Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kaddaranta ba, da yanzu ita ce a gefen Ummu Salma tana shawara da ita, amma ga Ummu Salma can a sama an zagayeta ta yi mata nisa, ita ko tana gefe in da take ma in ta ce za ta je ita ce za ta muzanta.

An yi taro lafiya an ta shi lafiya Ummu Salma ba daliɓai ba har malamai sun karɓi lambarta suna mata magana cikin girmamawa, balle mates ɗin su, an karɓi lambarta kamar ba gobe kowa ya na so ya shige mata.
Da za tafi ne ta nemi shamsiya ta ba ta dubu Hamsin tana da canji a cikin jakarta ta tausaya mata ne amma ba domin Habib ta yi ba. Shamsiya har tana hawaye.

"Na gode sosai Ummu Salama."

Kamar ta san suna cikin wani hali, ga kuɗin hayar in da Habiba take, ita ma ba ta lafiya tunda ta yi ɓarin nan lokaci bayan lokaci tana fama da zubar jini tana bukatar zuwa asibiti. Ga rashin abinci, komai dai ya kwaɓe albashinsu ita da Habib ba shi da yawa ba zai iya rike su ba sai ga tallafin Ummu Salma, kuma ta yi mata alkawarin za ta tallafa mata da zaran gidauniyarta ta fara aiki.

Haka Ummu Salma ta shiga mota ita da ya'yanta ta bar makarantar ana ta ɗaga mata hannu. Kowa sha'awa take ba shi, rayuwa kenan wasu a cikin sun yi karatun amma babu aiki yi wasu kuma an yi aure an haɗu da gwagwarmayan gidan miji ga ƴaya a lokacin duk wanda ya ji Ummu Salma ba ta cigaba da karatu ba sai ya ce ita ko me ya sa. ? Suna ganin kamar rashin ilmin da ba ta yi ba zai katangeta da samun alheri cikin su har da Shamsiya domin a baya tana ganin boko shi ne matakin arziki. A wajen suna ta cewa suna bibiyar girke girkenta ba su san ita ba ce sai yau da ta faɗa Shamsiya ta ce itama tana bibiyan Ummu Salma amma ba ta taɓa sanin ita ba ce duk da ranar da fara jin muryan sai da ta ji kamar ta san me muryan.

Yau ga shi Ummu Salma da iya sakandirin tana auren ɗan Sarki ta samu dukkan cigaban rayuwa. Su kuma ga kwalin degree ɗin amma suna cikin kalubalen rayuwa Rayuwar nan ka bi ta a sannu kawai abin da kake tunanin ba zai yuyu ba shi yake faruwa. Ilimi na da amfani amma kar ka dogara da shi, mu tashi mu nema mu dogara da kanmu, in karatun ya yi mana amfani muna da plan B ba za mu zauna jiran Gwamnati ba, yanzu Nigeria ta yi yawa ba zai yuyu kowa ya samu yadda yake so ba. A yi ilimi amma a nemi abin da za a dogara kar a sakankance da boko ce ƙarshen tsira.

*Janafty*
Received at 19:42
15 people reacted with ❤
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ummu Salma ta so su koma Daura first week of January ne saboda yara za su koma makaranta, har sun fara shiri sai kuma Adda Suwaiba ta haihu, Ummu Salma ta san tana da ciki amma ba ta taɓa tunanin cikin ya isa haihuwa ba tunda ba ta da girman ciki sai ko ga shi ta haihu da ta faɗa ma Mai martaba Lamiɗo ta nuna masa tana so ta zauna sai an yi suna ya ce ta yi yadda take so ba zai hana ta ba.

Dalilin tsaikon tafiyarta kenan amma ita Bilkisu ta koma Daura bayan an shiga sabuwar shekara. Islam na can tunda tare da su Hafsart suka koma Daura daga Abuja tana gidan Sarki mai murabus, tare da su Amira da Hafsat tunda Ummu Salma ba ta dawo ba.

Da suka yi magana ta waya Ummu Salma ta ce me ya sa ba ta zauna a masarauta ba tunda Bilkisu ta dawo

"Ya Umma ni fa ban wani saba da Anty Bilkisu ba gwara na zauna anan ga su Amira da Hafsat."

