Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tai Wani murmushi Jin abinda tazo dashi ya fara karyar wa da Ammie zuciya ta ce "wacece Kwa idan ba Agolar gidan nan ba ko akwai wata Agolar ne bayan ita wacce aka fifita ta akan 'yar gidan har ana Neman akashe 'yar masu gida akan ta" sai Kuma ta Wani tafe hannu ta ce "Au mantawa nai,Ashe fa har yanzu Baku fad'a mata ko ita wace ce a gidan nan ba ko? Da aje a kashemin 'ya akan agola gara ni nazo na fara sanar mata da matsayinta Agidan nan" ta fad'a tana kallan Huyaam.Ammie da ranta ya fara B'aci lokaci D'aya Irin Wanda bai tab'a B'aci ba ta ce cikin tsawar da batama San taiwa Fulani Salamatu ba "Fulani Mai ya faru haka ne da zaki zo kinayin wad'an nan magan ganun marasa tushe a gidan nan Dan Allah? Ta fad'a tana kallanta.Fulani Salamatu zata K'ara magana kuma Ammie tasan ba alkhairi ne zai fito daga bakin ta ba yasa ta ce "Dan Allah kiyi shiru muje b'angaren ki muyi maganar" Fulani Salamatu tai Wani murmushi ta ce "Babu inda zani agaban kowa Za'a yi wannan maganar.wato bakya son yarinya tasan matashin tasan ko wacece ita a gidan nan bane kome?To idan Baku fad'a mata yanzu ba yaushe kuka shirya fad'a matan, ko sai anzo Neman Auren ta tukunna? Ta fad'a tana kallan Ammie ido cikin ido ganin ta kasa magana.Su dai su yay zarah kalllan Fulani Salamatu kawai suke gabansu na fad'uwa suna k'ok'arin fahimcitar inda zancenta ya dosa ganin Ammien su tayi shiru tak'i magana hakama Huyaam da duk take cikin compused d'in zancen Fulani Salamatu.ganin duka yaran sun rud'e sannan itama kanta Huyaam d'in Bata fahimci zancen taba yasa fulani Salamatu ta Kalli HUYAAM ta ce "Kinga yarinya bari na fad'a miki Abinda ake ta b'oye b'oyen fad'a miki shekara da shekaru,ke ba 'yar gidan nan bace ba agola ce.Fulani Maryam da Mai martaba ba su suka haife kiba kamar yadda kike tunani ba" ta fad'a tana kallanta.Huyaam dai kallanta take Bata ko kiftawa tana nazarin zancen ta. Haka ma falon yayi d'iff kamar Wanda ruwa ya cinye...Jin muryar Afeef sukai Wanda tunda fulani Salamatu ta fara gayawa Huyaam ko wacece ita ya sauko stairs d'in Dan hayaniyar ta ce ma ya fito dashi daga b'angarensu Dan Yana zaune a falonsa yana Aiki a laptop kawai ya juyo magan ganun Fulani Salamatu a tsakiyar kansa, Hakan yasan ba lafiya ba,Babu shiri ya fito yaga mai ke faruwa.wata uwar tsawa ya dakawa Fulani Salamatu Yana nuna ta da yatsansa ya ce "ya isheki haka" da wata iriyar murya Lokaci D'aya idonsa ya kad'a yay jajir jijjiyoyin kansa duk suka fito rad'o rad'o yana cigaba da tafiya har ya k'arasa shigowa falon yana nuna mata kofa yace "gate out before I loss my control malama" Fulani Salamatu tana masa Wani kallo ta ce "bazan fita ba,duk abinda na fad'a k'arya nai koba Kaine ka tsintota ba? ka tsintota ka kawo ta nan gidan ko na ba haka akai ba? Ta fad'a tana masa Wani Irin kallo.Afeef dai kallanta yakeyi kirjinsa na bugawa sama da k'asa Yana Jin kamar ya shak'eta saboda irin abinda yakeji. Fulani Salamatu ta tafe Hannu ta ce "ko kasan asalinta idan k'arya nai saika fad'a" sai kuma ta k'ara masa Wani kallo ta ce "waya sani ma ko shigeya ce Bata da uba akai cikin ta aka jefar Dan kada asirin uwar ya tonu kai Kuma ka d'auko ta ka kawo ta gidan nan? kai shegiyar ce ma tunda nidai har yau Banga Wani nata da ya neme taba" ta fad'a tana kallan Huyaam wacce ke kallanta Bata ko kiftawa Jin abinda take fad'a. Afeef ya d'aga hannu zai Mari Fulani Salamatu jikinsa na karkarwa adai dai lokacin da Mai martaba Wanda tun d'azu ya shigo falon Amma babu Wanda yay noticing yay gyaran murya.gabad'aya suka juya suna kallan sa har Fulani Salamatu wacce zufa ta yanko mata lokaci D'aya ganin Mai martaba nan ta sunkuyar da kanta k'asa gabanta na fad'uwa tana salati tana sallallami..ihun Huda kawai sukaji tana K'iran sunan HUYAAM lokaci D'aya tai kanta.Ai a sukwane Afeef ya juya Ganin fad'uwa zatai yay sauri ya tarota zuwa jikinsa tun kafin taje k'asan, Ammie ma tai kanta tana fashewa da Kuka tare da K'iran sunanta.......


