Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shige D'aki Dan kwanciya. Bayan tafiyarsu itama Ammie barin falon tai bayan ta kashe kayan wutar falon gabad'aya sannan ta tafi kitchen ta had'awa Mai martaba black tea bayan ta gama ta juye a cup ta D'ora a plate ta wuce Falonsa da shi......



*Washe gari*


Tun kafin Afeef ya tashi daga baccin Daya koma bayan sallahn ASuba su Huyaam suka tafi ismaliya tahfeez bayan sun gama tambayar Ammie yayan nasu tace Yana bacci sai dai idan ya tashi ,haka nan suka tafi islamiya suna Mai kewar ganinsa.... k'arfe 11 da mintuna na safe Afeef ya sauka downstairs tashinsa kenan daga bacci wanka kawai yayi ya shirya cikin kayan sarauta Wanda sukai masa bala'in kyau Kamar ki sace sa ki gudu Dan kyau ya fito Yana gyara hannun rigarsa harya k'arasa saukowa downstairs d'in.mai aikin Ammie Dake goge goge a falon ta tsugunna har k'asa ganin fitowar Afeef d'in ta Shiga gaidashi cikin Ladabi .Batare da ya kalleta taba ya ansa mata ya K'araso tsakiyar falon.baba magajiya data fito daga dining hannunta rik'e da wata cooler zata k'arasa kitchen d'in ganin afeef yasa itama ta tsugunna ta har k'asa tace.

"Barka da safiya rankai Dad'e fatan mun tashi lafiya". Afeef ya D'an Kalleta ta gefen ido yace.

"Lafiya lau Alhamdulillah".tace .fatan ka dawo Lafiya rankai Dad'e jiya bansamu nazo mun gaisa ba."ta fad'a tana murmushi.Afeef yace. "Lafiya lau Alhamdulillah".baba magajiya tace.

"Masha Allah! nace "rankai Dad'e ko akwai abinda kake buk'ata ne ". Afeef ya D'auke kansa daga kallanta yace.

"Babu komai". Baba magajiya tace.

"To! to!! Shikenan,Amma Naga kamar yanzu ka fito zaka karya Dama an gama gyara tebirin abincin ne ko zaka k'arasa kaci ne?..."Afeef yace.

"Okay" atak'aice.baba magajiya ta mik'e ta bar wajen Bayan tai masa sallama.. Afeef ya k'arasa dining d'in ya ja kujera ya zauna,bayan ya gama yin breakfast d'in Wanda bama na kirki yayi ba ya goge bakinsa da tissue sannan ya d'auki wayoyinsa ya wuce b'angaren Ammie... Ammie na zaune Bakin gado tana ware Tsaraban da Afeef yayo musu zata aikawa da mutanan gidan kowacce nata dana yaransu akai knocking d'in k'ofar.ta juya tana kallon k'ofar sai Kuma tace.

"Waye?.."muryar Afeef taji Hakan yasa tace ya shigo .da sallama abakinsa ya turo k'ofar d'akin ya shigo kansa a k'asa sai Wani baza k'amshi yakeyi har ya k'arasa cikin d'akin ya zauna kan kujerar Dake d'akin.ya Kalli Ammie yace cikin cool voice dinsa.

"Barka da  
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~wannan lokaci". Ammie ta kalleshi tace.

"Barka ka tashi Kenan ya gajiya".yace.

"Lafiya lau Alhamdulillah". Ammie tace.

"Masha Allah! Sai Kuma tace.

"Yanzu Ina zaka?..."yace.

"Zance fadane wajen Mai martaba yace naje na sameshi acan a kwai inda zamu anjima da kad'an". Ammie ta Jin jina kai tace.

"To idan Kun dawo Koda da daddare ne ka k'arasa kaje ka gaida matan gidan karsu fara yad'a mun da magana"ta fad'a tana kallansa . kallan Ammie Afeef yayi azuciyarsa yace wai maiyasa Ammie take gudun maganar matan masarautar nan ne indai magana ce sun jima basuyi ba, kamar zaiyi magana sai Kuma ya fasa yana kallanta yace.

