Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

in Gwaggo ta miƙa hannu domin ta ƙarbeta sai taƙi yarda da ita har gwara ma Shamsiyan ta ƙamƙameta amma ba ta daina kuka ba.
Habib ya kasa motsi idanuwansa sun yi jajir ta madubin gaban motan yake kallon Hanan kukanta ma daɗi yake yi masa zuciyarsa ta yi wani irin ɗumi ya rasa yanayin da yake ciki na farinciki ne ko na ɗimaucewa da sanin abin daman hasashe ne da yaƙini kawai amma ba shi da tabbas ɗin Ummu Salma ta haifi wannan cikin.

In ya kalli Hanan sai Fargar jaji ya sake kama shi, lalle da ya zama cikin masu asara da ya yi sanadiyar zubewar cikin nan, da haƙƙin Hanan ba zai taɓa barin shi ya sake rayuwa cikin sukuni ba.

Hajiya Sahura tana ta cewa Ubangiji mai yadda ya so, ashe dai cikin nan sai da ya zo duniya.
Gwaggo na amsa mata da cewa Allah ya ce zai rayu ai bawa bai isa ya hana ba. Habiba na gefe tana ta taɓe baki tana hararan Shamsiya ganin yadda take wani zakewa a zuciyarta ta ce ai daɗin abin ma ba yarta ba ce, takaicinta ɗaya da ya kasance Yaƙinin Habib ya zama gaskiya ta so har abada kar ya samu abin da yake so.

Gidan Gwaggo suka sauka gabaɗaya nan Gwaggo ta dinga kiran kannen Habib a waya tana faɗa musu su zo gida su ga ɗiyar Habib.
An tasa Hanan a gaba ana kallo cikin birgewa da sha'awa ita kuma tana ta kuka. Shamsiya ce ta ɗauketa ta goyata da zani tana faman lallashinta.
A ɗakin Gwaggo ana ta mayar da magana Baba Usman na faɗin bai taɓa zaton ahalin Ummu Salma suna da sauƙin kai haka ba.

"Ai mahaifinta dattijon arziƙi ne. Mutumin kirki ne Allah ya yi masa rahama."

Alhaji Sherif ya faɗa sannan ya cigaba da faɗin" Ni da man na san cewa ba za su zubar da cikin ba, Habibu ka ga ikon Allah ko? Ka ƙara gode ma Ubangiji na son ka."

Ya gama faɗa yana kallon Habibu da ya sunkuyar da kansa ya kasa magana domin wani farincikin ma ba a iya magana.

"Nima haka na ce, Allah yana son shi da Rahama."

In ji Gwaggo, dukkansu kuma suna mai sake yi ma Habib ɗin nasiha da kuma cewa ya lura da rayuwa, ga shi dai yana ganin abubuwan da suka faru

"Ni uwar ce ma ta ba ni tausayi tana ta kuka."

Hajiya Sahura ta faɗa domin da gaske Ummu Salma ta ba ta tausayi.

"Nima sai da na yi mata ƙwalla, ga rasuwar uba ga shi kin ji an ce ta haihu ba rai, abubuwan ne suka yi mata yawa, sannan abin ne ya zo a lokaci ɗaya ni kaina ban taɓa tunanin za su kawo maganarka ba, tunda muna zuwa yarinyar ta shigo ko ba a faɗa ba ga kama nan da Habibu, shima kuma ya ki magana tunda yana ganin tunda shi ya ce ba ya so ba shi da ikon tambaya sai ga shi uwar ta ce a ɗauko ma na Hannatun. Sun yi mana karamci Ubangiji suma ya karrama su ranar gobe ƙiyama."

Gabaɗaya suka amsa adduar Gwaggo da Amin Amin.

"Tunda sun yi mana kara muma mu yi musu, ta yi kwana biyu kowa ya zo ya ganta ku mayar da ita wajen mahaifiyarta "

Alhaji Sherif ya faɗa yana kallon Gwaggo ta amsa da in sha Allahu.