A masarautar zazzau kuwa yanzu haka k'arfe biyu da mintuna ne na Dare.Shakunmdum na tsaye a tsakiyar d'akinta waya ce kare a kunnanta bayan ta gama shirin ta tsaf na b'adda kamar da tai Dan zuwa b'angaren gimbiya Aysha dan aiwatar da aikinta.idan ba k'ura mata ido kaiba baza ka Gane mace ce ita ko kuma namiji ba saboda yadda tai shigar Dan babu Wanda zai iya Gane ta.waya ce kare a kunnanta da sukeyi ita da barzuk.tana zagaye inda take tsayen kafin ta dakata ta ce "na Gane uban gida yanzun nan zan tafi" daga can b'angaren Barzuk ya ce "Babu kuskure acikin aikin Fulani idan kuma Kika sake kika kuskure D'aya daga cikin abinda muka fad'a miki asirinki zai iya to nuwa Kuma Babu ruwanmu" shakundum ta ce cikin Tabbaci "bama zan kuskure ba uban gida" barzuk ya ce "Sa'a taki Fulanin zazzau" shakundum ta ce "godiya nake uban gida" daga haka ya kashe wayar itama sauke ta_ta ta d'auki abinda zatai aikin dasu ta nufi k'ofar fita daga d'akin.Bud'e k'ofar tai a hankali ta fito tana tafiya a hankali harta nufi stairs cikin sand'a tabi ta k'aramar K'ofar ta fice daga falon gabad'aya Babu Wanda ya ganta.Harta gama ficewa gabad'aya.da bin bango take tafiyar Dan kada Wani ya ganta tai b'angaren gimbiya Aysha da sauri...zube ta tadda duka dogarayen b'angaren gimbiya Aysha kwance suna bacci bayan ta isa da kuma tai Sa'a babu Wanda ya ganta..Wani numfashin salama ta sauke a hankali ganin ta isa part d'in.cikin sand'a ta bi ta Baya ta k'aramar k'ofar falon b'angaren, k'ofar ta tab'a taji a Bud'e take Hannu tasa ta Bud'e a hankali yadda k'ofar bazatai K'ara ba ta shiga ahankali cikin sand'a take tafiyar harta shigo tsakiyar main falorn gidan.kalle kalle ta farayi ganin Babu kowa sai k'arar AC data fan yasa ta nufi stairs d'in da zai SADA ta da b'angaren gimbiya Aysha ta haura da sauri cikin sand'a tana waige waige harta gama haurawa gabad'aya.a corridor ta tsaya tana Sauke numfashi kafin ta nufi inda d'akin gimbiya Aysha yake .tana Isa ta Tsaya a bakin k'ofar ta kasa shiga tana waige waige.tafi mintuna biyar a bakin k'ofar ta kasa shiga kafin ta iya tab'a k'ofar ta sa hannu ta Bud'e a Hankali datai Sa'a ma k'ofar ba'a rufe take ba saboda Wani lokacin Hajiya inna tana shigowa duba gimbiya Aysha lokaci lokaci acikin dare, shiyasa yauma Anty Amina Bata rufe k'ofar ba.Ahankali shakundum ta shiga Bud'e k'ofar ta yadda bazatai K'ara ba harta gama bud'ewa gabad'aya. Nan ta fara lek'awa cikin d'akin.babu haske a d'akin sai dumb light blue Wanda baida haske sosai nan ta hango iya gimbiya Aysha ce kwance saman gadon sai Anam a D'aya gadon Anty Amina Kuma Bata nan. k'arar ruwa da shakundum taji a toilet yasa ta Gane Anty Amina ce aciki cikin sauri ta shiga d'akin gadan gadan kan gadon gimbiya Aysha ta nufa Babu Bat'a lokaci ta fito da wani Abu ta watsa mata a fuskarta da duka jikinta gabad'aya .take gimbiya Aysha ta Bud'e ido jin Wani Irin zafi ya ratsa ta, tana kallan shakundum Bata ko kiftawa, kafin ta farga daga zafin