Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ikleema ta kalli k'afar ganin Babu bandage d'in tace.


"Ikon Allah Kinga Yama cire". Ta fad'a da Mamaki.safna ta kalla itama tace .

"Ai kuwa dai Kinga Allah Mai iko wallahi k'afar ta warke Kai Masha Allah
Allah ya K'ara lafiya". HUYAAM na murmushi tace.

"Ameen" ita da ikleema.huda ce ta sauko falon ganin su safnah ta rik'e hab'a tace .


"Kune a gidan yau d'in to sannunku da zuwa". ta fad'a tana k'arasowa falon ta zauna kusa da Huyaam.ikleema tace.

"Da Suwa zaki Gani mune mana". Huda ta harareta tace .


"Dallah rufe min Baki yaushe kika fara ziyarar da har saki Fad'i haka". Safna tace. "Fad'a mata dai candy da taine yasa ta fara ziyarar.ikleema ta harari safna Huda tai murmushi ta Kalli HUYAAM tace .


"Ya zarah tace.

"Ki kai mata wayarta zatai Abu da ita".Babu musu HUYAAM ta Mik'e tace musu.

"Ina zuwa".daga haka ta nufi sama da sauri.Huda ta Maida hankalinta kansu tace.


"Ke Yanaga duk kunyi Wani haske kunyi k'iba " tana kallansu . ikleema tace.

"A'a Dama da haskenmu karatu ne yasa kika ga da d'inma munyi duhu.


Safna tace .

"Fad'a mata ikey hutun Candy ne ya dawo mana da hasken mu Kuma dama can muna dashi yo keko mun samu hutu babu inda muke zuwa daga gida sai islamiya Babu Wani tention na karatu ai dole kiga mun koma haka". Huda ta hararesu ta mike tace.

"Ina zuwa bari na kawo muku tunda yau dai kun zama Bak'i agidan".tana fad'ar haka tai hanyar kitchen ikleema ta d'aga murya tace.

"In zaki dawo gara ki dawo Dan mun Sha ruwa kafin mu fito".ko kula ta Huda batai ba ta shige kitchen d'in......




*China =*



Dawowarsa kenan daga companyn dayaje ya duba kayan da zasuyi order Wanda za'a kai musu can Ingiland d'in.gabad'aya a gajiye ya dawo gidan Dan jiya basu suka iso china ba sai wajen k'arfe D'aya Saura na dare direct hotel d'in da Yay mana tun acan ya sauka . Koda ma'aikatan suka kai masa kayansa ciki iya wanka kawai ya iya yi saboda gajiya yana Yi kuwa ya haye saman gadon ya kwanta ko abinci Bai ciba da yake dama shi abincin dare Bai Wani dameshi ba Barshi da Shan coffee ko tea idan yasha ya isheshi . washe gari Kuma Daya tashi bayan yay sallahn ASuba Bai koma bacci ba wanka kawai yayi ya shirya ya fita daga hotel d'in gabad'aya ya tafi inda zasu had'u da a bakon business d'in nasa .daga nan Kuma suka je company da zaiyi order kayan nasu Daya zo yi.to tunda yaje shine fa Bai dawo ba sai yanzu bayan sallahn isha'i wajen k'arfe 9 saura na daren ranar kenan Dan ma duka yayi sallolinsa a hanya.


Wanka Yay kawai ya shirya cikin pajamas d'insa masu taushi Wanda ko ba'a fad'a miki ba ido ma kad'ai ya isar ya tan tance Miki cewar kayan nan masu bala'in kyau ne da tsada ne. Fitowa Yay daga d'akin rik'e da wayar sa ya k'arasa falon ya zauna saman kujera ya Bud'e wayar tasa ya tura Sak'o Sannan ya ajiye nan Saman kujerar ya mik'e ya k'arasa wajen socket ya kunna sannan ya d'auki remote yay powering TV ya koma ya zauna a inda yake Zaune. babu dad'ewa Yana Zaune akai knocking d'in k'ofar falon ya d'aga kai ya Kalli k'ofar sannan ya Bada iznin shigowa.wata ma'aikaciyar hotel d'in ce tashigo falon hannunta rik'e da tray ta k'arasa har Cikin falon ta ajiye tray d'in nan kan center table d'in Dake tsakiyar falon bayan ta ajiye ta d'ago da kanta ta Kalli Afeef tace.


