Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi kamar saukar dalma, ta yi saurin goge su a jikin shaddar jikin Lamiɗo dakyar hawayen suka fita amma zafin su ya fi  zafin zaman su a zuciyarta tana hana kanta kuka ne saboda in ta yi kuka za ta iya mutuwa ko ta haukace saboda rashin sanin abin da za ta yi gwara ta bar komai a zuciyanta yafi mata sauƙi akan zafin fitan hawayen nata.

Shi ya lallashi Ammah aka kawo tuwo miyar ganye ya takura mata ta ɗan ci kaɗan ba da yawa ba ta haɗa da ruwa. Kowa ya jinjina ma ƙaunar dake tsakanin Ammah da Lamiɗo.
Ya sanyata ta ci Abinci kuma ta yi masa yadda yake so.

Mami ma ya shiga wajenta tana cikin ɗakin Ammah zaune saman darduma in da ta yi salla da hijabi ta haɗa kai da gwiwa tana kuka.
Ya daɗe da shigowa ɗakin ba ta sani ba sai da ya durƙusa a gabanta ya dafa kafaɗanta sannan ta dago fuskarta da idanuwanta jajir alamun dai ta sha kuka.

Tare da Hajiya Falmata suke zaune a ɗakin shigowar Lamiɗo ya sa ta tashi ta fita ta ba su wuri.
Ita kuma ta ɗauka ma Falmatan ne sai ta ga wanda ba ta yi tunani ba.

Gaishe ta ya yi ta amsa tana ɗan kauda kai tana ɗauke hawayenta.

"Mami ki yi haƙuri ki daina kuka haka nan."

"Allah ne ya bamu Baffa kuma shi ya karɓesa daga hannunmu, muma mutuwar nan muke jira Mami, ki daure ki daina wannan kukan kar ki samu wata matsalan"

Ya faɗa a sanyaye yana kallonta
Kawai sai ta kalleshi ta girgiza kai lokaci ɗaya ta fashe da kuka.
Daddy na nan bai koma ba yana tare da su Baffa Umaru sune manya masu karɓan gaisuwa.

Kukanta ya sake raunana masa zuciya kuka take yi har da sauti

"Lamiɗo na rasa Baffa kuma sai ka ce na daina kuka."

"Baffa ne uwata Baffa ne ubana, shi ne dangina gabaɗaya ba ni da kowa sai shi. Yau babu shi Muhammadu yau na rasa Baffa ya zan yi in ban yi kuka ba?

Take faɗa cikin gunjin kuka lokaci ɗaya tana riƙe hannayensa.

"Baffa shi ne gata na, wallahi shi ne gata na, na rasa gata na."

Take faɗa tana jijjiga hannayensa cikin gunjin kuka.
Ya rasa yadda zai yi mata kukan ta ya fara yawa.

"Ki yi haƙuri Mami ki daina kuka."

"Lamiɗo yanzu shike nan Baffa ya tafi ya barmu?
Sai ta sake fashewa da kuka.

"Tun iyayenmu na da rai Baffa ke amsa matsayin Uba a wajena. Lokacin da Gwaggo ta rasu Baffa ya so ya riƙeni amma aka hana shi riƙona lokacin da na koma Daura duk abin da Baffa ya samu sai ya raba shi da ni ya aiko mini da nawa. Baffa ya damu da rayuwata ya tattaleni ya mini dukkan gata. Lokacin da mahaifinka ya sake ni da a ce ba ni da Baffa da yanzu na mutu da yanzu ka mutu Lamiɗo. Baffa ne ya ba ni bayan shi na jingina Ammah ta ba ni Hannunta na kama, suka rumgume mu tare suka cicinɗa rayuwarmu Lamiɗo, Baffa ne gata na, na rantse da wanda raina ke hannun shi Baffa kaɗai nake da shi a duniya ta ya ba zan yi kuka ba."

Maganganun da take yi kamar ma ba a hayyacinta take yi ba jin ta kawai ta yi yi a cikin jikinsa ya rumgumeta.

"Na rasa Baffa. Na rasa farincikina na rasa gata na."

Take faɗa tana rumgume da shi cikin kuka.

