Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fad'a muryar ta na rawa.


Afeef yaji gabansa ya Wani K'ara fad'uwa Jin wai Ammie na asibiti to waye babu lafiya ko itace,Sai kuma yace .


"Asibiti kuma? Meya faru?..." Cikin rawar murya Huda tace.


"Huyaam ce Bata lafiya".gabansa yay dumm kad'an kaddai ace ko ciwon nata ne ya tashi, afili Kuma yace .


"Mai yasa mete?..."

Huda tace.

"Aziza ce ta take mata k'afa da takalminta shine k'afar ta fashe take zubar da jini shine aka tafi kaita asibiti". Huda ta fad'a tana sheshshek'ar kuka..shiru Afeef yayi kamar Wani Mai tunani har na tsawan 30 seconds har huda tayi tunanin koya Kashe wayarne ta duba sai taga Kuma Yana reading Bai kashe ba Hakan yasa tai shiru itama tana sauransa Saida ya maula Dan kansa sannan yace.


"How". nan Huda ta kwashe komai ta fad'a masa". Afeef yay shiru kamar bazai ce komai ba sai Kuma yace.


"It's okay,idan Ammie sun dawo let me know". Huda tace.


"to in Sha Allah".Daga haka ya kashe wayar huda tabi wayar da kallo wasu sabbin hawaye na zubo mata ,baba magajiya ta Kalleta tace cikin sanyin jikin daya shigeta itama tunda aka fita da Huyaam daga gidan.


"kiyi hak'uri Huda in Sha Allah zata samu lafiya Kinji ?...."Huda Bata ce komai ba tana rik'e da wayar a hannunta tana kuma goge hawayen fuskarta.


Afeef Yana sauke wayar ya kusan 4 minutes Bai iya tashi daga inda yake Zaune ba yana Mamakin Hali irin na Aziza kafin ya furzar da huci Mai zafi ya mik'e ya shiga toilet d'in Dan yin Wankan da zaiyi.....



*Hospital*


Ya haidar Yana yin parking a gaban A&E na hospital d'in direct ciki aka shiga da HUYAAM Saboda bleeding d'in da k'afarta keyi har lokacin.Ammie dai tana tsaye jikin motar bayan an shigar da Huyaam tana kallon bakin A& E d'in, dap d'in asibitin ne ya k'araso har wajen motar Yana kallan Ammie ya gaidata cikin girmamawa.Ammie ta ansa masa jikinta a Sanyaye .ya risinar da kansa k'asa yace .


"Am ranki Dad'e Mai zai Hana ku shiga office d'ina ku zauna kafin a fito da ita".ya fad'a Yana kallan Ammie.


Ammie ta kalleshi tace.

"Nan ma yayi doc zamu jira har ku gama aikinku sai mu tafi".doc ishaq yace cikin girmamawa.


"Ranki Dad'e ba musu nake Dake ba Amma ai ba girmanku bane tsayuwa anan Nima bazan so haka ba,gimbiya Kuma tana lafiya Ba Wani babban issue bane kawai wanke wurin zamuyi muyi dressing d'in wajen shikenan".ya fad'a da Ladabi.Ammie tai shiru batai magana ba ya haidar ya kalleta yay k'asa da murya yace.


"Kiyi hak'uri Ammie muje ciki Babu komai in Sha Allah". Ammie ta sauke ajiyar zuciya tace .

"Shikenan muje"doc yay gaba Dan Yi musu jagora ya haidar da Ammie suka bi bayansa.


Wajen 0ne hour Ammie na zaune kan sofan Dake k'aton parlon office d'in doc ishaq tai tagumi gabad'aya hankalinta baya tare da ita Yana can wajen HUYAAM tana tunanin halin da take ciki Gani take kamar komai ma zai iya faruwa da ita Dan tun d'azu da doc ishaq ya kawosu office d'in ya koma emergencyn Bai dawo ba har yanzu daga ita sai ya haidar Dake tsaye Bak'in k'ofar falon office d'in Yana tsaye shima gabad'aya ransa Babu Dad'i. Doc ishaq ne ya shigo cikin office d'in bakinsa d'auke da sallama.. Ammie da ya haidar suka ansa masa suka bishi da kallo har ya k'araso gaban table d'insa ya zauna kan kujerar Yana zare hand gloves d'in hannunsa.