"Good evening sir ur dinner is here".ta fad'a cikin girmamawa .Batare da Afeef ya K'ara kallan taba idansa Yana kan TV dan tunda ya kalleta saud'aya data shigo Bai K'ara kallantaba ya Motsa bakinsa kad'an yace.


"Okay". A tak'aice.ta juya ta fita daga falon ta kullo masa k'ofar.sai wajen 40 seconds da fitarta sannan Afeef ya iya jawo table d'in zuwa gabansa ya tsaya Yana kallan tray d'in,cup d'in coffee ne Wanda sai turiri yake saboda zafinsa sai milky donot d'in da aka d'oro akai.ya sauke numfashi iya cup d'in coffee d'in kawai ya d'auka ya kai bakinsa.ya fara sipping a hankali Bai shanye duka ba ya ajiye ragowar nan saman tray d'in ya d'auki wayarsa Yana Kallan time furzar da huci Mai zafi yay daga bakin sa ganin dai dole sai yayi two days a china baiso zai kai har Friday a china ba yaso ace ayau zai koma Amma Kuma Hakan Bai yuba dole sai dai gobe idan Allah ya kaimu,goben ma yasan bazai gama abinda yake da wuri ba Dan jirgin dare zaibi zuwa ingiland daga can Kuma yace zaiyi shirin tafiya Nigeria Dan dole sai ya koma tacan ingiland d'in yaga kayan da aka kai musu sannan ya wuce Nigeria.numfashi ya Sauke Yana cigaba da lissafin yadda zaiyi squeezing time a ranar Saturday ya isa Nigeria.wayarsa ya d'auka ya duba jirgin da zai tashi aranar Saturday d'in da Kuma time k'arfe biyu yaga jirgin zai tashi a ranar asabar Kuma iya na lokacin ne daga shi Babu wani take yay booking sannan ya Maida wayar ya ajiye sai Kuma ya mik'e ya kashe TV sannan ya shiga d'aki ya kulle k'ofar.k'arasawa yay cikin d'akin har inda kayansa suke brave case d'insa ya d'auka ya Bud'e ya ciro laptop d'in shi aciki sannan ya k'arasa saman gadon ya zauna ya fara duba abun da aka tura masa d'azu daga can Ingiland d'in ko mintuna 20 baiyi ba ya kashe laptop d'in sannan ya rufe ya Maida inda ya d'aukota ya haye saman gadon ya kwanta ya lumshe idonsa Yana karanto addu'ar bacci Ahaka nan da Nan baccin kuwa ya d'auke shi ASuba ta gari Afeef.......



_____________&


*Nigeria k'asa ta=*


*Friday 4:10pm*


Huda ce zaune a d'akin HUYAAM Dan yau anan tazo ta tare tana gaban mirror idar da sallahn ta Kenan ta mik'e ta zauna kan stool d'in mirror tana kwalliya. Bude k'ofar toilet d'in d'akin akayi Huyaam ce ta fito d'aure da towel sai hijab Data D'ora akai. daga wanka ta fito Dan naga sai d'igar ruwa takeyi ta tsaya daga nan Bakin toilet d'in Bata k'araso ciki ba tsaya tana kallan Huda da mamakin haryanzu bata bar d'akin ba ta Bat'a Rai ta tura Baki gaba tace.


"Meye haka Huda? dama Baki Fita daga d'akinba kinsan fa wanka nashiga fa ko".ta fad'a tana kallan Huda.batare da Huda ta jiyo ba ta k'arasa gaban wardrobe ta Bud'e ta d'auko Irin karan data sa ajikinta doguwar rigace ta atamfa Irin tata sak da tasa ta ajiye nan saman gadon sai Kuma ta juyo tana kallon Huyaam tace.


"To dana San zaki shiga wanka sai akai yaya ?. Ta fad'a tana Bud'e ido.. Huyaam ta karasa cikin dajin tace.

"Ban saniba ai kinsan dai idan na fito shiryawa Zanyi dai koh?.."Huda ta d'auki mayafinta ta nufi k'ofar fita daga d'akin tace.

