Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ummu Salma na renon Sadauki da taimakon su Harira sannan tana gudanar da Foundation ɗin su ƙarshen shekara na yi Bilkisu ta tafi Canada shekara ɗaya za ta yi sannan ta dawo yara kuma suna tare da Umma Salma ga Hadimai su Anitha ma duk suna nan amma sukan je garuruwansu hutu lokaci bayan lokaci.

Zuwa lokacin gidauniyar Ummu Salma ta kafu sosai sannan kuma yanzu ƙokarinta samar da wajen da za ta buɗe kamar makarantar koyon girki sun fara magana ma da Mai martaba ya ce za a gina mata tunda tana ra'ayi.

A lokacin shekaran Baffa uku da rasuwa shi kuma Lamiɗo yana da shekaru biyu a saman Ƙaraga.
Abubuwa sun canza domin ko can jimeta ma an ƙara gyara gida ya zama wani mansion. Hamma Saddam ya samu aiki da kamfanin leadership dake Abuja kiran sa kawai aka yi yaje aka yi masa gwaji kuma ya haye.

Baɗɗo ma wani cikin ne da ita amma hakan bai hana ta aikin alheri ba.
Shekaran ɗaya Bilkisu ta yi a Canada ta dawo Mai martaba ya kai mata ziyara har sau biyu tana dawowa sai ga ta da ciki har ya fito ma.

A shekaran Ummu Salma ta je Saudiya ta sauke farali ita da Mai martaba Lamiɗo suka je Bilkisu tana gida tare da yara, yanzu bayan dawowarta tana duba majinyata a clinic ɗin Masarauta bayan ta dawo daga Canada kuma sai ta koma aiki da Federal goverment.
Bilkisu ta haihu ta ƙara samun namiji Lamiɗo ya ba ta zaɓi ta zaɓa masa suna Aliyu.

Burin Ummu Salma ya cika ta je ka'aba ta yi ma Baffanta addu'a ta yi ma mijinta da yaransu ba wanda ba ta yi ma addu'a ba.
Foudation ɗinta na ta cigaba sun samu nasaran buɗe ofishi a Jimeta tunda nan ne mafarin komai, sukan je Jimeta da Babban salla in suka je ana kai Hanan gidan mahaifinta ta kwana biyu.

Mai martaba Lamiɗo ya cika alƙawari an siya fili a cikin garin Daura an kira magina da mazana sun zana, magina sun fara ginin center ɗin da Ummu Salma za ta buɗe na koyon girki, sannan duk shekara yanzu suke ba da tallafin jari ga mata, kuma alhamdullah matan da suka samu tallafin sun samu abin dogaro Shamsiya yanzu sabulun wanke wanke take siyarwa da turaren ƙamshi na ɗaki har da na tiolet a jarin da aka ba tana kuma ganin cigaba har Habiba ta kawo an ba ta jari da wasu
Received at 08:04
9 people reacted with ❤
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
ƙannen Habib ko bakomai su ci albarkacin Hanan.

Sai da suka samu ofishin Jimeta sannan suka samu na Katsina Hajiya Mardiya na kula da shi
Lamiɗo na da shekara huɗu a kan ƙaraga Fulanin Daura ta rasu mai Martaba mai murabus da ake ganin kamar shi ne ba shi da lafiya to ta riga shi tafiya mutuwar da ta girgiza ahalin Muhammad Shitu tsohon sarki gabaɗaya an yi rashi a masarautar Daura, bayan rasuwarta Lamiɗo ya so Ammah ta dawo Masarauta da zama ta ce tana nan a Jimeta. Tunda kuma Lamiɗo ya yi magana ta ce a'a ba wanda zai iya tanƙwarata.

Tuni an saka Banafsha a makaranta da itama bakinta ya buɗe, wannan karon sai da ta yaye Sadauki sannan Ummu Salma ta ƙara samu cikin. Kuma a lokacin ma ta gama yanke shawaran za ta koma makaranta ta haɗa degre ɗinta akan abin da take so wato girke-girke tunda yanzu tana mu'amala da mutane sosai.


