Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sallah.



Suko su Huyaam suna shiga part d'insu suka nunawa Ammie kayan da suka Siyo.Ammie tai godiya tace idan Mai martaba ma yashigo anjima suje suyi masa godiya suka ansa mata da to sannan suka shige D'aki Dan d'auro alwala suma suyi sallah.


Wajen k'arfe na daren ranar Mai martaba yana Zauna a falonsa tare da ya haidar suna magana su Huyaam suka shigo bakinsu d'auke da sallama suka k'arasa suka d'urkusa har kusa Mai suna suka had'a Baki wajen gaida shi.

Mai martaba Yana kishin gid'e jikin tuntun sarautan dake falon ya ansa musu da kulawa Yana gyara zamansa.


Sannan suka juya suka gaida ya haidar.ya haidar ya ansa musu . Suka juya Suka fuskanci Mai martaba huyaam tai murmushi tace .


"Abba munga Sak'o munje munyi shopping d'in d'azu mungode Sosai Allah ya K'ara Bud'i Allah ya K'ara girma". ta fad'a tana murmushi.itama Huda ma tai masa nata godiyar.mai marataba ya Jin jina kai Yana kallan su Yace.


"Babu komai Allah ya Bada good results". Ya fad'a Yana kallansu .sukai murmushi gabad'ayansu suna sunkuyar da kansu k'asa Basu Dad'e a falon ba sukai masa sallama suka tafi Dan zasu suje suyi karatu ne Saboda exam d'in gobe.....


Bayan fitar su Nan Mai martaba ya cigaba da maganar da yakeyiwa ya haidar....



____________&



*Graduation day*



Washe gari Friday ranar data zamto the best Rana awajen su Huda more especially ma Huyaam. wannan ranar ta zamto D'aya daga cikin ranakun da Huyaam take ganin bazata ta tab'a iya mantawa da ita ba saboda ayau idan Allah ya yarda zatai graduation na SSCE...karfe 8:30am dai dai a makarantar taiwa su Huyaam Dan exam d'in ta k'arfe 9 ce suna zuwa hole d'in exam d'in suka Wuce direct suka zauna nan zaman jiran a fara exam d'in.


K'arfe 11 dai dai su Huyaam suka gama paper su ta k'arshe.gabad'ayansu suka fito kowa sai murna yake gwanin ban sha'awa Babu Dede'wa Kuma suka wuce assembly ground Dan za'a Bada gifts d'in the Best students na this year Wanda suka fi cin maki tun daga first term har zuwa second term dama haka suke ko wanni year sukan bada gifts ga best students d'insu to wannan Karan ma hakace ta kasance.A cikin subjects d'in da sukeyi aka ware 3 sciences subjects including English wanda a shine za'a Bada gifts d'in.Assembly ground d'in ya cika mak'il da students kowa ka kalla fuskarsa tana bayyanar da farin ciki Yana yin da yake ciki... SS 3A fannin Biology HUYAAM M BELLO itace over role student wacce making ta yafi na kowa a b'angaren biology take wajen nan ya kaure da tafi da ihu haka ana congratulations Huyaam m Bello.Huyaam ta fito cikin jin kunya har gaban assembly ta tsaya ta sunkuyar da kanta k'asa.sai a fannin physics kuma aka K'ira Huda M BELLO sai wata 'yar SS 3B itace tai over role a fanning chemistry wacce k'awar su Huyaam ce itama Mai suna jidda . A fannin English ma dai Huyaam ce dai still over role nan ga akai ta tafi ana mata congratulations. take a wajen aka hau yi musu pictures Had'i da malamai sannan aka basu gifts d'in bayan anyi raping d'insu D'aya text book ne aciki wanda a kai rapping d'insa Wanda zasu musu amfani daga nan har jami'a sai agogon bangon da graduation gown da aka Basu sai enlargement pictures da akai musu tun tuni Wanda ke d'auke da pictures d'in ko wanne students a cikinsu haka aka bawa kowa nasa sannan aka K'ara Yi musu pictures kowa rik'e da gifts d'insu bayan an gama akaiwa graduate d'in addu'ar samun kyakkyawan saka mako daga k'arshe akai addu'a gabad'aya students d'in aka sallamesu..tunda suka baro assembly ground d'in ikleema da safna suka karb'i gitfs d'in suna Gani sai kace su aka bawa gifts d'in nan dai sai Wani murna suke suna Taya su Huyaam murna Amma Banda Aziza data had'e Rai Dan ita ba'a Bata ba k'iras ya rage ta saki Kuka kai tama Yi a b'oye Bata bari bane sun Gani ba,suko su Huyaam Basu ma San tana Yi ba har aka zo d'aukar su Aziza Bata Bud'e Baki tai musu magana ba bare Kuma tai musu murna Sukuwa Basu damu ba saboda sun riga da sun San halinta..