Haka ta faɗa, kuma gaskiya ta faɗa Bilkisu ba ta sakin jiki da kowa, matar nan rayuwarta ma na dabam ne, ba irin na sauran mutane ba ne shi yasa ba ta damun Ummu Salma domin ta fahimci har danginta ba da kowa take shiri ba sai wanda Allah ya haɗa jininsu, ballatana ita kishiya da zuwan ka zo na zo ne. Suna haɗa sati ba su haɗu da juna ba, ba ta shigowa bangarenta itama Ummu Salma ba ta shiga, amma yaran suna zuwa wajenta haka ma Banafsha, su Debora dai suna shigowa barin ma Hidaya, Sabuwa ce sai jifa jifa. Sun fi haɗuwa wani lokacin a bangaren Mai martaba ko kuma in ta je can gidan Sarki gaishe shi ta ganta, tana gaisheta duk in da ta ganta ta amsa a tsume, amma bayan gaisuwa wata mgana mai tsawo bai ta taɓa shiga tsakaninsu ba, miji ɗaya dai suke aure amma rayuwar kowa tsarin shi yake yi, shi kuma Hamma Lamiɗo bai damu ba, ba shi da yawan saka ido, kuma ya san haka suke tsarin su ya yi masa daidai muddin ba a zaman gaba kuma ba a faɗa.

Da niyyar zama ta yi sunan Adda Suwaiba ta tsaya amma kuma kana naka Allah ya gama na shi, mura ta yi mata mugun kamu da ta saka mata zazzaɓi mai zafi, kuma wannan cikin ma ba ta sha ruwan sanyi ba, ba ta yi laulayi mai zafi ba, amai ma sau uku ta taɓa yi ta dai san tana cin abinci sosai shi yasa ta fara kiba da naman wuya.
Ta yi tunanin sanyin December ne ya kamata a garin Adamawa. Har Banafsha ma sai da ta kwanta zazzaɓin nan sai da suka je suka ga likita aka ba su magunguna.

Sunan da ba ta samu ba kenan tana gida a kwance, muryanta har ta dishe ta yi ƙatuwa saboda mura, in suka yi waya da Mai martaba sai ya ce muryansu iri ɗaya yanzu ba maraba ta yi ta masa shagwaɓa tana masa kuka shi kuma yana jin daɗin tsokanarta.

Mami ta zo suna an yi suna lafiya mace ta haifa yarinya ta ci sunan mahaifiyar Adda Suwaiba Zainab, bayan sunan ne Ummu Salma ta yi ma su Mami bayanin haɗuwarta da Barrister Salamatu da shawarwarin da ta ba ta, da cewa sai ta koma Daura in sun sake yin magana da Hamma sai su ga ta yadda za su fara kudirinta kafin shekaran nan ta kare Foundation ɗin da za ta kafa ta yi ƙarfin da za ta fara aiki ba ɓata lokaci.

Sun yi na'am da shawaranta, Mami ta ji Ummu Salma ta gama birgeta duk abin da za ta yi za ta ce sai ta yi shawara da mijinta. Kenan hakan ya nuna tana girmama Lamiɗo ba ta iya aiwatar da komai sai ta faɗa masa ya amince sannan, tana alfahari da hakan, ko ita ba ta yin wani abu ba tare da sanin Daddy ba abu daya ta taba aiwatarwa bai sani ba haɗin auren Ummu Salma da Lamiɗo, wannan kuma ba ta son kowa ya sani ne shi yasa ba ta faɗa masa ba amma tana da tabbacin in da ta faɗa masa zai ba ta goyon baya tunda a komai na ta yana supporting ɗin ta, in ka samu miji mai goya maka baya a duk abin da ka saka ma gaba, to ka gode ma Allah domin watarana za ka cimma in da ba ka yi tsammani ba.

Kwana biyu Mami ta yi ta ce za ta koma ba ta zo da Faruk ba yana gida tare da Daddy, sai ta ce a ba ta Banafsha ta tafi da ita ta yaye ta a can tunda nan in ta ga Ummu Salma tana rigiman nono, Ammah ta ce a barta ta yi wata goma sha biyar sai a yayeta, Mami ta ce aa gwara a yayeta yanzu tunda shekararta ɗaya har da wata biyu, kuma lafiyanta lau ba abin da ba ta ci, babu matsala in an yayeta a yanzu.
Received at 08:04Reactions: ❤ 14, 👍 1
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ummu Salma ta ce bari ta kira Hamma Lamiɗo ta faɗa masa, ta kira shi bai ɗauka ba sai ta tura masa saƙo amma har dare bai kira ba sannan bai ba da amsa ba. Da ta hau whatsApp ta yi masa mgana ta ga ya duba saƙon ta amma bai ce komai ba sai ta yi masa uziri.

