Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce "Allah ya Baki hak'uri" tsaki taja ta Kalli wayar ganin har lokacin ringing take Bai hak'ura ba kamar Mai d'aukar wuta haka ta kai hannu ta d'auki wayar takai kunne bayan tayi picking tai Shiru batai magana ba "Assalamualaikum warahmatullah". haka ya fad'a da zazzak'ar muryarsa.da k'yar Huyaam ta iya ansa masa gaisuwar a saman lab'b'anta tana Wani had'e Rai kamar Yana gabanta.tana Jin saukar numfashinsa a hankali kafin ya ce "wai Dan Allah Mai yasa baza'a bani Aran time bane na Fad'i Sak'on da nazo dashi ne? Huyaam tai shiru ta k'yaleshi.ganin tak'i magana yasa yace "Huyaam"ya fad'a da zazzak'ar muryarsa kamar shine ya rad'a mata Sunan saboda yadda ya iya furtawa.Huyaam ta ce "Wai Dan Allah waye kai ayina ka sanni da har kake K'iran suna na haka ne?" ta fad'a cikin sanyin muryarta Amma ita aganinta fad'a takeyi. lumshe idonsa yayi Yana bud'ewa lokaci D'aya yay murmushi ya ce "ai Baki tsayama kinji sak'on nawa ba". Huyaam ta ce "ok Ina jinka ka Fad'i Sak'on da zaka fad'a Ina da abinda nakeyi" yay murmushi Yana shafa sajensa ya ce "ok nasan Baki sanni ba Nima Kuma bansan kiba banma tab'a Ganin kiba sai a shekaranjiya da muka had'u a Wani park Ina patan zaki iya tunawa? Huyaam tai shiru tana sauraransa Amma kuma Batai magana ba tana tunanin maganganun sa. Ya ce "ko har kin manta ne? Ta ce cikin k'osawa"ni ban sani ba gaskiya Dan bansan Wanda muka had'u a park ba ni tunda mukaje har muka dawo babu da Wanda muka had'u" yay murmushi ya ce "okay naji Amma zaki  iya tuna Wanda ya tareku time d'in da Kuka fito daga cikin wurin" sai a time d'in Huyaam ta tuna Amma Kuma sai ta girgiza masa kai kamar Yana kallanta ta ce "I don't recognize it" yay murmushi ya ce "nasan kin Gane kawai dai so kike ki bani Wahala Huyaam". Haka ya sake fad'ar Sunan ta.Huyaam ta ce cikin k'osawa "ka gama na kashe wayata? Yay saurin cewa Noo! banma Fad'i dalilin K'iran nawa ba ai" ta ce "ok am hear you"haka ta fad'a.ya ce "can I introduce my self before or you no need" Huyaam tai fari da ido ta ce "no need" ta fad'a atak'aice. Ya ce "ok let straight to the point a gaskiya tunda idanuwana suka sauka akanki naji gabad'aya natsuwa ta bar jikina zuciyata ta aminta Dake ma'ana Ina sonki HUYAAM" ya fad'a da Wani Irin sautin da Saida shi kansa zuciyar sa buga da sauri. Jitai gabanta yay Wani Irin Fad'uwa k'irjinta sai buguwa yake da mugun k'arfi yawun bakinta ya k'afe k'af ita ko ta shiga uku wannan mutumin zai jaza mata bala'i. Katse mata tunanin da take yay ta hanyar cewa "kinyi Shiru bakiyi magana ba" Huyaam ta ce cikin rawar murya "kaga kayi hak'uri agida ba'a barinmu mu kula samari dan Allah karka jamin fad'a ko Kuma duka kayi hak'uri karka sake k'irani kayi blocking number na Dan Allah" daga haka tai saurin kashe wayar ta Mik'e jiki na rawa ta haura sama da sauri tana fashewa da Wani Irin kuka. Suka bita da kallo Siyama ta juyo kalli Huda itama ta kalleta kafin ta ce " tashi mubita Babu Musu Huda ta Mik'e suka nufi d'akinsu.... kallan Huyaam da tunda suka Shigo d'akin dazu kawai Huda take ganin yadda take kuka bil hakk'i da gaskiya kamar wace aka fad'awa Wani mugun Abu.sauke numfashi Huda tai kai Zaune kusa da Huyaam tai k'asa da murya ta ce "wai Dan Allah kukan me kike haka ne Huyaam yanzu idan mummy ta jiyo ai sai ki tada mata da hankali" Huyaam ta d'ago ta kalleta da rinan nun idanuwanta Wanda kad'a suka rine lokaci D'aya Saboda kukan da Tasha ta ce cikin rawar murya "Huda wallahi tsoro nakeji bana son Yaya yasani ko kin manta Irin worning d'in da yay mana ni wallahi sai naji dama banje gunnan ba ke rik'e wayar ma gabad'aya yanzu nake Dana sani wallahi" ta k'arasa fad'a tana rik'o hannun Huda" Huda ta kalleta a nutse ta ce "yanzu ke meye damuwarki?" Huyaam ta ce Huda tun washe garin da nazo garin nan akwai wata number kullum sai tamin text message na kalamaun soyayya har cewa akayi wai na sauka Abuja lafiya wai yayi kewa ta tunda na bar kano Shima ya bar garin kano saina dawo zai dawo Dan Allah waye wannan Huda? Bama iya number bane akwai watama wacce itama ake min sms da kalaman soyayya Dan Allah Ina ake so nasa kaina dama haka rik'e wayar yake wallahi saina ajiye ba zan iya ba" ta fad'a tana fashewa da kunjin kuka" Huda da duk magan ganun Huyaam suka d'aure mata kai ta ce "ban Gane abinda kike nufi ba?" Mik'a mata wayar ta Huyaam tai tana kallanta ta ce "ki Karanta wannan zaki fahimci Mai nake nufi" karb'ar wayar Huda tai ta fara karanta sak'onnin D'aya bayan D'aya Saida ta gama Karantawa du sannan ta kalli HUYAAM Dake kallanta ta ce "na Karanta Amma suwaye wad'annan d'in? Huyaam ta Bud'e hannu alamar Bata sani ba ta ce "Taya zan sani tunda babu Wanda ya fad'amin waye shi acikinsu wallahi Huda so suke kawai su jaza min bala'i kawai Inba haka ba meye zasu Dunga yimin messages babban abinda ya K'ara bani mamaki bai wuci ayina suka samu contact d'ina ba nifa a iya sani na daga ke sai su ikleema sai 'yan gidan mu ne kawai kuke da contact d'ina" to ayina suka samu? ta fad'a tana kallan Huda. itama Hudan dai kallanta Kawai take.siyama da fitowar daga wanka kenan ta tsaya tana kallan su ta ce "to ayina suka samu contact d'in naki? Huyaam ta kalleta ta ce "oho" Huda ta sauke numfashi ta ce "Allah ya kyauta Amma Huyaam karki musu Rashin mutunci kamar yadda mummy ta fad'a kibi kowa a hankali har Allah yasa kisan waye sannan ku Rabu lafiya" Huyaam ta kalleta ta ce "naji Amma nidai bazan K'ara d'aga K'iran ko shi Wanda ya k'irani d'azu ba"Huda ta ce "shikenan" daga haka ta Mik'e ta koma saman gadon da take kwance Siyama ta k'araso tsakiyar d'akin tana Kallan HUYAAM ta ce "na fito kije kiyi wankan" mik'ewa Huyaam tai ta sauko daga saman gadon ta shiga toilet d'in bayan ta d'aura towel......



