Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba.

"Maganar girmamawa kuma."

"Hamma take kira na."

"Hamma in fullanci means Yaya."

Ya gama faɗa har gefe da gefen bakin shi na motsi.

"I love the name."

"Ranka ya daɗe da kike kira na kin sa kanki ne. Bilkisu ni mijinki ne, ke matata ce ba baiwata ba. Girmamanin da za ki yi na ibadar aure ne amma wannan girmamawan na tushe kuma na dabam yake."
Received at 08:42Reactions: ❤ 10, 😁 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
"A wajen mutane nake Yarima amma a wajen iyalaina da iyayena I'm still Muhammad Lamiɗo."

"So ni wannan bai dame ni ba. Ke ma you can start call me whatever you want. Ba ki da matsala."

Sai da ta yi nadamar yi masa maganar yadda ya dinga jera mata maganganu.
Ta ɗan daure dai tana yi masa yar shagwaɓa ta ce ai ita ba ya zuwa bangarenta sosai.

"Zan zo."

"In kina so."

"Ina so Papa."

"Nima ina so na sake samun ciki."

Ta faɗa masa abin da ke zuciyarta.
Ta ji tana son itama ta sake samun ciki duk da ita ta tsayar da haihuwanta da kanta

"As you wish. Zan yi farinciki da haka."

Ta gama tsayar da shawaran za ta je a cire mata abin da aka sanya mata. Itama za ta samu cikin ba za ta zauna tana ji tana gani ana ririta wata macen saboda ciki ba.

Duk a tunaninta ya za a yi wata macen da ba ta isa ba ta zo ta fita. Ta gaji da kiran Ya Hadiza tana ba ta hakuri. Kowa gani yake yi kishi ke damunta ba su hango abin da ke faruwa ba. Ta ya ya Lamiɗo zai ba ma wata macen muhimmanci sama da ita, a ganinta babban ci baya ne a gareta.
Shi ya sa ta kasa bari zuciyanta ya zauna lafiya

Kwana biyar Lamiɗo ya yi ya koma da zai tafi ya ce ma Bilkisu ta kula da Ummu Salma. Ta amsa masa ne kawai amma a zuciyanta ta ce ba za ta yi ba. Yarinyar da ba ta san darajan mutane ba, itama Ummu Salman da ya ce mata Bilkisu za ta dinga kula da ita a gida ba ta yi masa gaddama ba amma a zuciyanta ta ce bata bujata za ta iya kula da kanta.

Yana kuma tafiya kowa ya kama harkan gaban shi.
Tafiyarsa da kwana shidda aka fara azumin watan ramadana.
Ummu Salma ta ce ba za ta sha azumi ba duk da Lamiɗo ya ce ba ta da lafiya ta huta haka ma Mami ta ce mata ita kuma tunda ta gwada ta ga za ta yi ta ce ba za ta yarda ta sha azumi ko ɗaya ba.

Ga shi dai azumi ne amma ba sa sahur tare ballatana buɗe baki tare. Ummu Salma buɗe bakinta daman kayan marmari ne gwara yanzu ma tana ɗan cin wani abincin bayan tuwo sannan tana shan tea.
Bilkisu kuma ko damuwa da wata Umma Salma ba ta yi, yaran ma tunda ta ga sun koma shashenta ta yi ma Anitha magana tare da yaranta take buɗe baki Hanan kuma da rigima ta saba da su Sultan sai ta je duk da Bilkisu ba ta so. Shi kuma yaro bai son ana so ko ba a so ba.

Sai da aka yi azumi ashirin sannan Lamiɗo ya dawo. Ummu Salma ko ɗaya ba ta sha azumi ba. A ɓoye take yi ba ta bari Lamiɗo ya sani ba in suka yi waya sai ta ce ba ta ɗauka ba sai da ya dawo ne ya fahimci tana azumi bai yi mata faɗa ba ya ce tunda ta tabbatar da tana lafiya shike nan. Yanzu an samu sauƙi tana shakan ƙamshin abinci ta zauna lafiya amma har gobe ba ta daina shinshinar ƙasa ba.

