Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

d'auki zamansu matsayin kishi har ma abun yake damunta Amma ita ko kad'an ba zama kishi take da ita ba.Ammei ta kau da tunaninta ta koma sama wajen HUYAAM......



Wajen k'arfe biyar da Rabi Fulani Salamatu ce zaune acikin Wani d'akinta na musamman Dake nan samanta tana zaune kan kujera ita da Hajiya Lubabatu.hajiya Lubabatu ta numfasa tace.


"Ai ni ban d'auka raunin ya kai har haka ba Saida naje na gani yanzu?...." Fulani Salamatu ta tab'e Baki tace.


"To ke kin Gani ma ni ko zuwa gun yarinyar banyi ba iya kacina falon uwarta".. Hajiya Lubabatu ta sauke numfashi tace.


"Nima abinda yasa naje Dan kada ace agaban 'ya'yan ka akayi kuma sunje sun fad'a Maka Amma banjeba shiyasa najeni".


Fulani Salamatu tace.

"Kema kenan aini wallahi banyi niyyar zuwa ba Mai martaba ne kawai ya tilasta min zuwa Amma wallahi da Dan kaina ne ni kan banyi niyyar zuwa ba in yaso k'afar ta rub'e". Hajiya Lubabatu tace .


"Aikuwa dai k'afa tayi sun tum Baki Gani ba Anya mako k'afar nan zata warke kuwa?...."


Fulani Salamatu gyara zama tace.


"Dan Allah fa k'awata? Allah yasa ma karta warke ta zauna Ahaka".ta fad'a tana Wani murmushi.
Hajiya Lubabatu tai dariya ta Bata hannu suka tafa tace .

"Dad'i na Dake k'awata bakida dama". Fulani Salamatu tace .


"Dakinsa yadda na tsani yarinyar nan itada da Afeef ke duka yaran ma da bakiyi wannan maganar ba k'awata".Hajiya Lubabatu tace. "yauwa ni kin ma tuna min k'awata" saikuma ta fara kalle kallen d'akin kafin Kuma tai k'asa da murya tace.

"Ina fatan dai kin kora wad'an nan munafukan hadiman Baki waje dai ko?..."

Fulani Salamatu tace.

"Tun yaushe Ai yanzu idan sunga nayi Bak'i ma basa zaman nan can compound suke tafiya".


Hajiya Lubabatu tace.

"yauwa,to Kinma tuna min Ashe Afeef d'in ya kusan dawowa k'asar nan?..." Tafad'a tana kallan fulani Salamatu.

Fulani Salamatu tace with compused.


"Afeef d'in?..."Hajiya Lubabatu tace .


"Shidai Nima haka naji zancen Yana yawo agidan nan Dan ban tabbatar ba". Fulani Salamatu tace.


"Hmm Babu batun Wani tabbatar wa Tunda kika ji ana zancen ai ya tabbata kenan zai dawo d'in,Amma aini ko ubansa Bai fad'a min ba kodan ni bama ya sakoni cikin harkar yaransa yanzu". Hajiya Lubabatu tace.


"Aikuwa dai haka naji".. Fulani Salamatu tace.


"Aini d'aukata sai bikinsu bahijja zaizo ai". Hajiya Lubabatu tace .

"To dai gashi nan idan ma yazo d'in yanzu ya koma ai zai iya dawowar lokacin bikin. nifa k'awata so nake da angama bikin su bahijja so nake afara zancen nasu bikin shida salimata tunda ban samu za'ayi dashi da bahijja ba ai sai ayi dashi da saliman ko?..." Ta fad'a tana kallan fulani Salamatu.


Funali Salamatu da tunda ta fara magana take mata Wani kallo sai kuma tai saurin dai dai fuskarta tace.


"Indai wannan ne karki damu k'awata wai sau nawa zan fad'a miki aini nai miki ALK'awari Nima indai zaki tayani cikar burina ai Babu damuwa kamar Afeef ya AURI Salima ne". Hajiya Lubabatu tace.


