Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana wani tura Baki gaba.fulani salamatu tace. "Ai nace miki zan fad'a masa ko?.." sai alokacin Aziza ta saki ranta tace.
" Shikenan good night ". fulani Salamatu tace. "Allah ya tashe mu lafiya".daga Haka ta juya ta tafi ta haura stairs. Fulani Salamatu tabita da kallo sai Kuma ta d'auki tray d'in tea d'in data dafa tai b'angaren mai Martaba dashi......





#<9 HUYAAM
#<9 LAMID'O
#<9 AZIZ CHIROMA
#<9 AFEEF




*Muje zuwa mutanan MRS SARAKIES =؋.ke daga Jin salon labarin kinsan zai k'ayatar ya Kuma fad'akar.akwai chakwakiya sosai anan gaba Dan labarin ma yanzu muka fara shi*.


*ga masu buk'atar fara payments zaku iya sa kud'inku a yanzu before mu gama free pages Regular group akan naira 500 kacal idan kuma muka gama Free pages zai koma 700 ne.ga masu buk'atar Vip Kuma 2 pages a Rana zaku iya biyan nai 1000 kacal. ku hanzarta ku fara biya tun kafin mu gama free pages.zaku iya tura kud'in ta wannan account d'in =G*


2270127432 Naja'atu umar
Zenith bank

Evidence of payment (shaidar biya )via
07066508376

Da zarar mungama free pages Kuma zamu sa duk Wanda ya biya kud'in sa a paid group, karku bari ayi wannan tafiyar Babu ku =؃=؃ mutanan arziki.





07066508376________
'Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD



*<9HUYAAM <9*



*NA*



*__NAJA'ATU UMAR FAROOQ __*



*__(MRS SARAKIES =؋)__*



PAGE 2 2


*Tallah! Tallah!! Tallah!!!*


*Ina kuke hajiyoyin gidan nan,nace Ina kuke hajiyoyin gidan nan?to maza ku matso ga wata garab'asa ta zomu har inda kuke=؃=؃?.*


*Hajiya kaya Kikeso na fita kunya cikin taro ku Kuma so kike kallo ya koma akanki acikin Taron mata idan kika shiga biki ko suna ko Kuma Wani taro na musamman.to maza idan kina so ki kankarowa kanki mutunci kizo UK collection and gallery mu gwan gwajeki da kayanmu masu quality Wanda zaki gaji ki ajiye Dan kanki Amma badai ya mutuba Muna sai da kaya kamar haka=G*


*Atamfofi da lesses*
*Abaya*
*Shadda*
*Hand bag*
*Shoe*
*Veil na manya Dana Yara*

*Socks rin hands made d'in nan masu net*.

*Hula ta 'yan Gayu*

*Siyan D'aya ko sari*

*Duk zaki samu kan Farashi Mai sauki kedai ki garzayo UK collection & gallery Kisha Mamaki*

*Domin ganawa damu ko magana damu kai tsaye ku tun tub'emu kai tsaye ta wannan number kamar haka*=I08135305790

