Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cewa ba ta kira shi ba a e ɗin shima zai tafi.
Wayar a amsa kuwwa Mami ta saka tana fara ringing ya danna mata busy har tana tunanin ko yana cikin mutane ne sai ga kiran shi ya shigo ta ɗaga.

Muryan shi tarai, muryan da kan sanya Ummu Salama kasala da shauƙi a baya ban da yanzu.

Suka gaisa da Mami da tambayan mutanen gida.

"Yaushe za ka dawo?

"Da zarar Mai martaba ya ta shi zuwa London'

Ya amsa mata cikin yanayin maganarsa. Mami ta tambaya da cewa daman bai tafi ba? Sai ya ce sun samu tsaikon Visa ne ta yi fatan alheri.

Suka yi shuru dukkansu ba wanda ya yi magana.
Shi da man ba gwanin ɗago magana ba ne ko da akwai maganganun a bakin shi.

"Ɗiyata ta ce ta kira ka, ba ka ɗauka ba?

Sai ya yi shuru kamar bai ji ba sai da Mami ta sake maimaitawa.

"Ban lura da kiran na ta ba Mami."

Ya amsa kai tsaye amma a ƙasan zuciyarsa yana tunanin ko lokacin haihuwar nan Ummu Salama ta samu natsala ne? Shi dai yana ganin she is not okay.

"To ta kira ka ne ta ba ka hakuri kowa a gida ya ce ba ta kyauta ba. Amma kai ma ba zan fasa faɗa maka ba ka kyauta ba koma me ya faru ai ka duba yanayinta lallashi take buƙata ba faɗa ba."

"Mami."

Ya kira sunanta ta amsa.

"Ni cikin ɓacin rai na yi maganar da na yi, amma Mami Ummu Salama ta kyauta mganganun da ta faɗa ma Ammah? Ta kyauta abin da ta yi?

Ya faɗa a jere daga ji yana ƙokarin sarrafa fushinsa ne

"Ba ta kyauta ba, kowa ma ya faɗa mata kuma ta karɓi laifinta kuma har ta ba ta hakuri ma."

Ya yi shuru kawai bai yi magana ba.

"Kai ma sai ka yi haƙuri, kai ne babba. Ka lallasheta domin tana bukatar hakan."


"I will."

"Amma ni ma mganganun da ta faɗa mini ta kyauta?

"Ba ta kyauta ba, za ta ba ka hakuri."

"Better."

Ummu Salma na zaune haushi duk ya isheta har wani better ya ke faɗi tunda an ce za ta ba shi haƙuri to ya cigaba da jira.
Maganar komawarta asibiti Mami ta yi masa ya ce zai kira Ummu Salman za su yi magana ya tambayi ko an dawo da Hanan?

"Ba su dawo da ita ba, in ba su dawo ba za a je a karɓota ai kana dawowa za ku koma Lagos ɗin ko?

Ya amsa da in sha Alllahu ya kara da cewa shima hutunsa ya kare ga yara ma sun koma makaranta.

"Bilkisun fa?

"Tana nan tare da ni."

Ya amsa ma Mami, sannan ya cigaba da faɗa mata daman bayan sun gama biki a garin Abuja Kano ta koma, daga Kanon ne jiya ta zo Daura ta same shi gabaɗayansu tare za su taho nan Adamawa.

Yanzu akwai sakin jiki tsakanin Lamiɗo da Mami, sai su ɗau lokaci suna magana a waya ma ba su sani ba.
Ummu Salma kuma haushi ya turniƙeta, wato ma matarshi na can tare da shi, ita ce ya gasa ma maganganu ya yi tafiyarsa.

Ta ɗauka Mami za ta yanke wayarta ne amma kawai sai ta ga ta miƙa mata tana ce masa ga Ummu Salma ma su yi magana ta karɓa saboda Mami ce, a gabanta ta yi masa sallama ya amsa a ginshiƙe kamar ba zai yi magana ba.