Ammie tace.


"Doc Ina take".ta fad'a cikin damuwa.


Doc ishaq yay murmushi ya risinar da kansa alamar girmamawa yace.


"Lafiyanta lau ranki Dad'e na barta ne ana k'arasa mata dressing d'in but yanzu za'a shigo da ita in Sha Allah.ko rufe Baki doc ishaq baiyi ba aka turo k'ofar falon office d'in wata nurse ce ta shigo tana rik'e da wouldchair Wanda ake D'ora marasa lafiya akai wanda HUYAAM ke zaune aciki idonta sun kumbura sunyi suntum saboda Kukan da Tasha Dan alokacin da ake wanke mata ciwon bakiga Irin kukan da Tasha ba kamar Wanda ake k'ok'arin rabata da ranta.da sauri Ammie ta juya tana kallon Huyaam, idonta ya sauka akan k'afar Huyaam Dake nan nad'e da bandage gabad'aya an rufe k'afar da bandage d'in cikin damuwa Ammie ta taso Babu shiri ta k'araso wajen da HUYAAM take ganin haka yasa nurse d'in ta tsaya daga tura HUYAAM da take ta koma gefe.Ammie tasa hannu ta d'ago da fuskar HUYAAM tana kallanta tace cikin tausayawa.


"Sannu daughter".Huyaam ta kalleta da kumburun idanuwanta kafin ta gyad'a mata kai .ya haidar ya k'araso Yana kallon k'afar shima sai kuma ya kalli HUYAAM yace.


"Sannu HUYAAM". Batare da ta kalleshi ba ta gyad'a masa kai Ammie ta juya tana kallon doc tace.

"Shikenan ko doc zamu iya tafiya?..." Doc ishaq yace.


"Eh ranki Dad'e angama komai yanzu sai magun gunan da nai mata prescription suma gasu an had'o su,indai tana Shan magun gunan in Sha Allah nan da 3 to 5 days ciwon zai warke bandage d'in zai bushe ya d'aye da kansa gabad'aya bama sai an sake wankewa ba in Sha Allah". Ammie ta sauke numfashi tace.


"Allah yasa".ya Haidar ya k'arasa ya karbi ledar magun gunan sannan ya k'araso wajen su HUYAAM doc ya taso shima Yana kallan nurse d'in yace.

"Sister ki turata kuje har wajen motar su ki shigar ta ciki". nurse d'in ta risinar da kai ta ansa masa cikin girmamawa.sannan ta kama hannun wouldchair d'in ta juya suka fita daga office d'in doc ya kalli Ammie yace.


"Allah ya K'ara lafiya ranki Dad'e". Ammie ta ansa da Ameen. ya Haidar ya Mik'a masa hannu sukai musabaha sannan yabi bayansu Ammie yana ansawa doc ishaq da Allah ya kiyaye d'in da yake musu.


_____________¡&


K'arfe 9 da Rabi dai dai na daren ya haidar yay parking a gaban b'angaren su Dan har gaban part d'insu ya kawo mator Yay parking a kofar dama already ya k'ira ya Zarah akan tazo su shigar da Huyaam ciki..horn ya Haidar yay Babu dad'ewa ya Zarah ta fito ita da baba magiya harma dasu Huda.ya haidar ya fito ya zaga ya Bud'e wa Ammie back seat Ammie ta fito tana kallon ya Zarah bayan k'araso gunsu tace.


"Zarah zo tanan ki goyata".baba magajiya tai Saurin cewa.


"A'a ranki Dad'e ki bari na goyata meye anfanina".ta fad'a tana K'arasowa wurin.


Ammie tace .


"A'a magajiya barshi kawai Zarah ma zata iya".


Baba magajiya tai murmushi tace.

"Ranki Dad'e Dan dai karkice ina musu dake Amma da kin barni na goyotan ai zan iya ita da ba nauyi ne da ita ba".. ta fad'a tana sunkuyar da kanta k'asa.

