Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da lumfashinta saboda azaba lokaci D'aya ta saki hannun muneefa at the same time Kuma taji kamar an jawo ta ta baya, tai taga taga zata Fad'i kiris ya rage taje k'asa ya Zarah Dake bayan tai saurin tareta tana kallan tace cikin Damuwa. "Me ya faru Huyaam?..."Amma Ina Huyaam Bata jinta saboda yadda aka shak'e mata wuyanta ga idonuwanta dukan sun fir fito waje sai Kowa take da numfashinta.take ya Zarah ta rikice ta fara K'iran sunan HUYAAM cikin kid'imewa .wannan abinda Huyaam take yasa muneefa tasa ihu ganin Huyaam tana rik'e da wuyanta gashi ta kasa magana lokaci D'aya zufa ya keto mata .Huda da har ta k'arasa wajen motar ta juyo ihun muneefa Haka nan ta dawo wajensu da sauri cikin tashin hankalin abinda ta Gani ta fara tambayar ya Zarah da Mai ya faru? Ya zarah bata samu damar ansawa Huda tambayar taba saboda itama kanta a rikicen take da lamarin Huyaam.Su ikleema da safna suka k'araso suma gunsu da sauri suna tambayar lafiya? ya Zarah ta Kalli Huda cikin tashin hankali tace. "kamata mu kaita gida". Cikin sauri Huda ta kamata suka su nufi b'angarensu, ikleema kasa binsu tai hakama safna suka tsaya suka bi su ya Zarah da kallo saboda Suma kansu sun tsorata da lamarin Huyaam d'in. Salima ce ta k'araso gurin ganin su ikleema tsaye sunyi carko carko tace. " Ku Kuma me kuke jira anan da Kuka Wani ja kuka tsaya Baku shiga motar ba?ku taho mu tafi time na tafiya". Ta fad'a tana k'ok'arin k'arasa wajen motar.jiki a Sanyaye Ikleema tace. "Ya salima su ya Zarah muke jira". Salima tace cikin har zuk'a. " Wai dama Basu fito ba gashi lokaci sai tafiya yakeyi?".safna tace. ".sun fito Huyaam ce Babu lafiya shine suka tafi su kaita gida". Salima ta tab'e Baki tace. "Allah ya sawak'e to mudai ku taho a kaimu in yaso a dawo a d'aukesun daga baya Dan lokaci Yana tafiya, kuma ma ba musan Wani lokacin zasu d'auka kafin su fito ba".. Aziza tai gaba ta shiga motar tana cewa gaskiya dai ya Salima gara dai mu akaimun.ikleema tace. "A'a ya Salima Baza mu tafi ba mudai jira sun tukunna"..salima ta harareta tace. "Sai dai ke ki jira sun Amma ba Salima ba". Ta kalli driver tace. Kaga muje mu ka kaimu Dan time na tafiya".dogarin Dake musu rakiya ya duk'ar da kansa k'asa yace cikin girmamawa. "Ranki Dad'e da ki d'anyi hak'uri mu jira sun dai koh? ko Kuma Wani yaje ya gano mana halin da take ciki, Amma kimin afuwa idan na Fad'i ba dai dai ba". Ya fad'a Yana risinar da kansa k'asa.Salima ta wulla masa Harara tace a fusace."da kai nake da zaka Sako mun wannan k'azamin bakin naka ina magana?.naga da Wanda zai tuk'amun nake". Mutumin ya d'ago Ya kallate da mamakin abinda ta fad'a masa Dan wallahi ya kusan haifarta idan Bai haife taba. " Sai Kuma ya sauke idonsa k'asa yace. "Kiyi hak'uri Ranki dade". Salima ta sake wulla masa Harara sannan taja tsaki.sai Kuma ta kalli driver dashima yay shiru ya kama kansa tace. "Kai kuma inai Maka magana bakai magana ba kai shiru kamar gunki ko kaima kai mun ne baza kai ba? Idan kaima baza ka kaimun ba sai ka fad'a min". Ta fad'a cike da gadara.Driver ya girgiza kai yace. "Ba haka bane ranki Dad'e Amma da kin bari dai munga zuwa anjima idan Basu fito ba sai mu kaikun Dan kada Muyi laifi".mamaki ya kama salima Jin yadda suke mata gaddama gabad'ayansu.Sai Kuma can tace cikin takaici". Wai har ni Ina fad'a Maka Abu kana fad'amin yadda za'ayi".ya duk'ar da kansa yace cikin ladabi. "Kiyi hak'uri Ranki Dad'e"