Suna yin sahur tare a dinning haka ma Buɗe baki tare da yaran gabaɗaya.
Tunda Lamiɗo na nan dole in ya kira su, su fito su haɗu gabaɗaya.

Kayan salla daman yana dawowa suka fita shopping, suka yi siyayya ɗinki kuma Bilkisu ta kira telan dake yi mata ɗinki a wani plaza ne ya zo gida ya karɓa harda na Ummu Salma tunda Lamiɗo ya na nan kuma ya saka baki. Ma'aikata kuma kuɗi ya ba su kowanne ya je ya siya abin da yake so.

Harira ta ba ma Ummu Salma nata ta adana mata Daman kuma ta kira Baɗɗo ta je can wajen Ammah ta karɓi key ɗin gida ta je ta buɗe akwatinta ta ɗauko atamfa guda uku da leshi ta kai mata ɗinki na ta biyu na Harira biyu. Kayan salla su Ammah kuma kamar yadda aka saba Lamiɗo ya tura ma Hamma Abdullahi shi kuma Adda Suwaiba da ta saba siyowa ta siyo aka raba ma kowa. Wannan karon har da mutanen Mubi, Mami da iyalanta gabaɗaya.
Ummin ikki da yaranta kamar yadda aka saba kowani shekara.

Amma ta fita takaba ranar azumi ashirin da biyu. Kowa ya kirata a waya ranar sai ta zama kamar ranar ne Baffa ya rasu. Ummu Salma daman tun a ranar tunda ta tashi sukuku take, ta sha kuka idanuwanta sun kumbura Lamiɗo ne ya dinga lallashinta.
Mutuwar Baffa gibi ne ba ta tunanin za ta manta da wannan rashin. Ba ta taɓa tunanin za ta yi dariya bayan rasuwar Baffa ba, sai ga shi tana yi amma kuma rashin shi ba zai goge daga zuciyarta ba.
Received at 08:42Reactions: ❤ 12, 😢 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Wannan karon daga Lagos Daura suka sauka, tunda ba su taho da wuri ba ranar da aka ɗau azumi na ashirin da bakwai. Sun yi salla a Masarautar Daura kamar yadda suka saba lokacin cikin Umma Salma yana cikin wattani na biyar har ya fito.

Ta rage laulayi amma har yanzu tana yin amai in ta ci abin da cikinta bai karba ba. Mai martaba ya samu sauƙi sosai tunda yana zuwa ganin likita lokaci bayan lokaci Fulani ne ma ke fama da kafafu. Kowa ya ga Ummu Salma da ciki sai ya ce Allah ya kawo rabo da wuri haka Hajiya Kilishi da Hajiya Zaliha suka yi ta faɗa da addu'an Allah ya sa a sauke lafiya.

Mai Martaba ma ana gobe za su tafi Adamawa a daran sun daɗe suna hira da shi da ta je gaishe shi. Ya na bata labarin halin kirki irin na mahaifinta tana jin daɗi, ta tuna lokacin da ta rasa jaririnta ya kira wayarta ya daɗe yana yi mata nasiha da jan hankali akan hakuri da kaddara. A lokacin kuma ta ji daɗin maganganunsa sosai.

Yana da hikima da hangen nesa. Adali ne na gaske ta tabbatar da haka ta ga kuma in da Lamiɗo ya ɗauko karamci da yakana.
Bayan salla da kwana uku suka baro Daura zuwa Adamawa.

Daman da azumi Shamsiya ta ddame ta da kira sai da ta haɗa ta da Hanan har Habib ɗin ma an ba shi ya yi magana da Hanan ɗin. Shamsiyar ta tambaye ta ko za su zo da salla ta ce a Daura za su yi salla. Ko sun zo Adamawa ba za su daɗe ba zaman da za a yi na rabon gadon Baffa ne ma zai tsayar da su
Lokacin da suka isa sun iske Baffa Umaru da Baffa Salisu duk sun iso Hamma Jibo ma da Hamma Mustpha suna nan.