Driver Yana yin parking bayan an Bud'e musu motar duk suka fito fuskokinsu d'auke da mad'aukakin farin ciki saboda yau Rana ce ta musamman agaresu da suka Dad'e suna fatan Gani .safna da ikleema sukaiwa su Huyaam Sallama Suma sukai musu sannan kowa ya wuce part d'insu farin ciki bayyane a saman afuskarsu, na suma sun zama graduate, Amma Banda Aziza da ta cika tai fam k'iris ya rage ta fashe saboda haushi.



Aziza tana shiga part d'insu ko sallama batai ba su Ramlat suna zaune falon suna jiran dawowar Aziza su tayata murnar gama exam d'inta da kuma Murnar zama candidate da tai .ganin ta shigo falon yasa su walida duk suka mik'e sukai kanta suna K'iran sunanta tareda cewa.


"congratulations ya Aziza".suka fad'a suna k'ok'arin zuwa su rungumeta fuskokinsu d'auke da murmushi,Bayin Allah Basu kula da yadda Aziza ta shigo falon ba.... Aziza data daka musu wata uwar tsawa muryarta na rawa Basu San lokacin da suka tsaya a inda suke ba kowa ya k'ame ya kasa motsawa kusa da ita ..


Fulani Salamatu da itama da fuskarta take d'auke da farin cikin yau 'yarta ta zama candidate Amma sai fuskar ta Disha she ta maye gurbin farin ciki da damuwa ta tsaya tana kallan Aziza da Kuma tunanin Mai yasa meta haka da ita dai a saninta d'azu da safe da farin ciki Aziza ta bar gidan tana Murna tana komai Amma Shine yanzu Kuma ta dawo da b'acin Rai.fulani salamatu ta Mike ganin Aziza nata masifa ita kad'ai ta k'araso har gabanta ta kamo hannun Aziza ta zaunar ta kan kujera itama ta zauna kusa da ita tana kallanta tai k'asa da murya tace cikin lallashi...


"Meyasa meki Aziza?....", ta fad'a tana kallan Aziza.


Aziza ta fashe da Kukan da take son tayiwa Wani ko zataji dad'i tace cikin rawar murya.

"Mummy su Huda aka bawa gifts tsabar san kai Amma ni ba'a bani ba"ta fada tana sheshshek'ar kuka.


Fulani Salamatu ta dafata tace .

"Ayina aka Basu gifts d'in?..." Aziza tace. "A school ne mummy". Fulani Salamatu tace .

"Wai harda su ikleema aka bawa ne?.."Aziza ta girgiza mata kai tace.


"A'a banda su iya su biyu kad'ai aka bawa".ta fad'a cikin b'acin Rai.


Fulani Salamatu tab'e Baki kafin tace.

"Ki kwantar da hankalinki indai gifts ne kema zaki mallakeshi ai Babu Wani abun da zasu mallaka Wanda ke baza ko iya mallaka ba, saboda ki kwantar da hankalinki Dan ambasu Wani gifts d'in da Bai taka Kara ya karua ba ,Dan dai wannan D'an abinda da aka Basu ki bari kema zan aika asiyo miki iri D'aya da nasu sak babu abinda zai ban banta. next week kuma by this day kema saiki had'a party ki gayyato su ki nuna musu duk su Gani su San cewa ba wata tsiyar aka Basu ba Wanda Wani bazai iya mallaka ba bare su d'auki kansu amatsayin Wani Abun kinji ai ko?...".ta fad'a tana kallan Aziza...Aziza ta gyad'a kai.


Fulani Salamatu tace.

"karki Wani sawa kanki Damuwa Aziza kinsan banason ganin ki cikin damuwa,ki kwantar da hankalinki Babu Wanda ya isa ya fiki a gidan nan". Aziz ta k'ara gyad'a mata kai .Fulani Salamatu tace.