Allah ya taimaketa Mami ta ba su waje, tana fita ko ta yi zaraf ta kashe wayar, saboda ma an ce za ta ba shi hakuri dakyar yake amsa sallamanta.
Ya sake kiran wayar Mami ta ƙi ɗauka baya nan itama ya kirata sau biyu a wayarta ma ba ta ɗauka ba sai hararan wayar take yi tana sakin tsaki ita kaɗai.

Can ba jimawa sai ga saƙon shi.

"Umma Salama."

"Pick the Call."

Ko buɗe sakon ba ta yi ba ta sreen ɗin wayarta ta hango shi kuma ba ta ɗauka ba ko da ya sake kira sau ɗaya daga nan kuma bai ƙara kira ba.

Mami na dawowa ta miƙa mata wayarta ta yi mata ya ce zai kira wayarta su yi magana.

"Yauwa ko ke fa, yanzu maganar kayan gyara za mu yi bari na kira Hajiya Falmata na ji yadda za mu yi"

Da za ta iya da ta ce ma Mami kar ta ba kanta wahala. Ita ta daina yi ma namiji wannan rawan jikin duk ba yan goyo ba ne halin su saya. Nan jaririn Hamma Lamiɗo ne a cikinta wajen haihuwansa ta kusa mutuwa amma bai damu da ita ba har a yanayin yake cewa zai sake ta maza yan kutumar uba ne, ta yadda da maganar hausawa da suke cewa namiji ƙañin ajali. Namiji hankaka gabansa fari bayansa baki, namiji dafin shi ya fi dafin kunama namiji kuma ba ɗan goyo ba ne.
Received at 11:37Reactions: ❤ 7, 👎 1, 👏 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Lokacin da ta auri Habib tana ganin za ta goya namiji, sai ga shi da ta goyasa ga tozarcin da ya biyo baya, a lokacin tana ganin ta gama bama wani namiji yarda amma Hamma Lamiɗo ya mantar da ita wannan har take ganin namiji ɗan goyo ne sai da ya yi mata wannan abin ta fahimci shegu duk halin su ɗaya ta ɗauko ko a cikin maye ba zai iya cewa zai sake ta ba. Kalamansa sun munana a wajenta, tunda kuma ya furta an ce magana zarar buni ce ta fita ba halin ta koma. Tunda maganar nan ta fito daga bakinsa shike nan take ganin baƙin sa.

Tana jin Mami ta kira Hajiya Falmata suka gama magana.
Tana faɗa mata za ta siya mata babban package na maganin sanyi, da na haɗin maijgo a wajen Surayya Halin yau 080322773332
Bojuwa zuwa jibi sako zai iso ta fara amfani da shi kafin su koma Lagos, ta cinye kaza da ciccibinta anan da kayan sanyi, na garin kuma ta tafi da su.

Ta amsa da to kawai, amma a zuciyarta ta ce ba za ta ci ba ko da an kawo. Domin ita a yadda take jin zuciyarta ba za ta iya yin wani abu da sunan wani gyara ba. Lafiyanta take nema da tunanin ma za ta sake ɗaukan cikin? Ko kuma a wannan karon za ta haihuwa lafiya?ga shi dai an yankata sau biyu a waje ɗaya bawa bai isa ya guje ma kaddaransa ba.

Tana tunanin haka sai wata zuciyar ta ce kin manta kin ce ba za ki koma ba? Sai kuma ta amsa ma da kanta za ta koma in dai ya fara yin nadaman kalamansa ya bata haƙuri kuma ya janye su za ta iya yi masa afuwa ta bi shi su koma tare amma in dai bai yi haka ba sai dai kowa ya ga baƙinta ba za ta koma ba.

Ba ta furta ma kowa abin da ke zuciyarta ba. Amma za ta aiwatar da kudrinta sai dai a kore ta a gidan tunda ta fahimci kowa Hamma Lamiɗo yake goyon baya.

Washegari ma kafin tafiyarsu Mami haka ta yi ta mata faɗa, ta daina damuwa saboda halin da take ciki ta ce za ta daina.

