Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

d'in ya wangale suka bar gidan gabad'aya ma'aikatan suna musu fatan dawowa Lafiya.


A Wani k'aton mall Wanda ko a k'asar ma ba kowane yake iya zuwa ba Dan saika cika Mai kud'in gaske sannan mutum yake iya zuwa saboda tsadar kayan Dake ciki da Kuma had'uwarsa.driver yay ya parking ya fito da sauri bud'ewa Afeef bayan motar yana matsa baya da sauri,Afeef ya fito cikin nutsuwa sannu a hankali yake tafiya har ya shiga cikin Mall d'in driver Kuma ya tsaya Yana jiransa.


Koda Afeef ya shiga Dayawa ma'aikatan wajen sun sanshi nan suka hau gaidashi da bashi girma tunda kowa Yasan companyn su fuskarsa ba boyayyi bace ba sannan Kuma yakan zuwa yayi siyayya a wajen time to Time .haka suka hau gaishe shi yana ansa musu da kulawa a haka harya ya nufi wajen manager na Mall d'in Ganin Afeef yasa Shima ya taso da sauri ya nufo Afeef suka gaisa cikin harshen turanci nan Afeef ya buk'aci a had'a shi da worker Wanda zai d'auka masa trolley, Babu musu mutumin yay Kiran D'aya daga cikin workers d'insu na Mall d'in bayan ya k'araso yace ya d'auko trolley yabi Mr Afeef zaiyi siyayya Aciki,Babu musu worker din nan ya tafi ya d'auko Yana jin Dad'i aransa ganin afeef harya dawo ,ganin ya dawo yasa Afeef yay wa manager godiya sannan yay gaba shi kuma worker d'in Yana biye dashi a Baya rik'e da trolling.wajen dogayen riguna suka fara zuwa ya ilahi haka na ambata araina Dan wasu luxurious kayane na ajin k'arshe a wajen sai wani d'aukar ido suke Yi da walwalin duwatsu ajikinsu.idan Afeef ya sauka akan wasu dogayen riguna guda biyu Wanda suka kasance Iri D'aya sak kalar pitch color nan yasa aka d'auko masa su Dan Yana tunanin zasu yiwa HUYAAM da Huda babu musu aka d'auko aka Mik'a masa aikuwa Yana duba size d'in sai yaga zasu musu nan ya Mik'awa worker d'in shikuma yasa cikin trolling shikuma yay gaba Saida ya d'aukowa su Huyaam dogayen riguna guda hur hud'u duk masu bala'in kyau da tsada sannan kuma ya d'aukawa ya Zarah da muneefa,sai ya'yan Fulani Salamatu suma duk ya d'auka musu kai D'aya suda 'ya'yan baba turaki su ikleema dukansu Suma sai Kuma 'ya'yan baba wambai su safnah dukansu Suma gabad'aya haka ya siya musu babu abinda ya ban banta dan haka yake baya tab'a siyawa K'annensa Abu Bai siyawa duka Yaran gidan ba.


Daga wajen dogayen riguna Kuma sai ya wuce wajen kayan maza nan ya d'aukar su muneeb da duka Sauran yaran gidan Maza bayan ya gama dasu sannan ya wuce wajen hands bag da takalma nan ya siyawa su Huyaam masu bala'in kyau da tsada ko Wacce biyu biyu sai Kuma ya wuce wajen jewelleris nan ma ya d'ibar musu daham gabad'ayansu sai kuma ya d'aukowa su Ammie gold ko Wacce biyu biyu masu bala'in kyau da tsada daga k'arshe yasa sauran ma'aikatan suka Taya wannan worker d'in na farko suka tayashi d'aukar kayan saboda yawan su daga nan Kuma sukai wajen payments akai counting din kud'in gabad'aya aka fad'a masa babu Wani musu haka ya Mik'a musu card d'insa suka cire kud'in suka Mika masa ya karb'a ya fita waje wajen mota ma'aikatan suka biyo shi da kayan Nik'i Nik'i tunda driver ya hangoshi ya fito ya Bud'e musu boots d'in haka suka zube kayan gabad'aya aciki Bayan sun gama Afeef ya biya sannu ya shiga back seat Wanda driver ya Bud'e masa ya shiga daga nan Basu zarce ko Ina ba sai gida......







