Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsohon sarki ya sanar ma media team ɗin shi ya ba su izinin fitar da murabus ɗin ga duniya.

Matan Mai martaba mai murabus ji suka yi kamar a mafarki. Kuma ba wacce ta ji daɗi, ba wacce za ta so tana matsayin matar Sarki ta tashi daga wannan muƙamin na ta. Ko da suke ganin Mai martaba ya fi son babban ɗan shi ya gaje shi ba su taɓa tunanin da ranshi haka zai faru ba sai ga shi ya faru kuma abin ya tabbata.

Gimbiya Shahida da ake ganin za ta nuna rashin jin daɗin ta ma ba ta nuna ba, tunda an fi ganin cancantar Saleem a kan karagar Mai martaba, ba ta nuna damuwa ko a fuska ba, koma akwai ba ta bayyana ba shi kan shi Saleem ɗin bai nuna bore ba, shi kan shi ya faɗa Lamiɗo ya fi shi cancanta.
Gimbiya Hadiza ce ita da take da yara mata amma ba ta ji daɗi ba, tana matsayin Gimbiya matar Sarki darajanta zai yi ƙasa amma ta yi murna saboda zamowar Bilkisu cikakkiyar Gimbiya a Masarautar Daura.

A bangaren Gimbiya Maimunatu ta fi jin zafi ganin ga yaranta Yazeed da Sagir, da arziƙi a garin wasu ai gwara a garin ku a garin ma na ku ma a gidan ku a gidan na ku ma ya kasance kai ne ke da alhakin komai. Maganganu dai na ta tashi kowa na faɗin albarkacin bakin shi amma babu abin da zai dawo baya bakin alƙalami ya riga da ya bushe. Ƴa'ƴan Mai martaba ƙannen Lamiɗo suma duk haka suka ji batun wasu ma a kafafen sada zumunta suka fara sanin abin da ke faruwa wasu suna cewa an yi daidai wasu suna ganin Sarki ya yi son kai ko ya yi gaggawa.
Amma duk da haka sun fito group suna ta fatan alheri irin su Sakeena sun neme wayar Lamiɗo ba su samu ba amma sun tura masa saƙonnin ta ya murna.

Tunda tun ranar da tsohon Sarki ya yi murabus Sarki na yanzu Muhammad Lamiɗo ya fara gudanar da sha'anin mulki. Sarki ya haɗa shi da amintattun shi na fada irin su Waziri, Shamaki da madaki ya ce su zama idanuwan Lamiɗo tare da bashi shawarwari a mulkinsa tsohon Sarki ya yi ma Lamiɗo umarnin shima ya riƙe su domin za su taimaka masa, suma kuma ya ce su ji kamar shi ne domin inganta Masarautar Daura. Amma zai iya sauya wasu miƙaman na hakimai a matsayin shi na sabon Sarki yana da damar da zai yi sabon naɗe naɗe a tsarin mulkin shi.
Received at 15:16
14 people reacted with ❤
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Sannan tuni tsohon Sarki ya ba da umarnin a fara gyaran gidan shi dake cikin garin Daura shima babban gida ne nan za su koma shi da iyalansa da mahaifiyarsa Fulanin Daura.
Gidan Sarki na yanzu kuma shima za a yi masa gyara ciki da waje domin sabon Sarki ne yanzu da iyalansa za su zauna a cikin gidan komai da ya danganci Sarauta hadimai, dogarai masu kaki duka yanzu suna ƙarƙashin mulkin sabon Sarki Muhammad Lamiɗo ne a yanzu a Daura gabaɗaya maganarsa tana sama da ta kowa har ta Tsohon sarkin gabaɗaya.

Lamiɗo gani yake yi abin kamar wasa wai shi ne zaune a fada a kan kujeran Sarki yana hakimce da rawani da Alkeybba ga hakimai suna zagaye da shi, kamar a mafarki haka yake ganin faruwar komai kamar irin ya kwanta barci ya tashi ya ga ba haka ba ne.
Sai dai ba mafarki ba ne duk abin da ke faruwa gaskiya ne.

