Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tace. "To ga breakfast can kaje kayi an had'a Yana dining ko dai a kawo Maka nan d'in?." Ya langwab'ar da kai yace. "Ammie anya ko zan tsaya saboda time Yana k'ok'arin tafiya". Ya fad'a Yana kallan disigner watch d'in dake d'aure a tsintsiyar hannunsa.Ammie ta harareshi tace. "Ai da saura k'arfe nawa Yanzu ba kace jirgin k'arfe 10 bane ba?....".yace. "eh! but inaso ne naje wajen takawa kafin na tafi shima kinsan zan iya spending some minutes acan kafin na tafin". Ammie tace "duk da haka Afeef akwai sauran time kusan one hour fa". Ya Sauke numfashi ganin Ammien ta dage dole sai yayi breaking d'in yace. "Shikenan muje ko iya tea ne Nasha". Daga haka yabi bayan Ammie suka fita daga falon gabad'aya bayan ya kullo k'ofar falon nasa suka Sauka downstairs d'in....


Zama yayi kawai Yana kallan Ammie da mamakin yadda take loda masa abinda aka girka for breakfast kawai yake Kallo.gabansa ta kawo ta dire plate d'in tana kallansa tace. "Gashi nan kaci naga iya plate tunda kaga tafiya zakayi". Ta fad'a tana barin wajen kafin ya samu zarafin Yi mata complain.kallan abincin kawai Afeef yake Yana tunanin ta ina ma zai fara Dan shi ganin yawan breakfast d'in data had'a masa ma tsoro kawai yake bashi duk da itama kanta Ammien tasan ba iya cin ko Rabi zaiyi ba.sauke numfashi yayi ya d'auki spoon ya fara Shan tea d'in dake gaban sa shima baifi sipping hud'u yayi ba ya ajiye sannan ya d'auki fork spoon ya Dan caccakali Irish d'in with source stew d'in kafin yaji he is fully sannan ya ajiye fork d'in ya d'auki bottle water ya b'alle murfin ya kafa a bakinsa ya fara Sha cikin nutsuwa bayan ya gama Sha ya ajiye Sauran nan kan table d'in sannan ya d'auki tissue ya goge bakinsa da ita.mik'ewa yayi ya bar dining d'in ya k'araso nan tsakiyar falon inda box d'in nasa take ya duba wayarsa Jin shigowar text message Mai aikin b'angaren
Nasu data ke aiki zata wuce ta duk'a har k'asa ta gaidashi ansa mata yayi with out looking at her. Huyaam ce ta sauko downstairs d'in Dan tun bayan ASuba da tai sallahn sukai karatun Al'qur'ani ta d'auko wayar ta tafi d'akin ya Zarah akan ta Bud'e mata komai duk da dama dai tasan kusan komai daya Dan ganci waya acikin wayar Ammie tunda suna d'auka Wani time d'in ita da Huda suyi latse latsensu aciki idan suka gaji Kuma su ajiye,da Allah Kuma ya taimakesu duka akwai sim card masu register acikin wayoyin nasu .tsaye tai a stairs d'in tana kallon Afeef da yake latsa wayarsa yayi kyau cikin kayan Daya sa ba kad'an ba, ga facing cap d'in Daya D'ora akansa ta hannunsa D'aya a cikin aljannun Wandansa d'ayan kuma Yana latsa wayarsa dashi kwata kwata baiji motsin kowa ba tunda replaying message yakeyi.tsintar kanta kawai tai da shiga cikin Camara wayar Tata tashiga Yi masa pictures Wanda sukai kyau ba kad'an ba duk da daga nesa tai Amma Kuma yayi kyau wasu tai zooming kafin ta d'auka wasu kuma ahakan daga nan nesan tai masa su . murmushin tai Ganin harta gama d'aukar tasa Bai sani ba saboda