Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Gani ba ko sani to idan kikazo H.Empire <Øæß Lagos anan zaki samu duk Wani Irin kayan kitchen muna Saidawa akan farashi Mai sauk'i da rahusa siyan D'aya ko sari*.

*domun magana damu kai tsaye ko Kuma Neman K'arin bayani ku tun tub'emu ta wad'an nan numbers d'in kai tsaye kamar haka =ØIÜ+234 811 190 1302 /09020337676*


*Siyan na gari Mai da kud'i gida Hajiya ta*

*Sai mun Jiku=؃Ü=؃Ü*



07066508376________
'þFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD


*<Ø9ßHUYAAM<Ø9ß*


*NA*


*__NAJA'ATU UMAR FAROOQ__*



*__(MRS SARAKIES =Ø‹Ü)__*


My channel link =ØGÜ
https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y


*Bismillahirrahmanirrahim*


PAGE 3þã 8þã


___________¡&


Washe gari da safe wajen k'arfe shad'aya da Rabi na safe, Huyaam na zaune a main falon gidansu kusa da ya Haidar da yake Aiki a laptop d'in shi sai surutu take masa tana bashi labarin Irin wuraran da suke just for enjoying a Abuja Dan har wannan park d'in da suka je babu abinda ta manta Bata fad'a masa ba,ya Zarah dai tana zaune a gefe tana kallan yadda HUYAAM Bata tab'a gajiya da Bada labarin nan Dan Suma jiya da daddare Saida ta Basu labarin hadda Ammie kafin su kwanta bacci ta ishesu da surutu,to Shine Yanzun ma take sake bawa ya Haidar labarin.d'agowa da kansa ya haidar yayi daga kan laptop d'in nashi Yana kallan Huyaam Cikin k'osawa da surutun da take masa ta k'yale shima da pressure na aikin Dake kansa ma ya isheshi ya ce "to naji yanzu dai Dan Allah ki barni haka na k'arasa aikin da nakeyi kinji?" Ya fad'a Yana kallanta .tura Baki tai gaba tana wasa da yatsun hannunta ta ce "to Yaya zaka kaimu ko sau D'aya ne ance a kano ma akwai?" Rungume hannunsa Yay a k'irjinsa Yana kallanta kafin ya ce "ai dama nasan abinda zaki fad'a daga k'arshe Kenan na kaiku Toni banida da wannan time d'in" marai Rai ce masa tai tai k'asa da murya ta ce "Dan Allah Yaya?" Hararar ta yayi ya ce "tashi ki bani waje kafin nai ball Dake anan" mik'ewa tsaye tai tana tura Baki gaba tare dasa kukan k'arya ta haye sama da sauri har tana had'awa da gudu, ya haidar ya bita da kallo yay k'wafa kafin ya d'auke kansa ya Maida kan laptop d'in gabanshi.ya Zarah tai Murmushi ta ce "aikuwa yanzu zaka ga Ammie ta zo gunka tunda ka tab'a mata ita" Wani Irin kallo ya wullawa ya Zarah kafin ya d'auke kansa baice komai ba ya mik'e hannunsa rik'e da system d'in na shi ya wuce b'angaren su Dan ya k'arasa aikin nasa acan.ya Zarah ta bishi da kallo....in the next day .shirye shiryen bikin su ya zulaihat kawai akeyi Dan yau bikin baifi Saura sati D'aya da kwana hud'u ba, shiri ake na musamman more especially daga b'angaren Hajiya Lubabatu Dan ita wannan bikin ta d'auke shi da matuk'ar muhimmanci saboda zata aura da first daughter d'in tane, gayya kan Babu Irin gayyartar da batai ba k'awayenta matan masu kud'i da masu kud'in kansu duk ta gayya cesu. Hajiya Aysha itakan baiwar Allah shirin ta take a hankali cikin nutsuwa Bada wata Baragada ba, kuma komai zatai saitayi shawara da Ammie saboda tace Ammie ai itace uwar zulaihat ba ita ba,itako Hajiya Lubabatu tare suke k'ulla komai ita da Fulani Salamatu duk da ba ko Wani Abu take Sako ta aciki ba Amma Kuma saboda ita makira ce tasan ta kan duniya ta iya zaman ta da kowa saita ta dinga nuna ma Fulani Salamatu komai idan zatai saita nemi shawarar ta..Yanzu haka k'arfe hud'u da Rabi ne na yamman Ranar Laraba, ya Zarah ce ta sauko downstairs d'in cikin shirin fita da dukan alamu dai fita zatayi, tana kallan Huyaam da Huda da suke zaune a falon suna kallan screen d'in wayar Dake hannun Huyaam da dukan alamu d'aya ne yake nunawa D'aya Abu acikin wayar.maganar da ya Zarah tai musu ne yasa suka d'ago da kansu a tare suna kallanta ta ce "acikin ku waya gyara mun d'akina d'azu da safe?" Huyaam ta ce "nice" ya Zarah ta ce "Ina kika samun ATM d'ina Dana ajeye akan mirror? Huyaam ta ce "nasa miki cikin hand bag D'inki?" Ya Zarah tace "jeki d'auko min" mik'ewa Huyaam tai tana bawa Huda wayar Hannunta sannan ta wuce stairs d'in Babu dad'ewa ta dawo rik'e da ATM d'in ta Mik'awa ya Zarah,karb'a ya Zarah tai ta nufi hanyar k'ofar fita daga falon Ganin fita zatai yasa Huyaam ta d'aga murya ta ce "ya Zarah Ina zaki?" batare da ya Zarah ta juyo ba ta ce "inda kika aikeni" daga haka ta fita daga falon gabad'aya,kallan Huda Huyaam tai ta rik'e hab'a ta ce "ko Ina zata oho?" Huda ta Bud'e hannuwanta alamar itama Bata sani ba.sauke numfashi Huyaam tai nan suka Maida hankali kan abinda suke kallo a cikin wayar sunyi nisa da abinda suke. Ammie ce ta Sauko downstairs d'in ta k'araso har tsakiyar falon tana kallansu ta k'ira sunansu .d'agowa da kansu sukai a tare suna ansa mata . Ammie ta ce "kuje ku shirya za'a Kaiku wurin tailor za'a d'auki measurements D'inku" Huyaam ta ce "Ammie na miye?" Ammie ta ce . "Na bikin su zulaihat mana ba'a kawo ankon da wuri bane sai yanzu" Huyaam ta ce "waye zai kaimu Kuma? Ammie ta kalleta Jin tambayar da tai mata kafin ta ce "wannan ne Kuma bansani ba Dan Yanzu Hajiya Aysha ta K'irani take fad'a min ni Kuma ban tambayeta wannan ba" mik'ewa sukai suka haura sama zuwa d'akinsu.babu dad'ewa suka dawo falon cikin shirin fita doguwar rigar abaya suka Saka ash color sunyi rolling mayafin iri D'aya suka sa ita da Huda sunyi kyau ba kad'an ba, sallama sukai wa Ammie sannan suka bar falon gabad'aya...