*Sai mun jiku =؃=؃=؃*


<9<9<9<9<9<9



*Bismillahirrahmanirrahim*


____________&


Yau dai da shirye shiryen tarb'an Bak'i mata aka tashi acikin masarautar kano.Bak'in Kuma ba wasu bane face Dangin angon ya Bahijja ne zasu kawo lefenta. tunda bikin yau Saura wata D'aya da sati biyu. Ita ya zulaihat ba yanzu za'a kawo nata ba tunda Dangin mijin da zata aura d'in basa k'asar sai sun dawo sannan za'a kawo natan. A b'angaren su Hajiya Lubabatu kuwa masu girki suka d'auko na musamman wad'anda suka San kan aikinsu a fannin girke girke kama daga fannin abinci Dana kayan fulawa ,zamu iya cewa ma wannan b'angaren suka karanta. Kayan snacks ne kawai da kaji ake sarrafasu kala kala a Cikin k'aton kitchen d'in Dake b'angaren Hajiya Lubabatu.sannan Kuma Hajiya Lubabatu na zuwa Tayi monitoring d'insu time to Time idan taga Wani abun da Bai mata ba tai musu magana su gyara Dan tace kayan fita kunya ne Wanda za'a tarb'i Bak'in dashi wanda ko agaba idan zasu Bada labari zasuce masarautar kano kaza kaza Babu k'arya anyi komai cikin girmama da mutunci.yanzu haka ma saukowarta downstairs kenan daga d'akin ta take k'arfe 10am na safe ta nufi hanyar kitchen d'in Wannan Karan shine zuwanta na uku kenan tana zuwa tana duba su karsuyi mata abinda Bai mata ba duk da kuwa tasan sun k'ware wajen aikin nasu Amma dai komai sai anayi ana Saka ido .tsayawa tai daga nan k'ofar kitchen d'in bayan ta Isa tana kallansu Sai Kuma ta k'arasa wajen Wanda suke soya kaji gabad'ayansu suka duk'a har k'asa sunai mata barka da zuwa tare da gaisheta lokaci D'aya, Dan indai ta shigo to Saida sun K'ara gaisheta.ansa musu tai Babu yabo babu fallasa kafin tace. "kun ware Wanda za'ayi papper chicken d'in dasu Aiko?..." Ta fad'a da sigar tambaya.cikin girmamawa wacce ita zatai aikin tace. "Eh ranki Dad'e an ware". Hajiya Lubabatu ta Jin jina kai kafin tace. "Shikenan nidai abinda nakeso daku shine please kuyi min Aiki Yadda ya kamata Dan Allah kada kusa naji kunya a gaban manyan mutane". Ta fad'a da sigar worning. Cikin girmamawa suka ansa mata da in Sha Allah. Ta Jin jina kai sannan ta juya zata fita suka bita da fatan Sauka lafiya....


K'arfe shad'aya da mintuna ya Zarah ce tsaye a falon su cikin Shigar hijab har k'asa zata fita school yau lecture d'in tasu ta Rana ce k'arfe shabiyu, Huyaam take jira zata kawo mata ruwa a kitchen Amma shiru kamar Wacce aka aiki bawa garinsu bata dawo ba, Dan tafi minti D'aya a kitchen d'in. d'aga murya ya Zarah tai tak'ira sunanta da "Huyaam wai me kikeyi ne a kitchen d'in tafiya fa Zanyi time na tafiya kefa nake jira". Ta fad'a cikin k'osawa.Huyaam ta fito da sauri tana goge hannunta tana murmushi tace. "Kai ya Zarah sai kace wacce na Dad'e bandawo ba". Ya Zarah ta karb'i ruwan tana harararta tace. "Aikema kin sani idan kin dad'e d'in idan ma Baki Yi ba".ta fad'a tana karb'ar ruwan daga hannun Huyaam sannan tasa acikin jakar ta ta. Ya Afeef ne ya sauko falon cikin shigar kayan sarauta Wanda sukai masa bala'in kyau Dan sai wani tashin k'amshi yakeyi ta ko Ina .kallansa Huyaam takeyi harya k'arasa saukowa downstairs d'in ido hud'u sukai da Huyaam da Bata daina kallan Saba dan babu K'arya wankan Dayay yayi masa bala'in Kyau ya D'an tsuke fuska Hakan yasa HUYAAM tai dariya tace. "Wallahi Yaya kayi kyau sosai". Ta fad'a har dimples d'inta suna lostsawa hagu da dama Wanda ke K'ara mata kyau.bai ansa ba yace.

"Ina Ammie take?..."kafin ta bashi ansa Ammie ta sauko downstairs d'in ta k'araso har tsakiyar falon tana kallan Huyaam tace .

"Ina Huda take?..." HUYAAM tace.

"tana d'aki ai Baki ganta bane ba". Ammie tace.

" na lek'a d'akin banganta taba". Ya zarah tace. "Tana d'akina tana graya min kayana". Ammie ta Jin jina kai.
" tace shikenan". Afeef ne ya
K'araso har gaban Ammie ya D'an zame hular kansa sannan ya duk'ar da kan nasa agaban Ammie Hakan yasa Ammie ta D'ora hannunta kan nasa tana murmushi ta shafa kan nasa tace .


"Allah yay Maka albarka Ina zuwa haka?...." Ya d'ago yana Maida hukar kansa yace.