Salima tai tsaki tace. "To ka wuce mu tafi idan ba so kake ranku ya B'aci ba". Babu musu driver ya zaga sai shiga driver seat saiga ya zalaihat nan ta k'araso wajen Dan itama hadda ita za'a tafi islamiyar. ya Bahijja ce dai dama tunda aka kawo lefanta tace Bazata Kar'a zuwa islamiya ba.ya zulaihat tana kallonsu D'aya bayan D'aya Ganin yadda suke tsaye har lokacin Basu tafi ba iya K'annen su k'ana nun ne kawai ke cikin motar sai Aziza tace."au Ashe ma Baku tafi ba? ni har nake cewa na makara nasan ma Kun tafi k'ila sai dai idan ankai ku a dawo a kaini". Ta fad'a tana kallan su.salima tai saurin cewa yanzu za'a kaimu wai kinsan Huyaam ce Bata da lafiya bayan har sunzo nan shine wai sai mun jira sun dawo saimu tafi ga lokaci sai k'urewa yakeyi shine ni Kuma nace kawai mu tafi a dawo a d'aukesu daga baya, shine fa wai wad'an nan 'yan rainin hankali bayin sukace wai lallai sai dai mun jirasu". Ta fad'a tana wani hararar dogarin da driver da suke tsaye har lokacin.mamaki ya kama ya zulaihat ganin Wad'an da Salima kewa Rashin kunya ita d'aukar tama Koda su safnah take ashe wai da Wad'an nan dattijan take haushi ya kama ya zulaihat ganin yadda suma suka d'ago suna kallon Salima yadda ta ci musu fuska. ya zulaihat ta rasa me zata ce mata kawai ta wanke salima da Wani gigitaccen Mari tana nunata da yatsa tace. "Yanzu Salima wad'annan bayin Allah kike yiwa Rashin kunya basu haife kiba?". Ta fad'a cikin fad'a da b'acin Rai.Salima ta rik'e Kuncinta Jin yadda zafi ya ratsata tana kallan ya zulaihat da mamaki Amma Kuma ta kasa magana sai hawaye daya fara zubo mata Koda wasa batai gigin yin Magana ba Saboda tasan halin ya zulaihat Bata d'aukar wasa ko kad'an Dan ko acikin k'awayenta tane ko Bahijja da suke Sa'aninta Bata shiga sabagarsu sosai bare Kuma Salima.salima tai shiru hawaye na wanke mata fuska ya Zulaihat tace. "Badai Rashin kunya ma kika musu da bana nan ba?.Salima tai shiru Bak'in ciki ya isheta ganin yadda ya zulaihat ta Disga ta agaban bayin gidan, Bak'in ciki ne ya cikata ga zafin Marin da akai mata ga Kuma na zubar Mata da mutunci da ya zulaihat tai.kallan driver da dogarain kawai Salima take domin su kansu taga mamakin abinda aka mata a fuskokinsu.dogarin ne ya Kalli ya zulaihat yace cikin girmamawa. "Ranki Dad'e kiyi hak'uri ki Rabu da ita". ya zulaihat ta kalleshi tace. "Ku zata bawa hak'uri". Ta juya ta kalli Salima data sunkuyar da kanta k'asa tace. "ki Basu hakuri Kafin ranki ya B'aci". Salima na tura Baki gaba da k'yar ta iya Basu hak'uri tana k'unk'uni.ya zulaihat tai tsaki tace. "Kuma kisa aranki sai mun jira sun idan Basu fito ba na lek'a Nagano lafiyar Huyaam d'in sai dai ki mutu". Tana fad'ar haka fara duba wayar Dake vibrate a Cikin jakar ta .salima ta bar wajen fuuu ta shige motar tana k'unk'uni.Sudai su ikleema sun nutsu suna godewa Allah da ya zulaihat d'in tazo wajen Dan Suma basa so su tafi ba ba susan halin da Huyaam d'in take ciki ba......