A daran ranar kwana na biyar da zamowarsa Sarki sun yi ganawa mai tsawo da Mai martaba a bangaren shi. Bangaren da nan da lokaci kaɗan zai zama mallakin Lamiɗo a matsayin sa na sabon Sarki.

Ya yi masa batutuwa masu ratsa jiki da zuciya da suka saka Lamiɗo miƙa wuya. Ya kuma karɓi kaddaransa da hannayensa biyu. Mai martaba tsohon Sarki ya miƙa duka yardansa da yaƙininsa a kan Lamiɗo kuma yana fata ba zai ba shi kunya ba. Ya nuna masa muhimnancin miƙa wuya ga sabuwar rayuwarsa da kuma tunasar da shi irin nauyin da yahau kan shi na al'ummar mutanen Daura da ma arewancin nigeria gabaɗaya
Daga karshe Mai martaba mai murabus ya yi masa fatan alheri da fatan Ubangiji ya taya shi riƙo. Sannan daga ƙarshe ya ce yana tare da shi domin neman shawara ko wani abu da ya shige masa duhu na sha'anun mulki yana nan a gefen shi. Sannan sun yi magana kan haihuwan Ummu Salma, ya ce Gimbiya ta sanar da shi an samu ƙaruwa.

Ya tambayi Lamiɗo wani tsari gare shi, yanzu dai ba shi da ikon barin Fada sai komai ya natsa tukunnah. Amma zai iya tura wakili can ƙasar da Ummu Salma ta haihu tunda shi ba zai samu zuwa ba.

Nan Lamiɗo ya faɗa masa tsarin shi, ya tura Kabiru shi zai isa can ƙasar Egypt domin ya yi ma jaririyar huɗuba anan gida kuma zai kira Abdullahi za a siya raguna a can Adamawa a yanka.

"Hakan ya yi sosai Allah ya raya ya yi mata albarka wani suna za ku sanya mata?

Mai martaba mai murabus ya tambaya.

Cikin ƙanƙantar da kai, Lamiɗo ya ce" Ba mu riga mun yanke shawaran sunan ba Ranka ya daɗe."

"A'a yanzu ai kai ne ranka ya daɗe."

Mai martaba ya faɗa yana ɗan mirmishi.
Yana zaune a ƙasan cafet Lamiɗo na gefen shi.

"Allah ya yi albarka. madallah sai ka yi magana da duka matanka ku tsara lokacin da za su baro can su dawo nan. Yanzu ne nan ne muhallinsu har zuwa lokacin da Ubangiji ya iyakance."

Sannan ya cigaba da faɗin daga baya za a yi taron naɗi da za a yi masa za a yi gayya tare da gangami taron taya shi murnan zamowarsa Sarkin Daura. Ya daɗe a bangaren Mai martaba har wajen sha ɗayan dare sannan ya koma bangaren shi barcin ma yanzu rabi da rabi ne yana jin sa kamar ba shi ba.

Kamfaninsu sun turo masa amsar saƙon shi na ajiye aiki sun nuna rashin jin daɗin barin shi aiki tare da su, suna kuma cewa matujar yana neman ƙarin albashi ne ya zo su tattauna za su iya ƙara masa amma suna jin daɗin aiki da shi.
Duk yadda yake son aikin shi amma ya rasa shi ba shi da wani zaɓi ne.

Rayuwarsa kamar ƙifawan ido komai na shi ya sauya a kwanaki shidda baya shi Captain ne na jirgin ruwa amma a yau kuma shi Sarki ne, sarkin Daura mai ƙaraga.

Bai samu sararin kiran kowa ba, ba ya cikin natsuwarsa. Da Kabiru kaɗai ya yi magana da asuba ma sun sake magana daman ya ce ya matsa a samu visa da wuri tunda gobe ne bakwai da haihuwa to ya kira shi ya ce Visa ta samu jirgin shi zai ɗaga daran yau ta Abuja zai isa kasar Cairo a wayewar garin gobe. Da yake kuɗi ya saki a wajen Visa yanzu kuma kasar mu in dai da kuɗi abin da ma ba zai yuyu ba yuyu yake yi.
Received at 15:16Reactions: ❤ 5, 👍 2
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Bai kira Abdullahi ba saƙo ya tura masa na cewa ya tura masa kuɗi a siya raguna a yi ma jaririyar Umma Salama Shaƙika na suna, duk da tarin saƙonnin da mutane ke ta tura masa na fatan alheri bai buɗe ko ɗaya ba, har su Hamma Jibo duk sun yi masa saƙo ko zai iya duba wannan sai daga baya in hankalin shi ya kwanta wannan sabuwar rayuwar ta bi jikinsa tukunna.

