Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Hajara tai taiwa Hajiya inna sallama sannan ta bar falon gabad'aya cikin sauri.Hajiya inna ta bita da kallo harta bar falon kafin ta sauke numfashi ta haura sama Dan zuwa d'akin gimbiya Aysha ta tambayi anty Amina Mai ya kawo Hajara wannan b'angaren Kuma duk da tasan bazai wuce dubiyar data Saba zuwa bane ya kawo taba.....



K'arfe 8 da mintuna na dare Ammie ce ta sauko downstairs tana waya. su ya Zarah ma Dake zaune a falon downstairs d'in suka juya suna Kallan Ammein data shigo falon tana waya harta zauna nan Saman kujera tana cewa. "Khadija ki bari dai zan fad'awa Mai martaba idan ya amince in Sha Allah zasuzo ko one week ne sai suyi miki".ta fad'a tana murmushi.Daga can b'angaren Anty khadija tace. "Indai Mai martaba ne Koda kaina nai Masa magana bazai hana su Huyaam zuwa wajen hutu ba Anty! ,kawai dai k'ila kece bakyason Rabuwa da yaranki". Ammie tai murmushi tace. "To ki k'irashi mana ni wallahi da kin hutashsheni ma". Anty khadija tace. "A'a ki Dai tambayar min kawai Anty" Ammie tace. "To shikenan in Sha Allah zuwa gobe zakiji feedback". Anty khadija tace. "To shikenan nagode sosai Anty ki Gaida min da yarana". Ammie tace. "Zasuji in Sha Allah Nima ki Gaida min da nawa yaran" anty khadija ta ansa mata nan dai sukai sallama Ammie ta kashe wayar tana kallon su Huda Dake kallanta. Huyaam tace. Ammie dawa kike waya?." Ammie na murmushi tace. "Da mamanku Khadija Mana wai ta dage sai an kawo ku kunyi hutu ni Kuma ba bawai banason kuje bane islamiya ce banason kuyi missing".Huda tace. "Ammie gobe fa asabar zamu fara exam kuma one week kawai zamu kai muna exam d'in Kuma fa hutun 3 weeks za'a bamu Dan Allah Ammie idan muka gama ki barmu muje?."ta fad'a tana kallan Ammie.Huyaam kan da Murna ce ta kamata Jin zasuje Abuja tana kallan Ammie tace. "Dan Allah Ammie ki barmu muje idan mun gama". Ammie ta Sauke numfashi tace "to bari dai Mai martaba ya shigo idan na tambayeshi idan ya barku to sai kuje d'in" nan suka ce in Sha Allah ma zai barsu ya Zarah dai kallansu kawai take Amma Batace komai ba haka ma muneefa. suna zaune a falon har Wajen k'arfe Tara sukaji an Bud'e k'ofar falon tareda shigowa lokaci D'aya bakinsa d'auke da sallama. gabad'aya suka d'aga kai suna kallan Mai shigowar Afeef ne yashigo sai dogarin Daya rakoshi da kayansa.mamaki ne ya kamasu ganin shi a wannan lokacin.Amma Banda Ammie Dan dama ita ya fad'a mata cewa in Sha Allah ayau zai dawo dogarin gidan ne ya k'araso ciki ya ajiye akwatun kayan nasa Anan tsakiyar falon ya duk'a Yana gaida Ammien cikin girmamawa Ammie ta ansa masa kafin ya Mik'e ya juya ya bar falon gabad'aya.sannu da zuwa suka shiga Yi masa Yana ansa musu Batare da ya Kallesu ba.harya k'araso gaban Ammie ya duk'a Ammie ta kai hannu ta shafa kansa tana murmushi tace. "Ka dawo Lafiya?..." Ya d'ago Yana kallanta Yace cikin deep voice d'insa. "Lafiya lau Alhamdulillah Ammie". Ammie tai murmushi tace. "Masha Allah! sannu da zuwa". Mik'ewa yayi Yana kallon Ammie yace. "bari na je ciki" Ammie tace. "Ya kamata kan kaje kai wanka ma huta". Barin falon yayi ya nufi stairs muneeb kuma ya bishi da akwatun kayansa zuwa b'angarensa su ya Zarah suka bishi da kallo.....




