Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na ji ba Umma Balki tana faɗin akwai matar Baffa Umaru da wasu matan ba, ki faɗa mata da sassafe ta je gida akwai motar da za ta ɗauko su, gwara ta zo ta fuskanci ke Sakin da Habib ya yi miki kamar gobarar Ummu Salma ce a garin Jimeta."

Suka kwashe da dariya a tare har suna tafawa.

"Ta ce wai har da ƙarin zuwansu ta ga Hanan"

"Har uwar Hanan da uban Hanan duk za su gani."
Baɗɗo ba ta da mutumci sai zaginsu take yi Ummu Salma na faɗin akwai tausayi ga talauci ga rashin haihuwa.

"Ai bai kamata ma su haihu ba, sun wulakanta rai tun yana ciki fa."

Haka nan Ummu Salma ta kira Shamsiya ta faɗa mata. Sun rabu akan za ta yi ma Hamma Abdulrahim magana amma su tabbatar da safe sun je gida tunda tafiyar mota ce, kayan da suka bari ma acan duk Hamma Abdulrahim ɗin ne zai tattara in ta su Hamma Abdurrahaman ne ƙila sai sun iso sannan za su tuna da wasu kaya ma.

Sabbin ɗinkunanta kuma Mami ce za ta taho mata da su a gobe ba su ɗau kaya ba akwati ɗaya ne da jaka, kowa ka gani karamar jaka ce tunda ba daɗewa ba ne.

Bayan tantancewa, suka hau jirgi sai katsina misalin sha biyu saura suka sauka Katsina
Tawagan da za ta ɗaukesu tuni suna jiran su a filin jirgi. motoci sama da goma har da masu kakin masarauta ga dogarai da hadimai mata an taho da jakadiya a cikin masu tarban su.

Sun isa Daura da azahar ne lalle Masarauta ta sha gyara ko'ina na ƙyalli an sauya ma tsarin Masarautar gabaɗaya.
An haɗe shashen Mai martaba da bangaren Yarima rabi, rabin kuma aka shigar da shi a wani bangare na dabam.
Bangaren Gimbiya Shahida nan ne bangaren da Bilkisu ta sauka. An sake faɗaɗa shi kamar ba bangaren ba.

Sannan bangaren Gimbiya Hadiza an haɗe shi da na Gimbiya Maimunatu, an ɗiba an faɗaɗa bangaren.
Na Gimbiya Amratu ma an sake faɗaɗa shi an kuma sake fitar da wani bangare na dabam ga shashem Fuani ma an gyara shi, ga na hadimai da bangaren madafi komai dai ya samu kyakyawan sauyi.

Tawagan mutanen Jimeta kaf a bangaren Ummu Salma suka sauka zai ishe su. Daga Umarnin Sarki Hadima Tani ta jagoranci Ammah da su Ummin ikki zuwa masauƙin baki a cikin masarautar. Adda Safina a bangaren Bilkisu ta sauka su tun safe suka iso, tana jin yan Jimeta sun zo ta baro can tunda shima can ya cika da dangin Bilkisu ya'yan sarakuna ana ta baza capacity.

Bangaren Fulani akwai baƙi nan ne su Hajiya Kilishi da iyalansu suke sauka, suna ta shirye shirye.
Ƙannen Lamiɗo kuma duk sun iso suna can gidan Sarki mai murabus.

An kawo masu abincika kala kala da ababen sha, komai ga shi nan ne kawai. Komai sabo ne a bangaren nan Baɗɗo na faɗin sabon Sarki sabon Masarauta.

Yaran su Hajiya Kilishi sun shigo bangaren Ummu Salma sun yi musu maraba tare da ganin Banafsha.
Ba su kuma ga Maimartaba Lamiɗo ba sai dare ya je can bangaren da aka sauki su Ammah ya gaishe su, suna tare da su Hamma Kabiru da Saleem su Yazid ba su zo ƙasar ba suna jin haushi.
A daran Mai martaba ya ba da umarnin son ganin Ummu Salama da Banafsha a bangaren shi, lokacin da ta je bangaren sai da ta saki baki. Bangaren ya haɗu a cikin bedroom ɗin Mai martaba gadon sa mai rumfa ne da wasu labulaye na alfarma. Ta zo kenan Banafsha kawai ya ɗauka sai ga Bilkisu kuma taki fita Ummu Salma na son rumgumar mijinta ba hali.