Tafiyar Mami sai ya kara sa gidan ya zama shuru ba Faruk ba Islam.
Duk da Mamin ta ce za ta dawo nan ba da jimawa ba.

Mami na tafiya ko sauka ma ba su yi baa direba ya kirata tana da saƙo daga Kano. Ta san saƙon maganin nan ne sai kawai ta tura masa lambar Saddam, ta ce Direban ya kira shi zai karban mata saƙon in sun shigo gari.

Da yamma da Saddam ya shigo gidan yake tambayanta tana da sako ne daga Kano am kira shi ta ce e na ta ne.
Gida ya yi tsit Allahu Akbar babu Baffa ba ta ma san fita tsakar gida saboda sai ta ga kamar za ta gan shi ya fito daga cikin ɗakin shi, ɗakin ma yana kulle ne Ammah ma ba ta son shiga, wataƙila yana tuna mata da Baffa ne.

Ba su da matsalan komai, kayan abinci a store sai ya shekara, kafin tafiyan su Hamma sun ajiye komai, ko ruwa katan katan ne ba adadi ga lemu, sun yi cefane ga kudi masu yawa da suka bari har gobe ma kuɗin da Masarautar Daura ta ba da ko rabi ba a taɓa ba

Daddy ma ya ba da kuɗi mai yawa, haka ma Mami da za ta tafi. Baffa ne kaɗai suka yi rashi amma komai na rayuwa babu abin da babu shi a gidan nan amma gidan kowa ka gani babu karsashi.
Harira ita ke taimaka ma Umma Balki da wasu ayyuka tunda tana da ƙokari sosai.

Ranar monday da safe ita da Harira suka tafi asibiti. Hamma Saddam ya kai su, Hamma Abdulrahim ya tafi wajen aiki.

An yi mata cheekup, babu wata matsala mikin ta ma yana warkewa B.P ɗinta ne dai ya yi sama likita na ba ta shawaran ta daina tunani sannan ta dinga samun ishashen barci, kuma da gaske ne a kwanakin ba ta samun barci sosai ya sake rubuta wasu magungunar suka siya a cikin asibitin kafin su tafi, da ATM ɗin ta, ta yi amfani na Hamma Lamido ba ta taho da shi ba, ba shi kan shi ba duk abin da ya danganceta haushin shi take ji.

Daga asibitin ma tasha Saddam ya wuce suka karɓo saƙo kaya ne mai yawa har na mota Mami ta biya. Baiwar Allah tana son ta, so mara algus Ubangiji ne kawai zai saka mata.
Sai da suka koma gida ta kira Mami a waya ta faɗa mata saƙon ya iso.

"To sai ki fara amfani da shi ai na san jinin ya ɗauke ko?
Mamin ta san jinin ya ɗauke tun sati biyu da haihuwar, amma take sake tambayata ta ji kunya ta kasa amsa mata.

"Kina da lambar mai mganin ko? Ki yi mata bayanin ke ce mai wannan saƙon ta yi miki bayanin yadda zaki yi amfanin da komai."
Received at 11:37Reactions: ❤ 6, 👍 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ta amsa da to, domin ba za ta yi gaddama ba.
Amma yadda Harira ta shigo da ledan ta tura ta can bayan gado ba ta ƙara ma kallon su ba, ballatana ta yi tunanin cire su daga cikin ledan.
Ita abin da ke gabanta ta ga ɗiyarta ta dawo ga shi yau sati amma shuru har wajen yamma ba su dawo da ita ba.

*

Ta damu matuƙa ta ga kuma ba wanda ya damu a gidan
Ammah ce da Umma Balki ta san tana yi musu magana sai faɗa ya dawo sabo daman daƙyar ta samu Ammah ta fara amsa gaisuwanta cikin sakewa.
Bayan ta sake ba ta haƙuri ta nuna nadamarta.

