Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

so nake mu koma Egypt d'in nan ma kwana nan Dan baza mu gaji ba" anty Amina tace. "Nima dai da Hakan nace ko Allah zaisa wata Rana a dace"? Hajiya inna tace.
" sosai kuwa dan komai sai anayi ana Raba k'afa". Anty Amina tai murmushi tace. "To Allah dai yasa mudace" . Hajiya inna akace . "Ameen dai". knocking d'in k'ofar d'akin akayi Hajiya inna ta Kalli k'ofar kafin tace. "waye Kuma? sultan ne ya shigo cikin shigar shadda fara k'al Wacce tai masa bala'in kyau sai Wani k'amshi yakeyi gashin kannan nasa ya kwanta luf luf akansa . Hajiya inna ta bishi da kallo harya k'arasa shigowa d'akin ganin yadda yayi sallama k'asa k'asa gaida Hajiya inna yayi da anty Amina batare daya Kalli D'aya daga cikin su ba.duk suka ansa masa da kulawa.suna kallansa har lokacin. duk'awa yayi bakin gadon dai dai saitin kan gimbiya Aysha ya kamo hannunta ta kalleshi da kumburun idanuwanta ya sumnaci hannunta idansa Yana kan ta yace cikin yanayin muryarsa. "Mami Ina kwana ya jiki Allah ya K'ara lafiya" haka duk ya jero mata wannan gaisuwar. lumshe idonta tai sai Kuma ta Bud'e lokaci D'aya tana kallansa. Mik'ewa yayi anty Amina na kallansa tace. "Kayi breakfast d'in ne sultan?. batareda ya kallate ba ya gyad'a mata kai". Anty Amina Bata damu ba Dan Bai ansa mata ba tace. "Yanzu Kuma ina zaka?." Nan ma Bai jiyo ba yace. "School". Atak'aice. Hajiya inna ta zaro ido tana kallansa Jin abinda yace tace tana kallansa da mamaki. "Makaranta Kuma sultan? Wani Irin makaranta kaida baka da lafiya ko ka manta yadda aka dawo da kai gidannan shekaranjiya ne?...".ta fad'a tana sare ido.Batareda da ya juyo ba yay hanyar k'ofar fita daga d'akin yace. "Ni Babu wata jinya danai". Yana fad'ar haka ya Bud'e k'ofar ya fita daga d'akin.hajiya inna ta mik'e tsaye tana kallan anty Amina tace. "Kinji abinda yace ba? nifa Ina tsoron wannan al'amari Irin na sultan Abu kamar sihiri yau lafiya gobe Kuma akasin haka ,yo miye ma ai dama Shima sihirin ne akai masa". Sai Kuma ta d'aga hannayenta sama tace. "Allah mun gode Maka Allah mun tuba idan Wani babban Laifi muka aikata Allah ka yafe mana idan kuma Wani ne yake nufar wad'an nan Bayin naka da sharri ya Allah ka Mai da masa ya koma kansa". Ta fad'a tana Shafa addu'ar jiki a Sanyaye. Sai kuma ta kalli anty Amina tace. "Amina kina fa jin abinda yace wai a hakan zaije makaranta salon yau d'inma yaje adawomana dashi rai a hannun Allah kamar ranar, gaskiya bazan bari ya tafi ba zuwa Zanyi na fad'awa Abdallah ya hanashi tafiya danni tun ba yanzu ba nake tsoron fitar sultan daga cikin masarautar nan". Ta fad'a cikin damuwa.

Anty Amina ta sauke numfashi tana kallan Hajiya inna tai k'asa da murya tace. "Tunda kika ji yace shi baiyi jinyar ba Inaga Babu abinda yaje ji ayanzu kawai kiyi hak'uri mu k'yaleshi tunda Yanzu mun samu lafiyar ta fara samuwa sai mu godewa Allah,barema ai ba shi kad'ai yake tafiya ba akwai masu masa rakiyar". Hajiya inna tace. "A'a ke yarinya ce Amina Baza ki gane bane bakisan Irin wannan ciwon yadda yake ba dole sai anayi ana kula da taka tsan tsan dashi Dan Koda yaushe yakan iya tashin masa bari dai naje kawai". Daga haka ta nufi k'ofar fita daga d'akin .anty Amina ta bita da kallo tana girgiza kai dan tasan indai sultan ne ba lallai ya hanuba sai dai idan Mai martaba ne da Kansa yay Masa magana tukunna....