Amma har dare shuru kuma washegari Mami za ta koma Kaduna.
Tana ɗakin ta na cikin bangaren Ammah Mami ta shigo tana tambayanta yadda suka yi da Lamiɗon.

"Mami bai kira ni ba, na yi masa saƙo nan ma shuru."

"To ni bari na kira shi na faɗa masa."

Mamin ta faɗa tana barin ɗakin, Ummu Salma barci ta yi domin cikin nan cutar barci ya saka mata, ta yi da rana ta yi da safe daran ma ana mangariba za ta fara jin barci sai ta yi da gaske take zama sai ta yi sallar isha'i, ko gajiya da barcin ma ba ta yi amma ta farka sau nawa cikin dare in yunwa ta ƙwaƙuleta.

Yanzu ma sallar ta idar ta ci abinci ta bi lafiyan gado su Hanan suna can bangaren Baɗɗo can suke yi mata hiran, sun yi ma waya da Shamsiya da safe tana tunanin gobe za ta roƙi Hamma Saddam ya kai Hanan gidan babanta ta yi kwana biyu kafin su koma, ba saboda Habib ba ne saboda Shamsiya ce da take son Hanan tana yi mata so kamar ɗiyar cikinta watakila don ba ta samu haihuwa ba ne.

Ba ta san ko Mami sun yi wayar da Hamma Lamiɗo ba, sai da safe ta ga tana shiri ta ce a haɗa mata kayan Banafsha tare za su tafi, sai ta tambayi Mami ko sun yi waya da Lamiɗo sai ta amsa mata da sun yi magana.
Ba ta kawo tunanin wani abu ba, domin a mganarta ba ta yi tunanin ta yi laifi ba.

A ranar Mami ta koma Kaduna tare da Banafsha, ita murna take yi ba ta yi tunanin in ta tafi ba yanzu za ta dawo ba sannan Ummu Salma ba ta fito ba yaran ma aka hana su, domin kar ta gansu ta yi rigima. Bayan sun tafi itama Hanan Hamma Saddam ya kai ta gidan su Habib tare da su Sultan suka je tunda a mota ne, Hanan ta ce ita kwana ɗaya za ta yi gobe a zo a ɗauketa Hamma Saddam ya dawo yana faɗa ma su Ammah.

"Yarinya ta gaji da zuwa wannan gidan ta ce Uncle ni gobe ka zo ka ɗauke ni "

Ya gama faɗa yana ta dariya Ammah ma sai da ta yi mirmishi.

"Saboda su Sultan ne, ba ta son barin su ne."

Ammah ta faɗa Amma sai Hamma Saddam ya hau cewa ba saboda haka ba ne, wannan gidan ai suna fama da rayuwa shi bai ma ga amfanin kai Hanan wajen su ba, uban fa ya ce ba ya son cikin me ya sa yanzu kuma zai karɓa.

"Ai ba a canza ma tuwo suna Saddam, Habib shi ne uban Hannatu, kuma in ta je ba laifi ba ne ai ba wajen su take zaune ba, kuma ban da abin ka ma suna komawa kafin su dawo an ɗauki lokaci."

Suna cikin maganar ne Ummu Salma ta fito ta tashi daga barcin tana jin yunwa ta zauna a gefen Hamma Saddam tana tambayan Harira.

"Suna can bangaren Aisha."

Wayarta ta koma ɗaki ta dauko ta kira Baɗɗo tana tambayanta abin da ta dafa, ta ce tuwo ne miyar zogale.

"Bana jin ci, ki ce kawai Harira ta zo ta dafa mini wani abu."

Baɗɗo ke faɗin me take so sai ta dafa mata anan sai ta ce ta bari kawai Hariran ta yi bayan sun gama waya Ammah ke faɗin ga tuwon ma nan da Baɗɗo ta kawo da yawa ta ɗiba ta ci mana.

"Ammah ni ba tuwo nake so ba."

Ammah ta kalleta amma ba ta yi magana ba.

"Girman ki ne Sarauniyar Daurama, ko talo talo kika ce za ki ci sai a nemo miki."

Ya gama faɗa yana dariya Ummu Salma ta daki kafaɗan shi tana hararan shi, Ammah na zaune kanzil ba ta sake cewa ba sai da Saddam ke ba da labarin sun yi waya da Hamma Lamiɗo akan aikinsa ya ce ya jira shi soon, lokacin da ya tura masa VC ɗin sa ya ce ya tura Mai martaba mai murabus a wancan lokacin sai jikinsa ya tashi shi yasa aka samu tsaiko amma yanzu za a neme shi in sha Allahu.