Ammie ta sauke numfashi tace.


"Shikenan Zarah Tayata sai ta goyatan".Babu musu ya zarah ta ansa mata baba magajiya ta k'araso side d'in da HUYAAM take ta tsugunna ya Zarah ta taimakawa HUYAAM ta hau bayan baba magajiya Dan bazata iya taka k'afar ba..A haka Baba magajiya ta shiga da HUYAAM har cikin falon, Ammie na biye dasu ita dasu Huda bayan sun shiga falon Ammie ta Kalli baba magajiya tace.


"magajiya ki kaita d'akina".Babu musu baba magajiya ta ansawa Ammie cikin girmamawa ta kai Huyaam har d'akin Ammie ta ajiye ta saman gadon baba magiya ta fita bayan ta k'ara yiwa HUYAAM ya jiki... gabad'aya su ya Zarah sun shigo d'akin idonsu gabad'aya Yana kan k'afar Huyaam Dake nannad'e da bandage.

Huda ta kalleta tace .


"Sannu HUYAAM".ta fad'a jikinta a Sanyaye.HUYAAM ta gyad'a mata kai Amma batai magana ba Dan ita tasan rad'ad'in da take ji. ya Zarah tai mata ya Jiki itama ,nan ma da ka ta ansa musu gabad'aya Saida kowa yaywa HUYAAM ya jiki harsu muneefa....
Ammie ta zauna bakin gadon tana kallan Huyaam data kwanta ta rufe Idonta hawaye na zubo mata . Ammie ta jawota zuwa jikinta tace ..


"Sannu HUYAAM zafi yake Miki ne?..."HUYAAM ta rufe fuskarta a k'irjin Ammei ta fashe da Kuka tace.


"zafi take mun Ammie".ta fad'a tana kan k'ame Ammie... Ammie tai rapping hannunta a bayan Huyaam tana lallashinta tace.


"Zai daina In Sha Allah da kinsha magani ne shikenan zai daina zaki samu sauk'i in Sha Allah.yanzu ki fara cin abincin tukunna sai Kisha maganin". Ammie ta fad'a cikin lallashi.


HUYAAM ta girgiza mata kai tace cikin dashashshiyar Muryar Wacce kuka ya gama cinyeta.


"Na k'oshi Ammie". Ammie ta girgiza kai tace.


"A'a HUYAAM rabonki da abinci fa tun d'azu da Rana Shima bana kirki kika cigaba saboda haka baza ki zauna ki kwana da yunwa ba". HUYAAM ta girgiza kai tana cewa ita ta k'oshi Ammie Bata saurareta ba ta kalli Huda tace.


"Huda jike kitchen ki Had'o mata tea da abinci". babu musu Huda ta ansa mata ta fita daga d'akin.babu dad'ewa Huda ta dawo d'akin rik'e da mug na tea sai turiri yake Yi ta Mik'awa Ammie kafin ta koma da d'auko plate d'in data zubawa HUYAAM Abincin ta ajiye nan kan table d'in Dake d'akin.


Ammie ta Kalli HUYAAM tace .


"tashi Kisha tea d'in saiki ci abincin". HUYAAM ta marai raice tace.

"Nidai Ammie iya tea d'in kawai zansha na k'oshi da abincin".ta fad'a kamar zatai kuka .Ammie tace.

"Naji to tashi Kisha".da k'yar ta mik'e Ammie ta shiga Bata a baki baifi kurb'a hudu tai ba tace ta k'oshi.ya haidar ne ya shigo d'akin rik'e da ledar maganin Yana kallan Ammie yace.

"Ammie gashi"ya fad'a yana Mik'a mata ledar maganin.. Ammie ta karb'a ta Bud'e bayan duba yadda HUYAAM d'in zata Sha .ya haidar kalli HUYAAM yace.


"Allah ya sawak'e Ammie saida safe". Ammie tace .

"Sannu da k'ok'ari Allah ya tashe mu lafiya".ya ansa da ameen Yana fita daga d'akin gabad'aya..