"Da kinyi hak'uri ma kinsan ba zama Zanyi ba uwar iya".tana fad'ar Hakan ta fice daga d'akin HUYAAM ta murgud'a mata Baki kamar Huda na kallanta sai kuma ta tafi ta kullo k'ofar sannan ta dawo ta zare jihab d'in jikinta ta Mai da toilet d'in sannan ta fito ta k'arasa gaban mirror ta fara Shafa lotion d'inta .bayan ta gama ta shafa powder kafin ta k'arasa inda Huda ta ajiye mata kayan Data fito mata dashi tasa San ta dawo gaban mirror tai d'auri bayan ta gama ta d'auki lip balm ta shafa a lips d'inta sannan ta d'auki turare ta fesa ajikinta ta tsaya tana kallan kanta a mirror. "ya Allah". haka na ambata araina Huyaam she looks more gorgeous dan ba k'aramin kyau tai ba ko yaya tai kwalliya sai kinga tayi kyau sosai A rayuwar ta tana San kwalliya ko kad'an Bata tab'a zama da datti Babu laifi tana da tsafta sosai kai bama ita kad'ai ba har Hudan dukansu suna da tsafta iyaka yadda ake San mace da ita .matsawa tai daga gaban mirror ta k'arasa kan gadon ta d'auki mayafinta Irin na Huda Wanda ta ajiye mata sannan ta nufi k'ofar fita daga d'akin ta jawo k'ofar ta rufe.ta tabi Wani corridor Wanda zai sada ta ta d'akin Ammie saida tai knocking k'ofar kafin ta tura ta shiga d'akin Bakinta d'auke da sallama.Ammie ta tarar tana zaune kan darduma tana karatun Al'qur'ani tunda ta idar da sallahn ASR Bata tashi daga gunba . Ammie ta d'ago bayan ta kai aya ta amsa sallamar Huyaam tana kallanta . Huyaam tai murmushi ta k'arasa kusa da ita ta zauna k'asan carpet d'in d'akin tace.

"Ammie Ina wuni". Ammie ta ansa mata tana kallanta kafin tace .

"An shirya kenan?..."ta fad'a tana murmushi.Huyaam ta gyad'a mata kai.sai Kuma tace.

"Ina Hudan take?.." tun kafin Ammie ta rufe Baki Huda tai sallama daga bakin k'ofar tana shigowa ta kalli HUYAAM tace.

"Na shiga d'akin ba kyanan Ashe nan Kika zo to ki taso mutafi ke muke jira tun d'azu fa". Ammie tace.

"Tashi kuje sai Kun dawo ku gaida mutanan gidan dukansu".suka ansa mata kafin Huyaam tabi bayan Huda wacce har ta fita daga d'akin. Ammie ta Maida kanta ta cigaba da karatunta.


Koda suka fita daga b'angaren nasu ya Zarah ce agaba tana rik'e da Hannun muneefa D'aya hannun kuma tana rik'e da wayarta bayanta Kuma Huda da Huyaam ne suna tafiya suna hira k'asa k'asa harda murmushi da kin gansu gwanin sha'awa twins sak.har suka isa b'angaren fulani Salamatu suka k'arasa shiga falon bakinsu d'auke da sallama Babu kowa a falon sai hadimar ta guda d'aya wacce ta shigo falon yanzu Jin sallamar tana kallansu ta risina tace.

"Allah ya taimakeku Barkanku da zuwa gimbiyoyin masarautar kano"ta fad'a cikin kirari ya Zarah tace .


"Baba karima Ina mummyn take?...."


Baba karima data d'ago da kanta k'asa tace.

"eh to,sun fita d'azu Babu dad'ewa gabad'ayansu kuma ni bansan inda suka tafi ba".ya Zarah tace.

"shikenan Bari mutafi idan sun dawo kice mata munzo sannan Ammie tana gaida ta". baba karima tace.

"To to Shikenan zan fad'a mata in Sha Allah takawarku lafiya 'ya'yan sarki Kuma jikokin sarki ".ya Zarah ta ansa suka fita daga falon .bayan sun bar b'angaren su Aziza part d'in su ikleema suka shiga nan ma dai Basu Dad'e ba suka fito Dan Irin tarb'ar da aka Saba musu ita akai musu wannan Karan ma inda sabo su kan ai sun Saba ma ikleema ce kawai ta sake dasu har ta rakosu Bak'in part d'in sannan ta koma daga nan b'angaren antynsu ikleema suka shiga nan ma dai Basu Dad'e ba suka fito sai suka k'arasa last part wato part d'in su safnah.


Sun shiga sun Tarar da gabad'ayansu zaune a falon har lamid'o Wanda ke zaune suna magana da umminsu atare suka ansa musu sallamar su har suka k'araso suka zauna suka gaida ummi ummi ta ansa musu da kulawa kafin su gaida ya lamid'o.