"yanzu dai ki tashi kije kiyi wanka idan kika huce ki sakarwa 'yan uwanki fuska Kinga tun d'azu suke Zaune suna zaman jiranki ne ki dawo Dan suyi miki murna". Ta fad'a tana murmushi.

Aziza ta gyad'a mata kai ta kalli su Ramlat tace cikin dashashshiyar Murya.

"Am sorry sister's". sai kuma ta mik'e ta haura sama zuwa d'akinta su walida suka bita da kallo fulani Salamatu Kuma ta Sauke numfashi tana Jin Wani Bak'in ciki na K'ara ruruwa aranta wato komai sai yaran nan sunfi 'yarta tai tsaki tana Jin zuciyarta na mata zafi.....



Suko su ikleema Koda suka shiga b'angaren su murna suke tayi har ikleema take bawa mamansu labarin gifts d'in da aka bawa su Huyaam.bud'ar bakin Hajiya Lubabatu sai cewa tai. "Dalla rufe min Baki ke baza kiyiwa kanki fad'a ba kiyi Karatun da kema za'a Baki gifts d'in saidai kizo kina Bada labarin yadda aka bawa wasu". Ta fad'a cikin Jin haushin itama Dan itama ta tsani ace komai 'ya'yan Ammei ne akan gaba . Jikin ikleema Yay sanyi ta tashi ta bar wajen ta shige D'aki tana mamakin halin maman nasu.


Ita ko safna data fad'awa umminsu Hajiya Aysha itakan murna ta Tayasu tace zata k'ira Ammie ma tai mata murna......






07066508376________
'Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD




*<9 HUYAAM <9*



*PAID BOOK =*


*FREE PAGES*




*NA*




*__(MRS SARAKIES =؋)__*




*Littafin HUYAAM littafin kud'ine so please get ready to start payment Dan Free pages would be end soon*



*So Karku bari ayi wannan tafiyar Babu ku masoya =؃=؃*





*Bismillahirrahmanirrahim*





PAGE 1 1



____________&


Da sallama a bakinsu su HUYAAM suka shiga falon su. Koda suka shiga ciki gabad'aya suka tadda su ya Zarah a falon da muneefa sai muneeb zaune kan kujera da dukan alamu suma zaman jiran dawowar tasu suke yi. Da gudu muneefa ta taso daga zaunan da take ta nufesu, Huyaam ta fara rumgumewa tana Murmushi da cewa.


"congratulations ya HUYAAM".ta fad'a tana fad'a murmushi....HUYAAM ta rumgumeta itama tana cewa .


"Thank you so much Auta".kafin ta saki muneefa .nan muneefa ta k'arasa ta rumgume Huda tana Murmushi da cewa .


"Congratulations ya Huda". Ta fad'a tana k'an k'ame Huda.

Huda tai murmushi itama tace


"Thank you muneefa".ta fad'a tana shafa kanta Kafin su saki juna.Nan muneeb shima yay musu congratulations Yana zaune kan kujera.huda ta ansa masa Huyaam kan da sauri ta k'arasa wajen ya Zarah Dake mata murmushi ta zauna kusa da ita tace .


"Ya zarah yau Dai Allah ya cikamun burina na zama candidate". Ta fad'a tana k'an k'ame ya Zarah cikin farin ciki.


Ya zarah tai murmushi itama ta rumgume Huyaam tace .


"Congratulations sis Allah ya Baku good results". ta fad'a tana murmushi.huyaam ta rik'o hannunta tace .


"Thanks you so much big sis kafin ta mik'e tsaye daga kusa da ya Zarah tana tattare gifts d'in data zubar a falon. Ammie ce ta sauko downstairs jin hayaniyar yaran. Huyaam tana tsaye da gifts d'in da aka Basu zata je d'akin Ammie ta nuna mata kuma sai ga Ammie ta shigo falon da sallama abakinta tana kallansu, ai tuni HUYAAM ta zube kayan hannunta nan k'asan falon ta nufi Ammie ta rungumeta tana cewa.


"Alhamdulillah ya Allah, yau dai mun zama candidate Ammie". Ta fad'a tana Wani k'an k'ame Ammie.


Huda ma ta taho da gudu ta rumgume Ammie tana dariyar farin ciki tace .