Sun gaisa da Bilkisu sama sama kamar yadda suka saba. Kowa ya kalli ɗan'uwansa ya kauda kai, Bilkisu ta ga Ummu Salma ta yi mata wani kyau, itama Ummu Salman kyan Bilkisun ta gani ga shi kowacce ta sha ƙunshi ta yi fes.

Lamiɗo ne ya miƙa ma Balkisu Banafsha ta ɗauketa daman lokacin da suka iso ba ta shigo ba yaran ne suna isowa suka yo bangaren tun ɗazu saboda Banafsha.
Ta ɗauketa ta yi Allah ya raya ba wani kasarsashi. Ummu Salma ta karɓi ɗiyarta, ta koma bangarenta tana jin haushi da kishi amma ba ta bari ya yi tasiri ba. Bilkisu kuma har ta ji haushi ganin Ummu Salma a bangaren Mai martaba sai yanzu ta dawo cikin hayyacinta har abada fa ba za ta so kishiya ba.
Received at 15:21
7 people reacted with ❤
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Washegari da safe bayan sun yi wanka sun karya. Mai Martaba ya ba da mota aka ɗauki su Ammah da Ummu Salma zuwa gidan tsohon Sarki suka gaishe da Mai martaba da Fulani tare kai masa Banafsha.
Ya ɗauketa ya yi mata addu'a daga karshe ya ce Allah ya yi ma Batula albarka aka amsa da Amin.

Ba su daɗe ba suka dawo su Hamma Abdullahi tun shidda na safe suka kamo hanya motar daman tun a daran jiya ta isa Jimeta, irin doguwar motar nan ne ta masarauta lafiyayya.
Tare da su Shamsiya da matar Baffa Umaru da wasu cikin yaransu mata.
Mami kuma sai da yamma suka iso Daura, mota ta je filin jirgi a katsina ta ɗauko su. Sai ga Hajiya Fatima Baba ta sake saka kafafunta a garin Daura.

Garin da ta ji ya fita ranta ta tsane shi sama da shekaru talatin da biyar ba ta taɓa tunanin za ta dawo ba. Ta fita cikinsa cikin ƙunci da kuka ɗauke da Lamiɗo cikin jinin haihuwa yau ga shi ta dawo a matsayin uwar Sarki kuma surukar Sarki.
Ubangiji mai yin yadda ya so a lokacin da ya so.

Mami ta zo da ɗinkunan da aka yi ma Umma Salma rantatsu masu kyau,
Sun iso ba daɗewa sai ga Hajiya Zeenatu da Hajiya Zannura sai Hajiya Binta tare da zugan yaran su manyan mata sun shigo bangaren Ummu Salma ganin Banafsha suka haɗe, ba sai an faɗa maka ba kana ganinta ka ga fuskar Lamiɗo.
Balle ma Hajiya Binta ta faɗa musu tunda har da ita aka je Kaduna aka taho da Ummu Salama.

Mami ba ruwanta sun gaisa sama sama sai juyi take yi cikin wani leshi wuyanta da hannayenta gwalagwalai ne kowa ya ganta ya san ta wuce tsara ga Islam da ta zama budurwa yanzu tana ma SS2 ne, har Faruk ya girma.

Ammah suna can bangaren da aka sauke su da Mami ta je sai da ta yi magana.

"Son kai, wato masauƙin uwar Sarki ma na dabam ne."
Ammah ta ce ya son ranta su Umma Balki na ta yi musu dariya. Mami na faɗin ta ji ba komai da ka haifi Sarki ai gwara ka haifi matar Sarki Ammah ta amsa ta da cewa gwara ka haifi Sarkin. Suka bar su Ummin ikki da yi musu dariya.