__________&


Lokacin da aka shigar da Huyaam main falon b'angaren nasu.Ammie tana kitchen tana bawa baba magajiya umarnin abinda za'a dafa for dinner. kawai taji yadda su Huda ke k'wala mata k'ira daga nan falon. take gabanta ya yanke ya Fad'i Dan tasan wannan K'iran bana lafiya bane ba . barin abinda takeyi tayi ta fito.tana fitowa idonta babu a inda ya sauka sai akan Huyaam Dake jikin ya zarah da Huda sai faman kokawa da numfashinta take at the same time idanuwanta kuma duk suka firfito waje.cikin sauri Ammie ta k'araso wajen nasu ta rik'o HUYAAM zuwa jikinta tana kallanta cikin sanyin jiki tama rasa Mai zata fara at the same time Kuma tana tambayar su meya sameta? ya Zarah ce ta fad'a mata abinda ta Gani itama nan hankalin Ammie ya tashi ta kai zaune kan kujera tareda Huyaam ta cire mata hijab d'in jikinta Huda ta d'auko mafici ta fara yiwa HUYAAM fifita ganin yadda take gumi duk da AC da fan d'in Dake falon . Ammie taga Huyaam ta rik'e wuyanta idanuwan nata sai Kara fitowa waje sukeyi,tana ta juye juye ajikin Ammie.zuba Mata ido kawai Ammie tai Dan a farko Ammie ta d'auka wata diagnosis d'ince ta kama Huyaam sai Kuma yanzu taga Hannunta sun dunk'ule waje D'aya ta dunk'ule su da k'arfi sai k'afarta Kuma data lank'washe,to anan ta gano cewa ciwon na tane ya K'ara tashi.take ta fara tofa mata addu'o'in da duk suka so bakinta daga k'arshe Kuma kawai sai ta kai bakinta saitin kunnen Huyaam ta fara karanto mata ayoyin Al'qur'ani cikin suratul Bak'ara shafi na goma sha biyar aya ta D'ari da D'aya (101) wato shafin wattaba'u ma tatlushshai d'inu Ala mulki sulaiman .anan Huyaam ta saki hannunta Dake wuyanta sannan ta fara war ware su tana ture bakin Ammie Dake kunnenta da duka k'arfinta Duk da haka Ammie Bata fasa abinda take ba ganin karatun na ratsata. Ganin fa Ammie da Gaske take k'ona sun take Yi yasa Huyaam ta fara Wani Irin ihu tana Kuka tana cewa ya isa zasu tafi.. Amma Ina Ammie Bata fasa ba Saida tai musu kaca kaca ta K'ona su sannan ta k'yalesu ganin sun gudu .take Kuma taga Huyaam d'in taja Wani rin numfashi jikinta ya saki Ammie ta kwantar ta saman carpet d'in Dake malale a tsakiyar falon ganin bacci ya d'auke Huyaam d'in yasa Ammie ta sauke numfashi tana cewa.

"Alhamdulillah". Sai Kuma ta d'ago da kanta tana kallonsu Huda da jikinsu yayi sanyi tace.

"ku wuce ku tafi tunda ta samu bacci" ta fad'a tana kallan agogon bangon Dake manne a falon.dan lokacin har k'arfe 4 Saura tayi. Ya zarah ta sauke numfashi tace. "Allah ya sawak'e, wai Ammie yaushe zaku koma Egypt d'in ne?. Ammie tace. "Da naiwa Yayanku maganar ne yace na bari idan ya dawo sai muyi maganar Wallalhi Nima na Matsu mu tafi tunda muna da pass port viser ce kawai zamu jira". Ya Zarah tace. "Gaskiya dai yafi Ammie Amma maganar gaskiya Huyaam tana Shan wahala wallahi Allah ya sawak'e". Ammie da Huda suka ansa da Ameen. Kafin su juya su fita daga falon gabad'aya zuwa wajen motar. suka tadda Salima tana ciki ita da Aziza ta cika tai fam k'iris ya rage ta fashe Dan haushi sai sauran k'annunsu da su dama already suna ciki.safnah da ikleema kuwa suna waje Basu shiga ba Dan Wallahi har zuciyarsu suke tausayin HUYAAM kan wannan jinyar tata ya zulaihat ma dai tana tsaye tana kallan ta jiransu kafin ta Kalli ya Zarah tace. "Zarah ya Jikin Huyaam d'in?.ya Zarah tace. "Da sauk'i"
Ya zulaihat tace. "Allah ya sawak'e daga haka tace su shiga ,suka shiga Sai itama ta Shiga dogarin ya kulle k'ofar sannan ya koma front seat yashiga dama already Shima driver ya Shiga ya ta-da motar suka bar gidan gabad'aya......


