Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jik'e da gumi,ta K'ara d'iban Wani ta shafa mata a fuskarta .take HUYAAM taja wani dogon numfashi tana sakin jikinta a jikin Ammie.ganin haka yasa Ammie ta sauke ajiyar zuciya tana kallan Huyaam. ta juya bayanta Jin sautin Kukan muneefa ta kalli haidar tace.


"Wayece ku shigo da ita?maza kamata ku fita da ita"Babu musu haidar ya kama hannun muneefa yana kallan Huyaam yace .


"Allah ya K'ara lafiya".ya Zarah ta ansa da Ameen. daga haka ya fita daga d'akin rik'e da muneefa muneeb ma yabi bayansu.bayan Wani lokaci HUYAAM ta fara Bud'e idanuwanta ahankali a hankali ahaka har ta gama Bud'esu gabad'aya.ta tsaida su akan Ammie kafin ta juya Tana kallan sauran saikuma ta fara k'ok'arin mik'ewa zaune Ammie ta rik'eta tana cewa.

"Me zakiyi haka ?..
HUYAAM tana yamutsa fuska tace.

"Ammie meya faru?.."Ammie tai mata murmushi tace.

"Kankine ke ciwo shine na Baki magani"ta fad'a tana kallan yadda HUYAAM take rarraba ido.

Sai Kuma tace.

"Kan ya daina ciwon yanzu ?..."ta fad'a tana k'ok'arin parking gashin HUYAAM.


HUYAAM ta gyad'a mata kai sai kuma tace

"Ammie Ina Abba?..."Ammie tace .


"Yana masallaci Bai shigo ba "Huda ta kalli HUYAAM tace.


"Sannu HUYAAM". HUYAAM ta gyad'a mata kai ya Zarah ma tai mata sannu ta ansa mata sai Kuma ta fara zame jikinta Daga na Ammie tace .

"bacci nakeji". Ta fad'a tana juya bayanta.Ammie tace .


"A'a tashi Muje kici Abinci". Huyaam tace Batare da ta juyo ba.

"A'a sai anjima".daga haka ta K'ara gyara kwanciyar ta.


Ammie batace komai ba ta d'auki wayarta ta kunna Karatun Al'qur'ani ta mik'e ta ajiye nan saman mirror Dake d'akin ta barwa Huyaam tana kallan su ya Zarah tace .


"To muje mu barta ta huta anjima Huda sauki had'o mata abinci Dan kada ta kwana da yunwa"Huda tace.

"To Ammie".daga haka suka fita daga d'akin Ammie ta jawo k'ofar ta rufe.


Wajen k'arfe 9 na dare Mai martaba ya shigo part d'in Ammie Yana zaune a falonsa Dake nan part d'in bayan duk yaran sunzo sun gaida shi sannan suka fito daga falon.

Muneefa tana mak'ale da mai marataba Da take bashi labarin HUYAAM Babu lafiya.Ammie ce ta shigo falon bakinta d'auke da sallama Hannunta rik'e da D'an k'aramin plate Wanda ta d'orowa Mai martaba black tea akai ta k'araso har falon cikin ta risina ta ajiye nan gaban Mai martaba.tana kallan muneefa tace.


"Wato Baki tafi kin kwanta ba ko?..."Mai martaba yace cikin nutsuwarsa.


"Fulani! wai jikin Huyaam ne ya K'ara tashi?..."ya fad'a Yana kallan Ammie.


Ammie ta d'ago ta kalleshi sai Kuma ta Kalli muneefa wacce ke k'ifta ido tace.

"Wato ke uwar surutu kece kika fad'a masa koh?..."muneefa ta sunkuyar da kanta k'asa. Ammie ta sauke numfashi tana Maida dubanta kan Mai martaba tace cikin Damuwa.


"Shine rankai Dad'e Amma na Bata sauran maganin Daya rage Wanda da muka kaita Egypt muka karb'o Ina shafa mata nan da nan ta dawo hayyacinta".


