Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wuni". Ya juya ya kalleta ya ansa mata da kulawa har lokacin idonsa yana Kanta yace. "Ashe Kuma anyi waya shine ko fad'amin?...." Huyaam ta sauke idonta batai magana ba sai Huda ce tana Murmushi tace. "To muma mun Dad'e bamu gankaba ai shiyasa bamu nuna Maka ba". Ya shafa kansa Yace. "Eh wallahi two days bana zama idan na fita tun safe sai bayan 8 nake dawowa". Huda tace. "Ayya". Ta mik'a masa wayar Hannunta tace. "To gatawa ka Gani " yasa hannu ya karb'a Yana juya wayar a hannunsa yace. "Wow Masha Allah! lallai yarima Yana ji daku irin haka wannan latest phone". Huda tai murmushi Amma batai Magana ba ya d'ago ya Kalleta yace. "To abani contact ko ba'a badawa?..." Huda tace. "Mai zai Hana kuwa ya Aziz bari na Karanto Maka". Yana murmushi ya Mik'a mata wayarsa yace ungo kisamin taki". karb'ar wayar tasa Huda tai.itako Huyaam na jin haka ta Mik'e ta Kara wayar ta a kunnenta kamar wacce zatai answering call sannan ta haye sama da sauri.Aziz ya bita da kallon gefen ido. ita ko Huda hankalinta gabad'aya na kan wayar AZIZ da take sa masa contract d'inta.mik'a masa wayar tayi bayan ta gama tace. "Gashi ya chiroma". kallanta yayi yace. "Kinyi serving tace. "Nayi, da suna na nai serving". Yace "okay Samun ta Huyaam". Huda ta Kalli inda Huyaam ta zauna ganin wayan Bata nan yasa ta Kalli Aziz chiroma tace. "Yaushe ta tashi kuwa?. Aziz yayi murmushi yace. "Now ,Not long ago may be ko ansa waya zatai". Huda tai shiru sai Kuma tace. "To bari nasa Maka natan". nan tasa masa contract d'in Huyaam sannan ta mik'a masa wayar, karb'a yayi zaiyi serving adai dai lokacin da Ammie ta sauko falon Aziz ya tsugunna har k'asa ya Gaida ta. ansa masa Ammie tai da kulawa sannan tace. " Yaushe Kashigo kwa Aziz?..". Aziz na shafa kansa yana murmushi yace. "Not long ago Ammie". Ammie tai murmushi sannan ta tambaye shi aiki yace mata Alhamdulillah nan Ammie tace. "Allah ya taimaka" yace. "Ameen" Yana mik'ewa sannan yaywa Ammie sallama. Ammie tace. "Tafiya Kuma zakai Aziz?..." Aziz Chiroma na murmushi ya ansa mata da eh sannan ya fita daga falon gabad'aya......