#<Ø9ßHUYAAM
#<Ø9ßLAMID'O
#<Ø9ßAZIZ CHIROMA
#<Ø9ßAFEEF



*mutanan MRS SARAKIES =Ø‹Ü Kuna Ina ne? ana ta payments na book d'in Huyaam ku an barku a Baya to Maza ku garzayo yanzu kar wannan garab'asar ta wuce ku*.


*ga masu buk'atar fara payments zaku iya sa kud'inku a yanzu before mu gama free pages Regular group akan naira 500 kacal idan kuma muka gama Free pages zai koma 700 ne.ga masu buk'atar Vip Kuma 2 pages a Rana zaku iya biyan nai 1000 kacal. ku hanzarta ku fara biya tun kafin mu gama free pages.zaku iya tura kud'in ta wannan account d'in =ØGÜ*


2270127432 Naja'atu umar
Zenith bank


Evidence of payment (shaidar biya )via
07066508376



Niger <ØóÝ<ØêÝ_zaku iya biya (500 CFR)for regular group.VIP Kuma _(1000 CFR) my NITA=ØGÜ
07066508376



Da zarar mungama free pages Kuma zamu sa duk Wanda ya biya kud'in sa a paid group, karku bari ayi wannan tafiyar Babu ku =؃Ü=ØƒÜ mutanan arziki.