Itama dai daga karshe cewa ta yi ta kira ɗan gold ta ba shi haƙuri ta yanka ƙarya ta ce tuni sun yi magana ma an wuce wajen ahalin tunda ya kira ta ba ta ɗauka ba. Bai sake kiran wayarta ba, itama daman ba niyar nemansa a zuciyarta


Har bayan mangariba shuru haƙurinta ya gama ƙarewa za ta fita ta je har gidan su Habib ai ta san gidan a anguwan Doubeli ne, ko mai zai faru in dai ta dawo da Hanan sai ya faru daga baya.

Ta yi tunanin tafiya ita kaɗai sai ta ga ba mafita ba ne. Ta kira Baɗɗo ita ta ma manta wai suna fushi da juna ne, kamar Baɗɗo ma ba za ta amsa wayar ba sai da ta kusa katsewa sannan ta ɗaga wayar tana amsa mata magana a ciki a ciki.

Tana kan darduma ne daman bayan ta idar da sallar mangariba

"Baɗɗo za ki iya zuwa gida yanzu?

"Me zan yi miki?
Ta amsa mata a yangance

"Raka ni za ki yi wani waje."

"Ina kenan?

"Gidan su Habib, zan je na dawo da Hanan ne yau sati ɗaya ba su dawo da ita ba kuma na ga ba wanda ya damu ballanta ya yi magana."

"Mtsewww
Ba zan je ba, ki je ke kaɗai."

Daga haka Baɗɗo ta katse wayar ta bar Ummu Salma bakinta a buɗe sai a lokacin ta tuna sun rabu ba daɗi yau sati ɗaya kenan, idanuwanta ya rufe ta ma manta da wannan da ta tuna ba za ta kira ta ba

"Ai zan iya zuwa ni kaɗai."

Ta faɗa a fili tana mikewa tsaye darduman da ta yi salla ta ninke, ta ɗau karamar jakarta a saman madubi ta ɗauki kuɗi duk wanda ya tambayeta za ta faɗa masa in da za ta je ba amfanin kuma ɓoye ɓoye.

Hijabin jikinta take sauyawa, ta ɗauko gogagge a cikin wardrope.
Ta ji ana amsa gaisuwa a falo kamar wasa ta ji Ammah na kira sunan Hanan itama ta ji karaɗin muryanta.

Da sauri ta nufi falon, tana zuwa ko ta ga Hanan a jikin Ammah sanye da doguwar riga na atamfa ba ma cikin kayanta ba ne har sabon kitso an yi mata ga wata leda a hannunta sannan ga wata teedy na wasa a ɗayan hannun nata.
Umma Balki na ta cewa maraba da Hannatu.
Shamsiya na zaune a ƙasa da hijabi a jikinta gabanta kuma jakar kayan Hanan ɗin ne da suka tafi da ita.

"Hanan. "

Ta kira sunan ta da wani irin farinciki, a muryanta.

Hanan ta juya ganin uwarta, da gudu ta tashi daga jikin Ammah ta nufe ta, da murnan ganinta.
Tana zuwa Ummu Salma ta duka ta ɗaga ta sama.

"Hanan sai yau?

Ummu Salma ta tambayeta tana dariyan farinciki dariyan da tun tafiyan Hanan ba ta yi irin shi ba.
Ammah da Umma Balki na bin ta da kallo har da Shamsiya dake ta mirmishi.

"Mahma Anty ta kai ni kiso "

Ta ke faɗa tana nuna mata kanta, ta sha cuko duk an bishi da duwatsun yara.

"Abba ya siya mini Baby."

Ta sake faɗa tana mata Teddy dake hannunta.

"Anty ta siya mini sweet."

Wannan karon sai da ta nuna Shamsiya sannan ta ciro sweet da yawa daga cikin ledan hannunta. Haushi ya kama Ummu Salma Anty, Shamsiyar ce Anty kenan Habib Abba. Takaici ne kawai ke murkurkusanta amma ganin Hanan sai kamar ana rage mata zafin zuciya.