____________&


*Masarutar Kano*


Afeef ne zaune k'asan carfet a babban falon Mai martaba kansa a k'asa ya tank'washe K'afarsa yana sauraran abinda Mai martaba yake fad'a masa harya Kai k'arshen zancen na sa.Afeef ya gyara zaman sa yace cikin nutsuwa. "Eh Abba Babu damuwa Allah Ya kaimu ranar Monday d'in zanje in Sha Allah". Mai martaba ya Sauke numfashi yace."yauwa! am sannan ba komai ne yasa zan tura ka Lagos d'in ba sai Dan inaso ne kaje ka Gano min yadda suke tafiyar da harkokin nasu Duk da nasan Babu wata matsala suna aikinsu yadda ya kamata domin babu abinda lamid'o bayayi dama sauran ma'aikatan.Amma Kuma Muhammad komai sai anayi Ana samun sabbin abubuwan cigaba". Afeef yace. "Hakane rankai Dad'e kuma in Sha Allah zanje d'in". Mai martaba ya cigaba Yace. Sai Kuma zancen school d'in su Huyaam dama inaso muyi magana da kai wacce school kake ganin ya kamata akaisu ne dan da a San samu nane inasone akaisu k'asar waje idan results d'in nasu ya fito Amma kai ya kake ganin za'ayi?". Afeef yay shuri Yana Jin abinda Mai martaba yake fad'a sai Kuma can yay k'asa da murya cikin girmamawa yace. "Ai Abba duk yadda kace ayi haka za'a Yi". Mai martaba yace "A'a ni Ina tambayar taka shawarar ne amatsayinka na babban yayansu". Ya fad'a Yana kallan yanayin Afeef. Afeef ya K'ara gyara zaman sa yace. "Abba ni atawa shawarar kawai da a barsu a Nigeria kamar yadda su Zarah sukeyi sai Yafi ni bazanso akaisu out side of the Nigeria karatu ba, tunda akwai masu rawar kai acikinsu Amma agafarceni idan ban Fad'i dai dai ba".Afeef ya fad'a Yana K'ara duk'ar da kansa k'asa.Mai martaba yay shiru na Wani lokaci sai Kuma can yace. "Bakai laifi ba dama shawara na nema a wurinka Kuma naji opinion d'inka akan hakan so Nima abinda nai tunani kenan, but Any way dai bari mu jira har results d'in ya fito sai Muji Ina ya kamata akai sun". Afeef yace. "Hakanma yayi Allah ya taimakeka". Mai martaba yace "yauwa! Nace yaushe ne hutun naka zai k'are?.. Afeef yace. "Saura sati biyu Rankai Dad'e". Mai martaba yace. "Ok! da sauran kwanaki kenan har ka gama duk ayyukan Dana Saka kama". Afeef yace. "Eh in Sha Allah" Mai martaba yace. "Daga nan kuma sai bikin su zulaihat zakazo ko?..." Afeef yace. "Eh! In Sha Allah". Mai martaba yace "Shikenan Allah ya Taimaka". sai kuma ya cigaba Yace

"sai Abu na k'arshe tunda sun gama school har suna shirin shiga jami'a Mai zai Hana a Siya musu phones before dai su shiga jami'ar ya kamata ace an siya musu waya koh ya ka Gani?. Afeef yay murmushi Jin abinda Mai martaba ya fad'a wai Asiya musu waya shifa har yanzu gabad'ayansu kallan marasa hankali yake yiwa su Huyaam yaran da har yanzu basu gama sanin ciwon kansu ba Amma ace a Wani siya musu waya". Mai martaba yace. "Ya kake murmushi Muhammad ko Bai yi bane ba?" Afeef na kallan Mai martaba yace. "A'a Abba yayi yaushe za'a siya musun?" Mai martaba yace. ."ko yaushe ma before dai ka koma". Afeef yace. "To rankai Dad'e in Sha Allah gobe zan fita zai na taho musu da ita". Mai martaba yace. "Shikenan Allah yasa". Afeef ya ansa da Ameen". Sai Kuma suka koma tattaunawa akan kamannin Mai martaba take can Ingiland da tsare tsaren da zasuyi sai wajen k'arfe shabiyu sannan Afeef yayi WA Mai martaba sallama ya fita daga falon gabad'aya.......