Lamid'o ya ansa musu da murmushi a fuskarsa Yana kallan Huyaam kafin ya janye idonsa ya mik'e Yana kallan umminsu yace.


"Bari naje na dawo ummi".ummi tace.

"shikenan sai ka dawo".sai Kuma ta Maida kallanta kan su ya Zarah ganin sun zauna k'asan carpet tace.

"Ku tashi ku hau kan kujera mana ku Zauna Zarah".cikin Jin kunya suka mik'e suka hau saman kujerar ta Kallesu da murmushi tace.

"Ina Ammie?...".ya Zarah tace.

"Tana gaishe ki ". Ummi tace .

"Ina ansawa". Sai Kuma ta kalli HUYAAM tace.

"ya jikin daughter?jiki ya warke ko?.."Huyaam tai murmushi tace .


"Da sauk'i ummi".


Ummi tace .

"Allah ya Kara lafiya naje jiya ai kina bacci". HUYAAM tai murmushi Amma batai magana ba.ruwa da drink's safna ta kawo musu kafin ta koma ta zauna kusa dasu HUYAAM Suna hira.sun Dad'e a b'angaren su safna kafin suyiwa ummi sallama su tafi ganin ana K'iran sallahn magrib...A hanya suka had'u da Aziz chiroma ya fito daga part d'insu zai tafi masallaci Dan d'azu da suka shiga b'angaren su Basu ganshi ba Huda ta Bud'e Baki bayan ya k'araso tana kallansa tace.

"Ya chiroma yaushe kazo ka?.. ta fad'a da mamakin ganinsa .Yana kallan Huda da murmushi yace.

" jiya nazo Kuna islamiya naje har b'angarenku lokacin Baku dawo daga islamiya ba".Huda tai murmushi.ya Zarah ce ta gaida shi Yana murmushi Ya kalli ya Zarah yace .

"Lafiya lau Zarah ya school"tana murmushi tace.

"Alhamdulillah" yace.

"Masha Allah ". Huyaam ce ta D'an kalleshi itama ta gaida shi ya kalleta ya ansa mata da kulawa yace .


"Ya Friday HUYAAM".tace.

"Alhamdulillah" yace.


"Masha Allah".muneefa ce ta gaishe shi ya kamo hannunta yace.

"Muneefa tah! ya gida ya kike?.."muneefa na murmushi tace.

"Alhamdulillah". yaja kuma tunta yace.

"Good girl".Huda tai murmushi tace. "sannu da zuwa gaskiya we are happy to see u". Aziz chiroma yace.

"Yauwa Huda thank same to you ya gida anyi graduation koh?. ya fad'a Yana kallanta. Huda ta gyad'a masa kai tace.

"Munyi Ya Aziz lokacin baka nan".yay murmushi yace .


"Allah ya Sanya alkhairi gift d'inku Yana nan zan kawo muku in Sha Allah"Huda tai murmushi tace.

"Allah yasa ya chiroma muna jira".yay murmushi yace.

"In Sha soon Allah bari naje masallaci".suka ce saiya dawo daga haka yay gaba suma sukai gaba kafin su shige b'angarensu......



#<9HUYAAM
#<9Aziz Chiroma
#<9lamid'o
#<9Afeef
#<9MRS SARAKIES =؋






*Muje zuwa mutanan MRS SARAKIES =؋.ke daga Jin salon labarin kinsan zai k'ayatar ya Kuma fad'akar.akwai chakwakiya sosai anan gaba Dan labarin ma yanzu muka fara shi*.


*ga masu buk'atar fara payments zaku iya sa kud'inku a yanzu before mu gama free pages Regular group akan naira 500 kacal idan kuma muka gama Free pages zai koma 700 ne.ga masu buk'atar Vip Kuma 2 pages a Rana zaku iya biyan nai 1000 kacal. ku hanzarta ku fara biya tun kafin mu gama free pages.zaku iya tura kud'in ta wannan account d'in =G*


2270127432 Naja'atu umar
Zenith bank

Evidence of payment (shaidar biya )via
07066508376

Da zarar mungama free pages Kuma zamu sa duk Wanda ya biya kud'in sa a paid group, karku bari ayi wannan tafiyar Babu ku =؃=؃ mutanan arziki.