Ido kawai Ammei ta zubawa HUYAAM tun bayan tafiyar su Huda take zauna falon ta kasa matsawa daga kusa da ita tunanin yadda zasu rabata da wannan ciwon nata gabad'aya kawai
Take Dan wannan wahalar da Huyaam take Sha ta isa haka, Dan a yanzu takai ta kawo acikin sati biyu wannan ciwon nata ya tashi sau biyu da sai ta kai kusan shekara bai tashi ba tunda suka fara zuwa Egypt d'in nan Amma yanzu kwanan nan Abu ya dawo sabo.wannan ciwon na na Huyaam ba k'aramin damunta yake ba ko jiya Saida sukai maganar da Mai martaba yake ce mata ya kamata a Maida Huyaam Egypt d'in nan ita Kuma take ce masa ai Afeef yace idan ya dawo zasuyi magana, Amma kiga ciwo ko sati batai ba ya K'ara dawowa.juyawa tai Ganin Huyaam ta farka tai kanta da sauri tana faman jera mata sannu HUYAAM ta Dan Bud'e idonta kad'an da sukai Jajir tana kallon Ammie da k'yar ta iya Bude Baki tace. "Ammie ruwa".Ammie tace cikin kwantar da murya bari nakawo miki". Daga haka Ammie ta mik'e tai hanyar dining......




#<9HUYAAM
#<9LAMID'O
#<9AZIZ CHIROMA
#<9AFEEF


*mutanan MRS SARAKIES =؋ Kuna Ina ne? ana ta payments na book d'in Huyaam ku an barku a Baya to Maza ku garzayo yanzu kar wannan garab'asar ta wuce ku*.


*ga masu buk'atar fara payments zaku iya sa kud'inku a yanzu before mu gama free pages Regular group akan naira 500 kacal idan kuma muka gama Free pages zai koma 700 ne.ga masu buk'atar Vip Kuma 2 pages a Rana zaku iya biyan nai 1000 kacal. ku hanzarta ku fara biya tun kafin mu gama free pages.zaku iya tura kud'in ta wannan account d'in =G*


2270127432 Naja'atu umar
Zenith bank

Evidence of payment (shaidar biya )via
07066508376


*'Yan Niger <<_zaku iya biyan(500 CFR) a Yanzu before mu gama free page. idan muka gama Kuma zai koma(700 CFR) . for VIP Kuma (1000 CFR)MY NITA =G*
07066508376


Da zarar mungama free pages Kuma zamu sa duk Wanda ya biya kud'in sa a paid group, karku bari ayi wannan tafiyar Babu ku =؃=؃ mutanan arziki.




07066508376________
'Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD


*<9HUYAAM<9*


*NA*



*__NAJA'ATU UMAR FAROOQ __*



*__(MRS SARAKIES =؋)__*



PAGE 2 9



*TALLAH! TALLAH!! TALLAH!!!*


*Assalamualaikum*
*Ina kuke manyan mata masu capacity =؃=؃? Nace Ina kuke hajiyoyin gidan nan, to Maza ku Bud'e kunnuwanku ku saurarareni > da kyau.Dan a yau nazo muku da Wani kyakkyawan albishir=؃=؃ wanda zakuji dad'insa fiye da yadda zan fad'a muku.Nace ba, Bakuda Labarin hamshak'iya shahararriyar 'yar Kasuwar nan wacce tai K'aurin suna wajen kawo muku kayayyakinta na 'yan Gayu masu quality wato H.Empire < Lagos Mai gidan kayan sawa na mata na k'walisa da Kuma kayan kitchen?..."*

*To idan yau kuka tab'a ji ya kamata ace kun saurareni kunji da abinda nazo muku dashi. Kayan sawa kike so Wanda zaki zama tauraruwa a cikin 'Yan uwanki mata harma da Mai gida wato oga kwata kwata Hajiya ta , ko ko so kike duk inda kika gifta kallo ya koma kanki?. Ko Kuma kayan kitchen kikeso masu kyau da aminci daki bari. To Maza ku garzayo H.Empire < Lagos anan zaku samu duk Wani Irin Abu da kuke so, Dan mu kayan mu quaranti ne Hajiyata bakida tan tama akai, kudai ku gwada siya kawai zakusha mamaki Dan sai Kun bani labari. Muna Saida kaya kamar haka ka* =G

*1,Atamfofi*
*2, lesses*
*3, Abaya*
*4, kayan kwalliya ko Wani iri ne*
5,*D'an kunnaye(jiwelleries)*
*6,takalma*
*7,hand bag*
*8, mayafai*
*9, sai Kuma kayan kitchen shima Muna sai dawa, Dan duk Wani kayan kitchen d'in da kike nema harma da Wanda Baki tab'a Gani ba ko sani to idan kikazo H.Empire < Lagos anan zaki samu duk Wani Irin kayan kitchen muna Saidawa akan farashi Mai sauk'i da rahusa siyan D'aya ko sari*.