#<9HUYAAM
#<9LAMID'O
#<9 AZIZ CHIROMA
#<9AFEEF
#<9ABDALLAH



Littafin HUYAAM na kud'i ne regular group akan naira 500 before mu gama free pages muka gamawa Kuma zai koma 700 for VIP group Kuma 1k (1000) ku hanzarta ku biya ta wannan account d'in =G

2270127432 Naja'atu umar zenith bank

Evidence of payment =G
07066508376



*Yan Niger <<_zaku iya biyan(500 CFR) a Yanzu before mu gama free page. idan muka gama Kuma zai koma(700 CFR) . for VIP Kuma (1000 CFR)MY NITA =G*
07066508376



*TALLAH! TALLAH!! TALLAH!!!*


*Ina kuke manyan mata masu capacity ==؃=؃? Nace Ina kuke hajiyoyin gidan nan, to Maza ku Bud'e kunnuwanku ku saurarareni > da kyau.Dan a yau nazo muku da Wani kyakkyawan albishir=؃=؃ wanda zakuji dad'insa fiye da yadda zan fad'a muku.Nace ba, Bakuda Labarin hamshak'iya shahararriyar 'yar Kasuwar nan wacce tai K'aurin suna wajen kawo muku kayayyakinta na 'yan Gayu masu quality wato H.Empire < Lagos Mai gidan kayan sawa na mata na k'walisa da Kuma kayan kitchen?..."*

*To idan yau kuka tab'a ji ya kamata ace kun saurareni kunji da abinda nazo muku dashi. Kayan sawa kike so Wanda zaki zama tauraruwa a cikin 'Yan uwanki mata harma da Mai gida wato oga kwata kwata Hajiya ta , ko ko so kike duk inda kika gifta kallo ya koma kanki?. Ko Kuma kayan kitchen kikeso masu kyau da aminci daki bari. To Maza ku garzayo H.Empire < Lagos anan zaku samu duk Wani Irin Abu da kuke so, Dan mu kayan mu quaranti ne Hajiyata bakida tan tama akai, kudai ku gwada siya kawai zakusha mamaki Dan sai Kun bani labari. Muna Saida kaya kamar haka ka* =G

*1,Atamfofi*
*2, lesses*
*3, Abaya*
*4, kayan kwalliya ko Wani iri ne*
5,*D'an kunnaye(jiwelleries)*
*6,takalma*
*7,hand bag*
*8, mayafai*
*9, sai Kuma kayan kitchen shima Muna sai dawa, Dan duk Wani kayan kitchen d'in da kike nema harma da Wanda Baki tab'a Gani ba ko sani to idan kikazo H.Empire < Lagos anan zaki samu duk Wani Irin kayan kitchen muna Saidawa akan farashi Mai sauk'i da rahusa siyan D'aya ko sari*.

*domun magana damu kai tsaye ko Kuma Neman K'arin bayani ku tun tub'emu ta wad'an nan numbers d'in kai tsaye kamar haka =I+234 811 190 1302 /09020337676*