Hamma Kabiru sai washegari da safe zai taho.
Sai aka ce a bari zuwa da safe in kowa ya iso sai a yi zaman. Umma A'i daman na nan Umma Balki ce suka taho tare da su Baffa Umaru.
Mami kuma sai a gobe za ta biyo jirgin safe ta taho.

Su Umma Salma na zuwa Ammah ta ce ta kira Shamsiya su zo su tafi da Hanan. Anan ne ma Ammah ke faɗa mata da salla Shamsiyar da Habib ɗin sun zo gaishe ta har waina ma Shamsiyar ta kawo mata.
Ta ce tana ta kiran wayar Ummu Salman ba ta ɗauka ba.

"Auta da ace Ubangiji ba ya mana rahama da ba mu kawo yanzu ba. Ya kamata ki manta baya ki saki daga ƙullatan Shamsiya da kika yi a zuciyarki. Shi kuma Habib kun rabu Ubangiji kuma ya yi miki canji na alheri. Amma kuma akwai alaƙa tunda ga Hanan ya kama ta ki manta da duk abin da ya faru. Duniyar ma nawa take? in mune yau gobe ba mu ba ne! Yau ina Baffa? Yana can ƙasa ta rufe masa idanuwana"

Nasihan Ammah suka sanyaya ma Ummu Salma jiki. duk abin da ta faɗa gaskiya ne. Da Ubangiji ba ya mana afuwa da tuni an kife duniyar ta yafe amma alaƙa ce ba ta son ta ɗaure. Maganar Ammah na cewa an rabu amma ba a rabu ba gaskiya ne tunda akwai Hanan a tsakani. Ko tana so ko ba ta so alaƙa ta haɗu ba ta da yadda za ta yi.

Ammah ta yi ma Lamiɗo maganar cewa Hanan za ta je dangin babanta ta kwana biyu kafin su tafi. Ya ce ba komai, shima ta yi masa faɗan ba ya faɗa ma Umma Salma gaskiya. Ya dinga yi mata faɗa ta dinga haƙuri da rayuwa ya ce zai dinga yi mata in sha Allahu.

Ummu Salma da kira lambar Shamsiya ta ce ta zo su tafi da Hanan ta kwana biyu ba daɗewa za su za su yi ba za su koma Lagos.
Shamsiya ta ji kamar a mafarki da Ummu Salma ta kira ta daman ta ce ba za ta gaji ba. Wata rana Ummu Salma za ta sauko ta amince da nadamarta. Habib baya nan yana wajen Habiba ne ta kira shi a waya tana murna ta faɗa masa nan take ya taho ta shirya a daran suka zo suka tafi da Hanan.

Habib ɗin bai shigo ba a waje ya tsaya Shamsiyar ta shigo ta shiga har cikin ɗakin Umma Salma suka gaisa.
Ta ga Ummu Salma da ciki ta kalleta sai da hawaye suka kawo mata.

"Allah ya raba ku lafiya Umma Salma."

Ta amsa mata da Amin
Saboda Nasihan Ammah ya sa ta ɗan saurari Shamsiyar.

"Ke har yanzu shuru dai?

Ummu Salma ta tambaya

"Shuru ko ma na samu cikin ba zama zai yi ba. Habiba kuma ta ce ba za ta iya haihu da Habib ba."

Sai hawaye sharr, Ummu Salma ta kalleta sai kuma ta ba ta tausayi.

"Allah zai kawo mafita in sha Allahu."

Ta amsa da Amin tana mirmishi.

"Amin na gode Ummu Salma. Na gode."
Received at 08:42Reactions: ❤ 14, 🔥 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Tana faɗa tana sharan ƙwalla suna cikin haka ne sai ga Baɗɗo ta shigo. Zuwanta kenan ta kawo ma Ummu Salma ɗinkunan ta, tunda sun yi waya ta ce suna gidan Ammah. Bilkisu tana gida tare da su Sabuwa suna sauka ta ce gida za ta je ta huta. Ummu Salma ne kawai sai Lamiɗo da su Sultan a gidan.