*domun magana damu kai tsaye ko Kuma Neman K'arin bayani ku tun tub'emu ta wad'an nan numbers d'in kai tsaye kamar haka =I+234 811 190 1302 /09020337676*


*Siyan na gari Mai da kud'i gida Hajiya ta*

*Sai mun Jiku=؃=؃*


<9<9<9<9<9<9


*Bismillahirrahmanirrahim*


__________&


Har washe gari HUYAAM Bata dawo dai dai ba. Dan da Wani Irin ciwon kai suka tafi suka barta dashi.duk da Tasha maganin nata Amma bamu Wani sauiki aciki, haka Nan dai Ammie ta barta ganin iya ciwon kanne bawai jikin ba, Dan inda sabo irin wannan ciwon kan na Huyaam ta Saba dashi.tun k'arfe 8 na dare tacewa Ammie bacci take ji nan Ammie ta kaita d'akin Huda ta Kwantar ta saida Ammie taga tayi bacci sannan ta bar d'akin tareda da Huda .Dan Ammie tace tareda da Huda zasu kwana saboda ta dinga kula da ita kafin safiya. ahaka ta koma falon downstairs ta barsu tareda Huda....Washe gari da safe wajen k'arfe 7:30am Huyaam na zaune kan sallaya a nan d'akin Huda da tun bayan da tai sallan ASuba tayi azkar d'inta take nan Zaune tana karatun Al'qur'ani ita kad'ai ce zaune Huda Kuma tana kan gadon ta koma bacci.dan tunda ta tashi tajita saka yau kamar Bata tab'a Wani ciwo ba, ciwon kan ma dayak'i tafiya yanzu haka ya tafi Babu shi Hakan nema ya Bata damar yin karatun. knocking d'in kofar d'akin da akayi Tareda turowa aka shigo lokaci D'aya Yasa Huyaam ta juya tana kallon Mai shigowar.Ammie ce tashigo sanye da jihab a jikinta,ajiyar zuciya ta sauke ganin Huyaam d'in Zaune tana karatun Al'qur'ani Hakan na nufin Jikin da sauk'i kenan.sauke idonta Huyaam tai k'asa tana ansa sallamar Ammie tareda gaisheta lokacin D'aya.Ammie ta k'araso d'akin ta tsaya tana kallan Huyaam da kulawa ta ansa mata sannan tace. "Ya Jikin Huyaam?...
"Huyaam tace cikin sanyin murya. "Da sauk'i Ammie". Ammie tace. "Allah ya sawak'e , Allah ya K'ara lafiya, yanzu babu ciwon kan?..." Huyaam tace. "Eh yanzu Babu". Ammie tace. "To Alhamdulillah Allah ya K'ara lafiya idan Kina Jin yauwa dai ki taso muje Kisha ko iya tea ne before a gama breakfast d'in". Huyaam ta girgiza mata kai tace. "bana Jin yunwa". Ammie tace. "Kin tabbata Huyaam". Huyaam tai shiru ta Jin jina mata kai alamar eh.Ammie ta sauke numfashi tace. "Shikenan! Hudan Bata tashi bane ba?...." Ta fad'a tana kallan saman bed d'in da Huda ke kwance sai sauke numfashi takeyi.huyaam ta kalli gadon sai Kuma ta kalli Ammie tace."a'a tayi sallah ita ta tashe Nima mukai tare". Ammie tace. "Shikenan Allah ya K'ara lafiya". Huyaam ta ansa da Ameen daga haka Ammie ta fita daga d'akin bayan ta kullo Musu k'ofar.....


