Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

biyu na dare suka yi barci da asuba kuma ta yi masa zencen gobe Baffa zai cika shekara ɗaya da rasuwa za ta yi girki mai yawa za a yi sadaka ya ce babu matsala. Za a yanka Sa saboda a samu nama, abubuwan buƙata kuma ya ce ta rubuta ta ba ma Jakadiya ta amsa masa da to da safen ma sai da ta ƙara taƙalan shi, sannan suka yi wanka ya fita Fada ita kuma ta tattara ita da Banafsha suka koma bangaren su.

A bangarenta ta shirya yin girkin. an kawo cefane ma su yawa sai da ta ce su Harira su rage su kai babban Kitchen sannan an yanka sa an shigo da naman ta tara hadimai suka gyara aka tafasa. Jalof ɗin shinkafa za ta yi mai kayan lambu da nama, a daran har naman ta saka aka soya, sun yi waya da Ammah suma acan za su yi abincin Sadaka.

Buhu uku za su dafa na shinkafa da miya Lamiɗo ya tura musu kuɗi masu yawa, sauran kuma su Hamma Abdullahi Gabaɗaya suka haɗa, suma sun siya rago an yanka abincin da yawa ne za a kai masallatai da makarantun allo, har da su Adda Suwaiba duk za su zo su taimaka ayi girkin.

Mami da suka yi waya da Ummu Salma ma tun kafin ta faɗa mata za ta yi, Mami ta faɗa mata itama za ta yi abincin Sadaka saboda gobe Baffa ke da shekara ɗaya da rasuwa. Ashe kowa na lissafe Daran ranar ya yi ma Ummu Salma tsawo har mafarkin Baffa ta yi, ya zo ya ga Banafsha suna ta hira ya ce ta gaishe masa da Lamiɗo har tana cewa Baffa Hamma Lamiɗo ya zama sarki, ya ce na sani Auta ina yi masa fatan alheri ya horeta da ta zama mace ta gari.

"Ki yi duk abin da zaki yi ki zama mace ta gari a wajen mijin ki. Ki zama mai ilimin da za ki taimaki mulkin mijin ki ta bangaren alheri Auta "

Da Baffa zai tafi ta dinga kuka ashe a sarari take yi, sai da ta ji Hamma na kiran sunanta sannan ta farka ta ganta a jikinsa sai ta ga tana hawaye ashe da gaske kuka take shi ne take faɗa masa mafarkin Baffa ta yi ga abin da ya ce mata sai ya rumgumeta yana lallashinta.

"Baffa na cikin rahamar Ubangiji in sha Allahu."

Haka yake faɗa yana shafa bayanta alamun lallashi, ranar duk sukuku ta yini kamar ba ta da lafiya abincin Sadakar ma ya ce in ba za ta iya ba Hadimai su yi ta ce za ta iya. Rashin Baffa ne ya taso mata, wato duk wanda ya rasa mahaifi ya yi rashin bango, ballatana ita mai uba ma irin Baffa.

Haka ta zage suka yi wannan abinci takeway ɗari biyar suka yi, ga nama ga ruwa da lemu an raba wasu a cikin masarauta ga hadimai da kuma dogarai, sai kuma wasu dirobobin Masarauta suka fita da shi za su je cikin gari a raba ma mabuƙata.
Lamido kuma a safiyar ranar ya yi sadakar kuɗi, ya gana kuma da matasan garin Daura ya ji ta bakin su, masu karatu da ba su samu aiki ba, ya ce su tattaro tarkadunsu suma yanzu sun shiga gwamnati sannan na ɗa shugaban media team ɗin shi, su za su dinga zaƙulo masa abubuwan dake faruwa a yankin da yake mulka.

A masallaci ma da asuba sai da Mai martaba ya sanar da liman a yi addu'a ga mahaifinsa da ya rasu tare da sauran musulmai, da asuba an yi haka ma da mangariba ma Ummu Salma na bangarenta ta ji ana yi ma Baffa addu'a itama tana saman darduma ne ta idar da salla.

Ta girgiza kai tana hawaye a sarari ta ce Allah ya gafarta maka Baffa mganganun da ya faɗa mata suna mata yawo ya ce ta yi komai domin ta taimaka ma mijinta ta fuskar alheri ta shiga tunanin me za ta yi da za ta taimakama Hamma a wannan jagorancin na shi, sai ta ga buɗe gidauniyar da ta yi magana shi ne farko a ƙarƙashin gidauniyar za a tallafa ma mutane da dama daga wannan Masarautar
Received at 19:42Reactions: ❤ 15, 😁 1
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
A ranar ta kira Hamma Abdulrahaman ta yi magana da shi, shi ne lauya kuma shi ne ya siya mata filayen nan kuma takardun suna hannun shi, shi ta ba ma ajiya daga baya.