Tana faɗa ma Mai martaba, shi kuma ya ba ta goyon baya ta siya Jamb ta yi a garin katsina, kowa ya ji za ta koma makaranta sai ya yi mamaki Hamma Kabiru ya fi kowa jin daɗin haka ya ce lokaci bai ƙure mata ba.
Ta samu nasaran cin Jamb, ta yi kuma post UME ta samu nasaran samun course ɗin da ta ke so.

Bechelor of Arts BA in culinary Arts 4years program ne a Alƙalam University Katsina. Mai martaba Lamiɗo ya siya mata ƙaton gida ta koma can da zama, amma tana zuwa weekend duk sati ko shi in ya samu sarari ya leƙata tana tare da Harira da Asabe sai kuma direba guda ɗaya sai kuma escort mace tana aiki da DSS, sai maigadin dake kula da gidan suna zaune tare da ita yara kuma suna Daura Sadauki ne kawai tare da ita sai cikin jikinta.

Da ta fara karatun ta ji kamar ta bari saboda wahala amma da ta yi kamar ta juya sai kafaɗan Lamiɗo ya tare ta sai ta sake miƙewa ta jajirce, tana kuma karatunta tana cigaba da gudanar da gidauniyarta tare da tsare tsaren buɗe SARAUNIYA DAURAMA CATERING CENTER DAURA.

Tana so a yi gagarumin biki za ta gayyaci duka manyan Food bloggers na arewa wajen taron buɗewa sannan ɗaliban farko kyauta za su samu karatu, sannan za a ɗauki ƙwararrun malaman da za su dinga koyarwa itama tana so ta zama malama burinta ta gama karatu ta kara CHEF a gaban sunan ta.

Wato CHEF UMMU SALMA MUHAMMAD LAMIƊO..
burinta guda ɗaya ya cika sai godiya yanzu ɗayan ne take fatan ya cika kamar yadda ta ɗaura niyya.

*Janafty*
Received at 08:04
7 people reacted with ❤
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
RUFEWA.

BAYAN SHEKARA HUƊU.

Ƙarfe shidda na yammacin ranar laraba suka iso Daura. Direba ke jan ta a sabuwar motar ta corolla ta kamfanin Toyota shi dai Allah ya ƙara masa lafiya Mai martaba Sarkin Daura Muhammad Lamiɗo ya fi son kamfanin toyota in dai a bangaren motoci ne duka motocinsa kamfanin ne har waɗanda yake siya musu suma kamfanin Toyota ne.

Tare da Harira suke tafe sai Rukayya(Fulani) sai matashin cikin jikinta ɗan wattani biyar, sai dogari guda ɗaya da escort ɗin ta Fadila.

Harira ke riƙe da Fulani da jakar tarkacen kayanta dake ciki, ƙaramar jakar Ummu Salma tana hannunta ta hana Harira ɗauka kar kayan su yi mata yawa, tunda itama ba ita kaɗai ba ne akwai ƙaramin ciki a jikinta.

Harira yanzu matar aure ce, direban masarautar da Mai martaba ya ba ta suka koma katsina shi ya aureta a shekaran da ta gabata suna zaune a katsina tare da ita, Harira yar amana ce a wajenta ba ta fatan su rabu har abada shi yasa ta fi kowa jin daɗin auren Harira a kusa da ita. Sannan ita karan kanta ta ba ta ma jari ta fara kasuwanci domin dogaro da kanta.

Sanye take da atamfa mai blue sai abaya kalan blue da mayafi takalmin kafarta mai sauƙin tudu ne, Ummu Salma Sarauniyar Daurama ta yi wani irin kyau da jikin murjewa tana tafiya ɗaya bayan ɗaya Fadila da Harira na take mata baya, dogarai da Hadimai na zubewa wajen kwasan gaisuwa.