Shamsiya ta kalli Baɗɗo wacce ta yi kamar ba ta ganta ba. Ta haɗu da Habib a waje ta yi kamar ba ta gan shi ba sai da ya gaisheta ta amsa adaƙune. Nan ma Shamsiya ce ta gaishe ta.
Ta amsa sau ɗaya ta haɗe rai ita fa ba ta ga abin da zai saka Ummu Salma ta cigaba da mu'amala da Shamsiya ba.

Shamsiyar ma ganin ba fuska sai ta yi musu sallama. Tuni Harira ta haɗa ma Hanan yar jaka na tafiya Shamsiya ta ɗauke ta Hanan dai wannan karon ba ta yi rigima ba Beena ce dai ta yi rigiman ganin za a tafi da Hanan a barta sai da Ammah ta rumgumeta tana ta lallashinta.

Bayan fitan Shamsiya Baɗɗo ta dinga faɗa wai me ya sa take kula Shamsiya.

"Nadamar dole ce shegu sun ga uwar bari "

"Nima ba mu'amala nake son yi da ita ba. Ammah ce ma tayi mini faɗa shi ya sa kika ga na tsaya na saurare ta. Amma ni ko wayata ta kira bana ɗagawa."

"Wallahi na tsane su daga ita har Habib maciya Amana kawai."

"Na yafe musu kema ki yafe. Ni yanzu Ubangiji ya gama yi mini komai Baɗɗo."

Baɗɗo dai ba ta yi magana ba. Alaman dai ko ta yafen to ba ta faɗa ba. Saboda haushi ma ba ta daɗe ba Hamma Saddam zai fita ta ce ya sauketa a gida. Ta kawo mata ɗinkunan da ta ba da, sannan ta haɗo mata da wasu wanduba plazo guda huɗu da Baɗɗo ke siyarwa da ta ce tana so.

Nan gida Ummu Salma ta kwana Lamiɗo ne ya koma gida tare da Sultan, Beena ma wajen Ammah ta kwana.
Washegari tun goma na safe Hamma Kabiru ya iso, Mami kuma sai sha ɗaya da wani abu ta iso daman su kaɗai ake jira. Har Liman an kira tunda shi ne zai yi rabon gadon.

A falon Ammah aka tattaru kaf yaran Baffa mazan da cikon su Ummu Salma.
Sai Baffa Umaru da Baffa Salihu wakilan Baffa sai wakilan Ammah kuma Umma A'i da Umma Balki.

An buɗe taro da addu'a tare da nema ma Baffa gafara a wajen Allah sannan aka fara gudanar da abin da ya tara su. An fito takardun filayen da Baffa ya bari da na gida. Sannan daman lokacin da ya rasu Hamma Abdullahi ya ce ba a bin shi ba shi sai ma shi ne ke bin wasu, to duk sun dawo da kuɗin tunda shi ne suke kasuwanci da Baffa ya samu tattara kudaɗen da ya mutu ya rabi kudaɗe dai tsaba miliyan takwas ne sai gidan nan da suke ciki sai filaye guda huɗu sai mota sai kuma gadon shi dake can mubi na gida da gona.

An raba gadon cikin tsarin kamar yadda Ubangiji ya raba gado a cikin suratul Nisa'i. A shari'a namiji ke da kaso biyu mace kuma na da kaso rabi daga abin da namiji ya samu.

Matar da mamaci ya mutu ya bari tana da kashi ɗaya a cikin takwas. Tunda yana da yara maza, yan'uwansa maza ba su shigo gadon Baffa ba. Daga ya'yansa sai matarshi da a ce mahaifiyar Baffa na raye za ta shigo ciki a matsayin ɗaya bisa shidda amma tunda ta riga Baffa rasuwa babu lissafin ta a rabon gado.

Gida kuma tare aka raba kowa da kowa har da Ummu Salma kuɗi ma aka yi kasafi aka raba komai kamar yadda addini ya tsara.
Ana rabon Ummu Salma na sharan ƙwalla, shike nan Baffa ya rasu da gaske ne ba mafarki ba. Kowa ka gani jikinsa duk a sanyaye.
Shike nan fa an yi an gama. Sai dai fatan Ubangiji ya sa mu gama da duniya lafiya.