#<9HUYAAM
#<9LAMID'O
#<9AZIZ CHIROMA
#,<9AFEEF



*mutanan MRS SARAKIES =؋ Kuna Ina ne? ana ta payments na book d'in Huyaam ku an barku a Baya to Maza ku garzayo yanzu kar wannan garab'asar ta wuce ku*.


*ga masu buk'atar fara payments zaku iya sa kud'inku a yanzu before mu gama free pages Regular group akan naira 500 kacal idan kuma muka gama Free pages zai koma 700 ne.ga masu buk'atar Vip Kuma 2 pages a Rana zaku iya biyan nai 1000 kacal. ku hanzarta ku fara biya tun kafin mu gama free pages.zaku iya tura kud'in ta wannan account d'in =G*


2270127432 Naja'atu umar
Zenith bank

Evidence of payment (shaidar biya )via
07066508376

Domun yin magana Da marubuciyar Kai tsaye 07066508376 only chart


Da zarar mungama free pages Kuma zamu sa duk Wanda ya biya kud'in sa a paid group, karku bari ayi wannan tafiyar Babu ku =؃=؃ mutanan arziki.




07066598376________
'Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD


*<9HUYAAM<9*


*NA*


*__NAJA'ATU UMAR FAROOQ__*



*__(MRS SARAKIES =؋)__*



PAGE 2 5



*TALLAH! TALLAH!! TALLAH!!!*


*Ina kuke manyan mata masu capacity ==؃=؃? Nace Ina kuke hajiyoyin gidan nan, to Maza ku Bud'e kunnuwanku ku saurarareni > da kyau.Dan a yau nazo muku da Wani kyakkyawan albishir=؃=؃ wanda zakuji dad'insa fiye da yadda zan fad'a muku.Nace ba, Bakuda Labarin hamshak'iya shahararriyar 'yar Kasuwar nan wacce tai K'aurin suna wajen kawo muku kayayyakinta na 'yan Gayu masu quality wato H.Empire < Lagos Mai gidan kayan sawa na mata na k'walisa da Kuma kayan kitchen?..."*

*To idan yau kuka tab'a ji ya kamata ace kun saurareni kunji da abinda nazo muku dashi. Kayan sawa kike so Wanda zaki zama tauraruwa a cikin 'Yan uwanki mata harma da Mai gida wato oga kwata kwata Hajiya ta , ko ko so kike duk inda kika gifta kallo ya koma kanki?. Ko Kuma kayan kitchen kikeso masu kyau da aminci daki bari. To Maza ku garzayo H.Empire < Lagos anan zaku samu duk Wani Irin Abu da kuke so, Dan mu kayan mu quaranti ne Hajiyata bakida tan tama akai, kudai ku gwada siya kawai zakusha mamaki Dan sai Kun bani labari. Muna Saida kaya kamar haka ka* =G

*1,Atamfofi*
*2, lesses*
*3, Abaya*
*4, kayan kwalliya ko Wani iri ne*
5,*D'an kunnaye(jiwelleries)*
*6,takalma*
*7,hand bag*
*8, mayafai*
*9, sai Kuma kayan kitchen shima Muna sai dawa, Dan duk Wani kayan kitchen d'in da kike nema harma da Wanda Baki tab'a Gani ba ko sani to idan kikazo H.Empire < Lagos anan zaki samu duk Wani Irin kayan kitchen muna Saidawa akan farashi Mai sauk'i da rahusa siyan D'aya ko sari*.

*domun magana damu kai tsaye ko Kuma Neman K'arin bayani ku tun tub'emu ta wad'an nan numbers d'in kai tsaye kamar haka =I+234 811 190 1302 /09020337676*