A bangaren Bilkisu suka fara yada zango lokacin tana Katsina Mai martaba ya faɗa mata Bilkisu ba ta da lafiya har an yi addmmiting ɗinta a asibiti, ita da Aliyu ta ɗauka ma ko laulayi ne tunda tun bayan da ta haifi Aliyu ba ta ƙara haihuwa ba, ita ko ta yi Rukayya wacce ta ci sunan Fulani sai kuma ga ta ɗauke da wani cikin, to yaushe ma Bilkisu ta zauna a gida ta yi wata biyu? A cikin shuɗewar shekaru huɗu ta tafi karin karatu ƙasashe sama da uku bayan canada yanzu haka tana koyarwa a Deparment of health Sciences A ABU Zaria shima ɗin a wata sau uku take zuwa kuma bayan aikin ta na asibitin Federal medical center Daura, ba irin shawaran da ba a bata na cewa ta buɗe clinic ba amma ta ce ba ta so, ita ba ta son ta yi abu ace ta ga wani na yi ne har yanzu ta na nan matsayinta sai dai a kwaikwaya a wajenta.
Sannan tana son yin abin da wani bai taɓa yi ba, shi yasa take aiki a matsayinta na ƴar Sarki kuma matar Sarki.
A ɗakin su kaf ita kaɗai ce take aiki kuma hakan abin alfaharinta ne ba domin kuɗi ko mulki ba sai domin ra'ayinta ne hakan.

Yara duk suna nan suna ganin Umma Salma suka rufe ta da oyoyo Mahma suna rige rigen ɗaukan Fulani.
Sultan ne kaɗai ba shi a falon yana cikin ɗakinsa Sultan an girma an zama samari shekarunsa sha biyar yanzu haka yana jss3 ne a makaranta. Hanan shekarunta goma kenan Beena kuma sha biyu, Hanan na primay 5 ita kuma Beena na Jss1. Banafsha shekarunta takwas daidai da adadin shekarun zamowar Lamiɗo Sarkin Daura.
Sadauki shi ne shidda da wani abu sai Aliyu sai Fulani dukkansu suna makaranta Fulani ce kawai ba a saka ba sai ta shekara uku.

Bilkisu na ciki sai da Sabuwa ta shiga ta yi mata mgana, Sabuwa da Hidaya na nan yan amana, Anitha ce dai ta koma garinsu ta yi aure Debora ma da kanta ta bukaci tafiya aka yi mata kyakyawan sallama.

Lokacin da Bilkisu ta fito surutun yaran ya karaɗe falon kowa na faɗa ma Ummu Salma labarin abin da ya faru da ba ta nan, wani abun birgewa yaran su a tare suka taso cikin shaƙuwa, in Bilkisu ba ta nan yaran na wajen Ummu Salma in kuma dukkansu ba sa nan suna wajen Gimbiya Shahida a gidan Mai martaba tsohon Sarki burin Lamiɗo ya cika ya haɗa kan iyalansa a waje ɗaya.

Sun gaisa da Ummu Salma kamar yadda suka saba ta yi mata ya jiki ta amsa suna nan a yadda suke mu'amalansu amma an ɗan samu canji kaɗan tunda yanzu suna da lambar juna in wani abu ya faru ɗaya na shiga wajen ɗaya.

"Aliyu ma ya sha ciwo Ali sannu."

Ummu Salma ta faɗa tana shafa kan yaron da ya kwanto da kansa a saman cinyarta.

"Zazzaɓii ne kawai."

Bilkisu ta ba ta amsa a yanayin maganarta. Ummu Salma ta gane cewa ƙasaita da jin kai a jinin Bilkisu ne ba za ta iya bari ba

"Allah ya ƙara sauki ke kuma Alkah ya raba ku lafiya."
Received at 08:05
9 people reacted with ❤
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ta faɗa tana dariya Bilkisu ta kalleta ba ta ce komai ba ta kauda kanta.
Sai ta ɗan yi mirmishi daidai lokacin da Ummu Salma ta mike matashin cikinta ya bayyana ta bita da kallo.

Rayuwa kenan yau ga shi Ummu Salma ya'yanta uku tare da Lamiɗo har ga cikin na huɗu, a baya ji take yi in wata macen ta raɓu da Lamido har suka haihuwa za ta iya kashe kanta da taimakon Allah da taimakon Addu'a Allah ya saukaka mata kishi, shi yasa ta mayar da kanta Busy saboda kauce ma shiga tunani da ruɗani, itama da ta yi ta fama da ciwon jiki ta ɗauka ciki ma ta samu har Lamiɗo ma fatan da ya dinga yi kenan ashe ba ciki ba ne.