"Ammie munyi graduation yau". ta fad'a tana murmushi haka suka rungume Ammie kamar zasu kada ta suna murna.Ammie tai murmushi ta had'a hannayenta duka biyun ta rumgumosu jikinta kafin tace.


"Alhamdulillah ya Allah, Allah mungode maka daka nuna mana wannan ranar,I congratulate you once again daughters wishing you good results". Ta fad'a tana murmushi.


Gabad'aya suka had'a Baki wajen cewa Ameen.ya Zarah dai kallan su take tana murmushi haka su muneefa.Ammie ta rik'o hannunsu suka dawo cikin falon kafin ta saki hannun nasu ta zauna nan kan kujera sukuma suka d'auko gifts d'in da aka Basu da wata envelope Wadda ke d'auke da certificate d'insu aciki suka nunawa Ammie da cewa gifts d'in da aka Basu ne a school .Nan Ammie ta karb'a tana Gani tare fa tayasu murna Sosai.su ya Zarah suma duk suka Karb'a Suna Gani tare da Yi musu fatan alkhairi. Ammie ta dube su tace.


"To Kuje kuyi wanka ku sauya kaya sannan ku tafi da gifts d'in ku ajiye idan Mai martaba ya shigo anjima saiku nuna masa". ta fad'a tana kallanasu.


Suka ansa mata da girmamawa sannan suka kwashi kayan sukai sama zuwa d'akinsu dashi.



Da daddare Mai martaba yana d'akinsa Yana shiryawa su Huyaam suka shigo falonsa bakinsu d'auke da sallama.


Babu kowa a falon sai k'arar AC da fan.Dan haka suka k'araso cikin falon suka zauna nan k'asan carpet d'in falon suna zama jiransa Dan k'ila daki ya shiga.babu dad'ewa kuwa Mai martaba ya fito cikin shigar manyan kaya sai Hirami Daya yafa a kansa Irin shigar sarauta dai yayi ,bakinsa d'auki da sallama ya k'araso cikin falon Yana kallansu.


Su Huyaam Dake zaune nan k'asan carpet d'in falon batare da sun d'ago da kansu ba suka ansa masa kansu a K'asa.mai martaba ya samu waje a inda yake zama ya Zauna Yana kallansu suka had'a Baki wajen gaida shi.mai martaba ya ansa musu da kulawa.


Huyaam tana Murmushi tace.


"Abba yau dai munyi final papper mun zama candidate"ta fad'a 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~ tana murmushi.


Mai martaba ya Kallesu ganin yadda fuskokinsu ke d'auke da farin ciki ya Jin Jina kai Yana sakin murmushin shima yace.


"Masha Allah i congratulate you dears Allah yasa albarka". Fuskarsa na bayyanar da farin ciki shima..suka had'a Baki wajen cewa Ameen,nan suka Mik'a masa gifts d'in da aka Basu suka ajiye anan gabansa HUYAAM tace .


"Abba ga gifts d'in da aka Bamu a school for the best students of the year". Ta fad'a tana
murmushi.


Mai martaba yace .


"Masha Allah yaran kirki congratulations once again". ya fad'a yana d'aukar gifts d'in da suka ajiye anan gabansa yana Gani D'aya bayan D'aya.


Bayan ya gama ya d'ago Yana kallansu yace .

"I really appreciate daughters Allah ya Bada good results". Ya fad'a for happiness.suka had'a Baki wajen ansa masa.Nan dai sukai ta ta hira tareda da Mai martaba daga k'arshe dai Ya K'ara congratulations d'insu tareda Yi musu nisaha. Su kuma suna sauraransa ,Basu Dad'e a falon ba sukai masa sallama suka tafi Mai martaba ya bisu da kallo Yana Jin k'aunar yaran nasa na k'aruwa acikin zuciyarsa .dama acikinsu su ukun nan Huyaam da Huda suna da k'ok'ari sosai yadda ya kamata Amma Banda Aziza,d'azu fa da yaje b'angaren fulani Salamatu danyi mata sallama da Kuma duba yaran kafin ya shigo b'angaren Ammie Dan Kwanan tane har ya gama abinda zaiyi Amma baiga Aziza ta bashi Wani gifts da sunan ambata a school ba ,iya ka kawai data ce masa Abba munyi graduation yay mata Allah ya Sanya alkhairi kuma harya ya fito baiga Wani Abu Mai kama da gifts ba yoda ace ma ambata aida uwar tace zata fara fad'a masa saboda yasan halinta da fariya.kuma dama can yasan Aziza Bata da k'ok'ari huda da Huyaam ne kawai masu k'ok'ari Dan kan Aziza Kamar dusa haka yake Bai tab'a ganin ambawa Aziza Wani special Abu ba wai Dan tana da k'ok'ari a school ba ,kullum sai dai a bawa su HUYAAM yadda ya fahimci Aziza Bata da aiki sai shegen girman Kai da buri Irin na uwarta ya sauke numfashi Yana amsa sallamar Ammie data shigo falon.......