A ranar ma ya gana da duka wakilan fada da hakimai manya da ƙanana sannan ya gana da shugaban dogarai da magajiyar Hadimai na bangaren mata, sannan ya nemi zai gana da sarakunan ƙauyakun dake zagaye da garin Daura da Katsina gabaɗaya.

Jakadiya kuma daman tana nan a matsayin jakadiyar Sarki mai zamani a yanzu kuma abin sha'awa a gefen Lamiɗo ƙanin sa ne Saleem tare suke gudanar da komai hakan kuma ya yi ma Mai martaba daɗi, ko bakomai Saleem ma zai sake taimaka masa sosai. Sabanin Yazeed da yake can ƙasar da yake karatu cikin takaici yana son mulki sosai ko daga yadda yake jin ƙansa yaro ne matashi amma yana da izza da girman kai har ya fi Sageer da yake yayan shi son mulki da izza. Mai martaba ya shammace su sosai da a ce mutuwa ya yi za a yi zaɓe sun tabbata Lamiɗo ba zai taɓa kai labari ba.

A daran kuma a bangaren Fulani ya ci abincin dare itama sun daɗe suna tattaunawa kamar dai Mai martaba mai murabus, itama sake nuna masa muhinmancin zamowar sa Sarki tare da tunasar da shi nauyin dake kansa ta yi. Kowa sai ya ce ya cancanta shi kuma yana ganin bai cancanta ba a shekarunsa na arba'in da haihuwa a duniya gani yake yi ya yi ƙanƙanta da hawa wannan ƙaragar sannan yana ganin ba zai iya ba amma Mai nartaba ya saka yaƙini akan shi da zai iya haka ma Fulani.

Itama ta yi maganar sunan jaririya yadda ya faɗa ma Mai martaba haka ya faɗa mata.

"Na yi magana da ita Ummu Salaman da rana, ta ce har yanzu ba ku yi magana ba"

Lamiɗo ya jinjina mata kai.
Saƙo nan kawai ya tura musu daga ita har Bilkisu ba ma su ba, bai yi magana da kowa ba bayan Kabiru da Abdullahi. Fulani ta ce ya kama ta ya neme ta su yi magana duk asan abubuwa sun zo ba yadda aka yi tsammani ba.
Amma dai ya kira ta tunda haihuwa ta yi, ko yaya ne za ta ji daɗi. Ya amsa ma Fulani a ladabce da cewa zai kira in sha Allahu.

Shi yasa yana komawa bangaren shi wajen sha ɗaya na dare ya yi wanka ya yi shirin kwanciya lokacin sha biyu na dare a Nigeria yana tunanin Ƙarfe ɗaya na dare a can Egypt tunda tsakaninsu da Nigeria awa ɗaya.
Ya ga saƙon Aminin shi ma da cewa ya isa Abuja tun da yamma zai tsaya gidan Hamma Jibo, ƙarfe ɗaya na dare jirginsu zai ta shi. Ya ga saƙon amma bai ba shi amsa ba lokacin yana ganaawa da malaman fada ne.

Datar shi daman a kunne ta ke a kodayaushe Ummu Salama ya duba tana online sai ya kira ta vioce call har sau biyu ba ta ɗauka ba, ya san cewa ta yi barci tunda can dare ya yi nisa sai kawai ya yi ma Bilkisu waya direct call. Kira ɗaya kamar wayar na hannunta ta ɗaga kiran shi.