Ammie ta b'alli maganin ta d'auki gorar ruwa ta Mik'awa HUYAAM..nan HUYAAM ta d'auke kanta tace.


"Ammie banaso bazan shafa". Dan Huyaam Bata San magani ko kad'an saidai idan Ba'a cikin hayyacinta bane zata Sha .


Ammie tace cikin lallashi.


"Ki daure Kisha kinje HUYAAM D'ina".da k'yar Huyaam ta yadda ta karb'i maganin nan Tasha...bayan Tasha Ammie ta taimaka mata ta kwanta ya Zarah ta sauke numfashi tace.


"Allah ya sawak'e HUYAAM".Bata jira cewar taba ta Kalli Ammie tace.


"Ammie saida safe Allah ya K'ara lafiya..ta fad'a tana k'ok'arin juyawa zata fita daga d'akin.Ammie ta ansa mata da Ameen sai Kuma tai saurin cewa.


" Zarah ko zaki tafi da muneefa ta kwana agunki ni zan Kwana da Huyaam saboda bazan bari ta kwana ita kad'ai ba".babu musu ya zarah ta ansawa Ammie ta kama hannun muneefa suka fito daga d'akin. muneeb shima Yay wa Ammie sallama ya fita Huda ma taiwa Ammie bayan ta k'ara yiwa HUYAAM ya jiki har ta kai bakin k'ofa Kuma ta dawo tace.


"Laa! Ammie na manta d'azu Yaya yak'ira a wayarki yace idan Kun dawo na k'irashi".ta fad'a tana duba wayar Ammie.

Ammie tace .

"barshi kawai mayi waya da safe idan Allah ya kaimu".har Huda zata aje wayar sai Kuma taga Yana k'ira tace.


"Ammie gashi ma yana k'ira".ta fad'a tana mik'awa Ammie wayar Ammie ta karb'a ta kai kunne bayan tayi picking nan Huda ta fita daga d'akin bayan ta kullo Musu k'ofar....


Ammie tai sallama. daga D'aya bangaren Afeef Dake zaune a falonsa yana kallo ya ansa tare da gaida Ammie.. Ammie ta ansa masa nan yake tambayarta jikin Huyaam.ammie batai mamaki ba Dan tasan tunda Huda tace ya k'ira d'azu tofa itace ta fad'a masa nan Ammie ta ansa masa da da sauk'i.


Afeef yace.


"Allah ya K'ara lafiya".Basu Dad'e suna waya ba ganin yanzu a Nigeria dare yayi yasa yay mata sallama Ammie ta ajiye wayar tana kallon Huyaam Dake Sauke numfashi alamar har tayi bacci ta tashi ta d'auko bargo ta tufa mata ...Babu dad'ewa bayan Ammie ta zauna akai knocking k'ofar ta Bada iznin shigowa .Mai martaba taga ya shigo d'akin bak'insa d'auke da sallama.Ammie ta ansa masa har ya k'arasa shigowa cikin d'akin ya zauna kan sofan Dake d'akin Ammie ta gaidashi ya Ansa idansa yana kan k'afar Huyaam Dake nannad'e da bandage ya sauke numfashi yace.


D'azu haidar yace min Kun dawo ya Mai jiki?.."Ammie ta sauke numfashi tace.

da sauk'i rankai Dad'e".

Mai martaba ya Jin Jina kai yace.


"Allah ya K'ara lafiya". Ammie ta ansa da ameen.

Ya juyo Yana kallan Ammie yace.

"Yau kenan anan mamana zata kwana ko?"ya fad'a Yana yiwa Ammie Wani Irin kallo.Ammie tai murmushi saboda tagane kallan me yake mata kafin tace.

"Eh rankai Dad'e saboda ciwon nata banason na barta ita kad'ai ko Kuma ta kwana da Wani kar su fame mata ciwon".


Mai martaba ya Jin Jina kai yace.