"Mai zaina Hana kuwa k'awata Babu abinda zai Hana in Allah ya yarda yanzu dai yaushe ya kamata mu koma gunnan?..." Fulani Salamatu tace.


"yanzu baya nan yayi tafiya Amma da Zarar ya dawo zamuje d'in". Hajiya Lubabatu tace.


"To shikenan Allah ya kaimu lokacin".sai Kuma ta kalli agogon bangon Dake manne a bangon d'akin Ganin shida na yamman Ranar Saura yasa tace.


"Laa!! bari na tafi tun kafin yaran nan su dawo su Tarar mu".ta fad'a tana mik'ewa tsaye itama Fulani Salamatu mik'ewar tai tana cewa.


"tafiya Kuma?.." Hajiya Lubabatu tace.

"Wallahi sai dai Gani na biyu kuma". Fulani Salamatu ta rakota har k'ofar falon sannan ta koma ciki tana cewa azuciyarta lallai ma matar nan Kina ganin zan bari 'yarki ta AURI Afeef batareda da ni nawa burin ya cikaba ai ko ya cikama bazan tab'a bari 'yarki ta AURI Afeef ba tana fad'ar haka ta shige d'akinta....



Bayan magrib gabad'ayansu su Huda suna zaune a falon k'asa har Ammie Aziza ta shigo falon bakinta d'auke da sallama Ammie ce ta ansa mata Amma su Huda suna kallan itace suka d'auke kansu har ta k'araso cikin falon ta zauna kasan carpet tana gaida Ammie kamar wata miutuniyar kirki.


Ammie ta ansa mata da kulawa tace.

"Ina su Ramla?.."Aziza tace lafiya lau Ammie sai Kuma tace.


"Dama nazo duba Huyaam ne?..." Ta fad'a itama kanta tana Jin nauyin maganar.Ammie ta Kalli Huda tace.

"Huda raka Aziza d'aki tazo duba Huyaam ne.".


Babu musu Huda ta Mik'e daga zaunan da take Aziza tabi bayanta suka haura sama har zuwa d'akin Ammie suka Tarar da HUYAAM na bacci Aziza ta Kalli k'afar ganin yadda ta kumbura . Amma ko d'ar Bata jiba bare taiwa Huyaam d'in sannu haka nan ta juya ta fita daga d'akin.huda ta kasa hak'uri tabi bayanta a fusace tace.

"Aziza Yanzu ko sannu baza kicewa HUYAAM d'inba bayan ke kika ji mata ciwon?...".Batare da Aziza ta juyo ba tace.

"Ai na mata".Huda tace.

"Haka zakice? to bari Kiji Aiko kinyi na farko kinyi na k'arshe Aziza Dan idan ika K'ara yiwa HUYAAM Irin wannan muguntar wallahi ni da kaina zan rama mata". Aziza batace komai ba ganin sun Sakko kasa tana kallan Ammie tace.

"Sai anjima Ammie".

Ammie tace .

"To sai anjima". Aziza tana fita daga falon Ammie ta juyo tana kallon huda tace.


"Mai yasa baza ku ansa mata ba sallamar taba?..."Huda tace.


"Ammie dafa muka shiga d'akin ko sannu bataiwa HUYAAM d'in bafa ".


Ammie tace.

"Da tayi ta kartayi babu abinda zai Sauya 'yar uwarkuce dai bana son Haka".Huda tai shiru batace komai ba Ammie ta mik'e ta haura sama.......






07066508376________
'Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD


*<9 HUYAAM <9*



*NA*



*__NAJA'ATU UMAR FAROOQ__*


*__(MRS SARAKIES =؋)__*



*PAGE 1 5 *



*Tallah! Tallah!! Tallah!!!*


*Ina kuke hajiyoyin gidan nan,nace Ina kuke hajiyoyin gidan nan?to maza ku matso ga wata garab'asa ta zomu har inda kuke=؃=؃?.*


*Hajiya kaya Kikeso na fita kunya cikin taro ku Kuma so kike kallo ya koma akanki acikin Taron mata idan kika shiga biki ko suna ko Kuma Wani taro na musamman.to maza idan kina so ki kankarowa kanki mutunci kizo UK collection and gallery mu gwan gwajeki da kayanmu masu quality Wanda zaki gaji ki ajiye Dan kanki Amma badai ya mutuba Muna sai da kaya kamar haka=G*


*Atamfofi da lesses*
*Abaya*
*Shadda*
*Hand bag*
*Shoe*
*Veil na manya Dana Yara*

*Socks rin hands made d'in nan masu net*.