Sai gidan ya dawo kamar yau aka yi mutuwa. Ammah ta yi kuka irin wanda ko a lokacin rasuwar ba ta yi ba. Hamma Lamiɗo ne ke ta lallashinta Mami ma kuka har da sauti Liman ya zauna yana ta nasiha tare da ba ma su Hamma Jibo shawaran su haɗa kansu ko bayan ran Baffa su kasance ƴaƴa nagari a gare shi. Hamma Abdullahi sai share hawaye yake yi shi da su Hamma Saddam.

Mutuwar Baffa babban gibi ce da har abada ba za su taɓa mantawa da shi ba. Bayan an gama koke koken kowa ya share hawayensa.
Bayan Liman ya tafi su Hamma Jibo sun je sun raka shi sun dawo.

Sai aka sake wani zaman saboda tunanin wanda za a samu da zai zauna da Ammah saboda ɗebe kewa. Ammah kuma na faɗin ita su ƙyaleta za ta iya zama ita kaɗai. Umma Balki ta ce ba zai yuyu ba ko yaya ne a samu wacce za ta taya ta zama.
Received at 08:42Reactions: ❤ 11, 👎 2
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ita Ammah na faɗin ba matsala ga Ummin ikki a kusa da ita ga matan su Hamma Abdullahi suna zuwa akai akai ba ta da matsala. Umma Balki ta ce Umma A'i ya kamata ta ɗan zauna na wani lokaci saboda ita ce ba ta da kowa a gabanta. Ta amince za ta kara ko da wata ɗaya ne kafin ta koma.

Hamma Jibo ya ce shawara kawai cikin Saddam ko Abdulrahim wani ya zo ya yi aure.
A gyara gida ya saka matar shi a kusa da Ammah. Kowa kuma ya aminta da shawaransa.

"Ni fa ba yanzu zan yi aure ba, ban kama aiki mai girma ba sannan ina karatu."

Hamma Saddam ya yi saurin faɗa.

"Kuma ni ai ƙarami ne Abdurahim ne ya dace ya yi aure, kuma shi ai ya gama karatu har ya kama aiki."

"Kuma yana gaba da ni."

Ya faɗa har yana marairaicwa.
Umma Balki ta ce ai ya isa auren shima

"Umma Balki ban isa aure ba fa."

Tana cewa ya isa yana cewa bai isa ba diramansu ta ba ma kowa dariya.

"Ai na ce ka turo mini CV ɗinka zan tura ma Maimartaba za ka fara aiki in sha Allahu "

Lamiɗo ya faɗa yana kallon Saddam nan da nan ya washe baki ya ce ya sha'afa ne amma zai tura maasa daman ko aikin Abdulrahim daga Masarautar Daura aka samar masa.

Abdulrahim da aka tuntuɓe shi ko yana da budurwa karaf Ummu Salma ta ce yana da shi.

"A Abuja take anguwar su Hamma Jibo "

"Tabbas haka ne, suna ma raba dare suna waya a kwanaki can amma yanzu na ga kamar ba sa waya."

Hamma Saddam ya karɓe maganar.
Abdulrahim na ta hararan shi.

"To kai Abdulrahim ya ake ciki ne?

Hamma Mustpha ya tambaye shi yana dariya.

"Ko an ka sa ka ne?

Hamma Abdulrahaman ya faɗa yana dariya.

"Kamar ka sani, ba ni da kuɗi ta bar ni ta auri wani mai kuɗi bayan rasuwar Baffa ta yi aure."

"Subhanallah."

"Abu bai yi daɗi ba."

"Sannu Allah ya mayar kaffara ne"

Har da Hamma Kabiru a masu yi masa jaje.
Mami na yi masa tsiyan ko bai iya soyayya ba ne ya ce ya iya mana ana ta dariya.
Ammah na mirmishi kafin ta ce" Ita ce ta tafka asara ka ji, yanzu dai ka yi haƙuri ka zo ina da matar da zan ba ka kuma na san za ka ji daɗin ta."