"Zanje school d'in su Zarah ne akwai abinda zanje nayi". Ammie ta Jin jina kai tace. "Masha Allah! Sai ka dawo". ya Zarah da take tsaye zata gaida shi kafin ta tafi tace."Yaya ko zaka saukeni ne". Ta fad'a a d'ad'are Dan tasan bama d'aukar tata Zanyi ba . Amma ga mamakinta sai taji yace. "Ok".daga haka yay hanyar fita daga falon Huyaam na Jin haka tace. "Yaya Nima na biyoka sai mu dawo tare ko juyowa Bai yi ba balle ya ansa mata.ya Zarah tabi bayansa da Sauri bayan tai ma Ammie sallama.bayan fitar su Ammie na kallan Huyaam tace. "To idan ya tafi Dake d'in Ina zai kaiki?..."Huyaam tai shiru tana kallan Ammie". Ammie girgiza tace. "Wuce ki k'iramin Huda idan ta gama akwai aikin da zan saku". Babu musu HUYAAM ta haye sama da sauri.Ammie Kuma ta samu waje ta zauna a falon tana jiransu........


K'arfe biyu sauya fulani Salamatu ce tsaye a Wani k'aton store Dake b'angaren Hajiya Lubabatu inda aka ajiye kayan tarb'ar Bak'in anyi packaging d'insu an kammala komai tun Wajen k'arfe D'aya ,sannan an ajeye komai a inda ya dace komai yayi Masha Allah Bak'in kawai ake jiran zuwan nasu ta bakin na Hajiya Lubabatu Dake cewa ayi komai cikin girmamawa aikuwa anyi d'in Dan Babu laifi sunyi abu cikin girmamawa anyi Abun fita kunya sosai.Fulani Salamatu ta juyo tana kallon hajiya Lubabatu bayan ta gama ganin Komai tace. "K'awata komai yayi yadda ya dace Babu Wanda ya isa ya Raina mu gaskiya mutanan nan sun iya aiki sunyi komai yadda ya dace". Ta fad'a tana kallan Hajiya Lubabatu... Hajiya Lubabatu tace. "Babu laifi Nima naga k'ok'arinsu gaskiya sun iya aiki". Fulani Salamatu tace. "sosai ma kefa su suke yiwa gidan governor kano duk Wani kwangila da za'ayi indai anan government house d'in ne taro ko biki ke duk Wani Wanda yake ji da kansa a garin kano indai Yana so ya fita kunyar Bak'i na b'angaren abinda zai tarb'esu to ya k'irasu Dan sun iya aiki". Hajiya Lubabatu tace. "Gaskiya nima na shaida Kuma na Yaba musu". Fulani Salamatu tace. "To ni dai bari na koma tunda dai naga abinda ya kawonin anjima kafin suzo zan dawo saboda mu shirya komai yadda ya dace". Hajiya Lubabatu tace. "Gaskiya ne to Dan Allah ki dawo da wuri". Tace. "In Sha Allah da wuri zan dawo". Daga haka ta fita daga store d'in Hajiya Lubabatu na biye da ita har zuwa falon hadimar ta karima da tai mata rakiya ta mik'e daga zuben da take a falon tabi bayan ta bayan taiwa Hajiya Lubabatu sallama cikin girmamawa.......



___________&


K'arfe Hud'u da Rabi na Ranar Ammie ce ta fito cikin shiga ta Alfarma itama tayi bala'in kyau ba kad'an ba Dan kamar ba wacce ta haifi yara d'ai d'ai har bakwai ba . sanye take cikin Wani ubansun less Wanda yalashe mak'uden kud'ad'e ta D'ora alkyabba akai Mai tsadar gaske sai Wani walwali take kamar wacce zata gasar kyau tana kallan su Huyaam Dake zaune falon su biyu sai muneefa shi muneeb Bai dawo ba tunda ya fita sallahr ASR ya haidar kan dama Yana wajen aiki nan companyn Mai martaba Dake jihar kano, ya Zarah ma tunda ta fita school Bata dawo ba .garama Afeef ya dawo d'azu Dan Bai Dad'e da sake fita ba.tana kallansu tace.