Suna gab da shiga b'angaren su safna sai ga safna ma ta fito nan suka juya suka nufi parking lot ahanya suka had'u da ikleema ta fito daga b'angaren su had'uwa sukai suka k'arasa compound d'in suka tsaya daga gefe kusa da wata mota wacce aka fito da lta da dukan alamu acikin motar za'a kaisun.suna nan tsaye suka hango Aziza ta fito daga b'angaren su taci kwalliya ba kad'an ba sai Wata Irin tafiya takeyi kamar bazata taka k'asa ba, kallo D'aya Huyaam tai mata ta d'auke kanta tana kallan gefe kafin ta Maida kallanta kan safnah Wacce suke ta zance ita dasu Huda ta ce "waye zai kaimu wai? safna zatai magana suka hango lamid'o ya fito daga b'angaren su hannunsa rik'e da key d'in motar ya nufo compound d'in Yana tafiya cikin nutsuwa, kallan Huyaam kawai yake tunda ya hangota daga nesa Daya fito daga b'angaren nasu,itama Kuma Kallansa take daga nesan da take hangoshi tana mamakin yaushe ya dawo gidan? Bata farga ba harya ya k'araso wajen motar tasa inda suke tsaye.gabad'ayansu suka had'a Baki wajen gaishe shi ansa musu Yayi da Kulawa Yana k'ok'arin Bud'e driver seat zai shiga ya ce "enter" babu musu suka ansa masa gabad'ayansu. su Hud'un ne suka shiga back seat sai safna Data shiga front seat.ta_da motar yayi bayan sun shiga yay reverse ya nufi babban gate d'in palace d'in.tun kafin su k'araso aka wangale musu gate d'in suka fita daga cikin palace d'in gabad'aya fadawan Dake Bakin gate d'in sukai tai musu fatan dawowa Lafiya...tunda suka d'au titi ikleema da Huda suke da zance k'asa Amma Banda Aziza Wacce ta kama kanta agefe tana latsa wayarta,dan tunda suka shiga motar uffan Bata cewa kowa a cikin su Hudan ba Suma Kuma Babu Wanda yay mata magana Dama daga can left door d'in k'ofar motar ta shiga sai ikleema a kusa da ita sai Huda sannan Huyaam.lokaci Lokaci lamid'o Dake gaban motar ya ke d'agowa ya Kalli direction d'in HUYAAM ta mudubin motar Batare da ya bari su Huda sun lura da Hakan ba, itakan Huyaam Batama San yana yiba ta juyar da kanta tana kallan gefen titin ta window motar. juyawar da zatai idonta ya sauka akan na lamid'o Dake kallan ta ta cikin mudubin motar,nan taga lamid'o ya zuba mata Ido Yana mata Wani Irin kallo,ai tuni ta sunkuyar da kanta k'asa tana Jin Wani Irin Fad'uwar gaba ta takure jikinta waje D'aya Bata yadda ta k'ara dago da kanta ba.shiko lamid'o Wani Irin Abu yaji Wanda ya K'ara motsoma masa da wutar soyayyar Huyaam acikin ransa Yana Jin Wani Irin feeling a game da ita Nan ya K'ara d'aga kansa ya Kalli mirror yaga ko zata Kalleshi Amma sai yaga tak'i d'ago da kan nata ma bare su had'a Ido.sauke numfashi yayi a hankali Yana cigaba da tuk'insa cikin nutsuwa lokaci lokaci Kuma ya d'ago yaga Huyaam ko zata Kalleshi Amma saiya ga Tak'i d'agowa a haka har suka isa plaza d'in da aka kai musu D'inkunan nasu Amma har lokacin Huyaam Bata k'ara yadda ta k'ara dago da kanta bare ta k'ara had'a ido dashi ba....