"Ke dai Allah ya sauke lafiya. Amma ni ba ni da komai."

Bilkisu ta faɗa itama bayan ta miƙe tsaye.

"Kai wai ba cikin ba ne?

Ummu Salma ta tambaya tana riƙe baki.

"Na ce ma Hamma ko dai mun samu ƙaruwa ne ya ce e"

"Haka zai ce kin san shi ba ya son tambaya."

Bilkisu ta faɗa tana mirmishi, ta daɗe tana fafin Lamiɗo na musamman ne sai a yanzu ta fahimci ya fi na musamman.
Ba za ki taɓa jin mganarki a bakin kowa ba yana da kamewa da rike sirrin kowa ya san iya zama da matansa sosai.

"Ban ji daɗi ba gaskiya."

"Haka Allah ya so."

"Haka ne Allah ya kawo mai amfani "

Bilkisu ta amsa da Amin a saman leɓenta.
Tana kallon Ummu Salma, yanzu ko tana so ko ba ta so ta karɓi Ummu Salma a matsayin kishiyarta domin ta fahimci gaskiya tuntuni.

Tana kallonta tana mamakin yadda take da ƙoƙari ga haihuwa ga karatu ga sauran ayyukanta.
Tana ganin ƙoƙarinta sannan tana jinjina mata ga shi kusan a wata sau biyu ko uku tana hanyar dawowa Daura.

Sallama ta yi ma Bilkisu yaran suka tashi za su bita Bilkisu ta ce su je can bangaren Ummu Salma dama ta gaji da hayaniyar su.
Suka ɗumguma zuwa bangaren Ummu Salma, duk da ta so su zauna a bangaren Bilkisun saboda akwai ayyukan da za ta yi.
Amma ba ta da yadda za ta yi tunda sun maƙale mata, tunda suka koma bangarenta suka tasa ta suna kirga sunayen in da za su je hutu aƙarshen shekara.

Hanan da Beena suka ce Adamawa da Lagos, Banafsha ta ce Kaduna gidan Mami, Sadauki ya ce Abuja Ali ma ya ce Abuja Ummu Salma ta ce duk za su je duk in da suke so, daman ita ce ke tafiya da su hutun, ko wancan shekaran sun je Lagos tunda gidajensu na can su James na kula da su.

Sun je har Jimeta ba za su manta mafari ba daga can suka sauka a Kano wajen Bilkisu suka kwana ɗaya suka dawo tare Masarauta, ita ce daman mai biye ma yaran Bilkisu ba ta da wannan lokacin, Mai martaba kuma sha'anin mulki ba ya barin shi ma, amma wannan shekaran tana so su je hutun gabaɗaya har da shi da Bilkisu.

Kiran mangariba ya sa hayaniyar yaran ya ƙare, Sultan ya shigo ya ce Sadauki da Ali su zo su tafi masallaci sun san in ba su je ba Papa zai yi faɗa. Matan kuma suka yi a gida.

Ummu Salma na idar da salla ta faɗa kitchen yau 8 ga watan September yau Hamma Lamiɗo ke cika shekaru arba'in da takwas a duniya ita kuma tana da talatin da takwas a jibi kenan. Dalilin dawowanta kenan daman sai kuma za ta je Center ɗinta watan da ya fita ba ta samu sarari ba, sau abu na uku kuma ta duba Mai martaba ya dawo daga London ganin likita, Mai martaba tsohon Sarki yana nan da ran shi cikin ƙoshin lafiya sai dai jikin girma da tsufa.