Sun daɗe suna mgana ta faɗa masa niyyarta ya ji daɗi sosai ya ce su yayyenta ma ba su kawo wannan tunanin ba su tunaninsu su gina bohol ne saboda sauƙaka ma mutane wahalan ruwa da kuma gina rijiyoyi tabbas ya yaba da tunaninta ya ce zai bincika wannan babban filin za a damƙa shi a wata kungiyar domin samar da makarantar islamiya, ƙaramin filin kuma tunda magana ce ta gina masallaci shima zai bincika duk yadda ake ciki zai neme ta, ga shi dai ƙarama ce a cikin su amma ta yi tunani irin na manya.

Shi da kan shi ya je group ɗin su ya faɗi ƙudirinta yayyyenta suna ta saka mata albarka da fatan Allah ya jikan Baffa da rahama Ammah da ta ji sai ta yi kuka Mami ma ta ce itama za ta gina bohol anan cikin garin Kaduna, kowa dai ya ce zai yi wani abu domin Sadakatul jariya ga Baffa Allah ya yi masa rahama.

Ummu Salma ta yi shawara da Baɗɗo da Mami kan mganar ƙudirinta na buɗe gidauniya amma ƙarƙashin tsarin girke girkenta da za ta dawo da shi dukkansu sun ba ta goyon baya, ta ce za ta sauya suna daga oum Hanan Delecious, zuwa SARAUNIYA DAURAMA'S KITCHEN.
Mami ta ce sunan ya yi sosai, ta ce a ƙarƙashin sunan sai ta buɗe Sarauniyar Daurama Foundation, domin tallafama mata da jari da kuma duba marasa ƙarfi da masu neman tallafi na rashin lafiya.

Bayan ta yi mgana da su ta sake magana da Mai martaba ya ce ga kafaɗarsa ga bayansa shi zai yi supporting ɗinta har ta kai ga nasara. Komai take buƙata kawai ta yi masa mgana, wato shi fa a rayuwa in ka samu miji mai girmama duka ra'ayinka ka gama yin dace, sannam mu mata muna ɗan taɓa kuskure, sai mace ta dinga yi abu gaban kanta ba neman shawaran wanda kike zaune domin shi, ki sani shi ne fa mijinki kuma shugabanki sannan yana gaba dake a halitta da tunani gabaɗaya.

Komai lalacewarsa namiji ne ba faɗuwa za ki yi in kika nuna masa yana da muhimmanci ba, ko da ba zai ba ki komai ba in ya yi miki addu'a da fatan alheri ko shawara ya baki ai gama miki komai, mu daina ganin cewa shawara da miji ba wani abu ba ne, girmamawa ce da ganin ƙima Ubangiji Allah ya sa mu dace Amin.

Yanzu matakin farko shi ne ta dawo da handels ɗinta na social media shekara ɗaya kenan har da wattani ba ta ɗaura komai ba, ba ta ma tsayawa dubawa tun daga rasuwar Baffa da rashin jaririnta sai kuma ta zo ta samu cikin Banafsha abubuwa suka ƙaru amma yanzu tunda ta samu natsuwa za ta dawo gadan gadan.

Da canza sunan handels ɗinta ta fara, ta koma Sarauniyar Daurama's Kichen, daman ta fi ɗora video ɗinta a youtube ne da Tiktok. Youtube ɗin ma ya yi kasa saboda ta daɗe ba ta ɗora komai tiktok ma ta kai followers dubu hamsin a shekaran ɗaya sama da mutane dubu goma ne suka yi followiing ɗinta saboda ana kallon girke girkenta ana sharing kuma.

Tuni ta dawo bakin aiki, daman ita ke girkinta a bangarenta ta naɗa ta yi posting ana ta mata welcome back domin mutane na gane bayananta suna kuma gwadawa su ji daɗin girkin da ta ɗora musu a shafinta.
Sunan da ta canza ma ya jawo hankalin mutane sannan ga sabon kitchen dalilin haka ta ƙara tara mata mabiya sosai, ana yi mata Dm ana tambayanta da gaske ita ɗin sarauniyar Daurama ce? ba ta amsawa, domin ba yanzu za ta bayyana wace ce ita ba.
An shiga sabuwar shekara da burika ita dai burin Ummu Salma duk abin da ta yi kuɗiri ya tabbata kafin shekaran ta ƙare.

