Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da akai daga k'ofar falon ne yasa suka juya suna kallan Mai yin sallamar harta k'arasa shigowa falon.ansa mata sukai harta k'arasa ta Zauna kan kujera Huda na kallonta tace .

"sannu da zuwa ya Salima".Salima na murmushi ta ansa mata hakama Huyaam da muneefa duk suka gaida ta lokaci D'aya, nan ma ta ansa musu da kulawa sai kuma salima taiwa ya Zarah magana da cewa .

"Zarah Ina Ammie kuwa? Naga na shigo ban ganta ba". Ta fad'a tana Wani dube dube a falon kamar anan zata ga Ammien".
Ya zarah ta kallate a zuciyarta tace ji wata gulma Kuma?Koda zuwa take duba Ammien oho ,a fili kuma tace.

"Eh yanzu ta shiga ciki Amma nasan yanzu zata sauko".Salima ta Jin jina kai tace.

"Okay! Dama nazo gaida Ammien ne sannan kuma na gaida ya Afeef nai Masa barka da dawowa kinsan tunda yazo bamu had'u ba kuma Inaso ne mu had'u nai masa godiyar tsaraban da ya iyo Mana Allah dai yasa yau dai Yana nan Dan kullum idan nazo bana samunsa".ta fad'a tana Wani murmushi.ya Zarah tace.

"Okay! Ya dawo Yana b'angarensu".Salima tace.

"Indai zai Sakko Aiko zan jira shi yau dai mu gaisa".ya Zarah kan batai magana ba illa Wani kallo datai ma Salima . Ammie ce ta sauko falon tana cewa.

"Books d'in waye a k'asa tsakanin muneefa da muneeb?..." muneefa ta mik'e tana murmushi tace.

"Nawane Ammei homework nakeyi idan na gama zan kwashe". Ammie tace.

"Kin kyauta Kuma yin homework har Sai an watsar da littafai gobe Kuma idan Kun tashi tafiya school ki ishi mutane da cikiya ko? Muneefa tai shiru tana kallan Ammie.Ammie tace. "to kina gamawa Maza kije ki kwashe tun kafin na K'ara magana". muneefa tace. "To" tana komawa ta zauna.Ammie ta k'arasa shigowa cikin falon tun kafin ta zauna Salima ta zamo daga saman kujerar ta zugunna har k'asa ta gaida Ammie... Ammie ta ansa mata da kulawa tana cewa.

"A'a! Salima kece da daren nan?...." Salima na murmushi tace.

"Nice Ammie".


Ammie ta Jin jina kai tace. "Masha Allah ya karatun Kuma?...." Salima tace . "Alhamdulillah". Ta fad'a tana komawa kan kujerar ta zauna tana Wani sinne kai k'asa... Ammie tace. "Masha Allah! Allah ya taimaka". Salima na murmushi ta Ansa da Ameen.k'amshin turaran da sukaji Yana kusan toso Mai d'adin Gaske ne yasa duk suka juya suna Neman inda k'amshin ke fitowa .Afeef ne yake saukowa downstairs d'in sanye yake cikin k'ananun kaya Wanda sukai masa bala'in kyau sai baza k'amshi yake ta ko Ina tunda ya fara saukowa downstairs d'in Salima ta zuba masa ido tana kallansa Bata ko kiftawa ya Allah haka ta Ambata a ranta Dan Wani Irin kibiyar sanshi ne ya Kara chakarta a wannan lokacin.shiko Afeef Bai ma kula da ita ba Ammie kawai ya gani a falon sai 'yan uwansa Amma baiyi tunanin ma akwai wata Salima a wurin ba.dining zai nufa Hakan yasa Salima tai saurin cewa .