*Siyan na gari Mai da kud'i gida Hajiya ta*

*Sai mun Jiku=؃=؃*





07066508376_______
'Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD


*<9HUYAAM<9*



*__NAJA'ATU UMAR FAROOQ__*


*___(MRS SARAKIES =؋)__*



My channel link =G
https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y

*Bismillahirrahmanirrahim*


PAGE 3 6


____________&


Tun daga wannan ranar kullum sai wannan mutumin da Huyaam har yau bata San sunan saba bare Kuma shi kansa ya dameta da k'ira Babu dare babu Rana, Koda ko baza ta d'auka ba baya tab'a gajiya bare ya hak'ura daga k'arshe Kuma idan yaga bazata tab'a yin picking d'in ba sai yay mata zazzafar sms na kalaman soyayya masu raza zuciyar masoya.Amma ita Huyaam ko a kwalar rigar ta saima take Ganin haka a matsayin takurata kawai yakeyi Dan Daya turo ko Bata kula ba indai ta Gani baya K'ara ko minti D'aya a wayarta take gogewa.gefe guda kuma Suma wad'an nan numbers d'in da Bata san ko suwaye ba kullum sai sun mata text message na kalaman soyayya Suma babu dare babu Rana ta rasa suwaye suke mata wannan text message d'in har mutane biyu Dan har garama shi Wanda yake k'iran nata ta sani Amma su wad'an nan biyun masu mata sms d'in Bata San ko suwaye ba bare sunan su kuma sunk'i bayyana Kansu har Yanzu agareta duk da Bata buk'atar Hakan Amma at least tasan ko suwaye yadda zata d'auki mataki akai ai yafi akan dai abarta acikin duhu tayi tunanin duniya ta rasa Gano su bare tasan suwaye... yanzu haka kwance take saman gadon da tun suka zo yake amatsayin nata bayan da tai sallahn Azhar ta koma saman gadon ta kwanta ta kasa tashi su Huda sun fita can main falor tun d'azu sunyi_sunyi ta fito ta ce musu suje tana zuwa,tunani ne fal ranta ta rasa ya zatai ta yage shi wannan Wanda yake yawan k'iran nata a waya ita har ga Allah har yau bata ji zata so Shi ko makamcin haka ba,ke ita soyayyar ma har yau bata ji zata iya ba tunda har yayansu yasa Musu doka har ga Allah Bata son karya masa wannan dokar Daya gindaya musu harta iya kula wani a bayan idonsa.tana wannan tunanin ne wayarta tai K'ara Alamar shigowar message yasa ta juya tana kallon secreen d'in wayar,D'aya daga cikin 2 numbers d'in Dake mata message ne Yay sak'on.kallan screen wayar kawai take tana karanta contents d'in Bata ko kiftawa "good afternoon my sweet, hope kin tashi Lafiya. Anya ko bazan biyoki Abujan nan ba ko na samu Wani relief kan abinda nakeji akan Rashinki kuwa? Dan Allah ki tausayawa marayan Allah wallahi zuciya ta ta kasa jira har sai kin dawo Batare da na samu nayi tozali da kyakkyawar fuskar kiba " iya a binda ya rubuta kenan.gaban tane ya yanke ya Fad'i Jin abinda ya fad'a tana zare ido tana duba d'akin kamar Wanda take tsaron Wani yaga abinda aka rubuta matan na wai ya biyo ta Abuja? Kallan wayar ta sake Yi Jin Wani sak'on ya sake shigowa "zan iya k'iranki yanzu?" iya abinda aka rubuta kenan.k'ara zare ido tai k'irjinta na bugawa da sauri da sauri ita kan ta shiga uku Waye wannan waye yake Neman ja mata bala'i haka tana zaman zamanta share hawayen da bata ji saukar suba sai danshin su kawai taji tai, Karan farko data ji zatai replying message d'in taji ko waye shi d'in.k'ara damk'e wayar tai a