"Allah ya amsa Amin."

Ammah ta faɗa Ummu Salma da Saddam suka sake amsawa da Amin a tare.
Harira ce ta shigo ɗauke da Junior ta miƙa ma Ammah shi ta yi saurin karɓan shi, tana masa wasa tana kiran shi da maigida na, Saddam na gefe ya ce Ammah yanzu kamar Junior ne ya kwace son da kike yi ma Baffa mu ai ba ma kya maganar mu."
Received at 08:04
12 people reacted with ❤
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ta harare shi ba ta yi magana ba ya koma yana dariya. Ummu Salma na taya shi, kuma gaskiya ya faɗa Ammah yadda take son Junior kuma nunawa take kowa na gani ba kunya ba kamar sauran jikokinta da take nuna musu halin ko in kula, amma wannan har goya shi take yi ya yini a wajenta in ba nono zai sha ba, da yake ma ba shi da rigima sosai.

Suna ta gulmanta ƙasa ƙasa ba ta ma san suna yi ba tana ta yi masa wasa, yana bangala dariyansu na yara, Harira kuma ta tafi kitchen Ummu Salma ta ce ta dafa mata indomie ta saka kayan miya amma kar ya yi yaji. Mintina kaɗan ta gama ta kawo mata ba ta ci ita kaɗai ba Beena ta zo ta zauna ta ce za ta ci Sultan kuma ba shi da wannan yana da kamewa kamar baban shi. Beena ce kamar ba ɗiyar Lamiɗo da Bilkisu ba, kamar ɗiyar Ummu Salma shegen surutu da ƙiriniya irin ta irin Hanan shi yasa ta so ta zo ɗaya yanzu ɗin ma tambaya take yi yaushe Hanan za ta dawo Ummu Salma ta ce gobe.

"Mahma ni dai zan je wajen Hanan."

Beena ta faɗa tana kallon Ummu Salma.

"Aa ki bari za ta dawo."

"No ni ina so na je za mu yi wasa."

"Ke wannan gidan ai ba za su iya ɗaukan nauyinku ke da Hanan ba, madaran da kuke shan tea da ita ma ba za su iya siya ba."

Hamma Saddam ya faɗa yana dariya Ammah ta yi masa dakuwa tana ba zai daina ba ko?
"Na daina Amnah in sha Allahu "

"Ba ka dariyan kaddaran wani domin kai ma ba ka san mai gobe za ta haifar ba."

"Haka ne, amma mu dai ba mu cuci kowa ba Ammah, in sha Allahu rayuwarmu za ta cigaba da kyau har ƙarshe."

Ta amsa da Allah ya sa, rigimar Beena na sai ta je wajen Hanan Saddam ne ya ɗauke ta suka fita ta girma shekaran ta Bakwai da wattani Hanan ce biyar Sultan kuma yana cikin shekarunsa na goma sha ne shekara mai zai gama primary, Hanan na primary 1 Beena kuma 3.
Da yake yaran yan hutu ne suna cikin daula girman jikinsu ya ɗara shekarunsu ga wayau da iya mgana turanci da labarci kan ya zauna a bakinsu sosai a dangi ma yaran abin sha'awa ne kowa kallon su yake yi, mate ɗin ta ma da suka haɗu wajen renioun ma ta ga suna saka su a status har tambayanta suke yi wai yara nan nata wata makaranta suka yi ne? Ta ce a can Lagos ne, mamakin ƙoƙarin yaran suke gani.

Kowa yanzu neman ta yake yi a rana ba ta san adadin wayar da take amsawa ba, sai dai ta ji ana cewa wane ne kaza na makarantarku ana roƙonta don Allah ta yi saving lamba matan kuma suna ta kamun kafa suna kawo matsalolinsu da cewa in ta fara taimako ta saka sunan su ta ce ba matsala za a yi komai cikin tsari za kuma a ba da tallafin ga waɗanda suka cancanta ne.

Hanan washegari ƙanin Habib ya dawo da ita, sai bayan tafiyan shi ne Shamsiya ta kira ta tana magana dakyar ta ce ba ta da lafiya shi ya sa ba ta zo ba. Ga Hanan nan sun gode sosai. Ummu Salma ta ce ba komai, ta ga an dawo da ita da tsaraban bickit da su minti tana can falo tare da yan'uwanta.
Ta yi mata sannu da jiki, Shamsiyar na tambayar yaushe za su koma!? Ta ce ba ta saka rana ba amma a cikin satin da zai shiga saboda makarantar yara.

