Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Yaya ya ganmu,to yau d'inma so kike ya kamani Ina wayar ya kasheni ko ya_ya? gaskiya Huda bazan iya ba kiyi hak'uri wannan Karan bazan tab'a iya bin maganar kiba" ta fad'a tana kauda kanta gefe.Huda dai kallan ta Kawai take sai Kuma can ta ce "Dan Allah fa nace Huyaam, kiyi hak'uri ni wallahi tausayi yake bani shiyasa har nazo nake rok'ar ki wallahi karkiga Irin damuwar D'aya shiga ko ke kikaji sai kin tausaya masa ga magiya da rok'on Daya dinga min akan nazo na Baki hak'uri na taimaka na had'u kuyi magana sannan ki Bud'e wayarki shiyasa Yanzun ma nazo" Huyaam ta kalli Huda zatai magana wayar Huda tai ringing Huda ta kalli wayar sai Kuma ta dawo da kallonta kan Huyaam ta ce cikin sanyin murya "ya Aziz ne Dan Allah ki karb'a" Bata jira cewar taba tai picking ta ce "Hello Ya chiroma gata bari na Bata" daga haka ta Karawa Huyaam wayar kunnenta.uffan Huyaam Bata ce a wayar ba duk da Irin magiyar da Aziz yay tai mata Amma Bata tanka Saba.ita dai Huda kallan HUYAAM kawai take tana mamakin wai yau ya AZIZ ne yake mata magiya tare da ban hak'uri Amma Huyaam ta had'e Rai tak'i yin magana. tana ji yace Mata Dan Allah tai hak'uri ta kunna wayarta zai K'irata anjima, da k'yar ta ansa masa shima sai da huda tai mata magiya da Hannu sannan.godiya ya hau jero Mata kafin ya ce mata zaije masallaci.d'auke kanta tai Jin ya kashe wayar Huda tai murmushi ta ce "thank you so much sisto me bari naje nai sallah Nima" daga haka ta Mik'e.ita dai HUYAAM batace mata komai ba har Huda ta bar d'akin nan itama ta mik'e ta shige toilet d'in Dake d'akin nata Dan d'auro alwala....


Wunin yau haka Huyaam tayi shi a d'aki har dare Koda wasa bata yadda ta Sauko downstairs ba, Ammie data Kasa jurewa ta shigo ta duba ta ganin Lafiyarta lau yasa ta fice daga d'akin..har washe gari Huyaam bata fito ba sai wajen k'arfe hud'u da Rabi na yamma shima ta dalilin a ranar su Anty khadija zasu koma Abuja shiyasa ta fito saboda zasu musu rakiya zuwa airport,kuma da tai Sa'a ma Afeef baya gidan tun bayan Azhar ya fita Kuma har lokacin Bai dawo ba sannan ya Haidar NEMA zai kaisu. A hankali ta sauko downstairs d'in kowa kallanta yake ta Tarar da duka 'yan gidan suna tsaye a falon suna sallama dasu.Anty Khadija na sallama da Ammie Wanda har an Kai musu a kwatunsu zuwa mota.Anty khadija tai murmushi tana kallan Huyaam ta dafa kafad'ar ta ta ce "daughter yau zamu koma gida in Sha Allah" Huyaam tai mata murmushi ta rumgumeta ta ce "we are going miss you mummy" Anty khadija ta d'ago ta ta ce "Nima haka daughter Amma Baga waya nan ba zamu dingayi in Sha Allah" sai Kuma ta Kalli Ammie ta ce "Anty fulani zamu tafi" Ammie ta ce "Allah ya Sauke ku lafiya a gaida Ambassador" Anty khadija ta ce "zaiji in Sha Allah!" daga Haka tabi bayan su HUYAAM da siyama da Huda Wanda har sun fita daga falon gabad'aya... Anty khadija na kallansu su Huyaam Wanda suka rungume siyama bayan sun isa airport d'in da k'yar suka saki juna ganin time na tafiya suka K'ara yiwa Anty khadija sallama ta ansa musu suka tabmna rik'e da Hannun Imaan suka shiga cikin airport d'in.nan suma suka juya suka nufi Wajen motarsu Haka nan suka Rabu
Suna kewar Junan su k'afin su shiga mota Su koma gida......