Cewa kawai ta yi ta gani da fatan ta ce musu ta gode ta ɗaga kanta.
Sauketa ta yi ta nufi Ammah tana nuna mata sweet ɗin hannunta ta ba ta, Umma Balki ta ce itama a ba ta nata sai ta ɗibo biyu ta ba ta.

"Son kai, na kakarki ya fi nawa yawa."

Ta faɗa tana dungure ma Hanan din kai ta ko maƙale kafaɗa kamar ta san abin da ake yi.
Ammah na mirmishi, Umma Balki na fadin yarinyar nan akwai wayau.

"Sosai kowa fa mamakin wayaun ta yake yi ga zence a bakinta haka Babanta ya ce wayanta ya girmi shekarunta."

Shamsiya ta amsa tana mirmishi.
Ammah ta amsa da cewa Hannan ai akwai magana.

Ummu Salma na tsaye tana jin Shamsiya na ba da haƙurin ba su dawo da Hanan da wuri ba
Received at 11:37
4 people reacted with ❤
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
"A yi haƙuri babanta ne ya ce a ɗan tsaya ya samu kuɗi ya yi mata y'an siyayya."

Kallon ta kawai Umma Salma ke yi in ta ce babanta sai ta ji zuciyarta ta yunkuro.

"Ba komai, ai da yake ma baban nata na nan bai dawo ba. Sai ya dawo ne za su tafi."

Umma Balki ce ke bayar da amsa. Shamsiya ta ce sun gode sosai Habib ya na kofar gida ya ce a miƙa masa godiyar sosai.
Ammah da Umma Balki suka ce ba komai

"Da yake a can Lagos ɗin take makaranta amma in sun samu hutu su ka zo za a dinga kawo ta in sha Allahu."

Bakin Shamsiyar har kunne tana ta godiya.
Hanan kuma har ta fita tsakar gida in da Harira ke zaune a saman tabarma.

Ummu Salma ta juya za ta shiga ciki sai Shamsiya ta miƙe ta ce tana son za ta yi magana da ita.
Ko amsa ta ba ta yi ba, ta wuce ciki yanzu kam hankalinta ya kwanta magana kuma babu sauran wata magana a tsakaninsu a yanzu.

"Bita ciki mana."

Umma Balki ta yi ma Shamsiya magana sai ta ɗaga kafa ta bi bayan Ummu Salma har zuwa cikin ɗakin da ta san na Umma Salma ne tun tana budurwa ɗakin da ta kan zo su yini suna hira. Amma yau ɗakin ya zama baƙon ta.

Lokacin da ta shiga Ummu Salma na tsaye a gaban madubi kuɗi ta mayar a cikin jakarta sannan ta koma ta zauna a gefen gado ko kallon Shamsiya ba ta yi ba.

Ita kuma a ɗarare take, ta kasa zama tana tsaye daga jikin ƙofar ɗakin.

"Umma Salma."

Ta kira sunanta a sanyaye.

Ta kalleta amma ba ta amsa ba.

"Daman ina so na sake ba ki haƙuri kan abubuwan da suka faru a baya ne."

Sai ta ɗan dakata ta jan fasali tare da kallon yanayin Ummu Salman.

"Don Allah ki yi haƙuri ki manta baya, Hanan ta riga ta haɗa mu ba yadda muka iya."

Wani kallo Ummu Salma ta watsa mata amma ba ta yi magana ba.

"Ba don ni ba don Allah, ki yi ma Hanan kara ki ba ni lambar wayarki "

"Saboda mene? Na ce na yafe ba buƙatar haka."

Ummu Salma ta faɗa tana kallon ta.

"Akwai bukata mana, saboda mu dinga gaisuwa da ke da Hanan gabaɗaya."

"Don Allah."

Yadda take yi mata magiya ya sa taka sa musa mata.
Ta fara karanto mata lambar Shamsiya na lodawa a cikin wayarta.

"Na gode sosai."

Ta faɗa hawaye na taruwa a cikin kwarmin idanuwanta.