*Siyan na gari Mai da kud'i gida Hajiya ta*

*Sai mun Jiku=؃=؃*


<9<9<9<9<9<9



*Bismillahirrahmanirrahim*


____________&


Washe gari da safe har k'arfe shad'aya Saura Huyaam Bata tashi daga baccin safen da take nay Wanda ta koma bayan sallahn ASuba ba, dama tun jiya ta daddare ta kwanta da complain d'in kanta na mata ciwo.nan dai Ammie ta d'auko maganinta ta bata ta Sha,to anan ta samu har bacci ya d'auketa,to d'azu da ASuba ma dai Ammien ta k'ara lek'ata Taga jikin nata da sauk'i Dan har tashi tai tai sallahn ASuba ma. Shine Ammien fa tace kar kowa ya tashe ta a barta ta huta har sai ta tashi Dan kanta.to kuwa wannan maganar datai yasa babu Wanda yay gigin zuwa inda Huyaam d'in ma take har ita Kanta hudan.. Ammie ce ta sauko downstairs ta k'araso falon ta tsaya tana kallan Huda Dake Zaune afalon nan saman kujera tana karanta Wani book daya ke babu kowa Agidan sai iya Hudan tunda su su muneefa sun tafi school tun da safe ya Zarah ma dai itama ta tafi school d'in,Ammei na kallan Huda tace. "Huda Ina HUYAAM na lek'a d'akinta bangan taba?..". Huda ta juyo tana kallon Ammie sai Kuma tace. "Eh tana d'akina can ta koma d'azu". Ammie ta sauke numfashi tace. "To har yanzu Bata tashin bane?..." Ta fad'a tana kallanta .Huda tana kallon Ammien nasu tace. "Eh Ammie har yanzu Bata tashi ba d'azu na lek'a ta sai naji jikinta da zafi".gaban Ammie ya D'an Fad'i Jin abinda Huda ta fad'a sai kuma tace. "Shikenan Allah yasa dai lafiya?.Huda ta Mik'e tana kallan Ammie tace.
"Ameen, Amma Ammei bari naje na lek'ata kota tashi ta
yanzun?..."Daga haka Huda ta Mik'e daga zaunan da take tana ajiye book D'in hannunta nan saman kujerar data tashi ta haura sama zuwa d'akin nata da sauri.. tura k'ofar tai bayan ta isa Amma sai taji k'ofar a rufe K'ara turawa tai nan ma dai the same thing,Hakan yasa ta fara knocking k'ofar tana turawa lokaci D'aya Amma Kuma shiru Babu alamun za'a Bud'e sai Kuma ta fara K'iran sunan HUYAAM lokaci D'aya da cewa ta Bud'e k'ofar itace amma Shiru Babu alamun za'a Bud'e k'ofar nan dan tafi mintuna 10 tana knocking k'ofar Amma shiru Huyaam Bata Bud'e ba, gajiya Huda tai da knocking d'in ganin Huyaam bazata Bud'e ba Hakan yasa ta juya zata bar Wajen kenan taje ta sanar wa da Ammie cewar HUYAAM d'in Bata Bud'e k'ofar ba kawai taji Wani Irin K'ara da Huyaam tasa ata cikin d'akin Wanda yasa gabad'aya Saida part d'in ya amsa har Ammie Dake zaune falon downstairs tare da Afeef Wanda ya sauko yanzu Bada dad'ewa ba yana gaida Ammien, kawai Sai Kuma sukaji wannan ihun na Huyaam ga Kuma k'arar fad'uwar abubuwa acikin d'akin Mai kama da fashewar kwalabe kodai something like that.take gaban Huda ya Fad'i zata sauka k'asa kenan suka kusan cin karo da Ammie data hawo upstairs d'in cikin akid'ime hankali tashe Afeef na biye da ita har lokacin HUYAAM ihu take tana kuka Bata kuma fasa bige bigen ta takeyi ba. Ammie ta k'arasa bakin k'ofar ta fara bubbugawa da jijjigawa da k'arfi Tana K'iran sunan HUYAAM Amma shiru bata ansa ba. Afeef ya kalli Huda yace. "Wai meya sameta ne?...." Huda da kamar zatai kuka ta kalleshi tace. "Nima bansani ba Amma Inaga ko ciwon nata ne ya Tashi". Afeef yace. " Ya akai tasawa k'ofar key Kuma? Sannan Mai zaisa kema ki bar key ajikin k'ofar?....". Ya fad'a ransa a b'ace.Huda tai saurin cewa "A'a akan mirror na barshi k'ila d'auka tai Amma bari na d'auko nata sai agwada ko ta cire key d'in bayan ta kulle k'ofar". tana fad'ar haka ta bar wajen tai d'akin Huyaam da sauri" Afeef ya bita da Wani Irin kallo.ita kan Ammie Bai war Allah sai faman bubbuga k'ofar take tana K'iran sunan HUYAAM akan ta Bud'e k'ofar kamar zatai kuka Amma ko alamun Huyaam zata Bud'e k'ofar nan Babu Kuma har lokacin kuka take da ihu ahad'e , gabadaya hankalin Ammie ya gama tashi da halin da Huyaam take ciki ,ita kanta baba magajiya Saida ta lek'o daga kitchen amma Bata haura stairs d'in ba ganin mutanan gidan a wurin.ahaka har Huda ta kawo key d'in ta Mik'awa Afeef, kamar bazai karb'a dan Gani yake kamar Huyaam d'in tabar key d'in ajiki ne ,nan ya matsa kusa da k'ofar yana Kallan Ammie Dake ta K'iran sunan HUYAAM akan ta Bud'e k'ofar yay k'asa da murya cikin lallashi yace.

