Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

NECO da WAEC suke zanawa sune zasu fita this year yanzu haka sun zana kusan 5 papers Saura 4 su gama .


HUYAAM ta gyad'a kai kafin tace .


"Eh Abba yau bamu jeba saboda bamu da exam". Mai martaba ya Jin Jina kai sai Kuma ta cigaba tace.


"Abba kasan yaushe zamuyi graduation kuwa?..."Mai martaba ya Dan Bud'e ido Yana kallan HUYAAM yace. "Bansani ba HUYAAM.


HUYAAM tai murmushi ta k'ara gyara zamanta tace.


"Saura 4 papers mu gama, idan mukai ranar Monday to baza mu K'ara yiba sai next week by Tuesday idan Kuma mukai to bazamu K'ara yiba sai ranar Friday ,A ranar kuma zamuyi graduation Abba"ta k'arasa fad'a tana murmushin Jin Dad'i dan tana so ace yau tayi Candy.


Mai martaba yace.

"Masha Allah, Allah ya Bada sa'ar sakamako Mai kyau"wannan Karan gabad'ayansu suka ansa da Ameen.


sun Dad'e suna hira Da Mai martaba a falon ,Dan Mai martaba ya kan ware wa 'ya'yansa Wani time indai Yana gida yayi hira da iyalansa harma ya tambayi Matsalolinsu tahakane yake sanin matsalolinsu dukkansu.


Idan har yaga sun Wuce time d'in da suke zuwa yaga Basu zoba tofa shida kansa yake aikawa a k'irasu suzo su zauna tare dashi suyi hira Hakan ba k'aramin Dad'i yake jiba .to yauma hakane sun dad'e suna hira kafin suyi masa sallama su tafi ganin lokacin baccinsu yayi. Mai martaba ya bisu da kallo Yana Jin k'aunar yaran nasa na mamaye masa zuciya har suka fita daga falon gabad'aya...


Bayan tafiyarsu Babu dad'ewa Ammie ta shigo falon bakinta d'auke da sallama Mai martaba ya d'ago yana ansa mata ,har Ammie ta k'araso falon hannunta d'auke da tray Wanda ta kawowa Mai martaba fruit da green tea ta durk'usa har gabansa ta ajiye masa tana murmushi tace.


"Barka da dare rankai Dad'e". Ta fad'a tana ajiye kayan hannunta.mai martaba yay murmushi Yana yiwa Ammei Wani Irin kallo Wanda su kad'ai sukasan Ma'anarsa yace.


"barka dai Fulani,sannu da k'ok'ari Allah yayi albarka".ya fad'a Yana murmushi Shima.


Ammei tai murmushi tace.


"Ameen thumma Ameen rankai Dad'e" nan ta tsiya ya masa a cup sannan ta mik'a masa cikin girmamawa bayan ta had'a masa Irin had'in da yake so mai marataba yasa Hannu ya karb'a bayan ya Zauna dai dai Yana yiwa Ammei godiya Ammie tai murmushi ta zauna nan kusa dashi Yana Sha suna hira Irin nasu na manya .......






07066508376________
'þFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD





*<Ø9ß HUYAAM <Ø9ß*




*Paid book =ØÖÜ*


*Free pages*



*NA*



*____(MRS SARAKIES =Ø‹Ü)=Ø1Ý____*




*Bismillahirrahmanirrahim*



PAGE 7þã


____________¡&


Haka Huyaam sukai weekend d'insu Wanda gabad'ayansa a karatun exam ya k'are Dan Karatu suke kamar Babu gobe.


Yau Sunday gobe Kuma Monday ya kasance gobe suna da exam ,Dan haka wunin yau karatu suka Sha Yi ita da Huda suna cikin study room d'insu Dake nan kusa da d'akinsu.



Bayan Azhar HUYAAM ta sauko downstairs wajen k'arfe 2 : 30pm na rana lokacin sunyi sallahn Azhar ta fito zataci abinci dan wata Irin Yunwa takeji ,Dan rabonta da abinci tun na safe shima ba Wani na kirki taciba tun safe da suka fara karatu ita da huda Bata tsaya ba sai yanzu datai sallah Shine ta sauko k'asa zata Nemi abinda zataci.ta k'arasa har dining bayan ta a zauna ta bubbud'e warmers d'in ta d'ibi abinda zata iya ci ,bayan ta gama ta fito falo a dai dai lokacin da ya Haidar shima yake saukowa k'asa zuwa downstairs zai fita Huyaam ta k'araso wajensa da sauri ta Taya a gabansa tana murmushi kafin tace.