____________&


Washe har k'arfe Sha biyu Saura Huyaam Bata tashi daga bacci ba. itakan Huda tun K'arfe goma ta shi tai wanka ta fito Dan ita Bata Saba bacci Irin na Huyaam ba Wanda yake kamar na mutuwa tai tayi bata tab'a gajiya.dayake basuda islamiya yau Babar shugaban makarantar tasu ce ta rasu shiyasa aka Basu hutun one week kafin su koma .ganin haka yasa Ammie da Taga kowa ya tashi Amma Banda HUYAAM yasa tace tunda babu inda zasu yau a k'yaleta ta huta saboda karatun da suka Sha na exam.... k'arfe Sha biyu da kwata HUYAAM ta shi bakinta d'auke da addu'ar bacci tana Mik'a ta sauko daga saman gadon ta nufi toilet zatai wanka.babu dad'ewa ta fito ta k'arasa gaban mirror ta fara Shafa lotion d'inta masu dad'in kamshi da tsada bayan ta gama ta nufi wardrobe d'inta ta d'auko wato doguwar rigar abaya blue black Mai tsadar gaske wacce ta fito da ainihin kyanta ta k'arasa gaban mirror ta yafa mayafin a saman kanta fuskarta ta fito tayi kyau sosai ba kad'an ba,duk da bama Wani make up tai ba Amma ba k'aramin kyau tai ba ta shafa lips bolm a lips d'inta sannan ta feshe jikinta da turaruka masu Dad'in k'amshi sannan ta fito daga d'akin bayan ta jawo k'ofar ta rufe, d'akin Ammie ta lek'a taga Bata ciki ta rufe k'ofar ta sauko k'asa...


Da sallama ta sauko downstairs d'in ta Tarar da gabad'ayansu suna zaune a falon ga TV a kunne. Ammie tana zaune kan kujera 3 seater muneefa na kwance kusa da ita ta d'aura kanta saman cinyar Ammie ,sai muneeb Dake zaune k'asan carfet Yana rubutu acikin littafinsa da dukan alamu assignment yakeyi sai ya Zarah kuma Dake zaune itama kan kujera one seater tana latsa wayarta da dukan alamu chatting takeyi , Huda Kuma tana zaune tana kallo... gabad'aya suka juya suna ansa sallamarta tareda kallonta lokacin D'aya.


HUYAAM ta saki murmushi ta k'arasa wajen Ammie ta zauna kan kujerar da Ammie take zaune ta gefenta ta D'ora kanta saman kafad'ar Ammie tana cewa.


"barka da safiya Ammie". Ta fad'a tana lumshe idonta.Ammie ta kalleta ta gefen ido tace.


"Awurinki ne haryanzu safiya koh? Yanzu fa past 12 ai Rana tayi HUYAAM Safiya kuma ai saita gobe idan Allah ya kaimu". ta fad'a tana shafa kan muneefa.HUYAAM tai murmushi ta d'aga Idonta tana duba rantsatstsan agogon bangon Dake falon kafin ta rik'e Baki tana kallon Ammie da mamaki tace.


"Wallahi Ammie I think yanzu baifi 12 Saura ba fa?.." Ammie tace.


"dama kina can kin samu abinda kikeso bacci Ina zaki San time ya tafi?. HUYAAM tai murmushi tana D'ora kanta saman kafad'ar Ammie Amma Batace komai ba.


Ammie tace. "Oya tashi kije kiyi breakfast time na tafiya". Huyaam ta mik'e zata nufi dining d'in muneefa ta kalleta tace.


"Ya HUYAAM kinyi kyau" ta fad'a tana murmushi.huyaam tai mata fari da ido tace.