"A'a bayan Baffa Ammah nan nan muma muna nan za mu taɓa bari ku yi kukan maraicin Baffa ba."

Yake faɗa yana ɗan tapping bayanta alamun lallashi.
Amma Mami kuka take yi kamar ranta zai fita.
Received at 09:59Reactions: 😭 5, ❤ 3, 👍 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
"Baffa ya sha ce mini Fatima ki yi haƙuri wata rana sai labari. Baffa ya sha ce mini Fatima duk abin da ya faru dake ki ɗauke shi kaddara watarana komai zai wuce komai ya wuce Baffa ya yi gaskiya amma me ya sa tare da shi komai zai wuce ɗin me ya sa?

"Ubangiji ne ya fi mu son shi, shi ya sa ya ɗauke shi daga cikin mu."

"Da ni mutuwan nan ta ɗauka da ta sani ta bar Baffa.."

"Aa Mami kar ki yi saɓo don Allah."

Da a ce zai iya yin kuka da ya koka. Amma shima ɗin ya kasa sai da tafafarsan zuciya.
Yau ne rana ta farko da hankalin shi ya taɓa jin Mami a jikinsa.
Ko hannun juna a matsayin uwa da ɗa ba su taɓa kamawa ba sai yau.

Ita uwa ta dabam ne, wani irin yanayi ya ke ji yana lulluɓeshi, wani irin abu a ƙasan zuciyarsa yana motsi.
Sun fi mintina biyar yana lallashin Mami tana ta kuka gwanin ban tausayi.
Sannan ya ɗago ta ya share mata hawaye.

"Ki yi hakuri Mami, bayan kin rasa Baffa kina damu in sha Allahu ba za ki yi kukan maraicin Baffa ba."

Yana share mata hawaye wasu na taruwa.
Amma ta rage sautin kukan na ta.

"Tsakanin mu da Baffa alheri ne. Addu'a kawai za mu dauwama muna yi masa."

"Allah ya jiƙan Baffa Allah ya gina masa gida a aljanna saboda yadda hidimta mini, Ubangiji ya albarkaci bayansa."

Mami ta gama faɗa tana mai tsiyayan hawaye sannan ta saka gefen hijabinta ta share Lamiɗo na ta ya ta sharewa da hannayensa.
Ta bi hannayensa na sa da kallo zuciyarta ta yi nauyi amma ta kasa magana.
Fita falo ya yi ya ce a kawo ma Mami abinci sannan ya koma ciki bayan an kawo da kan shi ya zauna yana ba ta a baki kamar yadda ya yi ma Ammah tana karɓan abincin tana tsiyayan hawaye.

Har sai da ta ce ya bar shi haka ta ƙoshi.
Ya ba ta ruwa tasha, ta riƙe hannayensa.

"Allah ya yi maka albarka Muhammad. ubangiji ya albarkaci zuru'anka. Na gode sosai."

Take faɗa tana hawaye, yau dai ta faɗa ta sanya masa albarka a sarari

Sai da ya yi mirmishi sannan ya amsa da Amin Amin a ƙalla dai yau ya ji Mami ta kalle shi ta yi masa godiya kuma ta sanya masa albarka.

"Ka tashi ka tafi wajen Ɗiyata. An ce itama ba ta ci abinci ba."

"Yanzu zan shiga wajenta Mami."
Bai bar ɗakin ba sai da ya tabbatar ta daina kuka.
Ya fita ta bishi da kallo sannan ta girgiza kanta.

"Allah ya yi maka Rahama Baffa."

Ta furta tana mai tsiyayan ƙwalla.
Akwai mata a falon Ammah yan anguwa da suka shigo gaisuwa sai kawai ya fita.
A tsakar gida ya ga Bilkisu kamar ta gama waya ne ta gaishe shi ya amsa.

"Ya haƙurin mu?

"Mun gode ma Allah."