Yana zaune a cikin motar Yana jiransu su fito daga cikin shagon.tun Daga nesa yake kallanta baya ko kiftawa har suka k'araso gab da motar Bai d'auke idonsa akan taba, ita ko kallo D'aya tai masa ta d'auke kanta tana sunkuyar da kanta k'asa tana Jin Wani Iri. azuciyarta ta ce "ita kan ta Shiga uku da wannan Abu ace mutum yayi ta kallan ka, shi yanzu ya lamid'o Mai zaisa ya dinga mata Irin wannan Kallan haka" shiga motar itama tai da Sauri ganin duk sun shiga sun Barta.ta_da motar lamid'o yayi suka bar wajen gabad'aya..AWani k'aton store ya tsaya inda ake saida kayan sanyi irinsu ice cream da yogurt da sauransu, Bayan yayi parking ya juya Yana kallan su Yace "am coming" ansa masa sukai ya b'alle murfin motar ya fita yana tafiya a hankali har ya shige cikin store d'in.suna zaune acikin motar ya dawo Hannunsa rik'e da ledoji manya ya shiga ya Mik'awa safna Dake gaba Leda D'aya sauran Hud'un Kuma ya Mik'awa su Huyaam da suke bayan motar .Huda ce ta karb'a ta ce "thank you so much ya lamid'o" Suma sauran duk godiya sukai masa har Huyaam datai masa godiyar k'asa k'asa,ta-da motar yayi suka bar wajen sai palace....