"Ammie bari na Bud'e,ki kwantar da hankalinki bari na gwada ko k'ofar zata Bud'e". Ammie ta kalleshi tace cikin Damuwa. "Ka gafa Afeef sai ihu take tana fashe fashe kar naje ta jiwa kanta ciwo fa ?.." ta fad'a murya a karye . Afeef yace. "In Sha Allah babu abinda zai sameta bari nai trying idan ma baiyi ba sai a b'alla k'ofar kawai".ya fad'a cikin lallashi
da k'yar Ammie ta D'an matsa baya Afeef yasa key d'in Amma Kuma sai dai Kash akwai key ata ciki ajikin k'ofar ,nan shima hankalin Afeef d'in ya K'ara tashi Ganin to ta inama za'a fara, bare a cetota daga jiwa kanta ciwon da takeyi Dan yasan Hakan ce zata faru .sauke numfashi yayi ya kalli Ammie yace. "Da key ajikin k'ofar Ammie dole sai dai a b'alleta". Ammie ta girgiza kai tana kallonsa tace. "Afeef waye zai b'alle k'ofar gaskiya bazan iya jire har sai an k'ira Wani Mai b'alle k'ofa ya zoba ni tsorona ma karta jiwa kanta ciwo Dan Allah Afeef ya za'ayi?..." Ta fad'a cikin damuwa.Afeef ya K'ara k'asa da murya yace shima cikin damuwar Dan fa da Gaske Huyaam buge buge kawai take acikin d'akin nan tana kurma ihu lokaci D'aya yace. "Ni zan b'alla k'ofar Ammie ki kwantar da hankalinki Babu abinda zai sameta"? Ammie ta girgiza kai tace. "To Kuma yanzu Afeef idan kaje ka b'alla k'ofar ta fad'a a kanta fa?...." Afeef yace. "In Sha Allah ma Hakan bazai faruba ku matsa baya". Ya Kalli Huda wacce sai kuka take yace. "Taja Ammie suyi baya". Babu musu Huda ta rik'o hannun Ammie da k'yar ta iya yadda Huda ta kamata suka matsa baya Nan Afeef shima yay baya kad'an ya daki k'ofar da K'afarsa Amma ko gizau batai ba ya kuma Dakar k'ofar nan ma dai babu alamun k'ofar zata Bud'e.ya kusan 5 minutes Yana k'ok'arin ganin ya b'alla k'ofar Kuma da dukan k'arfinsa yakeyi Amma k'ofar nan ko gizau batai ba kamar wata k'ofar rodi,wata dubara ce ta tazo masa na Mai zai Hana ya daki dai dai inda key d'in yake. nan ya fara dukan saitin wajen key d'in k'ofar ,da k'yar da k'yar k'ofar ta Bud'e akai Sa'a Bata balle bama gabad'aya Dan iya wajen key d'in ne kawai ya tashi daga aiki sai dai a sake Saka Wani .. cikin sauri ya shiga Ammie ma ta k'araso da sauri ganin ya b'alle k'ofar har suna rige rigen shiga ita da Huda. tsaye suka Samu Huyaam a birkice, Sanye da kayan bacci riga da Wando, kannan nata da babu D'an kwalli bare hula ribbon d'in ma yay nasa wajen gashin nan nata ya bar baje nan tsakiyar kanta hannunta rik'e da wata kwalbar turare wacce ta fashe Kuma har lokacin Bata daina kuka da ihun da take ba tana ta dukan bangon d'akin da kwalbar turaren hannunta da duka k'arfin ta, ga yadda ta wargaza d'akin kamar Babu wata halittar data tab'a rayuwar acikinsa saboda yadda taiwa d'akin kaca kaca Dan kuwa babu matsakar tsinke acikinsa ko Ina kwalabene da kayan kwalliya data b'aro su daga kan mirrorn,ga k'afar ta da hannunta sai d'igar jini sukeyi alamar dai ta yanki jikinta.Afeef dai kallanta Kawai yake cikin tausayawa can ya taka zai kanta ya rik'o ta ganin haka yasa Huyaam tai baya da sauri