hannunta ta shiga Yi masa reply kamar haka "waye kai please?" kamar jira ake tai reply d'in nan da nan saiga reply ya shigo ko minti D'aya Ba'ayi ba "can I call you to introduce my self know?" iya abinda aka rubuta kenan. kallan sak'on ta dinga Yi bata ko kiftawa ta shiga Yi masa reply kamar haka "yes Yo can" alokacin Daya ga message d'in kasa gaskatawa yay Saida ya murza idonsa da kyau yaga dai da gaske ne wai yau Huyaam ce ke masa reply abinda Bai tab'a tunani ko tsammani ba, cikin sauri ya Maida akalar message d'insa zuwa k'ira yana Jin ta shiga zuciyar sa ta dinga bugawa da sauri da sauri har yaji ta katse ba'ai picking ba take Kuma jikinsa ya fara rawa ya K'ara dealing hopping tai picking azuciyarsa ya ce "gara na sanar miki da ko ni waye Dan bazan tab'a iya hak'ura har ku dawo batare da na bayyanar da kaina a gareki ba ko zanji abinda nakeji akanki ya ragu my sweet" Haka ya fad'a Yana Wani lumshe ido.ita ko Huyaam alokacin Daya k'ira kasa yin picking tai Saita tsinci kanta tana Mai fargaba da tsoron d'aga K'iran nasa take ta runtse idonta hawaye na zubowa zuciyar ta na bugawa da sauri da sauri ta runtse ido har K'iran ya katse tana ji aka sake k'ira sai da ta kusan katsewa sannan tai picking takai kunne tai shiru batai magana.shima kansa shirun yayi ya rasa Kuma Mai zai ce mata ya tsaya yana sauraran bugun zuciyarta Wanda ke bugawa da sauri da sauri ganin yak'i magana yasa Huyaam tai k'arfin halin cewa cikin rawar murya "Dan Allah waye kai? waye kai daka ke so ka sa ruyuwata acikin masifa da Bala'i kake so ka katsemin farin ciki da walwata Mai nai Maka Dan Allah?" ta fad'a tana rufe fuskarta da tafukan Hannunta Dan har ga Allah tun ranar su Suka fara tura mata da message d'in nan gabad'aya take a tsorace da damuwa tana fargabar ace yayansu ya sani ko Kuma Wanda yasa ya dinga sa Musu ido ace ya sani harya fad'a masa .Shiru yayi kamar Yana sauraran yadda take rera masa kuka a hankali Yana Jin
K'aunar ta na k'aruwa a duka sassan jikinsa dama ruhinsa gabad'aya, gyaran murya yayi ya ce Cikin muryar da ko a mafarki idan Huyaam taji ta sai ta Gane ta "okay let me introduce my self first" take Huyaam ta runtse idonta da k'arfi tana tsoron gaskata abinda zuciyar ta keson tuna tar da ita kaddai ace shine innalillahi wainna ilaihi raji'un kai Ina tasan ma bashi bane ba" maganar da yayi ne ya dawo da lta daga duniyar tunanin Data tafi " Dan Allah Huyaam duk abinda zakiji Daga gareni Dan Allah karki kice ba haka ba, Dan Allah idan kika fahimci ko waye Dan Allah karki kashe min wayata please & please Dan Allah ki tsaya ki Saurareni" Haka ya fad'a kamar zaiyi Kuka.tunda ya fara magana Bugun zuciyarta ya K'ara tsananta bugawa da sauri tana k'ok'arin rasa nutsuwarta gabad'aya shine fa shine fa. "Huyaam!" ya K'ara K'iran sunanta a karo na Biyu ya cigaba ya ce "suna na Abdul'Aziz shehu chiroman bicci Ina fatan kin Gane ni Kuma Zaki tsaya kisaura reni? Take Huyaam ta zaro ido waje Jin ko waye ya AZIZ CHIROMA fa? ya AZIZ dai na gidansu cikin rawar murya ta ce "ya chiroma dama Kaine kake ta yimin barazana da zuciya ta da wasa da hankali kasani a cikin damuwa kana tada min da hankali na Mai nai Maka Dan Allah Dana can