Gaskiya Mami ta faɗa domin masauƙin da aka sauki su Ammah ya haɗu, Hamma Jibo ma a ranar ya iso tare da Adda Nauwara.
Adamawa da Jimeta sun haɗu a waje daya sai son barka. A kuma daran su Hamma Abdullahi suka sauka bayan mangriba.
Suma a wani kayatattacen masauƙi aka sauke su gabaɗaya mazan, matan kuma aka kai su can wani masauƙin su Shamsiya Ummu Salma ta ce aka wo su bangarenta.

Komai suke buƙata ga Hadimai nan motsi kaɗan za ka yi za a yi maka abin da kake so. Asabe tuni ta tare a bangaren uwar ɗakinta sun haɗe da su Harira.

Washegari safiyar asabar aka tashi da shagalin bikin naɗi tare da shagalin sunan Fatima Banafsha. Ranar Ummu Salma na da kwana talatin da ɗaya da haihuwa
A fada aka yi taron naɗin gwamnoni sun zo, sarakuna da yan majalisu yan kasuwa da ma'aikatan gwamnati malamai da dattijan gari duk sun zo Hafiz ya zo tare da Salima sannan ya yi magana da wasu daga cikin yan'uwan su suma sun taho.

Fadar Daura ko na ce Masarautar Daura ta cika da mutane ta dumbatsa ga masu kaɗe kaɗe da masu buga tambura. Masu busa da maroƙa a cikin waɗanda suka zo har da mawaƙan mu na arewa.
Fada ta cika da busa sarewa da kaɗe kaɗe na tashi a status ɗin Hamma Saddam Ummu Salma ta fara ganin farin Sarki mai farar zuciya
Ya sha rawaninsa fari alkeybbansa ma fara ce mai zanen baƙi haka yana zaune a fada a saman kujeran ƙaragar mulki ga manyan ƙasa ne zagaye da shi wasu a saman kujeru ga walikan fada kuma suna zazzaune a ƙasa.Har da tsohon Sarki mai murabus a wajen shima yana zaune akan kujera cikin kayan Sarauta.

Suma a cikin gida kowa ya yi wanka ya yi shigar alfarma, Fulani da kaf matan Maimartaba da ƙannen Lamiɗo suna gidan su Hajiya Sakeena mutanen England duk sun zo ƙasar saboda taron naɗi nan.
Kowa ka gani da ɗanƙareran leshi da gwalai gwalai a wuya da hannaye.

Ummu Salma ma leshin ta saka mai kalan ja ya yi mata kyau ɗinkin bubu ne, wuya da hannaye gwala gwalai na ƙyalli, sannan Banafsha ma ta sha kayan alfarma.
Received at 15:21
7 people reacted with ❤
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ba su fita Fada ba sai gobe za a je a yi ma Sarki gaisuwa ta musamman amma a cikin gida an sha shagali a fada kuma acan an yi jawabai daga manyan mutane da wakilan fada har Sarki mai murabus ya yi jawabi haka ma sabon Sarki.
Ga shi nan su Hamma Saddam suna ta ɗorawa a status ɗin su.

A cikin gida kuma an yi busa manyan mata suna ta rangaji cikin kasaita da izza, an ci an sha abincika ba nau'in da babu ga shi an yi sevinors abin rabo an yi jakunkuna da hoton Mai martaba Lamiɗo, ga littafi mai biro, ga jakunkuna an yi mug da cokali an nannaɗe a kwali, an raba atamfofi iri ɗaya sak ga turarukan wuta, ga azkar ƙananu da aka rarraba ga key holder abin rabawar ne ba adadi ga su nan.

Ummu Salma ta shiga ta fita, kuɗi ko wata ƙwarya ce sai da aka cika mata shi da kudaɗe, ga gefen gadonta ya cike da kaya wasu ma akwatina ne guda suke kawowa kuɗi kuma daga masu saka milliyan sai masu dubu ɗari biyar.