Kowa ya zura mata ido yana jiran ya ji sunan da za ta kira. Umma Salma ta yi jagale daman tunda ta ji Abdurahim ya ce budurwansa ta yi aure take wani tunani.
Sai kuma ga maganar Ammah.

"Wace ce?

Abdulrahim ya tambaya yana addu'an Allah ya sa ba a ƙauye ba ne.

"Aisha ce."

"Aisha?

Kusan duk falon suka tambaya a tare.

"Aisha yar wajen Aminiya."

"Baɗɗo tawa?

Ummu Salma ta faɗa tana zaro idanuwa har tana dafa kafafun Hamma Lamiɗo domin tana kusa da wajen kafafunsa ne a zaune

"Ita, ni da mahaifiyarta aminai ne, ka je ka neme ta in kun daidaita ina maraba in kuma ba ku daidaita ba, ba tilastawa."

"Gaskiya tana da hankali Aisha."

Saddam ya faɗa yana dariya. Abdulrahim ya ture shi da kafar shi ya koma gefe yana dariya.
Hamma Abdullahi ya ce shi ya ɗauka ma soyayya suke yi da Saddam

"A'a ni wallahi ba soyayya muke yi ba. Ni fa bana son farar mace."

Ya faɗa da iya gaskiyarsa

"Ka yi mata yaro da yawa ma."

Ummu Salma ta shigar ma ƙawarta tana hararan shi.

"Ke ni ne yaron?

"Yaro ne mana ai gwara Hamma Abbdulrahim muma kai ba ajin mu ba ne "

Ya taso yana jijiyar wuya ana ta dariya.

"Ammah kamar kin shiga zuciyata. Ina ta so Baɗɗo ta samu miji cikin yayyena ni da har Hamma Abdulrrahaman na yi ma sha'awarta ma"

Da ya ballo mata wata harara sai da ta sunne kanta kafafun mijinta tana dariya.
Mami ta ce ai ta samu mijinta Abulrahim ƙin kowa ƙin wanda ya rasa shi dai ya yi shuru ya kasa magana kowa na tofa albarkashin bakin shi. Su Hamma Jibo duk sun ce zaɓin Ammah ya yi har da su Baffa Umaru ma.

Umma Balki ta ce da tana da yar auta mace da ta ba ma Saddam yana tura baki ya ce ba ya so

"Kai ka sani irin su Saddam ne, in ka ga matansu sai ka juya baya ka ɗauka yan aikin su ne saboda shigen zaɓe zaɓe."

Aka saka dariya gabaɗaya shi kuma yana kumfar bakin cewa za a ga matar da zai aura kaf surukan Ammah ba kamarta.

"Ba kamarta kam."

Hamma Abdullahi ya faɗa yana dariya Saddam ya kasa magana.

"Hamma wallahi ka amsa za ka ji daɗin Aisha sosai tana da kunya ga hankali ga natsuwa."

"Uhm kina yi ma ƙawarki yaki ne?
Received at 08:42Reactions: ❤ 7, 😁 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Hamma Abdullahi ya faɗa Ummu Salma ta fara dariya tana faɗin ba yaƙi ne ba ne sai gaskiya Hamma Lamiɗo ta kalla tana faɗin bai ce komai ba.

"Me zan ce?

"Ka faɗa ma Hamma Abdulrahim sa'ar da ya yi na samun Aisha a matsayin matarsa."

Ya yi shuru bai yi magana ba yana kallonta.
Sai ta marairaice fuska kamar za ta yi masa kuka.

"Hamma ka yi magana mana."

Har tana rumgume kafafunsa ta manta ma a inda suke ta ɗauka suna gidansu ne shi kuma da sauri kamar jani talau ya ce to sannan ya juya yana kallon Abdulrahim da duk aka saki baki ana kallon su.

"Abdulrahin ka ji ko? Aisha is a good girl ka yi abin da Ammah ta ce kawai.'

"Ko abin da Ummu Salma ta ce ba."

In ji Hamma Kabiru yana kallon shi
Aka kwashe da dariya a falon har Ammah sai da ta murmusa sai a lokacin da Ummu Salma ta san abinds ta yi da sauri ta saki kafafun Hamma Lamiɗo ta koma tana sunne kai a jikin Mami.