____________¡&


Suna isa gida adai dai alokacin da ake K'iran sallahn magrib.fitowa sukai gabad'ayansu daga cikin motar sukaiwa lamid'o godiya, ansa musu yay Yana lucking motarsa gabad'aya kafin ya bar wajen ya nufi masallacin cikin palace d'in.suma sukai sallama da junansu nan ko Wacce ta nufi b'angaren su..bayan sallahn isha'i wajen k'arfe 9 Saura na dare suna zaune a falon gabad'ayansu .Ammie ta juya Ganin taga kowa zaune a falon Amma Banda Huyaam wacce suka barta a dining tun d'azu bayan sun gama yin dinner ta ce "wai Huyaam Mai kike a dining d'in nan ne haka tun d'azu kowa ya gama Amma ke Baki taso ba?" Ta fad'a tana kallan Huyaam Dake ta faman Shan ice cream.jin muryar Ammie yasa Huyaam tai saurin d'auke robar ice cream d'in ta matsar gefe Dan tasan indai Ammie ta Gani k'wacewa zaitai tana goge bakinta tace "Gani nan fa Ammie" Ammie ta ce "meye kike Wani sid'e Baki haka? ya Zarah ta ce "Ice cream mana aikinsan sai shi tasan indai tazo nan tana Sha sai kin k'wace" Ammie ta Kalli ya Zarah da mamakin abinda ta fad'a ta ce "ice cream Kuma? wai nikan Bata sha d'azu ba?" Ya Zarah ta ce "aikinsan ita ba k'oshi take da ice cream ba saita Sha Wanda yay mata yawa tazo tana Hana mutane bacci a cikin daren nan tana cewa cikinta na ciwo" Ammie ta juya da sauri tana kallan Huyaam ta ce "kawo min nan kafin ki ta-da min da hankali a cikin daren nan" mikewa Huyaam tai tana tura Baki ta fito daga dining d'in ta k'araso har gaban Ammie ta mik'a mata" Karb'a Ammie tai gabad'aya tana kallan robar, wannan sabone ma ta Bud'e take Sha Dan ba na d'azu bane Wanda Tasha ba"da mamaki Ammei ta ce "wato Wani kika d'auko kike sha Bayan Wanda kika Sha d'azu ko?" sunkuyar da kanta k'asa tai tana sosa Kai Dan tasan bata Isa taiwa Ammie k'arya ba. Ammie ta ce "shiyasa d'azu da kowa yaci Abinci Amma ke kika k'i ci Ashe wannan abun kike so Kisha Idan kika faki idona? Huyaam ta girgiza mata kai ta ce "Ammie naci fa" Ammie ta ce "rufe min Baki" sai Kuma ta kalli ya Zarah ta ce "kinsan d'azu a dining Dana ga ta zauna ta nutsu d'auka ta fa ko abincin da Bataci d'azu bane take ci yanzu" ya Zarah ta ce "hmmm da dai ba Huyaam bace ba " Ammie ta sauke numfashi tace "Allah ya kyauta" ta k'ira hadimarta D'aya wacce ta rage Bata koma bangaren su ba tana kitchen tana gyarawa Bayan ta k'araso Ammie ta mik'a mata Ice cream d'in hannunta ta ce ta kai Mata kitchen ta ajiye"karb'a hadimar tai cikin ladabi ta juya ta wuce kitchen d'in, Huyaam ta tura Baki gaba ta zauna kusa da Ammie ta D'ora kanta saman kafadar Ammie....