"Allah ya jiƙan shi"

Ya amsa da Amin in da Umma Salma take ya tambayeta sai ta nuna masa ɗakin Baffa lokacin an yi mangariba amma gidan tunda akwai nepa ko'ina ya da wadatu da haske.
Bilkisu ta bishi da kallo har ya shige ajiyar zuciya ta sauke, ita ko kallon fuskarta ma bai yi ba yafi damuwa da Umma Salma a kanta zuciyarta ta cika da kishi.
Jibi za ta wuce Abuja daman bikin sai wannan satin ne tuni wasu daga cikin yan'uwanta yau sun tafi Abuja itama ba domin wannan rasuwar ba da yanzu tana can ta kasa komawa ciki saman tabarman dake tsakar gidan ta zauna hankalinta na kan kofar ɗakin Baffa kamar ta yi tsuntsuwa ta shiga ta ga abin da ke faruwa. Mutuwa dai an san da zafi amma sai take ganin kamar makirci ne ka ƙin cin abinci Ummu Salma sai an ta so kamar Lamiɗo ya zo yana lallasheta.


Lokacin da ya kira ta a jiya ya ce ta duba masa Ummu Salma taƙaici kamar ya kasheta ba ta je ba kawai cewa ta yi to, can da ya sake kira ta ce ai taje lafiyan ta lau. Tana jin sa har numfashi ya sauke haushi da kishi suka sanya ta kashe wayarta ko sallama ba ta yi masa ba.

Tana ganin yadda Gimbiya Shahida ke kafa kafa da Ummu Salma kar wani abu ya same ta. Ita ko kallo ma ba su isheta ba. Saboda kawai tana da ciki? Kafin Ummu Salma ta yi ciki ta haihu ita ta fara yin cikin Lamiɗo kuma ta haifa masa yara har biyu amma ta fahimci an fi murna da abin da ke cikin Umma Salma.
Received at 09:59Reactions: ❤ 17, 😭 2
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Nadama take yi, nadaman me ya sa ta tun farko ba ta shiga ta fita ta raba Lamido da Ummu Salma ba, yanzu lokaci ya ƙure mata in ma ta ce za ta yi wani abun darajanta ne da ƙimanta zai yi kasa. Amma har abada ba za ta taɓa son Umma Salma ba, ba ta da maƙiyiya sama da ita. Domin duk macen da za ta yi tarraya da abin da take so ta zama maƙiyiyarta. Tana zaune tana hararan ɗakin barin ma da ta ga Baɗɗo ta fito kenan su kaɗai ne a ciki. kishi da baƙinciki sun mantar da ita rashi ne mai girma ya samu Ummu Salma tana buƙatar lallashi.

*

Lokacin da Lamiɗo ya yi sallama a ɗakin Baffa Baɗɗo ce kawai a ciki.
Itama saboda kar a barta ita kaɗai ne su Adda Suwaiba suna waje suna wanke wanke n kwanukan da aka ɓata.

Ta gaji ma da lallashinta ta haƙura ta ƙyaleta.
Sai ga Lamiɗo ya shigo ta miƙe da sauri tana gaishe shi ya amsa sau ɗaya ba tare da ya kalleta ba.
Ficewa ta yi domin ta ba su wuri ya zo a daidai domin daman tana tunanin ta aika can haraba a kira shi wataƙila in ya zo a samu Ummu Salma ta daina kuka ta ci abinci.

Tsaye ya yi a saman kanta tana kwance a saman gadon Baffa ta juya baya ta dunƙule a waje daya kamar wata yarinya.

Tausayinta na tsirga masa, mata uku mafi muhummanci a rayuwarsa yau suna cikin damuwa suna kuka, kukan da ba zai iya hana su ba tunda abin kuka ne ya same su

Ya duƙa a gaban gadon yana kiran sunanta amma ba ta amsa ba.
Ya sanya hannu ya juyo da ita tana fuskantar shi.

Kuka take yi, irin kukan zucci nan mai tahowa da hawaye.
Sai kawai ya miƙe ya hau gadon ya tarairayota daƙyar yana nishi domin ta saki jikinta ya ɗora ta a saman cinyarsa.

"Why?

"Ummu Salama Why?

"Kin manta halin da kike ciki ne?

Ya faɗa yana kallonta lokaci ɗaya yana shafa cikin jikinta.

Fashe masa da kuka ta yi domin ta rasa ma abin da za ta ce.

Baffa ne fa ya rasu, ba ta tunawa da kanta ma a wannan halin da ta ke ciki.
Rumgumeta ya yi ƙam ƙam a cikin jikinsa yana ɗan tapping ɗin bayanta alamun lalallashi bai hana ta ba ya ba ta lokaci duk ta ɓata masa shadda jikinsa da kuka da majina.