Tunda ta fara magana Mai martaba yake kallanta yay Jimm alamar tunani kafin ya sauke numfashi yace.


"Allah ya Bata lafiya"Ammie tace .

"Ameen ya Rabbi".

Mai martaba yace .

"Yaushe ne zaku koma?..."


Ammie tace." nan da wata uku ne in Sha Allah.


Mai martaba ya Jin Jina kai . Amma baice komai ba.Ammie ta kalli muneefa wacce ta fara gyangyad'i ta d'auke ta ta fita da ita daga d'akin Dan zuwa ta kwantar da ita .tana kwantar da ita ta shiga wanka ta fito ta kimtsa cikin kayan bacci bayan ta gama ta feshe jikinta da turaruka masu bala'in kamshi da tsada ta d'auki dogon hijab d'inta tabi tanan corridor Dake gefen d'akinta tai part d'in Mai martaba Dan yau kwanan tane.





07066508376________
'Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD




*<9 HUYAAM <9*


(The love e& story)



*Paid book =*


*Free pages*





*NA*



*___NAJA'ATU UMAR FAROOQ ___*




*___(MRS SARAKIES =؋)=1___*



*Bismillahirrahmanirrahim*




PAGE 5



__________&


Washe gari haka HUYAAM ta tashi kamar Bata tab'a wata jinya ba.baccin tama tasha babu Wanda ya tasheta sun bari ne ta tashi da kanta .Sai wajen k'arfe 11:30am ta tashi ,sannu a hankali ta sauko daga saman gadon daga ita sai rigar bacci ajikinta ta mik'e tsaya tana Mik'a kafin ta tafi ta d'auko towel ta d'aura ajikinta bayan ta cire rigar baccin tai hanyar toilet Dan yin Wanka . Babu dad'ewa ta fito d'aure da towel ajikinta kanta sai d'igar ruwa yake ta k'arasa wajen hanga Dake d'akin ta d'auko Wani k'aramin towel ta fara tsane gashinta kanta dashi, bayan ta gama ta d'auki hand dryer ta busar da gashinta bayan ta gama ta Maida ta ajiye a inda yake sannan ta koma gaban mirron ta d'auko lotion d'inta masu dadin kamshi da tsada ta fara shafawa saman lallausar fatarta. bayan ta gama ta k'arasa gaban wardrobe d'inta ta d'auko wata cotton d'in doguwar riga marar nauyi wacce Bata kama taba Sosai sannan ta D'ora hula akai kalar rigar sannan ta fito daga d'akin zuwa main falorn gidan.


Iya Huda da muneefa ta tarar a falon zaune suna kallo ta k'araso cikin falon bakinta d'auke da sallama. Huda ta juya tana kallonta kafin ta ansa mata sannan ta Maida kanta kan tv tana cigaba da kallonta .muneefa kuma ta tafi da gudu ta rumgume Huyaam tace.


"oyoyo ya Huyaam tun d'azu nake lek'aki Baki tashi ba sai Yanzu".ta fad'a Tana murmushi . Huyaam ta ja mata kumatu tana murmushi tace.


"Gani yanzu na fito ai, Ina Ammie take?..."ta fad'a tana duba falon kamar zataga Ammien . muneefa tace.


"tana D'aki tanana shirya ya muneeb zazu tafi masallaci". HUYAAM ta Jin jina kai ta rik'o hannun muneefa suka k'arasa shigowa falon tare.


Huda ta juyo tana kallon HUYAAM tace.

"Ya jikin?...."

HUYAAM tai murmushi tace.


"Alhamdulillah shine wato ko ki tasheni koh?..."ta fad'a tana Wani tura Baki gaba.Huda ta harareta kafin ta d'auke kai tana cewa.


"Hmm borin kunya kawai kikeyi ,ked'in ce zakiso na katse miki baccinki idan kinayi keda kamar kasa haka kike indai kina bacci ai ko tashin ki nai bazaki tashi ba..." HUYAAM ta harareta kafin tace.


"Me kike nufi wato nice ma kasa ko?....