"Ai ka ji mahaifiyar Ummu Salman ta ce a can Lagos suke zaune komawa za su yi."

"Can uwar ke aure?

Hajiya Sahura ta tambaya.

"Ina jin can take aure, ai ɗan'uwanta take aure yaron sarkin Daura ne."

"Ɗan Sarki?

Hajiya Sahura ta sake faɗa da sigar tambaya.

"E, ai shi Sarkin Daura ya taɓa auren ƙanwar ita mahaifin Ummu Salma ta haihu da shi suka rabu tun kafin ya zama sarkin ma, ni lokacin na sani tunda Habibu ya faɗa mini , yanzu kuma an ce shi take aure ban dai sani ba ko yana cikin mazan da muka gani a gidan"

"Yana nan"

Habib ya amsa a sanyaye

"Yana nan wani fari dogo baya magana, domin har muka tafi ban ji ya yi magana ba."
Received at 11:37Reactions: ❤ 3, 🥰 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Gwaggo ta ce ba ta kula da shi ba, Hajiya Sahura ta ce ai duk kusan yaran farare ne suna kama da junan su.
Alhaji Sherif da Hajiya Sahura ba su jima ba suka tafi tunda mangariba ta yi Gwaggo na ta yi musu godiya.
Baba Usman ma gida ya tafi amma Habiba na nan so take yi ta ga abin da zai faru a gidan sai ta ce ma Gwaggo anan za ta kwana sai da safe za ta koma gidanta

Ai ko ta sha kallo, domin haka yan'uwa Habib ke tururuwan zuwa ganin Hanan washegari Hanan ta gaji ta daina kuka, Shamsiya ta yi mata wanka ta kuma dafa mata indomie da safe, amma har cikin dare ta tashi da rigima tana kiran sunan Mahma da Mami
Shamsiyar ta goyata a daran ta kwana jijjiga Habib kuma bai yi barci ba, farincikin da yake ciki ya hana shi barci kwana ya yi yana kallon Hanan yana hawaye, yana cewa yanzu wannan yarinyar ɗiyarsa ce! Ya yi ma Allah godiya a fili da sarari bai san iyaka ba, bai ɗauketa ba domin sai ya ji ya kasa amma saboda kallo har ya haddace kamaninta


Hanan ta sha ɗauka, ta shiga hannun wannan ta fita ta koma hannun wannan
Kowa sha'awarta yake yi, kuma kowa in ya zo sai ya ba ta kuɗi ko wani abu, tun tana ƙiyuwa har ta dawo ta daina sai dai bin mutane da kallo, kowa mamaki yake yi ashe cikin da Ummu Salma ta fita da shi ta haife shi, ga Hanan sun gani a matsayin shaida.

Hanan ta fara sabawa da Shamsiya tunda ita ke wahala da ita, sannan in Gwaggo za ta ɗauketa ba ta ƙiyuwa yanzu Habib kuma sai dai ya tasa ta kawai yana kallo Habiba ta gaji da ganin takaici ta koma gida ranar a wajenta Habib ya kwana ko tarin ta bai ji ba, ta saba ta dinga masa habaici da tijara amma ranar tunda ta shige ciki sai da safe ya ganta da alamun dai jikinta ya yi sanyi, ko kuma ba haka ta so ya faru ba.


*
BAYAN KWANA HUƊU.

Ranar asabar misalin ƙarfe goma na safe Hamma Jibo ne da iyalansa ke ta haraman komawa Abuja.

Gabaɗaya suna falon Ammah har su Hamma Abdullahi duk sun taho domin yin sallama dashi duk da jiya har wajen sha ɗaya na dare da shi da Hamma Abdulrahaman duk suna gidan.