"Ranka ya daɗe"

Ta faɗa cikin zumuɗi domin wayar na hannunta tana I.g tana kalle kalle.
Ita fa ba ta san haka zamowar matar sarki ke da daraja ba sai da ta zamo, ta shaida zamowar yar Sarki da matar Yarima amma zamowa Gimbiya ne sai yanzu ta san yadda ake ji.
Ashe ko a baya kishi ne ya rufe mata idanuwana take ganin gwara Lamiɗo kar ya zama Sarki da ya zama Sarki ya ƙaro auro, yanzu kuma wannan ba ya gabanta tunda dai ta zama Gimbiya tana tunanin ta sha gaban kowa. Har Umma Salaman ta manta da ita, duk da ta ga jaririyar su Hamma Saddam na ta sawa ba ta da lambarta ba ta yi mata barka ba amma ta kira Ammah sun yi magana.

Tun yanzu har an fara kiran ta Gimbiya Bilkisu, kafin ta shiga Masarautar Daura ta fara zuba mulki da iko lokacin da ta ga kiran Lamiɗo ta ɗauka wasa ne domin tun saƙon da ya tura mata ta chart ba ta sake jin sa ba.
Shi ya sa jikinta na rawa ta daga kiran a muryanta ma za ka fahimci tana cikin tsananin farinciki.

Gyaran murya ya yi,amma bai yi magana ba. Shi fa mulki ba ƙarya ba ne yawo ma yake yi a cikin jini. Ko ba ya so yanzu shi Shugaba ne sannan wakilin Alumma, ba ya ma sanin lokacin da komai na shi ke sauyawa yanzu ko magana zai yi za ka fahimci natsuwa da kamewa a cikinta.
Received at 15:16
10 people reacted with ❤
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
"Ranka ya daɗe muna murna ni da yara mun yi kewar ka."

Ta sake faɗa cikin bayyana farincikinta.

"Congratulations Papa. Allah ya taya ka riƙo."

"Amin"

Karo na farko da ya yi magana sannan a kame ya ce ya gida yana fatan tana lafiya tare da yaran gabaɗaya.?
Ta ce duk suna nan lafiya sai dai kewarsa.

"Yaushe za ka zo?

"Ku ne za ku taho."

Ya faɗa a rabe kafin ya sanar da ita cewa in komai ya daidaita an gama gyara Masaurata za su tattaro su dawo nan gabaɗaya.

Bilkisu ta washe baki kamar yana ganin ta, murna da farinciki sun cika ta. Tana tambayan shi wai dukkansu gabaɗaya har da su Debora ya ce in tana so ba shi da matsala.
Farincikin Bilkisu ya kasa ɓoyuwa, tana faɗa masa Umman Kano ta ce ta kira shi ba ta same shi ba, ya ce bai ɗaga wayar kowa ba amma daga baya zai kira ta.

Sun jima suna mgana yara daman ta ce sun yi barci amma ba su da magana sai na shi, ya ce yana gaishe su zai samu lokaci ya kira lokacin da suke gida sun yi maganar makarantarsu, yanzu sun kusa fara jarabawar second term ne, wataƙila ma ba lalle ko an fara jarabawan a gama da su ba da zaran lokaci ya yi za su bar Lagos gabaɗaya su koma Daura.

Har suka yi sallama bai yi mata maganar Ummu Salma ba, itama ba ta yi masa ba daman kuma shi ba zai yi ba. Bai taɓa kawo mata maganar ta ba in dai ba ita ta kawo ba ko ta kawon ma yana kaucewa.
Lokacin da suka gama waya da Bilkisu ɗaya saura na dare sai ya sake kiran Ummu Salama ta vioce call, har ya cire rai da zai same ta sai kuma kawai ya ji ta ɗaga kiran.

"Hello."

Ummu Salma ta faɗa cikin barci, barci take yi ba ta ma ko duba mai kiran ba. Cikin magagin barci ne wayar ta dame ta da kara ta zura hannu idanuwanta a rufe suke.

Ta ce Hello amma ta ji shuru ba a yi magana ba ta ƙara cewa Hello nan ma shuru gyaran murya da ya yi ne ya sa ta fahimci wane ne.