"In Sha Allah! Zanje".Ammie tace.

"To Shikenan Allah yay Maka albarka sai Kun dawo d'in". Tana fad'ar haka Afeef ya mik'e yay wa Ammie sallama sannan ya fita daga d'akin bayan ya kullo mata k'ofar.Ammie ta Sauke numfashi ta d'auke idonta daga kallan k'ofar ta cigaba da abinda takeyi.....



____________&


K'arfe biyar Saura na yamman Ranar Hajiya Lubabatu ce Zaune a d'akin da suka Saba zama ita da fulani Salamatu.. Hajiya Lubabatu tai k'asa da murya tace.

"Oh!! wai kina nufin kema Daya dawo tun jiyan Amma baizo ya gaida keba?..."ta fad'a cikin alhini.. Fulani Salamatu tace Cikin fushi da b'acin Rai.

"hmmm! Lubabatu kenan Ina zaizo ai yanzu wuyansa ya isa yankan da Yana ganin yakai Wani matsayi,ai yanzu Bai d'auke ni amatsayin matar ubansa ba sai dai amatsayin abokiyar kishinsa,kamar yadda uwarsa ta d'auke ni". ta fad'a tana Wani Irin hucin b'acin rai .Hajiya Lubabatu tace.

"Uhmm Tab' > d'ijan Amma wallahi fulani Maryam bata kyauta ba ai ko shi Afeef d'in baizo Dan kansa ba, ita ai ta sashi yazo ya gaida ke ko Dan kina a matsayin matar ubansa ma? Abarshi ma mu ba dolensa bane yazo ya gaida mu tunda mu a amatsayin matan k'annin Mai martaba muke Amma ke dai dolensa ce tunda mahaifinsa Mai martaba kike AURE. bama iya wannan ba Karya manta kece fa hasken idaniyar masarautar kano".... ta fad'a cikin zuga.Fulani Salamatu tace.


"Hmm! ina zan zama dolensa tunda Yana da uwa aini ba dolensa bace ba Lubabatu kima daina fad'ar haka ,da ace iyayensa sun nuna masa Ina da mutunci a idonsa da tuni yazo ya gaida ni kina fa ganin Mai martaba dayazo d'azu koya tambayeni Yace min Afeef d'in yazo gaidani Bai fad'a haka ba, Kinga ko Shima Ina zai ganni da mutunci tunda ba'a nuna masa Ina da mutunci ba?...". Hajiya Lubabatu ta rik'e baki tace.

"Tab' d'ijan Amma lallai fulani Maryam ta cika marar mutunci". fulani Salamatu tace. "Hmmm ". Amma batace komai ba ranta na cigaba da tafar fasa.... Hajiya Lubabatu ta sauke numfashi tace. "Allah ya kyauta". Kamar wacce ta tuno da Abu tace.

"Yauwa! Kinga abinda nakeson fad'a mikin ma tun d'azu sai yanzu yazo min,nace ba,D'azu dai sai ga hadiman fulani Maryam su biyu ta Aiko su kawowa su ikleema kayan Tsaraba mu Kuma gold da less guda biyu kema an kawo mikin koh?..."ta fad'a da sigar tambaya. fulani Salamatu tab'e Baki tace.


"Nima Ankawo min d'azu , wallahi da har zance da wacce ta kawo d'in ta Maida mata sai kuma kawai na Karb'a kar ta k'ara had'ani da Mai martaba yazo Yana min k'ana nun maganganu ,sai Kuma Wani tunanin ma ya K'ara zuwamin nace nida dukiyar 'ya'yana anje an sakar masa ita yana can ya mamaye mana Yana facaka da kud'i yadda ransa yakeso ai dole ya iyo wannan uwar siyayyar ta kaya masu bala'in tsadar gaske Dan wallahi iya kayan da aka kawowa su Aziza yafi million biyar bare kuma namu".