"Huyaam ku zauna zanje b'angaren Hajiya Lubabatu zamu tarb'i Bak'in nan".so banaso na ganku ko a compound ne kunji ai?.." duk da tasan ba fitar suke ba, kuma baza su fara yanzu ba amma dai tana musu worning ne.dayake yau alhamis babu Islamiya Kuma Babu inda zasu yasa suke Zaune a falon bayan sun gama karatun Al'qur'ani d'azu da sukai ASR prayer.har Suka had'a Baki wajen ansa mata da to kafin HUYAAM tace. "Ammie Kinga yadda kikai kyau kuwa?..." Ta fad'a cikin zuzu tawa .Ammie tai mata murmushi tace. "Ni bangani ba kece dai kika Gane min". HUYAAM tace . "Ai kuwa kinyi kyau sosai sai Kin dawo". Tace. "Allah yasa" ta fad'a tana gyara zaman alkyabbar jikinta.hadimarta baba magajiya itace take tsaye daga Bayan Ammie Dan ita zatai mata rakayi har b'angaren Hajiya Lubabatun .Ammie tai gaba Baba magajiya na biye da ita da Jakarta a hannunta tana ansawa muneefa Dake mata adawo lafiya.huyaam sukabi Ammie da kallo har ta fice daga falon gabad'aya.. Ammie da taje b'angaren Hajiya Lubabatu ta iske Fulani Salamatu tare da k'awar tata dukansu suma cikin shiga ta Alfarma kowacce Tasha less sai Wani walwali sukeyi. Fulani Salamatu sai Wani jiji da kai take da k'yar ta iya ansa sallamar da Ammie tai musu har suka gaisa Amma ita Hajiya Lubabatu da yake ita tasan ta kan duniya faran Faran suka gaisa da Ammie har take cewa "Fulani nayi fushi Kuna manyan iyaye sai Yanzu kuka zo? Ammie dai murmushi tai tace ai mata afuwa haka nan tai ta janta da zance kamar ba ita bace take zaginta idan suka had'u da Fulani Salamatu ba .itama kanta Fulani Salamatu kallan Hajiya Lubabatu take da mamakin yadda ta sakewa Ammie Amma Kuma batai magana ba tai shiru tana kallan iKon Allah.k'annenn Hajiya Lubabatu da 'yan uwanta da sisters d'in ta duk sunzo dasu za'ai tarb'an bakin suka risina suka shiga Gaida Ammie cikin girmamawa, Ammie ta ansa musu itama da kulawa, sisters d'in su baba turaki dai suna hanya Basu k'araso ba Amma ance saua k'iris su k'araso iya k'anwarsu ce D'aya da ba'a nan take AURE ba bazata samu damar zuwa ba.Ammie na nan zauna kusa da antyn su Ikleema Babu dad'ewa saiga Hajiya Aysha nan wato maman su safna, nan suka zauna suke gaisawa.ita dai Hajiya lubabatu ta juyar da kanta gefe sai faman latsa wayarta takeyi.......



K'arfe Hud'u da mintuna arba'in Bak'in suka iso bayan 'yan uwan su Mai martaba sun zo .take dogarayen Dake Bakin gate d'in suka mik'e aka wangale musu gate d'in. wasu Manyan Manyan motoci ne suke ta shigowa k'aton compound d'in kamar bazasu k'areba Dana k'irga su d'ai d'ai har guda biyar hud'u Bak'in da suka kawo lefan ne sai d'ayar Wacce itace k'atuwar ciki nai K'irar limozing wacce a itane aka sako lefen aciki.bayan drivers d'in sunyi parking haka suka fito suka bud'e duka motocin tareda matsawa baya Dan bawa wad'an da suke ciki damar fitowa sannu a hankali naga wasu manyan mata suna fitowa daga cikin motar D'aya Bayan D'aya har suka gama fitowa gabad'aya.Dana k'irgasu su su goma sha hud'u ne cif cif dukkansu cikin shiga ta Alfarma Babu K'arya gaskiya sun Sha suturu keda kingansu kinsan badaga k'aramin gida suka fito ba.drivers d'inne suka fiddo da manyan boxes d'in suna shiga dasu inda aka ce nan zasu kai. Ka'nnen Hajiya Lubabatu ne su biyu suka fito zasu shiga da Bak'in nan b'angaren nata. Bayan sun iso sukai musu barka da zuwa tareda Yi musu jagora har zuwa b'angaren.da sallama abakinsu suka shiga falon lokacin har angama kawo akwatunan suna nan an ajiye anan tsakiyar k'aton falon. Ammie da fulani Salamatu duk suna zaune saman kujera guda biyu ajere sai su Hajiya Aysha da antynsu safnah harda ma ita Kanta Hajiya Lubabatun duk suna zaune.