"Shii is Okay."

Sannan ya ɗago fuskarta ya tallabeta yana faman goge mata hawaye.

"Ya isa ki daina kuka."

"Hamma."

Ta kira shi da muryanta da ba ta fita.

"Hamma ya zan yi? Kaina kamar zai fashe."

Ta gama faɗa tana kama kan na ta, da hannu bibbiyu.

"Subhanallah kin ga abin da nake tsoro ko? Tun yaushe ya fara miki ciwo?

"'jiya."

Ta amsa mishi tana hawaye
Wani irin yanayi take ji da ba ta taɓa jin irin shi ba Hamman ma dake gabanta ba ta iya ganin shi sosai ta ƙura masa idanuwana amma duru duru take iya ganinsa.

"Hamma"

"Yes"

"Bana ganin ka sosai."

Ta faɗa a daburce tana kallonsa.

Ya kalleta cikin mamakin kalamanta, sai dai ganin numfashinnta na sarƙewa ne ya sa ya ruɗe.

"Ummu Salama what wrong with you.?

Hannunta ya riƙo sai ya ga hannun ya kumbura kuma a jiya da suka taho ba haka hannunta yake ba a ruɗe ya kai kallon shi kan kafafunta ya ga suma sun kumbura.

Fuskarta ya bi da kallo ya ga tana ta fama da sarƙewa numfashi.
Ya ruɗe yana ta kiran sunanta ta kasa amsawa tana so ta yi magana ta kasa.
Tana irin jan numfashi da ƙarfi jikinta na shaking yadda yake kiranta da ƙarfi ne ya sa mutanen dake tsakar gida hankalinsu ya faɗa kansu, Baɗɗo na gaba wajen rumtumawa zuwa cikin ɗakin har da Bilkisu.

Halin da suka ga Ummu Salma suma ya ba su tsaro.
Bilkisu ta ƙarisa tana duba Ummu Salma.

"Ta ce kanta na ciwo, sannan ta ce ba ta ganina yanzu kuma ta kasa numfashi."

Yake faɗa cikin ruɗewa.
Bilkisu ta ɗaga hannunta ta ga ya kumbura ga sarƙewan numfashi ga shi ta ce ba ta gani sannan tana wani kakkafewa jikinta na mimmiƙewa.

A ruɗe ta kalli Lamiɗo yadda yake a firgice itama ta ɗan firgita.

"Lamiɗo a tafi asibiti da gaggawa."

"Eclampsia. Antepartum Eclampsia. Is accurs before delivery"
Bai gane ma bayaninta ba ya sa ta sake kallon shi.

"Tsinkau tsinkau in hausa. A tafi asibiti da gaggawa domin a cire abin da ke cikimta in ana so ta rayu."
Received at 09:59
13 people reacted with ❤
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ba ta ma gama rufe baki ba ya sunkunci Ummu Salma ya yi waje da ita ba takalmi a kafarsa haka ya fita da ita haraba. Baɗɗo ta ruga falon Ammh tana kuka tana faɗa musu abin da ke faruwa Mami na cikin ɗaki ta rumtuma ta fito tare da Gimbiya Shahida da su Umma Balki Ammah na zaune ba ta motsa ba.

Haka suka bi bayan Lamiɗo har haraba tuni har ya saka ta a motar Abdulrahaman. Domin yadda ya fito a gigice ga Umma Salma a hannu kowa ya san ba lafiya.
Hamma Kabiru ne ya yi saurin shiga bangaren tuki Abdullahi ya zauna a gefensa kafin su Mami da su Baɗɗo su ƙariso tuni har sun yi riverse da yake get ɗin a bude yake suka fice da gudu.

Daddy ne ya ce ya kamata mata su bi bayan su.
Adda Nauwara ce ta ce ba takalmi ma a kafar Lamiɗo Hamma Saddam ne ya shiga gida ya ɗauko masa.
Mota biyu suka yi Hamma Jibo ya tuƙa su a motar Abdulrahim sai kuma shi Saddam ya tuƙa su a tashi motar.