*Hula ta 'yan Gayu*

*Siyan D'aya ko sari*

*Duk zaki samu kan Farashi Mai sauki kedai ki garzayo UK collection & gallery Kisha Mamaki*

*Domin ganawa damu ko magana damu kai tsaye ku tun tub'emu kai tsaye ta wannan number kamar haka*=I08135305790

*Sai mun jiku =؃=؃=؃*


<9<9<9<9<9<9


*Bismillahirrahmanirrahim*



__________&


Haka Huyaam ta dinga fama da k'afarta har bayan kwana biyu. A wannan lokacin ne Kuma ta samu sauk'i daga zugin da k'afar take mata, duk da tana Shan magun gunan da akai mata prescription Amma sauk'i na Allah ne saboda ba k'aramin rauni Aziza ta ji mata ba a k'afar nan wai a Hakan ma Dan tana samun kulawa sosai..yau Laraba yanzu haka tana zaune a falon downstairs wajen k'arfe biyar da Rabi na yamman Ranar tana Zaune tana Shan iska a nan falon,zaman d'akin ne ta gaji dashi shiyasa tasa Ammie ta kawota ta zaunar da ita. k'afar ma da sauk'i tunda gashi har bandage d'in ya fara d'agowa sama da Kansa alamar dai zai iya fita da kansa tana zaune tana kallo hankalinta gabad'aya Yana kan TV tana kallan Indian series d'in da ake a tashar Bo 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~llywood.knocking d'in k'ofar falon da akai tare da sallama yasa ta d'aga kai tana kallon k'ofar harya Bud'e ya shigo ta Bud'e ido da mamaki take kallansa harya k'araso tsakiyar falon kafin Huyaam ta sauko idonta k'asa daga kallonsa da takeyi ta Dan motsa lips d'inta kad'an tace.


"Sannu da zuwa ya chiroma".ta fad'a tana k'ara sunkuyar da kanta k'asa".Aziz chiroma da tun shigowarsa falon da Yay tozali da Huyaam yake murmushi ya zauna nan saman kujerar falon idonsa na kanta har lokacin yace cikin k'asa da murya.


"Lafiya lau Huyaam ya kike?..."ya fad'a Yana murmushi.

HUYAAM tana wasa da yatsun hannunta tace.

"lafiya lau".


Yace " Ina Ammie take ? ke bakije islamiyar ba yau?...." Ya fad'a Yana kallanta kamar zai cinye ta .


Huyaam tai shiru batai magana ba Yana kallan k'afar ta_ta yace .

"Subhanallah"! Meyasa sameki? Dan Daya shigo Bai kula da k'afar ta_taba.."ya fad'a Yana kallan k'afar Huyaam da tausayawa.


Kamar Huyaam baza tai magana ba sai Kuma tace.


"Ciwo naji". ta fad'a a tak'aice.Aziz chiroma yace.


"Garin Yaya Hakan ta faru?..." Ya fad'a da tausayawa.huyaam zatai magana Ammie ta shigo falon, take HUYAAM ta Sauke ajiyar zuciyar salama Dan taji Dad'i da Ammie tazo da Batasan ya zatai ba dama ,duk a takure take jinta zaman nan a Aziz yayi, da zata iya tashi ma da tuni ta tashi ta Bar falon... da murmushi a fuskar Ammie ta k'arasa saukowa stairs d'in tana kallan Aziz tace .


"A'ah! WA nake Gani agidan kamar Aziz chiroma". Ammie ta fad'a tana murmushi ta k'arasa shigowa cikin falon ta Zauna nan saman kujera.