Arziki na in da yake, Shamsiya ta ga duniya a Daura suna gefe amma babu abin da suka nema suja rasa suma. Habiba kam ta ruɗe faɗi kawai take yi Allah ya azurta su, sun ga Hanan sun saka leshi iri ɗaya da Beena yara ne amma gwal ne a wuyansu da hannayensu.
Hanan ma kaɗai abin a tsaya a kalleta ne.
Ba ma Ummu Salma ba Shamsiya sai hawaye a ɓoye, Ubangiji ya yi ma Ummu Salma kyakyawan sakayya.

Bilkisu ma ta yi shirgar alfarma itama leshin ne mai tsada daman ga ta yar gayu sai kuma ya haɗe da yau Gimbiya take shiga kawai take yi tana fita. Dangin ta sun shigo bangaren Ummu Salma sun ga Banafsha itama ta zo ta rako Umman kano yau suka zo kuma a ranar suka koma. Kowa ta kalli yaruwanta ta kawar da kai. Cikin su ba wacce za ta ce ba ta ji kishin yaru'wanta ba. Umman Kano dubu ɗari biyar ta ba ma Ummu Salma, kuɗi akwai su ba ma ajin zafin fitar da su Ammah suna bangaren su tare da su Ummin ikki suma can Hadimai na kula da su.

Washegari kuma baki suka kai gaisuwa fada ga Sabon Sarki yau ɗin ma farin rawani ya saka yana zaune akan ƙaraga dukkansu har da Bilkisu da yara suka fara zuwa suka kai gaisuwa, fadar ta cika da mata da maza sai ga Mami a fada tare da Ammah Lamiɗo na zaune kan ƙaraga Sarkin dogarai na faɗin Sarki ya amsa Sarki ya gaishe ku.
Ga su Hamma Jibo a gefe a zazzaune abu kamar a mafarki kuma a zahiri ne.

Lamiɗo na zaune ya hakimce ko iya ɗaga idanuwana baya yi saboda Sarauta da ƙasaita. Ubangiji ne in ya ce kum ya fakum ba wanda ya isa.
An yi hawan dawakai. Sarki ma ya hau farin dokinsa ya zagaya cikin gari ya dawo tare da tawagansa sannan Bilkisu Gimbiya ta sauke shi a saman doki. An yi ma Bilkisu naɗin Gimbiya bayan an saka mata alkeybba ita kuma Ummu Salma aka saka mata alkeybban a matsayin Sarauniyar Daurama.

Da yamma kuma Mami ta ce a kaita gidan Sarki Mai murabus ta duba shi, aka ba da mota aka kaita ita da su Islam da Hajiya Falmata tunda gobe baƙi za su yi halin su.

Yau ga Mai martaba tsohon Sarki Nasiru ga Fatima Batula sun haɗu a garin Daura ba a matsayin mata da miji ba, sai a matsayin Baba da Mama, iyayen Mai martaba Sarkin Daura Muhammad Lamiɗo su Gimbiya Maimunatu sai kallo domin dai yanzu sun san kishin Fatima ma ba shi da amfani tana da mijinta.

Fulani ta yi mata karɓa na karramawa sosai domin ita tun bayan abin da ya faru komai ya wuce a matsayin y'a ta ɗauki Mami.
Da za su tafi Tsohon Sarki ya yi ma Faruk da Islam kyautar kuɗaɗe Fulani ma haka ta yi musu kyauta haka Hajiya Falmata ma ta samu farar takarda cike da sabbin kuɗaɗe.

Ranar litini baƙi suka fara watsewa. Mami ta riga kowa tafiya Daddy ma da ya zo a ranar asabar ya koma. Tawagan mutanen Adamawa duka jirgi Mai martaba Sarkin Daura Muhammad Lamiɗo ya ɗau nauyin su har da su Shamsiya da kowa da kowa. Kowanne da abin arziki bayan abin rabo ga kuɗaɗen da Masarauta ta raka su da shi.