kwata kwata hankalinsa na kan wayarsa.dan tasan idan ya sani saiya kusan tattaka ta. k'arasa saukowa stairs d'in tai Jin motsi foot steps a bayanta Ammie ce take saukowa sai alokacin afeef ya d'ago d a kansa daga latsa wayar tasa da yakeyi ya Kalli Ammie Dake saukowa downstairs d'in Wadda direct hanyar kitchen d'in tai tana ce masa tana zuwa,ansa mata yayi da okay sannan ya Kalli HUYAAM data k'araso ta D'an tsaya kusa dashi tana murmushi tace. "Good morning Yaya".yana kallonta yace. "Morning". Ta D'an tura Baki kad'an tana langwab'ar da kai tace. "Yaya Ashe wai tafiya zakayi". Yace. "Ba gashi kin Gani ba". Tace. "Yaushe zaka dawo Kuma?." Batareda ya kallate ba yace. "I don't know". Atak'aice . Huyaam Tai murmushi tace. "Wallahi ka sani". Ya kalleta Fuskarsa a had'e yace. "Yaushe na fara wasa Dake HUYAAM da zan Fad'i Abu kice min wai nasani". Tai murmushi tana Toshe Bakinta da hannunta duka biyun tace. "Kayi hak'uri bazan sake ba". Ya d'auke kansa Amma Baice komai ba.Ammie tafito Daga kitchen dai dai lokacin da a kai knocking k'ofar wata Mai aikin Ammie ce Dake goge goge a falon ta ajiye dust d'in hannunta tafi Jin Muryar namijine ta Bud'e k'ofar D'aya daga cikin drivers d'in gidan ne Yana kallanta yace. "Kicewa yarima an fito da Motar?. juyowa tai ta Koma cikin falon ta tsugunna har k'asa kanta a k'asa tace. "Rankai Dad'e driver ne yace an fito da motar". Afeef yace. "Okay". Daga haka ta Mik'e ta koma ta cigaba da aikinta.Afeef na kallan Ammie yace. "Ammie bari na tafi". Ammie tace. "shikenan Allah ya kiyaye ka gaida lamid'o idan kaje". Afeef ya ansa mata da in Sha Allah! Dan dama lamid'o ya Dad'e da komawa tun time d'in da AFEEF yazo lokacin Baifi 4 days da dawowar AFEEF d'inba ya koma. Ya zarah ce da Huda suka sauko falon dama tun 7:30 su muneefa suka tafi school.suna kallon yayan nasu Dayay hanyar k'ofar zai tafi sukai masa Allah ya kiyaye ya ansa musu Yana fita daga falon.drivern da zai kai Afeef Airport d'in Dake tsaye can gefe dama Bai tafi ba Yana tsaye Yana jiran fitowar sane yay Maza ya k'araso wajen sa ya karbi trolling hannunsa cikin girmamawa yake masa barka da fitowa. Ansa masa Afeef Yayi at the same time Yana tafiya bai tsaya ba yana kallon time ganin da D'an sauran lokaci yace. "Kaji rani ina zuwa". Daga haka yay Hanyar fad'a gun Mai martaba.cikin girmamawa driver ya ansa masa Yana yin gaba wajen inda yayi parking motar... k'arfe 9:50am taiwa su Afeef airport d'in,fitowa yayi daga cikin motar bayan an Bud'e masa back seat ya fita dogarin na kallansa cikin girmamawa yace. "Allah ya dawo dakai lafiya magajin masarautar kano". shidai Afeef Bai ansa ba har driver ya k'araso da trolling a hannunsa Yana kallan Afeef yace. "A raka ka da akwatun ciki rankai Dad'e?... Afeef yace. "No! badamuwa ku wuce kawai".daga haka yasa hannu ya k'arfi trolling ya bar wajen ya wuce inda ake boarding classes da har an fara dan ma shi Yana VIP ne ba Wani layi zaibi ba.driver da dogarin nan da sukai masa rakiya suka shiga motar suka koma palace....