"Ya haidar albishirinka" ta fad'a tana kallansa har lokacin murmushi ne shimfid'e a saman kyakkyawar fuskarta.
Ya tsaya yana kallanta kafin yace. " goro" Huyaam tace .


Na kusan zama candidate na gama secondary school na shiga university kamar yadda ya Zarah takeyi" ta fad'a tana Wani fari da ido tare da murmushi.


Ya haidar ya gimtse dariyarsa Dan shi wallahi dariya ma ta bashi wai murna take Dan zata gama secondary school sai Kuma yace a fili.


"Hmm yarinyar nan bakida hankali naga alama,yanzu ke Dan ZAKI gama secondary school shine kike wannan murnar". Huyaam ta tura Baki gaba jin abinda ya fad'a ya cigaba Yace.


"to idan zaki daina murna ma gara kindaina Dan a b'angaren boko dai babu abinda kikayi" daga haka rab'a ta gefenta ya fice daga falon gabad'aya.huyaam ta bishi da kallo jin abinda ya fad'a jiki a Sanyaye ta haura sama zuwa d'akinsu Dan ta D'an kwanta ta huta kafin bayan ASR Kuma ta cigaba da karatunta.


Har bayan sallahn isha'i su Huyaam suna studying room d'insu suna karatu sallah ce Kawai da a Abinci yake ta-da su .

Yanzu ma Hakan ce ta kasance bayan sunyi dinner suka koma d'akinsu .Mai martaba Kuma Yana zauna a falonsa da Ammie da Kuma ya zarah wacce tazo gaidashi,mai martaba ya kalli ya Zarah yace.


"Zarah Ina su mamana suke ne?....." haka yake fad'awa su Huyaam Wani lokacin.


Ya zarah ta d'ago ta Kalli Mai martaba kafin tace da ladabi.

"suna can d'aki suna karatu gobe Monday suna da exam" kafin ta rufe Baki su Huyaam suka shigo falon bakinsu d'auke da sallama.su Ammie suka ansa Musu ,har suka k'araso falon suka zauna nan saman carpet d'in suna gaida Ammie Kafin nan suka juya suna gaida mai marataba .

Mai martaba ya ansa musu Yana kallansu yace.

"Ya Karatun?...suka ansa da Alhamdulillah ,Mai martaba ya Jin Jina kai Kafin yace. "Allah ya Bada sa'a". suka ansa da Ameen .sun D'an Dad'e a falon suna hira har ya haidar ma ya shigo kafin daga k'arshe suyi musu sallama suka fito daga falon gabad'ayansu kowa ya nufi d'akunansu Dan kwanciya.


Suna fita Mai martaba ya dubi Ammie yace .

"Fulani! nace ba kunya waya da Afeef kuwa?..." Ya fad'a Yana kallan Ammie.


Ammie ta sauke numfashi kafin tace.

"Munyi waya d'azu rankai Dad'e ya k'irani yace min nan da two weeks zai dawo".


Mai martaba ya jin jina kai yace.


"Eh Nima haka yake fad'amin yace zaizo break koma two weeks ne to 3 ?..." Ammie tace.


"Eh Allah ya kawo shi lafiya" Mai martaba ya ansa da ameen daga haka suka cigaba da hira kafin daga bisani Kuma su tashi Suma wuce d'aki Dan su kwanta Dan dare ya riga da yayi.


Washe gari da safe ya kasance Ranar Monday ,wacce ko baturema Yana tsoron Monday.


Huyaam ce tsaye a gaban mirrorn Dake d'akinsu wajen k'arfe 8 Saura na safe tana sanye da uniform d'inta na school tana graya zaman hijab d'in jikinta sai Wani murmushi takeyi ita kad'ai.Huda ce tashigo d'akin itama cikin shigar uniform Irin na Huyaam Sak zata dauki Wani text book d'inta data ajiye jiya a d'akin shine ta shigo zata d'auka ta tsaya kawai tana kallan Huyaam da mamakin Ganin yadda take wani murmushi ita kad'ai a d'aki.had'a idon da sukai da Huda ta cikin mirrorn Hakan yasa Huyaam ta juyo tana fuskantar Huda tai mata fari da ido tace.