K'arfe 12:30am na dare shakundum ce tsaye a cikin toilet d'in d'akinta waya ce kare a kunnenta.magana take k'asa k'asa wadda koda kana kusa da ita idan ba Mai k'arfin jiba bazaka tab'a sanin Mai take cewa ba.tace Cikin k'asa da murya "barzuk Ina cikin tashin hankali na rasa ta Ina zan fara? wannan kakartasu ta dawo part d'in da zama gabad'aya bansani ba ko ta fara fahimtara Wani abunne?..." Ta Fad'a cikin tashin hankali. Daga can b'angaren Barzuk yace da wata iriyar murya marar dad'in saurare "ita tsohuwar ce Mai wannan aikin". Cikin tashin hankali shakundum tace. "Itace mana barzuk! Ga tsabar masifa sai ta kai har kusan k'arfe d'ayan dare tana falon Bata shiga d'aki ta kwanta da wuri bare na samu na aiwatar da aikin nawa ba". Ta fad'a cikin damuwa.barzuk yay Wani wata mahaukaciyar dariya kafin ya tsagaita yace da bu d'add'iyar muryarsa. "Ai wannan tsohuwar da kike ganinta NEMA take Taga ta karya mana aikinmu". cikin damuwa shakundum tace. "Kamar Yaya barzuk'! na shiga uku Dan Allah kada ai mun haka kada ka Bata dama barzuk". Ta fad'a tana share zufar data karyo mata lokaci D'aya. Barzuk ya K'ara shekewa da wata uwar Dariya kafin ya tsagaita yace. "To idan ba kyason haka gara ki zama jaruma kema ki Hana idonki bacci kibi duk wata hanyar daya kamata kibi wajen aiwatar da aikin naki batare da kin Bat'a aikin ba,ko Kuma kina an kamaki ba". Shakundum tace. "Barzuk duk Wani Abu da kace nayi nayi na bunne komai a B'angarena yanzu haka b'angaren Ayshan ne kawai banjeba kullum idan zanje sai na ga bayin b'angaren nata suna nan basa tab'a, matsawa ko kad'an Amma kuma barzuk nasan yadda Zanyi dasu akwai mafita ta yadda babu Wanda zai tab'a ganina bare Kuma har a zargeni kamar yadda nai a waccen Karan ma". Ta fad'a cikin k'warin gwiwar Daya shigeta lokaci D'aya.barzuk yace. "Ko kefa haka ya kamata kiyi,Dan Inaso ne kina gamawa idan kika dawo a sannan ne mu Kuma zamu cika miki aikin". Shakundum tace. "Godiya nake uban gidan su faisak". barzuk yace. "Angaisheki baragurbin masarautar zazzau" tai murmushi tace. "Sai munyi waya saurin katse wayar tai Jin kamar motsi daga cikin d'akin duk da tasan ta kulle k'ofar kafin ta shigo nan ta damk'e wayar a hannunta k'irjin ta na bugawa da sauri da sauri Sannan ta Murd'a key d'in k'ofar ta fito tana sauke numfashi kamar wacce tai gudun tsere tareda da kallon k'ofar Lokaci D'aya......