Tun bayan tafiyar Afeef dasu HUYAAM sukai breakfast suke Zaune a falon ita da Huda.ya Zarah kan ciki ta koma zatai shirin tafiya school Dan k'arfe shad'aya suke da lecture. Knocking akai a k'ofar falon tareda turo k'ofar aka shigo lokaci D'aya.. ikleema ne da safna kowa da wayarsa a hannunsa suka shigo falon bakinsa a washe kamar gonar auduga.. mamaki ne ya kama su Huyaam ganin su Ikleema Amma Kuma sai suka kauda tunanin nasu tunda dai sun San bazai wuce akan wannan wayar bace ta kawo su.k'arasowa falon sukai cikin sand'a kamar wasu marasa gaskiya suka zauna nan k'asan carpet.huda ta rik'e hab'a tace. "Meye kuke Wani sand'a kamar wasu marasa gaskiya?..." Ikleema ta Saka yatsanta abakinta alamar tai shiru".Huda tak'i yin shiru sai ma cewa da tai ".Yau Kuma kune da wannan lokacin". Ta fad'a tana musu Hararar Wasa". Ikleema ta k'ara k'asa in da murya tace. "To ko mu koma ne?...." Sai Kuma ta rik'e baki tai k'asa da murya tace. "Yaya Yana nan ne? shiyasa fa nake tai Miki alamar kiyi shiru Amma kika k'i,Dan kan naje na saki baki ina ta suturu ya fito ya sameni".. Huyaam tai murmushi tace. "Baya nan matsora ciya".. ikleema tace. "Au! Tunda baya nan shikenan ai gara na saita bakin nawa kar naje na saki layi". Huda tace. "Kima Saki bakin mana". Ta fad'a tana murmushin.ikleema tace. "A'a gara dai nai shirun duk da baya nan" Sai kuma tace." Uhmm Kinga zuwa mukai fa mu karb'i contact D'inku tunda dai yanzu muma mun samu 'yan cin kanmu". Ta fad'a tana Wani fari da ido.Huda tasa dariya tace. "Yanzu karb'ar contact d'inne har sai kunzo? ah lallai ko yanzu munsan kunyi waya farin shiga". ikleema tace tana hararar Huda. "ke
Banda kenan?...". Huyaam tai murmushi tace. "Ina ko harda ita mana to jiya in Baku labari Huda kasa bacci tai saboda murna". Mai ikleema da safna zasuyi inba dariya ba .Huda ta harari Huyaam tace. "Wallahi kairya take itace ma batai baccinba.Safnah tace. "Kinga malama bama San borin kunya idan bazaki bamu contact d'in naki ba ita Huyaam sai ta bamu ai ba'a dole". Huda tace." Keda wasa nake muku bari na fara Baku tawa". nan ta fara karanto musu duk suka shiga adding numbers d'in Cikin wayoyinsu haka nan dai sukai exchanging numbers a tsakaninsu,har ya Zarah ta fito zata tafi school ta Tarar suna ta hauka da wayoyinsu suka Gaida ta da fatan mata dawowa Lafiya ta ansa musu Sannan ta fita daga falon nan fa Abun NEMA ya samu sai faman latsa waya sukeyi ana dariya ana shewa har Ammie ta fito itama ta samesu.....



_____________¡&


Hajiya inna na Zaune nan main falon b'angaren gimbiya Aysha tana kallan TV da ake haska wa'azi daga bakin Wani babban malami a k'asar nan a tashar Sunnah TV sallama akai Tareda da shigowa falon . ta d'aga kai tana kallon Anam data dawo daga islamiya k'arfe b'iyar da Rabi na yamma.har ta k'araso shigowa falon ta risina ta gaida Hajiya inna.hajiya inna ta ansa mata tana cewa". Andawo Zainabu?..." Anam ta gyad'a mata kai . Hajiya inna tace. "Sannu da dawowa Zainabu Allah ya Bada ilimi Mai amfani".Anam ta Ansa mata tana mik'ewa Hajiya inna tace. "Maza ta kwara jeki sauya kaya kizo ki k'arb'i abunda Dana akeyi miki". Anam ta gyad'a mata tace. "To" sannan ta wuce zuwa d'akin gimbiya Aysha Dake nan upstairs d'in....baba uwani ce ta fito daga kitchen d'in downstairs ta k'araso falon ta tsugunna har k'asa kusa da Hajiya inna tace. "Mai babban d'aki an gama dafa maganin". Hajiya inna ta juyo tana kallon uwani tai k'asa da murya tace. "Ba haka ya kamata kice ba uwani yanzu idan wannan yaron Yaji me kika fad'a min fa?kinsan fa Yana nan d'akin k'asa Yana karatu kar yaji Mai kike cewa anjima idan na Kai masa yace bazai shaba".baba uwani ta sunkuyar da kanta k'asa tace. "Tuba nake Mai babban d'aki ban sani ba." Hajiya inna tace."to yanzu abinda za'ayi ki samu wankakken mazubi Mai Fad'i ki juye bayan kin tace ki barshi yasha iska anjima zan Miki magana saiki kawomin". Baba uwani tace. "To ranki Dad'e a tashi lafiya". daga haka ta koma kitchen d'in bayan kamar mintuna 10 ganin Anam Bata saukoba gashi sai K'iran sallahn magrib akeyi yasa Hajiya inna mik'ewa ta shiga wani sapare d'aki Dake nan downstairs d'in Dan nan ta D'an tattaro kayan ta tadawo tun lokacin da sultan ya fara k'ok'arin guduwa idan ciwonsa ya tashi tace gara ta dawo b'angaren nasu ta zauna kar aje wata Rana ya gudu ba'a sani ba su shiga uku.ita anty Amina abun ya mata yawa ga jinyar uwa Kuma gata d'a ai dole a tausaya mata.toilet d'in d'akin ta shiga bayan ta shiga d'akin Dan d'auro alwala....