Hajiya Lubabatu ta gyara zamanta tace.

"ai gara ma da Baki Maida ba yo muma kanmu kayan yafi na million biyar d'in tunda duka iri D'aya yake mana.to muma ya kashe mana wannan uban kud'in Ina Kuma ga 'yan uwansa da uwarsa ai sai dai zancen million goma sha". Fulani Salamatu tai Wani murmushi tace .

"Hmmm! Ai bazai tab'a dai dai tamu da uwarsa ba Lubabatu dole abinda zai mata sai yafi namu shiyasa nace Ramla ta b'angaren mechanic engineering zata Karanta Dan wannan hanyar ce kad'ai zaisa muma dukiyar Mai martaba ta shigo Hannunmu Kinga dole ya Bata taja ragamar D'aya daga cikin companynsa ". Hajiya Lubabatu tace . "Wannan ma yayi Fulani Allah yasa ya amince". Fulani Salamatu tai mata Wani kallo tace .

"Kema kinsan dole ya Bata tunda abinda ta Karanta kenan". Hajiya Lubabatu tace.

"Wannan haka yake Allah yasa to danni ma babban burina ace kema yau 'ya'yanki suna juya dukiyar Mai martaba yadda ransu yakeso". Fulani Salamatu tace .


"Hmmm kijira lokacin kawai k'awata". Hajiya Lubabatu tace .

"Allah koh? Aiko Muna nan muna jira,aini yanzu tunda ya dawo so nake salima ta fara jan hankalinsa zuwa kanta,so nake sai ya huta Kona Kwana hud'u ne tukunna sai na fara tura Salima tana zuwa b'angarensu da duk inda tasan Yana zama Dan so nake ana gama bikin su bahijja sai nasu". Fulani Salamatu ta sauke numfashi tace.


"Hakanma yayi".daga haka Bat'a K'ara cewa komai ba. Hajiya Lubabatu ta Kara k'asa da murya tace.

"Yauwa ban fad'a miki ba Kinsan d'azu Aziz ya shigo yake cemin Mai martaba sun fita shida Afeef?nace wato daga dawowar tasa har za'a fara fita dashi duk inda Mai martaban zashi kenan".ta fad'a cikin b'acin Rai ita adole tana Taya Fulani Salamatu kishin abinda ake mata. Fulani Salamatu tai saurin kallanta bakinta na karkarwa tace.


"Fita Sukayi tare kuma? Dama d'azu da Mai martaba yazo yamin sallama tare da Afeef d'in zasu fita". Hajiya Lubabatu tace .


"Gashi dai har za'a D'ora daga inda aka Tsaya daga dawowar tasa ba". fulani Salamatu tai shiru tama kasa magana sai kuma can taja dogon numfashi tace.


"Wallahi Lubabatu bazan tab'a zuba Ido ana mun abinda aka ga dama acikin gidan nan ba wallahi sai na kawo k'arshen wannan abun".hajiya Lubabatu tace.


"Dadai yafi kan danni ma abun Yana damuna wallahi ace daga dawowar sa har an fara fita dashi komai ace shi".fulani Salamatu tai shiru ta zubawa waje D'aya ido k'irjinta sai sama da k'asa yake saboda b'acin Rai, Hajiya Lubabatu sai kallan k'asa k'asa take mata tana Wani Irin murmushi a cikin zuciyata sai Kuma ta kalli time ganin k'arfe shida Saura yasa tai k'asa da murya tace cikin lallashi.

"Ki kwantar da hankalinki fulani ni Ban fad'a miki wannan maganar danki ta-da hankalinki ba iya ka kawai dai Dan ki d'auki mataki daga daga abinda ake miki Kinji?..." Ta fad'a tana tab'a fulani Salamatu...fulani yaran ta d'ago da idonta ta kakketa batace komai ba Hakan Hajiya Lubabatu ta Mik'e tai wa Fulani Salamatu sallama tabar part d'in ta koma nasu Ranta fess...