#<9HUYAAM<9
#<9LAMID'O
#<9AZIZ CHIROMA
#<9AFEEF



*mutanan MRS SARAKIES =؋ Kuna Ina ne? ana ta payments na book d'in Huyaam ku an barku a Baya to Maza ku garzayo yanzu kar wannan garab'asar ta wuce ku*.


*ga masu buk'atar fara payments zaku iya sa kud'inku a yanzu before mu gama free pages Regular group akan naira 500 kacal idan kuma muka gama Free pages zai koma 700 ne.ga masu buk'atar Vip Kuma 2 pages a Rana zaku iya biyan nai 1000 kacal. ku hanzarta ku fara biya tun kafin mu gama free pages.zaku iya tura kud'in ta wannan account d'in =G*


2270127432 Naja'atu umar
Zenith bank


'yan Niger kuma kumin magana ta phone number na chart only.=G

07066508376


Evidence of payment (shaidar biya )via
07066508376


*'Yan Niger <<_zaku iya biyan(500 CFR) a Yanzu before mu gama free page. idan muka gama Kuma zai koma(700 CFR) for VIP Kuma (1000 CFR)MY NITA (evidence of payment*)=G
07066508376


Da zarar mungama free pages Kuma zamu sa duk Wanda ya biya kud'in sa a paid group, karku bari ayi wannan tafiyar Babu ku =؃=؃ mutanan arziki.





07066508376________
'Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD



*<9HUYAAM<9*


*NA*


*__NAJA'ATU UMAR FAROOQ__*


*__(MRS SARAKIES =؋)__*



PAGE3 0


*TALLAH! TALLAH!! TALLAH!!!*


*Ina kuke manyan mata masu capacity ==؃=؃? Nace Ina kuke hajiyoyin gidan nan, to Maza ku Bud'e kunnuwanku ku saurarareni > da kyau.Dan a yau nazo muku da Wani kyakkyawan albishir=؃=؃ wanda zakuji dad'insa fiye da yadda zan fad'a muku.Nace ba, Bakuda Labarin hamshak'iya shahararriyar 'yar Kasuwar nan wacce tai K'aurin suna wajen kawo muku kayayyakinta na 'yan Gayu masu quality wato H.Empire < Lagos Mai gidan kayan sawa na mata na k'walisa da Kuma kayan kitchen?..."*

*To idan yau kuka tab'a ji ya kamata ace kun saurareni kunji da abinda nazo muku dashi. Kayan sawa kike so Wanda zaki zama tauraruwa a cikin 'Yan uwanki mata harma da Mai gida wato oga kwata kwata Hajiya ta , ko ko so kike duk inda kika gifta kallo ya koma kanki?. Ko Kuma kayan kitchen kikeso masu kyau da aminci daki bari. To Maza ku garzayo H.Empire < Lagos anan zaku samu duk Wani Irin Abu da kuke so, Dan mu kayan mu quaranti ne Hajiyata bakida tan tama akai, kudai ku gwada siya kawai zakusha mamaki Dan sai Kun bani labari. Muna Saida kaya kamar haka ka* =G