Turo k'ofar d'akin akayi bayan anyi sallama. Hajiya inna Dake kan darduma tana lazumi ta juyo Jin anshigo mata d'akin. Anam ce ta Gani ta shigo ta k'araso cikin d'akin ta haye saman gadon tana kallan Hajiya inna tace. "Na zo ki bani abinda kikace zaki banin?..." Hajiya inna ta kalleta tace. "Ayya wuceki tunda Baki dawo da wuri ba sai yanzu". Anam ta tura Baki gaba tace. "Ai na dawo bansameki ba shine nace bari nima naje nai sallahn saina dawo". Hajiya inna ta tab'e Baki tace. "Kedai kika sani Mik'o min wancan k'waryar abun Yana ciki". Anam ta juya tana kallon inda Hajiya inna ke nuna mata ta k'arasa ta d'auko k'waryar ta Mik'a mata sannan ta koma ta zauna.Hajiya inna ta Bud'e k'waryar nan Anam taga miye aciki Ashe zuma ce.hajiya inna ta d'auki Wani spoon ta d'ibi Zuman ta Mik'awa Anam.Anam ta gyara zamanta tace. Ki Mik'o min mana". Hajiya inna tace. "Ta ya ya zan Mik'o mikin ina zaune". Anam ta taso ta karb'a tace. "Kuma iya D'an wannan zaki bani inna". Inna ta mik'a hannu tace" idan baza kishaba ki bani kayata". Anam ta harareta sannan ta mik'e ta koma saman gadon ta fara Shan Zuman...

K'arfe takwas da mintuna inna tashigo d'akin gimbiya Aysha ta samu anty Amina tana goge mata Bakinta da tissue bayan ta gama Bata abincin data kawo mata.anty Amina ta juya tana ansa sallamarta. Hajiya inna ta k'araso d'akin hannunta rik'e da Wani jug ga extra cup a hannunta tana kallan gimbiya Aysha tace. "Sannu Aysha Allah ya K'ara Miki lafiya". gimbiya Aysha ta lumshe idonta alamar ansa mata". Hajiya inna na kallan anty Amina tace."Amina maganin Da aka kawo min ne nasa uwani ta dafa musu gashi wannan natane a jug ki fara bata tun daga Yanzu na kwana ukune duk bayan da ta ci abinci shi zakina Bata tana Sha "Anty Amina ta karb'a tace ."to shikenan inna in Sha Allah za'a na batan Allah ya Saka da Alkhairi". Inna tace.

"Ameen bari naje na kaiwa sultan danshi sai dai na ajiye nasa agunnawa Ina bashi Dan Kinsan halinsa" Anty Amina tace."hakane kan inna". Inna tace. "Bari naje". Daga haka tai hanyar k'ofar fita daga d'akin anty Amina tai ta mata godiya....


Hajiya inna ce tsaye bakin k'ofar dak'in sultan tana knocking ta kusa minti Biyu tsaye .kafin ya taso ya bude k'ofar Yayi tsaye Yana kallanta yak'i ya Bata hanyar ta shiga Yana kallonta sama da k'asa."Hajiya inna ta zuba masa ido sai itama ta tsuke tata fuskar ta had'e Rai tace. "Muje ciki mana ka tsaya min aka kak'i bani hanya kana kallona". juyawa sultan yayi ya koma Cikin d'akin ya zauna nan gefen gadon Yana kallan Hajiya inna data zauna kan kujera da cup a hannunta.ta Mik'a masa tace. "Ungo wannan shanye yanzu ka bani cup d'in maganin sammu ne". Sultan ya Kalli cup d'in yaga Wani Bak'in ruwa kamar tea kamar ba Shiba sai Kuma ya kalli Hajiya inna ya girgiza kai yace.