Da sauri ta watsaƙe ta miƙe zaune akan gadon da take, daga gefen gadon ta ta latsa wani abu sai fitilar ɗakin ta kawo gabaɗaya haske ya haskaka ɗakin ta cire wayar a kunne ta duba sai ta ga Hamma ne yake kiran ta.
Daman tunda ta ga saƙon shi kewar sa ya ta so mata. Ko ba ta ganshi ba ta yi magana da shi ko ta ji sanyi.

Ta mayar da wayar kunne a shagwaɓe ta ce.

"Hamma."

"Hamma ka manta dani."

"Ka manta da ƙanwarka."

Sai da ya yi mirmishi, gefe da gefen bakin shi suka motsa.
Mirmishin da tun da ya zama Sarki bai yi irin shi ba.

Shi a wajenta ba Sarki ba ne mijinta ne da kuma Hammanta.

Kuka kawai ta saka masa tana masa shagwaɓa da rigiman ya manta da ita.

"Shike nan haka ake yi tunda ka zama Sarki ka manta da ni"

Ta gama faɗa har tana matse murya, kuma kukan da gaske take so ta yi.

"I'm sorry."

Ya furta a hankali.

"Ba wani sorry, na haihu amma ba ka damu da ni ba ballatana jaririyar da muka haifa."

"I'm sorry na damu mana"

Ya furta a hankali yana mai lumshewa idanuwana ya san halinta da rigima daman.

"Ummu Salama."

Ya kira sunanta a kausashe.
Bai jira ta amsa ba ya cigaba da faɗin.

"Ba ki san na zama Sarkin Daura ba ne? Abubuwa sun zo ban shirya musu ba."

"Ni ina ruwana da zamowarka Sarki, Ni Hamma na sani, da mijina ba ruwana da wata Sarauta."

Ta gama faɗa har tana tura baki kamar yana ganinta.
Ya yi mirmishi mai sauti.

"Ummu Salama."

"Mu yi video call?

Ya tambaye ta cikin wani narke murya, yana kwance ne amma kuma kewar Ummu Salama duk ta gama mamaye shi daurewa kawai yake yi da abin na hausawa da ake cewa sahun giwa ya take na raƙumi.

Bai jira cewarta ba ya katse vioce call nan take ya kira ta video call itama kamar tana jira ta ɗauka suna masu kallon juna.

Ta yi kewarsa sosai kuma har kewar ya bayyana a idanuwanta. Ƙwallar da suka taru suka sauko mata ta saka hannu ta share, shi kuma yana kwance kansa kawai ya ɗan dago jikinsa ba riga amma ya rufe da blanket.
Ummu Salma ce ta zuro kafafunta ƙasan gado ta saka tattausan silafas ɗin dake wajen.

Yana kallonta yana jin zuciyarsa na tsukewa a waje ɗaya. Ta kara masa fari sannan ya ga ta kumbura.

"Me ya same ki? Fuskarki ta kumbura."

"Haihuwa ce."

Ta amsa mishi tana shafa fuskarta.

"Kina lafiya?

"Ba wata matsala?

"Ina Babyn mu?

Ya tambayeta a jere amma a rarrabe.
Received at 15:16Reactions: ❤ 14, 🥰 2
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
"Lafiya lau na haihuwa cikin kulawa baby tana lafiya bari ka ganta."

Ta tashi ta isa in da ɗan gadon jariiyar in da take ciki tana barcinta ta haska mishi ita. Ya ƙura mata idanuwana yana kallonta cikin wani shauƙi.

"She is so cute."

"Kama da kai take yi "

"A'a ke ce."

"Ka duba da kyau Hamma."

Tana cewa shi ne yana cewa ita ce, daga karshe ya sakar mata da cewa da shi take kama duk da shima ya ga haka.

Ɗauko yarinyar ta yi ta koma gefen gado ta zauna tana riƙe da ita suna cigaba da magana.
Nan yake faɗa mata Hamma Kabiru na hanya da kuma yankaar da za a yi gobe a can gida Adamawa.