Bak'in ne suka shigo bakinsu d'auke da sallama gabad'aya aka ansa musu da kulawa ana basu wurin zama suka k'arasa suna k'arewa mutanan Dake falon kallo ko ba'a fad'a musu ba sun San Ammie dai itace matar sarkie ita da fulani Salamatu saboda yadda shigar su ta fita daban dana sauran mutanan Dake falon Basu zauna kan kujerar da ake tai Musu tayin su zauna ba sai da suka zo har gaban su Ammie suka kwashi gaisuwa a wajen su.duk suka ansa musu da kulawa sannan suka mik'e suka k'arasa wajen zamansu Dama a gaban sarakai duk mun kud'inku da mulkinku kune dai a k'asan su dole sai ambasu wannan Girman. Zama sukai akan kujera wasunsu Kuma a k'asa kan k'aton carpet d'in da aka shimfid'a musu awajen.K'ara gaisawa sukai cikin girmamawa aka kawo musu ruwa da drink's da abincin da kai musu mu duk babu abinda suka tab'a.sannan akai addu'a aka shiga Bud'e kaya. Akwatuna ne guda 24 cif cif Wanda kowanne suke shak'e da kaya mak'il .Gud'a ce kawai ke tashi a falon nan Dan ko Wacce a kwati da za'a Bud'e sai anyi Gud'a kayane Wanda suka ansa sunansu kaya Wanda aka kashe mak'udan kud'ad'e wajen siyan su Masha Allah! kawai ake ta furtawa. haka aka gama Bud'e kaya da naiya million Daya kud'in D'inki nan ma wata gud'ar ce ta K'ara tashi Dan suma Dangin angon suna da sarauta Kuma 'yan kasuwa ne Dan baban angon shattiman kano ne suna da kud'i Babu laifi .haka aka gama Bud'e kaya aka rufe Taro da addu'a kafin nan Bak'in suka fara shirin tafiya suma an Basu kud'in takuici naira dubu D'ari takwas Wanda Ammie ce ta ciro acikin Jakarta ta Bada, kuma karkice Rance a'a kyauta ta Bada .Dan Da million Daya tai niyyar bayarwa to taga su sun bada million Daya kud'in D'inki yasa tace kawai karsukuga anrainasu yasa ta Bada dubu Dari takwas d'in.mamakine ya kashe kowa ganin Ammie ta Bada wannan uban kud'in kafin Hajiya Lubabatu ta d'auko ta Basu . Fulani Salamatu kamar ta mutu Dan haushi Dan ta tsani ace Ammie tai Abu ita batai ba musamman ma agaban bak'uwar fuska .da tasan hakane da ita zata Bada wannan kud'in Amma sai gashi Ammie tai mata kisan gilla agaban mutane tasan duk inda akaje haka za'a ce matar saiki tai kaza tai kaza ita batai ba, Amma Haka nan ta shanye ta nuna farin ciki itama Batasan Hajiya Aysha na lura da ita ba.da k'yar suka Karb'a suna ta godiya Ammie tasha kirari Wanda k'iris ya rage Fulani Salamatu tai bindaiga saboda haushi. Sai Kod'a Ammie ake kamar me.kayan da akai musu da Wanda Basu ciba da wanda za'a Basu su tafi dashi aka d'auko aka Rakasu dashi har gaban motarsu sun rabu cikin aminci suna ta godiya suka shiga motocin da suka zo acikinsu bayan sun shiga drivers ma haka aka Bud'e musu gate suka fice daga gidan D'aya bayan D'aya har suka gama fita gabad'aya..bayan tafiyarsu suma su Ammie duk tafiya sukai bayan sunyiwa Hajiya Lubabatu sallama tareda da Bak'in nata sai aka Bar iya k'awarta Fulani Salamatu sai sisters d'in su baba turaki Wanda suka ce zaso zo b'angarensu Ammie kafin su tafi zuwa anjima........




#<9 HUYAAM
#<9 LAMID'O #<9
#<9 AZIZ CHIROMA
#<9 AFEEF




*Muje zuwa mutanan MRS SARAKIES =؋.ke daga Jin salon labarin kinsan zai k'ayatar ya Kuma fad'akar.akwai chakwakiya sosai anan gaba Dan labarin ma yanzu muka fara shi*.