"Ko da ba za mu koma da amintar mu ba. Don Allah ki daina jin haushina."

Ta kalleta amma ba ta yi magana ba.

"Zaman Hanan tare da mu na kwana bakwai kamar shekara bakwai ne a wajen mu, ta wanzar mana da farinciki sosai yan'uwa sun ganta kowa ya yi murna. Habib na son yara an jarabesa nima ina son na haihu ga shi da kamar wuya tunda ko na samu cikin baya kai labari yake ɓarewa."

Ta gama faɗa tana sharan kwalla.

"Don girma Allah kar ki yi mana katanga tsakanimmu da Hanan, har abada taki ce ba wanda zai raba ki da ita. Amma muma ki yi mana alfarman aron ta na wani lokaci duk sadda damar haka ya zo"

Ummu Salma ta kalleta yadda take hawaye sai ta ba ta tausayi.
Ta san ya zafin ka ɗauki ciki ka rasa shi yake.

"Ba damuwa."

Yadda Shamsiya ke yi mata godiya kamar ta ba ta duniya.
Nan take ta kira ta a waya sai ga lambar Shamsiyar ta fito ita ce dai lambarta tun na baya tana ganin lambobin ta gane sun yi amimta har ya sa ta haddace lambar Shamsiyar a lokacin baya.

"Ga lambata nan ki yi saving don Allah."

Ummu Salma ta ce za ta yi, Shamsiya ta yi mata sallama da cewa za ta tafi Habib na can kofar gida yana jiran ta.

"Ki gaida gida."

Kawai Ummu Salma ta iya cewa.
Sai Shamsiya ta ɗan waiwaya tana kallonta.

"Habib ya ce na sake ba ki haƙuru."

"Ya wuce"

"Mun gode sosai."

Har ta juya za ta fita Ummu Salma ta kira sunanta.
Ta juyo tana amsawa.

"Ke ma Allah ya ba ki haihuwa"

"Amin na gode sosai."
Ta amsa hawaye na kace mata. Da a ce baya za ta dawo da watakila suna nan da ƙawancen su da Ummu Salama amma yanzu abubuwa sun sauya har abada ba za su taɓa komawa kamar baya ba

Haka ta fita falo ta yi ma su Ammah Sallama a tsakar gida ta ga Hanan ta yi mata Bye bye ta ga Harira sai ba ta damu da Shamsiyar don za ta tafi ba haka ta fita tana waigen Hanan kamar ta sake ɗaukanta su koma tare

A ƙofar gida ta ga Habib jikin get ɗin in da ta bar shi yana jiran ta.

"Na fito"
Received at 11:37
8 people reacted with ❤
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ta faɗa tana yin gaba ba ta so ya ga tana kuka shi kuma ya riga ya gani.
Bayanta kawai ya bi, shima yana ji kamar ya koma ya ɗauko Hanan amma babu daman haka, kwaannta bakwai tare da su amma kamar shekaru haka yake kallon kwanki nan. Kwana bakwai kawai ta shiga ransa yarinyar nan da zai iya ba da komai saboda ya kasance da ita rayuwarsa a cikin kwana bakwai ta yi sauyi mai yawa a cikin kwana bakwai kawai ya tsinci kansa cikin tsananin farinciki.

Hanan ga hira sannan Bakuntar kwana ɗaya zuwa biyu ta yi musu daga nan ta saki jikinta. Shamsiya tana son Hanan ta shiga ranta sai ya ji da yana da iko da ya ba ta rijon Hanan na har abada amma ina ya rasa wannan damar na shi a matsayin shi na uba tun lokacin da ya furta baya son cikin nan yanzu kuma bayan an haifi ciki ba shi hurumin yanke wani hukunci sun gode ma da aka ba su damar sanin akwai Hanan da ba su damar zaman da ta yi da su har na tsawon kwana bakwai amma ji yake yi kamar jiya ne ta zo yau za ta koma ƙunci yake ji a zuciyarsa na kewar Hanan
Haka ma Shamsiya, har suka hau adaidaita ba ta daina kuka ba

Bai ce mata komai ba sai da suka koma gida ta shiga ɗaki ta kwanta a saman gado tana ta kuka.