canci haka daga gareka"? Haka ta fad'a tana toshe bakinta duka biyun"lumshe ido Aziz yayi yana sauraran yadda take rera kuka "yay karfin halin K'iran sunan ta da "Huyaam!" K'ara toshe bakinta tai jin Kuka na k'ok'arin kufce mata tun kafin Wani acikin su Huda ya jita.jin tana rera kuka yasa Aziz yay k'asa da murya ya ce "please Huyaam Dan Allah ki saurareni Kiji Abinda zan fad'a miki wallahi na kasa b'oye abinda na Dad'e tun tuni Ina fama da shi ne azucita,yanzu ne danaga bazan iya ba na kasa jurewa na zab'i Dana sanar Dake tun wuri" tsayawa yayi yana Sauke numfashin ya cigaba ya ce "tun lokacin da nake Zaune a palace ta kano na kamu da sanki Amma na kasa furtawa Miki nake ganin yanzu ne dai dai lokacin Daya dace na fad'a miki tun kafin Wani ya riga ni. Dan Allah Huyaam karki ce Bakya Sona wallahi zan iya shiga Wani Hali" ya fad'a da wata iriyar murya kamar Wanda shima zai saki Kukan. Runtse idonta ta K'ara Yi tana Jin saukar kalamansa kamar saukar ruwan dalma a kunnuwanta.jin tayi shiru yasa ya ce "say something please" ya fad'a da murya me ban tausayi.Huyaam Dake jinsa Amma Kuma ta kasa magana yasa ta Dake kai k'arfin hali ta ce "ya Aziz Yanzu Dan Allah Mai nai Maka da Zaka ce kana Sona duk 'yan matan garin kano karasa wacce zakace kana so Saini? yanzu ni nawa neke da har Zaka tsareni da kalmar soyayya ko ka manta a yanzu ne na gama secondary school zan shiga jami'a Dan Allah ka rabu Dani karka Kara k'irana kaje ka nemi dai dai dakai" ta fad'a cikin rawar murya.Aziz chiroma Da Lokaci D'aya ya dawo sense d'insa Jin abinda Huyaam ta fad'a ta fara girgiza kai ya ce cikin Tashin hankali "please Huyaam karki ce haka Dan Allah ki daure ki ansa soyayya ta wallahi Ina sonki zan iya rasa Raina idan na rasa ki" ya fad'a cikin karyewar murya. ta ke Huyaam ta k'walo ido waje Jin abinda ya fad'a duk da firgicin da take ciki ta ce "wai Dan Allah so kake Yaya ya kasheni ne? yafa hanamu kula samari Dan Allah ka k'yaleni karka sake k'irana na rok'eka Dan Allah" ta fad'a tana sheshshek'ar kuka.Aziz ya girgiza kai ya ce "indai Afeef ne zan fad'a masa cewa Ina sonki na tabbatar bazai hanaki kula niba"da sauri Huyaam ta girgiza masa kai ta ce "A'a karka k'irashi wallahi kasheni zaiyi idan yaji Dan Allah" ya ce "to naji, Amma Dan Allah zan rok'i wata Alfarma agunki, Dan Allah idan na k'iraki ki d'inga d'agawa Koda Baza kiyi magana" cikin k'osawa Huyaam ta ce "eh naji Dan Allah ka rabu Dani" tana Jin buguwar Zuciyasa . Cikin Mamakin abunda ta fad'a ya ce "da gaske kike my sweet" Bata ansa masa ba cikin sauri ta ce "please leave a lone" daga haka ta kashe wayar tana sauke numfashi kafin ta jefar nan saman gadon ta kifa kanta cikin filo tana sheshshek'ar kuka Saida tai Mai isarta sannan ta hak'ura ta koma sauke numfashi a jejere anan bacci ya d'auketa.....the Same da magrib Huyaam tana kwance saman gado har bacci ya fara d'aukar ta saboda Kukan da tai tayi d'azu da Rana yasa ciwon kai ya saukar mata Mai zafi da k'yar dai ta samu ya sauka bayan tasha magani. wayar ta Dake gefen ta ce tai ringing alamar shigowar k'ira,jawo wayar tai tana duba Mai K'iran take ranta ya B'aci taja tsaki tana K'un K'uni, wannan Mai K'iran ba