"Yaya sannu da zuwa Barka da dare". Ta fad'a tana Wani lank'washe murya tare da k'ura masa ido".ba su Huyaam ba hatta Ammie saida ta taji Wani banbara kwai Jin yadda Salima ta sauya murya Lokaci D'aya, Amma Basu yi magana ba, bama Wanda ya kawo komai a ransa illah d'auke kansu da sukai suka nuna bama susan Mai tayi ba.shima kansa Afeef d'in mamakine ya kama shi jin yadda aka lank'washe murya anai masa magana kamar bazai juyo ba sai kuma ya juya Yana kallan Mai maganar ganin Salima ce yasa ya d'auke kansa daga kallanta Yana ansa mata da "yauwa". Atak'aice. ganin zai juya ya cigaba da tafiyar sa yasa Salima tai saurin cewa. 'Munga Sak'o mun gode Allah ya K'ara Bud'i Yaya". ta fad'a cikin wani Irin salo.bai ansa ba iyaka kawai da ya cigaba da tafiyarsa harya k'arasa dining d'in yaja kujera ya zauna. Sharetan da Afeef yayi baisa Salima taji haushin Saba illa sansa ne ma da taji ya K'ara ruruwa a azuciyarta ta lumshe idonta ta Bud'e lokaci D'aya ta cigaba da kallonsa kamar ta samu TV juyawar da tai suka had'a ido da ya Zarah ne yasa ta d'an ji kunya kad'an sai Kuma ta mik'e cikin Jin kunya tace . "Bari na tafi Ammie sai anjima". Ammie ta juyo tana kallonta tace.

"Tafiya Zakiyi Salima?..." Salima na murmushi tace. "Eh Ammie sai da safe". Ammie tace.

"To shikenan Allah ya tashe mu lafiya ki gaida Hajiya Lubabatun". Salima na murmushi tace. " Zataji in Sha Allah". daga haka tai hanyar fita daga falon tana Satan kallan Afeef ta gefen Wanda yak'i kallanta dan tunda ya zauna falon Bai d'ago da kansa ba Yana cin abincinsa ne kawai gefe D'aya Kuma Yana kallan screen d'in wayar sa..
A hanya Salima ta Had'u da yayansu Aziz chiroma zai shigo b'angaren Ammie hannunsa rik'e da Manyan bags, da yake gidan da a kwai haske ta ko Ina kamar Rana Yasa Salima ta ganeshi,mamakine ya kamata ganin wannan uban kayan da yay b'angaren Ammie dasu bama bangaren suba .lab'ewa tai cikin wasu flowers d'in Dake compound Dan kada Aziz ya ganta ta zuba masa ido tana kallansa tana tunanin kodai ba nan d'in zashi ba Amma Kuma sai taga nan d'in dai yake nufa Hakan yasa ta cigaba da kallonsa harya shige b'angaren Ammie, fitowa tai daga cikin flowers d'in ta nufi b'angarensu da sauri Dan kaiwa mamansu rahoto tana waige waige harta k'arasa shiga b'angaren su......




#<9HUYAAM
#<9 LAMID'O
#<9 AZIZ CHIROMA
#<9 AFEEF




*Muje zuwa mutanan MRS SARAKIES =؋.ke daga Jin salon labarin kinsan zai k'ayatar ya Kuma fad'akar.akwai chakwakiya sosai anan gaba Dan labarin ma yanzu muka fara shi*.


*ga masu buk'atar fara payments zaku iya sa kud'inku a yanzu before mu gama free pages Regular group akan naira 500 kacal idan kuma muka gama Free pages zai koma 700 ne.ga masu buk'atar Vip Kuma 2 pages a Rana zaku iya biyan nai 1000 kacal. ku hanzarta ku fara biya tun kafin mu gama free pages.zaku iya tura kud'in ta wannan account d'in =G*


2270127432 Naja'atu umar
Zenith bank

Evidence of payment (shaidar biya )via
07066508376

Da zarar mungama free pages Kuma zamu sa duk Wanda ya biya kud'in sa a paid group, karku bari ayi wannan tafiyar Babu ku =؃=؃ mutanan arziki.





07066508376________
'Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD


*<9 HUYAAM <9*


*NA*



*__NAJA'ATU UMAR FAROOQ__*



*__(MRS SARAKIES =؋)__*



PAGE 2 1



*Tallah! Tallah!! Tallah!!!*


*Ina kuke hajiyoyin gidan nan,nace Ina kuke hajiyoyin gidan nan?to maza ku matso ga wata garab'asa ta zomu har inda kuke=؃=؃?.*


*Hajiya kaya Kikeso na fita kunya cikin taro ku Kuma so kike kallo ya koma akanki acikin Taron mata idan kika shiga biki ko suna ko Kuma Wani taro na musamman.to maza idan kina so ki kankarowa kanki mutunci kizo UK collection and gallery mu gwan gwajeki da kayanmu masu quality Wanda zaki gaji ki ajiye Dan kanki Amma badai ya mutuba Muna sai da kaya kamar haka=G*


*Atamfofi da lesses*
*Abaya*
*Shadda*
*Hand bag*
*Shoe*
*Veil na manya Dana Yara*

*Socks rin hands made d'in nan masu net*.