Aziz Chiroma na murmushi ya zamo daga saman kujerar da yake kai ya gaida Ammie.


Ammie na murmushi ta ansa masa tace.

"Lafiya lau Alhamdulillah Ya bichin chiroma?..."

Aziz Chiroma yay murmushi yace.


"lafiya lau Alhamdulillah Ammie ".

Ammie tai murmushi tace.

"yaushe kazo ka?...."

Ya koma kan kujerar ya zauna yace .


"Ban Dad'e da zuwa ba d'azu nazo". Ammie tace.

"Masha Allah sannu da zuwa,Amma ai zaka mana kwana biyu kafin ka koma ko kuma ma dai ka dawo Kenan?...." Ta fad'a tana kallansa ".


Aziz Chiroma ya shafa kansa Yana murmushi yace.


"Ai Ammie tunda aka had'ani da wahalar nan kuma shikenan zaman gidan nan yamin wahala kwata kwata bana samun zama".

Ammie tace .


"Gaskiya ne to Allah ya taimaka yasu fulani Asiya?..." yace. "Lafiyansu lau suna gaida ku...." Ammie tace.


"Muna ansawa".Baba magajiya ce ta shigo falon bakinta d'auke da sallama Hannunta rik'e da tray Wanda ta d'orowa Aziz chiroma ruwa da drink's akai ta k'arasa har gabansa ta aje tray d'in nan saman center table d'in sannan ta tsugunna har k'asa ta gaidashi. chiroma ya ansa mata da kulawa baba magajiya ta mik'e ta bar falon.

Ammie tana kallan Aziz chiroma tace.

"Kasha ruwa chiroma". Aziz chiroma yay murmushi baice komai ba. ita dai HUYAAM tunda ta samu Ammie ta shigo falon idonta Yana kan TV tana kallanta Amma Kuma tana Jin idon Aziz chiroma akanta lokaci lokaci Yana Kallanta.


*Waye Aziz chiroma?*

A tak'aice.


Ai nihin sunansa Abdul Aziz ne shine ake ce masa Aziz.


Aziz Chiroma D'a ne ga Hajiya Lubabatu shine D'an ta na fari yayan su bahijja ne Amma ba ubansun D'aya ba uwa kawai suka had'a.ma'ana dai ba baba turaki bane babansa ba kamar yadda yake mahaifin su bahijja.shi Aziz chiroma D'an gidan sarkin bici ne Wanda ya rasu. Dan baba turaki ba'a budurwa ya AURI Hajiya Lubabatu ba,matar sa ta farko rasuwa tai kusan shekararsu biyar da ita to Basu ta'ba haihuwa da ita ba har Allah ya karb'i Ranta bayan gajeriyar jinyan data Sha. to shine bayan kamar shekara Uku da rasuwarta baba turaki ya auri Hajiya Lubabatu sakamakon itama da mijinta sarkin bici na farko daya rasu alokacin shekarar Aziz Wanda ake ce masa chiroma ayanzu D'aya a duniya, to shine bayan tayi idda da kusan shekara D'aya aka had'asu da baba turaki har suka amince da juna sukai AURE. data tare kuma tace zatazo da Aziz chiroma baba turaki Bai Hana taba ya amince mata. da k'yar ma Dangin babansa suka yarda ta taho tashi gidan acewarsu d'ansu bazai zauna zaman agolanci awani gidan ba. A tak'aice dai Saida aka kai ruwa Rana sannan Dangin mijinta suka yarda ta taho da Aziz masarautar kano.anan yay Karatunsa tunda ga nursery, primary,har secondary zuwa tertiary institutions.saida ya girma Kuma sannan suke so su janyeshi ta hanyar bashi sarautar da yake kai ayanzu wacce ba'a Dad'e da yin bikin bashi sarautar ba Amma sarautar an Dad'e da Yi mishi ita tunda dad'ewa bikin nad'a shinne dai ba'ai ba sai kwanan nan wato chiroman bici itace sunan sarautar da aka bashi .tunda aka bashi kuma sai nauyi Yay masa yawa Dan sai yayi wata D'aya baizo kano ba. da baya wuce 2 weeks Baizo ba Amma yanzu sai ya kai wata D'aya Bai zo ba .wannan kenan Ina fatan Mai karatu ya Gane.