Mami da Hajiya Falmata ne sai Umma Balki sai Baɗɗo da Adda Nauwara sai Gimbiya Shahida da Abdulrahim da Saleem suka bi  bayan su ba ma su san asibitin da suka je ba sai da suka kira wayar Hamma Kabiru shi ya faɗa musu private hospital ne da sunan asibitin suna zuwa suka same su a bakin emargency haka kuma kafar Lamiɗo ba takalmi sai da Hamma Saddam ya miƙo masa takalmin sannan ya farga da babu takalmi ma a kafarsa.

An shiga da Umma Salma ciki ba yadda take domin a lokacin ma har ta fara jijjiga.
Ba ɗadewa likita ya fito ya ce ina mijinta Lamiɗo ya isa gare shi.

"Matarka na ciki haɗari, Eclampsia ya kama ta sakamakon jininta ya haura sosai 270 ga ciki a jikinta in za mu ceto ta ya zama dole mu cire cikin dake jikinta. Ku sanya mana hannu a wannan takardan sannan kuje ku biya kuɗin aiki."

Ba Lamiɗo kaɗai kowa a wajen nan ya firgita
Hannunsa na rawa ya karɓa takardan ya zura hannu aljihunsa ya laluba ya ɗauko wallet ɗinsa tuni har Hamma Kabiru ya wuce wajen biya.

"Hamma Kabiru ya tafi ya biya kuɗin ."

Saddam ya faɗa cikin tashin hankali shekaranjiya ne Baffa ya rasu amma yau sun kara fuskantar wani tashin hankalin.

"Cikin ya isa haihuwa ne?

Hamma Jibo ke tambaya.

"Wata bakwai ne da kwanaki."

Mami ta amsa tana tsiyayan hawaye

"Allah ya dube ki Ummu Salama."

Kowa jikinsa a sanyaye, ana biyan kuɗin aka shirya yi ma Umma Salama tiyatar gaggawa.
Suna asibtin nan har goma na dare.

Sai dai mazan sun fita sun yi salla. Adda Nauwara ce ta ɗauko waya ita ta kira gida ta ce a sanya Auta a cikin addu'a tana cikin haɗari.
Karfe goma da rabi aka gama yi mata tiyata.

Likita ya fito ya sanar da su an ciro jariri amma an saka shi a kwalba saboda ya yi ƙanƙanta
Ita kuma Umma Salma za a yi obsarving ɗinta 48hours daga lokacin ta farka lafiya lau in sha Allahu za ta fita daga cikin hatsari.

Sun samu salama kaɗan da hamdala. Lamido ne kawai da Hamma Kabiru aka bar su, suka shiga ɗakin jariran nan suka ga mai sunan Baffa ɗan cukili da shi a cikin kwalba. Ummu Salma kuma tana cikin wani ɗaki na musamman sai ta farfaɗo sun tabbatar da ba ta cikin hatsari sannan za a kawo ta ɗakin da za ta huta har a samu ganinta.

Sha biyu na dare suka bar asibitin Mami aka bari da Baɗɗo za su kwana tare da Umma Salma. Sauran kuma suka koma gida.
Da asuba likita ya zo ya sanar da su jaririn da suka ciro ma Umma Salma Hadi Allah ya yi masa rasuwa.

Mami tana hawaye tana ta kabbara daman jiyan ita da Baɗɗo ba su runtsa ba.
Ana cikin wani rashin ga shi an sake yin musu wani da Baffa da mai sunan Baffa duka Ubangiji ya karbesu.

"Allah ya sa mai sunan Baffa ya yi ceton mu ranar gobe ƙiyama. Umma Salma kuma Allah ya ba ki lafiya."

Baɗɗo na amawa da Amin tana hawaye ta san yadda zuwan wannan yaron ya zama abin kirgawan kowa ashe ba mai zama ba ne jiya ya zo duniya yau kuma ya koma ga mahallincinsa

Ba waya a hannunsu, sai da Mami ta karɓi ta wata nurse ta kira Daddy ta ce ya sanar da Lamiɗo jaririn Umma Salma ya koma cikin dare.
Received at 09:59Reactions: ❤ 11, 🔥 1, 😁 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ranar yinin uku da rasuwar Baffa aka wayi gari da wannan rashin na jaririn Ummu Salma.
Lamiɗo ya damu domin har damuwan ta bayyana a saman a fuskarsa.
Sun gama tsara na su Ubangiji ya gama na shi tsarin. Da safen suka tafi asibitin duka mazan suka yi cike cike sannan aka ba su gawar jaririn sak Lamiɗo kamar ya yi kaki.