*Hula ta 'yan Gayu*

*Siyan D'aya ko sari*

*Duk zaki samu kan Farashi Mai sauki kedai ki garzayo UK collection & gallery Kisha Mamaki*

*Domin ganawa damu ko magana damu kai tsaye ku tun tub'emu kai tsaye ta wannan number kamar haka*=I08135305790

*Sai mun jiku =؃=؃=؃*


<9<9<9<9<9<9



*Bismillahirrahmanirrahim*



___________&


Da sallama a bakin Aziz chiroma ya k'arasa shigowa falon bayan yayi knocking an bashi iznin shiga.da mamaki kowa ke kallonsa ganin yadda ya shigo da kaya rik'i rik'i a hannunsa ,har Afeef Wanda ke zaune Bai tashi daga dining d'in ba kallan sa yake shima.duk suka ansa masa sallamar tasa ,Aziz chiroma ya zauna nan kan kujera Yana ajiye kayan Dake hannunsa anan gabansa kansa a k'asa ya shiga gaida Ammie.. Ammie na murmushi tace. "Lafiya lau Alhamdulillah Aziz ya gida ya aiki?..." Ta fad'a tana kallan sa.Yana shafa kansa tare da D'an murmushi yace. "Lafiya lau Ammie". Ammie ta Jin jina kai tace. "Masha Allah! Allah ya taimaka".ya ansa da ameen har lokacin kansa Yana k'asa Bai d'ago ba.Su ya Zarah ne suka shiga gaida shi ya d'ago da kansa Yana ansa musu tareda kallansu lokaci D'aya.har lokacin Bai lura da Afeef Dake zaune a dining ba, Shiko Afeef Yana kallansa bayan ya gama cin abincin ne ya tsaya Yana replying messages d'in da aka turo masa Yanzu ta wayarsa sa ,Dan tun shigowarsa ya ganshi.Aziz chiroma na d'an kame kame ya D'an sauke numfashi kad'an yace. "Ammie dama na Kawowa su Huyaam graduation gift d'in su da nai musu ALK'awari zan kawo musu, to bansamu naje nai musu lokacin graduation d'in ba sai yau dana samu time na fita,gashi Babu yawa ma". Ya Fad'a yana Satan kallan Huyaam ta gefen ido wacce tunda ta kalleshi sau D'aya bayan ya shigo ta d'auke kanta Bata k'ara yarda ta had'a Ido dashi ba ....


Ammie tana kallan sa tace. "Chiroma Mai yasa zaka wahalar da kanka wajen siya musu Wani gifts bayan Wanda duk suka samu". Aziz na D'an murmushi yace. "Ai Ammie Babu komai Duka sud'in sisters d'ina ne Kuma ba iya su kad'ai na siyawa ba gabad'ayansu duka na siyawa." Ammie tace. "Tom shikenan Allah ya Saka da Alkhairi ya K'ara Bud'i". Aziz ya ansa da Ameen a kunyace. Huda na murmushi tace. "Mungode ya chiroma Allah ya Saka da Alkhairi ya K'ara Bud'i". Ta fad'a cikin Jin Dad'i.Aziz ya kalleta yana murmushi yace. "No thanks sis".kamar Huyaam bazatai magana sai kuma ta D'an juyo kad'an ta kalleshi Karan farko data K'ara kallansa tace. "Thank you ". Ta fad'a a tak'aice.Aziz yay mata murmushi yace. "No thanks sister". Kamar ance ya juya ya hango Afeef Yana kallan screen d'in wayar sa Wanda ya Bada attention sosai akai ke kyace Bai San me akeyi a falon ba nan ko Babu abinda bayaji .Aziz Yana kallan Ammie yace. "Wancan yarima ne?..." Ammie ta kalli Afeef sai kuma ta kalli Aziz chiroma tace. "Eh shine kaje ku gaisa mana?..." ta fad'a tana kallan sa.Babu musu Aziz ya mik'e ya k'arasa dining d'in har wajen Afeef ya Mik'a masa hannu Yana cewa. "Barka da dare yariman kano". Ya fad'a da murmushi a fuskarsa.Sai a lokacin Afeef ya d'ago ya kalleshi sannan ya Mik'a masa nasa hannu sukai musabaha.Aziz yana D'an murmushi yace.