Ammah kuma tsohon Sarki ya sake biya mata kujeran Makka za ta sake komawa ta sauke farali.
Su Hamma Jibo duk sai da suka je suka kai gaisuwa kafin su tafi.
Received at 15:23
13 people reacted with ❤
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Aka bar Ummu Salma da Banafsha da tarin dukiyar da suka tara. Tun da suka tafi Hadimai suke gyaran ko wani bangare. Ba su kaɗai ba har sauran dangin su na Daura suma sun koma da sha tara na arziƙi sai a lokacin suka ga Mami wasu ma ba su santa ba sai dai labarinta. Waɗanda suka santa ɗin iyayensu ne sun kuma rasu sai yara da jikoki an yi zumunci kuma sun ji daɗi kwarai.

Sun tafi sun bar Daura da Sarkin su Muhammad Lamiɗo da matanshi tare ya'yan shi a cikin Masarautar Daura in da za su fuskanci Sabuwar rayuwa.



*Janafty*
Received at 15:23
12 people reacted with ❤
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
*FJ littafin kuɗi ne 1k a manhajar Telegram tura kuɗin karatu ta wannan acct ɗin 9069067488 Opay Jamila Umar shaidar biya ko tuntuɓa ta waɗannan lambobin.*
08032773332
09069067488.

Alhamdulillah baƙin da suka zo Daura duk sun koma gidajensu cikin ƙoshin lafiya da aminci kowa na ta son barka tunda sun koma gidajensu da sha tara na arziƙi sai dai fatan Allah ya ta ya Mai martaba Sarkin Daura Muhammad Lamiɗo riƙo Ubangiji ya ba shi sa'a ya kuma tsare shi.

A satin kaf duka platform na social media da manyan bloggers ɗin arewa hotunan Lamiɗo ne kawai ke yawo cikin shigar Sarauta ya yi kyau har ya gaji da kyau saboda shi ɗin mai kyau ne, yan comments section na ta faɗin albarkacin bakin su mafi yawancin su dai suna yabon kyau da zati ne irin na sabon Sarkin Daura wasu kuma suna masa laƙabi da matashin Sarki, suna ganin cancantarsa wasu kuma suna ganin kamar shekarunsa sun yi ƙanƙanta kowa dai na faɗin albarkacin bakinsa ba tunda ba wanda aka hana faɗin ra'ayinsa.

Ummu Salma ta kira duka danginta da suka zo ta yi musu bangajiya da godiya. Ita kaɗai a bangarenta daga ita sai Harira sai Asabe da Banafsha Hanan na can bangaren Bilkisu ita da su Sultan da Beena amma kusan a bangaren Ummu Salma suke yini saboda Banafsha.

Daman ita Ummu Salma ba ta ce za ta karɓi Hanan ta dawo bangarenta ba. Ta san Lamiɗo ba ya son a raba ko makwamcin Beena da Hanan  ne kuma tunda Bilkisun ba ta nuna komai ba ta cigaba da zama a can ba za ta taɓa mgana ba, a baya ma ta zauna tare da ita kuma ba abin da ya same ta ballanta ma yanzu da suke ƙarƙashin rufi ɗaya na gida ɗaya.

Tuni Mai martaba Lamiɗo ya miƙa a mulkinsa ya yi sabon naɗe naɗen hakimai ya sauya wasu sarakunan ƙauyaku sannan ya sauya masu sarautunsu.
Sannan an ƙaro hadimai da dogarai tare da dirobobin masarauta.

Ummu Salma an ba ta hadiman bangarenta sai ta naɗa Harira a matsayin shugabansu ita da Asabe. Bilkisu kuma daman Debora da Anitha sun taho bayan taron naɗi ta tabbata dai ba za ta barsu ba suma kuma ba za su barta ba, sun shigo har bangaren Ummu Salma sun gaisheta sun kuma ga Banafsha Debora ke faɗa ma Ummu Salma James da Baban Adila na can Lagos za su kula da gidaje da motocin dake can. Ummu Salma ta san daman ba za su tafi ba, yadda suke jin daɗin aiki a ƙarƙashin Hamma Lamiɗo ta san ko da suma sun amince zai ce ne su taho Masarauta su cigaba da aiki can ɗin ma da za su zauna ba duk wata suna da albashi sauran buƙatunsu ma ba zai taɓa gajiyawa ba. Kamar maigadinsu na Jimeta ne, shima aikin shi kawai ya kwana ya kula da gida amma tarin alherin da yake samu ta hannun Lamiɗo ko wani ma'aikacin gwammati sai haka.