"Wannan kallan fa?..."


Huda ta sauke numfashi tace .


"Dole na kalleki ke kad'ai a d'aki ki tsaya gaban mirror kiyi ta murmushi ke kad'ai". ta fad'a tana kallan Huyaam wacce ta k'ara fad'ad'a murmushinta .


Huyaam ta k'ara mata fari da ido kafin tace.


"Dole ki ganni cikin farin ciki mana Huda nida zan zama graduate na shiga university kamar yadda ya Zarah takeyi yarinya".
Ta fad'a tana Wani bouncing. dariya ce ta kama Huda Jin abinda Huyaam ta fad'a Amma sai batai ba tace .


"Uhmm!! nidai Dan Allah yanzu ki taso muje kiyi breakfast ke kad'ai ce bakiyi ba tun d'azu ake jiranki time na tafiya kinsan fa 10 zamu shiga exam" tana fad'ar haka ta k'arasa gefen kan side drawer inda ta ajiye book D'in nata ta tafi zata d'auka.Huyaam ta bar gaban mirror tace .


"Muje ai nagama Nima" ta fad'a tana d'aukar school bag d'inta.suna fita falor babu kowa a falon Dan kowa ya tafi inda zashi su su muneefa sun tafi school tun 7:30am ya Zarah Kuma tana d'aki sai anjima zata tafi school d'in itama .


HUYAAM ta k'arasa dining ta fara breakfast d'in,ita kuma Huda ta shiga kitchen d'auko musu ruwa....bayan HUYAAM ta gama breakfast ta mik'e ta fito daga dining d'in zuwa nan cikin falon adai dai lokacin da Ammie ta sauko k'asa zuwa falon tana kallan Huyaam tace.


"Kinci abincin ne?.." Ta fad'a tana kallanta .

HUYAAM ta shafa cikinta tana k'ok'arin d'aukar school bag d'inta tace .


"eh naci Ammie yanzu ma zamu tafi". ta fad'a tana rataya jakar.

Ammie ta jin jina kai tana kallansu ganin sun gama shirin Suma tafiya zasuyi.HUYAAM ta k'araso har gaban Ammie tai mata side huge tace.


"Mun tafi Ammie" ta fad'a tana murmushi.Ammei ta shafa kanta ganin haka yasa itama Huda ta k'araso ta rungume Ammie ta D'aya side d'in nan ma Ammie Shafa kanta itama kafin tace.


"Allah ya kiyaye ya Bada sa'ar exam daughters"ta fad'a tana murmushi.duk suka ansa da Ameen daga haka Ammie ta sakesu suka fito daga falon ganin lokaci na tafiya.


Tun kafin su fito tuni Aziza da su ikleema sun fito suna zaune a cikin motar suna jiransu,tun daga nesa da Aziza ta hango su ta d'auke kanta tana kallan gefe har suka k'araso suka shiga cikin motar ko zama basuyi ba Aziza taja Wani uban tsaki Kafin tace.


"Aikin banza aikin wofi sai yanzu Kuka ga damar fitowa tun d'azu mu muna nan muna zaman jiranku Kun kama kun Bat'a mana time akan aikin banza,to wallahi daga Yanzu idan kuka K'ara yin let wallahi tafiya zamuyi mu barku saidai kusan ya zakuyi aimu ba bayinku bane bare mu jiraku"ta fad'a tana hararar HUYAAM.adai dai lokacin da aka rufe k'ofar motar dogarin Dake Rakasu school ne ya rufe murfin Motar sannan ya Bud'e front seat ya shiga.driver Kuma ya ta-da motar.


Huda ta Kalli Aziza fuska d'aure itama tace.

"Dan Allah Aziza karki fasa kisa d'in a tafi a barmun sai me idan har kinga zaki iya sawar tunda ke Neman masifa baya miki kad'an".Huda ta fad'a tana hucii ikleema ce tasa musu Baki tace.