Ummu Salma na cikin ɗakinta duk hayaniyar da ake yi ba ta fito ba. Tun bayan abin da ya faru ta daina ma kowa magana ta daina hira ta daina dariya ko falo ba ta fitowa tana cikin ɗaki abinci sai dai Harira ko Mami su shigar mata da shi.

A gidan ma su kaɗai ne ke shigowa in da take, Ammah ko ɓarayin ɗakin ba ta sake kallo ba, ballatana Umma Balki da ta ce ba ta da kunya itama ta fita bayanta kan abin da ta yi Mami ce kawai ba ta taɓa juya mata baya ba sai Hamma Saddam da shi Abdulrahim suma ɗin ta ji haushin su domin suna bayan Lamiɗo kuma duka maganarsu ta kira Lamiɗo ta ba shi haƙuri ne ita an kasa gane yanayin ta shi ne mai gaskiya ita ce mai laifi.

Hamma Abdulrahaman kuma a gabanta jiya da Hamma Jibo ya kira ta da daddare yana yi mata faɗa ya ce ya so ne ma Lamiɗo ya kikkifa mata mari saboda ta yi rashin kunya.
Duk a cikin abin da ya faru abu ɗaya ne ta yi nadamar shi maganganun da ta faɗa ma Ammah sune ta yi nadama kuma har haƙuri Hamma Jibo ya saka ta duƙa ta ba ma Ammah a jiyan
Daga yanayin yadda Ammah ta amsa mata itama haushin ta take ji.

"Ni ba ki yi mini komai ba Ummu Salama, kukana ɗaya ko wata ɗaya ba a yi da kasa ta shafe idanuwan Baffa ba amma har kin fara yi mini gaddama da nuna cewa ban isa dake da abin da kika haifa ba."

Kowa laifinta yake gani an kasa samun mutum ɗaya da zai fahimci raunin ta? Sun manta itama mai rai ce tana da zuciya a kirjinta uba fa ta rasa a tsakani kwana biyu ta rasa jaririnta me ya sa ba za ta damu don za a raba ta da ɗiyarta ba a matsayinta na uwa bai dace a ji ta bakin ta ba? Sai kawai a yanke ma rayuwarta hukunci don ta ce ba ta amince ba sai kowa ya koma yana ganin laifinta.

Kuka kawai take yi in ta tuna da rashin da Baffa yau da yana raye da duk haka ba ta faru ba ko da zai yanke hukunci ba zai yi kai tsaye ba sai da amincewarta ba zai yi mata dole ko tursasa ta ba. Har yau da Baffa da ke da kwana ashirin da biyar da rasuwa ta kasa gasgata mutuwarsa gani take yi kamar mafarki ne kamar tafiya ya yi zai dawo nan ba da jimawa ba
Received at 11:37Reactions: ❤ 6, 👍 1, 🔥 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Duk da yadda yan'uwanta suka gasa fahimtar ta ya yi mata zafi, amma duk bai kai kwatankwancin abin da Hamma Lamiɗo ya yi mata. Ga kewar Hanan da ya yi mata rami a zuciya gani take yi kamar za ta rasa ta ne alhalin a lokacin ita kaɗai gare ta.

Yadda suke da shi ta ɗauka zai fi kowa fahimtar halin da ta ke ciki. Ta rasa mahaifinta ta rasa jaririnta duk a lokaci ɗaya shin ba ta cancanci tausayawa ba ne? Abin da ya yi mata ya fi rashin Hanan zafi a zuciyanta. Shi ne fa ya buɗe baki a gaban mutane ya ce wai zai sake ta, ta koma wajen Habib in ta tuna ma da kalamansa sai ta ji kamar ta kurma ihu, komai zai faru tsakaninsu ba ta ɗauka a tsakanin ita da shi ma zai iya kallonta ya faɗa mata zai iya sakinta ba, ballatana a bainar nasi gaban kowa da kowa.