tana zare masa ido tana yin baya at the same time tana sakin Wani ihun da k'arfi , Afeef Bai kula ta ba ya bita ya rik'o ta Cikin dabara da sauri, ganin ya rik'o ta yasa ta rikice masa ta fara k'ok'arin k'wacewa daga rik'on da yay mata Tana ya gunsa tana Kuma K'ara sakin wani ihun da iya k'arfinta, Wanda Saida yasa Afeef ya rintso idonsa ya rik'o ta zuwa jikinsa Bata fasa kokawa dashi ba tana Neman k'wacewa hakan yasa Ammie ta k'araso ta rik'e ta itama Afeef ya sakar mata ita ganin Ammien ta rungumeta zuwa jikinta tana cewa. "HUYAAM menene? Stop it please sorry daughter ya Allah! Innalillahi wainna ilaihi rajiun". haka kawai Ammie take fad'a sannan ta jawota suka Zauna nan gefen gadon har lokacin huyaam tana jikinta rungume da ita .Afeef ya D'an matsa kusa dasu ya rik'o hannun Huyaam d'in Dake k'ok'arin fusge gashinta nan ya fara Yi mata addu'ar duk da tazo bakinsa Ammei na tayashi kafin ta kalli Huda Dake kallan Huyaam da tausayawa tana jero mata Sannu tace. "jeki d'auko mun maganinta a d'akina Yanzum nan". Babu musu Huda ta fita daga d'akin cikin sauri". Babu dad'ewa ta dawo Hannunta rik'e da goran maganin ta Mik'awa Ammie. nan Ammie ta karb'a ta Bud'e ta shafa mata a fuskarta sai da tai mata Sau uku har lokacin Afeef addu'a yake mata kafin can ta daina ihun ta fara sakin numfashi tareda ajiyar zuciya lokaci D'aya shi dai Afeef kallanta Kawai yake cikin tausayawa yadda fuskarta tai jaga jaga da hawaye,saida sukaga bacci ya d'auketa sannan Afeef ya daina mata addu'ar.Ammei ta kwantar da Huyaam nan saman gadon bayan sun gyara shi ta fara duba K'afar HUYAAM Dake d'igar jini da Hannunta take hankalinta ya K'ara tashi Ganin yadda kwalbar duk ta yanki Huyaam ta kalli Afeef tace cikin Damuwa. " Kaga fa Afeef ta yanke ko kwalbar ma ta shiga k'afar tata ne naga sai d'igar jini takeyi?..." Afeef da shima kallan k'afar Huyaam d'in yake da kuma hannun nata yace. "Bari a k'ira doc". Ammie na kallansa tace. " To Maza Dan Allah" Sai Kuma yace. "Wai dama har yanzu Bata daina wannan abun ba?.." Ammie tace cikin Damuwa "Eh! har yanzu Bata daina ba, Da ya lafa Amma naga Kwanan nan Yana yawan tashin mata".ta fad'a cikin Wani Irin sauti . Afeef ya Jin Jina kai yace. "Allah ya sawak'e". Ammie Tace. "Ameen jiki a Sanyaye so nake ma mu koma Egypt d'in tunda naga abun ya dawo". Afeef yace. "Bari na d'auko waya ta na kira doc". Ammie ta gyad'a masa kai batace komai ba harya fita daga d'akin.
Babu dad'ewa ya dawo yace. "Doc yace min gashi nan zuwa". Ammie tace. "Shikenan" daga haka afeef ya fita daga d'akin gabad'aya...bayan fitar sa Babu dad'ewa baba magajiya tai knocking k'ofar aka Bata iznin shiga, tashigo d'akin Bakinta d'auke da sallama suka ansa mata ta tsugunna ta gaida Ammie cikin girmamawa, Ammie ta ansa mata da kulawa.baba magjiya tace. "Ranki Dad'e ya Mai jiki". Ammie tana kallan ta tace. "da sauk'i". Baba magajiya tace. "Allah ya sawak'e bari naje zan dawo anjima". Ammie ta gyad'a mata daga haka ta fita daga d'akin......