07066508376________
'þFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD


*<Ø9ßHUYAAM<Ø9ß*


*NA*



*__NAJA'ATU UMAR FAROOQ__*



*__(MRS SARAKIES =Ø‹Ü)__*


PAGE 3þã 1þã



____________¡&


*Bayan kwana biyar*



Da yamman Ranar Alhamis wajen k'arfe biyar da Rabi su Huyaam sun dawo daga b'angaren su safna ita da huda. tun daga nesa suka hango wata rantsatstsiyar mota ta shigo cikin palace bayan an wangale mata gate d'in.motar da danno kai ta shigo cikin harabar palace d'in.tun daga nesa su Huda ke kallan motar Dan Basu San waye aciki ba. Har motar isa tai parking a parking lot suna tafiya suna kallon motar. Aziz chiroma ne ya fito daga cikin motar sanye yake cikin k'ananun kayan da sukai masa bala'in kyau riga da Wando rigar blue black sai Wandon Daya kasance blue jeans ba k'aramin kyau kayan sukai masa ba tafiya yake cikin nutsuwa kamar ance ya d'aga kansa sukai ido hud'u da Huyaam tareda da Huda wacce tai saurin d'auke kanta Dan har ya kusan cimma masu basu farga ba,ya fara takowa zuwa harabar gidan Cikin saurin da shi kansa Bai San Yana Yi ba saboda yadda zuciyar sa ta harba da ganin Wacce idan ya kalleta a Koda yaushe ko Kuma ya tuna ta Hakan ke faruwa dashi.ganin direct gunsu yake nufowa yasa Huyaam ta damk'e hannun Huda da k'arfi tana K'ara saurin tafiyar ta itama .Huda na Jin yadda HUYAAM ke janta yasa ta kalleta da mamakin Irin wannan saurin da takeyi tace. "Ke saurin me kike haka ne? ki tsaya mugaisa da ya chiroma shine fa yazo kinganshi can". Ta fad'a tana juyawa tana K'ara kallan Aziz chiroma Wanda har ya kusan cimmasu . batareda da Huyaam ta kalleta ba tace suna cigaba da tafiya. "Kinga fa dare nayi kuma kinsan fa Ammie tace mudawo da wuri fa". Huda ta ja burki ta tsaya ta rik'o hannun Huyaam da k'arfi tace. "Dan Allah ki tsaya Kinga fa magana yake mana fa wai Dan Allah Huyaam Mai yasa kike yiwa ya chiroma haka ne ke kwata kwata bakya son sakewa dashi sai kace Wanda ya tab'a miki Wani abun". ta fad'a tana kallan Huyaam.Tsayawa Huyaam tai batareda tasan tayi Hakan ba tana kallan Huda da Mamakin abunda ta fad'a .Batasan Mai yasa ba kwata kwata Batasan taga ta tsaya inuwa D'aya da Aziz chiroma ba, Kuma bawai Wani abun ya tab'a mata ba Amma kuma ko kad'an Bata k'aunar Hakan .zatai wa Huda magana kenan Aziz chiroma ya iso Wajen su ya tsaya Yana murmushi tareda kallansu kafin ya tsaida idonuwansa a kan HUYAAM data Wani tura Baki gaba tana tana sunkuyar da kanta k'asa tana rik'e da Hannun Huda har lokacin...Huda na murmushi tace. "Ya Aziz dama Kaine cikin motar can mukai ta kallo muna tunanin waye Saida ka fito sannan muka ga ashe Kaine". Ta fad'a tana murmushi.Aziz chiroma na murmushi yana Shafa kansa yace. "Nine mana da Baku Gane Motar ba?..." Huda ta D'an Bud'e ido tana kallansa ta girgiza kai tace. "Ko kad'an danni banma tab'a Ganin motar nan agidan nan ba". Yana kad'a key d'in motar Dake hannunsa yace. "Oh! gaskiya ne na tuna baku sanni da motar ba Agidan nan dan yau na fara zuwa da ita da naje bichi na d'auko". Huda na kallonsa tace. "Shiyasa kan Bamu sani ba". Huyaam ce ta D'an kalleshi tace. "Ina wuni". Ta fad'a kamar wacce Batasan yin magana. Aziz na murmushi ya langwab'ar da kansa yana kallanta ya kwai kwayi irin muryarta yace. "Lafiya lau". Mai Huda zatai inba dariya ba itama kanta Huyaam d'in Saida ta D'an murmusa saboda yadda yay maganar. Yace. "Wai Huda Mai naiwa HUYAAM ne da Batasan sakewa Dani ne yanzu?.
Ya fad'a Yana kallan Huda Dan jiran ansarta. Huda ta Kalli HUYAAM sannan ta Kalli Aziz tace. "Wallahi ya chiroma Nima bansani ba gata nan ka tambayaeta.." ta fad'a tana kallan Huyaam.Aziz chiroma ya kalli HUYAAM ya D'an duk'o kad'an Yana kallanta kafin yace. "Mai yasa bakyason sakewa dani ne ko dai Wani Abun nai miki?" Huyaam ta girgiza masa kai tana K'ara Damk'e hannun Huda Dake cikin nata.Aziz.ya d'ago Yana sauke ajiyar zuciyar salama yace. "Okay,so please nidai Abinda zan rok'a shine Dan Allah kidaina yimin abinda Kike mun idan kinganni kinji my sister?Dan bana jin dad'in yadda kike min, ko bakya Ganin yadda muke da huda brother and sister ne? Huyaam tai shiru batace komai ba.ya cigaba yace. "Kinyi shiru ko Baki d'auke ni kamar su yarima bane ba? HUYAAM ta girgiza masa kai yace. "So please idan har kin d'auke ni kamar su haidar Dan Allah ki daina guduna kinji?" Nan ma kai kawai Huyaam ta gyad'a masa batai magana ba.Huda ta d'auke kanta daga kallan Huyaam ta Mada kan Aziz chiroma tace. "Kar ka damu Ya chiroma in Sha Allah zata sakene kasan Huyaam d'ince dole Saida lallab'awa". ta fad'a tana kallan Huyaam tareda murmushi.Huyaam ta d'ago ta kalleta tana Maka mata harara.Aziz yay murmushi yace. "Thank You so much sisters". Ya fad'a Yana kallansu.Huda tana murmushi itama tace. "U are welcome".Ganin ana K'iran sallahn magrib yasa yay musu sallama ya juya zai nufi b'angarensu a dai dai lokacin da ya Afeef ya fito daga nasu b'angaren kenan zai tafi masallaci. bayan AZIZ kawai Afeef ya kalla Amma harya ganeshi Ido hud'u sukai dasu HUYAAM yay musu Wani kallo ya k'araso zai wuce su sukai k'asa da kansu suna masa Allah ya kiyaye Amma ko juyowa Baiyi ya kalasu. HUYAAM ta juya tana kallon Huda tace kamar zatai kuka. "kinga abinda kika jawo Mana ko?.." Huda da itama jikinta yay sanyi ganin Irin kallon da Afeef yay musu tace. "Ke naga yasan Yaya Aziz ne babu abinda zai mana fa".. Huyaam ta k'wace hannunta tai saurin shiga b'angaren nasu da sauri Bata kula huda ba Dake tai mata magana akan ta a tsaya ta ba Dan ita hankalinta ya tashi tun gargaad'in da yay musu na kwanaki yana rik'e akanta.huda ta bita Abaya itama jiki babu k'wari Amma Kuma deep down tasan Babu abinda zai musun tunda tasan ai Aziz ne ba Wani ba...