Bayan sallan Isha'i su ikleema ne zauna a falon Ammie ita da safnah sunzo yiwa Afeef barka da zuwa da Kuma godiyar kayan daya siya Musu Amma Banda Aziza Daman Babu Wanda yasaka ran zata zo ta dan jiya basu samu sunzo ba.hira kawai suke a falon ganin Afeef d'in Bai dawo daga masallacinba.daga Huyaam sai Huda ne kawai a falon sai su ikleema Dake zaman jiran shigowar Afeef d'in.muryarsuce kawai take tashi a falon suna hira...shiko Afeef Bai shigo b'angaren nasu ba sai wajen k'arfe 9 saura na daren Dan Saida ya fara Zuwa ya gaida Matan gidan kamar yadda Ammie ta fad'a sannan ya shigo b'angaren nasu . sallamar da akayi da Kuma Muryar wanda sukaji yasa sukai shiru suka juya suna kallansa sai kuma suka Ansa masa sallamar suna sunkuyar da kansu k'asa.kallo D'aya Afeef Yay musu ya d'auke kansa a zuciyar sa yace wato yaran nan suna nan haryanzu da halinsu baza su sauya ba, k'arasa shigowa falon yay har ya wuce su sukai saurin had'a baki wajen cewa. " sannu da zuwa yaya". Batare da ya juyo ba ya ansa musu sai saikuma su safna sukace ". barka da dawowa Yaya munga tsaraba mun gode Sosai Allah ya K'ara girma".suka fad'a cikin Jin Dad'in abinda yay musun.sai alokacin ya juyo Yana kallansu Babu Wanda ya iya kallansa yace cikin deep voice d'insa.

"Thank you".daga haka ya haura sama zuwa b'angarensa.ikleema ta sauke numfashin da take ta rik'ewa tace .


"Wai!! kinsan Allah d'aukata zai mana fad'a daya shigo ya tadda mu muna surutu?.....". safna tace .

"Wallahi Nima haka d'aukata zamu Sha fad'a". Huyaam ta hararesu tace.

"To Tunda ya bar falon ikleema k'arasa mana labarin?...."ikleema ta zaro ido waje tace.

"A'a banshirya jikina yayi tsami ba HUYAAM yanzu kina ganin fa ya dawo Amma kice Acigaba da labarin?..." ta kalli safnah tace.


"Tashi mu tafi tunda mun Mai Sannu da zuwa kar Kuma jikinmu yayi tsami". safna ta mik'e tace.

"Aikuwa dai Muje". Huyaam tace.

"Haba kukuwa Dan Allah ku dawo zauna mana Babu abinda zai muku wallahi". ikleema ta rik'e baki tace.

"Ke wallahi bazamu zauna ba kija mana fad'a ko Kuma duka barema dare yayi ma Had'u gobe na k'arasa muku labarin".daga haka ta kama hannun safna sukai hanyar k'ofar fita daga falon.Huda ta bisu tace.
Muje in taka muku zuwa k'ofa"ikleema tace.


"A'a barshi mun gode"Huda tai murmushi tace.

"Matso rata kawai". sai Kuma ta dawo falon tana kallan Huyaam tace.

"Tashi muma mu wuce d'aki ko zaki jira yayanne?..."Huyaam ta mik'e tana tab'e Baki tace .

"A'a ma Had'u gobe Dan wallahi bacci Nima nake ji".daga haka tabi bayan Huda suka haura sama......




#<9 HUYAAM
#<9 LAMID'O
#<9 AZIZ CHIROMA
#<9 AFEEF





*Muje zuwa mutanan MRS SARAKIES =؋.ke daga Jin salon labarin kinsan zai k'ayatar ya Kuma fad'akar.akwai chakwakiya sosai anan gaba Dan labarin ma yanzu muka fara shi*.