K'arfe Hud'u da Rabi na yamma, dayake yau Al'hamis babu Islamiya yasa gabad'ayansu basuje ko Ina ba suna zaune a gida. Huyaam da Huda ne kad'ai zaune a falon ita da muneefa Dan muneeb tunda ya tafi masallaci sallahn ASR Bai dawo ba.ya Zarah ma dai tana school Bata dawo ba.Ammei Kuma tana sama tunda ta haura Bata sauko ba.Baba magajiya ce ta fito daga kitchen ta k'araso falon hannunta rik'e da Wani D'an k'aramin tray Wanda ta d'ora jug da cup akai data damawa Huyaam kunu dan tace shi take son Sha.da sallama ta k'araso falon ta k'arasa nan gaban HUYAAM ta ajiye tray d'in tana kallanta tace. "Gashi an dama kunun 'yar gidan Ammie...."
"Ta fad'a cikin girmamawa.huyaam ta d'aga ido ta kalli baba magajiya sannan ta kalli tray d'in tace. "Sannu baba nagode". Baba magajiya tai murmushi tace. "babu abinda kike buk'ata Kuma?..." Girgiza mata kai Huyaam tai tace. "Babu komai". Baba magajiya tace. "Allah ya K'ara lafiya ranki Dad'e". Huyaam ta ansa mata da Ameen.mik'ewa Baba magjiya tai ta bar falon ta koma kitchen d'in.huyaam ta d'auki cup d'in ta tsiyayi kunun ta kai Baki ta fara Sha sai taji yayi mata Dad'i sosai abakinta.bayan Kamar mintuna 15 suna Zaune afalon akai Sallama a k'ofar falon, safnah ce da mamansu Hajiya Aysha.Huda da Huyaam suka ansa musu sallamar tasu har suka k'araso falon. Huda da Huyaam suka had'a Baki Wajen gaida Hajiya Aysha.hajiya Aysha ta ansa musu da kulawa tana tambayar Huyaam jikinta.huyaam ta ansa mata a Kun yace.huda ta Mik'e tace. "Ummi ki zauna bari naiwa Ammien Magana tana sama".Daga haka Huda ta nufi stairs d'in.Hajiya Aysha tai murmushi ta zauna nan saman kujera . safnah ta k'arasa ta zauna kusa da Huyaam tana kallanta da kulawa tace. "Huyaam ya jikin?..." Huyaam na D'anyi murmushi tace. "Da sauk'i". Safna tace. "Allah ya K'ara lafiya". Huyaam ta ansa mata da Ameen k'asa k'asa.d'aya daga cikin hadiman Ammie ce tai sallama a falon hannunta d'auke da tray data D'ora ruwa da drink's akai ta ajiye saman table Dake nan gaban Hajiya Aysha sannan ta tsugunna har k'asa ta gaida Hajiya Aysha. Ansa mata Hajiya Aysha tai da kulawa sannan ta mik'e ta koma kitchen d'in.Huda ce ta sauko downstairs d'in tana kallan Hajiya Aysha tace. "Ummi Ammien tace kije falon sama" Mik'ewa Hajiya Aysha tai tana ansa mata da to daga haka ta nufi stairs Wanda zai sadan ta b'angaren Ammien..