Burukan Umma Salma sun gama cika a duniya.
Gidauniyarta ta shahara a cikin shekaru shidda a arewa wajen tallafama mutane, suna da afisoshi yanzu a garin Kaduna da Abuja bayan na Daura da Katsina ga na Jimeta.
Sannan shekaru biyu da suka gabata ta samu nasaran buɗe Cooking center ɗinta, gini ne mai girma akwai ajujuwa ga ɗakunan girki ba abin da babu, an ɗauki malamai ƙwararru da suka cancanta suka samu ƙwarewa a bangaren da za a yi taron buɗe wajen Ummu Salma da taimakon mijinta Mai martaba Sarkin Daura Muhammad Lamiɗo ta gayyaci manyan mutane, sannan ta gayyaci manyan masu girke girken online na arewa sannan a ɗaliban farkon da aka fara da su training ne na wattani uku kyauta sannan an ba su certificate da jarin dubu hamsin daga Gidauniyar Sarauniyar Daurama.
Received at 08:05Reactions: ❤ 10, 👏 1
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ana yin tranning na wata uku, wata ɗaya, sati uku, har na wattani shidda wajen ya samu karɓuwa sosai kuma kamar tallafawa ne ga mata da garin Daura gabaɗaya.

SARAUNIYAR DAURAMA COOKING CENTER ya samu shaidar Rigister NAFDAC National Agency for Food  and Drug Administration and control in Nigeria. Ummu Salma na can katsina tana karatu amma in ta samu sarari ta zo Daura tana zuwa itama ta koyar duk da ta ce itama har yanzu tana koyo ne.Ɗayan burinta ne ke gabda cika, yanzu haka tana shekaran ƙarshe a Jami'a a ƙarshen watan gobe za su fara final exams ɗin su, Finally bayan duka wahalhalu da rashin barci yau burinta zai cika za ta haɗa Degree a bangarenta da take so wato girke girke, da gaske ne karatu yana da wahala amma in ka saka yaƙini da jajircewa Allah zai tallafa maka.

In ta tuna gudummuwar da Lamiɗo ya ba ma rayuwarta sai ta ji tana hawaye anan duniya babu abin da ba za ta iya yi masa ba ciki har da rayuwarta ga fansar na shi rayuwar. Ya nuna ma duniya shi Miji ne, uba, Yaya kuma shugaba. Ya ba ta kafaɗarshi ta jingina ya juya mata baya ta kishingiɗa ya zama ginshiƙi na rayuwarta. Mami ce sanadi shi yasa har gobe ba kamarta a wajenta.

Yanzu haka Mami aikinta na koyarwa ta ajiye tana zaune a gida tana hutawa tunda shekaru sun ja, sai dai kawai ɗan harkokin Foundation ɗin da take gudanarwa anan Kaduna. Islam ta gama degree ɗinta ta ɗora master ɗin ta tana Kano BUK.
Faruk kuma yana jami'ar madina can ya fara karatun shi, mahaddaci ya ke son zama.

In ta yi salla biyar a rana kamar yadda take saka Baffa a cikin addu'o'inta haka take saka Mami, ita ce tsanin da rayuwarta take kan wannan bingiren har kuma gobe ita ce ɗiyar ta Lamiɗo har abada ɗan Ammah ne.

Tunda ta ce ta ba shi tun yana ƙarami har abada ta yi kyautarsa ba ta taɓa nuna duniya ɗanta ba ne. Har Kaduna suna zuwa da yara su yi mata hutu Ammah na Jimeta, tunda ta ƙi yarda ta dawo Daura ta zauna.
Shekara ɗaya da rabi kenan Hamma Saddam ya yi aure, ya auro buzuwa daga adagex gashinta har gadon baya amma irin baƙaƙen buzayen nan ne masu kyau suna zaune a garin Abuja, amma ya gyara bangaren su na gida Jimeta nan suke sauka in sun je gida, Ammah girma ya zo amma tana cikin jin daɗi Baɗɗo haihuwanta uku duka maza su Adda Suwaiba ma duk suna zaune lafiya Hamma Abdullahi ne ya gaji Baffa tunda daman tare suke kasuwanci ya cigaba da gudanar da kasuwancin su har kuma gobe komai Mai martaba Lamiɗo zai yi ta hannun Hamma Abdullahi ne akwai amana a tsakaninsu.