Abin takaicin ma wai ta koma ma Habib, mutumin da ta tsana. Ai tunda ya gama da ita, itama ta gama da shi har gaban abada. Gwara ta mutu ba ta sake aure ba, in ta kama Hanan ɗin ta koma wajensa ko son yarinyar zai kasheta ta gwammace ta yafe ta har abada. Abubuwa biyun nan suka sake raunana zuciyarta suka tafiyar da sauran fatan ta ga cigaba da rayuwar farinciki.

A daran ranar sai asuba barci ya kwasheta, kuka kawai take yi ga tunanin Hanan ta na can wani wajen za ta kwana ba ta san sau adadin nawa ta yi addu'an da Allah ya nesanta Hanan da Habib da zuru'an shi na har abada ba. Shi ya ce ba ya son cikin nan kuma akan shi ya yi mata wulaƙanci ya saketa sannan ya ce ta je da cikin baya so me ya sa Ammah za ta tusa masa abin da ya ce ba ya so ya bar mata? Don ya yi nadama ba ya nufin cewa ta sadaukar da Hanan ga nadamarsa in kuma wasiyya Baffa ce ta tabbata da shi ne ba haka zai yi ba duk abin da zai aikata ko zai yanke akan rayuwarta sai ya tuntuɓeta sai ya tabbatar da ta gamsu da niyyarsa amma daga Ammah har su Hamma Jibo ba wanda ya tsaya ya fahimceta kowa ita yake ganin laifinta.

Sannan ga baƙincikin kalaman Hamma Lamiɗo da suka zame mata dalma, saboda haka ya sa ko sunan shi ba ta son tunawa, mutumin da a baya ko sunan shi ta ji sai zuciyanta ta yi rawa amma ban da yanzu da tuna sunan shi ma kaɗai na kara sanyata jin haushin shi mai tsanani ya kama hanya ya yi tafiyarsa bai yi mata sallama ba, bai kuma sake nemanta ba ko a waya haushinta ɗaya wato shi ma a ganin shi bai yi laifi ba ita ce ta yi masa laifi don ya ce zai saketa ta ce sai me? Ita ce yake jira ta kira shi tana ba shi haƙuri ita kuma a yadda ta ke jin zuciyarta ko za su dauwama a haka ba za ta ce ya yi haƙuri ba domin shi ya fara rusa yarda da amincin dake tsakaninsu.

Gani ake yi kamar in ya rabu da ita wani abu ne, a yadda take jin kanta da yadda duniyar ta fita kanta ba za ta taba damuwa don Hamma Lamiɗo ya sake ta ba. Haushin shi da take ji yasa ta ji ba ta son shi yanzu, ko ya sake ta babu abin da za ta rasa domin ita an gama yi mata rashi a duniya. Har jiya da aka zauna zaman meeting din da Hamma Jibo ya haɗa a daran an kira Hamma Kabiru a waya aka saka a amsa kuwwa tana ji yana faɗin ya so Lamiɗo ya sake ta da gaske ya ga yadda za ta ƙare. Cikin izza yake faɗin ba za ta samu wanda yake ƙasa da shi ba kamar ma kuma ya yi mata nisa ta yi kuka sosai hawayenta har da majina kowa ita yake gani a matsayin mai laifi shi da ya fara furta kalaman shi bai yi laifi ba sai ita da ya mayar ma martani, ba zununci ba ko menene sai da ya lalace za ta nuna ma kowa Lamiɗo ba don shi aka haife ta ba, shima ba don ita ya zo duniya ba kowa ma zai iya rayuwa ba ɗan'uwansa kuma ya zauna lafiya.

Hamma Jibo ya yi maganganu sosai barin ma ita ya yi mata nasiha haƙuri sannan daga ƙarshe shima ya ce ta kira Hamma Lamiɗo ta ba shi hakuri haka ma su Hamma Abdullahi duk suka ce har da Mami, su suna ganin ita ce ba akan gaskiya ba jin su kawai take yi ba za ta ba shi hakuri ba domin ba ita ta fara maganar ba shi ya fara.