Kafin Huda ta Bata ansa Ammie ta K'araso cikin falon tana kallan Huyaam tace .


"Daughtern Ammie ya jiki?..."Huyaam na murmushi tace.


"Naji sauk'i Ammie?..."Ammie tace .


"To Allah ya K'ara lafiya hope kinyi breakfast dai?..."


Huyaam tai murmushi ta Mik'e ta nufi hanyar dining tace.


"yanzu Zanyi Ammie".

Ammie ta girgiza kai tace "Allah ya shirya min ke Huyaam ace mutum Ya zauna har 12 baici abinci ba sai kin jawa kanki ulcer".


Huyaam tace. "Yi hak'uri Ammie yanzu Zanyi".har lokacin murmushi ne a saman fuskarta.


"Ammie ta girgiza kai tana zama kan D'aya daga cikin kujerun falon

Muneeb ne ya sauko k'asa har zuwa falon cikin shirin tafiya masallacin juma'a yasha farar shadda tareda babbar riga ya tsaya kusa da Ammie Yana juya hular hannunsa yace.


"Ammie ya haidar fa ya fito koya tafi masallacin ya barni?...."ya fad'a Yana kallan hanyar part d'in su ya haidar.kafin Ammie ta bashi ansa ya haidar ya sauko nan downstairs cikin shigar manyan kaya shima sai baza k'amashi yakeyi.Huyaam tai saurin cewa.


"ya haidar kayi kyau ta fad'a tana murmushi.

haidar ya kalleta yace .

"Thank You sis". sai Kuma ya maida kallansa kan Ammei yace.


"Ammie zamu tafi masallaci". Ammie tace.


"Allah ya kiyaye". ya ansa da Ameen.sai Kuma ya Kalli muneeb yace .


"Zo mu tafi time na tafiya". Ya fad'a Yana yin hanyar k'ofar fita daga falon.muneeb yabi bayansa bayan yayiwa Ammie sallama, Ammie ta Rakasu da fatan dawowa lafiya.


Wajen k'arfe biyu da Rabi na Ranar aka sauko daga masallacin juma'a Dake nan cikin palace d'in dayake anan Mai martaba yake sallahn juma'arsa shima. yasa bakiga yadda masallacin ya cika da mak'il da mutane ba.sannan yawancin wad'anda ke zuwa yin sallahn ma yawancin su wad'an da ke kusa da gidan sarkin ne shiyasa duk nan masallacin palace d'in suke zuwa yin sallahn juma'arsu da .


Can na hango yaran cikin palace d'in da samarin gidan irinsu ya haidar suna ta k'ok'arin shiga cikin palace d'in .


Bayan sun shiga kuma
kowa sai ya kama Hanyar part d'insu suna ta k'ok'arin shiga b'angarensu.


kafin na hangi ya haidar Dake tafiya Yana duba wayarsa muneeb Kuma yana gefensa suna tafiya tare har suka k'araso b'angaren su.bayan sunyi knocking suka shiga cikin falon bakinsu
d'auke da sallama.


Huyaam ce kad'ai falon tana parking labulayen windows d'in falon Zatai parking d'insa jiki k'arfen da ake hanging labulayen.ta juya tana ansa musu ya haidar ya zauna kan D'aya ya cikin kujerun falon Yana cigaba da pressing wayarsa muneeb ya tunkaro Huyaam Dake kokawa da babbar rigarsa wadda ya kasa cirewa yace.


"Ya HUYAAM cire min na kasa" Huyaam tace .

"Tom". Ta fad'a tana matsawa kusa dashi Nan ta cire masa rigar sannan ta bashi ya karb'a ya haye sama wajen Ammie da sauri.


Ganin ya haidar zaune a falon Yana latsa wayarsa yasa Huyaam ta k'araso cikin falon da murmushi a saman fuskarta ta zauna kusa da ya Haidar tace.


"ya Haidar sannu da Zuwa "Sai Kuma tai shiru ta fara wasa da yatsun hannunta .