Sannan duk da yanzu Lamiɗo Sarki ne Amincin dake tsakaninsa da Hamma Kabiru bai rusuna ba.
Shi ne amininsa da zai iya tattauna komai na shi da shi. Hamma Kabiru da iyalansa suna zuwa Daura su yi musu hutu duk lokacin da suka samu sarari suma suna zuwa tunda har naɗin sarauta Lamido ya yi masa maji daɗin mutanen Daura.

Rayuwa ta yi kyau sai dai godiya Allah Baffa shekarar sa tara kenan da rasuwa amma har a wannan lokacin mutuwarsa na yawan fami ga iyalansa Baffa Salihu ma ya rasu shekaru biyu kenan yanzu Baffa Umaru ne kaɗai ya rage su Umma Balki duk suna nan suna cikin godiya da aminci. Ummi ikki da Ammah amintarsu tun na yarinta babu abin da ya canza sun manyata amma kuma amintarsu bai yi rauni ba.

Rayuwa juyi juyi na gaba ya koma baya, an yi wayi gari yanzu Ammah ba ta wannan rawan jikin ga Bilkisu. Ita dai Ummu Salma ta ga canji sosai ta yi mamakin me Bilkisu ta yi ma Ammah! Duk da ko a fuska ba ta nuna wani abu amma ta rage zaƙewa kan lamarinta ko rawan jikin in suka zo Jimeta, tana so ta yi ma Ammah magana sai ta sha'afa sai da Baɗɗo ta faɗa mata abin da ya faru ta san ba banza ba canjin Ammah, ashe tun tana da cikin Banafsha, lokacin da matar mai martaba sarkin kano ta rasu, Ammah ta kira Bilkisu a waya ta yi mata gaisuwa bayan sun gama mgana ita Ammah ba ta kashe wayar a can bangaren ba, haka itama Bilkisu ta ɗauka Ammah ta kashe ne, ana ta mganar Ummu Salama da su Gimbiya Hadiza, Bilkisu ta buɗe baki ta ce ta tsani Ummu Salma da iyayenta da mganganun da take yi na raina su Ammah, ba ta san Ammah ta gama ji ba tas sannan ta kashe wayarta, Ammah ashe ta sha kuka jikinta ya yi sanyi, ta kasa faɗa ma kowa
Received at 08:05
13 people reacted with ❤
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
kar a yi mata dariya.

Da Ummi ikki kawai ta tattauna mganar ita kuma ta ce ishara ce, gwara ta riƙe ƴaƴanta Ummu Salama dai ɗiyarta ne, haka ma Lamiɗo, Bilkisu kuma ta bar ta da halinta ga ta ga duniyar nan, Ummu Salama kuma da Lamiɗo kuma smutu ka raba. Shike nan Ammah ta kama kanta, yanzu kawaicin duk da take yi ma Auta ta rage sosai da Baɗɗo ke ba ta labari ga dariya ga takaici wato rayuwar nan darasi ne mai zaman kanta abin da ya sa ka dariya watarana kuka zai sanya ka, ta wani bangaren ta ji daɗi da Ammah ta fahimci halin Bilkisun an ce Bilkisun har Ammah ta kira a waya tana tambayan ko ta yi mata wani abu ne ta ga ta canza mata Ammah ta ce ba komai.
Amma tabbas Bilkisu ta sha jinin jikinta, ganin Ammah da ke ta kanta ma yanzu ta daina dole ta yarda makaman yaƙin ta.

Shamsiya ta samu canjin rayuwa ta sillar Ummu Salma, har yanzu tana aiki da su a Foundation ɗin su sannan Habib ya samu aiki a wani kamfani sarrafa takalamin fata anan garin Jimeta sun samu canjin Rayuwa. Suna nan tare da Habiba wacce ta haihu ɗiya mace har takwara aka yi ma Ummu Salma yanzu ta daina adawa itama, tunda ga shi sanadiyar Umma Salma ta samu jari tana kasuwancin online, sannan Habib ya samu rufin asiri ta yarda ta haihu da shi Shamsiya dai har an juya mata mahaifa domin ta yi rauni ta gaji da ɗaukan ciki tana ɓarin shi, Hanan tana zuwa musu hutu in dai ta je Jimeta.