An yi maganar in Baffa ya yi kwana arba'in da rasuwa Umma Balki za ta koma gida, wa zai zauna da Ammah? Tunda zaman shurun ba daɗi, ita cewa ma take yi za ta iya zama ita kaɗai.
Received at 11:37Reactions: ❤ 4, 👍 1, 🔥 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Umma Balki ta ce bayan arba'in ɗin za ta je ta duba gida sai Umma A'i ta zo, ta yi ko da sati biyu ne ita kuma sai ta dawo su dinga karɓa karba kafin Ammah ta fita takaba, sannan ga Ummin ikki ma da kullum tana zuwa.

Maganar girki kuma Hamma Jibo ya ce za a ɗauki yar aiki Umma Balki ta ce ba sai an ɗauka ba, za ta iya yin komai da kanta.
Hamma Abdullahi ma ya ce matayensu da yaransu za su dinga leƙowa akai akai saboda kar gida ya yi shuru.
Daga karshe aka tsaya da sai Ammah ta fita takaba za a yi maganar raba gado.

Da gaske kenan Baffa ya rasu! Tunda ga shi ana maganar rabon gado. Mutuwar Baffa mutuwa ce mai zafi ga iyalansa amma a wajen Umma Salma ba a taba mata wani abu da ya daketa da zafi irin mutuwar Baffa ba, ko lokacin da Habib ya saketa ashe abin da ta ji a lokacin wasa ne yanzu ne ta ke jin raɗadin abin da hausawa ke faɗin wasa farin girki.

*

Ta yi niyar ba za ta fito ba, ba ta san ma wani ya yi mata magana amma kudirinta bai cika ba twins Hassan da Hussaini da su Ammi suka shigo suna yi mata sallama.
Sai ga Saudat itama ta shigo tana faɗin Anty Ummu za mu tafi.

Ba a son ranta ba, yaran suka sanya ta fitowa sai ga shi sun haɗe da Adda Nauwara a falo tana ganin ta ta hau yi mata tsiyan ta ɗauka har su tafi ba za ta fito su yi sallama ba.
Ummi ikki ta gani ashe ta zo, ta gaisheta ta amsa tana kallonta.

"Kullun fuska a kumbure Ummu Salma, ko uwar taki ba ta gasa ki da ruwan zafin ne?

Ummu Salma ta yi shuru ba ta yi magana ba. Kanta na kasa tana wasa da Hannun Isma'il da ya riƙe ta.
Tana sanye da hijabinta dogo har da safa tunda Mami ta hana ta zama ba safa hijabi kuma tun dawowarta asibiti take yini da shi barci ne kawai ke raba ta da shi.

Ammah da Mami tare da Umma Balki duk suna falo, mazan ne suna tsakar gida.

"Ba dole ki ga fuskarta kullum a sumtume ba, ba ta da aiki sai shigewa ɗaki tana kuka, kin ga ko ai yanzu idanuwana da fuska suka fara kumbura in dai kuka ta mayar abin yin ta."

Umma Balki ta faɗa tana hararanta, ba ta kuma yi magana ba Mami ce ke amsa mata da cewa ta fa daina kuka.

"Kar ma ta daina yarinya daga faɗa mata gaskiya, sai rashin kunya sai fushe fushe. Kin ba ni kunya Ummu Salma ban za ci haka kike da taurin kai ba, to shi Lamiɗon ma ya yi fushi ya yi tafiyarsa gidansu ki ci kan ki."

Umma Balki ke ta faɗa ta in da take shiga ba ta nan take fita ba.
Mami na tare mata aka haɗa da ita.

"Auta ki daina haka kin ji ko? Ba ki kyauta ba, Ki kira shi ki ba shi hakuri, har yar'uwan ta ki ma ta yi fushi dake yau ma na ce ta zo mu je ta ce ba za ta je ba."