Ya haidar Yana jinta bai dago ba.ganin yayi shiru Bai ansa ba yasa Huyaam ta k'ara k'asa da murya ta marai raice tace .


"Ya haidar magana fa nake maka".ta fad'a tana kallansa .sai a sannan ya d'ago da kansa Yana kallanta kafin yace.

"Menene?.... atak'aice.


Huyaam tace .


"Uhmm!! dama aran wayarka zaka bamu muje mu K'arasa game d'in ranar nan da bamu gama ba nida Huda".ta fad'a tana Wani langwab'ar da kai tana kuma kallansa .


Shi dariya ma ta bashi, waishi zataiwa wayo.sai Kuma yace .


"Bayanzu ba amfani nake da wayata".


Huyaam tace.

"To Dan Allah ya Haidar sai yaushe zaka bamu?..."ya kalleta a fusace yace.


"Ke bansani ba"Karaf a kunnan Huda wacce take k'ok'arin saukowa downstairs d'in tace .


"lahh yaudai na ganku a Rana Ashe bani kad'ai ake hanawa wayarba harda ke"ta fad'a tana yiwa HUYAAM gwalo.


Huyaam ta harareta sai Kuma ta kalli ya haidar ta k'ara marai raicecewa tace.


"Ya haidar kagafa dariya take min fa?ta fad'a kamar zatai kuka..."ya haidar ya juya Yana yiwa Huda Wani kallo sai Kuma ya juya ya Mik'awa HUYAAM wayar yace.


"Ungo"Huyaam ta karb'i wayar da sauri tana murmushi tace.

"Thank you ya Haidar"sai kuma ta juya ta rama gwalan da Huda tai mata tace.


"Indai nida ya haidar ne ya rinya bazaki tab'a Ganinin mu arana ba koh ya haidar?....". Ta fad'a tana kallan ya haidar Wanda Bai kalleta ba.baiyi magana ba gyad'a mata kai kawai yayi.


Huda ta tura Baki gaba tace kamar zatai kuka.


"Allah sarkie ni wato Dan Kunga Yaya baya nan shiyasa duk kuke min haka". Ta fad'a tana tura Baki gaba.


Ya haidar ya juya Yana kallanta da mamakinta jin abinda ta fad'a.


Ganin Irin kallon da ya haidar yake mata yasa Huda ta juya Dama a stairs ta tsaya ta koma zuwa d'akinsu .Huyaam da itama tabi Huda da kallo Jin abinda ta fad'a ta Kalli ya haidar tai k'asa da murya tace.


"Yaya bari naje muyi tare kagafa taji haushi". ta fad'a cikin marai rai cewa.ya haidar yace.


"Ke Babu inda zaki ta fashe ma ba haushi ba".

Huyaam ta marai raice tace.

"Dan Allah Yaya kayi hak'uri "ta fad'a kamar zatai kuka. yay shiru baiyi magana .tace . "Dan Allah ya haidar nanma dai baiyi magana ba Hakan yasa ta Gane ya amince ta mik'e da sauri tabi bayan Huda wacce har takai d'akinsu.



___________&


Da yamma wajen k'arfe 4:30pm na yamma su Huyaam suka fito Daga part d'insu zasuje su gaida mutanan Dake cikin palace d'in gabad'aya Dan dama haka suke duk ranar Friday sai sunje sun gaida Matan Dake gidan ,kuma wannan ba tarbiyar kowa bace saita Ammie.


Dukkansu sanci kwalliya cikin shigar less d'inkin doguwar riga Huda da Huyaam iri d'ayane nasu Dan komai nasu iri d'ayane, indai za'ai musu D'inki to iri D'aya ake musu ba'a tab'a ban banta musu.less d'in kalar green ratsin golding mayafin shima kalar kayan jikinsu.kalar nasu ya Zarah daban itada muneefa.


B'angaren Dake jikin nasu suka fara zuwa wato bangaren uwar gidan mai Martaba Fulani Salamatu.