Ta riga ta san cewa Papa ba babanta ba ne, ta tambayi Ammah ta faɗa mata gaskiya sannan ta tambayi Lamiɗo ya amsa mata da cewa shi ne babanta amma mahaifinta Habib ne wanda take ce ma Abba. Duk da ta ji ba daɗi amma ta gode ma Allah, tunda tana da baba guda biyu. Riƙon ta da duka rayuwarta na Hannun Lamiɗo da Ummu Salma ne, amma in ta je Habib da danginsa na iya ƙokarin su wajen kyautata mata duk da sun san ba za su iya yi kwatanta mata gatan da Hanan take da shi ba.

Sai dai su yi abin da za su yi Hanan ko kayan jikinta kaɗai ka kalla kasan yarinyar yar gata ballatana fatar jikinta, ga turanci ga labarci ga tarin ilimi, Habib ya saduda ya fahimci rayuwa ya gane kuskuren shi  ya fahimci cewa Ummu Salma na sama shi kuma yana ƙasanta.

Har yau har gobe tana ɗora girke girke a shafukanta na yanar gizo, ta samu jama'a ta samu duniya sai godiya sannan har Pandora award ta karɓa a wancan shekarar a matsayinta na jajircacciyar mace mai tallafama gajiyayyayu da marasa ƙarfi sun je tare da Mai martaba Lamiɗo da yara suka karɓo award din tare, da aka bata shi ta ba mawa domin ta ce duk abin da ta kai a yau kafaɗarshi ce ta cinciɗata.
Haka ta faɗa a wajen bayan yan jaridun sun tambaye ta ya take ganin nasaranta ko matakin da ta kai a yau?

Hotunansu suka dinga trending a kafafen yaɗa zumunta ana faɗin sun bala'in dacewa ga shi suna kama da juna aka fara yawo da faɗin yan'uwan juna ne shi ya sa suke kama da juna, ga yaran su gwanin sha'awa kamar ya'yan turawa
A garuruwa da dama sun ba da an yi rijiyoyi da bohol sadakatul jariya ga Baffa ta yi sannan suma yayyenta duk sun yi.

Sau uku ta je Saudiya Umra kuma ba ta san adadi ba.
Fulani ma a England ta haifeta wannan haihuwan ta ce a Saudiya za ta haihu. Bilkisu ma haihuwan Ali a Abuja ta haihu.

Kasashen ƙetaren da ba ta je ba kaɗan ne sai ga ta har ƙasar Jordan ta kai ma Jamila Umar takwaran Janafty ziyara sanadin marubuciyar nan ta online ta san ta. Namesake tana da mutumci da girmama baƙonta Allah ya ƙara ma rayuwa albarka.

Rayuwa ta cika da tarin ni'ima sai godiya.
Lamiɗo na gudanar da mulkinsa cikin tsanaki, talakawa da mutanen gari suna son shi Yazeed da Sagir duk sun dawo gida sun yadda makaman yaƙin su, sun zo sun haɗa kai domin cigaban Masarautarsu.
Sun yi aure sannan Lamido ya yi musu sabon naɗe naɗe, gabaɗaya manyan hakiman yan gidansu ya ba mawa, tunda kwanaki rigima ya ta so yaran ƙannen marigayi tsohon Sarki Muhammad Shitu kakansu Lamiɗo, sun ta so suma sai Sarauta ta dawo gidan su. Tuni su Lamiɗo suka haɗe kai suna fatan har nan da shekaru tamanin sune za su cigaba da mulkan kasar Daura. Burin Mai martaba kenan yau kuma burin shi ya cika.
Received at 08:05Reactions: ❤ 4, 👏 1
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Amir ne kawai ke Delhi yana can yana karatun likita, Amira ma tana Base Abuja, Hafsart ce ta yi aure tana auren yaron Sarkin Adamawa.

Sarakuna sun sha kawo ma Mai martaba Lamiɗo tayin auren ƴa'yan su amma ya ce baya

Please Login or Register in order to submit comment