*1,Atamfofi*
*2, lesses*
*3, Abaya*
*4, kayan kwalliya ko Wani iri ne*
5,*D'an kunnaye(jiwelleries)*
*6,takalma*
*7,hand bag*
*8, mayafai*
*9, sai Kuma kayan kitchen shima Muna sai dawa, Dan duk Wani kayan kitchen d'in da kike nema harma da Wanda Baki tab'a Gani ba ko sani to idan kikazo H.Empire < Lagos anan zaki samu duk Wani Irin kayan kitchen muna Saidawa akan farashi Mai sauk'i da rahusa siyan D'aya ko sari*.

*domun magana damu kai tsaye ko Kuma Neman K'arin bayani ku tun tub'emu ta wad'an nan numbers d'in kai tsaye kamar haka =I+234 811 190 1302 /09020337676*


*Siyan na gari Mai da kud'i gida Hajiya ta*

*Sai mun Jiku=؃=؃*


<9<9<9<9<9<9


*Bismillahirrahmanirrahim*


____________&


Da k'yar shakundum ta iya d'aga k'afarta daga nan Bakin toilet d'in ta fara Takawa zuwa cikin d'akin nata a hankali fargaba da tsoron waye yake mata knocking a wannan tsohon daren kawai ke mata kai kawo a cikin zuciyarta .dai ta Dai daita kanta ta fara k'ok'arin Yi saboda yadda jikinta yake Wani Irin rawa kamar mazari jiki a Sanyaye da k'yar ta iya Bud'e Baki tace. "Waye?..." A tsorace. Safara ce Dake Bakin k'ofar tai saurin cewa k'asa k'asa . "Nice ranki Dad'e". Ta fad'a kamar wata munafuka .Take shakundum ta Sauke wata wawuyar ajiyar zuciyar salama Jin muryar safara Dan duk d'aukarta ko Mai martaba ne Dan tasan Babu Mai zuwa mata b'angaren a wannan dare in ba Shiba, Amma Kuma ko shi d'inma Bai tab'a zuwa mata b'angare a Irin wannan lokacin ba,kawai dai abunka da Marar gaskiya shiyasa ta firgita Lokaci D'aya.d'aga murya tai tace. "Meya faru zaki zomin b'angarena a Irin wannan lokacin?..." Ta fad'a a fusace.safara tace cikin ladabi. "Ranki Dad'e sak'on da kika ce na kawo Miki k'arfe D'aya na dare saboda kada kowa ya ganni shine na kawo mikin".ta fad'a tana jiran ansar shakundum.Ajiyar zuciya shakundum ta sauke Dan shaf ta manta da maganar da sukai da safara d'azu wajen k'arfe goma na dare akan zata kawo mata Sak'o.Batace komai ba illa Bud'e k'ofar da tai tana kalle kallen Dan kada Wani ya gansu kafin ta mik'awa safara hannunta akan ta Bata . cikin girmamawa safara ta fito da Hannunta Dake cikin k'aton hijab d'in data Saka ta fito da abun data kawo matan ta mik'a mata Wani Abu Wanda ni kaina bansan menene ba ke d'aure acikin Leda an nannad'e shi da kusan linki biyar na Leda wanda yasha Nad'i bana wasa ba.karb'a shakundum tai tai k'asa da murya tana kallan safara tace. "Kin tabbata Babu Wanda yaga fito warki?. Tafad'a da sigar gargad'i.Jin Jina mata kai safara tai kafin tace cikin k'asa da murya. "Eh! Babu kowa ranki Dad'e". Sha kundum ta Jin jina kai kafin tace. "Shikenan jeki".daga haka tai saurin kulle k'ofar ta koma ciki.barin bakin k'ofar safara tai tana kalle kalle itama ta bar b'angaren gabad'aya ta koma nasu...Koda wasa shakundum batai gigin Bud'e wannan abu da safara ta kawo mata ba, iyaka kawai tsayawa tai a tsakiyar d'akin ta zuba masa ido tana kallansa Bata ko kiftawa tana sakin murmushi lokacin D'aya ga Wani Irin farin ciki na shigarta tana ganin kamar tana gab da Samun nasarsa ta ne. jujjuya shi ta fara yi a hannunta kafin ta K'ara sakin Wani shu'umin murmushin tana Ganin burinta na gab da cika .Sauke numfashi tai tareda takawa a hankali ta k'arasa inda duk take aje kayan k'ulle k'ullenta irin wannan tai masa mazauni Mai kyau Wanda Babu Wanda ya isa ya Gano inda yake inba ita data ajiye ba.barin wurin tai ta Koma saman gadonta ta kwanta tana lumshe ido.koda ta kwanta d'in ba bawai baccin tai ba duniyar tunani kawai ta fad'a tana tsare tsaren yadda zata samu mafitar samun gudanar da aikinta yadda zai tafi successful batareda an samu wata matsala ba haka ta dinga sak'awa da kwancewa Wanda da k'yar bacci b'arawo ya iya saceta a wannan dare Dan zamu iya cewa ma sai kusan asuba ta samu baccin yay awan gaba da ita........