Wanda Designed sin ginin da komai Irin na part d'insu ne komai Babu abinda ya ban banta.suna zuwa k'ofar part d'in sukai knocking kofar tare da sallama Abakinsu .Saida sukai knocking sau biyu sannan aka Bud'e musu k'ofar .haka suka shiga bakinsu d'auke da sallama.


Sun tadda Aziza da K'annanta gabad'aya Zaune a falon Ramla ce kawai Batanan mummynsu ta aiketa part d'in su ikleema.dama su ukune ya'yan Fulani Salamatu Aziza itace Babbar 'yarta wacce take sa'arsu Huyaam sai Mai bi mata Ramla sai walida itace Autar Fulani Salamatu.


Fulani Salamatu itace uwar gidan mai Martaba Allah ne Bai Bata haihuba da wuriba Saida aka auro Ammie ta haifi 'ya'ya uku sannan ita da Ammie suka samu cikin Aziza tare dasu Huda Wanda yanzu haka suna Shrekara 17 to 18 ne,Ramla kuma sa'ar muneeb ce sai walida kuma sa'ar muneefa.to daga nan kuma haihuwar saita tsaya musu duka su biyun.ita Fulani Salamatu Bata da d'a namiji ko D'aya.'ya'yanta duka matane.


Tun kafin su k'araso cikin falon Aziza take kallansu bayama HUYAAM ganin Irin yadda tai kyau ba kad'an ba arayuwar Aziza ta tsani taga Wani yafita , Ina anata burin saidai tafi Wani ,saidai Kuma Hakan Bai yuba saboda gabad'aya 'ya'yan Ammei kyawawane .haka ta K'ara had'e Rai bayan Sun had'a Ido da Huyaam ta harareta sai Kuma ta juya tana kallon ya Zarah kamar wacce aka matsewa Baki tace.


"sannunku da zuwa ya Zarah" ta fad'a tana sakin murmushin yak'e.

Ya zarah tace Batare da ta kalleta ba.


"yauwa, Ina mummy?..."sunan da 'ya'yan fulani Salamatu suke K'iranra dashi kenan.


Aziza ta mik'e tace.


"sallah takeyi bari nai mata magana".tana fad'ar haka ta nufi stairs tai hanyar d'akin Fulani Salamatu.


suka k'arasa falon suka samu waje suka zauna waleeda ta k'arasa wajen su HUYAAM inda suke Zaune ita da Huda tana kallan Huyaam tace .


Ya HUYAAM kinyi kyau Sosai". ta fad'a tana murmushi.


HUYAAM ta Maida mata da Martanin murmushin tace .

"Nagode sosai walida"

Huda ta Kalli Walida tace .

"Wato iya Huyaam kika gani ko Walida?..." Tafad'a tana yiwa walida Hararar Wasa .

Walida ta rufe fuskarta da tafukan Hannunta tace.


"A'a ya Huda kema kinyi kyau keda ya Zarah da muneefa".ta fad'a tana murmushi.huda ta d'auke kanta daga kallan ta.


Aziza ce ta dawo falon tace .


"Ya zarah mummyn Tana zuwa "ta fad'a tana zama kan kujerar data tashi.bahu dad'ewa Fulani Salamatu ta sauka k'asa sanye da jihab alamar dai da Gaske sallahn tai ba fad'ar Aziza bace . Fulani Salamatu ta sauko tana kallansu har ta k'araso cikin falon ta zauna kan kujera one seater cikin tak'ama Fuskarta Babu yabo babu fallasa.


Tare suka gaida ta tana kallansu ta ansa kadaran mahadan. daga nan Bata k'ara cewa komai ba suma sukai shiru inda sabo sun Saba idan sukazo b'angaren fulani Salamatu tai banza ta k'yalesu Dan Suma ba'a San ransu suke zuwa b'angaren ba tunda suma sun San ba k'aunar take ba bayama HUYAAM Dan ita har Bataso ace yau Friday Dan kada ace suzo part d'in d'in falani salamatu saboda ita Kanta tasan ba k'aunar ta take ba daga ita har 'yarta Aziza.haka kowa yay shiru a falon sunkai kusan 2 minutes ahaka Babu Wanda ya K'ara magana.sai can fulani Salamatu ta kalli Aziza tace .