An saka su Hanan wata makarantar kuɗi mai kyau a Daura sannan aka sanya su a islamiya yamma, rana ku biyar alhamis da Jumma'a suna gida weekend kuma an ɗauko musu wani malami yana koyar da su Haddar AlQur'ani a cikin Masarauta, Ummu Salma ta ba da shawara ta ce hakan zai taimaka musu, duk da itama tana koya musu musamman azkar, hadisi, kuma yaran suna da ƙokari balle ma makarantarsu ta can Lagos mai kyau ne sun samu matashiya mai kyau.
Received at 19:42
11 people reacted with ❤
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Bilkisu ma ta fara aiki a General Hospital Daura. a garin Daura. Ta nuna ma Lamiɗo tana son ta cigaba da aikinta shi kuma ya ba ta goyon baya duk da a al'adun sarautu na gargajiya matan sarakuna ba sa aikin gwammati, amma ba addini ba ne ya hana sannan ba doka ba ce, shi kuma Lamiɗo
mutum ne mai girmama ra'ayin kowa da ba ma duka matansa dukkan dama, Bilkisu likita ce ba za a tauyeta ba sannan yanzu ma sarautun sun koma na zamani ana samun matan sarakuna da ayyukan gwamnati kamar koyarwa, aikin asibiti da NGO wasu kuma suna yin kasuwancin su. Shi yasa ta da bukaci cigaba da aikinta ya yi supporting ɗin ta.

Yanzu direban masarauta ne ke tuka ta tare da Sabuwa in za ta je asibiti, sai su yi sati ba su haɗu da Ummu Salma ba kowa na bangaren shi yana harkan gaban shi, ita Ummu Saalma ta duƙufa kan abin da ta saka ma gaba, so take nan da tsakiyar shekara ta yi online class na mutane ɗari bayan an gama na sati biyar sai ta tallafa musu da kudaɗe, haka ta saka a diary ɗinta domin yanzu duk wasu abubuwan da take son cimmawa tana rubutawa.
Yanzu maganar ginin masallacin ne a gabanta babban filin ma tuni an bayar da shi a gina makarantar islamiya sadakatul jariya takardun filin ma ya tashi daga nata ya koma ƙarkashin kungiyar da za su gina makarantar.

Yanzu filin da za a gina masallacin ne aka nemo amintattu aka ɗora su a wajen aikin ta tura kudaɗe sama da miliyan goma da za a fara aikin da shi, kuma kuɗin ta ba su kare ba ga Mai martaba ya ce in ana buƙatar wani abu ta yi masa magana tana so ta yi komai da kanta ne sai ta kai ƙarshe in tana bukatar tallafi sai ta yi masa mgana. Cikin lokaci aka fara ginin wannan masallacin daman gini in dai da kuɗi ba a ɓata lokaci.

Duka duka wattani uku aka ɗauka kafin a kamallah gina masallacin nan. Ga masallacin mai kyau ne kamar a saudiya Mai martaba ya saka kuɗin shi shima sama da miliyan biyar, ga shi an yi bohol a masallacin bayan an gama aka damƙa ma limanin masallacin da Baffa ke salla shi ya je ya samu malaman anguwan da limaman masallaci suka zauna da shi ya yi musu bayani suka yi ta saka albarka.

An yi taron Buɗe masallacin bayan ƙaramar salla ne Ummu Salma da Mai martaba Sarkin Daura sun zo, amma ba su kwana ba a ranar suka koma, Mai martaba mai murabus yana can London wajen wattani biyu kenan yana hutawa sannan yana ganin likita, tare da Gimbiya Shahida suka tafi amma ta dawo Gimbiya Hadiza ta koma wajensa.

Fulani ce da su Gimbiya Amratu ke gida, itama Fulani wannan shekaran za ta koma Saudiya Ammah ma ana ta shirin tafiya.
Tare za su tafi da Fulani da Gimbiya Maimunatu.

Baɗɗo ta samu ciki har ya fito. Tana gida tare da Ammah, da yake kasuwancinta na online ne tana gida tana cigaba da kasuwancinta.
Da babbar salla ba su zo salla ba tunda Ammah bata nan sai da ta dawo suka taho gabaɗaya har da Mai martaba da yaran suka yi mata sannu da zuwa Banafsha, ta yi wayau har ta fara zama tunda yanzu tana wattani na biyar cikin na shidda ne da haihuwa, Mai martaba kwana ɗaya ya yi ya koma sune sai da suka yi sati Bilkisu kuma daga nan Kano ta wuce tare da su Sultan Hanan kuma an kaita gidan babanta.