____________¡&


*Bayan sati D'aya*

Da daddare Afeef na zaune a falon Mai mar taba kansa a k'asa Yana yiwa Mai martaba magana cikin ladabi har ya kai k'arshen zancen sa. Mai martaba ya Sauke numfashi bayan ya gama sauraran Afeef kafin ya ce "to Alhamdulillah! yanzu dai ka gama Musu registration din Kenan? Afeef ya ce "eh Abba" Mai martaba ya ce "yaushe zasu fara zuwa Kuma? Afeef ya ce "nan da sati biyu in Sha Allah rankai Dad'e" Mai martaba ya ce "okay ai harma Za'a Kai Huyaam Egypt d'in su dawo kafin su fara zuwa ko? Afeef ya Jin Jina kai ya ce "eh in Sha Allah Abba" Mai martaba ya ce "to masha Allah! Allah yay Maka Albarka" Afeef ya ce "Ameen rankai Dad'e" Mai martaba ya ce "jibi ne tafiyar ko? Afeef ya ce "eh rankai Dad'e jibi ne" Mai martaba ya Jin Jina kai ya ce "Kai kuma yaushe zaka koma Ingiland d'in?" Afeef na Shafa kansa ya ce "nan da one weeks ne in Sha Allah!" Mai martaba ya ce "da kai za'a kai Huyaam Egypt d'in ne ko ya_ya? Afeef ya K'ara sunkuyar da kansa k'asa ya ce "eh haka nake tunani rankai Dad'e" Mai martaba ya Sauke numfashi ya ce "Allah yayi jagora yasa adace ita kuma Allah ya Bata lafiya" Afeef ya ansa da Ameen.daga nan Kuma suka koma hirar company....


Da daddare Wajen k'arfe 2 na dare cikin masarautar zazzau.Razik'a ce tsaye a cikin wannan d'akin inda suke had'uwa ita da maina a duk lokacin da zasu k'ulla duk wani makircinsu da suke k'ullawa a cikin palace d'in. Ta kalli maina Wanda yake ta kai da komowa acikin d'akin duk da duhun dake Dakin Wanda Babu haske ko kad'an, Amma Hakan Bai Hana maina safa da narwar da yake Yi ba,Dan tunda yaji abinda Razik'a ta fad'a ya kasa nutsuwa waje D'aya Sak'awa da kwancewa kawai yake Saida ya maula Dan kansa sannan ya tsaya kusa da Razik'a fuskar sa daf da tata Yana kallanta ya ce "Razik'a kika ce jibi za'a koma da gimbiya Ayush Egypt d'in? Razik'a ta ce "eh Maina jiya Dana shiga dubata naji k'anwar ta Ameenah Suna waya da 'yar uwarta tana fad'a mata" Jin jina kai maina yayi ya ce cikin wata iriyar murya "indai hakane aikinmu a daren gobe zamu aiwatar dashi kenan" Razik'a ta ce "tabbas wannan haka yake" maina yayi Wani murmushi ya ce "shikenan kije kiyi shiri Nima Zanyi nawa kamar yadda mukai wancen Karan haka zamuyi wannan, Amma karki manta da abinda na Baki waccen lokacin" Jin jina masa kai Razik'a tai.Maina ya gyad'a kai ya ce "zan sa abawa gabad'aya dogarayen da bayin Dake b'angaren ta maganin bacci Irin na mutuwar nan yadda zasu kwanta da wuri kuma baza su tab'a farkawa ba sai washe gari,ke Kuma ki biyo ta inda kike biyowa sannan ki fita ta inda kike fitowa zan tsaya a inda nake tsayuwa nake gadinki Ina fatan kin Gane" Razik'a tai Wani murmushi na Ganin burinta na gab da cika ta ce" godiya nake sarkin masarautar zazzau na gobe" wata iriyar dariya Maina ya saki Jin abinda Razik'a ta fad'a, a duk lokacin da zatai masa wannan kirarin wani Irin Dad'i yakeji kamar yayi hauka ya ce "godiya nake sarauniyar masarutar zazzzu ta gobe" itama murmushin tai daga Haka Sukayi sallama suka fito daga cikin d'akin Kowa ya nufi b'angarensa ta boyayyiyar hanyar da suke biyowa a duk lokacin da zasuyi zama Irin wannan.....