"Aziza kawo musu mana". Ya fad'a tana kallan Aziza. ya zarah ta mik'e tace .


"A'a mommy munsha ruwa a gida tafiya ma zamauyi" ganin haka yasa suma su Huyaam duk suka mik'e Wanda kamar suna kan k'aya .fulani Salamatu tace.


"Tafiya Kuma? To nagode ku gaida gida"daga haka Bata k'ara cewa komai ba.walida tace.

"ya HUYAAM ya Zarah,ya Huda muneefa bye bye" ta fad'a tana murmushi.suka ansa mata suna Fita daga falon .


Suna fita Aziza ta mik'e tana kallan walida tace.


"Kedai wallahi ba akwai marar zuciya ba banza kawai suna Wani shash shareki Amma kina Wani cusa kai". Ta fad'a tana hararar walida kamar idanuwanta zasu zazzago k'asa Saboda masifa.


Walida ta tura Baki gaba tace .

"Kai ya Aziza Mai nai kuma?..."ta fad'a tana juya kanta gefe.


Aziza da haushi ya gama cikata idan ta tuno da yadda gabad'aya su Huyaam sukai mugun Kyau tace .


"Ni kike fad'awa me kikayi Dan Bakida mutunci eh!!..."ta fad'a kamar zata doki Waleeda. walida tai saurin Matsawa baya tana tura Baki gaba ganin Aziza zata doketa.


Bak'in ciki yasa Aziza tai k'wafa ta bar wajen ta haye sama zuwa d'akinsu tana ta masifa ita kad'ai .itadai Fulani Salamatu batai magana tabi Aziza da kallo kafin ta tab'e Baki itama ta mik'e ta wuce zuwa d'akinta tana Jin Wani Irin tsanar yaran na yad'uwa azuciyarta barin ma babban yayansu ta tsaneshi shida HUYAAM tsana mafi Muni ma kuwa.




07066508376________
'Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD





*<9 HUYAAM <9*




*Paid book =*


*Free pages*





*NA*




*___(MRS SARAKIES =؋)=1___*




*Bismillahirrahmanirrahim*




PAGE 6



___________&


Daga b'angaren fulani Salamatu ,b'angaren Dake yamma da part d'insu suka nufa wato b'angaren sauran matan Dake gidan. b'angaren farko na baba turaki ne wato k'anin Mai martaba shima dai matansa biyu Kuma ko Wacce bangaren ta daban. part d'in farko shine na uwar gidansa Mai suna Hajiya Lubabatu .


Hajiya Lubabatu 'ya'yanta s 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~hida hud'u mata biyu maza .acikin matan biyun farko sune manya bahijja wacce a shekaru zatai 25 itace babba sai Mai bi mata Salima ita Kuma shekararta 22 itace sa'ar ya Zarah sai ikleema wacce itace sa'ar su Huyaam Mai shekaru 17 sai maza biyu Sai kuma autarsu Ameera . Tunda suka baro part d'insu Aziza gaban HUYAAM fad'uwa kawai yake har suka k'araso part d'in kwata kwata Bata son zuwa b'angaren nan guda biyu.wato b'angaren su Aziza da b'angaren su ikleema saboda duk gidan babu Wanda yake k'aunarta musamman ma wad'annan matan guda biyu wato fulani Salamatu da Hajiya Lubabatu wato babarsu ikleema ,Basa k'aunar HUYAAM ko kad'an iya mamansu safna ce kawai take Santa sai kishiyar hajiya Lubabatu wato antynsu su ikleema, ita Irin matan nan ne Irin 'yan I don't care d'in nan ce, ita baka Gane inda ta dosa shiyasa kwata kwata babu part d'in da HUYAAM take zuwa ta zauna ta sake sainasu safnah.