*ga masu buk'atar fara payments zaku iya sa kud'inku a yanzu before mu gama free pages Regular group akan naira 500 kacal idan kuma muka gama Free pages zai koma 700 ne.ga masu buk'atar Vip Kuma 2 pages a Rana zaku iya biyan nai 1000 kacal. ku hanzarta ku fara biya tun kafin mu gama free pages.zaku iya tura kud'in ta wannan account d'in =G*


2270127432 Naja'atu umar
Zenith bank

Evidence of payment (shaidar biya )via
07066508376

Da zarar mungama free pages Kuma zamu sa duk Wanda ya biya kud'in sa a paid group, karku bari ayi wannan tafiyar Babu ku =؃=؃ mutanan arziki.





07066508376________
'Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD



*<9 HUYAAM <9*



*NA*


*__NAJA'ATU UMAR FAROOQ __*


*__(MRS SARAKIES =؋)__*



PAGE 2 0



*Tallah! Tallah!! Tallah!!!*


*Ina kuke hajiyoyin gidan nan,nace Ina kuke hajiyoyin gidan nan?to maza ku matso ga wata garab'asa ta zomu har inda kuke=؃=؃?.*


*Hajiya kaya Kikeso na fita kunya cikin taro ku Kuma so kike kallo ya koma akanki acikin Taron mata idan kika shiga biki ko suna ko Kuma Wani taro na musamman.to maza idan kina so ki kankarowa kanki mutunci kizo UK collection and gallery mu gwan gwajeki da kayanmu masu quality Wanda zaki gaji ki ajiye Dan kanki Amma badai ya mutuba Muna sai da kaya kamar haka=G*


*Atamfofi da lesses*
*Abaya*
*Shadda*
*Hand bag*
*Shoe*
*Veil na manya Dana Yara*

*Socks rin hands made d'in nan masu net*.

*Hula ta 'yan Gayu*

*Siyan D'aya ko sari*

*Duk zaki samu kan Farashi Mai sauki kedai ki garzayo UK collection & gallery Kisha Mamaki*

*Domin ganawa damu ko magana damu kai tsaye ku tun tub'emu kai tsaye ta wannan number kamar haka*=I08135305790

*Sai mun jiku =؃=؃=؃*


<9<9<9<9<9<9


*Bismillahirrahmanirrahim*


__________&



*Bayan Kwana biyu*


Da safiyar ranar tun K'arfe bakwai da Rabi su muneeb suka tafi school,ya Zarah ma k'arfe Tara Saura ta tafi school d'in Dan suna da lecture na k'arfe 9am.sai ya Haidar da shima ya fita wajen nasa aikin Hakan yasa Babu kowa a gidan ya rage daga Huyaam sai Huda .sukan suna gidan tunda babu inda zasu sunyi candy suna zaman jiran results sai anjima da yamma Kuma su tafi islamiya.yanzu haka k'arfe goma da mintuna ne na safe Amma har lokacin HUYAAM Bata tashi daga baccin ba tun bayan da tai sallahn ASuba data koma bata tashi ba.har Huda ta tashi ta barta Dan ita tunk'arfe 9 ta tashi tai wanka ta shirya har tai breakfast yanzu haka tana zaune a falon downstairs wajen k'arfe goma da mintuna tana kallo Tayi nisa a kallon series film d'in da take kallo taji motsin foots step daga b'angaren mazan gidan nasu ta juyar da kanta tana kallan direction d'in da take Jin foots step d'in.yayan nasu ta gani yana saukowa Hakan yasa tai saurin d'auke kanta daga kallansa ta Maida kan TV harya k'arasa saukowa downstairs d'in.ganin zai gif tata zaiyi hanyar dining yasa tai saurin cewa.