daya ratsa ta tuni shakundum ta haye saman gadon ta d'agota ta zuwa jikinta nan ta fito da layar da tazo da ita zata cusa mata a cikin Bakinta. adai dai lokacin da Anty Amina ta Bud'e k'ofar toilet d'in ta fito.taku D'aya tai taji wani Irin nishi da K'aka Kari Had'i da kamar kokawa na tashi a Cikin d'akin nan da nan gaban ta ya yanke ya Fad'i ta d'aga kanta ta fara dube_dube a d'akin nan ta hango mutum ne a saman gadon gimbiya Aysha tana k'ok'arin cusawa gimbiya Aysha Abu a Baki,ai da Wani Irin speed ta nufi gadon tasa K'ara cikin kid'imewa tana cewa waye? shakundum da tayi nisa a San cimma burinta har Batama son lokacin da aka Bud'e k'ofar toilet d'in ba sai K'ara taji, cikin rud'ewa ta sauko daga saman gadon fuskarta a rufe da Wani Bak'in Abu da bama ka iya ganin komai sai k'waryar idonta.ganin Anty Amina ta nufo gunta zata kamata yasa ta nufi k'ofar fita a Wani mugun speed.da gudu Anty Amina tabi bayanta ganin tana k'ok'arin fita ta shak'o wuyan ta baya. Sha kundum ta rik'e hannun Anty Amina Dake wuyanta na ganin Anty Amina na k'ok'arin yage mata abinda ta rufe fuskarta dashi.nan dai suka fita daga d'akin Anty Amina na ihun a tai Maka musu, shakundum Kuma nata k'ok'arin k'wace kanta Dan kada Azo a kamata.Anty Amina kuwa tak'i sakinta saima Kara shak'eta da take tamau. nan Shakundum ta shiga kokawa da Anty Amina ita ko ta rik'eta gam tak'i sakinta tana cewa azo a taimaka mata ga Wani ya shigo musu d'aki .adai lokacin da Hajiya inna ta hauro stairs d'in tana tambayar meya faruwa cikin tashin hankali Jin hayaniyar tak'i k'arewa, kawai taga yadda mutum yay shigar b'adda kama baka gane shin macene ko namiji. ai shakundum ma ganin Hajiya inna ta zo ta kuma tasan tsaf zasu had'u su kamata kar asirin ta ya tonu, tuni tai k'ok'arin d'aga hannunta ta bugawa Anty Amina guiwar hannun a gefen cikin ta Babu shiri Anty Amina ta saketa da sauri jin wata azaba ta saukar mata nan ta fad'i a k'asa.shakundum tai hanyar stairs d'in da gudu zata sauka Hajiya inna ta ruk'ota Aiko nan ma shakundum ta juyo ta hankad'a Hajiya inna nan itama ta fad'i ta baje a k'asa har tana buguwa da k'arfen stair d'in. ganin duk ta gama dasu Babu mai iya tashi ya biyota yasa ita Kuma ta fara saukowa stairs d'in cikin sauri har tana had'awa da gudu _gudu ganin. guduwa fa zatai yasa Hajiya inna ta mik'e da k'yar Jiri na d'ibanta tabi bayanta tana ihun a taimaka musu ga wani yashigo musu b'angare a kama shi.mik'ewa Anty Amina itama tai tabi bayan Hajiya inna suka sauko stairs d'in. Nan suka tadda har shakundum ta kusan fita daga falon gabad'aya. adai dai da Wani dogarin ya farka agigice Jin ihun su Hajiya Inna nan shima ya yashigo falon sukai kicib'us da shakundum Dake k'ok'arin fita daga falon.Hajiya Inna ta ce cikin ihu "ka kama shi gashi nan zai fita" ganin wadda yaga Hajiya ita na nunawa tana ihun cewa ya kama shi yasa ya fisgota da k'arfi Hajiya inna ta ce "yauwa lurwanu Maza rik'e mana ta da k'arfi karta k'wace......