Suka isa part d'in Saida sukai knocking bayan an Basu iznin shiga sannan suka shiga. sun tadda ikleema dasu ya bahijja wacce take zauna kan kujera tana danna wayarta, ita kan ma ansa musu ranar AURE itada yayarsu safnah Mai suna zulaihat nan da 2 month ne bikin nasu idan Allah ya kaimu Dan an kawo kud'i anyi komai kawo legefe ne kawai ya rage yanzu.sai K'annan ikleema mazan sai autarsu Ameera.suna zaune a falon suna kallo . ikleema ta mik'e da murmushi a fuskarta ganin su Huyaam tana kallansu ta ce.


"sannunku da zuwa ya Zarah" .ta fad'a tana murmushi

Ya zarah ta ansa mata suka k'arasa har cikin falon suka zauna na kan kujera suna gaida ya bahijja ta ansa musu tana barin falon da wayarta a hannunta ikleema tace.

"Bari na k'ira mama tana d'aki"daga haka tabar falon .Babu dad'ewa ikleema suka dawo falon tare da Hajiya Lubabatu cikin shiga ta Alfarma sai wal walwali take ta k'araso har cikin falon ta zauna a nan kan kujera tana kallansu .


Gabad'aya Suka had'a Baki wajen gaidata.ta ansa musu tana murmushin da Bai kai zuciyarta ba .kafin kice me ikleema ta kawo musu ruwa da drink's ta ajiye agabansu tana kallansu tace.


"kusa ruwa ya Zarah tana fad'ar haka ta koma kan kujerar da take Zaune ta zauna.


Nan ma dai shiru falon yayi sai ikleema ma ce kawai da take Jan su Huyaam da hira,sukan bama Wani sakewa sukai ba kawai dai suna Zauna ne .Basu Dad'e a falon ba, Dan babu Abinda suka tab'a na D'aya daga cikin abinda aka kawo musun suka mik'e sukace tafiya zasuyi.hajiya Lubabatu tana kallansu tace .


"Tafiya kuma zakuyi Zarah?...."ta fad'a tana kallan ya Zarah.


ya Zarah tai Murmushi tace. "eh mama tafiya zamuyi" .ta fad'a tana k'ok'arin mik'ewa tsaye. Hajiya Lubabatu Tace .


"To nagode Ku gaida fulanin idan kun koma"


Suka ce in Sha Allah zataji daga haka suka nufi k'ofar fita daga falon
Hajiya Lubabatu tabisu da kallo tana tab'e Baki kafin ta Mik'e itama tabar falon.....Har k'ofar part d'in ikleema ta rakosu tai musu rakiya bayan ta rakosu ta koma ciki.


Daga b'angaren su ikleema part d'in antynmu su ikleema suka nufa .wato kishiyar hajiya Lubabatu Mai suna Hajiya hauwa itakan 'ya'yanta biyu mace da namiji ,namijin shine Babba Mai suna sayyid Sa'an muneeb ne sai macen Kuma maybe suna husna itace autar ta ita kuma sa'ar muneefa ce bayan sun shiga sun sameta a falon tana zaune tareda da yaranta .ta karb'e su cikin mutuntawa tana Basu wurin zama,bayan sun zauna kan kujerun falon suka gaida ta,ta ansa tana tambayar su Ammie sukace tana lafiya,daga haka Kuma falon yay shuri Babu me magana acikinsu.nanma dai Basu fi mintuna biyar ba saukai mata sallama suka tafi.


Daga b'angaren Hajiya hauwa b'angaren Baba wambai suka nufa wato b'angaren su safnah. shi kan matarsa D'aya Hajiya Aysha itakan tana Sansu sosai tunda k'awar Ammie ce kaf gidan itace suke mutunci da Ammie, take Kuma zaune da Ammie da zuciya D'aya.ita kan 'ya'yanta hud'u.babban d'anta namiji ne Mai suna Bello Amma ana ce masa lamid'o Saboda sunan Marigayi Mai martaba Wanda ya rasu yaci ,shekararsa 28 Dan yafi ya haidar,baya nan Yana Lagos Yana Aiki a componing Mai martaba Dan shike kula Dana can sai zulaihat yayar safna Mai shekara 25 sa'ar bahijja ce sai namiji D'aya sannan sai safnah sai autarta Aneesa....basu tadda kowa a falon ba sai safna da Anisa ya zulaihat Batanan taje unguwa.da murmushi a fuskar safna ta ansa musu sallamar su ta taso ta rumgume Huyaam da Huda bayan ta gaida ya Zarah tana kallan Huyaam ta rik'e baki tace.