07066508376________
'Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD



*<9HUYAAM<9*


*NA*


*__NAJA'ATU UMAR FAROOQ __*



*__(MRS SARAKIES =؋)__*



*PAID BOOK =*


*FREE PAGES*



*PAGE 1 7 *



*Tallah! Tallah!! Tallah!!!*


*Ina kuke hajiyoyin gidan nan,nace Ina kuke hajiyoyin gidan nan?to maza ku matso ga wata garab'asa ta zomu har inda kuke=؃=؃?.*


*Hajiya kaya Kikeso na fita kunya cikin taro ku Kuma so kike kallo ya koma akanki acikin Taron mata idan kika shiga biki ko suna ko Kuma Wani taro na musamman.to maza idan kina so ki kankarowa kanki mutunci kizo UK collection and gallery mu gwan gwajeki da kayanmu masu quality Wanda zaki gaji ki ajiye Dan kanki Amma badai ya mutuba Muna sai da kaya kamar haka=G*


*Atamfofi da lesses*
*Abaya*
*Shadda*
*Hand bag*
*Shoe*
*Veil na manya Dana Yara*

*Socks rin hands made d'in nan masu net*.

*Hula ta 'yan Gayu*

*Siyan D'aya ko sari*

*Duk zaki samu kan Farashi Mai sauki kedai ki garzayo UK collection & gallery Kisha Mamaki*

*Domin ganawa damu ko magana damu kai tsaye ku tun tub'emu kai tsaye ta wannan number kamar haka*=I08135305790

*Sai mun jiku =؃=؃=؃*


<9<9<9<9<9<9



*Bismillahirrahmanirrahim*



____________&


Da Daddare wajen k'arfe 12 da mintuna na dare jirginsu su Afeef ya sauka a airport d'in ingiland.sannu a hankali yake saukowa daga matattakalar jirgin cikin nutsuwa yake takunna sa sanye yake cikin Shigar k'ana nan kaya sai sweater daya D'ora a saman rigar jikinsa ya rufe har Rabin fuskarsa da ita har k'arasa Saukowa.bayan ya d'auki box d'insa ya bar wajen .tuni drivern sa john dayazo d'aukarsa ya k'araso da sauri ya tari Afeef ya sunkuyar da kansa k'asa cikin girmamawa yace.

"Well come Boss".ya fad'a Yana Mik'a hannunsa zai karb'i box d'in Dake hannun Afeef . Babu musu Afeef ya Mik'a masa Yana ansa gaisawar da yake masa. Kafin yayi gaba zuwa wajen motar John yabi bayansa da Sauri har ya wuce shi yay Maza ya Bud'e masa back seat Afeef ya shiga da sauri John ya matsa wajen boots d'in ya Bud'e yayi dropping box d'in sannan rufe ya bar wajen ya k'arasa driver seat da sauri ya shiga ya ta-da motar Suka bar airport d'in...k'arfe D'aya da mintuna 10 ya kawosu gidansa.bayan John yay parking yay Maza ya Bud'ewa Afeef bayan motar ya matsa baya cikin girmamawa Afeef ya sauko a hankali ya tsaya Yana k'arewa gidan Kallo kamar Wanda ya shekara bai gansa ba.gate man da workers d'in gidan ne suka k'araso wajen motar da sauri suna yiwa Afeef barka da dawowa cikin Kulawa yake ansa Musu kafin ya fara tafiya zuwa interance d'in cikin gidan John na da biyi shi a Baya rik'e da box d'in shi. a falon farko Afeef ya tsaya ya juya Yana kallan John Daya ajiye masa box d'in a nan falon .Afeef na kallansa yace cikin deep voice d'insa.

"Follow me upstairs".daga haka ya juya ya nufi upstairs d'in. Babu musu john ya d'auki box d'in yabi bayan Afeef har zuwa bakin k'ofar d'akin sa Dake nan sama Afeef ya juya ya karb'i box d'in daga Hannun John sannan Yace.

"Thank you". A saman lab'b'ansa.John na murmushi yace.

"U are welcome boss good night".ya fad'a Yana juyowa ya bar wajen Afeef ya danna wani D'an Abu take k'ofar ta Bud'e kafin ya shiga ciki rik'e da box d'in nasa cikin gajiya....rage kayan jikinsa ya farayi kafin ya nufi toilet Dan had'a ruwan wanka....