Wajen k'arfe goma da rabi na dare har Huyaam ta kwanta bacci taji wayarta Dake gefenta tayi k'asa alamar shigowar message, juyawa tai daga kwancen da take ta d'auki wayar tana kallon secreen d'in wayar tare da Bud'e duka message d'in tana karanta contents d'in Bata ko kiftawa,wannan number ce da bata San ko ta waye ba har yau tai mata message d'in, Mai zazzau Maita sak'on kawai take kamar Wanda Bata fahimci Abinda aka rubuta ba "danai tozali Dake yau sai naji duk wata kewar ki da nai ta tsawan watannin da bangan kiba naji wata Irin nutsuwa ta musamman ta saukar min a tareda ni, tafiyar da nai kuwa tare da Dake daga gida har inda muka je muka dawo ji nake Ina ma ace mu Kasance tare da ke a k'ark'ashin inuwa D'aya har Abada? Amma Ina fatan zuwan wannan ranar Ina so ne ki fara arba da kalamai na kafin ki bani damar had'uwa Dake na bayyana miki da kaina ido da ido a matsayin masoya. Please heart e&þ beat ki aminta Dani Dan Allah ki soni Koda ko baza kimin Irin soyayyar da nake miki ba.bari na barki haka Karna cika ki da surutu good night bye bye I love you from AMT" iya abinda aka rubuta kenan sai emojies na love... lumshe ido Huyaam tai tana Jin Wani Irin zufa na keto Mata lokaci D'aya a duka jikinta, ita ko waye wannan wanda suka fita dashi d'in tare? Waye Shi,waye yake son K'ara tarwatsa mata zuciya Haka?Abinda ya d'arsu azuciyar ta ne yasa ta kifa kanta tana Hana zuciyar ta gaskata mata wanda take tunani, ita kan ta shiga uku yanzu su uku kenan, Yanzu idan yaya ya sani ko Ammie Mai zata ce musu wallahi babu Mai yadda da ita kome zatai kuwa har gara ma Ammie zata iya fahimtar ta Amma yayansu tasan ko boka da malami zata had'iya bazai tab'a fahimtar taba Wani Irin tashin hankali ne ya K'ara saukar mata yin wannan tunanin da tai take ta fara Jin Jikinta ya fara rawa.tana wannan halin Huda ta tai knocking tare da ta turo k'ofar ta shiga batare da Huyaam ta sani ba Dan tayi nisa a duniyar tunanin Data tafi.Mamaki ya kama Huda ganin yadda HUYAAM ta takure jikinta waje D'aya kamar wacce take Jin sanyi.k'arasawa kusa da gadon Huda tai ta kai hannu ta ta tab'a ta Tana K'iran sannan Huyaam cikin sanyin murya.a firgice Huyaam ta juyo Jin an tab'a ta, Sauke numfashi tai Ganin Huda ce,Huda dai kallan ta take sai Kuma ta sauke numfashi ganin lafiyar Huyaam d'in k'alau Dan d'aukar tama ko Bata da lafiya ne ta ce "ko kin fara bacci ne? Girgiza mata kai Huyaam tai alamar a'a,Huda ta ce tana kallanta "bani blanket d'ina da kika d'auko jiya Kinga nakin kuwa? Mik'a mata Huyaam tai ta ce "eh na gani" karb'a Huda tai kafin tace"meya sameki na ganki Wani Iri?" tun kafin Huda takai k'arshen zancen ta Huyaam ta fashe da Kuka,dan kamar dama jira take a tambayeta damuwarta.nan gaban Huda ya Fad'i ta zaune a bakin gadon ta rik'o HUYAAM tana tambayar ta da lafiya Mai ya sameta? Huyaam Bata ansa ba sai ma kukan da ta dinga rerawa,Huda dai kallan ta Kawai take tana tunanin Mai yasa sameta haka .Saida Huyaam tai Kukan ta Mai isarta sannan ta ta d'ago ta Mik'awa Huda wayarta. Karb'a Huda tai tana Karanta Sak'on Saida ta gama Karantawa tass sannan ta kalli HUYAAM ta ce "waye wannan d'in? Huyaam ta ce cikin sheshshek'ar kuka "wannan d'aya number ne da bansan ko waye ba ya tura min" huda ta k'ara kallan number sannan ta kalli HUYAAM ta ce "na kasa fahimtar inda ya dosa,wai da Kuka fita? To keda waye kuka fitan? Nidai a iya sani na yau da iya ya lamid'o kawai muka fita Bada kowa ba? Gyad'a Mata kai Huyaam tai kafin ta ce cikin rawar murya
"Nima haka na gani ai".. Huda ta sauke numfashi ta ce "to iKon Allah waye wannan shi Kuma? Shiru Huyaam tai batai magana ba sai Kuma can ta k'ara fashewa da Kuka tace "na shiga uku Huda wallahi bansan Shiba bansan waye shiba wallahi so suke kawai Yaya ko Ammie wani ya kasheni indai suka sani" saurin toshe mata Baki Huda tai tana girgiza mata kai ta ce "a'a kidai na cewa haka" Huyaam ta k'wace bakinta zatai magana wayar tai k'ara alamar shigowar k'ira, a tare suka kalli wayar kafin Huda ta Mik'a mata ta ce "ana k'iranki" Huyaam ta ce "waye? Huda ta ce "number ne ki karb'a ki duba ki Gani" karb'a Huyaam tai sai Kuma taja tsaki tai rejecting call d'in,Huda tace "waye? Huyaam ta ce "ya Aziz ne mana" tana hararar wayar .sauke numfashi Huda tai tana kallan Huyaam sai Kuma can tai k'asa da murya ta ce "Huyaam kina son Yaya Aziz ne?" ta fad'a da sigar tambaya tana kallan yanayin Huyaam d'in .wata iriyar muguwar harara Huyaam tai mata na ashema bakida hankali.Huda tai murmushi ganin rin hararar da take Mata sai kuma ta ce "Abdallah fa?" Huyaam ta ce a fusace "karki K'ara yimin Irin wannan tambayoyin banaso Huda" Huda tai murmushi ta ce "seriously nake tambayarki Huyaam ta Hakane kad'ai zamu magance Abun" Huyaam ta ce "Allah ya sawak'e ni kaf cikin su Babu Wanda nake so, ke ni Soyayyar ma banji zan iya ba bare Kuma har nai musu Wani gurbi a cikin zuciyata ba.Dan Allah tashi ki tafi bacci nake ji" ta fad'a cikin b'acin Rai.mik'ewa Huda tai da bargon a hannunta tana kallan Huyaam ta ce "zan tafi Amma kafin nan Inaso kiyi nazarin tambayar da nai miki" daga haka ta fice daga d'akin gabad'aya bayan ta kullo mata k'ofar . kallon Huda kawai Huyaam take har ta kai k'arshen zancen ta tafita daga d'akin tana mamakin Mai Huda take nufi da har zata ce tai tunanin tambayar da tai mata? tsaki Huyaam tai tana Jin Wani Irin haushin maganar da Huda tai mata kafin ta d'auki wayar ta kashe gabad'aya ta kwanta tana lumshe ido tunani fal ranta da k'yar ta samu bacci ya d'auketa a haka .......