"Uhmm! wato jiki ya ware koh? shiyasa akaci wannan gayun kenan?..." Ta fad'a tana murmushi.

HUYAAM ta Maida mata da Martanin murmushin Amma bataci komai ba suka k'arasa har cikin falon suka zauna suna zama Hajiya Aysha wacce suke K'iranta da ummi ta fito daga kitchen tana kallansu tai murmushi tace.


"A'a!! kuce yaran Ammie ne agidan kenan?...." ta fad'a tana k'arasowa har cikin falon ta zauna kan kujera .


Sukai murmushi dukansu kafin su had'a baki wajen cewa.

"Ummi Ina yini" ummi ta ansa musu har lokacin murmushi Bai gushe Daga saman fuskarta ba.tana kallansu tace.


"Lafiya lau Alhamdulillah Ina Ammie?...."sukace lafiyanta lau" ta Jin jina kai kafin tace .

"to Masha Allah,ya juma'a Kuma?...".suka ansa da Alhamdulillah nan ta fara Tambayarsu school suna Bata ansa.kan kace me safnah harta cika musu gabansu da ruwa dasu drinks da fruits sai abinci da ummi tasa aka kawo musu duk da dai Baci zasuyi ba haka suka zauna suke ta hira tare da ummi da yake ita macace da Babu ruwanta ga safnah itama da suke ta hira da ita sai Aneesa Dake tare da muneefa suna ta wasansu a falon .sun Dad'e a part d'in Dan Sai wajen k'arfe shida suka koma part d'insu. Lokacin Ana K'iran sallahn magrib....


suna shiga b'angaren su basu tsaya a ko Ina ba sama suka haura Dan suna shiga ya Zarah ta wuce d'aki ita da Huda Dan cire kayan jikinsu Dan Wani Irin damunsu sukaji kayan yanayi ita ko Huyaam d'akin Ammie ta tafi Dan zuwa ta sanar da ita sun dawo Tunda Basu tadda kowa a falon ba.



____________&




Da daddare wajen k'arfe 9 na dare bayan su HUYAAM sunyi dinner. Mai martaba yana zaune a falonsa Dake nan part d'in Ammie ,Dan shima b'angaren daban a part d'in ya Zarah ta shigo ta gaida Mai martaba Dan dama haka sukeyi indai Yana b'angarensu ,to sai sunzo sun gaidashi .bayan ta fita HUYAAM da Huda ne suka shigo falon sanye da jihab har k'asa bakunansu d'auke da sallama.


mai marataba dake kishin gid'e jikin tuntun sarautan dake babban falon nasa Yana hutawa.ya d'ago yana kallansu bayan ya ansa sallamar tasu cikin nutsuwarsa da kamewarsa har suka k'araso cikin falon.


Suka d'urkusa suka zauna nan saman carpet d'in Dake malale a tsakiyar falon ,bayan sun zauna Suka had'a Baki wajen gaida Mai martaba suka ce.


"Abba barka da dare, ina wuni".. suka had'a Baki wajen gaida shi.


Mai martaba ya Dan d'ago Yana gyara zamansa Yana kallansu da kyau kafin yace.


"Barka dai 'yan biyun Ammie ya kuke?..."ya fad'a Yana murmushinsu na manya. sukace "Lafiya lau Alhamdulillah Abba".Mai martaba ya Jin Jina kai Kafin yace .

"Masha Allah ,ya exam kuma?yau ba'a je school ba koh?...."ya fad'a Yana kallansu.dan

Please Login or Register in order to submit comment