*End book one*

K'arshen littafi na D'aya.bazance komai akan rayuwar gidajen sarautar nan guda biyu ba. Amma ke daga Jin tafiyar labarin Kin san yanzu aka fara ta. Amma bari na Dan Baku tsokaci kad'an daga ciki.

*Tofa masu karatu Mai ke Shirin faruwa ne?shin wacece Huyaam acikin masarautar kano? shin da Gaske ne Huyaam ba 'yar gidan bace ma'ana ba Ammie da Mai martaba ne suka haifeta ba kamar yadda fulani Salamatu tazo tai baran bararma ta fad'a ko ya ya abun yake>ØÝ??*

*Mai Cece makomar Huyaam a gidan idan Hakan ta kasance?*

*shin Wani Hali Ammie zata shiga?*

*Wani mataki Mai martaba zai d'auka akan Fulani Salamatu?*

*Shin yaya soyayyar HUYAAM da AZIZ CHIROMA da Kuma ABDALLAH SHATTIMA harma da LAMID'O duk da dai shi har yanzu ta bayan fage yake Bai fito ya bayyana mata kansa ba kamar u add Sauran sukayi BA? Shin acikinsu waye zai iyi samun soyayyar Huyaam harma ya samu nasarar auren ta?*

*Shin burin Hajiya Lubabatu zai cika na ganin Salima ta auri Afeef ko Kuma bazai cika ba*?

*Shin burin Fulani Salamatu zai cika na ganin ta aurawa Aziza Wanda take cewa zata had'a ta dashi ko bazai yuba*?

*Mai zai faru idan akaje Egypt*?

*Shin asirin shakundum na tunowa ko bazai tonu ba*?

*Shin gimbiya Aysha da sultan zasu samu lafiya ko Kuma baza su samu ba*

*Shin ya labarin jaririyar gimbiya Ayush da Sha kundum ta sace ta, da Gaske ta mutum ko Kuma tana raye? shin Idan tana raye ayina take rayuwar,shin zasu had'u da iyayenta gimbiya Aysha da Mai martaba sarkin masarautar zazzau ko Kuma basa had'uwa?>ØÝ**

*Suwaye Razik'a da maina?>ØÝ

Duka amsoshin wannan tambayar suna cikin littafin HUYAAM book 2.
'yan uwa karku bari ayi wannan tafiyar Babu.

Kamar yadda na fad'a muku =ØGÜ

Littafin HUYAAM na kud'i ne a man hajar WhatsApp regular group akan naira 700 for VIP group Kuma 1k (1000) ku hanzarta ku biya ta wannan account d'in =ØGÜ

2270127432 Naja'atu umar zenith bank

Evidence of payment =ØGÜ
07066508376



*Yan Niger <ØóÝ<ØêÝ_zaku iya biyan(500 CFR) a Yanzu before mu gama free page. idan muka gama Kuma zai koma(700 CFR) . for VIP Kuma (1000 CFR)MY NITA =ØGÜ*
07066508376


Alhamdulillah! Anan na kawo k'arshen Free pages na littafin HUYAAM book one.Book 2 Kuma na kud'i ne. akan naira dariyar 700 kacal. Amma akwai discounts ga Wanda suka fara biya zasu Bada naira dariyar kacal daga yanzu zuwa ranar da zuwa ranar da zamu cigaba da paid book idan ya wuce Kuma Zaku biya normal price wato 700. Ga masu bukatar magana da Marrbuyar Kuma zakuyi tun tubarta Mai tsaye ta wannan number =ØGÜ07066508376.




Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD
*<Ø9ßHUYAAM<Ø9ß*


*NA*


*__NAJA'ATU UMAR FAROOQ __*



*__(MRS SARAKIES =Ø‹Ü)__*



*Bismillahirrahmanirrahim*


PAGE 4þã 2þã


_____________¡&


Tun bayan dasu HUYAAM suka kai Anty khadija airport suka dawo gida har yau kimanin sati d'aya kenan Afeef baiyiwa Huyaam maganar komai ba Daya dangin wai ya ganta da Aziz ko Kuma yay mata tambayar Mai yasa ya gansu tare shi.ko kad'an ko da wasa Bai mata Hakan ba, tun tana b'oyewa idan ta ganshi tana 'yar wasan b'uya dashi na karsu had'u har ta dawo da daina ta saki jikinta ta cigaba da sabgoginta ganin shi ko kallo ma Bata ishe shi ba, tun tana tunanin wata rana zai iya Mata maganar har ta dawo ta daina Damuwa da hakan ta cigaba da harkokin ta a gidan harma watarana su zauna tare dashi a main falon gidan ya gama zamansa ya tashi batareda da ya nuna mata alamar wai Yana rik'e da ita ba.Hakan yasa itama ta manta da zancen..A b'angarenta da Aziz chiroma kuwa tun tana basar dashi idan ya K'irata a waya har ta dawo tana picking call d'insa.yay ta janta da hira Wani lokacin ta tanka masa Wani lokacin kuwa tai Banza dashi ta k'yaleshi har ya gaji Dan kansa ya k'yaleta. daga baya Kuma abinda ta Gane idan tak'i tankasan Huda yake k'ira ya fadawa ya rok'e ta akan tazo ta rok'ar masa Huyaam ta dinga kula shi.to ita Kuma Huda idan taji haka saita ce masa karya Damu zata shawo masa kan Huyaam, haka zata to tai ta rok'ar Huyaam dayi mata rik'o da magiya da nasihu kala kala akan ta dinga kula Aziz ko yaya yane tana sakar masa fuska. tun Huyaam Bata sauran ta yau da gobe har ta dawo take sauraran Huda, ta yadda take D'an Kulashi sama sama harma ta dinga D'an bashi ansa a hirar da sukeyi. tun Huyaam Bata saki jikinta dashi ba harta dawo ta fara saki suke hira abinsu.to tun daga wannan Wani al'amari ya fara d'arsuwa azuciyar Huyaam game da AZIZ bawai taji tana sonshi bane sannan Kuma bawai Bata son shi ba, Haka dai take Jinsa a zuciyar ta a Wani sashe na Daban inda da Bata bashi wannan matsayin ba.ga wata iriyar shak'uwa da suka fara Yi ita dashi har mamakin kanta take Wani lokacin... tsakaninta da Abdallah shattima ma kuwa Shima dai kamar yadda take Jin Aziz haka Shima take Jinsa.sai dai har a zaciyarta bawai sonsu take ba kawai dai ta d'auke su ne matsayin masu Bata kuluwa da Kuma da d'ad'an maganganu da suke Yi a gareta....
Yanzu haka Zaune take a d'aki saman gadon ta wajen k'arfe 12 da Rabi ne na Rana. gama wayar su kenan da Aziz tana tunanin last words d'in daya fad'a mata tana murmushi.kamar wacce ta tonu da wani Abu Kuma sai tai saurin firgita ta sauko daga saman gadon da sauri tunawa da tai Ammie ta ce mata ta had'a kayanta a box Wanda zata buk'ata idan sunje Egypt Dan gobe ne idan Allah ya kaimu zasu tafi Egypt d'in,jirgin nasu na k'arfe biyu da Rabi ne na rana. da Huda ce ta ce ita zata had'a mata kayan tun d'azu data shigo d'akin ta fad'a mata,Amma gashi shine har yanzu bata zoba. Ganin time na tafiya har Yanzu wajen k'arfe shabiyu da Rabi Bata zoba yasa tai deciding gara Kawai tayi d'in kada Ammie ta K'ara zuwa tai mata magana akan had'a kayan.sauke numfashi tai nan ta K'arasa wajen box d'inta Dake a d'akin ta d'auko D'aya daga ciki ta k'arasa gaban press ta Bud'e ta fara fito da kayan da tasan zata buk'ata har suje su dawo.duk da Bata Son yaushe zasu dawo