Tuni Masarautar ta ragu, baƙi duk sun koma gidajensu har da na ƙasashen waje da suka taho. Yau sati ɗaya da yin taron naɗin nan, kimanin kwana talatin da takwas da haihuwan Ummu Salma saura kwana biyu su yi arba'in ta dage da kula da jikinta kamar yadda Mami ta faɗa mata in dai suka yi waya sannan ta dage da shan magungunar wajen Surayya Halin yau, domin ta kame ta yi tsam yadda Mai martaba zai manta cewa ta haifi Banafsha.

Ita tun da aka yi taron naɗin  ba ta je bangaren Mai martaba ta kwana ba, ta kan je da safe kafin ya fita fada ta gaishe shi ta kai masa Banafsha wani lokacin kuma sai da daddare in ya shigo ta aiko jakadiya ta yi mata iso, in kuma ta je ba ta wani daɗewa take dawowa bangarenta duk da ta yi kewarsa amma tuna tana jego ya sa ba ta yi tunanin kwana a wajensa ba. Ta ɗauka Bilkisu na zuwa wajensa ganin bai taɓa mata magana ba, a tunanin ta ya san in mace ta na jego in tana da abokiyar zama ta kan ɗan ɗaga kafa da zuwa turaka amma ba addini ba ne al'ada ne kawai.

Shi kuma ya na ganin ba ta kwana a wajen sa in Bilkisu ta yi kwana biyu, ba ta sake zuwa sai bayan kwana biyu a tunaninta yana tare da Ummu Salma ne, shi kuma ba ta zuwa ko ma ta zo sai ya ga ta tafi ba ya son dogon magana ko tambayoyi shi ya sa bai tambaya ba. Sannan ga sha'anin mulkin da ya yi masa tsaye a rayuwarsa. Duk yadda ba ya son mulki sai da ya zo ya sarƙe shi a lokacin da bai yi tunani ba.
Received at 19:42
12 people reacted with ❤
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Duk yadda ya kai ga hasashen wahalan mulki ashe wasa yake yi sai da ya gan shi ya ciki ya tabbatar da wahalansa ya fi hasashensa yawa. Tunda Mai martaba tsohon Sarki ya yi murabus bai kwanta tun daga dare har wayewar gari yana barci ba, bai samu kebewa da iyalansa tun daga safe zuwa yamma ba. Bayan an yi taron naɗi kuma ba shi ma da lokacin kansa yana ta ganawa da sarakunan ƙauyaku da malamai da dattawan gari sannan jiya ya fita sun je wani ƙauye nan kusa da aka samu barkewan cutar amai da gudawa a dare ɗaya yara goma sha suka rasu, yau ɗin ma sai da yamma ya dawo fada ya biya wajen Mai martaba tsohon Sarki domin ba ya gudanar da komai sai da shawaransa kuma yana ganin amfanin haka.

Sai dare ya baro fada sun ci abincin dare tare da wakilan fada da Saleem da tare suke yini a fada, Mai martaba Lamiɗo ya yi masa masauƙi a cikin Masarauta wani lokacin ya kwana anan wani lokacin kuma ya koma gida, ya gama karatunsa yanzu aiki kawai ya ke jira, daman ya yi degree ɗin sa da farko ya dawo gida ya yi service sai ya koma domin ya haɗo masters ɗin shi yanzu kuma ya gama shi ya sa ya dawo gida.