Aziz bane ba wannan Wanda ya ce d'in sun Had'u a park ne Ranar shine ya K'iratan.kallan Huda tai Ganin tana kallanta yasa ta kauda kanta kamar bazatai picking ba sai Kuma tai ta kai kunne tai shiru batai magana ba "Assalamualaikum warahmatullah. barka da dare ko harma kin fara bacci ne na tasheki?" shiru tai batai magana ba yasan dama bayin zatai ba ya ce tun ya Saba ya cigaba ya ce "wai har yau Baki shirya sanin waye ni da suna na ba?" Ya fad'a Yana sauraran Mai zata ce .nan ma dai Shur6un ne ya biyo Baya kamar bazatai magana sai Kuma can ta sauke numfashi ta ce cikin k'osawa "Dan Allah waye kai mai Kuma kake buk'ata daga gareni da kuka takura min?" Ta fad'a Tana Hararar wayar.murmushi yayi har tana Jin sautinsa daga can ya ce "sanin wane ne ni abun bamai Wahala bane sarauniya ta, sannan sanin Mai nake buk'ata daga wajenki Kuma ai na fad'a miki tun tuni sai dai ko kina so na K'ara Mai Mai ta Miki ne sai nayi" ya cigaba ya ce "suna Abdullah shattima nida iyayena muna Zaune a garin Abuja kuma Ina Son HUYAAM so Mai tsananin Gaske, Kuma idan har ta bani dama zan iya zuwa har Inda take na gabatar mata da kaina a gidansu sannan ki ganni Tunda Dama kince Baki sanni ba"ya fad'a cikin sassanyar muryarsa. Huyaam ta murgud'a Baki kamar Yana kallanta ta ce "bana buk'ata" yay Wani killer smile ya ce "Mai yasa"? Ta ce "saboda mu agida ba'a barinmu kula samari tunda bamu isa ba" ya ce "okay naji Amma zaki bani dama nazo na samu Abba zan jira har lokacin da zakin fara kulasamarin nayi ALKawarin zan iya jiranki" cikin tsoro da fargaba Huyaam ta ce "a'a nidai Babu ruwana sai anjima" ta fad'a tana k'ok'arin kashe wayar yay saurin cewa"Dan Allah to ki barni na dinga k'iranki Ina Jin Jin daddad'ar Muryar ki Koda Baza ki barni Nazo gida ba?" Girgiza masa kai tai tana kashe wayar lokaci D'aya ta juya ta kwanta tai rufda ciki tana sheshshek'ar kuka...siyama Dake zaune kan gado kusa da Huda tana sauraran duk conversation d'insu ta d'aga kanta ta Kalli HUYAAM ta ce "ke wallahi wannan mutumin daga Jin muryarsa ma ko Baki ganshi ba kinsan kyakkawane wai Dan Allah waye shi? Huda ta ce "ina Wanda ya taremu ranar a park har yake cewa Huyaam ta bashi Aran lokacinta? Siyama tai Jimm alamar tunani sai Kuma can tace "tabbas na gane shi" Huda tace "to shine fa" ai tuni siyama ta mik'e Zaune da sauri tana kallan Huyaam ta ce "wallahi Huyaam Wannan mutumin ya Had'u kinsan Allah karkiyi wasa da damarki ki saurareshi Koda Baza ki bari yazo gidan bane ba ko iya waya kuke yima ai ta isa,ko Huda?" ta fad'a tana kallan Huda.Huda ta gyad'a mata kai tana murmushi Amma batai magana.can Kuma Siyama ta ce "to abin mamakin ayina ya samu contact D'inki nan ma banza tai ta k'yaleta. Huda tace "Nima Abinda nake tunani kenan Amma haryan na kasa samun ansa ta" Siyama ta ce "ita Huyaam d'in ta tambaya shi ne?" Huda ta ce "inama ma ta saurara shi da har zata sani? Siyama ta ce "uhmm to bari Idan ta huce na tambayeta".Ita dai Huyaam tana Jin su batai magana ba Dan Bata jin ko uwar had'uwa yayi zata tab'a kula shi ba, ita su barta ma da abinda yake damunta.tana wannan tunanin har bacci ya d'auketa tana jinsu suna ta hirar had'uwar da yayi sama sama...