"Dan Allah kuyi hak'uri ya isa haka" , sai kuma ta Kalli Aziza tace. "kema Aziza ba'a haka Bai kamata ki fad'a musu haka ba kema yaushe kika daina yin let d'in da har zakiyi wasu cewa sunyi letting ko kin manta time d'in da muke zaman jiranki kafin ki fito mu a time d'in sai muce me? kika San Mai yasa yau d'in Basu fito da wuri ba" ta fad'a cikin ruwan sanyi...


Aziza ta juya ta harari ikleema kafin tace.


"Eh dole kiyi magana tunda na tab'o iyayanki, To bari Kiji in fad'a miki karki K'ara samun Baki idan Ina magana da su Bada ke nake ba"ta fad'a tana juya ido.


A dai dai lokacin da suka fice daga cikin palace d'in gabad'aya za'a kaisu school d'in.


Ikleema ta tab'e Baki tace.

"A'a!! ni baza kiyi Dani ba sai dai ki nemi abokin Yi" tana fad'ar haka ta juyar da kanta gefe.ita dai HUYAAM dama Batai magana ba ita da safnah Dan ko kad'an Huyaam Batasan hayaniya.bugu da Karima taiwa Aziza uzuri tunda ta riga tasan halim Aziza tunda ba k'aunarta take ba.


Wani malolon bakin cikine ya tsayawa Aziza A wuya tai ta masifa ganin Huyaam Bata kula taba Dan ta tsani Irin wannan halin na Huyaam na tai banza da mutum , sannan ta bawa banza ajiyar sa Aziza tafiso ace Huyaam ta tankata ita Kuma tai mata tass sai Kuma taga ko ta d'ago kai ta kalleta Huyaam batai ba bare ta Maida ta mutum,nan Aziza ta cigaba da fad'ar magan Ganu duk dan Wani ya tankata Acikinsu sai dai hak'arta Bata cimma ruwa ba Dan dukkansu babu Wanda ya kulata saima hira da suka kama yi duka ukun Amma Banda HUYAAM wacce take kallon hanya .Babu dad'ewa suka k'araso school d'in wacce take ta 'ya'yan manya Dan daga 'yay'an gomna saina sarakai irinsu Huyaam sai kuma Wanda yake da kud'i Mai suna kud'i ne kawai zai iya sa 'ya'yansa a school d'in saboda tsadarta,ga kyau da Kuma tsari uwa uba Kuma ga karatun da ake koyar musu acikinta Dan school d'in Babu k'arya tayi sosai ta ko Ina. bayan sun shiga ciki driver yay parking anan inda akeyin parking. Dogarin nan Dake gaban motar yay saurin Bud'e inda yake Zaune ya fito ya Bud'e musu k'ofar duk suka fito D'aya bayan D'aya Aziza ce ta karshe wacce ta cika tai fam k'iris ya rage ta fashe saboda haushi.



Suna gama fitowa Kowa ya nufi hole d'in exam d'insu, HUYAAM da Huda da safna a hole D'aya sukeyi sai Aziza da ikleema da sukeyi a hole D'aya Suma driver ya juya suka koma palace d'in idan sun tashi kuma su zo su d'aukosu.



____________¡&


Har ya Zarah ta dawo daga lecture su HUYAAM Basu dawo daga school ba saboda paper biyu sukai yau hadda practical sukayi basu suka tashi ba sai k'arfe biyar da Rabi na yamma suka taso ,duk agajiye suka dawo gidan da sallama suka shigo falon nasu babu kowa a falon sai k'arar AC direct sama suka haura zuwa d'akinsu nan suka tura k'ofar suka shiga suka tadda ya Zarah tana zaune gefen gadonsu tana waya sai Wani murmushi take.

HUYAAM ta Bude ido ta juya suka had'a ido da Huda ganinsu yasa ya Zarah ta fita daga d'akin nasu bayan ta kullo k'ofar ta koma nata d'akin .ganin ya Zarah ta fita daga d'akin yasa huyaam tai k'asa da murya tana kallan Huda tace.


"Ko waye yayan namu ne?..."ta fad'a tana gimtse dariyar ta.huda ta juya tana kallon k'ofar Ganin ya Zarah ta fita kafin ta juyo ta k'araso kusa da Huyaam Tai mata rad'a a kunne tana dariya .take itama HUYAAM tasa dariyar tana rufe Baki tace.