"Bazan Sha ba ni wai na ce Miki bani da lafiya ne da kullum zaki na kawomin jik'e jik'e kina cewa Nasha".ya fad'a Yana had'e Rai.

Hajiya inna tai k'asa da murya tace. "Haba sultan Kasan dai bazan tab'a baka Abinda zai cutar dakai ba ko?nace Maka maganin sammu ne na Wani abun ba Ka daure kasha magani ne komai sai anayi ana daurewa". Ta fad'a tana kallansa. Sultan yace. "Nifa Inna bazan Shaba Lafiyata k'alau kullum sai kuyi ta D'ora min jinya". Hajiya inna ta marai raice tace cikin lallashi."naji lafiyar ka k'alau sultan Amma Kuma so nake ka K'ara samun wata lafiyar akan wacce kake da itan". sultan ya girgiza mata kai alamar shifa bazai shaba.hajiya Inna ta dinga lallashinsa daga k'arshe tace. "yanzu sultan zan baka Abinda zai cutar da kai ne naga kai Jini nane jika nane fa Kai wanda nake k'auna Kuma Dan bansan me nake ba sai na cutar da kai?bama fa iya kai kad'ai na bawa ba na kaiwa har babarka ma itama Kuma Tasha In Sha Allah muna sakaran samun sauk'inta" Saida sultan yaji haka tukunna ya Karb'i cup d'in daga Hannun hajiya inna ya kai bakinsa Yana Sha Yana yamutsa fuska. itadai Hajiya inna kallansa kawai take tana Jin Dad'i tareda godewa Allah data samu yaSha d'in harya gama Shanyewa ya Mik'o mata cup d'in ta karb'a tana murmushi tace. "Yauwa Mai gida Kuma Mai babban suna haka nake so Allah ya K'ara Muku lafiya Baki D'aya.Amma fa maganin na kwana ukune Mai gida duk da lafiyarka k'alau Amma inaso Dan Allah idan na K'ara kawo Maka Wani kada kacemin baza kasha ba". sultan ya gyad'a mata kai Yana yamutsa fuska saboda testing d'in maganin da babu Dad'i Hajiya inna tacce. "To kaci abinci dai ko?.nan ma sultan gyad'a mata kai yayi.tace. "to ayi azkar kafin ka kwanta Saida safe". Daga haka ta Mik'e sultan ya bita da kallo har ta fita sannan ya tashi ya kullo k'ofar ya dawo ya haye saman gadon ya kwanta Yana d'aukar handouts d'insa Yana karantawa......




#<Ø9ßHUYAAM<Ø9ß
#<Ø9ßLAMID'O<Ø9ß
#<Ø9ßAZIZ CHIROMA
#<Ø9ßAFEEF




*mutanan MRS SARAKIES =Ø‹Ü Kuna Ina ne? ana ta payments na book d'in Huyaam ku an barku a Baya to Maza ku garzayo yanzu kar wannan garab'asar ta wuce ku*.


*ga masu buk'atar fara payments zaku iya sa kud'inku a yanzu before mu gama free pages Regular group akan naira 500 kacal idan kuma muka gama Free pages zai koma 700 ne.ga masu buk'atar Vip Kuma 2 pages a Rana zaku iya biyan nai 1000 kacal. ku hanzarta ku fara biya tun kafin mu gama free pages.zaku iya tura kud'in ta wannan account d'in =ØGÜ*


2270127432 Naja'atu umar
Zenith bank

Evidence of payment (shaidar biya )via
07066508376

Da zarar mungama free pages Kuma zamu sa duk Wanda ya biya kud'in sa a paid group, karku bari ayi wannan tafiyar Babu ku =؃Ü=ØƒÜ mutanan arziki.