Aziz chiroma ya mik'e Yana kallan Ammie yace.

"Bari naje Ammie".


Ammie ta d'aga kai ta kalleshi tace.

"tafiya zakai Aziz?..."


Aziz yay murmushi yace.


"eh Ammie ai Ina nan zan D'anyi kwana biyu kafin na koma in Sha Allah ".


Ammie tace.

"To shikenan Aziz mungode sosai kahuta gajiya". Yace.

"in Sha Allah Ammie". Yana kallan Huyaam yace.

"Allah ya K'ara lafiya HUYAAM.

HUYAAM ta D'anyi masa murmushi Wanda iya karsa saman lab'b'anta tace cikin zazzak'ar muryarta.


"Ameen nagode". ta fad'a a saman lab'b'anta.Aziz ya fita daga falon gabad'aya". Ammie juya tana kallan Huyaam Ganin Yadda mood d'inta ya canza lokaci D'aya tace .


"Kina Jin Wani ciwo Yanzu ne Huyaam?..." HUYAAM ta juyo tana kallon Ammie sai Kuma ta girgiza mata kai tace..

"Babu komai Ammie kawai dai k'afar ce take min nauyi".


Ammie tace.


"Itama Zata daina in Sha Allah indai Kina takawa da kad'an kad'an zata saki gabad'aya". Huyaam ta gyad'a mata kai ta juya ta cigaba da kallanta.Ammie tai Shiru tana kallan Huyaam tunani fall ranta.lokaci D'aya taji Wani Abu ya soki zuciyar ta Mai kama da rauni take ta runtse idonta tana ambatan sunan Allah.takaf cikin yaran nan HUYAAM itace raunin ta itace wacce take jinta aduka sassan jinkinta tana matuk'ar k'aunar Huyaam so bana wasa ba ko kad'an Bata tab'a k'aunar Wani Abu da zai B'ata mata rai ko Kuma ya tab'a lafiyarta wannan ciwon Dake jikinta ma ji take dama ya dawo kanta hawaye ne ya kawo idonta tai saurin gogewa tana dai dai ta fuskarta....


Aziz chiroma na koma b'angarensu ya zauna nan kan D'aya daga cikin kujerun falon ya d'auko wayarsa Yana latsawa the falor was so silent for some minutes.can Hajiya Lubabatu tashigo falon tana kallan Aziz da mamaki tace.


"A'ah! kai kuma Ina kaje tun d'azu daga zuwanka harka fita ko zaman kirki bakai ba".ta fad'a tana zama kan kujerar kusa dashi.


Aziz ya d'ago da kansa daga latsa wayarsa da yakeyi Yana kallan Hajiya Lubabatu yace.


"Daga b'angaren Ammie nake naje gaisheta ne".

Take ran Hajiya Lubabatu ya B'aci nan da nan annurin fuskarta ya gushe tana kallan Aziz tace .


"B'angaren fulani kuma? Yanzu kai daga zuwan naka har ka kwashi k'afa ka tafi b'angarenta Dan Rashin hankali to uwarke ma ya kaika tukunna". ta fad'a ranta a b'ace.


Da mamaki Aziz chiroma ya ajiye wayar Hannunsa Yana kallan maman nasu Jin abinda ta fad'a yay k'asa da murya yace.


"Haba mamah?yanzu Dan naje b'angaren Ammie na gaisheta shine zakice Rashin hankali?..."Hajiya Lubabatu tace .


"To ai Gani nai ko ni uwarka gaisawa kawai mukai ka fita daga nan kitchen fa na shiga zan kawo Maka abinci shine na dawo na Tarar ka fita kabar falon ko gaisuwar kirki bamu yiba kawai sai dawowa nai naga baka nan".