d'in ba Amma tasan baza su wuce 4 to 5 Days acan su dawo Nigeria ba.. tana cikin had'a kayan aka turo k'ofar d'akin, juyowa tai tana kallan k'ofar.Huda ce ta shigo nan ta d'auke kanta ta maida kan Abinda takeyi. Huda ta k'arasa shigowa cikin d'akin ta zauna nan Bakin gadon tana kallan yadda Huyaam ke had'a kayan nata ta ce "Mai yasa kike had'a kayan Bayan nace ni zan had'a miki?" Huyaam ta d'ago ta kalleta bayan tai zipping box d'in ta langwab'ar da kai ta ce "naga ne Baki zoba d'auka ta ma Ko kin Manta ne ni Kuma banaso Ammie ta k'ara zuwa tai min magana shiyasa kikaga nayi" Huda ta kalleta ta ce " shikenan kin kyauta ai" ta fad'a tana juyar da kanta gefe.HUYAAM tai murmushi ganin alamar Huda fushi tai ta k'araso kusa da ita ta rungumeta ta gefe ta ce "am sorry sis kiyi hak'uri kinji?" Huda ta fara tureta daga jikin ta ta ce "ni dai ki Rabu Dani" Huyaam ta ce "okay tunda Baki hak'ura ba bari naje na fito da duka kayan in yaso sai ki sake had'a min" ta fad'a tana k'ok'arin mik'ewa. Rik'o hannunta Huda tai da Sauri ta ce "karki fito dasu na hak'ura" komawa Huyaam tai ta Zauna ta ce "thank you so much sis Kinga fa tun daga Yanzu harna fara kewarki" ta fad'a tana Wani Marai raice fuska.Huda ta kalleta ta ce "same to you wallahi Amma ai naji Ammie ta ce baza ku Dad'e ba idan kuka je ko? Huyaam tai fari da ido ta ce "eh Bai fi 4 to 5 days kamar yadda muka Saba" Huda ta sauke numfashi ta ce "Allah ya Kaiku lafiya" Huyaam ta ansa mata da Ameen.bud'e k'ofar d'akin akayi gabad'ayansu suka juya suna kallan k'ofar ya Zarah ce ta lek'o ta tsaya daga nan Bakin k'ofar tana kallansu kafin ta ce "ku Kuma zaman daki Kuka koma Yi Yanzu kenan?" Tafad'a tana kallansu.murmushi Huyaam tai tana sosa Kai ta ce "laa! ya Zarah Mai kika gani? Ya Zarah ta hararesu ta ce "ai nagane kwanan bakwa zaman falo koda yaushe zaman d'aki,ke tunda kuka dawo daga Abuja na kula Kun daina zaman falo yanzu" Huda ta ce "a'a ya zahra ba Haka bane ba yanzun dai Huyaam nake Taya had'a kayanta" ya Zarah ta tab'e Baki ta ce "aishikenan intai tsami maji nidai yanzu ku taso nasa ka ku Wani aiki please" Huda ta ce "Wani aiki? Ya Zarah ta ce "Dan Allah kuje ku gyara min d'akina na samu emergency call ne daga school yanzu zan tafi Dan Allah kuyi Maza kuje kumin yanzu kafin na dawo" ansa mata sukai da Ladabi sukai mata fatan dawowa Lafiya. ansa musu tai itama sannan ta juya ta bar Bak'in k'ofar.Huyaam na kallan Huda bayan ya Zarah ta tafi ta dafe k'irji da tsoro a fuskarta ta ce cikin sanyin murya"na shiga uku Huda karfa ya Zarah ta Gane ana K'irana a waya fa?" ta fad'a tana zare ido.huda ta girgiza mata kai ta ce" bana tunanin ta Gane gaskiya Dan Kinsan ya Zarah Bata shiru indai daga Abu tofa sai tayi Magana" Huyaam ta sauke idonta k'asa ta ce "Anya kuwa Huda nifa wallahi har yanzu Ina tsoron ranar da yaya ko Kuma Ammei wani acikinsu ya sani wallahi kasheni za'ayi" Huda ta rik'o hannunta ta ce "Dan Allah kidaina zancen kisan nan Babu Dad'i bare ma Babu Wanda zai sani idan ma sun sanin Babu abinda zai faru in Sha Allah! tunda ai kowa Yasan Ya Aziz d'in" Huyaam tai shiru batai magana ba tana tunanin maganar huda. Huda ta Mik'e tsaye ta ce "Dan Allah ki taso muje muyi aikin kafin lokacin sallah yayi" numfashi Huyaam ta sauke ta d'auki wayarta suka fita daga d'akin gabad'aya jikinta Duk a Sanyaye.....