K'arfe goma da Rabi na daren ranar ,Mai martaba ne zaune a k'aton falonsa yana kishin gid'e jikin tun tun sarautan Dake jera a k'asan carpet d'in falon.Ammie Kuma tana daga Zaune a gefensa yay shiru Yana sauraranta har ta gama kafin can Kuma ya Sauke numfashi yace. "Tom Babu laifi naji abinda kika fad'a fulani Amma bawai zank'i bane ba Ina tsoron kada suje can ciwon nata ya sake tashi a gidan Khadija ne bawai fata muke ba Amma duba da yadda yake yawan tashin ne nake dubawa". Ammie ta sunkuyar da kanta k'asa tana Jin abinda Mai martaba ya fad'a Dan itama tabbas tayi wannan tunanin duk da tasan Anty khadija zata kula da ita Amma Kuma tana tsoron ace ciwon ya tashi acan duba da yadda anan suke Shan wahala idan suka tasan mata anan d'in.sauke numfashi Ammie tai k'asa da murya tace. "Gaskiya ne ranki Dad'e Nima abinda nake ta tunani kenan tun lokacin da Khadija tai min maganar". Mai martaba ya Sauke numfashi yace. "Bazan iya hanasu zuwa ba Fulani Allah shine Mai iko akan komai idan muka bita da addu'a shikenan sai kigama har suje su dawo baba abinda zai faru". Ammie tace. "Wannan gaskiya ne rankai Dad'e". Mai martaba ya Jin Jina kai yace. "Yaushe zasu tafin?.." Ammie tace. Da nayi tunanin su tafi tareda da Afeef tunda kaga ta Abuja Jirgin nasu zai tashi.." Mai martaba yace. "Okay Babu laifi ranar Monday kenan?.." Ammie tace. "Eh". Yace "Tom Allah ya kaimu" Ammie ta ansa masa da Ameen. Hira suka ci gaba Dayi akan yadda dai idan su Huyaam d'in sun dawo daga Abujan idan komai ya zamana ready kamar yadda suke fata akaita Egypt d'in....