"Hakan ma yayi Allah ya K'ara lafiya". Ammie ta ansa da Ameen Mai martaba Bai Dad'e a d'akin ba yay wa Ammie sallama ya fita daga d'akin gabad'aya .Ammie ta mik'e ganin Mai martaba ya fita ta sauke numfashi ta k'arasa wajen da HUYAAM ke kwance ta gyara mata k'afarta Mai ciwon wacce harta kumbura tai sun tumm ta girgiza kai cikin tausayawa sannan ta shiga toilet danyin wanka Dan Wani Irin zafi take ji.........





07066508376________
'þFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD


*<Ø9ß HUYAAM <Ø9ß*



*NA*



*__NAJA'ATU UMAR FAROOQ__*


*__(MRS SARAKIES =Ø‹Ü)__*



*Page 1þã 4þã *


*Tallah! Tallah!! Tallah!!!*


*Ina kuke hajiyoyin gidan nan,nace Ina kuke hajiyoyin gidan nan?to maza ku matso ga wata garab'asa ta zomu har inda kuke=؃Ü=؃Ü?.*


*Hajiya kaya Kikeso na fita kunya cikin taro ku Kuma so kike kallo ya koma akanki acikin Taron mata idan kika shiga biki ko suna ko Kuma Wani taro na musamman.to maza idan kina so ki kankarowa kanki mutunci kizo UK collection and gallery mu gwan gwajeki da kayanmu masu quality Wanda zaki gaji ki ajiye Dan kanki Amma badai ya mutuba Muna sai da kaya kamar haka=ØGÜ*


*Atamfofi da lesses*
*Abaya*
*Shadda*
*Hand bag*
*Shoe*
*Veil na manya Dana Yara*

*Socks rin hands made d'in nan masu net*.

*Hula ta 'yan Gayu*

*Siyan D'aya ko sari*

*Duk zaki samu kan Farashi Mai sauki kedai ki garzayo UK collection & gallery Kisha Mamaki*

*Domin ganawa damu ko magana damu kai tsaye ku tun tub'emu kai tsaye ta wannan number kamar haka*=ØIÜ08135305790

*Sai mun jiku =؃Ü=؃Ü=؃Ü*


<Ø9ß<Ø9ß<Ø9ß<Ø9ß<Ø9ß<Ø9ß


*Bismillahirrahmanirrahim*




PAGE 1þã 4þã


__________¡&


Washe gari da safe Huyaam na kwance saman gadon Ammie har wajen k'arfe 9 Bata tashi ba saboda sai bayan sallahn ASuba ma ta samu baccin ya d'auketa Dan daga ita har Ammie Basu Samu sunyi baccin kirki ba a daren jiya, saboda zugin da k'afar Huyaam take mata haka ta farka tsakar dare babu shiri tai ta kuka dole itama Ammie ta tashi take lallashin ta duk da dama bawai baccin take a lokacin sosai ba a lokacin .yanzu haka tana kwancen ta Bud'e idonta ta yunk'ura ta tashe zaune ta Jin jinar da jikinta a fuskar gadon ta lumshe idonta kamar Mai bacci Amma kuma ba baccin take ba....


Ammie ce tashigo d'akin rik'e da mug na tea sai turiri yake sai Huda data ke bayanta rik'e da tray Wanda ke d'auke da breakfast na huyaam.sanye take cikin shigar uniform na islamiya Dan Yanzu suke shirin tafiya.huda ta k'arasa har wajen table d'in Dake tsakiyar d'akin ta ajiye tray d'in kafin ta jawo shi zuwa gaban gadon inda Ammie ta zauna nan gefen gadon.Ammie ta ajiye cup d'in tea d'in tana kallan Huyaam data Bud'e ido tana kallanta kamo hannunta Ammei tai tace .

"Kin tashi?..." Huyaam ta gyad'a mata kai Amma batai magana.huda tai murmushi magana ce a Bakinta Amma tai shiru.ita abinda ya Bata mamaki ace yau Huyaam ce ta tashi i wannan lokacin ah lallai yau Babu lafiya sai Kumata furta a fili .


"sannu HUYAAM ya jikin?..." Huyaam ta kalleta ta motsa bakinta kad'an tace.


"Da sauki...."