Lamiɗo ya miƙa ma Mami shi a cikin zanin Ammah da suka taho da shi daga gidan ta kalli jaririn ta rumgume shi.

"Allah ya sa ka cece mu"

Aka amsa da Amin Baɗɗo ma ta leƙa shi ta ganshi tana hawayen tausayin ƙawarta sannan Hamma Kaburu ya karɓe shi ya ce za su je a yi masa wanka da salla tunda ya zo da rai.

"Allah ya sa ya cece mu. Amma ku ɗau hotonsa saboda Ummu Salma."
Mami ta faɗa tana sharan hawaye.

Suka amsa da in sha Allahu Lamiɗo tuni ya fita ma haraban asibitin ya kasa ma tsayawa tunda ya ga jaririn komai ya kwance masa ga Ummu Salma da ake jiran farkawanta.
Sun gode ma Allah kawai domin ya jarabesu a lokaci ɗaya da jarabawowi masu zafi da radaɗi.



*Janafty*
Received at 09:59
4 people reacted with ❤
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
*FJ littafin kuɗi ne 1k a manhajar Telegram tura kuɗin karatu ta wannan acct ɗin 9069067488 Opay Jamila Umar shaidar biya ko tuntuɓa ta waɗannan lambobin.*
08032773332
09069067488.

A ranar da aka yi addu'an rasuwar Baffa kwana uku a ranar aka sallaci jaririn Ummu Salma aka yi masa salla sannan aka kai shi maƙabartan da aka rufe Baffa shima aka rufe shi, sai dai ba ma a layi ɗaya ba ne bayan rasuwar Baffa mutanen da suka mutu aka zo aka binne su ba su da adadi jama'a ana mutuwa fa sai dai kawai fatan mu Allah ya sa mu yi kyakyawan ƙarshe.

Zaman gaisuwan sai ya zama biyu, duk baƙin da suka zo daga baya sai dai su ji Umma Salma na asibiti ta haihu jaririn bai zo da rai ba. Mami da Baɗɗo na asibitin har yamma lokacin da ta farfaɗo ba kuma wanda suka bari ya sake ganinta sai da suka tabbatar da ta fita daga cikin haɗari sannan aka kawo ta ɗaki na musamman.

Likita ya ce za su kula da ita saboda daidaitawar jininta eclampsia ya sake ta amma tana buƙatar kulawa ta musamman sannan ga mikin aiki a tare da ita. Sun shiga sun ganta tana barci domin likita ya ce tana buƙatar hutu sosai saboda jininta ya yi ƙasa sannan ba su son cikowar mutane saboda yanayin mai jinyar.

Ummu Salma ta rame duk ta zabge Mami da hawaye ta fito haka ma Baɗɗo ita kawai tunanin ta yadda Ummu Salma za ta ji in har ta dawo hayyacinta aka ce jaririn cikinta ya koma. Ubangiji ne shi ne mai tsara gaskiya mu bayinsa duk ƙarya muke tsarawa duba da yadda duk aka gama shirin zuwa wannan jaririn duniya har suna an raɗa masa ashe ko yazo duniya shi ɗin ba mai zama ba ne.

Ummu Salma ta tsallake rijiya da baya, eclampsia ce ta kamata ma'ana ciwon tsinkau tsinkau kamar yadda muka sani a hausan ce.

Shi ciwon Eclampsia(Tsinkau-Tsinkau) cuta ne da ke da hatsari kuma hatsarinta shi ne tana kama masu juna biyu ne.
Sanadinta kuma hauhawar jini in ya haye ƙwaƙwalwa shike nan sai mace mai juna biyu ta shiga cikin hatsari in ba a yi gaggawan kai ta asibiti ba za a iya rasa ta tare da abin da ke cikinta.