___________¡&


Ranar Saturday da dayay dai dai da saura wata D'aya da sati D'aya bikin su ya Bahijja aka tashi da shirye shiryen tarb'an Bak'in da zasu kawo kayan lefen ya zulaihat. Kamar dai yadda akai na ya Bahijja to wannan Karan ma dai haka akayi.Dan masu girki aka d'auko na musamman sukai duk Wani nau'i na abinci da snacks kala kala wanda za'a tarb'i Bak'in dashi kusan store guda aka cika da ruwa da drink's kala kala sai kayan snacks d'in Wanda akai raping d'insu da poel paper.komai dai anyi shi yadda ya dace Irin dai na masu dashi kundai Gane ai mutanan arzik'i =ØÞ.bayan sun gama aka sallamesu da kayan abun arzik'i Bandama kud'in aikinsu da aka biya su tun tuni.da farin ciki suka tafi ba kamar yadda suka tafi lokacin da sukai na bahijja ba Dan wannan kulawa aka Basu na musamman.komai ya kammala zuwan Bak'i ne kawai ya rage... K'arfe hud'u da mintuna main falon b'angaren ummi ya cika mak'il da 'yan uwanta da k'awayenta harma da abokan arzik'i haka aka cika falon nan ana zaman jiran zuwan Bak'i kowa kika gani yana cikin shiga ta Alfarma sai Wani walwali sukeyi .wuyansu kuwa sanye yake da gwala gwali wasu kuwa daham ce Wanda kud'i sukai kuka a wajen siyan su.su Hajiya Lubabatu da k'awar ta Fulani Salamatu wacce ke zaune akan kujerar kusa da Ammie wacce aka tana deta saboda su tunda matan sarkie ne dole a Basu wannan girman. itama cikin shiga ta Alfarma take sai Wani walwali kawai takeyi tana wani Shan k'amshi ita a dole matar sarki (uhmm! kodan matar sarkin ce mana ai ba k'arya tai ba).sauran matan Dake falon kuwa duk suna Zaune saman carper ne wasu Kuma saman kujerun... Hud'u da Rabi dai dai Bak'in suka iso gidan bayan an wangale musu gate.haka motocin nan suka danno kai zuwa harabar gidan alaye kusan guda shida kamar Wanda akazo d'aukar Amarya. Bayan sunyi parking a harabar gidan driver's d'in sukai saurin fitowa daga cikin motar suka k'araso suka bud'ewa wad'an da ke bayan motar kafin su matsa baya da sauri cikin girmamawa.. D'aya bayan D'aya haka manyan matan Dake bayan motocin suka shiga fitowa cikin shiga ta Alfarma kowacce Tasha sutura Mai tsadar gaske.tsayawa sukai bayan duk sun gama fitowa Daga cikin motocin.Dana k'irgasu su shida ne Basu da yawa Dan Amota biyu kawai suke. sauran motocin hud'un Kuma kayan lefen ne Kawai aciki.drivers d'in sauran motocin suka had'u suka shiga fiddo da akwatunan da sukazo dasu. Bayan sun gama fitowa dasu suka tsaya adai dai lokacin da Ka'nnen Hajiya Aysha suKa zo zasu yiwa Bak'in iso bayan sun nuna inda za'a kai akwatunan nan drivres d'in suka Shiga d'aukar boxes d'in suna shiga dasu b'angaren Hajiya Aysha.k'annen Hajiya Aysha ne suka k'araso kusa da Bak'in suna gaishesu da kulawa".ansawa musu sukai Suma cikin Kulawa kafin suyi musu iso lokacin har angama kai boxes d'in.gaba sukai bak'in suka bi bayansu har zuwa b'angaren Hajiya Aysha...Bak'in sun shiga falon bakinsu d'auke da sallama nan suka tadda mutanan Dake cikin falon ga boxes d'in da aka ajiye su nan tsakiyar falon kan carpet sun sha decorations na flowers.atare mutanan falon suka ansa sallamar Bak'in suka k'araso shigowa cikin falon.ko ba'a fad'a musu ba sun san su Ammie sune matan sarkin ganin yadda suke cikin shigar matan sarakai sun Sha alkyabba Mai bala'in tsada ga kyau.k'arasawa cikin falon sukai har gaban su Ammie Dake zaune saman kujera suka duk'a suka shiga kwasar gaisuwa Ammie kad'ai ta ansa musu da kulawa Amma Fulani Salamatu ansa musu tai tana wani jijji da kanta. mik'ewa sukai bayan sun gama gaisawar suka koma wajen zaman su da aka tana da musu nan kan wasu kujeru.suka zauna suna gaisawa da mutanan Dake cikin falon . Nan Da nan aka cika musu gabansu da ruwa da drink's sai fruits.basu Sha ba nan aka Bud'e taro da addu'a kafin a Asha fa. Sannan aka shiga Bud'e kayan lefen akwatu na ne guda 26 masu bala'in tsada. kayan ciki kuwa Masha Allah Dan Suma kansu kayan masu bala'in tsada ne komai dai luxury ne inbanda Gud'a Babu sautin a binda ke tashi afalon nan ga kud'in D'inki da suka Bada shima milion D'aya da Rabi nan ma dai wata gudu d'ar ce ta K'ara tashi da Masha Allah amarya tayi goshi sai dai muce Allah ya kaimu ranar biki .. Hajiya Lubabatu kuwa Saida jikinta yay sanyi ganin Irin kayan da aka kawowa zulaihat duk da itama dai Bahijja kayan nata masu tsadar Gaske ne Amma ita gani take na zulaihat yafi na 'yarta kodan ganin akwatunan da aka k'ara guda biyu akai ne oho?. Saboda Rashin godiyar Allah! Irin nata. Dan ita ana ta tunnanin d'aukar ta kayan bahijja zasu fi na zulaihat kyau da tsada Amma Kuma sai taga sab'anin haka.. Fulani Salamatu kuwa tana daga Zaunen da take tana kallan kowa D'aya bayan D'aya bata farga ba a wannan Karan ma dai Ammie ta Sha gabanta Dan kuwa one million ta Bada kud'in takuici nan ma dai wata gud'ar ce ta tashi aka shiga yiwa Ammei kirari da Kod'a ta Wanda yasa Fulani Salamatu ta kusan fallasa abinda ke ranta Dan da k'yar ta iya controllin kanta kallon Ammie kawai take tana Jin Wani Irin tsanarta na K'ara k'atuwa a ranta.itako Ammie batama San tanayi ba...bayan an gama murna da gud'ar da ake tayi da Ganin kayan lefan aka rufe taron da addu'a.nan bak'in suka mik'e bayan sunyi kusan 40 minutes dazuwa sukace tafiya zasuyi.nan da nan aka shiga fiddo musu da abubuwan da akai musu aka fitar musu da shi zuwa wajen motar su godiya sukai tayi na Jin Dad'in abinda akai musun nan dai aka rabu cikin aminci da mutuntawa tuni fulani Salamatu ta silale tabi ayarin masu kawo lefe ta koma b'angarenta.babu Wanda ya kula da ita....