#<Ø9ßHUYAAM
#<Ø9ßLAMID'O
#<Ø9ßAZIZ CHIROMA
#<Ø9ßAFEEF
#<Ø9ßABDALLAH SHATTIMA



Saura 1 page mu gama free pages.kuyi Maza ku hanzarta ku biya kud'in Karatunku ta wannan account d'in =ØGÜ



Littafin HUYAAM na kud'i ne regular group akan naira 500 before mu gama free pages muka gamawa Kuma zai koma 700 for VIP group Kuma 1k (1000) ku hanzarta ku biya ta wannan account d'in =ØGÜ

2270127432 Naja'atu umar zenith bank

Evidence of payment =ØGÜ
07066508376



*Yan Niger <ØóÝ<ØêÝ_zaku iya biyan(500 CFR) a Yanzu before mu gama free page. idan muka gama Kuma zai koma(700 CFR) . for VIP Kuma (1000 CFR)MY NITA =ØGÜ*
07066508376



*TALLAH! TALLAH!! TALLAH!!!*


*Ina kuke manyan mata masu capacity =؃Ü=؃Ü? Nace Ina kuke hajiyoyin gidan nan, to Maza ku Bud'e kunnuwanku ku saurarareni >ØÏÝ da kyau.Dan a yau nazo muku da Wani kyakkyawan albishir=؃Ü=ØƒÜ wanda zakuji dad'insa fiye da yadda zan fad'a muku.Nace ba, Bakuda Labarin hamshak'iya shahararriyar 'yar Kasuwar nan wacce tai K'aurin suna wajen kawo muku kayayyakinta na 'yan Gayu masu quality wato H.Empire <Øæß Lagos Mai gidan kayan sawa na mata na k'walisa da Kuma kayan kitchen?..."*

*To idan yau kuka tab'a ji ya kamata ace kun saurareni kunji da abinda nazo muku dashi. Kayan sawa kike so Wanda zaki zama tauraruwa a cikin 'Yan uwanki mata harma da Mai gida wato oga kwata kwata Hajiya ta , ko ko so kike duk inda kika gifta kallo ya koma kanki?. Ko Kuma kayan kitchen kikeso masu kyau da aminci daki bari. To Maza ku garzayo H.Empire <Øæß Lagos anan zaku samu duk Wani Irin Abu da kuke so, Dan mu kayan mu quaranti ne Hajiyata bakida tan tama akai, kudai ku gwada siya kawai zakusha mamaki Dan sai Kun bani labari. Muna Saida kaya kamar haka ka* =ØGÜ

*1,Atamfofi*
*2, lesses*
*3, Abaya*
*4, kayan kwalliya ko Wani iri ne*
5,*D'an kunnaye(jiwelleries)*
*6,takalma*
*7,hand bag*
*8, mayafai*
*9, sai Kuma kayan kitchen shima Muna sai dawa, Dan duk Wani kayan kitchen d'in da kike nema harma da Wanda Baki tab'a Gani ba ko sani to idan kikazo H.Empire <Øæß Lagos anan zaki samu duk Wani Irin kayan kitchen muna Saidawa akan farashi Mai sauk'i da rahusa siyan D'aya ko sari*.

*domun magana damu kai tsaye ko Kuma Neman K'arin bayani ku tun tub'emu ta wad'an nan numbers d'in kai tsaye kamar haka =ØIÜ+234 811 190 1302 /09020337676*