Aziz yay k'asa da murya yace .


"To ai gashi Yanzu na dawo Mama". Hajiya Lubabatu tace.

"To ga abinci can a dining na kawo Maka kaje kaci".


Aziz Chiroma Yace .

"Zanci idan nai sallahn magrib".Hajiya Lubabatu tai shiru tana kallan TV ranta a had'e Jin abinda Aziz ya fad'a.shiko Aziz ganin haka yasa ya d'auki wayarsa ya cigaba da abinda yakeyi can Hajiya Lubabatu ta mik'e tace.

"Ina zuwa". daga haka ta shige D'aki Aziz ya bita da kallo kafin ya d'auke kansa ya dawo dashi kan screen d'in wayar tasa can Kuma sai ya mik'e Yana zura wayar a aljihunsa ganin time d'in sallah ya kawo kai harma ana K'iran sallahn ya fice daga falon gabad'aya ya nufi masallacin cikin palace d'in......


______________&



*Ingiland =*


05:50pm

Dawarsa kenan daga wajen aiki ko zama baiyi ba bare ya huta Yana shiga d'akin ya ajiye brave case d'insa wacce ke d'auke da laptop d'inshi ya zare agogon hannunsa sannan ya fara rage kayan jikinsa. bayan ya gama ya k'arasa cikin toilet d'in ya shiga Dan yin wanka.babu dad'ewa ya fito d'aure da towel a k'ugunsa kansa sai d'igar ruwa yakeyi hannunsa kuma rik'e da k'aramin towel Daya d'aura akansa Yana tsane gashinta kansa dashi shaf shaf yake shirinsa nasa saboda tafiya ce dashi zuwa k'asar china nan da awa biyu jirgin nasu zai tashi wato k'arfe 8 na dare.so yake aya Dad'e acan yayi one to two days Dan a San samunsa yanaso ya tafi Nigeria ne a ranar Friday or Saturday a San samunsa fa kenan idan har ya gama abinda ya kaishi akan lokaci kenan. Amma ita tafiya itace da kai ba Kaine da itaba sai yadda ta yiyuwa tukunna.sauke numfashi yayi ya Ajiye towel d'in hannunsa yayi ya k'arasa gaban mirror Dake shak'e da kayan shafe shafe sai kace mace saboda Afeef Dan Gayu ne na ajin k'arshe Yana da tsafta ta kin K'arawa ga baya San k'azanta ko kad'an komai nasa na musamman ne shiyasa zakiga baya tab'a shiri da k'azami bare ya zauna kusa da shi ma .bayan ya gama tsane kan nashi ya ajiye towel d'in nan inda yiwa Ajiyewa sannan ya d'auki Wani lotion mai kyau da dad'in k'amshi ya fara shafawa ajikinsa bayan ya gama ya k'arasa wajen drowersa ya Bud'e Dan d'auko kayan da zaisa .wasu K'ana nun kaya ya d'auko ya ajiye agefe dan su zaisa idan zai tafi sannan ya d'auko gogeggiyar jallabiyarsa ash color yasa ajikinsa dama already yayi alwalarsa kafin ya fito daga toilet d'in ya d'auki turarukansa masu k'amshi ya feshe duka jikinsa dasu bayan ya gama ya maida ya ajiye sannan ya nufi k'ofar fita daga falon ganin lokacin sallah na k'ok'arin wucewa ya nufi wani masallaci Wanda ke a jikin gidansu


K'arfe bakwai da Rabi ya fito daga masallacin bayan ya Zauna anyi sallahn isha'i dashi ya shigo falon ya k'arasa har d'akinsa sannan ya zare jallabiyar jikinsa ya d'auki wannan kayan Daya d'auko d'azu yasa ya k'arasa gaban mirror Yana fesa turare Aduka Jikinsa bayan ya gama ya d'auki pacing cap dinsa yasa. ya Allah haka na ambata araina ba k'aramin kyau kayan sukai masa ba ya k'arasa ya d'auki box d'insa Daya had'a kayansa aciki tunda Safe Wanda kafin ya fita aikin ya had'a kayan nasa ya d'auka ya kai falo ya ajiye sannan ya dawo d'akin ya kashe duka kayan wutar d'akin harda switch d'in sannan ya rufo k'ofar bayan ya danna Wani D'an Abu take k'ofar ta rufe Yana shigowa falon adai dai lokacin da driversa yake shigowa shima ya k'arasa ya d'auki box d'in Yana kallan Afeef ya sunkuyar da kansa kasa yace cikin girmamawa.