"Allah ya maida ke lafiya."

Ummu Salma ta amsa mata da Amin suka yi shuru na wani lokaci.

"Ummu Salma."

Ta kira sunanta ta amsa tana sauraranta.

"Don Allah ki yi haƙuri."

"Ba komai ai na faɗa miki ya wuce."

"Habib..'

Ta yi shuru ta kasa faɗin maganar da take son faɗa.
Ita ko Ummu Salma tuni ta haɗe fuska kamar Shamsiya na ganinta. Ita fa tsanar da ta yi ma Habib ko sunan shi ta ji an kira sai ranta ya ɓaci.

"Ki yafe masa, don Allah."

"Na ce na yafe ba wani abu."

Ta faɗa cikin kosawa tana son katse wayar ne ta gaji da jin mgana ɗaya.

"To in haka ne ga shi ku gaisa."

Ummu Salma ta yi kasaƙe, tana jin Habib ya amshi wayar ya yi sallama da muryansa, wacce ba za ta bace mata ba muryan da a baya ta kasance lu'u lu'u a gare ta amma a yanzu ba muryan da tsana sama da muryansa.

Ta ji ya yi sallama ya ƙara yi ta yi shuru ta kasa amsawa daga ƙarshe ma sai ta kashe wayarta. Tana gani Shamsiyar na sake kiran ta ba ta ɗauka ba.
Received at 08:04
12 people reacted with ❤
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ba ta fatan wata mu'amala ta sake haɗa ta da Habib har abada Shamsiya ma kawai saboda Hanan ne sannan tausayinta take ji amma ko ita ba ta son ta shigo jikinta har abada ƙawancen dake tsakaninsu ya ƙare tun a shekarun baya.

Sako ta tura ma Shamsiyar domin ba ta so nan gaba ta sake yi mata wannan gangancin.

"In kina so na cigaba da amsa wayarki ki nisanta ni da mijin ki, ba ni da wata alaƙa da shi, laifi ne ya roke ni tuntuni na ce na yafe ba bukatar wani abu kuma. Don Allah mu girmama junan mu ko saboda Hanan."

"In sha Allahu hakan ba zai sake faruwa ba. Ki yi haƙuri."

Shamsiya ta turo mata reply ta karanta ba ta bi ta kanta ba. Habib yana cikin wani shudaɗɗen babi ne na rayuwarta ya shuɗe har abada yanzu Lamiɗo ne a rayuwarta saboda haka ba ta buƙatar tuna rayuwarta ta baya Hanan ce tana zuwa wajen su amma har abadan ba za ta ba shi ɗiyarta ba kamar yadda ya ce ya bar mata, to haka ne Hanan ɗiyarta ce har gaban abada sai dai ya dinga samunta a matsayin aro.

Habib daman ya san Ummu Salma ba za ta yi magana da shi ba Shamsiya ce ta matsa masa saƙon ma na Ummu Salman suna tare ya shigo shi yasa ya gani.

"Ka yi haƙuri."

Shamsiya ta faɗa tana kallon shi, ya girgiza kai kawai yana ɗan mirmishi.

"Ba komai ni daman ban matsa ba, mai muhimmamcin yafiyar ne kuma tunda ta yafe shike nan."
Bai sake magana ba ya tashi ya fita ta bi shi da kallon tausayi tana hawaye.

Ko bai fada ba ta san yana son Ummu Salma har yanzu, sun sha suna mu'amalan aure ta ji yana kiran sunan Ummu Salma ba ta taɓa nuna masa ba, ita kaɗai take shan kukanta, koma mai ya faru ita ce sila, ita ce ta yi shuru amma Habiba ƙara ta kawo shi gidan su wai yana tare da ita amma yana tunanin matar auren da har ya mutu ba zai sake samun zama da ita ba, ta tona masa sirrin shi a idanuwan kowa har sakinta ya so yi Shamsiya ce ta hana shi ta danne shi. Habiba kaɗai aka bar Habib da jarabawarta mai zafi ce a gare shi, bayan wasu matsalolin rayuwa musamman talauci da halin babun da suke ciki, aikin koyarwa ne sai karshen wata karshen watan ma kafin nan duk an ci ba shi ga albashin babu yawa.