*Siyan na gari Mai da kud'i gida Hajiya ta*

*Sai mun Jiku=؃Ü=؃Ü*




07066508376________
'þ*<Ø9ßHUYAAM<Ø9ß*


*NA*


*__NAJA'ATU UMAR FAROOQ __*



*__(MRS SARAKIES =Ø‹Ü)__*



*Bismillahirrahmanirrahim*


PAGE 4þã 2þã


_____________¡&


Tun bayan dasu HUYAAM suka kai Anty khadija airport suka dawo gida har yau kimanin sati d'aya kenan Afeef baiyiwa Huyaam maganar komai ba Daya dangin wai ya ganta da Aziz ko Kuma yay mata tambayar Mai yasa ya gansu tare shi.ko kad'an ko da wasa Bai mata Hakan ba, tun tana b'oyewa idan ta ganshi tana 'yar wasan b'uya dashi na karsu had'u har ta dawo da daina ta saki jikinta ta cigaba da sabgoginta ganin shi ko kallo ma Bata ishe shi ba, tun tana tunanin wata rana zai iya Mata maganar har ta dawo ta daina Damuwa da hakan ta cigaba da harkokin ta a gidan harma watarana su zauna tare dashi a main falon gidan ya gama zamansa ya tashi batareda da ya nuna mata alamar wai Yana rik'e da ita ba.Hakan yasa itama ta manta da zancen..A b'angarenta da Aziz chiroma kuwa tun tana basar dashi idan ya K'irata a waya har ta dawo tana picking call d'insa.yay ta janta da hira Wani lokacin ta tanka masa Wani lokacin kuwa tai Banza dashi ta k'yaleshi har ya gaji Dan kansa ya k'yaleta. daga baya Kuma abinda ta Gane idan tak'i tankasan Huda yake k'ira ya fadawa ya rok'e ta akan tazo ta rok'ar masa Huyaam ta dinga kula shi.to ita Kuma Huda idan taji haka saita ce masa karya Damu zata shawo masa kan Huyaam, haka zata to tai ta rok'ar Huyaam dayi mata rik'o da magiya da nasihu kala kala akan ta dinga kula Aziz ko yaya yane tana sakar masa fuska. tun Huyaam Bata sauran ta yau da gobe har ta dawo take sauraran Huda, ta yadda take D'an Kulashi sama sama harma ta dinga D'an bashi ansa a hirar da sukeyi. tun Huyaam Bata saki jikinta dashi ba harta dawo ta fara saki suke hira abinsu.to tun daga wannan Wani al'amari ya fara d'arsuwa azuciyar Huyaam game da AZIZ bawai taji tana sonshi bane sannan Kuma bawai Bata son shi ba, Haka dai take Jinsa a zuciyar ta a Wani sashe na Daban inda da Bata bashi wannan matsayin ba.ga wata iriyar shak'uwa da suka fara Yi ita dashi har mamakin kanta take Wani lokacin... tsakaninta da Abdallah shattima ma kuwa Shima dai kamar yadda take Jin Aziz haka Shima take Jinsa.sai dai har a zaciyarta bawai sonsu take ba kawai dai ta d'auke su ne matsayin masu Bata kuluwa da Kuma da d'ad'an maganganu da suke Yi a gareta....
Yanzu haka Zaune take a d'aki saman gadon ta wajen k'arfe 12 da Rabi ne na Rana. gama wayar su kenan da Aziz tana tunanin last words d'in daya fad'a mata tana murmushi.kamar wacce ta tonu da wani Abu Kuma sai tai saurin firgita ta sauko daga saman gadon da sauri tunawa da tai Ammie ta ce mata ta had'a kayanta a box Wanda zata buk'ata idan sunje Egypt Dan gobe ne idan Allah ya kaimu zasu tafi Egypt d'in,jirgin nasu na k'arfe biyu da Rabi ne na rana. da Huda ce ta ce ita zata had'a mata kayan tun d'azu data shigo d'akin ta fad'a mata,Amma gashi shine har yanzu bata zoba. Ganin time na tafiya har Yanzu wajen k'arfe shabiyu da Rabi Bata zoba yasa tai deciding gara Kawai tayi d'in kada Ammie ta K'ara zuwa tai mata magana akan had'a kayan.sauke numfashi tai nan ta K'arasa wajen box d'inta Dake a d'akin ta d'auko D'aya daga ciki ta k'arasa gaban press ta Bud'e ta fara fito da kayan da tasan zata buk'ata har suje su dawo.duk da Bata Son yaushe zasu dawo d'in ba Amma tasan baza su wuce 4 to 5 Days acan su dawo Nigeria ba.. tana cikin had'a kayan aka turo k'ofar d'akin, juyowa tai tana kallan k'ofar.Huda ce ta shigo nan ta d'auke kanta ta maida kan Abinda takeyi. Huda ta k'arasa shigowa cikin d'akin ta zauna nan Bakin gadon tana kallan yadda Huyaam ke had'a kayan nata ta ce "Mai yasa kike had'a kayan Bayan nace ni zan had'a miki?" Huyaam ta d'ago ta kalleta bayan tai zipping box d'in ta langwab'ar da kai ta ce "naga ne Baki zoba d'auka ta ma Ko kin Manta ne ni Kuma banaso Ammie ta k'ara zuwa tai min magana shiyasa kikaga nayi" Huda ta kalleta ta ce " shikenan kin kyauta ai" ta fad'a tana juyar da kanta gefe.HUYAAM tai murmushi ganin alamar Huda fushi tai ta k'araso kusa da ita ta rungumeta ta gefe ta ce "am sorry sis kiyi hak'uri kinji?" Huda ta fara tureta daga jikin ta ta ce "ni dai ki Rabu Dani" Huyaam ta ce "okay tunda Baki hak'ura ba bari naje na fito da duka kayan in yaso sai ki sake had'a min" ta fad'a tana k'ok'arin mik'ewa. Rik'o hannunta Huda tai da Sauri ta ce "karki fito dasu na hak'ura" komawa Huyaam tai ta Zauna ta ce "thank you so much sis Kinga fa tun daga Yanzu harna fara kewarki" ta fad'a tana Wani Marai raice fuska.Huda ta kalleta ta ce "same to you wallahi Amma ai naji Ammie ta ce baza ku Dad'e ba idan kuka je ko? Huyaam tai fari da ido ta ce "eh Bai fi 4 to 5 days kamar yadda muka Saba" Huda ta sauke numfashi ta ce "Allah ya Kaiku lafiya" Huyaam ta ansa mata da Ameen.bud'e k'ofar d'akin akayi gabad'ayansu suka juya suna kallan k'ofar ya Zarah ce ta lek'o ta tsaya daga nan Bakin k'ofar tana kallansu kafin ta ce "ku Kuma zaman daki Kuka koma Yi Yanzu kenan?" Tafad'a tana kallansu.murmushi Huyaam tai tana sosa Kai ta ce "laa! ya Zarah Mai kika gani? Ya Zarah ta hararesu ta ce "ai nagane kwanan bakwa zaman falo koda yaushe zaman d'aki,ke tunda kuka dawo daga Abuja na kula Kun daina zaman falo yanzu" Huda ta ce "a'a ya zahra ba Haka bane ba yanzun dai Huyaam nake Taya had'a kayanta" ya Zarah ta tab'e Baki ta ce "aishikenan intai tsami maji nidai yanzu ku taso nasa ka ku Wani aiki please" Huda ta ce "Wani aiki? Ya Zarah ta ce "Dan Allah kuje ku gyara min d'akina na samu emergency call ne daga school yanzu zan tafi Dan Allah kuyi Maza kuje kumin yanzu kafin na dawo" ansa mata sukai da Ladabi sukai mata fatan dawowa Lafiya. ansa musu tai itama sannan ta juya ta bar Bak'in k'ofar.Huyaam na kallan Huda bayan ya Zarah ta tafi ta dafe k'irji da tsoro a fuskarta ta ce cikin sanyin murya"na shiga uku Huda karfa ya Zarah ta Gane ana K'irana a waya fa?" ta fad'a tana zare ido.huda ta girgiza mata kai ta ce" bana tunanin ta Gane gaskiya Dan Kinsan ya Zarah Bata shiru indai daga Abu tofa sai tayi Magana" Huyaam ta sauke idonta k'asa ta ce "Anya kuwa Huda nifa wallahi har yanzu Ina tsoron ranar da yaya ko Kuma Ammei wani acikinsu ya sani wallahi kasheni za'ayi" Huda ta rik'o hannunta ta ce "Dan Allah kidaina zancen kisan nan Babu Dad'i bare ma Babu Wanda zai sani idan ma sun sanin Babu abinda zai faru in Sha Allah! tunda ai kowa Yasan Ya Aziz d'in" Huyaam tai shiru batai magana ba tana tunanin maganar huda. Huda ta Mik'e tsaye ta ce "Dan Allah ki taso muje muyi aikin kafin lokacin sallah yayi" numfashi Huyaam ta sauke ta d'auki wayarta suka fita daga d'akin gabad'aya jikinta Duk a Sanyaye.....