"nagode sis". Ammie ta kalleta ta girgiza kai tana murmushi halin Huyaam sai ita .har Huyaam ta nufi hanyar dining sai Kuma tsaya a inda take tsaye tana kallon ya Zarah tace.


"Ya zarah barka da Rana."ta fad'a tana murmushi.


Ya zarah ta d'ago da kanta daga latsa wayarta da take tana kallan Huyaam tace.


"Sannu maji Dad'in kano Wato sai yanzu kika ga damar tashi ko? kodan ba laifinki bane ba ,mu mun Isa muyi Irin wannan baccin ai sai ke ".ta fad'a tana d'auke kanta daga kallan Huyaam.Huda da batai magana ba ta juyo tace.


"Wallahi fa ya zarah ni ban isa ma nayi Irin wannan baccinba". ta fad'a tana kallan Huyaam

Ya zarah tace.

"Ai wallahi itama ta kusa dainawa Yaya Yana dawowa ne".ta fad'a tana kallan Huyaam wacce ta take kallanta da mamakin abinda ta fad'a.


Huda ta Mik'e zaune daga kishin gid'en da take jikin kujera jin abinda ya Zarah ta fad'a da Mamaki tace.


"Da Gaske ya Zarah Yaushe zai dawo?...."ta fad'a tana kallan ya Zarah.


Ya zarah tace uhmmm.

"Ki tambayi Ammie ita tasan yaushe zai dawo". ai Jin haka yasa Huyaam ta dawo falon da sauri babu shiri k'arasa ta tsaya gaban Ammie tace.


"Ammie yaushe yayan zai dawo?..." Ta fad'a tana kallan Ammie.


Ammie ta d'ago ta kalleta tace.


"Nan da two weeks ne in Sha Allah aikinji ko? To Dan Allah jeki ci abincin" ta fad'a tana kallan Huyaam.


HUYAAM ta saki murmushi ta d'aga hannayenta duka biyun sama irin dai yadda yara sukeyi idan Wani abun farin ciki ya samesu tace.


"Yeeh Yaya zai dawo,Aiko Yana dawowa Muma za'a siya mana waya irinta ya Zarah dama haka Abba yace idan Yaya dawo za'a siya mana waya".ta fad'a tana Wani Irin juyi anan tsakiyar falon.ba Ammie ba hatta ya Zarah da huda Kai harma dasu muneefa kallon Huyaam kawai sukeyi da mamakn abinda tai. Ammie ta rik'e baki tace.


"Oh!!! Ni Maryam nagodewa Allah Daya bani 'ya Mai hankali". Ta fad'a tana kallan Huyaam sai a lokacin HUYAAM ta lura a abinda tai Dan wallahi ita murna ce ta sata tai hakan .ta sunkuyar da kai k'asa cikin Jin kunyar abinda tai tace.

"wallahi Ammie mantawa nai ba ni kad'ai bace murna ce ta sani haka".ta fad'a tana nufar dining d'in.ya Zarah tace.


"Allah ya shiryeku keda Huda itama badan a Zaune take ba had'uwa zasuyi suyi juyin tare Ammie Dan naga Tunda suka fara zana WAEC kansu yake rawa nasu zasu zama graduate sai kace akansu aka fara candy".ta fad'a tana hararar su.


Huda tai murmushi tace.

"Wallahi ya Zarah banda ni iya itace ke Yi"ta fad'a tana kallan Huyaam.


Ya zarah tace .


"Hmm kudai cigaba karku nutsu har Yaya ya dawo Baku nutsu ba Kunsan ai baya d'aukar shirmenku ko?.."HUYAAM tai murmushi tace.


"In Sha Allah kafin nan ma nikan na nutsu tunda nayi graduation d'in ai zan dawo kamar da"ta fad'a tana kallan Huda.


Huda ta harareta tace.


"Ai ke Huyaam ko zaki daina komai Banga alamar zaki daina bacci ba". kafin Huyaam ta Bata ansa sukaji Muryar Ammie tace.


"ya isa haka kuyi shiru ku barta taje taci abincin mana time na tafiya".Babu Wanda ya K'ara magana acikinsu .Huyaam ta zauna kan kujerar dining d'in ta Bud'e warmers d'in ta zuba abincin da Yay mata ta fara ci gefe D'aya Kuma tana tunanin dawowar yayan nasu Dan tabbas tasan baya son hayaniya indai Yana gidan nan to Baki isa kunyi wani motsi ba sai Dai idan baya nan ta sauke numfashi ta kauda tunaninta gefe tana cigaba da cin abincinta........