Washe gari wajen k'arfe goma da Rabi na safe.Anty Amina ce Zauna a d'akin gimbiya Aysha tana Bata tea. Bayan gimbiya Aysha ta gama sha ta fara goge mata bakinta da duk inda ta Bat'a da tissue sannan ta d'auko maganinta ta Bata Tasha.knocking k'ofar d'akin akayi Hakan yasa Anty Amina ta juya tana kallon k'ofar kafin tace.

"waye?.."


Muryar baba uwani taji tace itace Hakan yasa Anty Amina ta Bata iznin shigowa.turo k'ofar baba uwani tai tashigo d'akin hannunta rik'e da Wani kullin magani a farar leda ta k'arasa inda anty Amina take tana kallanta tai murmushi ganin yadda anty Amina ta zubawa hannun nata Ido.tun kafin Anty Amina tai magana baba uwani tace. "Ranki Dad'e Mai babban d'aki ce tace idan za'a yiwa fulani wanka mudinga d'iba kad'an kad'an muna zuba wannan maganin a cikin ruwan wankan". Ta fad'a tana kallan yanayin Anty Amina. "Anty Amina ta sauke numfashi kafin ta Kalli baba uwani tace. "to shi wannan d'in maganin meye?. Baba uwani tai murmushi tace. "Ranki Dad'e tace maganin karya sihine". Anty Amina ta tab'e Baki tace. "Nifa banasan Irin wannan magun gunan na gargajiya da inna take cewa ayiwa Yaya gimbiya amfani dashi Dan wallahi ba so nake ba,Dan Wani ma bakasan ayina aka samo Shiba,Mai kyau ne marar kyau ne sai Allah Amma inna ta dage tace wai dole sai anyi amfani dashi". Ta fad'a cikin damuwa.baba uwani murmushi kawai tai kafin tace. "To Ranki Dad'e kar ayi amfanin dashi kenan?..." Anty Amina tai saurin cewa a'a ai dole idan Ba'ayi bama idan tazo kinsan saita tace mun Raina mata k'ok'arinta da takeyi". Baba uwani tai murmushi tace. "gaskiya kan to bari na shiga na Had'a ruwan wankan". Anty Amina ta ansa mata da to...Babu Dede'wa baba uwani ta had'a ruwan wankan ta fito daga cikin toilet d'in tana kallan anty Amina tace. "Ranki Dad'e an had'a". Anty Amina tace.
"to shikenan k'araso mu kamatan". Ta fad'a tana mik'ewa baba uwani ta k'araso suka kama gimbiya Aysha da dabara da komai kamar yadda suka Saba suka shigarta toilet d'in...Bayan Wani lokaci suka fito da gimbiya Aysha suka zaunar ta nan Saman wata kujerarta Dake nan d'akin Wacce idan ta gaji da kwanciyar suke dawo da ita Kai ta huta.baba uwani tana kallan anty Amina tace. "Ranki Dad'e Adama mata kunun yanzu ko sai anjima". Anty Amina tace. "A'a ki bari zuwa anjima da Rana ko Kuma da yamma sai adama matan tunda Kinga yanzu ta gama cin abincin". Baba uwani tace. "To to Shikenan babu damuwa bari naje na k'arasa aikin da nakeyi"..anty Amina ta kalleta tace. "Allah ya saka Miki da Alkhairi baba muna godiya sosai da d'awai niyar da kike tayani Yi da Yayata Allah ya bar zumunci". Ta fad'a cikin Jin dad'in yadda baba uwani Bata Wani damuwa ko nunawa afuska alamar gajiyawar d'awainiyar da take da gimbiya Aysha.baba uwani da har ta juya ta juyo tana kallon anty Amina tai saurin cewa. "Haba haba ranki Dad'e yanzu duk abinda naiwa Fulani Aysha kina ganin na Fad'i ne? Ai ko kad'an ban biyata kan abubuwan datai min ba,idan ban tsaya kan duk Wani Abu da ya sameta na farin ciki ko na Bak'in ciki ba Mai Zanyi ni uwani?ashema na zama butulu indai ban tsaya tsayin daka na kula da ita halin da take ciki ba , saboda haka Dan Allah ranki Dad'e karki K'ara min godiya akan wannan D'an abinda nake Yi , wallahi Ranki Dad'e Ina Jin gimbiya Aysha ne araina kamar 'yar data fito daga cikina.damuwar ta damuwa tace ,Haka samun lafiyar ta Nima shine farin cikina a kullum muna addu'a da Allah ya tashi kafad'unta Allah ya Bata lafiya". Tafad'a cikin rauni.anty Amina ta sauke numfashi tace. "Shikenan baba mungode Allah ya bar zumunci". Baba uwani tace. "Ameen thumma Ameen bari naje" daga haka ta nufi k'ofar fita daga d'akin..Anty Amina Kuma ta d'auki lotion ta fara Shafawa gimbiya Aysha kafin ta gama ta shiryata cikin wata doguwar rigar tsaddan material d'inkin doguwar riga wanda dai bazai takura taba. bayan ta gama tai parking d'in doguwar kitson kalbar datai mata two days ago da rinbbom tana Kallon gimbiya