*ga masu buk'atar fara payments zaku iya sa kud'inku a yanzu before mu gama free pages Regular group akan naira 500 kacal idan kuma muka gama Free pages zai koma 700 ne.ga masu buk'atar Vip Kuma 2 pages a Rana zaku iya biyan nai 1000 kacal. ku hanzarta ku fara biya tun kafin mu gama free pages.zaku iya tura kud'in ta wannan account d'in =G*


2270127432 Naja'atu umar
Zenith bank

Evidence of payment (shaidar biya )via
07066508376

Da zarar mungama free pages Kuma zamu sa duk Wanda ya biya kud'in sa a paid group, karku bari ayi wannan tafiyar Babu ku =؃=؃ mutanan arziki.






07966598376________
'Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD


*<9HUYAAM<9*



*NA*



*__NAJA'ATU UMAR FAROOQ __*



*__(MRS SARAKIES =؋)__*



PAGE 2 3



*Tallah! Tallah!! Tallah!!!*


*Ina kuke hajiyoyin gidan nan,nace Ina kuke hajiyoyin gidan nan?to maza ku matso ga wata garab'asa ta zomu har inda kuke=؃=؃?.*


*Hajiya kaya Kikeso na fita kunya cikin taro ku Kuma so kike kallo ya koma akanki acikin Taron mata idan kika shiga biki ko suna ko Kuma Wani taro na musamman.to maza idan kina so ki kankarowa kanki mutunci kizo UK collection and gallery mu gwan gwajeki da kayanmu masu quality Wanda zaki gaji ki ajiye Dan kanki Amma badai ya mutuba Muna sai da kaya kamar haka=G*


*Atamfofi da lesses*
*Abaya*
*Shadda*
*Hand bag*
*Shoe*
*Veil na manya Dana Yara*

*Socks rin hands made d'in nan masu net*.

*Hula ta 'yan Gayu*

*Siyan D'aya ko sari*

*Duk zaki samu kan Farashi Mai sauki kedai ki garzayo UK collection & gallery Kisha Mamaki*

*Domin ganawa damu ko magana damu kai tsaye ku tun tub'emu kai tsaye ta wannan number kamar haka*=I08135305790