"Ashe ka dawo k'asar Kuma? Sai dai tunda ka dawo Allah baisa mun had'u ba sai yanzu Allah yayi". Ya fad'a Yana murmushi.Afeef ya D'an Saki fuskarsa kad'an tareda motsa bakinsa yace.

"Eh! Alhamdulillah!". Aziz yace. "Masha Allah sannu da dawowa". Afeef yace. "You are welcome". Aziz yace. "Thank you good night". Afeef yace. "Alright thank". Daga haka Aziz ya bar wajen Yana zuwa falo yay wa Ammie sallama Ammie tace masa ya gaida gida bayan ta k'ara Yi masa godiya.. AZIZ CHIROMA na barin falon kamar jira Huda take ta taso daga Inda take da sauri ta dira akan kayan.ta fara bud'ewa D'aya Bayan D'aya Ammie dai sai kallanta take hakama su ya Zarah itadai Huyaam tana zaune daga nan inda take zaune take kallanta.har Huda ta fiddo da wasu dogaraye riguna iri D'aya masu bala'in kyau.rike Baki tai tana kallan kayan da mamaki sai Kuma ta mik'e ta Kara D'aya ajikinta taga tayi mata dai dai nan ta Kalli HUYAAM tace. "Ki taso kiga kayan mana kika Wani zauna kina kallo na?...." Ta fad'a tana Wani zare ido.Huyaam tai murmushi ganin yadda Huda ta Wani susuce akan kayan sai Kuma tace. "Ki dai gama Gani ni idan kika waremun nawa na Gani daga baya". Tana fad'ar haka tana dariya lokaci D'aya..Huda ta tab'e Baki tace. "Ai shikenan". Nan ta cigaba da fiddo da kayan Saida ta gama fiddo su gabad'aya sannan Kuma ta kalli Ammie tace. "Ammie Kinga kayan Daya siyo manan". Ta fad'a cikin farin ciki.itama Ammie tai mamakin wannan uban kayan da aziz ya kawo musu tace. "Masha Allah kungode".ya Zarah ma tace". Masha Allah gaskiya kayan sunyi kyau yayi k'ok'ari sosai" Huda na murmushi tace.

"Kinga ya zarah gashi ma harda rings". Jin haka yasa Huyaam tai saurin juyowa Dan tana bala'in son rings sosai tuni ta sauko daga saman kujerar tayo wajen da Huda take tsaye tana kallanta tace. "Muga". Ta fad'a tana Mik'a hannunta. Huda ta Mik'a mata nan HUYAAM ta karb'a tasa a hannunta tace. Wow wallahi yayi kyau sai kace yasan size d'inmu kema Saka muga nakin".ta fad'a tana kallan Huda.Huda ta d'auki nata itama tasa Huyaam tace. "Wallahi kema yayi Miki dai dai size d'inmu yasiyo Kuma yayi Miki kyau wallahi, i like it so much inason ring". ta fad'a da Wani sautin Dayasa Afeef Saida ya juyo ya Kallesu take ya hango ring d'in Dake Hannun HUYAAM Wanda sai jujjuya hannun take Yi ga yadda hasken wutar ya haske shi ya fito sosai yana Wani fidda hasken stone"Muneefa data ke ganin kayan tace "ai Ga Wani ma anan". ta fad'a tana Mik'o musu take Huyaam tai saurin Karb'a tace .