Aysha tai k'asa da murya tace. "Na barki kan kujerar ko Kuma na kaiki saman gadon?..." Tafad'a tana kallanta Dan jiran ansarta. Gyad'a mata kai gimbiya Aysha tai kamar da wasa.take Anty Amina ta saki murmushi tace cikin Wani irin shaukin farin ciki Daya shigeta lokaci D'aya ganin yadda yau dai gimbiya Aysha ta gyad'a kai da kanta da da ko d'aga kan nata batayi Amma yau itace tai nudding kanta ai da Wani Irin farin tace. "Yaya gimbiya yanzu kece kika gyad'a mini Kai haka?.."ta fad'a har sannan murmushi ne a saman fuskarta.Lumshe idonta gimbiya Aysha tai,anty Amina ta d'aga hannunta sama tace.
cikin Wani irin farin ciki. "Alhamdulillah ya Allah! Allah mun gode Maka da wannan ni'ima da kafara mana ,ya Allah ka bawa wannan baiwa taka lafiya Mai d'orewa ta har abada gabad'aya da ita duk Wasu masu fama da jinya" sai Kuma ta Sauke hannunta k'asa nan ta fara gyara mata zamanta akan kujerar. Bud'e k'ofar d'akin akayi Hajiya inna ce ta shigo.Anty Amina ta juya tana kallon k'ofar Jin anbud'e taga Hajiya inna ce take ta saki murmushi tana kallanta .Hajiya inna ta ta rufo k'ofar tana kallan anty Amina tace. Haya niyar me nake ji Ina falo lafiya dai ko?.." Anty Amina na murmushi tace. "Wallahi inna yanzu Ina tambayar yay gimbiya akan na barta nan Saman kujera ko Kuma na kaita kan gado kawai naga ta gyad'a mini kanta abinda ban tab'a Gani ba ko tunani tunda ta fara jinyar nan.." Ta fad'a tana no kasa b'oye farin cikinta. Mamaki ya bayyana sa 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~man fuskar Hajiya inna itama Batasan lokacin data k'arasa shigowa cikin d'akin ba tana kallon Anty Amina tace. "Ke da Gaske Dan Allah Amina ko dai wasa kikeyi?.Anty Amina na murmushi tace. "Wallahi Hajiya". Hajiya Inna itama ta d'aga hannayenta sama tace cikin farin ciki. " Allah mun gode Maka,ya Allah yadda ka nuna mana wannan Rana ya Allah ka nuna mana ranar da Aysha zata samu Lafiya gabad'aya". Anty Amina na murmushi ta ansa mata da "Ameen ya Allah inna". Hajiya Inna ta shafa addu'ar ta Kalli gimbiya Aysha Dake Kallansu itama tace. "Aysha Allah ya cigaba da Baki lafiya Kinji?.." this time around lumshe idonta tai sai Kuma ta gyad'a musu kan ahankali". Inna tace. " Wallahi kuwa Nima na gani Allah mun gode maka". Sai Kuma ta kalli Anty Amina tace. "Ina fatan Babu Wanda kika fad'awa wannan maganar dai ko? Anty Amina da har lokacin murmushi ne with surprised a fuskarta ta gyad'a ma inna kai tace. "Babu Wanda na fad'awa inna". Hajiya inna tai k'asa da murya tace. ",to banaso kowa yaji wannan maganar dagani saike Amina Dan ko Mai martaba bazan fad'awa ba gudun sub'utar Baki wannan abun yazama sirrin da har sai munga komai Yana tafiya da cigaba sosai Dan bamu sani ba ko akwai Wad'anda suke da sa hannu a cikin jinyar Aysha suke mana zagon k'asa ba.idan suka ji Kuma Kinga ai sai su Bat'a Mana aiki" anty Amina na murmushi tace. "In Sha Allah inna babu Wanda zan fad'awa".Dan da harta yanke hukuncin zata k'ira can gidansu ta fad'a harma ta fad'awa gimbiya Bilkisu Amma yanzu ta fasa tunda Hajiya inna tace Kar a fad'awa kowa Dan ita Kanta batai wannan tunanin ba sai a yanzu da Hajiya inna tai maganar.maganar da Hajiya inna take yasa ta maida hankalinta Kanta. hajiya Inna tace. "D'azu uwani ta kawo maganin da nace idan zakuyi mata wanka kudinga sawa acikin ruwan kuna amfani dashi?. Anty Amina tace. "Eh ta kawo dashima muka mata wankan". Hajiya inna tace. "To shikenan Dan Allah ki cigaba da mata Wankan dashi harya k'are, sanna ki cigaba da Bata ruwan mananin Dan antabbatar min Mai kyau ne". Anty Amina tace. "In Sha Allah inna Allah ya Saka da Alkhairi"..inna tace. "Zamu koma Egypt d'in ma dai dole saboda lokacin komawar tamu ya kusa fa".anty Amina tace . "Eh hakane Allah ya kaimu". Hajiya inna tace. "Ameen" daga Haka tace. "bari zan dawo anjima ta Kalli gimbiya Aysha tace. "Allah ya K'ara lafiya Fulani".daga haka ta bar d'akin bayan anty Amina tai mata fatan sauka lafiya.....