"barka da safiya yaya". Ta fad'a cikin ladabi.batareda Afeef ya juyo ba bare ya kalleta ba ya ansa mata .ya k'arasa dining d'in yaja kujera ya zauna Yana zube wayoyinsa kan table d'in. Ammie ce ta sauko downstairs d'in cikin shiga ta Alfarma ta k'araso falon tana kallan Huda tace.

"Ina HUYAAM d'in? badai har yanzu Bata tashi daga baccin ba?...." Ta fad'a tana kallan Huda. Afeef Dake dining Yana cin abinci ya d'ago da kansa ya Kalli Ammie Jin abinda take fad'a sai Kuma ya Maida kansa ya cigaba da cin abincin.Huda ta juya tana kallon Ammie tace .

"Eh Bata tashi ba".ta fad'a tana kallan Ammie. Ammie ta sauke numfashi tace .

"Ya Allah! Ni kan bansan ya Zanyi da yarinyar nan ba Agidan nan akan k'in yin breakfast da wuriba, ni damuwa ta D'aya kartai ta bacci kuma Bata ci abinci ba banason Wani ciwon ya kamata ta". Sai Kuma ta kalli Huda tace. "Jeki taso ta maza yanzu".Babu musu Huda ta Mik'e Afeef ya bita da kallon gefen ido azuciyarsa yace wato yarinyar nan har yanzu Bata daina wannan baccin nata ba kenan ya lura tunda yazo gidan nan kullum haka ake fama da ita.tuna ninsa ya katse ne lokacin da Ammie ta kalle shi tace.

"Ka fito kenan?...." Sai a lokacinYa d'ogo ya kalli Ammie da sexy eyes d'insa ya gyad'a mata kai kamar Wani k'aramin yaro Hakan yasa Ammie tace.

"Aishikenan" sai Kuma tace. " k'arfe nawa yau d'in zaku fitan". yace.

"k'arfe shad'aya ne in Sha Allah". Ammie ta Jin jina kai tace. "Allah ya kaimu, Kai wannan bama hutu kazo ka aiki kazo Yi ai".yay murmushin da Bai shirya ba Wanda yay masa bala'in kyau Amma baice komai ba.huda ce ta dawo falon tana kallan Ammie tace.

"Na tashe ta tak'i tashi Ammie".ta fad'a tana kamae Zatai kuka... Ammie ta sauke numfashi tace.

"Bata tashi ba da kika ce Huda? Na rasa ya Zanyi da Huyaam akan wannan baccin nata a gidan nan ni damuwata ma shine ta tashi taci abincin kar ulcer ta kama mun ita, badan haka ba tai ta baccin har sai ta ga dama ta tashi". Afeef dai Yana jinsu baiyi magana ba Ammie ta kalli Huda tace.


"Wai Huda Bakice mata nice na Aiko kiba? kema fa nasan halinki Huda zuwa zakiyi kiyi mata ta k'arfi ita Kuma ta biye miki tak'i tashi". Huda tace .


"Wallalhi Ammie babu abinda nai mata zuwa nai kawai na tashe ta nace kince ta tashi baccin ya Isa haka". Ammie ta sauke numfashi tace.


"To ki koma yanzu kice nace lallai lallai ta tashi tun Kafin na shigo da kaina na sameta".Huda tace. "to" har tai gaba Afeef da yake cin abincin sa batare da ya d'ogo ba yace cikin husky voice.

"Kije kice ta tashi injini".ya fad'a Yana cigaba da cin abincinsa kamar bashi ne yay maganar ba.huda ta juya ta haura stairs bayan ta ansa masa da to...Koda Huda ta shiga d'akin HUYAAM har lokacin tana a yadda ta barta tana kwance cikin lallausan blanket d'in ta,ta lullub'e duka jikinta dashi sai sauke numfashi take a hankali tana baccinta cikin kwanciyar hankali.Huda ta haura saman gadon ta d'age bangon tana kallan Huyaam tasa hannu ta fara Tashinta Huyaam tai juyi ta Bud'e idonta kad'an, sukai Ido hud'u da Huda ta yamutsa fuska tace .