Daman sun yi vioce call da Baɗso ɗazu ita ta ba ma Ammah waya suka yi magana. Ta faɗa mata an siya raguna guda huɗu za a yanka sunan yarinyar suka yi magana ta ce ba su yi magana da Hamma ba tukunna, na zuwan Hamma Kabirun kuma kafin Mami su tafi masauki ta faɗa mata ya yi mata saƙo yana tafe.

Cewa ya yi ta yi ta haska masa baby yana kallonta.
Ta yi masa abin da yake so, ga shi tana da barcinta ba ta ma san ana yi ba.

"Hamma."

Ta faɗa tana karkato da wayar a fuskarta.

"Ba ka faɗi sunan da za mu saka mata ba! Ko ka faɗa ma Hamma Kabiru ne?

"Aa ban faɗa masa ba "

"Shima na ce in ya zo ya tambaye ki."

Ya amsa mata yana kafe ta da idanuwansa masu sanyata jin kamar tana jin sanyi.

"Ni zan faɗi sunan Hamma?

Ta faɗa tana mirmishin jin daɗi

"Na ba ki zaɓi"

"Da namiji ne mai sunan Baffa ne, amma tunda mace ce Allah ya ba mu na ba ki zaɓi"

"FATIMA."

"NA ZAƁA MATA FATIMA."

Ta furta tana kallon shi. Sai ya jinjina kai ya gyara kwanciya yana faɗin.

"Allah ya raya mana mai sunan Mami, Allah ya yi mata albarka."

Ta amsa da Amin tana dariya.
Shima mirmishin yake yi, Ummu Salma kamar tana shiga zuciyarsa yawanci tana cika muradinsa tun kafin ya furta tun lokacin da na'ura ta nuna mace Ummu Salama za ta haifa a zuciyarsa ya ce zai yi ma Mami takwara, tunda ya yi ma Ammah to ya ba ma Ummu Salma zaɓi ne yana tunanin ra'ayinsu zai zo ɗaya sai ga shi ba ta ba shi kunya ba.

Sun yi shuru kawai suna kallon juna shi ne ya katse ta da cewa ba ta jin komai ba ta da wata matsala ta ce babu nan ta shiga ba shi labarin yadda ta haihu.

"Hamma abin mamaki ko awa ɗaya ban yi ina naguda ba na haihu, kuma jinina normal na haihu lafiya"

"Alhamdulillah."

Ya faɗa yana cigaba da sauraran ta tana cigaba da ba shi labarin Mami ta matsu su koma gida saboda wai ta yi mata wankan jego na gargajiya, sannan ruwan nonon ta, bai zo da yawa ba ta ce in sun koma gida a nemi maganin gargaji yanzu Baby sai dai ana haɗa mata da madaran yara. Shi kuma ya ce za su dawo gida in dai likitoci sun tabbatar da ba matsala in Hamma Kabiru ya sauka zai yi masa waya kawai ya jira su taho tare.

"Hamma wani suna za mu dinga yi ma Baby alkunya?

"Ni kuma? Ta ya zan sani"

"Mu kira ta Baana tunda muna da Beena?

"Baana?

Ya maimaita cikin sigar tambaya.

"Mene ne ma'anarsa?

Ta fara dariya tana faɗin ba ta sani ba.

"Nima ban sani ba ko Beena Bilkisu ce ta saka mata."

"Ki samu suna mai ma'ana kar ki je ki saka ma ƴata sunan mayu."

Ya faɗa har yana yi mata gargaɗi da hannu ta fara dariya har sai da baby Fatima ta farka ta yi saurin danne bakinta.
Cewa ya yi ta ba ta nono yana gani sai ta ajiye wayar ta saita a saman ɗan drower ɗin dake gefen gadon ta fara ba ta nono yana kallon su cike da sha'awa da kewa ba domin wannan sarautar ba da yana tare da su a halin yanzu. Ita kuma tana so ta tambaye shi Hanan tana jin kunya, ta san ko ta nan ko ba ta nan Hanan tana cikin ƙoshin lafiya.

Kallon su kawai yake yi, Ummu Salama ce ke magana shi dai na shi kallo ne da ji, sai da ta gama ba ta nonon ta ƙoshi sannan ta je ta kwantar da ita aɗan gadon ta saboda ta koma barci.