"Dan Allah fa Huda?..."Huda tai murmushi tace. "Babu ruwana wallahi idan taji, Kinga nidai ban fad'a miki ba Dan ki fad'a mata danni ma ban tabbatar ba".


HUYAAM ta rik'e baki tace.

"Yo nima hau ne akaina da zan fad'a mata salon ta dokeni"

Huda tace.

"To dai gara kiyi shirun". daga haka ta ajiye Jakarta ta fito daga d'akin HUYAAM Kuma ta fara rage kayan jikinta zata shiga toilet Dan yin Wanka.



Bayan magrib gabad'ayansu suna zaune a main falorn gidan kan babban carpet d'in Dake shimfid'e anan tsakiyar falon suna karatun Al'qur'ani Dan dama haka suke duk ranar da suke da paper wacce zata kaisu har k'arfe biyar zuwa biyar da Rabi na yamma Basu Samu damar zuwa ismaliya ba to to da daddare sai sun biya wannan Karatun Daya wuce su yadda idan sunje islamiya saidai kawai su Bada hadda kawai ,wannan tarbiyar Ammie ce.yanzu haka suna cikin karatun aka fara K'iran sallahn isha'i Hakan yasa zasu tak'aita saboda K'iran sallahn da ake Saida suka kai aya sannan suka tsaya saukai addu'o'i sannan suka mik'e zasu kabbara sallah ganin ana k'ok'arin shiga sallahn a masallacin palace d'in.


Suna idarwa suka shige D'aki Dan cire hijab d'in jikinsu sannan Kuma saisu fito suyi dinner.....






07066508376_______
'þFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD




*<Ø9ßHUYAAM <Ø9ß*




*paid book =ØÖÜ*

*Free pages*



*NA*



*___(MRS SARAKIES =Ø‹Ü)=Ø1Ý___*



*Bismillahirrahmanirrahim*



PAGE 8þã



____________¡&


Washe gari HUYAAM basuda paper Dan haka basuje school ba itakan batama tashi daga bacci ba sai after 10:00am sannan ta fito daga d'aki bayan tayi wanka ta sauya kaya daga na bacci zuwa na gida ta fito daga d'akinta zuwa k'asa Dan yau a d'akin da yake mazaunin nata ta Kwana ba'a na Huda ba Wanda suke kwana da Huda tare,a k'a'ida d'akin kowa daban agidan to sune dai har yau Basu Raba wajen kwana ba ita da huda kodan sun taso tare ne oho. bayan ta sauko downstairs ta k'araso dining ta zauna Bataga kowa a falon ba harta ta fara breakfast da kusan mintuna nan ma dai Bataga kowa ba ya sauko k'asa ba. Dan bayan da tai sallahn ASuba taje ta gaida Ammie Mai martaba ba kuma a time d'in Bai dawo daga masallaci ba Kuma tasan dai yanzu baya nan tunda 10 ta wuce.babu dad'ewa ta gama cin abincin Wanda duk caccakala ma tai dam ba Wani na kirki taci ba ta goge bakinta da tissue .ta fito falor kenan zata hau stairs ta koma dak'i aka Bud'e k'ofar falon ta juya tana kallon Wanda ya shigo ta D'an Bud'e ido kad'an tana kallansa da mamaki har ya k'arasa shigowa cikin falon ta Bud'e Bakinta kad'an tace.


"sannu da zuwa ya lamid'o". ta fad'a tana kallansa . lamid'o yay mata murmushi ya zauna kan D'aya daga cikin kujerun falon idonsa Yana kan Huyaam har lokacin yace .


"Lafiya lau HUYAAM kintashi lafiya?....ya fad'a Yana Wani k'ure ta da ido .ta d'auke kanta tace .


"Lafiya a Sanyaye" Dan ita har ga Allah Bata son kallo ko kad'an ko akan 'yan uwanta mata ne bare Kuma akan namiji.tana wannan tunanin taji yace.

"Ina Ammien mu take?..."ya fad'a Yana k'arewa falon kallo.


Batare da Huyaam ta k'ara kallansa ba tace.


"tana d'aki bari na K'irata". Bata jira cewar Saba ta haura sama da sauri lamid'o ya bita da kallo kafin ya sauke numfashi ya zaro wayarsa Daya gaban rigarsa Yana dubawa.