__________&


Da daddare misalin k'arfe biyu Saura na dare a cikin masarautar zazzau, lokacin idanuwa sun rufe ma'ana kowa yayi bacci,shiru babu motsin ko wanne Maha luk'i a Cikin wannan dare,Dan ko Kukan tsuntsu bakyaji sai daddad'ar iska Dake Kad'awa tana kad'a bishiyun Dake shuke a cikin palace d'in.a Kuma wannan lokacin a Wani sashe Dake nan cikin masarautar cikin Wani d'aki mai bala'in duhu Wanda bakya tab'a ganin komai aciki ko da hannun Kane.daga tsakiyar d'akin na hango wasu mutane su biyu mace da namiji suna tsaye da dukan alamu magana sukeyi. muryar ta namijin da naji ta doki dodon kunnuwana Yana cewa macen Dake kusa dashi a tsaye "bazai yuba Razik'a,bazai yuba,Dan ko Bazan tab'a kashe sultan a yanzu ba har sai lokacin dana tsara yayi,ai ni ba sultan ne yamin Laifi ba da zan kashe shi? ni ubansa ne yamin Kuma Kinsan fansa nake d'auka akan sultan ba akan ubansa ba,saboda haka sultan Babu abinda yamin kawai dai so nake na k'unta tawa ubansa akan sarautar sarki da aka bashi Mai makon ni shiyasa nake so ciwon zuciya ya kashe shi lokaci D'aya zuciyar sa tai bundaga ya Fad'i ya mutu ta hanyar jinyar ciwon haukan da muka sawa sultan yakeyi shiyasa kikaga nake bin Komai a hankali bana gaggawa kema Kuma nake goya Miki baya kike duk abinda kika ga dama"

Please Login or Register in order to submit comment