"Wow! wannan ai gold ne ya Allah! Gaskiya ya chiroma mun gode Sosai we really appreciate it". Ta fad'a kamar Yana wajen.sai Kuma ta Mik'awa Huda d'ayan bayan ta d'auki nata tace "kema ga naki".Huda ta karb'a tana murmushi tace. "Wallahi ya Aziz Yana da kirki sosai gaskiya mun gode komai yayi kyau". Huyaam na kallan hannunta ganin yadda zoben ya hau hannunta tace. "Kedai bari ai nasamu nayin Gayu kuma". ta fad'a da Wani Irin farin ciki. Afeef ne ya taso daga dining d'in yazo zai wuce zuwa b'angaren su Huyaam na kallansa ta k'arasa gabansa da sauri ta tsaya tana murmushi ta kalleshi tace. "Yaya kaga zoben da ya chiroma ya kawo mana".ta fad'a tana Mik'a masa Hannun nata Wanda ke d'auke da 2 rings.. kallan yatsun nata Afeef yayi na Wani lokaci sai Kuma ya d'ago ya kalleta Ganin yadda take masa murmushi alamun taji dad'i.ya d'auke kansa yace. "Okay na gani bani hanya na wuce".ya fad'a a maganarsa Babu alamun wasa .Huyaam ta Wani tura Baki gaba tana kallansa tace. "Yaya baka Kalli sauran kayan ba kuma Zaka tafi". Ya d'ago ya mata Wani kallo tun kafin yayi magana ta matsa daga gabansa tana murmushi. ya kalli Ammie yace. "Saida safe". Ammie tace . "To Allah ya tashe mu lafiya".ya ansa da ameen Yana yin gaba.huyaam ta koma kusa da ya Zarah tace. "Ya Zarah Kinga zoben Aiya min kyau koh? Tunda yaya Bai fad'a ba". Ya zarah ta Kalli hannun Huyaam taga rings d'in sun K'arawa yatsun nata kyau tace. "Masha Allah yayi kyau sosai akashe lafiya". Tai murmushi tace. "Thanks". Sai kuma ta bar wajen muneefa ta taso tace "muga hannun ya HUYAAM?.." Huyaam na murmushi ta nuna mata hannunta Saida ta kalla sannan ta d'ago ta Kalli HUYAAM da murmushi tace. "Yayi kyau". Huyaam na Maida mata da Martanin murmushin cikin Jin Dad'i tace. "Thank you Auta". Ya Haidar ne yashigo bakinsa d'auke da sallama duka suka ansa masa har ya k'arasa shigowa falon ya Gaida Ammie.Ammie ta ansa masa gabad'ayansu suka shiga Yi Mai Sannu da zuwa Yana kallansu ya ansa musu sai Kuma yaga yadda suka baje kaya anan falon Yana kallansu yace. "Wannan Baja kolin kayan da akai fa".kafin kowa ya bashi ansa Huyaam tazo gabansa da sauri ta tsaya tana murmushi tace. "Kaga Ya chiroma ne ya kawo mana". ta fad'a tana nuna masa Hannunta alamar Yaga zoben.ya haidar ya Kalli hannun Nata ganin yadda rings din sukai mata kyau.yana kallanta yace. "Rings ya kawo muku?...." HUYAAM na murmushi tace. "Ba iya shine ba duka wannan kayan da kake gani shiya kawo mana". Ya haidar ya Jin Jina kai yace. "To Masha Allah". Ya fad'a yana rab'awa ta gefenta ya wuce . Huyaam tace da D'an k'arfi. "bakace yayi min kyau ba". Batare da ya juyo ba yana hayewa stairs yace.." yayi kyau shikenan". Huyaam Ta kad'a kai tana murmushi tace. "Nagode".sai Kuma ta juyo ta k'arasa gaban Ammie tace. "Ammie Yamin kyau ko?...".ta fad'a tana juya hannun Ammie ta kalli hannun tace". Oh ni Maryam yanzu kowa ma sai annunawa wannan zoben?..". Ya zarah tace. "Hmmm HUYAAM ce fa ai har Abba sai ta nunawa da Yana nan.Huyaam ta tura Baki gaba tace. "Ammie kyau fa Yamun". Ammie ta Jin jina kai tace . "To ko Allah ya kyauta". Huyaam tai murmushi tace. "To kuma Bakice Yamin kyau ba". Ta fad'a tana Wani tura baki.Ammie ta sauke numfashi ganin bama ta maganarta take ba ta gyada mata kai tace."to yayi Kyau shikenan". Huyaam tai murmushi tace. " Eh". Ammie tace. "to ku kwashe komai kukai d'aki sai Kuma kuje ku kwanta". Ta fad'a tana mik'ewa suka ansa mata da to" ta kama hannun muneefa suka haura sama ya Zarah ma ta tashi tabi bayan Ammie rik'e da wayarta aka bar su Huyaam da kwashe kayan....



____________&



Bayan fitar Aziz chiroma daga b'angaren Ammie direct Wajen Motar sa ya nufa ya dauk'o sauran kayan Daya siyawa su ikleema da safna da Aziza yayi b'angaren su dashi, anufinsa tunda dare yayi idan ya bawa ikleema nata kayan sai ya Bata nasu Aziza ta kai musu da safe. Da sallama a bakinsa ya shiga falon nasu . Hajiya Lubabatu ya Gani zauna akan kujera da Salima Wacce ke Zaune kusa da Hajiya Lubabatu da dukan alamu shi Suke jira.sauran yaran duk sun shiga d'akinsu sun kwanta bacci ya Bahijja ma tana d'akinta.da k'yar Hajiya Lubabatu ta iya ansa masa sallamar tasa tana juyar da kanta gefe ranta a b'ace .Aziz ya K'arasa shiga cikin falon ya ajiye kayan hannunsa nan tsakiyar falon Yana kallan maman nasu yace. "Ina ikleema?...".ya fad'a Yana zama kan kujerar dake kusa da shi...