Babu dad'ewa Afeef ya fito daga toilet d'in Yana d'igar ruwa da k'aramin towel a hannunsa Yana tsane gashin kansa dashi .bayan ya gama ya ajiye sannan ya fara shafa lotion d'insa ,ya k'arasa wardrobe ya d'auki payments d'insa ya feshe jikinsa da turaruka.a gajiye yake Hakan yasa Babu Bat'a lokaci ya haye saman gadon ya kwanta yana lumshe ido at the same time Kuma Yana Karanto addu'ar bacci......



*Nigeria*


K'arfe 8:30 am na safe. HUYAAM ce tsaye gaban mirror tana fesa turare a jikinta.sanye take cikin shigar uniform na islamiya Dayake yau Saturday suna da islamiya kuma har k'arfe biyar da Rabi zasukai. hijab d'in har k'asa yake ba k'aramin kyau hijab d'in yayi mata ba..fitowa tai daga d'akin bayan ta rufo k'ofar Hannunta rik'e da bag d'in islamiyarta wacce ke d'auke da Al'qur'ani da sauran littafan da sukeyi..d'akin Ammie ta fara lek'awa ganin Bata ciki yasa ta sauka downstairs sanin Ammien baza ta wuce nan ba..a stairs suka had'u da Huda wacce tazo K'iranta Jin shiru har lokacin HUYAAM Bata sauko ba.Dan tun d'azu su suka shirya ita kawai suke jira .Huda na kallon HUYAAM tace.


"Haba Dan Allah kefa muke jira tun d'azu fa?...."Huda ta fad'a kamar zatai kuka.huyaam ta k'yalk'yale da Dariya tace .


"To mama Huda ai Gani na fito yanzu ko?.."ta fad'a tana k'ok'arin rab'awa ta gefenta zata sauka.huda ta harareta tace .

"Wato abin dariya ma na zama ko?...."Huyaam ta zaro ido tace .

"A'a nidai bance haka ba Ya Huda ta fad'a tana gimtse dariyarta ganin Irin kallon da Huda take mata.Huda tai k'wafa tace.

"Wallahi HUYAAM ki canza hali Dan wannan ba Hali Mai kyau bane ba.Ace kullum kece k'arshen bacci a gidan nan Amma Kuma kece k'arshen tashi ga Kuma shirin ma kullum kece k'arshe". Ta fad'a tana biyo bayan Huyaam wacce har ta sauka k'asa tana dariya k'asa k'asa.A falor Huyaam ta Tarar da Ammie ta k'arasa ta rungumeta tace .


"Nagama shiryawa Ammie Sai mun dawo".t a fad'a tana murmushi.Ammie tace.

"Allah ya tsare".Huda tai hanyar k'ofar fita daga falon tana cewa. "Idan ma bakiyi breakfast ba ke kika sani mudai tafiya zamuyi,Kuma wallahi Baki isa kin makarar damu kince sai kin tsaya kinyi breakfast ba ku taho mu tafi time fa na tafiya". ta fad'a tana k'ok'arin fita daga falon.Ammie ta kalleta da mamaki tace.


"Huyaam d'in Bata ci abinci ba zakice wai ku taho ku tafi Huda? naga shi kansa karatun Sai anci Abinci yake yiwuwa ko?...". HUYAAM na
kallan Ammie tace.


"Laaa!! Ammie nayi breakfast d'inma fa tun d'azu". Ammie na kallanta tace.


"Yaushe kika Yi d'in?..." Huda itama kanta fasa fita tai ta juyo, tsayawa tai tana kallan Huyaam jin abinda ta fad'a, sannan taji Irin ansar da zata bawa Ammie.. Huyaam na murmushi tace.

"Wallahi d'azu nai time d'in duk Kon bar dining d'in,Dan Ina expecting ma Kuna gamayin breakfast ni Kuma na fito Saida nayi sannan naje nai wanka ma". Ammie tace.

"Nidai ban Yardaba zoki wuce kije kiyi breakfast D'inki su tafi su barkin nasan halinki Huyaam yin breakfast d'in ne kawai bakya son Yi". Huyaam ta marai raice Jin Ammie zata K'ara sata cin Wani abincin tace.


"Wallahi Ammie nayi idan Kuma Baki yadda ba ki tambayi baba magajiya ma Ina zaune ta shigo falon kuma taga lokacin da nakeyi".ko rufe Baki HUYAAM batai ba sai ga baba magajiya nan ta shigo falon hannunta rik'e da Jakar muneefa wacce ta d'auko mata a d'aki ta Mik'awa muneefa tana cewa.