Alamomin cutar Eclampsia su ne; Ciwon kai mai tsanani  kumburin kafafu ko hannuwa, sarƙewaan numfashi da ganin duru duru mafi hatsari shine  jijjiga ga mace. In ya faru da mace mai ciki to ana gaggawar fitar da abin da ke cikinta ne ko da bai isa haihuwa ba, saboda ceto ta daga hatsari, za a kula da lafiyanta na tsawon lokacin da jininta zai sauka ta fita daga hatsari.

Rukunin cutar Eclampsia:
Antepertum Eclampsia.
Shi yana faruwa ne kafin mace ta haihu.
Shi ne kuma irin Eclampsia da ya kama Ummu Salama.
Intrapartum Eclampsia; shi ne ke faruwa a lokacin da mace ke naƙuda.
Sai kuma Postpartum Eclampsia; shi yana faruwa ne bayan haihuwar mace within 48hours.

Cutar Eclampsia cuta ce mai hatsari, ana iya rasa mace da cikin jikin nata gabaɗaya. Zuwa awo na da matukar amfani sannan da lura da yanayin hauhawar jinin mace mai ciki tunda jinin ne yake hayewa saman kwakwalwa sai cutar ta bayyana ga gangan jiki a kiyaye shiga damuwar masu juna biyu. Da kuma kula da blood pressure saboda shiga hatsari faruwan haka kuma a yi gaggawan zuwa asibiti domin samun taimakon gaggawa.

*

Ba a barin mutane masu yawa suna shiga in da Ummu Salma take, da safe da rana da yamma duk wanda ya zo gaisuwa sai dai ya tsaya can ya yi mata fatan samun lafiya. Amma da Hajiya Kilishi tare da Hajiya Zaliha suka taho gaisuwa da duba Umma Salma sun zo asibitin kuma an bar su sun shiga sun dubata.
Da yake kowa ya ji labarin abin da ya faru domin a ranar Saleem ya faɗa a group na su na iyalan Mai martaba.
Ƙannen Lamido ba wacce ba ta kira shi ta yi masa gaisuwa da jaje ba.

Tana farke ma a lokacin  da su Hajiya Kilishi suka zo ranar kwana biyar da rasuwar Baffa domin tunda ta dawo hayyacinta ta ga ba ciki a jikinta sannan ɗinki ma a in da aka yi mata na haihuwan Hanan a wajen aka sake yi mata wannan ma sannan ta ga har kwana biyu ba a ce mata komai ba sannan ba a nuna mata abin da ta haifa ba ta cire rai da shi.
Received at 10:00
8 people reacted with ❤
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Saboda ko Lamiɗo kullun da safe zai zo asibitin ya duba ta amma bai taɓa mata maganar cikin ba sai dai kuma damuwar dake zuciyarsa wannan karon ta bayyana a saman fuskar shi ko bai faɗa ba ta saka ma ranta cewa yadda ta rasa Baffa shima mai sunan Baffa ta rasa shi.

Sannan ko Mami da Baɗɗo da suke kwana da ita ba su taɓa mata maganar abin da ke cikin ta ba. Ita ba yarinya ba ce in abin da ke cikinta na da rai ai za ta gan shi amma tunda ta ji shuru ta saka ma zuciyarta cewa koma me ta haifa shima babu shi kamar Baffa ba ta yi kuka ba amma kuma raɗaɗin dake zuciyarta bawa bai isa ya kwantanta ba.
Sannan ana gobe bakwai ɗin rasuwar Baffa ranar da aka buɗe wajen da aka yi mata C.S aka yi dressing ɗin wajen ba daɗewa Lamiɗo ya zo shi ya haɗa ta da Fulani a waya ta gaisheta.

Ta yi ta tambayanta ba wata matsala dai ko? Ta ce babu sai ɗan abin da ba za a rasa ba. Asibitin babban asibiti ne tunda kuma asibitin kuɗi ne akwai ƙwarrarun ma'aikata  suna kula da majiyantan su sosai tun ballatana ita da take matsayin VIP.
Ta faɗa ma Fulani kawai yanzu rashin karfin jiki ne sai kuma rashin daɗin bakinta an fara ba ta abinci amma ba ta jin taste ɗin komai.

Sai kuma sai

Please Login or Register in order to submit comment