Shamsiya ta faɗa ma Ummu Salma ta samu ciki wata biyu da kwanaki ta yi ɓarin shi, har tausayi take ba ma Ummu Salma, ga wahalan rayuwa tana tunanin in dai ta buɗe foundation ɗin ta, Shamsiya za ta shiga cikin waɗanda za ta fara tallafamawa, sannan ta roƙeta yan ajinsu na makaranta suna ta tambayan lambarta tana neman izinin ta tura musu? Ummu Salma kuma ta ce ta ba su ba komai ikon Allah kenan yanzu tunda ta zama matar Sarki kowa neman ta yake yi an mayar da ita group na makaranta girmamata suke yi ranki ya daɗe sama da ƙasa ba mai kiran sunanta ko kuma su ce Sarauniyar Daurama.

Ita dai sama sama, duk wanda ya kira ta za su gaisa amma tun daga kan Shamsiya ta daina aminci da yarda da ko wata ƙawa.
Received at 19:42
8 people reacted with ❤
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Tana da Baɗɗo ba ta neman kowa a halin yanzu, amma in abu ya faru na buƙatar taimako tana taimakawa iya ƙarfinta ko kwanaki wata class mate ɗinsu ta samu hatsari za a yi mata aiki a kugu ana neman dubu ɗari takwas, mijin ba shi da karfi ana neman taimako ta yi ma Mai martaba mgana ya ba ta kuɗi ta tura musu dubu 1M mazan su da matansu haka suke yi mata godiya. Sannan sun ce suna so su shirya haɗuwa na mates ɗin su, ta ce su shirya ba sai sun jira ta ba, ƙarshen shekara aka ce ta ce lokacin suna Abuja bikin Saleem amma daga can za ta zo Adamawa.
Saleem zai auri ƴar sarkin zazzau ne kuma a garin Abuja za a yi duka bikin angon ma a can za su zauna tunda anan yake aiki.

Sagir ne ma ya dawo garin amma ya koma ya ce sai ya haɗo Phd ɗinsa Yazeed kuma yana masters ne. Mai martaba mai murabus kuma ya samu lafiya da kwanciyar hankali ya dawo yana gida yana hutawa.
Ummu Salma su ta riƙe a matsayin iyayen ɗakinta duk sati tana hanyar zuwa, da abinci domin Mai martaba mai murabus har jiran girkinta yake yi Lamiɗo ya faɗa masa abin da take so kenan harkan girke girke Mai martaba ya ce za a buɗe mata har gidan abincin in dai tana so tana ta godiya. Burinta ya kusa cika ta kai in da take so ta shahara, ta samu ƙwarewa daga mabambamta makarantu na online sun fi biyar sannan ta zo ta yi online class na mutane ɗari sannan bayan an gama ta raba musu dubu hamsin hamsin ta ce su je su ja jari ko wacce ta je ta kafa abin da ta iya.

Wannan dalilin ya sa ta yi suna sosai kaf arewa a cikin masu girke girke za ka ji ana zencen Sarauniyar Dauramas Kitchen, cikin ƙanƙanin lokacin sunanta da komai na ta ya tafi viral tuni mutane sun fara yarda matar Sarkin Daura ce wasu har sun lalubo hotunanta ana yawo da shi, yanzu social medi ba tsaro in suka taso ka gaba sai Allah.

In da ta gode ma Allah ba ta samu ciki ba ga shi har Banafsha na shirin shekara har ta fara tafiya ba in da ba ta zuwa. Shi yasa sai komai ya zo mata da sauki Baɗɗo ce kamar P.A ɗinta Mami kuma mai ba ta shawarwari ita da Hamma Saddam kuma tana jin daɗin haka sosai.
Har sun fara maganar foundation da Hamma Abdulrahaman ya ce zai haɗa ta da wata Barrister Salamatu Doma, a nan Abuja take tana aiki da suprime court Abuja, itama suna da wata foundation da take jagoranta za ta taimaka mata sosai. Yanzu sun ajiye mganar in suka je Abuja bikin Saleem za ta je har gida ta samu Barrister Salamatu Doman su yi magana.
A karshen watan november Baɗɗo ta haifi ɗa Namiji ya ci sunan Baffa, suna kiran shi Junior.