Da yamma wajen k'arfe biyar da Rabi,Anty Amina ce tsaye a jikin pres d'in kayan gimbiya Aysha tana zab'ar mata kayanta da zata sa da Wanda zata buk'ata Idan sukaje can Egypt d'in.knocking k'ofar akai bayan wasu seconds aka turo k'ofar aka shigo lokaci D'aya.Anam ce ta shigo d'akin sanye da uniform d'in islamiya a jikin ta da dukan alamu daga can ta dawo.ta k'araso shigowa har cikin d'akin bakinta d'auke da sallama , Anty Amina ta ansa mata tana cigaba da aikinta.Anam ta ajiye Jakar Hannunta Wacce take ta islamiya nan Saman kujerar dake d'akin.ta nufo Anty Amina ganin tana had'a kayan Maminta a box ta ce "Anty Ina Mami zata? Anty Amina tana cigaba da abinda take ta ce "Egypt" Anam tai murmushi ta ce "harda ni za'a? Anty Amina ta ce "a'a Banda ke" Anam tai shiru lokaci D'aya Jin ba da ita za'a tafi ba" juyowa Anty Amina tai tana kallan ta Sai Kuma ta sakar mata murmushi ta ce "Da wasa nake miki daughter Dake mana za'a Hajiya inna ta ce wa za'a barwa ke idan muka tafi muka barki ai k'afar ta k'afar ki" ta fad'a tana murmushi.ai sai Anam ta washe Baki ta ce "yeh! I love inna" nan ta ta fara murna Jin da ita za'a" Anty Amina ta ce "to jeki cire uniform d'in tukunna" juyawa Anam tai ta wuce wajen press d'in kayanta ta Bud'e ta d'auki wata doguwar riga marar nauyi sannan bar wajen ta nufi Wani D'an corridor Dake nan cikin d'akin ta fara cire uniform d'in ta sauya zuwa na gida sannan ta fito ta daga ciki ta k'araso cikin d'akin ta haye Saman gadon inda gimbiya Aysha take ta zauna nan kusa da ita tanai Mata magana kamar wacce zata ansa mata. ita dai gimbiya Aysha binta kawai take da ido.mik'ewa Anty Amina tai bayan ta gama had'a kayan ta ajiye box d'in a gefe inda nata trolling kayan yake tana kallan Anam ta ce "ki zauna tare da ita bari naje na gano Idan sultan ya had'a kayan nasa" gyad'a mata kai Anam tai ta ce "to Anty" daga haka Anty Amina ta fita daga d'akin bayan ta k'ullo musu k'ofar..Anam ta Maida hankali tana cigaba da yiwa Mamin ta zancen da take mata duk da tasan ba ansa mata zatai ba Amma Kuma ita tana Jin Dad'i aduk lokacin da take yiwa Maman nata zance.....