#<Ø9ßHUYAAM
#<Ø9ßLAMID'O
#<Ø9ßAZIZ CHIROMA
#<Ø9ßAFEEF
#<Ø9ß ABDALLAH SHATTIMA



Littafin HUYAAM na kud'i ne regular group akan naira 500 before mu gama free pages muka gamawa Kuma zai koma 700 for VIP group Kuma 1k (1000) ku hanzarta ku biya ta wannan account d'in =ØGÜ

2270127432 Naja'atu umar zenith bank

Evidence of payment =ØGÜ
07066508376



*Yan Niger <ØóÝ<ØêÝ_zaku iya biyan(500 CFR) a Yanzu before mu gama free page. idan muka gama Kuma zai koma(700 CFR) . for VIP Kuma (1000 CFR)MY NITA =ØGÜ*
07066508376



*TALLAH! TALLAH!! TALLAH!!!*


*Ina kuke manyan mata masu capacity =؃Ü=؃Ü? Nace Ina kuke hajiyoyin gidan nan, to Maza ku Bud'e kunnuwanku ku saurarareni >ØÏÝ da kyau.Dan a yau nazo muku da Wani kyakkyawan albishir=؃Ü=ØƒÜ wanda zakuji dad'insa fiye da yadda zan fad'a muku.Nace ba, Bakuda Labarin hamshak'iya shahararriyar 'yar Kasuwar nan wacce tai K'aurin suna wajen kawo muku kayayyakinta na 'yan Gayu masu quality wato H.Empire <Øæß Lagos Mai gidan kayan sawa na mata na k'walisa da Kuma kayan kitchen?..."*

*To idan yau kuka tab'a ji ya kamata ace kun saurareni kunji da abinda nazo muku dashi. Kayan sawa kike so Wanda zaki zama tauraruwa a cikin 'Yan uwanki mata harma da Mai gida wato oga kwata kwata Hajiya ta , ko ko so kike duk inda kika gifta kallo ya koma kanki?. Ko Kuma kayan kitchen kikeso masu kyau da aminci daki bari. To Maza ku garzayo H.Empire <Øæß Lagos anan zaku samu duk Wani Irin Abu da kuke so, Dan mu kayan mu quaranti ne Hajiyata bakida tan tama akai, kudai ku gwada siya kawai zakusha mamaki Dan sai Kun bani labari. Muna Saida kaya kamar haka ka* =ØGÜ

*1,Atamfofi*
*2, lesses*
*3, Abaya*
*4, kayan kwalliya ko Wani iri ne*
5,*D'an kunnaye(jiwelleries)*
*6,takalma*
*7,hand bag*
*8, mayafai*
*9, sai Kuma kayan kitchen shima Muna sai dawa, Dan duk Wani kayan kitchen d'in da kike nema harma da Wanda Baki tab'a Gani ba ko sani to idan kikazo H.Empire <Øæß Lagos anan zaki samu duk Wani Irin kayan kitchen muna Saidawa akan farashi Mai sauk'i da rahusa siyan D'aya ko sari*.