K'arfe 9:30pm na dare su Huyaam suna zaune a main falo suna ta hira . Afeef Kuma na zaune a dining Yana yin dinner gefe D'aya Kuma Yana latsa wayarsa.Huyaam ta juya tana kallon Ammie tace.
"Ammie Yaushe muma zamuje muga lefen?.."Ammie ta kalleta tace. "Duk lokacin da Kuka shirya". Huyaam na murmushin Jin Dad'i tace. "To gobe zamuje". Ammie tace. "Allah ya kaimu" suka ansa da Ameen ita da Huda. Afeef ne ya fito daga dining d'in ya shigo falon zai wuce b'angarensu Huyaam ta juya tana kallonsa tai murmushi tace. "Yaya kaima yaushe zakai Auren ne?.. ba ya Zarah da huda ba hatta Ammie saida ta Kalli HUYAAM sannan ta juya ta kalli Afeef Wanda ya Tsaya a inda yake d'in Bai juyo ba har lokacin Amma Kuma Yana tsaye ya kasa tafiya.shiko Afeef a wannan moments d'in daskarewa yayi a inda yake tsayen Yama kasa K'ara d'aga k'afar tasa bare Kuma yayi Wani yun k'urin Dan kuwa gabansa ne yay Wani Irin Fad'uwa Jin abinda Huyaam ta fad'a.Ammie tai Wani murmushi tace. "Fad'a masa dai tunda ya kasa fitowa da matar AUREN har yanzu". Sai a lokacin ya juyo yana kallon Huyaam da idanuwansa Wanda suka sauya launi lokaci D'aya take gaban HUYAAM ya Fad'i ta daina murmushin ta sunkuyar da Kanta k'asa gabanta na fad'uwa kar dai ace laifi tayi.Afeef dai kallanta Kawai yake Yi Kamar bazai magana ba Sai Kuma can yace cikin deep voice d'insa"Ina wasa Dake". Ya fad'a cikin b'acin Rai.Huyaam ta girgiza masa kanta alamar a'a yay k'wafa Yana kallan Ammie yace. ""Good night Ammie". Ammie tai murmushi tace. "Good night".Dan tasan ba san San zancen yake ba bare Kuma ya kula ya juya ya bar wajen suka bishi da kallo harya haye stairs d'in b'angaren su.