____________¡&


Aziza ce ta shigo b'angarensu da gudu tana dafe da Kuncinta tana kuka kamar ranta zai fita, tana ihun mommy na makance. Fulani Salamatu da take d'akinsu su Ramla ta taje kwantar da walida ta fito da sauri jin ihun Aziz wacce kamar ranta zai fita.take k'irjinta ya buga da k'arfi Jin abinda aziza ke cewa na wai ta makance.tuni ta nufeta da sauri ganin ta zube a tsakiyar falon har lokacin ihun kuka take. D'agota Fulani Salamatu tai cikin tashin hankali tana tambayar Aziza da lafiya? Aziz ta kasa magana sai ma Wani Irin kuka da take tana k'ok'arin shid'ewa.ai tuni hankalin Fulani Salamatu ya K'ara tashi ta ce cikin rawar murya "Aziza ki fad'a min Mai ya faru Maiya sameki? Da k'yar Aziza ta iya cewa "mummy yaya ne" ta fad'a tana kasa k'arasa zancen saboda Kukan Daya kufce mata.fulani Salamatu da duk hankalinta ya gama tashi lokaci D'aya tsabar rud'ewa tama kasa Gane wanne yayan Aziza take nufi ta ce "waye Kuma wani Yaya?" Aziza ta ce "ya Afeef mana" Fulani Salamatu ta ce "to Mai Yay miki? Aziza ta ce "marina yayi sannan yay ta ball dani" fulani Salamatu ta ce "Mai kikai masa yay miki wannan zalincin haka? Aziza ta ce tana sheshshek'ar kuka "Akan Huyaam ne wai Dan mum had'u a hanya nafito daga b'angaren su ikleema zan wuce ta gaban b'angaren su ita kuma sun fito ita da Huda ko Ina zasu ban sani ba kawai ta harare ni Nima na rama sannan na wanka mata Mari Ashe yayan Yana bayansu kawai ya fusgoni ya wanka min Mari har Sau uku sannan ya dinga Ball dani" ta k'arasa fad'a tana fashewa da gunjin kuka" fulani Salamatu dai kallanta kawai take tun lokacin da take Bata labarin har ta kai k'arshe. lokaci D'aya fuskar Fulani Salamatu ta sauya zuwa B'acin Rai Jin Afeef ne wai yaywa 'yarta haka ya kumbura mata duka fuska Kuma wai akan HUYAAM.bata ce komai ba saboda Tama kasa furta ko da kalma D'aya ce ,nan ta juya ta nufi sama zuwa d'akinta, Babu dad'ewa ta dawo da mayafi a ahannunta. Aziza ta mik'e ganin mommynsu ta d'auko mayafinta da k'yar ta ce "mummy Ina zaki? Fulani Salamatu ta juyo ta ce "zuwa Zanyi wallahi yau komai zai faru Saidai ya faru na gaji da cin zalin da yake Miki Aziza akan wata can zai Yi miki wannan marin ya kumbura miki fuska Bai tsaya nan ba shine harda yay ball Dake saboda ya riga da ya Raina min hankali sannan Babu Mai d'aukar mataki akai daga uwarsa har shi kansa Mai martaba saboda zalinci sannan ace ni Kuma bazan Yi magana ba ko Kuma na d'auki mataki ba, wallahi zuwa Zanyi nayi Abinda ran kowa zai Baci a gidan nan harshi kansa mai martaban sai dai yau ya sakene" tana fad'ar haka ta juya ta nufi k'ofa. Aziza batai gigin binta ba saboda karta je ta k'ara jawa manya Afeef ya K'ara mata Wani Marin....