"Ɗan Ammah dai ya shiga hannu "

Mami ta faɗa tana dariya.

"Ai ya zama jani talau kuma laifin Fatima ne."

Umma Balki ta faɗa tana dariya. Haka ma Hamma Jibo ya ce nan duk ana magana bai saka baki ba amma Auta na marairaicewa ya bi umarninta yana jin su kawai mirmishi yake yi bai yi magana ba.

"Amini ai ya canza sosai ni yanzu ma ina tsoron yin hira da shi kar ya kwashe ya faɗa ma yarinyar nan ta dinga mini kallon biri ni kuma ina yi mata na ayaba."

"Wallahi ka kiyaye "

In ji Hamma Abdulrrahaman
Falon sai dariya ake yi shi kuma gogan bai yi magana ba illa Hamma Kabiru da ya kalla ya ce.

"Bana faɗa mata komai fa."

"Ban yarda da kai ba."

"Wallahi Hamma ba ya faɗa mini hiran ku, hiran mu kawai muke yi ko Hamma? "

Ummu Salma tana kallon Hamma Lamiɗo har tana yi masa fari da gaske ne ba ta sanin komai kai in dai wajen zurfin ciki ne da riƙe magana ba ta ga kamar Hamma Lamiɗo ba.

"Tell him."

Lamiɗo ya faɗa yana kallon Hamma Kabiru.

"Kai dai ka kiyaye kawai tsakanin miji da mata.."

Su Hamma Abdullahi suka ƙarisa da sai Allah ana ta dariya.

"Auta ta nuna mana capacity ɗin ta yau."

Hamma Saddam ya faɗa yana kallonta sannan ya dunkule hannu yana yi mata jinjina

"Allah ya taimake ki ranki ya daɗe. Ai ke ce ma Yariman gabaɗaya."

Gabaɗaya aka kwashe da dariya. Ammah na ta duƙar dakai tana share ƙwalla ta tuna da Baffa na raye da yanzu yana cikin nan ana hira da shi ana raha.
Ummu Salma ma haka take tunani a zuciyarta.

"Allah ya jiƙan ka Baffa "

Sai da ta ji duk sun amsa da Amin sannan ta gane a sarari ta yi maganar. hawaye suka kece mata a saman kumatunta sai kawai ta kife kanta a kafafun mijinta ta fashe da kuka, shi kuma sai ya dora tafin hannun shi a saman kanta yana ta ɗan tapping alamun lallashi.

"Ya isa Okay."

"Kin san condition ɗin ki so please ki daina kuka nan ya isa."

Ta ɗago fuskarta shi kuma ya rankwafo yana share mata hawaye

"Ya isa kin ji ko? Ba ga ni ba! Ba za ki taɓa kukan wani abu ba in dai ina raye."

"I promise to love you, support you care for you. I promise to give you everthing matuƙar za ki yi farinciki."

"Hammaaaa...'

Ta faɗa tana gunjin kuka saboda kewan Baffa da kuma kalamamsa da suka tsuma mata zuciya.

"Na ce ya isa."

Yake faɗa yana goge mata hawaye ganin kamar sun manta da kowa ne ya sa Hamma Kabiru ya yi gyaran murya.

"What?

Hamma Lamiɗo ya juya yana tambayansa.
Sai yakasa magana lalle Lamiɗo ya canza shi ne zai iya kama mace a gaban mutane bai damu ba.

"A'a bakomai ci gaba."

Sai kuma ya ga ya koma ya ci gaba da lallashin Ummu Salma amma hannunta kawai ya riƙe sai dai kanta na saman kafafunsa.
Allah ya sa Baffa Umaru da Babba Salisu sun fita waje da an yi abin kunya.
Ammah ta dukar da kai tana yi ma Allah godiya. Tsam ta ta shi ta bar falon Umma Balki da Umma A'i suka bi bayanta Mami ta juyar da kai tana hamdala burinta ya cika Itama falon ta bari tana mai tsananin farinciki.

Sauran kuma sai

Please Login or Register in order to submit comment