"Wai ke Dan Allah meye hakan ke idan Baki katse mini bacci ba arayuwar ki bakyajin Dadi wai?...." Ta fad'a tana Wani tura Baki gaba.huda ta sauka daga saman gadon ganin ta tashi tace.

"Bani d'in bace da kika Raina Yaya ne yace ataso ki ko Kuma yazo da kansa". Ai Jin haka yasa Huyaam tai saurin mik'ewa zaune tun Kafin Huda ta k'arasa kaiwa zancen,ta sauko daga saman gadon tana zare ido tace .

"Dan Allah fa da Gaske kike ko Kuma wasa?..." Huda na gimtse dariyarta tace .

"Wallahi da Gaske nake ko kin d'auka wasa nakeyi". HUYAAM ta d'auki hularta tasa ta kalli Huda kamar zatai kuka tace.

"Dan Allah kice masa na tashi yanzu zan fito". tana fad'ar haka tai hanyar toilet ta shige ta kullo k'ofar.Huda tai murmushi tana cewa ga tsoro kuma ga tsiwa ta fice daga d'akin ta Sauka downstairs ta tarar da har Afeef d'in ya fita ta samu Ammie Zaune kan kujera ta k'arasa wajen ta tace.

"Ammie ta tashi, Ina kuma yayan yake?..." Ammie tace. "Yanzu ya fita".Huda ta sauke numfashi ta koma wurin zamanta ta zauna.


K'arfe uku Saura na Rana, Hajiya Lubabatu ce tare da Salima Wacce suke zauna a d'akinta saman kujerar Dake a d'akin tana kallan salima tai k'asa da murya tace.

"Salima Abinda yasa na k'iraki Nan ba Wani abun bane ba illa kisan yadda zakiyi kijawo hankalin Afeef zuwa kanki ya zamto Babu wacce yakeso sai ke Nima zan tayaki ta bayan fage idan Allah yaso ya yarda,Dan san samu na ace ana gama bikin su Bahijja zan cen naku za'a fara".ta fad'a tana kallan yanayin salima...Salima ta sauke numfashin farin ciki Dan d'aukar ta wata maganar hajiya Lubabatu zatai mata ba wannan ba tace cikin farin ciki. "Wallahi mama kamar kinsan abinda yake Raina kenan inason Yaya Afeef so bana wasa ba Amma wallahi Bai tab'a yimin k'wakwk'waran Kallo ba Dan kwata kwata tunda yadawo gidan nan wallahi sau D'aya na ganshi Shima daga nesa ne lokacin sun dawo tare da Mai martaba Kuma duk lokacin Danaje sashensu sai na tadda baya Nan jiyama a islamiya Dana tambayi Zarah cewa bana ganin ya Afeef tace mun ai baya zama kullum suna fita tareda da Mai martaba ne Kuma idan suka fitan sai Dare suke dawowa". Ta fad'a kamar zatai kuka .Hajiya Lubabatu ta gyara zamanta ta k'ara tai k'asa da murya tace.


"Eh nasan da wannan, sannan ke Kuma meye damuwarki da Wani kallo Kinga indai akan wannan ne karki Wani damu Dan Baya kallanki tunda ba ke kad'ai yeke yiwa haka ba .Kuma shi namiji D'an lallab'awa ne saboda haka mu bishi a hankali da sannu komai zai dai dai ta karki Wani ta-da hankalinki akan Hakan, sannan batun Kuma baya zaman gidan nan duk Mai sauk'i ne tunda idan suka fitan ba kwana suke ba duk mun dare suna dawowa gidan ai da sauk'i".salima dai kallanta Kawai takeyi Sai kuma ta k'ara gyara zama tai k'asa da murya tace.