Gabad'aya su Ammie suna zazzaune a falon Mai Huyaam sun kallo kawai sukaga an Bud'e k'ofar falon da k'arfi anshigo har k'ofar tanayin k'ara.mik'ewa sukai gabad'ayansu da sauri ganin yadda aka han kad'o k'ofar aka shigo da mamakin waye?Amma Banda Ammie wacce ke zaune tana kallon Mai shigowar, ganin Fulani Salamatu ce ta shigo tana huci kamar wata zakanya yasa Ammie mik'ewa tsaye itama cikin nutsuwa tana kallon fulani Salamatu Wacce ke mata mugun kallo tare da sauran yaran. Amma Sai Ammie ta basar tana murmushi ta ce "sannu da zuwa fulani" Wata muguwar hararar Fulani Salamatu tai mata kafin ta ce cikin hargowa "Kinga ga alamun zama ne ya kawo ni Maryam? Nace Kinga alamun zamane ya kawomini Maryam? zuwa nai gunki ba gun mahaukacin d'anki da idan haukarsa ta Motsa yake dakar min 'ya ba. Amma kafin nan bari na fara ta Kansa Ina yake? Nace Ina yake shi marar mutuncin? Ta fad'a tana dube dube a falon kamar Wanda zata ganshi.ganin baya nan yasa ta ce da sigar warning"nazo ne na tuna masa matsayin wannan a golar yarinyar nan agidan nan da yake fifita ta akan Aziza idan har shi ya manta to ni bari yau na tuna masa" ta fad'a tana nuna Huyaam.a tare Ammie dasu ya Zarah da Huda suka kalli HUYAAM wacce fulani Salamatu ke nuna ta da yatsa.itako Huyaam Kallan fulani Salamatu kawai take tana nazarin zancen ta.Ammie ta juyo tana kallon Fulani Salamatu gabanta na Wani Irin fad'uwa lokaci D'aýÿÿÿ‚
ƒ




ˆ

Š

Œ

Ž









˜

š

œ

ž
Ÿ
 
¡
¢
£
¤
¥
¦
§
¨
©
ª
«
¬
­
®
¯
°
±
²
³
´
µ

·
¸
¹
º
»
¼
½
¾
¿
À
Á
Â
Ã
Ä
Å
Æ
Ç
È
É
Ê
Ë
Ì
Í
Î
Ï
Ð
Ñ
Ò
Ó
Ô
Õ
Ö
×
Ø
Ù
Ú
Û
Ü
Ý
Þ
ß
à
á
â
ã
ä
å
æ
ç
è
é
ê
ë
ì
í
î
ï
ð
ñ
ò
ó
ô
õ
ö
÷
ø
ù
ú
û
ü
ý
þ
ÿ
 ya Jin zancen da fulani Salamatu tazo musu dashi yau a b'angaren nata.da k'yar Ammie ta iya had'a kalamanta ta ce "Fulani Mai kike fad'a Haka ne, waye matsayin su ba D'aya da Aziza ba Agidan nan? Fulani Salamatu mata

Please Login or Register in order to submit comment