07066508376________
'Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD




*<9 HUYAAM <9*




*paid book =*



*Free pages*




*NA*



*___(MRS SARAKIES =؋)__*




*Bismillahirrahmanirrahim*




PAGE 9



____________&



Sai da su Huyaam sukai kwana biyar cif basuje school ba saboda Interval d'in exam da Suke dashi.basa zuwa ko Ina sai dai suyi karatu da yamma Kuma su tafi islamiya....Ranar Sunday da safe Huyaam tana kwance saman gado tana bacci har wajen k'arfe 11 :20am Bata tashi ba ta baje akan gadon ga gashin kanta yadda ya bar baje nan saman pillow sai sharar bacci take abinta.bud'e k'ofar d'akin akayi Huda ce ta shigo shigowarta na ukune kenan tana zuwa tana duba taga ko Huyaam ta tashi?, Amma sai dai ta tadda Bata tashi ba. yanzunma Ammie ce ta aikota akan lallai ta taso Huyaam ko Bata tashi ba, shine yasa tazo ta.


Tsayawa tai kawai Daga nan Bakin k'ofar tana kallan Huyaam da mamakin yadda take sharar baccinta hankalinta kwance ,Huda ta sauke numfashi ta k'arasa shigowa har cikin d'akin zuwa gaban gadon ta kai hannu ta yaye blanket d'in da HUYAAM ta rufa dashi har saman kanta tana Kuma K'iran sunanta at the same time.


Cikin bacci Huyaam taji muryar Huda tana K'iran sunan ta, nan ta Bud'e idonta kad'an Wanda suke cike da bacci tana kallan Huda dasu .Huda tana rik'e da bargon a hannunta har lokacin tace .


"Kike Kallona? ki tashi baccin ai ya isa haka koh?..." ta fad'a tana Jan blanket d'in. HUYAAM ta had'e Rai ta damk'e blanket d'in da k'arfi ganin Huda na Neman yaye mata shi tace cikin shak'akk'iyar murya Irin ta Wanda bacci Bai ishe ishe Shiba.


"Banaso Huda miye Hakan? banaso ki K'yaleni". ta fad'a tana tura Baki gaba.


Huda tai murmushi ta k'ara Jan bargon da k'arfi tana cewa.


"Wallahi sai kin tashi Ammie ce tace nazo na taso ki ai,baccin ya isa haka sai kace Mai baccin mutuwa"ta fad'a tana k'ok'arin fusge bargon daga rik'on da HUYAAM tai masa .


Ganin haka yasa Huyaam ta yunk'ura da sauri ta mik'e Zaune itama ta fara jan bargon nanfa suka fara jaye jayen bargo da ko kawa. ganin da Gaske fa Huda take saita janye bargon yasa Huyaam Tai kanta da sauri cikin b'acin Rai tana yiwa Huda magana. Ganin haka yasa Huda ta saki bargon da sauri ta nufi k'ofar fita daga d'akin da gudu tana K'iran sunan Ammie .. Huyaam tai murmushi Jin abinda Huda keyi ta Maida bargon nan saman gadon sannan ta wuce toilet Dan yin brush da Kuma wanka.