07066508376________
'þFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD



*<Ø9ßHUYAAM<Ø9ß*


*NA*


*__NAJA'ATU UMAR FAROOQ __*


*__(MRS SARAKIES =Ø‹Ü)__*


PAGE 2þã 8þã


*TALLAH! TALLAH!! TALLAH!!!*


*Assalamualaikum mutanan arziki barkanmu da wannan lokaci*

*Ina kuke manyan mata masu capacity =؃Ü=؃Ü? Nace Ina kuke hajiyoyin gidan nan, to Maza ku Bud'e kunnuwanku ku saurarareni >ØÏÝ da kyau.Dan a yau nazo muku da Wani kyakkyawan albishir=؃Ü=ØƒÜ wanda zakuji dad'insa fiye da yadda zan fad'a muku.Nace ba, Bakuda Labarin hamshak'iya shahararriyar 'yar Kasuwar nan wacce tai K'aurin suna wajen kawo muku kayayyakinta na 'yan Gayu masu quality wato H.Empire <Øæß Lagos Mai gidan kayan sawa na mata na k'walisa da Kuma kayan kitchen?..."*

*To idan yau kuka tab'a ji ya kamata ace kun saurareni kunji da abinda nazo muku dashi. Kayan sawa kike so Wanda zaki zama tauraruwa a cikin 'Yan uwanki mata harma da Mai gida wato oga kwata kwata Hajiya ta , ko ko so kike duk inda kika gifta kallo ya koma kanki?. Ko Kuma kayan kitchen kikeso masu kyau da aminci daki bari. To Maza ku garzayo H.Empire <Øæß Lagos anan zaku samu duk Wani Irin Abu da kuke so, Dan mu kayan mu quaranti ne Hajiyata bakida tan tama akai, kudai ku gwada siya kawai zakusha mamaki Dan sai Kun bani labari. Muna Saida kaya kamar haka ka* =ØGÜ

*1,Atamfofi*
*2, lesses*
*3, Abaya*
*4, kayan kwalliya ko Wani iri ne*
5,*D'an kunnaye(jiwelleries)*
*6,takalma*
*7,hand bag*
*8, mayafai*
*9, sai Kuma kayan kitchen shima Muna sai dawa, Dan duk Wani kayan kitchen d'in da kike nema harma da Wanda Baki tab'a Gani ba ko sani to idan kikazo H.Empire <Øæß Lagos anan zaki samu duk Wani Irin kayan kitchen muna Saidawa akan farashi Mai sauk'i da rahusa siyan D'aya ko sari*.

*domun magana damu kai tsaye ko Kuma Neman K'arin bayani ku tun tub'emu ta wad'an nan numbers d'in kai tsaye kamar haka =ØIÜ+234 811 190 1302 /09020337676*


*Siyan na gari Mai da kud'i gida Hajiya ta*

*Sai mun Jiku=؃Ü=؃Ü*


<Ø9ß<Ø9ß<Ø9ß<Ø9ß<Ø9ß<Ø9ß


*Bismillahirrahmanirrahim*

____________¡&


K'arfe 10am Saura na safen ranar Wednesday AFEEF ya fito daga Wani k'aton bedroom room dake cikin k'aton gidan Abban nasu dake garin Lagos Wanda ke kusa da companyn motocin da lamid'o ke jagorantar companyn.tafiya yake cikin nutsuwa zuwa cikin k'aton falon gidan.sanye yake cikin k'ananun kaya riga da Wando,rigar farace K'al Mai layi layin Bak'i sai Wandan Daya kasance Bak'i kayan sun masa kyau ba kad'an ba tamkar ki sace sa ki gudu.dan tunda yazo garin Lagos agidan ya sauka kuma kullum saiya fita yaje companyn Mai martaba sai dare yake dawowa gidan shida lamid'o,har yau Daya kasance Ranar wednesday da yay dai dai da kwanan sa biyu a gidan.tsakiyar falon ya ya tsaya bayan ya k'araso ya tsaya Yana k'arewa sauran bedroom d'in Dake cikin k'aton falon kallo,a d'akin Daya kasance na lamid'o ya tsaida idonuwansa akai Yana kallo kamar Wanda zaiga ma mallakin d'akin ya fito daga cikinsa, d'auke kansa yayi ya cigaba da takawa har ya k'arasa dining d'in tunowa dayay lamid'o ya fita tun Wajen k'arfe 9 na safen ya shigo har bedroom d'insa yay Masa sallama akan ya fita saboda urgent call Daya samu daga companyn. sauke numfashi yayi yaja kujera ya zauna Yana zube wayoyinsa nan Saman table d'in.kafin Yasa hannu ya Bud'e wasu tsadaddun wamers yana ganin abinda aka girka for breakfast.rufe Sauran warmers d'in yayi ya bar D'aya Wanda aka dafa masa abinda aka San shine favorite d'insa a breakfast ya d'ibi abinda Yay masan Dan dama tunda yazo gidan da workers d'in suka tambaye shi me yakeso adinga girka masa d'in ya fad'a musu abinda yake so to shine tun daga nan suka San abinda zasu girka masa fo breakfast and dinner Wani time d'in ma baya dinner saidai kawai yasha tea or coffee ya kwanta .bayan ya gama breakfast d'in ya Mik'e Yana gyara hannun rigarsa .d'aya daga cikin masu musu girkin gidan ne ya fito daga kitchen d'in sanye yake da rigar girkin cikin sauri ya k'araso wajen da Afeef ke tsaye ya risina yace. "Sir good morning". Ya fad'a cikin ladabi Afeef ya ansa masa ba tare da ya kalleshi ba.kukun yace."sir! you need anything?. Afeef ya d'ago da kansa ya kalleshi kafin ya d'auke idansa akansa yace. "Nothing". Izic ya duk'ar da kansa cikin girmamawa ya bar wajen ya koma kitchen d'in dama goge goge yakeyi.... Afeef kuma ya d'auki wayoyinsa ya fito daga falon gabad'aya zuwa compound ma'aikatan gidan sai faman gaida shi suke cikin ladabi Yana ansa musu.motarsa Daya zaba yake fita acikinta tunda yazo aka fito masa da ita,an wanke masa ita sai faman shining takeyi ya k'arasa ya shiga ya ta-da motar.tun kafin yayi horn gate man d'in ya wangale masa gate ya fita da motar gabad'aya direct companyn nasu ya wuce Wanda tsakanin sa da gidan da suke ciki baifi 5 kilo meters ba.....