___________&


Da yamma wajen k'arfe 5pm shakundum ce tai sallama anan k'ofar main falorn b'angaren gimbiya Aysha tareda rakiyar hadimanta harda amintacciyar hadimar ta wato safara .basu shigo falon ba suka tsaya daga nan Bakin k'ofar bisa ga umar nin uwar d'akin nasu.iya safara ce kawai ta tabiyo bayan shakundum danyin sallama a uwar d'akin nata ta k'arasa falon da sauri ta tsaya nan tsakiyar k'aton falon ta shiga yin sallama. shakundum ta Shiga falon cikin shiga ta Alfarma sai Wani walwali take da tashin k'amshi babu kuwa a falon sai K'arar AC data fan Dake Kad'awa a hankali.baba uwani ce ta fito Daga kitchen d'in downstairs jin yadda.hadimar shakundum ke k'wada sallama da cewa ga sarauniyar masarutar zazzzu ta k'araso.k'arasowa cikin falon baba uwani tai ta zube har k'asa nan ta hau gaishe da gimbiya Hajara cikin salon gaisuwa Irin ta gidan sarauta.da ka kawai Shakundum ta iya ansa mata tana Wani hararar ta kafin baba uwani tace. "bari aje ayi miki iso ranki Dad'e". Daga haka ta Mik'e ta haura sama zuwa b'angaren gimbiya Aysha.bayan tafiyar baba uwani Shakudum ta shiga k'arewa falon kallo tana nan tsaye sultan ya fito daga cikin d'akinsa yasha Wani rantsatstsan yadi na Maza Mai bala'in tsada fari K'al sai baza k'amshi yakeyi ga yayi Wani fresh dashi kallo D'aya yay mata ya d'auke kansa kamar zai juya ya koma Cikin d'akin nasa sai Kuma kawai ya fasa ya fara takowa zuwa cikin falon cikin nutsuwa a hankali dama kitchen zashi Haka ya k'araso ya wuce ta gaban shakundum da ko gaisheta baiyi ba Haka nan yashige kitchen d'in,ko minti D'aya baiyi da shiga ba ya fito dama cup ya shiga ya d'auka hayan ya d'auka ko ya fito nan ma ya K'ara wucewa ta gabanta ya koma d'akin nasa ya kulllo k'ofar da k'arfi.har Saida falon ya ansa . Mamaki ne kawai ya kashe shakundum anan inda take tsaye Tama rasa wani yanayi take ciki,mamakin yadda taga sultan lafiya lau kamar Babu abinda yake damunsa ko Kuma mamakin yadda ko gaisheta baiyi ba haka yazo ya wuce ta gabanta ya sake dawo wa ya wuce ta d'in? ita data d'auka yauma zata shigo ta ganshi Yana kulle a d'aki Yana hauka tuburan kamar yadda ya saba Amma shine yau ta shigo ta sameshi lafiya lau lallai ashe ko zama Bai kama taba me yake shirin faruwa ne? Lallai dole sultan ya koma yadda yake ada dole sultan ya koma haukansa da yakeyi ada .tsabar shock d'in da take ciki Batama san har baba uwani ta dawo tana mata magana ba".dai dai kanta kawai tai tana sauke ajiyar zuciya ahankali kafin ta Kalli baba uwani tace. "Yauwa na..nagode" ta fad'a Cikin inda inda abinka da Marar gaskiya" daga haka ta nufi stairs d'in da zai kai ta b'angaren gimbiya Aysha tana kalle kalle.da kallo kawai baba uwani ta bita ganin yadda shakundum take a figice bayan ta tafi ta barta lafiya lau. sauke numfashi tai ta wuce kitchen d'in Dan cigaba da aikin da takeyi.tunani da mamakin Maiya samu gimbiya Hajara fal ranta....


Anty Amina ce tsaye tana kallon shakundum Dake tsaye bakin k'ofar bayan ta Bud'e mata k'ofar.kafin ta Bata hanya akan ta wuce.shiga ciki shakundum tai tana k'arewa d'akin kallo kafin ta tsaida idanuwanta kan gimbiya Aysha sannan ta k'arasa cikin d'akin ta zauna nan saman kujera Dake d'akin tana murmushin da take Yi a kullum idan tazo duba gimbiya Aysha.Kallan Anty Amina tai Dake gaida ta .ansa mata tai tana tambayar ta Mai Jiki Anty Amina tace. "Da sauk'i" Sha kundum data Ari fuskar tausayi lokaci D'aya tace. "Allah ya K'ara mata lafiya yasa kaffarane". Anty Amina ta ansa da Ameen .Anam ce Dake Zaune kusa da gimbiya Aysha nan Saman Gadon ta gaida Shakundum.gimbiya Hajara ta ansa mata da kulawa tana tambayar ta school..nan Anam ta ansa mata tana d'auke kanta daga kallanta.bud'e k'ofar d'akin akayi bayan anyi sallama baba uwani ce ta kawo wa shakundum ruwa da drink's sai fruits a k'aton tray ta duk'a har k'asa ta ajiye mata anan gabanta cikin girmamawa sannan ta mik'e ta Bar d'akin.shakundum ta jima a d'akin kamar Wacce tazo dubiyar da Gaske.nan Kuma ba komai ne ya kawota taba iyaka kawai yadda zata aiwatar da aikin cikin sauk'i ne kawai take tunani bayan Wani lokaci ta mik'e taiwa gimbiya Aysha Allah ya sawak'e sannan taiwa anty Amina sallama ta bar d'akin gabad'aya..a falon downstairs ta Had'u da Hajiya inna ta fito daga cikin d'akinta shakundum ta duk'a har k'asa ta gaida ta .ita dai Hajiya inna kallanta Kawai takeyi kafin ta ansa mata tana kallanta da mamakin Maiya kawo ta.mik'ewa gimbiya

Please Login or Register in order to submit comment