Hajiya Lubabatu ta juyo tai masa Wani kallo tace.

"meye wannan d'in ka Wani ajiye anan". Aziz na sauke numfashi yace". Gifts d'in graduation d'insu ne na Siyo masu sai yau na samu time"..ya fad'a Yana jinginar da kansa Jikin kujerar.... Hajiya Lubabatu tai masa Wani kallo tace.... " To Yanzun Daga Ina kake? nasan ba direct daga wajen siyayyar kake ba". Aziz ya d'ago ya kalleta da mamaki Jin abinda ta fad'a.sai kuma yace "eh saida na fara zuwa wajen Jafar sannan na dawo gidan".... Hajiya Lubabatu tace a fusace. Ba haka nake son jiba daka dawo gidan ina ka fara zuwa kafin kazo nan?..."Aziz ya Kalli maman nasu da mamakin Irin tambayar da take masa kamar Wanda yay mata Wani mugun abun sai kuma ya Sauke idansa k'asa yace. "Eh naje b'angaren Ammie na kaiwa su Huda nasu kayan kafin nazo nan". Hajiya Lubabatu tai masa Wani kallon takaici tace .

"Hmm! ai dama na sani daga wajen k'anwar uwar take kake,kaje ka kaso musu mak'udan kud'ad'e ka d'auko saura ka kawo nan ,bama wannan ba shi kuma wannan kayan na nasuwaye da waye?..."Aziz ya sauke numfashi yace. Nasu Ikleema da safna da Aziza". Hajiya Lubabatu tai masa Wani kallo kafin tace.

"Me yasa Su d'in Baka kai musu nasun yanzu ba?..." AZIZ yace . Saboda dare yayi shiyasa gobe sai ikleema ta kai musu nasun."Hajiya Lubabatu tace.

"Oh! mai zaisa suma Wad'anda ka kaiwan ka bari duk ka had'a ikleema takai musun da safen ko sun fisu Wani matsayi ne a gunka da ka tafi ka kai musun Yanzu da kanka". ta fad'a cikin b'acin Rai.Aziza yace cikin k'osawa da tambayar da maman nasu ke masa