___________&


*Masarautar Zazzau*

"Ko baka fahimci Abinda nake ce Maka bane eh Abdallah da yaran Hausa nake maka magana fa?..." Hajiya inna ta fad'a tana kallan Mai martaba Dake zaune a falonsa . sarki Abdallah ya d'ago Yana kallanta sai Kuma yay k'asa da murya yace. "Eh inna da sanina ya tafi school d'in kuma abunda yasa ma na barshi naji yace suna da test d'in da zasuyi 11:30am kuma Kinga yau Friday da wuri ma zasu gama 12 ma zakiga ya dawo in Sha Allah".Haka sarki Abdallah ya fad'a Yana kallan mahaifiyar tashi.
Hajiya inna tace. "Amma wallahi kaidai Abdullah bakai tunani Mai kyau ba ya za'ayi ka biye masa kawai ka Barshi ya tafi wata boko bayan kasan shekaranjiya yadda muka ga Rana haka mukaga wannan dare da yaran nan yadda yadinga ihu Yana wasu surutai tsakiyar dare badan Allah yasa duk muna kusa ba munjiyoshi da wuri da haka zai gudu cikin dare bamu sani ba". Hajiya inna ta fad'a cikin b'acin rai..


Takawa yay shiru Yana kallanta sai kuma yace. "To Yanzu dai Inna na fahimceki Amma kuma Dan Allah kiyi hak'uri tunda yanzu dai test zasuyi kuma nasan ma yanzu haka sun kusan zuwa school d'in koma sunje,saboda haka Dan Allah ki kwantar da hankalinki in Sha Allah Babu abinda ma zai sa meshi in Sha Allah tunda kullum muna addu'a sannan ba shi kad'ai ya tafi ba,harda rakiyar fadawan gidan nan Kuma kinga hakanma ai mugodewa Allah tunda har Yana iya zuwa school d'in harma ya fuskanci Abinda ake koya masan, da da baya iya zuwan fa?...". Ya fad'a Yana kallan Hajiya inna.Hajiya inna tai shiru sai muka ta sauke numfashi tace. "Gaskiya ne wannan to Allah ya K'ara masa lafiya Amma wallahi ni abinda yay daren shekaranjiya ne shiya tsoratani , Amma tunda kace haka Allah ya K'ara tsareshi ya kuma Kara musu lafiya Baki D'aya". Mai martaba yay murmushi ya ansa da Ameen ,yace.

"nima yanzu Zanyi shirin tafiya masallacin juma'a naga lokaci Yana kusantowa". Hajiya inna tace


"Eh kuma Hakane to bari Nima na koma wajen su Ayshan duk da itama dai jikin alhamdulillah".daga nan Hajiya inna taiwa Mai martaba sallama ta fita daga falon nasa gabad'aya.a k'ofa sukaci karo da shakundum zata shigo falon cikin shiga ta Alfarma Hakan yasa tai saurin matsawa baya ganin Hajiya inna zata fito daga falon tana sunkuyar da kanta k'asa tace. "Barka da wannan lokacin Mai babban d'aki".ta fad'a kanta a k'asa.hajiya inna tace. "Yauwa" atak'aice tana yin gaba.shakundum ta bita da Harara kafin ta shige cikin falon takawa..... k'arfe Sha biyu da Rabi na Ranar anty Amina ce zaune a kusa da gimbiya Aysha waya ce a hannunta vedio call suke da Gimbiya Bilkisu wacce ke tambayar ta jikin gimbiya Aysha.anty Amina tana Murmushi tace. "Da sauk'i Yaya Bilkisu bari ma na Kara mata wayar a fuskarta ki ganta ko zaki fi yarda Dani". Daga haka ta kai wayar dai dai fuskar gimbiya Aysha Dake kwance akan gadon kamar yadda take a Koda yaushe.gimbiya Bilkisu tace tana kallanta cikin sanyin murya. "Ya jiki Yaya gimbiya " lumshe ido gimbiya Aysha tai alamar

Please Login or Register in order to submit comment