motocin su na nan da shi suka zaga gari da suka zo da yake a can Daura Ummu Salma na amfani da GLK ɗinta da Mai martaba ya ba da ta da haihuwan Banafsha ne sannan akwai motocin Masarauta sai wanda ka ga dama za ka shiga direba da masu kakin masarauta su tuƙa ka bayan haka a ƙarshen wancan shekaran ma Lamiɗo ya siya musu sabbin motoci jifa jifai ita da Bilkisu.

A watan july farko Ummu Salma ta sake haihuwar ɗan ta namiji kato mai kama da Mai martaba Lamiɗo ma a wannan karo daman tun a scan aka ce namiji za ta haifa, ba kuma jira Mai martaba ya dira a ƙasar ya yi ma yaro huɗuba da Hadi, daman a tare ya nema musu visa sune dai suka fara yin gaba daga baya shi ya biyo su, ba su daɗe ba wannan karon tunda lafiya lau ta haihu ba wata matsala kwanansu goma suka dawo Nigeria, sun sauka ta Abuja amma wannan karon a ɗaya daga cikin gidajen Mai martaba suka sauka suka kwana ɗaya washegari suka juya Daura bayan Adda Nauwara da Hamma Jibo sun je sun gan su.

Tuni social media ta ɗauka Sarauniyar Daurama ta haifi ɗa namiji, waya ko har sai da ta gaji da amawa.
Da suka dawo baƙi manya manya suna ta zuwa, musamman amaryan Gwamnar Katsina da suka zama ƙawaye da Ummu Salma, ga Hajiya Mardiya matan sarakuna waɗanda ma ba sa aminta suna girmama ta itama haka sannan kama daga mates ɗin ta wasu ma ba ta iya gane su ba, a can Adamawa ma yan anguwa wasu ma ba ta san su ba suna kiran ta a waya don dai ta zama wani abu shi shi ya sa kowa ke son raɓarta rayuwa kenan.

Rayuwa ta saka yau ita abar girmamawa ce ga kowa, kowa na son ya raɓe ta saboda ta zama wani abu. Shamsiya ko kamar ta yi mata sujjuda, rayuwarsu akwai tausayi har ciki ta sake samu bai zauna ba.
Shi yasa itama Ummu Salma ta yi magana suka ɗauki Shamsiya ta a cikin agent ɗinsu, tana kawo musu sunayen mabuƙata su tantance sannan duk tallafin da za a ba da ana bayarwa da ita, ita kanta Baɗɗo da ke adawa yanzu ta daina daman ta ce burinta kenan Ummu Salma ta samu arziƙin da watarana daga Shamsiyar har Habib a ƙarkashinta za su samu sai ga shi ya faru tun a duniya suna ganin ƙarshen su.
Received at 08:04
14 people reacted with ❤
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
A Masarautar Daura wannan karon aka sake yin taron sunan Hadi wanda Ummu Salma ta ce za su dinga kiran shi Sadauki, tabbas mai sunan Baffa ya cancanci ya zama Sadauki finally dai ta samu mai sunan Baffa shi ya sa aka ce wani hanin ga Allah baiwa ne sannan wani jinkirin alheri ne. Taron sunan da ya haɗa manyan mata masu ji da kansu, ma su ji da mulki da kuɗi bayan Baɗɗo yanzu Ummu Salma na da wasu mutane da suke da muhimmanci amma ba wanda zai kama kamar Baɗɗo a wajenta.

Akwai Badi'a ga Sakeena mutanen England ga Amaryan Gwamnar Katsina duk da ta girme mata sannan ga Hajiya Mardiya ga kuma Hajiya Hauwa(Anty Hairi) sai kuma Dr. Fadila Kabir, Anty Fadila suna da alaƙa da Masarautar Bunza shi yasa Ummu Salma ta san ta, ga Barrister Salamatu Doma, ga Hajiya Aisha Ahmad iya, ta santa sanadiyar Foundation, mace ce mai son kyautatawa da taimakon marasa karfi ga kuma Hajiya Zainab Inuwa(Antysis) itama sanadiyar Gidauniya ta san ta ana ɗaukan nauyi tana kai ruwan sadaka asibitoci da makarantu, itama mace ce mai kirki da karamci. gidauniyar Sarauniyar Daurama ma na shirin tallafa mata domin aikin alherin da take yi ya zagaya garin Funtu'a gabaɗaya.

Kamar sunan Banafsha wannan sunan ma haka Ummu Salma ta sake tara dukiya kamar ba son zafin ta ba wannan karon Ummu Balki da Ummin ikki sai da ta yi sati uku da haihuwa suka koma Mubi Mami ta zo taron suna ba ta kwana ba ta koma gidan ba kowa tunda Barira ta yi aure ba ta samu wata mai aikin ba sannan ga makaranta, Allah ya sa ma Islam na kusa to itama karatu ya saka ta gaba ko sunan Sadauki ba ta samu zuwa ba.

Bilkisu ta shigo ta yi barka ta dauki Sadauki ta gani, daga nan ba ta ƙara shigowa ba amma ta aiko da kayan jarirai masu kyau ta ce a ba ma Sadauki Ummu Salma ta ji daɗi a zuciyarta ta ce Bilkisu ta fara canzawa, sannan har shi kan shi Mai martaba da ta faɗa masa ko da bai yi magana ba amma gefe da gefen bakinsa ya motsa alamun ya ji daɗi.

Rayuwa ta cigaba da gangarawa gefe ɗaya

Please Login or Register in order to submit comment