Sannan ta dawo ta ɗauki wayar suka cigaba da hira.

"Hamma."

"Matar Hamma"

"Kana cikin damuwa ko? Na sani ba ka san sha'anin mulkin. Amma ina so ka sani haka Allah ya kaddaro mana ba mu da yadda za mu yi."

Ta dakata tana kallon shi yana lumshe idanuwana yana buɗewa.

"Gani nake yi kamar ba zan iya ba. Akwai wahala mulki Ummu Salama akwai wahala."

Ya gama faɗa a muryansa za ka gane yana cikin kasala da sanyin jiki.
Received at 15:16Reactions: ❤ 17, 🤗 2
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Sannan ya ga Hamma Saddam online jin yana gida sai ya kira video call na gabaɗayan su a group na Ammah da Baffa, waɗanda ke kusa suka ɗaga kamar Hamma Saddam da Hamma Abdulrraham da Hamma Abdulrahim sai Hamma Abdullahi Hamma Mustapha ne bai ɗaga ba sai Lamiɗo, Ummu Salma ma ta kama a wayarta.

Hamma Saddam ya je falon Ammah tana tare da Umma Balki da ta iso a daran jiya, shi kuma Hamma Abdulrahin yana tare da Baɗɗo ne.
Kowa na ganin kowa nan ya ce ga shi ya iso har an yi ma yarinya huɗuba da Fatima.

"Allahu akbar Allah ya raya mana Fatima."

Ammah ta faɗa tana cigaba da addu'a. Umma Balki ma ta yi fatan alheri tunda har Ummu Salma tana kai.

"Gimbiya Auta ya jikin na ki?

Umma Balki ta faɗa ta saka kowa dariya sai yi ma Mami tsiya take yi wai ta yi takwara baki yaƙi rufuwa.

"Ina shi Lamiɗon na ɗauka ni zai yi ma takwara sai ya yi ɗanwaken zagaye? Idona idon sa sai na ci ƙaniyarsa."

"Umma Sarki ne fa, yanzu ko magana kika faɗa mara daɗi dogarai za su yi miki ladabi."

Hamma Saddam ya amsa mata ana ta dariya bayan ta ce ƙaniyarsa. Tana faɗin suna murna ga Lamiɗo Allah ya ta ya shi riƙo.
Sannan da cewa yaushe za su dawo? Mami ce ta amsa da cewa sun kusa dawowa ƙila ma su dawo tare da Hamma Kabiru gabaɗaya.

Bayan an gama ganin juna da gaisawa aka haska ma Umma Balki da Ammah takawaran Mami suka ganta, sauran duk sun bar video ca ɗin tunda Hamma Abdullahi ya ce zai zo gidan yanzu da masu yanka mahauta kenan za a yanka ragunan a gyara.
Ammah ta ce ta faɗa ma maƙota da sauran abokan arzuƙa za ta ɗan yi taron suna a yau ɗin Mami ta ce hakan ma ya yi.

Daga karshe Baɗɗo kawai aka bari da Ummu Salma suna magana, Hamma Abdulrahim ya bar mata wayarsa.

"Sisna, Allah ya raya mana takawaran Mami ko na ce Sarauniyar Daurama."

"Amin"

Ummu Salma ta amsa tana mirmishi.
Tana yi ma Baɗɗo tsiyan ya amarci ta ce gamu cikin shi Ummu Salma ta ce Allah ya ba da sa'a.

"Wani inkiya za mu dinga kiran takawaran Mami?

"Banafsha na daɗe ina son sunan nan."

"Miye ma'anarsa? Mai Martaba Sarkin Daura Muhammad Lamiɗo ya ce kar na saka ma ɗiyarsa sunan mayu."

Ta faɗa ƙasa ƙasa kar su Mami su ji Baɗɗo ta fara dariya.

"Suna ne mai kyau da tarihi. Sunan larabawa ne, kuma yana nufin mace mai kamewa da natsuwa"

"To shike nan, ki faɗa ma kowa sunan da

Please Login or Register in order to submit comment