Huda tace.

"Allah ya K'ara lafiya". gyad'a mata kai kawai Huyaam tai.


Ammie tace.


"Bari na kaiki kiyi brush ko?sai mu dawo kiyi breakfast d'in". HUYAAM ta gyad'a mata kai Huda ta k'araso ta Taya Ammie suka tai makawa Huyaam suka kaita har toilet d'in d'akin Huda ta tatsa mata maclean kan Wani sabon brush dake toilet d'in Ammie ta Mik'a mata Huyaam ta karb'a ta wanke bakinta bayan ta gama suka dawo da ita d'akin. Ammie ta tai Maka mata ta zauna kan gadon itama Ammien ta zauna Bakin gadon kafin ta Kalli Huda tace.


"Huda Mik'o tea d'in na Bata Tasha". Babu Musu Huda tai abinda Ammie tace mata ,Ammie ta matsa kusa da Huyaam sannan ta karb'i cup d'in tea d'in da Huda ke Mik'a mata ta kaiwa Huyaam bakinta, sipping hud'u Kawai tai tace ta k'oshi Ammie ta kalli cup d'in tea d'in sannan ta kalli HUYAAM tace cikin lallashi.


"Haba Huyaam please ki Bud'e bakin Kisha mana Kinga magani zaki Sha saboda k'afar nan taki tai saurin warkewa uhmm...." Ammie ta fad'a tana kallanta.huyaam ta ya Mutsa fuska kamar zatai kuka tace .


"Ammie I have no test in my mouth at All"ta fad'a cikin rawar murya.


Ammie ta kwantar da murya tace.


"Am sorry dear dama dole Kiji haka da kad'an kad'an bakin zai dawo normal okay please daure Kisha".ta fad'a tana kaiwa cup d'in bakinta da k'yar da k'yar Huyaam ta Bud'e bakin tasha tea d'in nan D'an kad'an ta rage nan Ammie tasa Huda ta zuba mata fargesun kayan ciki sai I Irish da suka soya iya farfesun kawai Ta iya ci shima ba sosai ba Ammie ta Maida plate d'in nan saman tray d'in tana kallan Huda tace.

"Mik'o min ledar maganin Huda". Babu musu Huda ta d'auko ledar maganin Dake nan saman drower ta Mik'awa mata.Ammie ta karb'a ta Bud'e ta b'alla ta bawa Huyaam da k'yar Huyaam ta iya had'iye maganin nan tana Yi tana ya Mutsa fuska kamar zatai amai . Ammie tace .


"Daurewa zakiyi Huyaam in Sha Allah soon zaki samu lafiya okay". Ya zarah ce tashigo d'akin Bakinta d'auke da sallama tana sanye cikin babban hijab har k'asa na islamiyar sune Hannunta Kuma rik'e Dana muneefa wacce ke sanye cikin shigar uniform na islamiya itama da dukan alamu islamiyar zasu tafi muneefa tace tana kallan Huyaam.


"Sannu ya Huyaam".ta fad'a tana zagawa ta D'aya side d'in da HUYAAM take zata haura saman gadon Ammie ta kalleta tace.


"A'a Ina zaki muneefa?..."muneefa ta tsaya daga hawa gadon tana Kallan Ammie tace cikin shagwab'a.

" zanje naga k'afar ne fa Ammie?.._

Ammie tace.

"A'ah! kuma baza ki iya Gani ahaka ba dole sai kin hau gadon salon ki fama mata ciwon oya dawo nan". Ammie Ta fad'a tana nuna mata kusa da ita .

Muneefa tai narai narai da ido kamar zatai kuka tace .


"Ammie bazan iya Gani a Hakan bafa?..." Ta fad'a tana tura Baki gaba .

Ammie ta saki Baki tana kallanta tace.


"muneefa ke makauniya ce da zakice bakya Gani ahakan?..." Muneefa ta gyad'a mata kai kamar zatai kuka. ba Ammie hatta Huyaam Saida tai dariya duk da yadda take d'in nan Huda tana dariya ta rik'o muneefa zuwa jikinta tace .