Goma da wasu mintina ya iso bangaren shi.
Ya yi wanka ya saka sauƙaƙun kaya duk yadda ba ya shiri da zafi yanzu ya fara. Tunda yini yake cikin manya kaya da rawani.
Ya ƙoshi tunda sun ci abinci amma sai ya ji yana marmarin shan ruwan zafi a daran nan kafin ya kwanta kuma ma a ce Ummu Salma ce za ta dafa masa, ya samu saƙon ta, ta hannun jakadiya kuma itama ta yi masa test messages ta faɗa masa tana son a kawo mata kayan abinci a store ɗin bangarenta da cefane za ta dinga girki da kanta.

Ya ba da umarnin a yi mata yadda take so yana marmarin girkinta bakin shi na buƙatar ɗanɗanon abincinta da ya daɗe bai ci ba, sannan kuma ya yi kewarta, hirarta kawai yake so ya ji kafin ya kwanta ya rasa me yasa take gudun sa? Kwana biyu Bilkisu ke ɗebe masa kewar dare, to kuma kowa da abin da ya iya, ita ba ta iya hira ba shi kuma yana so a yi masa hira ya saurara ko da ba zai yi magana ba.

Ba faɗa masa ta yi ba ya fahimci ta ɗauka Ummu Salma na zuwa ne shi ya sa in ta kwana biyu sai ta ɗauke kafa sai bayan wani kwana biyun bai taɓa faɗa mata ai Ummu Salma ba ta zuwa ba, bai cika magana ba sannan ba ko wani ƙaramin abu ke saka shi magana ba.

Wayarsa ya ɗauka ya kira Ummu Salma a jiya Bilkisu a wajensa ta kwana yana sane yau ba za ta zo ba. Ita kuma Ummu Salma a waya suka gaisa yau jiya ne kaɗai suka haɗu da safe da ta zo gaishe shi ita da Banafsha.

Wayar har ta katse ba ta ɗauka ba, sai ya ƙyale ta a tunanin shi ta yi barci kamar ko ya sani ta yi barci domin da wuri suke kwanciya yanzu. Cikin barcin ta ji kiran wayar ta dake gefenta ko da ta farka wayar ta katse tana dubawa ta ga Hamma na sai ta watsake ta bi bayan kiran na shi.

Lokacin Bilkisu ya ke so ya kira ta kawo masa coffea mai zafi, yana so ya sha kafin ya kwanta. Wayar ta shiga ta ɗauka ta fara gaishe shi kenan kiran Ummu Salma ya shigo a waiting call yana dubawa ya ga ita ce sai ya fasa faɗin abin da yaso ya faɗa.

"Kuna lafiya? How are my childreen?

Ta amsa masa da suna lafiya, ɗazu ma suna tare da Sultan wani lokacin yana zama tare da shi a fada, ko kuma in zai je can wajen Mai martaba tare suke tafiya. Beena ce da Hanan jiya da Safe sun taho bangaren shi, su ne yake yini bai gan su ba.

Ya sauya maganarsa da cewa ya kira ya ji lafiyarta ne da ta yara ta ji daɗi. Daman tana zaune da waya ne amma tana tunanin shi yana can tare da Ummu Salma duk da abin ya fara mata sauƙi zafin kishin yana raguwa tunda Umman Kano ta ce ta dage da addu'a yanzu da za ta ga Ummu Salma ta ji zuciyarta ta fara zafi yanzu za ta fara kiran sunan Allah, sannan tana yawan addu'an Ubangiji ya rage mata zafin kishi tunda dai ta fahimci Ummu Salma ba za ta bar mata Lamiɗo ba gwara ta koyi yadda za ta rayu da ita a matsayin kishiyarta sai dai har abada ba za ta so ta ba.
Received at 19:42
6 people reacted with ❤
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ya zura mata idanuwana yana kallonta.
Sai ta sadda kanta ƙasa.

"Hamma kar Anty  Bilkisu ta zo ta ganni ba daɗi."

Ya yi mata wani kallon ƙasa ƙasa sannan ya ɗauke kansa kamar bai ji abin da ta ce ba.

"Ya aikin? Ka

Please Login or Register in order to submit comment