Ummu Salma ta zo suna, Bilkisu lokacin ba ta nan ta je Canada hallatar wani Seminar na su na likitoci. Da za ta koma da Islam ta koma ta gama jarabawar fita babban sakandiri kafin sabuwar shekara za ta fara jami'ar a Kasu dake Kaduna in da Mami ke aiki.

Tana komawa Daura ta fara zazzabin dare sai amai ana duba ta sai ga ciki har ya yi wattani uku ma ba ta san da shi ba. Duk da tana jin canje-canje a jikinta.
Ta ji daɗi amma ba ta ji ba saboda cikin zai yi mata cikas da shagalin biki, sannan ga shi Mai martaba ya yi mata alƙawarin zuwa Saudiya, yanzu kuma ciki na ɓulla ya ce sai ta haihu yaro ya yi ƙwari, sai da ta yi kuka ta so ta je Saudiya ta yi ta ibadu tana roƙa ma Baffa gafara a harami.

Allah ya sa ma cikin bai ba ta wahala kamar na Banafsha ba. Shi ya sa har ta samu daman shiga ciki ana ta shirin biki da ita.
Gimbiya Shahida da ya'yanta suna girmamata shi yasa itama ba ta sanya a duk abin da ya shafe su. Islam sun haɗe da Amira da su Hafsat, da yaran Sakeena, Amiran ma wannan shekaran za ta yi candy Hajiya Zaliha suke da biki a zaria ƙanwar mijinta ne Saleem zai aura.

Tun a satin biki suka tafi Abuja, akwai gidan Mai martaba acan suka sauka ana ta shirin biki.
Ango kuma yana Daura sai sun ɗaura aure a zaria za a taho da Amarya Abuja a yi dinner. Saddam na cikin abokan ango shi da Hamma Abdulrahim sun saje da yaran manya nan ma tare da Adda Nauwara ake yin komai tunda suna gari.
Received at 19:42Reactions: ❤ 7, 👎 1
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Kowa ya ga Ummu Salma ko ba ta faɗa ba sai a ce tana da ciki, ta yi kiba kamar ba ita ba. Gimbiya Shahida na Daura nan za ta yi taron ta sai ranar Dinner za ta taho.
Ammah da Ummin ikki Daura suka fara sauka.
Daga can ne ranar ɗaurin aure suka taho Abuja a jirgi suna isowa ba daɗewa ango da tawagarsa tare da amarya da danginta suka sauka.

An sauketa a ƙayattacen gidanta mai kama da aljannar duniya A daran aka yi wata lafiyayyiyar Dinner a ɗaya daga cikin manyan hall na garin Abuja, an barar da dukiya kamar ba san zafinta ba an ƙure adaka ankon leshi ne amma kowa ya saka kalan na shi Ummu Salma ta yi makeup, duk da ba ta ji daɗi ba Baɗɗo ba ta zo ba saboda jego, Hamma Abdulrahim ƙiri kiri ya ce ba za ta zo ba ga shi ta saka rai.

Bilkisu ma ta zo, yaran ma duk tare da su suka zo suma sun kure adaka, Hanan da Beena sun girma in ka gansu kamar wasu yan biyu, yanzu Mahma suke kiran Ummu Salma tunda suka ji Hanan na faɗa Bilkisu kuma Momi, Lamiɗo kuma Papa, Sultan an girma shekaransa sha biyu yanzu amma yana da girman jiki da tsawo kamar ɗan shekara sha biyar.
Mawaƙa sun zo sun baje kolinsu sun kwashi kuɗi.
Anan ne Ummu Salma ta haɗu da Hajiya Hauwa Inuwa Aminu(Anty Hairi) daga haɗuwarsu suka gaisawa shikenan suka yi ta hira da Ummu Salma, Anty Hairi sune tawagan amarya daga masarautar Zazzau, sai ga shi har suna sharing contanct. Anty Hairi akwai kirki sosai mace ce mai karamci Allah ya kara wadata ya kuma raya mata zuru'a Amin.

Ummu Salma ta tura ma Lamiɗo hoton ta ita da yaran da ta ɗauke su, sai dare ya duba ya tura mata emojin harara. Cewa ya yi sun tafi sun bar shi, ta ce ya zo shima ya ce in ya tafi wa zai bar ma Daura, ta yi ta masa dariya.
Amma ya ce ta yi kyau sosai ya yi kewarta. Ummu Salma ma har videon Bilkisu ta ɗauka a wajen ta tura masa, ita ba ta da wannan Ummu Salma ce komai da ruwan ka, kuma a hakan Lamiɗo ke son kayansa ba Bilkisu kaɗai ba har video ta dinga masa tana tura masa wai kar ya ji kewa shi bai zo ba, gwara ya ji kamar yana wajen shi dai ta saka shi mirmishi kamar wani yaro ƙarami.
Shi dai na shi karɓo aure ne kuma sun je Zaria sun karɓo aure sun dawo Daura.