"kina jina bari nai miki wata dabara Mai zai Hana kije sashen nasu da daddare na tabbatar lokacin duk inda yake ya dawo Tunda ai ance da daddare yake dawowa ko?..." Salima ta gyad'a mata kai.hajiya lubabatu ta k'ara gyara zama tace .

"To abinda nake so Dake shine idan kiga je b'angaren nasu ko an tambayeki mai ya kawoki kice kinzo gaida shine,sannan Kuma Zaki Mai godiyar tsarabar Daya kawo muku...." Ta fad'a tana kallan Salima. Salima tai Jimm sai Kuma tace.

"Amma mama kinsan fa ko mutum yaje baya Wani bashi attention d'insa idan kai Sa'a nema ya ansa gaisawar ka".ta fad'a kamar zatai kuka. Hajiya Lubabatu ta Bat'a Rai sai Kuma tai k'asa da murya tace.

"Yo ke in Banda abunki Salima Ina ruwanki da Wani Shan k'amshinsa indai keda kike nema aiko hantararki Yaya ki jure wata Rana sai labari labarin ma baza'a jiba, kuma zaki ce nina fad'a miki, kinsan Allah Salima da kansa zai sauko kedai kawai abinda nake so Dake shine ki bishi a hankali mudai burinmimu shine ya soki kuma ya aureki shikenan wata Rana sai kinyi mamakinsa zakice na fad'a miki" ta fad'a tana sakin fuskarta.salima ta rausayar da kai tace.

"shikenan mama Allah yasa, anjima da daddaren naje ni". Hajiya Lubabatu tace. "Yauwa ko kefa kiyi kwalliya tajan hankali kije ki sashen nasu". Salima tace "to" sallamar da sukaji da Muryar wanda sukaji yasa Hajiya Lubabatu cewa. "Tashi muje Aziz ne karya fara NEMA na.daga haka duk suka mik'e Salima ta fita daga d'akin Hajiya Lubabatu tabi bayanta......


___________&



Da yamma bayan sallahn magrib Aziz chiroma ne tsaye a Wani k'aton mall Yazo yin siyayya Yana tsaye gaban wasu rings na gold masu bala'in kyau da tsada sai Wani walwalin haske sukeyi ya d'auki Wani Mai Dan Karan kyau Wanda yake ganin zaiyiwa Huyaam kyau ya d'auka mata dai dai size d'inta duk da ba sani yayi ba gassing kawai yayi sannan Kuma ya d'aukawa Huda ma irinsa Amma design d'in ko wanne daban sannan ya bar wajen ya k'arasa wajen dogayen riguna nan ma ya d'aukar musu guda biyu iri D'aya ita da Huda sai Kuma ya d'aukarwa su Ikleema ma da safna da Aziza dukansu kowa set D'aya sannan ya bar wajen ya k'arasa inda ake saida chocolates nan ma ya d'aukar musu package package kala kala masu bala'in tsada da Dad'i sannan ya bar wajen ya k'ara wajen payments bayan ya gama duk abinda zai Siya... fitowa yayi daga cikin Mall d'in gabad'aya D'aya daga cikin workers d'insu ne ya rakoshi da kayan daya siya d'in ,boot d'in motar ya Bud'e mutumin ya zube masa kayan aciki sannan ya rufe ya sallameshi ya karasa ya Bud'e driver seat ya shiga ya ta-da motar ya bar wajen direct Wajen Wani abokinsa ya tafi dayake ta doka masa K'iran tun d'azu......


Wajen k'arfe 9 saura na dare gama yin dinnersu Kenan suna Zaune a falon k'asa Huyaam na mak'ale kusa da ya Zarah wacce ke nuna mata abuba wayarta Huda Kuma tana nunawa muneefa yadda zatai homework d'in da aka Basu a school,Ammie Kuma tana d'akinta Bata Dad'e da Shiga ba taje yin abune .sallamar

Please Login or Register in order to submit comment