Da yamma wajen k'arfe biyar da Rabi,Anty Amina ce tsaye a jikin pres d'in kayan gimbiya Aysha tana zab'ar mata kayanta da zata sa da Wanda zata buk'ata Idan sukaje can Egypt d'in.knocking k'ofar akai bayan wasu seconds aka turo k'ofar aka shigo lokaci D'aya.Anam ce ta shigo d'akin sanye da uniform d'in islamiya a jikin ta da dukan alamu daga can ta dawo.ta k'araso shigowa har cikin d'akin bakinta d'auke da sallama , Anty Amina ta ansa mata tana cigaba da aikinta.Anam ta ajiye Jakar Hannunta Wacce take ta islamiya nan Saman kujerar dake d'akin.ta nufo Anty Amina ganin tana had'a kayan Maminta a box ta ce "Anty Ina Mami zata? Anty Amina tana cigaba da abinda take ta ce "Egypt" Anam tai murmushi ta ce "harda ni za'a? Anty Amina ta ce "a'a Banda ke" Anam tai shiru lokaci D'aya Jin ba da ita za'a tafi ba" juyowa Anty Amina tai tana kallan ta Sai Kuma ta sakar mata murmushi ta ce "Da wasa nake miki daughter Dake mana za'a Hajiya inna ta ce wa za'a barwa ke idan muka tafi muka barki ai k'afar ta k'afar ki" ta fad'a tana murmushi.ai sai Anam ta washe Baki ta ce "yeh! I love inna" nan ta ta fara murna Jin da ita za'a" Anty Amina ta ce "to jeki cire uniform d'in tukunna" juyawa Anam tai ta wuce wajen press d'in kayanta ta Bud'e ta d'auki wata doguwar riga marar nauyi sannan bar wajen ta nufi Wani D'an corridor Dake nan cikin d'akin ta fara cire uniform d'in ta sauya zuwa na gida sannan ta fito ta daga ciki ta k'araso cikin d'akin ta haye Saman gadon inda gimbiya Aysha take ta zauna nan kusa da ita tanai Mata magana kamar wacce zata ansa mata. ita dai gimbiya Aysha binta kawai take da ido.mik'ewa Anty Amina tai bayan ta gama had'a kayan ta ajiye box d'in a gefe inda nata trolling kayan yake tana kallan Anam ta ce "ki zauna tare da ita bari naje na gano Idan sultan ya had'a kayan nasa" gyad'a mata kai Anam tai ta ce "to Anty" daga haka Anty Amina ta fita daga d'akin bayan ta k'ullo musu k'ofar..Anam ta Maida hankali tana cigaba da yiwa Mamin ta zancen da take mata duk da tasan ba ansa mata zatai ba Amma Kuma ita tana Jin Dad'i aduk lokacin da take yiwa Maman nata zance.....


____________¡&


Aziza ce ta shigo b'angarensu da gudu tana dafe da Kuncinta tana kuka kamar ranta zai fita, tana ihun mommy na makance. Fulani Salamatu da take d'akinsu su Ramla ta taje kwantar da walida ta fito da sauri jin ihun Aziz wacce kamar ranta zai fita.take k'irjinta ya buga da k'arfi Jin abinda aziza ke cewa na wai ta makance.tuni ta nufeta da sauri ganin ta zube a tsakiyar falon har lokacin ihun kuka take. D'agota Fulani Salamatu tai cikin tashin hankali tana tambayar Aziza da lafiya? Aziz ta kasa magana sai ma Wani Irin kuka da take tana k'ok'arin shid'ewa.ai tuni hankalin Fulani Salamatu ya K'ara tashi ta ce cikin rawar murya "Aziza ki fad'a min Mai ya faru Maiya sameki? Da k'yar Aziza ta iya cewa "mummy

Please Login or Register in order to submit comment