Ba'a d'au lokaci ba Ammie ta sauko falon ita kad'ai ba tare da Huyaam ba Dan itakan Bata dawo ba d'aki ta wuce zatai karatu kafin anjima k'arfe uku na yamman su tafi islamiya.


Da fara'a Ammie ta sauko downstairs bayan tayi sallama tana kallan lamid'o Wanda ya d'ago shima Yana kallanta da murmushi a fuskarsa ya ansa mata sallamarta..


Har k'asa lamid'o ya gaida Ammie bayan ya zamo daga saman kujerar.Ammie tai murmushi tace.


"Lafiya lau Alhamdulillah lamid'o andawo lafiya?..."ta fad'a tana murmushi har lokacin.


Lamid'o ya sunkuyar da kansa k'asa yace.


"lafiya lau Alhamdulillah Ammie". Ammie tai murmushi tace.


"Ya Lagos d'in?...'lamido yace.


"Alhamdulillah Ammie".Ammie ta jin jina kai tace .


"Masha Allah, Allah ya taimaka yasa albarka".

Lamid'o Yana murmushi yace.

"Ameen thumma Ameen Ammie nagode sosai". baba magajiya hadimar Ammie ce ta kawowa lamid'o ruwa da drink's sai fruits ta ajiye a table d'in Dake gabansa tana murmushi ta gaida lamid'o.

Lamid'o ya ansa mata Yana kallanta.

Sai Kuma ta mik'e tana kallan Ammie tace cikin girmamawa.


"Niko ranki Dad'e Huyaam ta tashi daga baccin taci abincin kuwa?Sau uku Ina zuwa Ina dubata naga ko ta tashi Amma sai naga Bata tashi ba".ta fad'a tana murmushi.


Ammie ta kalleta kafin tace .

"Eh ta tashi harma taci abincin ita ta K'irani ma tace min lamid'o yazo". Baba magajiya tai murmushi tace.


"Auto shikenan ranki Dad'e dama na d'auka bata tashin bane shiyasa nake tambaya Amma tunda ta tashin ai shikenan,Allah ya K'ara lafiya da Nisan kwana ranki Dad'e". Ta fad'a tana murmushi.


Ammie ta ansa da Ameen daga haka Baba magajiya ta koma kitchen,Ammie Kuma ta Maida hankalinta kan lamid'o suka cigaba da hira sun jima suna hira a falon har su ya Zarah suka fito suka gaida shi Amma Banda HUYAAM dam tunda ta shiga d'aki bata k'ara yarda ta fito ba ,can lamid'o yayi wa Ammie sallama ya tafi Dan dama haka lamid'o yakeyi yakan shigowa for time to Time ya gaida Ammie indai Yana masarautar to yanzu ne Kuma da yake a Lagos saidai yazo musu break haka ya koma.



K'arfe uku na yamman Ranar saura su Huyaam sukai shirin tafiya islamiya ko Wacce tai shiri cikin dogon hijab na islamiya.suka fito daga part d'in nasu har Inda motar da ake kai school ke jiransu bayan sunyiwa Ammie sallama Dan gabad'ayansu ne suka tafi harda ya Zarah tunda su su Huyaam yau basu da paper.



__________¡&


*Ingiland =ØéÞþ*


*Metallic industrial limited and car resources*



Company ne Wanda ya ansa sunansa company a wannan k'asa.Wanda,ake sarrafa k'arafa da Kuma k'era motoci acikinsa .wannan company ma mallakin bak'ar fatane a nan k'asar mu ta gado wato Nigeria.


Companyn babban company ne iya hasashen Mai karatu Dan fad'ar na zayyane muku ma b'ata lokacine saboda girmansa da Kuma had'uwarsa kawai abinda Zance shine ku k'iyasta a ranku.


A cikin wani babban office Wanda ya gaji da tsaruwa Had'i da had'uwa Wanda bana kowa bane saina na head of companyn . acikin office d'in na hango Wani matashin saurayi zauna kan kujerar Dake gaban Wani had'add'en table wasu turawa kuma suna zaune kan visitors chair d'in Dake gaban table d'in inda matashin nan ke zauna . Da dukan alamu magana suke Mai matuk'ar muhimmanci koma nace business ne ya kawo su, tunda naga ya Basu All ears d'insa Yana sauraransu Saida Wanda yake maganar ya kai point sannan matashin nan ya sauke ajiyar zuciya kafin ya zuba hannuwansa kan table d'in Yana kallansu ya motsa lips d'insa kad'an yace cikin husky voice d'insa.