"Sorry Auta Ammie ce? Kiyi hak'uri kina gani a haka Aikoh?... muneefa ta gyad'a mata kai idonta sun ciko da k'walla.ya Zarah ta daina murmushin da take tana Kallan HUYAAM tace.


"Ya jiki Huyaam?..."Huyaam da itama ta daina dariyar da take Yi ta kalle ya Zarah tace ." Ina Kwana ya Zarah?".ya Zarah tai Murmushi tace.

"Lafiya lau Alhamdulillah ya Jikin?...". Huyaam tace.

"Da sauk'i Alhamdulillah".ya Zarah ta Jin jina kai kafin tace.


"Allah ya sawak'e". Sai Kuma ta Kalli Ammie tace .


"Ammie zamu tafi?". Ammie ta kalleta tace.

"Allah ya kiyaye?.sai Kuma ta kalli Huda ganin daga ita sai uniform ko hijab d'in ita Bata Saba.


"Huda itama ta Kalli jikinta ganin Irin kallon da Ammie take mata taga daga ita sai uniform ko hijab d'in Bata Saba Dan tama manta ma tace .


"Laa ya Zarah Dan Allah kijirani nima na Sako hijab D'ina".ta fad'a tana nufar Hanyar k'ofar fita daga d'akin Ammie tace.


"Huda" .

huda ta ansawa Ammie tana juyo.Ammie tace.

" idan kunje ki fad'awa ya USTAZ d'in naku HUYAAM Batada lafiya baza ta samu damar zuwa ba har sai ta samu lafiya". Huda tace .

"Eh In Sha Allah zan fad'a". Ammie ta Jin jina kai tace.

"kuje Allah ya kiyaye". Huda ta ansa da Ameen ta fita daga d'akin ya Zarah Kuma ta rik'o hannun muneefa suka fita daga d'akin......


Wajen k'arfe goma Saura akai knocking k'ofar d'akin Ammie lokacin har Huyaam ta koma bacci .Ammie data fito daga toilet ta Bada iznin shigowa.

Mai martaba ne ya shigo bakinsa d'auke da sallama Ammie ta ansa masa tana sunkuyar da kanta k'asa har Mai martaba ya k'arasa shigowa cikin d'akin ya zauna nan kan sofan Dake d'akin Ammie ta zauna bakin gadon ta gaida shi duk da sun gaisa da ASuba Mai martaba ya ansa mata Yana kallan Ammie yace .

"Ya jikin maman nawa?..."Ammie tace .

"da sauk'i Alhamdulillah Bata Dad'e bama da yin breakfast ta kwanta". Huyaam Da har bacci ya fara d'aukarta taji kamar Muryar Abban nasu ta juya Ganin shine da Gaske ta mik'e zaune Dak'yar ta Jin Gina jikin gadon tana murmushi tace.


"Sannu da zuwa Abba Ina kwana". Mai martaba yana kallanta yace.

"Yauwa mamana kin tashi Lafiya ya jikin naki". Huyaam tana Murmushi tace .

"Da Sauk'i Abba".Mai martaba ya Jin Jina kai yace.


"Allah ya K'ara lafiya". Huyaam tana Murmushi tace.

"Ameen".

Sai Kuma yace.

"yanzu babu inda yake Miki ciwo?..."

Huyaam ta gyad'a masa ka tace.

"Eh Babu komai Abba".

Mai martaba ya Jin Jina kai yace .


"Allah ya K'ara lafiya ". Huyaam ta ansa da Ameen.

Sai Kuma ya Kalli Ammie yace.


"Babu kumburun yanzu ne?..." Ammie ta kalli k'afar tace.


"Eh ba kamar jiya ba dai da sauk'i Yanzun". Mai martaba ya Jin Jina kai yace.

" in Sha Allah shima kumburin zai sab'e aide tana Shan magun gunan koh?...." Ammie tace.

"Eh tana Sha".Mai martaba yace.