"Gashi Auta na Samo miki". Ammie ta kalli baba magajiya tace.

"Magjiya da Gaske ne d'azu bayan barinmu dining Huyaam ta fito tayi breakfast tsakani da Allah zaki fad'a min?...."baba magajiya tana D'an murmushi ta kalli Ammie tace.


"Eh ranki Dad'e d'azu bayan Kun gama karyawa naga itama ta fito taci abincin". Ammie ta sauke numfashi tace.


"Shikenan na yarda tunda magajiya ta ganki". Huyaam tai murmushi Ammie tace.

" ai dama na fad'a miki.

Ammie tace.

"Yau yayanku zai dawo bansani ba ko zaku rigashi dawowa ko Kuma shi zai rigaku".ta fad'a tana kallansu. gabad'aya sai faskarsu ta washe da murmushi. Huyaam tace.


"Wayyo Ammie! yau Yaya zai dawo? Ta fad'a cikin farin ciki .


Ya zarah dasu huda suka ce Allah ya dawo dashi lafiya. Huda Kuma ta K'ara da cewa.

"Allah yasa mu rigashi dawowa Ammie". Muneefa tace.

"Ameen".Huyaam Kuma tana tura Baki gaba tace.

"shine Kuma dawowa unexpected ko a fad'a mana day d'in?...." Ammie ta rik'e hab'a tace .


"iKon Allah to Nima bai fad'a mini exact day d'in ba shiyasa ban fad'a muku ba, saboda shima Bai d'auka zai dawo a yau d'in ba saboda yanayin tafiyar tasu Dan zuwan nasa k'ila wa k'ala ne". Huyaam ta rausayar da kai tace.

"Shikenan Allah ya dawo dashi lafiya". Ammie tace.

"Shikenan wannan itace addu'a Mai kyau,ku kuce ku tafi time na tafiya". juyawa sukai suka fita daga falon bayan sun K'ara yiwa Ammei sallama...


____________&


Tun k'arfe 10 na safe Afeef ya bar gidansa bayan yay sallama da ma'aikatan gidan ya Kuma barmu su ragamar kula dashi tunda dama sun Saba su suke kula masa da gidan ko Yana nan ko Baya nan to yanzu ma Hakan ce ta kasance... John ne yay parking a dai dai Wani k'aton building Dake cikin companing nasu fitowa daga cikin motar yay bayan John ya Bud'e masa.sannu a hankali ya fara takawa zuwa wajen Wani bature Wanda ke tsaye Yana jiran Isowar Afeef d'in tareda da yaransa Kuma shine Head na b'angaren gabad'aya ya taho da sauri da takarta a ahannunsa Afeef ya tsaya ganin ya Mik'a masa hannu suka gaisa baturen na murmushi yace.

"Well come Boss.the orders is here since yesterday afternoon".ya fad'a Yana kallan Afeef.

Afeef ya Jin Jina kai yay gaba Yana cewa "Alright, let's go nd see". Daga haka suka bi bayansa... Abubuwan da yay ordering nasu gabad'aya babu Wanda ba'a kawo musu ba komai sai da aka kawo su. fitowa Yay daga wajen bayan yaga komai Yana kallan baturen Dake rubuce rubuce jikin jotter hannunsa yace cikin harshen turanci.


"Mr Patrick I will take my lift not long in Sha Allah,so make sure everything is going well before I came back". Ya fad'a Yana kallansa.mr Patrick ya Jin Jina kai in a serious talk yace.

"I promise boss".Afeef ya Jin Jina kai yace.

"Thank you so much, but let me go to the office before I Left".Mr Patrick yay murmushi yace.


"Self trib boss u have great Nigeria also".ya fad'a Yana murmushi Afeef yay Murmushi da Bai shirya ba Bai San Mai yasa ba mr Patrick Yana San Nigeria indai akace Afeef zai tafi Nigeria tofa sai yace ya gaida Nigeria.dain murmushin yayi ya shige motar John ya shiga driver seat yay zoom off suka bar wajen sukai Wani building inda anan office d'in Afeef yake..... k'arfe D'aya da Rabi Saura idar da sallahr sa kenan ya fito daga office d'insa Yana kallan time .John Dake zaune cikin motar Yana jiransa yana kallan fitowarsa tun kafin Afeef ya k'araso Yay Maza

Please Login or Register in order to submit comment