"Alright, don't worry mr.but are you with your own choice or something like u wanted" ya fad'a Yana kallansu.


D'ayan yay saurin cewa.

"No! No!! No!!! we didn't have it, but if you have yours u would find it to us Mr Afeef"ya fad'a Yana murmushi.


Afeef ya Jin Jina kai Kafin yace cikin deep voice d'insa.

"ok I understand.so we have a new design that would find it this year can I show it to you ,then may be you would find yours here".ya fad'a Yana kallansu suka Jin jina masa kai alamar yes yace.

"Ok" Yana fad'ar haka ya Bud'e wata locker Dake nan gaban table d'in nasa ya d'auko musu album d'in da aka zana new design car da za'a k'era su this new year a fitar da su .


Ya Mik'a musu suka Karb'a nan suka zab'i wata latest car wacce itace the best car da za'a fitar da ita this year a wannan company Amma fa sai uban kud'i bayan sunyi pointing out wadda suke so d'in suka nunawa Afeef. Afeef ya karb'a bayan ya Gani yace.

"Ok don't worry we would do it in Sha Allah"nan da nai sukai appreciating sukai ta godiya kamar Wanda za'a Basu kyauta kafin su karb'i account number na companing take a wajen sukai payment sannan saukai masa sallama suka tafi.Daga nan Afeef ya cigaba da karb'ar Baki har k'arfe biyar da Rabi tai time d'in tashinsa daga company yayi kenan.nan ya d'auki brief case d'insa ya fito nan harabar office d'in nasu ya Tarar Drivernsa da yake Zaune Yana jiransa tuni ya taso da sauri ganin uban gidan nasa ya a fito nan ya karb'i brief case d'in Hannunsa ya wuce zuwa wajen motar Afeef na biye dashi a Baya duk inda ya gifta ma'aikata wajen ne kawai suke gaida shi dayake gabad'ayansu turawa ne su suke aikin k'era motocin bak'ak'en fatar Basu da yawa haka sukai ta gaida shi shi Kuma Yana ansa musu har ya k'araso motar ya shiga bayan already driver ya Bud'e masa back seat drivern Kuma ya zaga driver seat ya shiga suka fita daga cikin company gabad'aya direct gidansu suka wuce g Dake Nan ingiland d'in.



Da Daddare wajen k'arfe 8 da Rabi na daren Ranar bayan Afeef yayi wanka yasauya kaya ya fito daga falon gidan gabad'aya zuwa compound d'in gidan Dan fita zaiyi zaije Mall ne ya rage siyayyan da zaiyi idan zai koma gida Dan haka yake indai zashi gida tofa ba haka yake zuwa ba dole sai yayiwa kowa siyayya ya kai musu,Dan baya zuwa haka,yanzu ma Dan Dan zaiyi tafiya me zuwa k'asar china akwai kayan aikin motocin da zai Gani a can yayi order su akawo kafin ya tafi to shiyasa yakeso ya rage siyayyan Dan Bai San for how long tafiyar zata d'auke shi Bai dawo ba...haka ya fito xuwa compound d'in gidan sanye yake cikin k'ananun kayan da sukai masa bala'in kyau kansa Daya sha gyara sai Wani shining yake kamar ba dare ba Dan Afeef kyakkyawan ne na ajin k'arshe dogone Shi, sannan shi ba fari ba kuma Shiba Bak'i ba haka yake tsaka tsakiya ne gashi da manyan idananuwa da dogon hanshi dai dai da fuskarsa sai Wani baza k'amshi yake har ya k'araso compound d'in gidan dama already driver ya fito da motar da zasu fita acikinta Dan tun suna hanyar dawowa gida d'azu daga company Afeef yake fad'a masa cewa zasu fita.shiyasa baiyi nisa ba ya Tsaya yana jiran uban gidan nasa har ya k'arasa gaban motar ma'aikatan gidan sai gaidashi suke cikin girmamawa Yana ansa musu .Nan yashiga back seat bayan driver ya Bud'e masa ya shiga already Mai gadi ya danna Wani D'an Abu take Gate

Please Login or Register in order to submit comment