"Allah ya sawak'e". Ammie ta ansa da Ameen.babu dad'ewa Mai martaba yay wa Ammie sallama ya nufi k'ofa Ammie tabi bayansa suka fita daga d'akin gabad'aya HUYAAM Kuma ta koma ta kwanta.


bayan Ammie ta raka Mai martaba nan Bakin k'ofar falon ta dawo cikin falon baba magajiya ta fito daga cikin din Dake downstairs ta k'araso falon da sauri.


"ta zugunna har k'asa ta gaida Ammie.Ammie ta ansa mata da kulawa.baba magajiya tana murmushi tace .


"Dama ranki Dad'e nazo ne naji ya Jikin Huyaam d'in?..."Ammie ta tace.


"da sauk'i magajiya Alhamdulillah". Baba magajiya tace.

"Allah ya Kara lafiya". Ammie ta ansa da Ameen tace..


"Bari naje magajiya kije bari na koma d'akin". Baba magajiya tace.


"To shikenan ranki Dad'e afito lafiya". Ammie ta ansa mata daga haka ta haura sama itama Baba magajiya ta mik'e ta shige kitchen d'in tana addu'ar Allah ya bawa Huyaam lafiya.....




____________¡&


Da yamma wajen k'arfe 4:30pm na yamman Ranar fulani Salamatu ta shigo b'angaren Ammie tareda rakiyar hadimanta Wanda suka tsaya Daga nan Bakin k'ofar falon Amma Basu shigo ba suka tsaya suna zaman jiranta.

Da sallama fulani Salamatu ta shigo main falorn bata k'arasa shigowa cikin ciki ba sai ta tsaya daga nan k'ofar falon tana sallama cikin shiga ta Alfarma sai Wani walwali takeyi.baba magajiya Dake kitchen ta fito da sauri jin sallama ganin Fulani Salamatu ce yasa ta k'araso falon cikin sauri ta duk'a a gabanta ta sunkuyar da kanta cikin girmamawa tace .


"Barka da Zuwa ranki Dad'e". fulani Salamatu ta kalleta da k'yar ta iya ansawa tace.

"Kije ki fad'awa uwar d'akin ki Isowa ta".tana fad'ar haka taja bakinta tai shiru.baba magajiya ta k'ara sunkuyar da kanta k'asa tace.

"An gama ranki Dad'e".daga haka ta Mik'e ta haura sama zuwa d'akin Ammie Dan sanar mata .babu dad'ewa Ammie ta sauko itama cikin shiga ta Alfarma ta k'araso saukowa daga stairs d'in ta shigo falon tana kallon fulani Salamatu da mamakin Mai ya hanata zama tace.


"Sannu da zuwa fulani ki zauna mana".ta fad'a tana murmushi Fulani Salamatu ta k'arasa ta zauna kan kujera tana kallan Ammie .Ammie ta Kara fad'ad'a murmushinta tace.


"Barkanmu da yamma Fulani fatan mun yini lafiya?..."babu yabo babu fallasa Fulani Salamatu ta ansawa Ammie kafin tace.

"Ya mai Jiki Kuma?..."Ammie tai murmushi tace.

"Jiki da sauk'i Alhamdulillah yasu Waleeda?..." Fulani Salamatu tace.


"Lafiyansu lau". Ammie tace.

"Masha Allah".shiru ne ya biyo Baya harna tsawan 2 minutes Babu Wanda ya K'ara magana acikinsu har baba magajiya ta cikawa Fulani Salamatu gabanta da ruwa fa drink's sai fruits sannan tabar wajen kallo D'aya taiwa kayan ta kauda kanta sai can fulani Salamatu ta mik'e tace.


"Bari na tafi ".


Ammie ta mik'e tace.

" tafiya kuma Fulani ko ruwa fa Baki shaba?..."Fulani Salamatu tace.


"Eh Alhamdulillah Nasha ruwa sai anjima". daga haka tai hanyar k'ofar fita".Ammie ta bita da kallo tana mamakin Irin halin fulani Salamatu yadda ta d'auke take mata kallan kishiya har yau Dan ita in ta itane wallahi ba zaman kishi take da Fulani Salamatu ba Amma fulani Salamatu ita ta

Please Login or Register in order to submit comment