Fulani Salamatu ce zaune a cikin d'akin Aziza tana kallan Aziza Dake zaune a falon tun d'azu sai chatting takeyi.Aziza ta d'ago tana kallan mummyn nasu Dake tai mata magana tun d'azu akaro na Babu adadi Amma Kuma batai mata magana ba yanzun ma gajiya tai tace. "wai mommy yanzu Dan Allah Mai kikeso nace miki ne? nifa wallahi banasanshi ko kad'an kuma kinsan ma Karatu Zanyi ba wai soyayya ba ni gaskiya kark'i k'aramin zancensa banaso". Ta fad'a a fusace tana Wani tura Baki gaba.fulani Salamatu kallan Aziza kawai take da mamakin abinda ta fad'a yanzu Aziza so take ta Bat'a mata duk Wani shiri da buri akan abinda take ganin shine kad'ai mafitar ta kome? Ita fa a yanzu babban burinta bai wuce ace 'yarta ta auri D'an sarki mai jiran gado ba tunda ita Bata haifi D'a namijin da zai gaji sarautar gidan ba ai gara ace 'yarta na Auren D'an sarki Koba komai wata Rana 'yar tace matar sarki harma ta haifi yarima .sauke numfashi tai ta k'ara gyara zamanta tana kallan Aziza tai k'asa da murya tace. "Haba Aziza Yanzu ni kenan ban isa na fad'a miki magana Kiji ba? Haba Aziza komai fa da kikaga Inaya danke nakeyi fa badan Komai ba, Amma yanzu ni zaki kunyata ko yaya?.." Aziza tai shiru batai magana tana cigaba da danna wayarta.fulani Salamatu ta cigaba tace. "To Yanzu da kike cewa bakyason sa Dan Allah meye laifinsa da zakice bakyason nasa sai kace bakisan Shiba Aziza? Ga kyau ga kud'i ga Aji to Dan Allah Kiko Aziza me kikeso awurin D'a namiji Wanda shi ba shida shi?..bana tunanin koke zaki fad'a masa kyau.
"Aziza ta Kalli mommyn nasu Jin abinda ta fad'a tace. "Wai mommy Dan Allah shine yace Yana Sona ko Kuma kece dai kike son ni na so shin?.ta fad'a tana jiran ansar mommyn nasu.Fulani Salamatu ta K'ara gyara zamanta tai k'asa da murya tace. "Waya ce Miki baya sanki Aziza? Kema kinsan babu Wani d'a namiji da zai ganki baiji kin masa ba". Aziza ta tura Baki gaba tace .
"To Dan Allah mommy abar zancen nan kawai yanzu AURE za'a min ko Kuma karatu Zanyi?. Falani salamatu tace. "Karatu zakiyi Aziza, Amma Kuma inaso ne na ga kin amince da maganar nan tawa yadda ko zuwa gaba ne nasan bani da matsala akan wannan Abu Da nakeso ya k'ullu". Aziza ta Bat'a Rai tace. "To Dan Allah tunda sai nayi karatu ki K'yaleni da wannan maganar ki bari har sai lokaci yayi".fulani Salamatu tai shiru tana kallan Aziza tana tunanin ta yadda zata b'ullo mata Dan Kada ta watsa mata k'asa a ido ta Bat'a mata duk Wani shirin ta,Dan Aziza ce kad'ai take tunanin zata had'a ta da shi Wanda take wannan burin akan nasa. Sauke numfashi tai tace. "Shikenan tunda kince haka Amma inaso kiyi tunnani akai". Da k'yar Aziza ta iya ansa mata da to sannan fulani Salamatu ta mik'e ta fita daga d'akin gabad'aya.......


_____________&


Tun bayan da su Huyaam sukai sallahn magrib suka d'auko Al'qur'ani suke karatu anan falon kamar yadda suka Saba,har yanzu da ake K'iran sallahn isha'i kafin su tsaya da karatun bayan sunkai Aya sannan suka rufe Al'qur'anin .Addu'o'i sukai Sosai kafin su shafa suka Mik'e Jin anshiga Sallahn, jam'i sukabi suka bi sallahn.....k'arfe 8:30pm suna Zaune a falon downstairs bayan sunyi dinner ko Wacce rik'e da wayarta a hannunta daga Huyaam har Huda ya Zarah ce bata a falon tana d'akinta tun bayan da sukai dinner ta shige d'akin Bata fito ba har yanzu.muneefa da muneefa kuma suna zaune a falon suna game. Knocking k'ofar falon akai Tareda Sallama lokaci D'aya a aka turo k'ofar aka shigo.kallan k'ofar sukai Huda na ansa sallamar tasa harya k'arasa shigo falonwa falon bakinsa d'auke da sallama.huda na murmushi tace. "Ya chiroma sannu da zuwa". Ta fad'a tana kallansa har lokacin murmushi ne a saman fuskarta.Aziz chiroma ya zauna anan saman kujera Yana kallan Huda."yace.yauwa Huda." Muneeb da muneefa ne suka juyo suna gaida shi ,ansa musu yayi Yana murmushi Yana tambayar su school suka ansa masa da Alhamdulillah. Yace. "Good,Masha Allah! Ya Fad'a Yana kallan Huyaam ta gefen ido data sunkuyar da kanta idonta na kan screen d'in wayar ta kamar Batasan Yana wajen ba.Huda tana kallansa tace. "Ya chiroma Ina wuni?" Yana murmushi yace. "Lafiya lau Alhamdulillah ya huta?. Huda tace. "Lafiya lau". Huyaam ta d'ago da kanta tana kallansa ta D'an saki fuskarta kad'an tace. "Ya chiroma Ina

Please Login or Register in order to submit comment