*Sai mun jiku =؃=؃=؃*


<9<9<9<9<9<9


*Bismillahirrahmanirrahim*


_____________&


*Masarautar zazzau*


Thursday day,11:20am


Wata matashiyar yarinya ce k'arama wacce a shekaru a k'alla baza ta wuce 13 year's ba, Zainab kenan Mai sunan inna Babar Mai martaba wato sarkin masarautar zazzau na yanzu.saukowa take daga stairs d'in da zai SADA ta da k'aton falorn wannan b'angaren. dogowar rigar abaya ce a jikinta bak'a Mai adon stones sai Wani walwali suke Yi wacce ta fito da ainihin haskenta domin farace K'al kamar ki tsaga Jikinta kikaga jini haka fatarta take, wajen kyau kuwa kamar ki sace ta ki gudu Dan kyau, bak'in gashinta Wanda yake har saman goshinta Wanda ya K'ara fito da ainihin kyanta anyi mata parking d'insa anan tsakiyar kanta sai mayafin abayar data D'ora anan saman kanta Amma Kuma Hakan Bai Hana gashin kan nata lek'awa ta k'asan mayafin ba. hannunta Kuma rik'e yake da Wani glass bowel madai daici Dake shak'e da kayan fruits. sannu a hankali take tafiya cikin nutsuwa harta gama saukowa downstairs d'in, Wani D'an corridor tabi Wanda zai SADA ta da d'akin matar gidan wato amaryar Mai martaba Mai suna gimbiya Aysha!, Bud'e k'ofar bedroom d'in tai bayan ta isa tai knocking k'ofar. "shigo". haka aka fad'a daga ciki . bakinta d'auke da sallama ta shiga d'akin ta tarar da wata matashiyar mata wacce a k'alla a shekaru zatai 28 years haka.sai wacce ke kwance a saman gadon kanta saman filo an lullube'ta da bargo har saman kanta.kamar babu lafiya dai a yadda naga yanayin nata. "sai yanzu kika dawo?..." Matashiyar matar Dake zaune gefen gadon tai mata tambayar tana tsare Zainab wacce ake K'iranta da Anam da ido.Anam ta k'araso cikin d'akin bayan ta rufe k'ofar ta ajiye bowel d'in hannunta nan saman table d'in Dake gab da gadon kusa da matar ta marai Rai ce tace. "babu a kitchen d'in downstairs fa Saida na Haura sama". Ta fad'a tana fiki fiki da ido .Matar na kallonta tace. "ai dama bance kije kitchen d'in downstairs fa Anam haka nace Kije sama ki kawo mata,bance ki Daina zuwa kitchen d'in downstairs fa?..."Ta fad'a da sigar worning.Anam ta D'an rausayar da kanta tana kallan matar tace. Na manta ne Anty". Matar ta d'auke kanta daga kallanta ta d'auki bowel d'in ta rik'e a hannunta sannan ta kai hannunta ta yaye blanket d'in da matar take ciki ta kaishi dai dai kirjinta, Bud'e idon tai tana kallan anty Amina idanuwanta a kumbure bakinta a bushe kamar Wanda ba'a kula dashi ,sai dai a'a ba haka bane ba ana kula dashi har ita Kanta matar yadda ya kamata.anty Amina ta sakar mata murmushi tai k'asa da murya dai dai yadda zata jita tace cikin lallashi da kalamai masu da Dad'i da ratsa zuciya Wanda a kullum take mata su . "Yaya gimbiya ga fruits d'in an kawo Miki wanne zakici water milon ko Kuma bana nan?." Ta fad'a tana kallanta kamar Wanda zata ansa mata .sai kuma ta cigaba tace. "Anam ce ta yanko Miki da kanta Kamar yadda kika buk'ata".ta k'arasa fad'a tana sakar mata murmushi.gimbiya Aysha ta lumshe idonta.hakan yasa anty Amina ta Gane Mai take nufi bi ma'ana dai zata Sha d'in kamar yadda anty Amina ta tambayeta.mik'ewa Anty amina tai ta dag'o da Gimbiya Aysha sannan ta jinginar da ita jikin gadon bayan ta tokare ta da filos yadda baza ta fad'i ba. Ganin ta zaunarta dai dai yasa ta d'auki bowel d'in ta fara Bata water milon d'in a Baki Wanda da k'yar ma take Sha Dan Saida dabara inba haka ba gabad'aya zubewa zai dingayi tun kafin ma yaje bakin nata .Anam dai ta haura saman gadon tana zaune kusa da mamar tata ta rik'o hannunta tana kallan yadda take shan fruits d'in cikin tausayawa.kallanta kawai take kamar ta samu TV..Bata shanye fruits d'in ba ta lumshe idonta alamar ta takoshi Hakan yasa anty Amina ta ajiye a nan kan table d'in ta Kalli Anam tace. "Mik'o min tissue na goge mata bakin?..." Matsawa Anam tai daga kusa da maman nata ta Sauka Saman gadon ta k'arasa gaban mirror ta d'auko  
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~tissue ta dawo ta Mik'awa anty Amina.anty Amina ta karb'a ta goge mata Bakinta da duk inda water milon d'in nan ya Bat'a mata Jiki.knocking d'in k'ofar akayi anty Amina ta juya tana kallon k'ofar kafin tace. "Waye?....". Baba uwani ce tai magana da nice Hakan yasa anty Amina Bata iznin shigowa.....


Da sallama a bakin Baba uwani ta shigo d'akin ta K'araso ciki tana kallon anty Amina da ladabi tace. "Yauwa gimbiya Amina nace na gama bari na shiga na Had'a ruwan wanka yanzu ko?..." Ta fad'a tana kallan anty Amina..Anty Amina tace. "Eh to baba jeki had'a d'in".baba uwani ta ansa mata da to Sannan ta shiga toilet d'in Dake cikin d'akin. Babu dad'ewa ta fito tana kallon anty Amina tace. "Na had'a". Anty Amina tace. "To zo mu kamata sai akaita ai matan". Babu musu baba uwani ta matso suka kama gimbiya Aysha wacce babu inda yake motsi ajikinta suka shigarta cikin toilet d'in da dabara da komai .kafin su fito har Anam tashi ta canza bedsheets d'in saman gadon tasa Wani ta graya d'akin ta kunna borner sannan ta fita da bowel d'in zuwa kitchen. Tana dawowa d'akin ta tarar har amfito da gimbiya Aysha anty Amina ma tana shiryata, k'arasawa tai cikin d'akin ganin ansa wa gimbiya Aysha wata doguwar riga marar nauyi Mai bala'in tsada sai gashinta Wanda har yau Yana nan saidai raguwar da yayi kad'an anty Amina ta gyara mata

Please Login or Register in order to submit comment