Ummu Salma ta kalli Ummin ikki amma ba ta yi magana ba. Wai har da Baɗɗo a masu jin haushinta. Kar ta zo ta je itama ta yi ta fushin tunda itama ta kasa fahimtar yanayinta.

Shi ya sa ba ta son fitowa saboda ba ta son magana, ranta baci ma yake yi.
Sai da su Hamma Jibon za su tafi ne ta fita tsakar gida Harira da Islam sune masu ɗaukan kaya zuwa haraba Hamma Abdullahi ne zai kai su filin jirgi.

Faruk take kallo yana ta bin bayan Islam da gudu yana rigiman sai ta ba shi wata karamar akwatin da ta ɗauka Hanan kawai ke yi mata gizo yau kwana huɗu ba su dawo da ita ba.
Ita abubuwa da dama ma gizo suke yi mata tunda ta dawo daga asibiti, sai ta ga abu kamar wani abu dabam, ranar fulas ɗin ruwa zafi ganin shi ta yi kamar tunkuya abubuwa dai suna sauya mata a idanuwanta tun bayan fardaɗowanta daga asibiti kuma ta kasa faɗama kowa to waye ma zai saurare ta? Kowa na jin haushin ta wanda ta ke zaune domin shi bai damu da ita ba cewa ma ya yi zai sake ta.

Gabanta faɗuwa yake yi in ta tuna cewa wataƙila gidan su Habib su ƙi dawowa da Hannan da ko mai zai faru sai dai ya faru amma sai ta karɓo yarta ba za ta bar musu ita ba har abada.

A tsakar gida ta tsaya da rakiyar ta yi komawarta cikin ɗaki bayan Hamma Jibo ya jadadda mata ta kira Hamma Lamiɗo ta ba shi haƙuri ta amsa da to amma a zuciyan ta ce shi ya kamata ya ba ni hakuri ba ni ce zan kira shi ina ba shi hakuri ba.
Received at 11:37Reactions: ❤ 4, 👍 1, 🔥 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Baɗɗo ma ta daɗe ba ta yi fushin ba itama ba ta ga laifin da ta yi mata ba, akan gaskiyanta take ai ta san fushi ta yi domin tun ranar ba ta dawo kuma ba ta kira ta a waya ba, itama ba ta kira ta ba.

Tunda Baffa ya rasu ta rasa jarrinta taurin zuciyarta ya karu ba ta jin taushi taushi, ta san tana da taurin kai a baya amma yanzu ya yi ƙamari tana ji ko za a yi tashin ƙiyama ne ba ta yarda a ce ita ce ke da laifi ba shi ya sa ko kaɗan zuciyarta ba ta rusuna ba.
Wanda zai yi fushi da ita ya daɗe bai yi ba.

Tafiyar Hamma Jibo da iyalansa sai gida ya yi shuru.
Hamma Abdullahi daga kai su filin jirgi ma bai dawo ba, Saddam kuma ya fita Hamma Abdulrahim ne kawai muka yana bangaren su.

Harira ta shigo ta gaisheta tana tambayanta ko akwai abin da za ta yi mata, yan zannuwanta da take sawa da dogayen riguna ta ce ta kwashe ta ɗan wanke mata. Bayan fitan Hariran ne Mami ta shigo ɗakin ta ba ta waya Daddy ne ya yi mata ya jiki suka gaisa shi yake faɗa mata ba zai samu zuwa ba tafiya ta kama shi zuwa Lagos amma gobe Mami da su Islam za su bi jirgi su koma Kaduna tunda duk sun koma makaranta.

Bayan sun gama wayar ne ta miƙa ma Mami wayarta.
Ta karɓa tana kallon ta kur kamar tana nazarinta, ita kuma tana kwance ne daman lokacin da Mami ta shigo sai ta ɗan zauna a saman gadon ta cire hijabin jikinta doguwar rigar atamfar dake jikinta ta bayyana kanta akwai hula amma ana ganin gashin ta, a tsefe yake ta so ne in suka zo nan a yi mata kitso to ba kwanciyar hankali, ga rasuwar Baffa ga abin da ya same ta, gashin duk ya yi biji biji.