Da yamma ya haidar ya shigo falon bakinsa d'auke da sallama Babu kowa afalon hakan ya k'araso shigowa ciki zaiyi hanyar b'angaren da d'akinsu suke HUYAAM ta fito daga kitchen d'in downstairs da ruwan roba a hannunta tana ganinsa tai saurin cewa.


"Ya haidar!!".

Bai ansa ba ya juyo Yana kallanta. HUYAAM ta k'araso har wajen sa ta tsaya a gabansa tana kallan sa kafin ta tura Baki gaba tace.


"Ya haidar Jiya Ina ka tafi bayan kasan cewa zamuyi graduation shine baka dawo da wuri ba".ta fad'a tana Kallansa.


Ya haidar ya sauke numfashi yace.

"Bana nan Abba ne ya aikeni shiyasa".

Huyaam tai murmushi tace.

"to munyi graduation,ya Haidar na zama candidate".ta fad'a with confidence.


Ya haidar ya kalleta sama da k'asa kamar zai maketa dan haushin Abinda ta fad'a Amma saiya danne yace cikin k'asa da murya.


"To congratulations to you, yanzu Kuma sai a k'yalemu da zancen zama candidate d'in nan Wanda baya k'arewa tunda yanzu kin zama ko?..."ya fad'a Yana kallan ta .Huyaam ta gyad'a masa tace.


"Sai Kuma university ba".

Yace.


"Uhmm"kafin yay gaba.huyaam tai saurin cewa.


"ya haidar baka ga gifts d'in da aka Bamu ba fa?..."Batare da ya juyo ba yana cigaba da tafiya yace . "zan Gani anjima".

Huyaam tace.

"Na kawo Maka d'akinka?..."yace.


"Karki dameni fa nace miki sai anjima"Daga haka ya haye stairs d'in da zai kaishi b'angarensu da sauri.Huyaam ta juya ta haura sama itama tana Murmushi ita kad'ai Aranta, Dan idan ta tuno da wai yau tayi Candy sai taji Wani sabon Dad'i ya lullub'e ta ....






07066508376________
'Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD



*<9 HUYAAM <9*



*PAID BOOK =*


*FREE PAGES*



*NA*



*__(MRS SARAKIES =؋)__*



*Bismillahirrahmanirrahim*



PAGE 1 2


___________&


Haka su HUYAAM suka cigaba da Shan hutunsu na waiting results kafin kuma su shiga university.ita kan HUYAAM Bata da aiki a wannan lokacin sai na bacci, Dan Wani sabon babin bacci ta Bud'e agidan nan, Kuma Babu Mai mata magana idan Huda tai magana sai Ammie tace abarta ta huta tunda yanzu lokacin hutun sune,Suma ba'a hanasu su Huta ba ,bare su sa mata ido idan Batai huta Yanzu ba yaushe zata Zata huta suna shiga jami'a Kuma shikenan baccin ya k'are, baka Ammie take fad'a ga duk Wanda yay magana akan baccin da Huyaam takeyi.jin haka yasa Basu K'ara magana ba suka k'yaleta take Shan baccinta San ranta har Sai lokacin da ta gaji da baccin ta tashi Dan kanta......



*Bayan sati D'aya*

*After One week*



Ranar Friday da yamma wajen k'arfe 4:30pm na yamman Ranar Huda na tsaye gaban mirror d'akinsu tana d'aurin Dan kwali,Huyaam kuma har ta gama shiryawa tana zaune gefen gado tana kallan Huda Dake shiryawa lokaci D'aya ta d'auke kanta daga kallan Huda ta Maida gefe tana kallan bango.huda tana yafa mayafinta saman kayan jikinta tace.


"Huyaam Baki cemin nayi kyau ba". ta fad'a tana murmushi idanta na kallan mirror..dan fita zasuyi zasuje b'angaren fulani Salamatu Dan yau dai Aziza zatai parting ta na graduation kamar yadda fulani Salamatu ta fad'a Kuma har nan b'angaren aziza tazo ta

Please Login or Register in order to submit comment