Godiyarsa Allah Shamsiya tana taimaka masa shi yasa in ya kalleta sai ya gode ma Allah da ya sa itama bai rasa ta ba da yanzu rayuwarsa na cikin uku, yana karɓan sakamakon abin da ya aikata daki daki, ga takardun amma aiki ya gagara har ya gaji da tura CV Alhaji Sherif ma duk ya karɓa ya tuttura amma ba a dace ba a hakan ma godiya yake yi ma Allah da ya barsa da lafiyarsa. Lafiya jari ce in da ya rasa lafiya da komai ya kwaɓe masa. Shi ya yakice Ummu Salma a cikin rayuwarsa yana tunanin ita ce za ta shiga garari sai ga shi, ita ce ke cikin ni'ima shi kuma rayuwarsa na cikin garari, soyayyarta dake zuciyarsa ma kaɗai ishara ce ga masu hallayar irin na shi.


*

Ummu Salma da yara sun koma Daura bayan watan January ya raba tsakiya. Ko da ta koma ba ta samu Islam ba ta koma Kaduna za ta fara registration ɗin fara jami'ar Kaduna.

Ranar da suka dawo ko bangaren Mai martaba ba ta je ba, tana idar da sallar isha'i barci ya rinjayeta.
Washegari sai ta je can bangaren tun mangariba saboda cutar barcin dake damunta yanzu ko ita ba ta iya yi ma kanta wani abu, girkin ma Harira ce ta kama mata suka yi.

Ko da ya shigo bangaren daga Fada har ta kwanta ta fara barci amma barcin bai yi nisa ba, ta kunna littafin Rufaffen Duma na marubuciya Ummulkhairi Sani Panisau a tashar tsakar gida tana sauraro, ta fara ji amma barci ya tafi da ita, wato kana girma rayuwarka na canzawa yanzu ko da kuɗi aka ce ta tsaya ta yi kallo ba za ta yi ba, karatun ma sai dai ta ji Audio.

Ta san dai sun yi magana da Hamma amma ba za ta tuna me ta ce masa ba barci ya fizgeta sai da ya dawo daga masallaci ne sallar asuba tana zaune saman darduma tana azkar lokacin da ya shigo, ya cire babban rigan shi da wani farin harami sannan ya hau saman gado ya ɗau wayarsa yana dubawa.
Received at 08:04
14 people reacted with ❤
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ta shafa addu'arta a duka jikinta sannan ta miƙe ta yaye hijabin jikinta, rigar jikinta fara ce mai santsi ta ɗora zani a saman rigan da za ta yi salla duka ta cire ta watsa su saman kujeran dake bedroom din sai jin ta kawai ya yi a saman jikinsa.

"Good morning my king."

Ya kalleta amma kuma bai bar kallon wayarsa ba.

"Kin tashi lafiya?

"Sarauniyar barci."

Ya gama faɗa yana ɗan jan karan hancinta.
Mirmishi ta yi kafin ta ce" Babynmu ne ke saka ni yawan barci da kasala."

Ta gama faɗa tana jan hannunsa zuwa ƙasan maran ta dole ya ajiye wayar ya tallabeta, shafa cikin yake yi ita kuma tana shafa hannunsa, cikin na ta har ya ɗan turo.

"Shi ne ya sa shekaranjiya aka ƙyale ni ko?

"Ban ma san na yi barci ba."

Ta gama faɗa tana yar dariya, ta cigaba da ba shi labarin barcin da ta dinga yi a Jimeta har Ammah na faɗin kamar wata kasa.

"Ba fa na gajiya ko yini zan yi na kwana ina barci fa."

"I see."

"Jiya ina mgana shuru, kina ta dai kiran sunana na gaji da amawa na ƙyale ki."

Ta ƙyalƙyace da dariya tana shafa ƙirjinsa.

"Ni dai na san na ji muryanka amma ban san abin da ya faru ba."

"Kina magagin barci."

"Ga waya a kunne sai da na kashe"

Ya ba ta amsa yana shafa gashin kanta zuwa wuyanta ƙamƙame shi ta yi

"I miss you."

Ya yi shuru bai yi magana ba amma ya ɗora kan shi a saman kanta, ita kuma tana kwance a saman jikinsa ya yin da shi yake kwance a saman gado.

"Ka ji."

"Na ce na yi kewar ka? Ko ba ka yi kewata ba ne?

"Na yi"

Ya faɗa muryansa a dishe kamar mai jin barci ta ɗago tana kallon shi akwai haske a ɗakin suna masu kallon

Please Login or Register in order to submit comment