A garin Abuja suka ci bikinsu suka suɗe, daman ita Ummu Salma Jimeta za su wuce tare da su Ammah, amma kafin tafiyarsu sai da ta je ta gana da Barrister Salamatu Doma.
Hamma Abdulrrahaman ya tura mata lambarta ta kira ta, adireshinta ta tura mata direba ya kaita sai da suka haɗu a a fili sannan ta ga kirkinta da Hamma Abdulrrahaman ke faɗa, sum yi batutuwa sosai ta ba ta shawarwarin yadda za ta tafiyar da ƙudirinta, kuma ta ji daɗin magana da ita sun rabu da cewa za su dinga tattaunawa ta waya in sha Allahu.

Sun bar Abuja 28 ga wata ne, tunda bikin 25 ne aka yi, ta je Jimeta saboda talatin ga wata za su yi class reunion ɗin su kuma yadda suke kiran ta ana buƙatarta a wajen da ta faɗa ma Mai martaba ya ce ta je ba matsala dalilin wucewarta Adamawa kenan amma Bilkisu Daura ta koma, ita kuma Ummu Salma ta taho da yaran Adamawa tare da Harira yar amanarta da duk in da za ta je tana tare da ita Islam na Abuja tare da su Hafsat Daura za su koma ta ce ba za ta je Jimeta ba.

Baɗɗo ta sha takaicin rashin zuwa bikin nan haushin ma ya ragu tunda shi Hamma Abdulrahim bai je Abuja ba daga Zaria gida ya dawo saboda Baɗɗo tunda Ammah bata nan. Ranar reunion ɗin su shigar alfarma Umma Salma ta yi na super wax sai ta naɗa lafaya jakarta da takalminta ma abin kallo ne kama daga kyawawan ya'yanta Hanan da Banafsha ga su Sultan, Harira ce ke rike jaka da Banafsha ga matashin cikinta ya fara fitowa da ya ƙara mata kyau da ƙwarjini.

A toyota ɗin Lamiɗo ta tuka su, zuwa makarantar a can aka shirya taron a babban hall ɗin makarantarsu ta Ahmadu ribaɗu Collage
Kowa a wajen nan Ummu Salma kawai yake kallo da ya'yanta da motar da ta tuƙo, Shamsiya ko duk ta bushe gaisawa kawai suka yi da Ummu Salma, ta ɗauki Hanan tana yi ma Banafsha wasa, wasu sun samu labarin matsalan da aka samu tsakanin Ummu Salma da Shamsiya tunda abin duniya ba ya ɓoyuwa, ana ta kuskus ganin Shamsiyar gefe ko Harira Hadimar Ummu Salma ta fita kyan gani.
Received at 19:42Reactions: ❤ 11, 👍 1, 👏 1
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ummu Salma ta haɗu da Madeena Jaafar lokacin lokacin suna makaranta sun yi mutumci sosai ta yi aure da yaranta uku tana koyarwa.

An ci an sha an yi hotuna tunda sun haɗa kuɗi Ummu Salma 2M ta ba su, su Hanan sun sha ɗauka kamar yaran turawa. An yi jawabai sosai tare da cewa za a kafa asusu domin tallafawa in wani abu ya taso na biki ko suna ko ciwo a cikin su, an naɗa shugabanin rikon kwarya sai ga shi sun ba ma Ummu Salma matamakiyar shugaba, ta ce ba za ta karɓa ba suka ce sai dai in ba ta so ne shi yasa ta yi shuru. Yanzu duniya in kana da shi kai Sarki ne ta karɓi mic ta yi jawabai anan ta yi maganar za ta buɗe foundation domin tallafawa ma mata da ƙananun yara ana ta mata fatan alheri sun gayyaci wasu malamansu wasu ma duk sun rasu, a jin na su ma an rasa wasu, an fara saka kuɗi a asusun nan take ta saka kuɗaɗe masu kauri hall ya ɗau ihu ana faɗin Allah ya taimaki Sarauniyar Daurama.

Shamsiya na gefe tana hawaye tana mai nadamar biye ma zuciya da sheɗan ba domin soyayyar Habib da ta zama

Please Login or Register in order to submit comment