"good evening sir". Batare da Afeef kalleshi ba Yana kallan disigner watch d'in hannunsa Yana kallan time yace.


"Let's go".ya fad'a Yana nufar k'ofar fita daga falon cikin sauri ganin k'arfe 8 Saura.driver Mai suna John ya d'auki box d'in yabi bayan Afeef da sauri ,kafin Afeef ya k'arasa wajen motar har John ya k'arasa ya Bud'e masa back seat da sauri sannan ya tafi ya zaga ya Bud'e boots d'in motar ya ajiye box d'in aciki ya rufe Afeef kuma Daya tsaya Yana magana da ma'aikatan gidan ya k'araso Motar da sauri ya shiga bayan motar yana picking call d'in Daya shigo wayarsa Yanzu. John ya zaga driver seat cikin sauri ya shiga ya ta-da motar suka bar gidan bayan Mai gadi ya wangale musu gate d'in suka dinga d'aga musu hannu har suka bar gidan gabad'aya.


K'arfe 8 Saura mintuna biyar motarsu ta Isa air port. John ya fito cikin sauri ya bud'ewa Afeef bayan motar ya koma baya da sauri ya tsaya Yana duk'ar da kansa k'asa.Afeef ya fito cikin nutsuwa yana k'arewa harabar air port d'in kallo ganin har anfara boarding classes John ya zaga boots ya Bud'e ya fito da box d'in yabi bayan Afeef da ita Wanda har yay gaba zuwa cikin air port Afeef ya juyo ya karb'i box d'in a Hannun John Yana kallansa yace.

"Thanks". John yay murmushi yace.


"Safe trip sir". Afeef ya gyad'a masa kai kafin yay gaba.john ya koma inda motar take ya shiga yay reverse ya fita daga airport d'in ya koma gida ... k'arfe 8 da Minti goma jirginsu Afeef ya d'aga zuwa kasar china...




#<9 HUYAAM
#<9 LAMID'O
#<9 AZIZ CHIROMA
#<9 AFEEF






07066508376________
'Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD



*<9 HUYAAM <9*


*NA*



*__NAJA'ATU UMAR FAROOQ __*



*__(MRS SARAKIES =؋)__*





*PAGE 1 6 *



*Tallah! Tallah!! Tallah!!!*


*Ina kuke hajiyoyin gidan nan,nace Ina kuke hajiyoyin gidan nan?to maza ku matso ga wata garab'asa ta zomu har inda kuke=؃=؃?.*


*Hajiya kaya Kikeso na fita kunya cikin taro ku Kuma so kike kallo ya koma akanki acikin Taron mata idan kika shiga biki ko suna ko Kuma Wani taro na musamman.to maza idan kina so ki kankarowa kanki mutunci kizo UK collection and gallery mu gwan gwajeki da kayanmu masu quality Wanda zaki gaji ki ajiye Dan kanki Amma badai ya mutuba Muna sai da kaya kamar haka=G*


*Atamfofi da lesses*
*Abaya*
*Shadda*
*Hand bag*
*Shoe*
*Veil na manya Dana Yara*

*Socks rin hands made d'in nan masu net*.