Mami ta faɗa mata cutar da ya kamata, har goggle ta yi na cutar ta yi daga nan ta san tana da sauran kwana a gaba ne, amma cutar tana da hatsari ga mata masu ciki.

"Yaushe ne za ki koma ganin likita?

Mami ta katse shurun da ya gifta a tsakanin su, itama yanzu Ummu Salma ba ta mata hira in ba ita ce ta tsare ta da magana ba.

"Ranar monday ne jibi."

"Kuma ga shi gobe za mu tafi, ke da wa za ku je?

"Ni kaɗai, Harira za ta raka ni."

"Baɗɗo fa ko kuma Umma Balki ta raka ki."

Mami ta faɗa tana kallonta.

"To."

Kawai ta ce tana kauda kanta.
Ba haushin Mami take ji ba kawai itama ta san tana bayan masu cewa ba ta kyauta ba. E ta san maganganun da ta faɗa ma Ammah ba ta kyauta ba, wannan ta yarda ta kuma karɓi kuskuranta amma a kan maganar Lamiɗo tana da ja akan masu cewa ita ce ta yi masa laifi.

"Ummu Salma."

Mami ta kira sunan ta lokaci ɗaya tana matsawa kusa da ita har tana riƙo hannuwanta.

"Ɗago ki kalle ni nan."

Ta ɗago idanuwanta tana mai kallon Mami.

"Ki yi haƙuri ki daina damuwa. Baffa addu'a za mu yi ta masa, maganar Hanan kuma ki kwantar da hankali babu wanda ya isa ya karɓe ta daga hannun ki."

Idanuwan Umma Salma suka kawo ƙwalla suka kece mata a saman kumatunta.

"Mami yau kwana huɗu amma ba su dawo da Hanan ba."

"Za su dawo da ita, in ma ba su dawo da ita za a je a ɗauko ta."

Mami ke share mata hawaye da tafin hannunta.

"Ke da za ku koma Lagos da zaran Muhammadu ya dawo, tare da ɗiyar ku za ku koma in sha Allahu.'"

Hankalinta ya ɗan kwanta ta tabbata koma me zai faru Mami tana tare da ita.

Ba za ta koma Lagos ba sai Hamma Lamiɗo ya janye kalamansa in kuma bai janye ba ta rantse da wanda ranta ke hannun shi ba za ta bi shi ta koma ba.
Mami ta sake lallashinta da cewa ta sake zuwa ta samu Ammah ta sake ba ta haƙuri.

"Ko ɗazu da safe ma na shiga na gaisheta dakyar ta amsa gaisuwa ta Mami."

"Ki sake zuwa ki ba ta haƙuri abin ne ya dame ta."

"Mami nima fa ba a kyauta mini ba."

"An ji ke ma ba a kyauta miki ba, amma ke ce ƙarama ke ce ba ki da gaskiya."

Sai kawai ta yi shuru.

"Uwa ce ita, duk wanda zai so ki da cigaban ki bayan ita ne."

"Haka ne."

"To ki sake zuwa ki same ta daga ke sai ita, ki sake ba ta haƙuri."
Ta amsa da to za ta je.

"Shi Lamiɗon kin kira shi?

"E bai ɗauka ba."

Ta yi ma Mamin ƙarya domin ita dai ba za ta kira ba.
Kawai sai Mami ta ɗau wayarta tana cewa bari ta kira shi.
Received at 11:37Reactions: ❤ 4, 👍 1, 🔥 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ummu Salma na zaune ko fargaba ba ta yi domin ta san halin shi ba zai taɓa

Please Login or Register in order to submit comment