"Haba Mama wai Dan Allah Mai kike tunanine akaina? yanzu Dan na Siya musu Abu na kai musu shine abin yimin wannan tambayoyin haba Dan Allah! Yanzu shi Afeef da yake musu siyayyar wacce ta linka tawa sau Dubu Ammie batai k'orafi fa sai ke ko shi kyauta ake basa haba Dan Allah!".ya fad'a k'irjinsa na sama da k'asa Saboda b'acin Rai". Hajiya Lubabatu ta saki Baki da hanci tana kallan Aziz da mamakin abinda yake fad'a mata sai kuma can tace. "Wato ni kake yiwa wannan shouting d'in ko Aziz? To kaje ka tattare dukiyar ma gabad'aya ka kai musu shine zansan Maryam tafini matsayi awurinka".shidai AZIZ huci kawai yakeyi.hajiya Lubabatu tai tsaki ta cigaba tace. "Ya bazan bazan Maka fad'a ba kana can kana almobazzaranci da kud'inka akan Wand'anda Basu ma damu da kai ba". Aziz ya kalleta yace. "Waya fad'a miki wannan maganar na tabbatar baki sani ba zuwa akai aka fad'a miki"
Hajiya Lubabatu tai masa Wani kallo tace. "Ni Babu Wanda ya fad'amin kawai jiki nane ya bani".shidai Aziz kallanta kawai yake". Hajiya Lubabatu tace ai kaima kasan Dole zan sani". Aziz yace. Amma mama kema Kinsan ko Mai naiwa 'ya'yan Ammei da Mai martaba kinsan ban biya suba ko? Kiduba kiga Irin wahalar da sukai Dani ko ko Mai martaba,aini d'aukata kece ta kan gaba wajen cewa nai musu Abun duniya Koda ko banyi niyyar yin hakan ba , Amma yau kece kike ganin nayi asara idan nai musu Abu ". Hajiya Lubabatu tace a fusace. "Karka sauya min magana ta ni ba haka nace ba Amma komai zakai Mai zaisa baza ka nemi shawarata ba,Aziz kasan mahaifinka kai kad'ai ya mutu ya bari yanzu dukiyar taka zaka sa agaba sai ka kashe musu ita du sannan Hankalinka zai kwanta ko yaya?..."shaidai Aziz yay shiru Yana kallanta da mamakin abinda take fad'a.haka Hajiya Lubabatu tai ta fad'a kamar zata Ari Baki ganin baza ta fasa ba Yasa Aziz ya Mik'e tsaye ya shiga k'walawa ikleema k'ira Dake cikin d'aki. ikleema da har ta fara bacci taji muryar Yayan nasu ta fito da sauri tana mitsuka ido har ta k'araso falon tana cewa. "Yaya Gani". Ta fad'a tana kallan yanayinsa Yace. " ki d'auki wannan kayan kishiga dashi ciki sai ki d'auki naki ki ajiye sauran gobe da safe Kuma ki kaiwa su safnah da Aziza". Yana fad'ar haka ya fita daga falon ko juyowa Bai yiba da K'iran da Hajiya Lubabatu ke masa ba Saboda gabad'aya ransa ya gama B'aci da abinda tai masan .da murnar ikleema ta k'arasa ta d'auki kayan ta koma d'akinta... Hajiya Lubabatu ta Kalli Salima tana huce tace. "Yanzu badan Allah yasa kin Gani ba da shikenan haka zaita kashe musu uwar kud'i ni uwarsa Bai kawomin komai ba". Salima ta tab'e Baki tace . "Saima Kinga uban kayan Daya siya musun wannan ai Kashi D'aya ya kawowa su ikleema akan Wanda yakai can b'angaren". Hajiya Lubabatu tai k'wafa tace ."rabu dashi zai dawo ya samenine kina fa ganin inai masa magana Amma ya fice ya barni saboda Ina fad'a masa gaskiya akan abinda yake ba dai dai bane shine ya gaba ya barni ni ban tab'a ganin Sha Sha marar hankali Irin Aziz ba kwata kwata bashida wayo ko kad'an "Salima tace . "Hmmm ai wallahi mama sai Kin tashi tsaye in ba haka ba haka zaita zuwa Yana kashe musu kud'i". Hajiya Lubabatu tace. "Aikuwa Wallahi bai Isa ba dai dai nake dashi". daga haka ta Mik'e tana kallan salima tace . "Tashi muje mu kwanta kuma Ina nan Ina jiransa Allah ya kaimu goben ai ba zama zaiyi a inda yaje d'inba ko".salima mik'e tai d'akinsu itama Hajiya Lubabatu tai nata d'akin tana ta masifa ita kad'ai datai Sa'a ma yau ba kwananta bane ba.......




Aziza ce ta sauko downstairs tana Neman mummynta motsin da taji a kitchen ne yasa ta K'arasa tashiga kitchen d'in ta Tarar da fulani Salamatu tsaye gaban gas tana kallan mummyn nasu tace. "Mummy". Fulani Salamatu Dake juye green tea a cup zata kai WA Mai martaba ta juyo tana kallon Aziza sai Kuma ta sauke ajiyar zuciya tace. "Har kin ban tsoro Mai ya fito Dake yanzu bakije kin kwanta ba?...."

Aziza Tana mutsuka ido tace. "Harna Kwanta na tashi Bayan na tuna abinda zan fad'a miki". Fulani Salamatu tace. "Menene abinda zaki fad'a d'in Baki fad'a min tun safe ba ko Kuma ki bari sai gobe?..." Aziza tace. "Dama so nake idan kinje wajen Mai martaba ki tuna masa zancen wayar tamu naga Yayan ya dawo Kuma har yanzu ba'a siya mana ba bayan naji ance Yana dawowa Za'a siya mana". Ta fad'a tana Wani tura Baki gaba. Fulani Salamatu ta sauke numfashi tace. "To naji zan fad'a masa".tafi ki Kwanta Aziza tai murmushi tace. "Thank you mummy wallahi gabad'aya friends d'ina kowa da wayarsa Amma Kuma yani ace Banda waya". Ta fad'a

Please Login or Register in order to submit comment