*domun magana damu kai tsaye ko Kuma Neman K'arin bayani ku tun tub'emu ta wad'an nan numbers d'in kai tsaye kamar haka =ØIÜ+234 811 190 1302 /09020337676*


*Siyan na gari Mai da kud'i gida Hajiya ta*

*Sai mun Jiku=؃Ü=؃Ü*




07066508376________
'þFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD


*<Ø9ßHUYAAM<Ø9ß*


*__NA*


*__NAJA'ATU UMAR FAROOQ__*


*__(MRS SARAKIES =Ø‹Ü)__*


My channel link =ØGÜ
https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y


*Bismillahirrahmanirrahim*


PAGE 3þã 9þã


___________¡&


Kwance tashi Babu wuya a wurin Allah,satika suna wucewa Kwanaki suna shud'ewa harya kasan ce yau saura kwanaki biyu kacal bikinsu su ya zulaihat.a Kuma yau da safe Anty khadija ta sauka a cikin palace nan b'angaren Ammie ita da iyalanta gabad'ayansu Wanda suka zo Dan halarta wannan bikin har siyama wacce ta shige cikin su Huyaam ana ta hada_hada tare da ita. yau alhamis da yamma za'ayi cocktail Wanda anan cikin palace d'in za'ayi.sai Kuma gobe Friday idan Allah ya kaimu za'a Yi dinner sai Kuma ranar Saturday da za'ayi d'aurin AUREN.su Huyaam ansha lalle both red and black Wanda ya d'auki fatar ta yay mata mugun kyau ba kad'an ba kamar kisace ta ki gudu haka zakiji saboda yadda lallan ya tsaru ba kad'an ba,Dan saida suka samo k'wararriya wacce ta iya sosai zatai musu Dan wacce taiwa amarya ita tai musu. D'inku nan suma tailor ya gama ya kawo musu har gida d'azu da safe. Yanzu haka k'arfe hud'u da Rabi ne na yamman ranar,Huyaam na zaune kan stol Dake gaban mirror a Wani k'aton bedroom Dake nan gefen d'akinsu anai Mata kwalliya, an gama yiwa ya Zarah da Huda da siyama yanzun ita akayiwa.kallan kayan jikin Huyaam kawai nake wanda shine ankon cocktail partyn,Wani rantsatstsan material ne kalar army green gabad'aya jikin material d'innan stones ne dan sai Wani walwali yeke yana Wani bada different hasken stones d'in,d'inkin ya zauna mata ajikinta das. ga itama kanta kwalliyar da ake mata wani Irin K'ara mata kyau takeyi,Dan Mai kwalliya Ammie ta d'auko musu ta musamman saboda a samu a tsan tsarawa 'yan matan nata kwalliya ta kece raini.kallon Huyaam kawai Mai kwalliyar take bayan ta gama Mata kwalliya da d'aurin head gabad'aya.a fili ta furta "Masha Allah! Kinyi kinyi kyau sosai gimbiya" ta fad'a tana kallan Huyaam.murmushi Huyaam tai mata kafin ta ce "thank you" cikin sanyin muryarta .Huda ce ta turo k'ofar d'akin ta shigo bayan tayi sallama tana Kallan HUYAAM ganin yadda tai kyau ba kad'an ba itama Irin kayan jikin Huyaam d'in ne ajikinta. Mik'awa Huyaam Wani D'an k'aramin box tai Dake hannun ta ce "gashi inji Ammie ta ce a kawo Miki" karb'a Huyaam tai tana kallan box d'in lokaci D'aya tana bud'ewa har ta gama bud'ewa gabad'aya taga wata sabuwar sark'ar gold ce Mai Bala'in tsada da kyau,ta d'aga manyan idanuwanta Wanda suka Sha lashes ta Kalli Huda dasu ta ce "Kinga fa ansa min wata? Huda ta ce "eh! Ammien ta ce ki ajiye agunki gobe saiki sa" Jin jina

Please Login or Register in order to submit comment