*Hula ta 'yan Gayu*

*Siyan D'aya ko sari*

*Duk zaki samu kan Farashi Mai sauki kedai ki garzayo UK collection & gallery Kisha Mamaki*

*Domin ganawa damu ko magana damu kai tsaye ku tun tub'emu kai tsaye ta wannan number kamar haka*=I08135305790

*Sai mun jiku =؃=؃=؃*


<9<9<9<9<9<9



*Bismillahirrahmanirrahim*



____________&


Washe gari Ranar Alhamis da yamma Ya zarah tana zauna a falon downstairs bayan sallahn ASR tunda yau Babu islamiya tana karatun test d'in da zasuyi ranar Monday. huyaam Kuma tana zauna daga gefenta a saman kujera tana game da wayar ya Zarah data bata aro tayi nisa cikin yin game d'in da take Huda ta shigo falon da sauri rik'e da wayar Ammie Tayo wajen HUYAAM da ita ta karawa Huyaam wayar a kunnenta,Huyaam ta d'ago ta kalleta da alamar tambaya sai Kuma tai k'asa da murya tace.

"waye?.." Huda tai k'asa da murya tace.

"Anty Khadija ce zatai miki ya jiki".take Huyaam ta saki murmushi ta ajiye wayar ya Zarah nan gefenta cikin D'oki ta rik'e wayar Ammie tace.


"Hello Anty Ina yini".ta fad'a tana K'ara fad'ad'a murmushinta.daga D'aya b'angaren Anty khadija Dake zaune a tamgamemen falonta Dake nan garin Abuja tace itama tana sakin murmushi.


"Lafiya lau Huyaam ya gida ya jiki Kuma Ashe abinda ya faru kenan?... Huyaam tace.


"Eh Alhamdulillah anty". Anty Khadija tace .

"Allah ya sawak'e fatan dai yanzu k'afar ta warke ko". Huyaam ta Kalli k'afarta wacce har bandage d'in ya cire jiya da daddare da tana bacci kawai sai tashi tai taga babu komai sai tabon ciwon kuma cikin iKon Allah tana tashi taji ta take k'afar sai taji Bata jin ciwon komai awurin tace.

"Eh anty naji sauk'i". Anty khadija tace .

"Masha Allah daughter Allah ya K'ara lafiya Nima bana k'asar ne bamu Dad'e da sauka ba shiyasa tun tuni banzo ba Amma tunda mun dawo soon zaki gammu a kano in Sha Allah". Huyaam tai murmushi tace.

"Allah yasa anty sannunku da dawowa". Anty Khadija tace.


"Yauwa ashe anyi graduation Kuma?..." Huyaam tace . "Eh munyi". Anty khadija Tace. "Congratulations my dears Wishing you good results". Huyaam tace.

"Thank you so much anty inasu siyama?..."anty khadija tace.

"yanzun nan ta haura sama". Huyaam tace.

"A gaida su".anty khadija tace. "Zasuji in Sha Allah bawa Ammie wayar Huyaam ta Mik'awa Huda wayar tai k'asa da murya tace.


"ki kaiwa Ammie". Ta fad'a a hankali.huda ta karb'i wayar ta haura sama da sauri zuwa d'akin Ammie.bayan tafiyar Huda Huyaam ta d'auki wayar ta cigaba da game d'inta......


Sallama akai daga nan kofar falon aka turo k'ofar aka shigo Huyaam ta d'aga kai ta kalli k'ofar har suna had'a Baki wajen ansawa ita da ya Zarah.ikleema da safna ne suka shigo suna murmushi suka k'araso falon kafin su zauna kan kujera tare suka gaida ya zarah.ya Zarah ta Kallesu ta ansa musu sallamar su kafin ta mik'e ta haura sama zuwa d'akinta Dan tasan tunda sukazo Kuma takura Mata zasuyi ba barinta zasuyi tayi karatun ba.huyaam ta ajiye wayar nan gefenta ta Kallesu tana murmushi tace .


"Sannunku da zuwa wato sai yau ake Ganinku ko?..."ta fad'a tana hararsu.safna tai murmushi tace .


"Kiji fa naga ko washe garin ranar ma munzo duba ki kuma jiya munzo da safe Ammie tace kina bacci".

Huyaam ta tab'e Baki tace.

"Aishikenan".

Please Login or Register in order to submit comment