"Cewa suka yi ba za su sake kawo mana ita ba?

"Aa Ammah ta ce in dai suka samu hutu suka zo garin za su kawo ta."

Ta faɗa tana share hawayenta.

"To kuma mene ne na kuka? Hakuri za mu yi gabaɗaya."

Ya faɗa yana zama a gefen gadon.

"Kukan nadama nake yi, da a ce ban ci amanar ƙawata ba da kaddaran rayuwata bai fara ba. Da kana tare da matarka da Hanan har ma da wasu yaran cikin farin ciki. Nima da watakila na yi aurena ina tare da mijina da ya'yana cikin farinciki."

Sai ta ba shi tausayi ya dafa hannunta yana faɗin.
"Haka Allah ya so, sai mu yi hakuri mu ce mun gode."

Hawayenta sun ƙi tsayawa shi ke share mata yana lallashinta.
Ce mata yake yi ai mun tuba, tubar mu zai saka Ubangiji ya ba mu abin da muke so
Hanan kuma tana tare damu har abada.



*Janafty*
Received at 11:37Reactions: ❤ 5, 👍 2
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Baɗɗo ma ta daɗe ba ta yi fushin ba itama ba ta ga laifin da ta yi mata ba, akan gaskiyanta take ai ta san fushi ta yi domin tun ranar ba ta dawo kuma ba ta kira ta a waya ba, itama ba ta kira ta ba.

Tunda Baffa ya rasu ta rasa jarrinta taurin zuciyarta ya karu ba ta jin taushi taushi, ta san tana da taurin kai a baya amma yanzu ya yi ƙamari tana ji ko za a yi tashin ƙiyama ne ba ta yarda a ce ita ce ke da laifi ba shi ya sa ko kaɗan zuciyarta ba ta rusuna ba.
Wanda zai yi fushi da ita ya daɗe bai yi ba.

Tafiyar Hamma Jibo da iyalansa sai gida ya yi shuru.
Hamma Abdullahi daga kai su filin jirgi ma bai dawo ba, Saddam kuma ya fita Hamma Abdulrahim ne kawai muka yana bangaren su.

Harira ta shigo ta gaisheta tana tambayanta ko akwai abin da za ta yi mata, yan zannuwanta da take sawa da dogayen riguna ta ce ta kwashe ta ɗan wanke mata. Bayan fitan Hariran ne Mami ta shigo ɗakin ta ba ta waya Daddy ne ya yi mata ya jiki suka gaisa shi yake faɗa mata ba zai samu zuwa ba tafiya ta kama shi zuwa Lagos amma gobe Mami da su Islam za su bi jirgi su koma Kaduna tunda duk sun koma makaranta.

Bayan sun gama wayar ne ta miƙa ma Mami wayarta.
Ta karɓa tana kallon ta kur kamar tana nazarinta, ita kuma tana kwance ne daman lokacin da Mami ta shigo sai ta ɗan zauna a saman gadon ta cire hijabin jikinta doguwar rigar atamfar dake jikinta ta bayyana kanta akwai hula amma ana ganin gashin ta, a tsefe yake ta so ne in suka zo nan a yi mata kitso to ba kwanciyar hankali, ga rasuwar Baffa ga abin da ya same ta, gashin duk ya yi biji biji.

Mami ta faɗa mata cutar da ya kamata, har goggle ta yi na cutar ta yi daga nan ta san tana da sauran kwana a gaba ne, amma cutar tana da hatsari ga mata masu ciki.

"Yaushe ne za ki koma ganin likita?

Mami ta katse shurun da ya gifta a tsakanin su, itama yanzu Ummu Salma ba ta mata hira in ba ita ce ta tsare ta da magana ba.

"Ranar monday ne jibi."

"Kuma ga shi gobe za mu tafi, ke da wa za

Please Login or Register in order to submit comment