Daya isa companyn ya tarar Lamid'o Wanda dama already Ya iso Yana cikin office d'insa tare da wasu abokan bussness d'insu da suka zo siyan motor Dan duk idan garin Allah ya waye sai anzo an Siyan motoci a wannan companyn nasu Kuma ba D'aya ba biyu ba Sannan kar kice k'ana nun mutane ne suke Zuwa su Siya, a'a manyan mutane ne Wanda kud'i ya gama ratsawa ke aikowa asiya musu wasu ma da kansu suke zowa Dan aka ce zuwa da kai yafi Sak'o tunda babu Wanda Bai San companyn motocinsu a fad'in Nigeria ba Wanda ke garin lagos ba.Wanda saboda kyau da quality kayansu yasa ake San siyan motoci a wurinsu nasu...


Saida mutanen suka ragu sosai sannan lamid'o ya taso ya K'araso inda Afeef ke Zaune a Wani D'an falo Dake cikin office d'in ta ciki Wanda falo biyu ne awurin.nan suka zauna da Afeef suka cigaba da aikin Daya kawo afeef d'in na sabbin tsare tsaren da za'a yiwa company da Kuma abubuwan da ake buk'ata yadda idan ya koma Ingiland za'a parking komai na wannan companyn yadda idan ZA'A Aiko sai a Aiko dasu completely Batare da sauran Wani Abu ba.sun kusan 5 hours suna Zaune suna tattaunawa sallahn Azhar ne kawai ya ta-da su suka d'auro alwala suka tafi masallacin Dake cikin companyn.....



K'arfe 3 Saura na yamma su Huyaam har sun gama shirin tafiya islamiya suna tsaye a falon ko Wacce Tasha hijab har k'asa ga face mask a fuskarsu saboda yanayin garin hannunsu rik'e da bag d'in islamiyar tasu muneefa suke jira itace kawai Bata fito ba Babu dad'ewa kuma suka sauko downstairs d'in tare da Ammie data rakota suna saukowa Huyaam ta kama hannunta sukai wa Ammie sallama.Ammie tai musu fatan dawowa Lafiya sannan ta wuce kitchen d'in. ansa mata sukai suka fita daga falon gabad'aya.fitowar su Kenan daga b'angaren nasu ko k'arasawa wajen motar Dake jiran su Basu yi ba kawai Huyaam taji kanta ya Wani Irin Sara mata da k'arfi kamar Wanda aka doka mata guduma akan natan, lokaci D'aya Kuma taji kamar ansha k'e mata wuya da hijab d'in jikin nata tamau Wanda harta Kai ga ta fara kokawa

Please Login or Register in order to submit comment