Ya Zarah tana kallan Huyaam bayan Afeef ya tafi tace.."tab' wallahi wata Rana Huyaam akan wannan bakin naki marar saiti wata Rana Sai Yaya ya saita miki shi". Huda tace. "Yo aini mamaki ma ta bani shiyasa na kasa magana". Huyaam dai batai magana ba sai tura Baki gaba kawai takeyi.Ammie tace.
"Kunga ya isheku dan ta fad'i gaskiya Shine abun magana? To Babu ruwanku". Ta fad'a tana kallansu .basu K'ara magana ba sukaja bakinsu sukai shiru ita dai HUYAAM ta kasa dawowa dai dai har lokacin.......




#<Ø9ßHUYAAM
#<Ø9ßLAMID'O
#<Ø9ßAZIZ CHIROMA
#<Ø9ßAFEEF




*TALLAH! TALLAH!! TALLAH!!!*


*Ina kuke manyan mata masu capacity =ØÞ=؃Ü=؃Ü? Nace Ina kuke hajiyoyin gidan nan, to Maza ku Bud'e kunnuwanku ku saurarareni >ØÏÝ da kyau.Dan a yau nazo muku da Wani kyakkyawan albishir=؃Ü=ØƒÜ wanda zakuji dad'insa fiye da yadda zan fad'a muku.Nace ba, Bakuda Labarin hamshak'iya shahararriyar 'yar Kasuwar nan wacce tai K'aurin suna wajen kawo muku kayayyakinta na 'yan Gayu masu quality wato H.Empire <Øæß Lagos Mai gidan kayan sawa na mata na k'walisa da Kuma kayan kitchen?..."*

*To idan yau kuka tab'a ji ya kamata ace kun saurareni kunji da abinda nazo muku dashi. Kayan sawa kike so Wanda zaki zama tauraruwa a cikin 'Yan uwanki mata harma da Mai gida wato oga kwata kwata Hajiya ta , ko ko so kike duk inda kika gifta kallo ya koma kanki?. Ko Kuma kayan kitchen kikeso masu kyau da aminci daki bari. To Maza ku garzayo H.Empire <Øæß Lagos anan zaku samu duk Wani Irin Abu da kuke so, Dan mu kayan mu quaranti ne Hajiyata bakida tan tama akai, kudai ku gwada siya kawai zakusha mamaki Dan sai Kun bani labari. Muna Saida kaya kamar haka ka* =ØGÜ

*1,Atamfofi*
*2, lesses*
*3, Abaya*
*4, kayan kwalliya ko Wani iri ne*
5,*D'an kunnaye(jiwelleries)*
*6,takalma*
*7,hand bag*
*8, mayafai*
*9, sai Kuma kayan kitchen shima Muna sai dawa, Dan duk Wani kayan kitchen d'in da kike nema harma da Wanda Baki tab'a Gani ba ko sani to idan kikazo H.Empire <Øæß Lagos anan zaki samu duk Wani Irin kayan kitchen muna Saidawa akan farashi Mai sauk'i da rahusa siyan D'aya ko sari*.

*domun magana damu kai tsaye ko Kuma Neman K'arin bayani ku tun tub'emu ta wad'an nan numbers d'in kai tsaye kamar haka =ØIÜ+234 811 190 1302 /09020337676*


*Siyan na gari Mai da kud'i gida Hajiya ta*

*Sai mun Jiku=؃Ü=؃Ü*

______________


Paid via =ØGÜ
Naja'atu umar
2270127432
Zenith bank

Evidence of payment =ØGÜ
07066508376


*Yan Niger <ØóÝ<ØêÝ_zaku iya biyan(500 CFR) a Yanzu before mu gama free page. idan muka gama Kuma zai koma(700 CFR) . for VIP Kuma (1000 CFR)MY NITA *=ØGÜ*
07066508376




07066508376________
'þFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD


*<Ø9ßHUYAAM<Ø9ß*


*NA*


*__NAJA'ATU UMAR FAROOQ__*



*__(MRS SARAKIES =Ø‹Ü)__*



PAGE 3þã 2þã


____________¡&


Ranar Monday da safe wajen k'arfe 10:30am su Huyaam har sun gama shirinsu tsaf na tafiyarsu Abuja.saukowar downstairs kenan bayan sun ajiye boxes d'in kanyansu anan tsakiyar falon.Huyaam ta kalli Huda tace "Nayi mantuwa" daga haka ta nufi stairs d'in cikin sauri. Afeef ne ya sauko downstairs d'in shima har ya gama shiryawa ,Sanye yake cikin shigar k'ana nun kaya riga da Wando,rigar long sleeve shirt ce white color sai Wandon Daya kasance blue jeans dayay masa bala'in kyau, sai facing cap d'in Daya D'ora saman kansa kalar blue yayi kyau ba kad'an ba sai Wani sassanyen k'amshi yake ta ko Ina .ya haidar na biye dashi da box d'in kayansa har suka k'araso tsakiyar falon Ammie na kallonsa tace. "Kayiwa mutanan gidan sallama ne?" Yana kallanta. Ya gyad'a mata kai kawai baice komai ba.Sauke numfashi Ammie tai tana kallan haidar tai tace. "Idan ka kaisu airport d'in ka wuce ka Karb'omin sak'on" ansa mata haidar yayi da to Ammie.Huyaam ce ta sauko downstairs d'in sanye cikin shigar Abaya coffee colour Wacce tai Mata bala'in kyau ba kad'an ba iri D'aya suka sa ita da Huda.kallanta ya Zarah tai tace. "Me kika koma kikayi ne?. Ammie tace. "Duk ba wannan ba ke Yanzu Zarah so kike su tafi wallahi ni tun daga yanzu harna fara Jin kewarsu". ta fad'a tana kallansu.Huyaam ta k'araso ta rungume Ammie tana murmushi tace."I gonna miss you too Ammie". Huda ma k'arasowa tai ta rumgume Ammie ta D'aya side d'in tana murmushi.hawayen Huyaam kawai Ammie taji a kafad'arta take ta d'ago ta cikin damuwa gabanta na fad'uwa tana kallanta da tambayarta da lafiya?kan k'ameta Huyaam ta sake Yi nan Ammie ta saki murmushi tana patting Bayanta tace.

Please Login or Register in order to submit comment