Sai k'arfe Sha biyu Saura Huyaam ta fito daga d'aki,ta sauko downstairs nan main falorn gidan cikin shigar atamfa D'inkin doguwar riga A shape wacce tai mata bala'in kyau sai Wani walwali take acikinta saboda d'inkin da aka zubawa rigar. haka tafito sauko daga stairs d'in.Babu kowa a falon daga Huda sai muneefa ne kawai a falon suna zazzaune kan kujera suna kallo a TV kamar ance muneefa ta juya sukai ido hud'u da Huyaam wacce ke shigowa falon cikin sand'a zatai wajen da Huda take. muneefa ta Bud'e Baki zatai wa HUYAAM magana Huyaam tai saurin d'aura Hannunta saman Bakinta tana kallan muneefa alamar kada tai magana . muneefa ta koma ta zauna a hankali Dan kada Huda ta ganta tana gimtse dariyarta Dan tasan mai Huyaam take nufi tunda sun Saba.


Huyaam ta sauke numfashi a hankali ta fara takowa cikin sand'a har zuwa wajen da Huda ke zaune wacce tai backing d'inta ta Bata Baya tana zuwa tai saurin rufe mata fuskarta da tafukan Hannunta ta baya Huda.me muneefa zatai inba dariya ba nan ta saki dariyar da tai ta rik'ewa.itako Huda batai mamakin waye ba tunda ga k'amshin turaran HUYAAM nan tana shak'a nan ta Gane itace.


Ta rik'e hannun Huyaam wacce ta rufe mata fuskarta K'am tak'i saki, Huda ta Bud'e Baki tace .


"Huyaam miye haka ki cire Hannunki daga fuskata banaso"ta fad'a tana k'ok'arin cire Hannun HUYAAM daga fuskar tata.nan Huyaam tak'i saki saima K'ara damk'e fuskar Huda da tai, nan fa Huda ta fara k'ok'arin k'wace fuskarta Amma ta kasa ita Kuma HUYAAM sai murmushi take can Huda ta kai hannunta zata kamo rigar HUYAAM,tuni HUYAAM ta saketa tai baya da sauri Huda ta Mik'e zatai kan Huyaam tuni HUYAAM ta haye stairs tai d'akin Ammie da sauri har tana had'awa da gudu tana yiwa Huda dariya.Huda tai k'wafa ta koma ta zauna tana murtsuke idonta.


Ammie na zaune bakin gadonta tana gyara wasu kayanta HUYAAM tai knocking k'ofar Had'i da turawa ta shigo tare da sallama a bakinta.


Ammie ta d'ago tana kallanta ta ansa mata sallamarta. Huyaam ta k'araso d'akin tana sauke numfashi tana Kuma murmushi Had'i da juya banyanta tana tunanin ko Huda ta biyo bayan ta.


Ammie tana kallan Huyaam da mamaki tace .


"A'a keda waye Kuma? Kika shigo kina haki?...."ta fad'a tana kallan bayan Huyaam ko zataga me Huyaam d'in takewa waigen oho.


Huyaam ta sauke numfashi tace.


"Babu kowa fa Ammie".

Ammie ta sauke numfashi tace.

"keda Huda ne ko?..."


Huyaam tai murmushi batace komai ba nan Ammie ta Gane itada da Huda ne k'ila abinda suka Saba sukayi wato tsokanar juna.


Ammie tana kallan Huyaam tace.

"Yanzu kika tashi daga baccin ko?...."

Huyaam tai shiru tana shafa kanta . Ammie tace .


"Wallahi Huyaam idan Baki daina Irin wannan baccin ba Agidan nan ki kai har wannan lokacin Baki tashi ba zansa k'afar Wando D'aya nida ke agidan nan,sai kinje ulcer ta kama ki kizo kina ciwo ciwo Allah ma ya kiyaye". Ammie ta fad'a tana kallan HUYAAM.


Huyaam ta sauke idonta k'asa tana sauraran Ammie.


Ammie tace .


"Kinji ko Baki jiba?..."Huyaam ta d'ago kanta tana kallan Ammie da raunan nin idanuwanta Dan arayuwarta bata so taga Ammie cikin damuwa.a hankali ta k'araso kusa da Ammie ta rungumeta tace cikin sanyin murya.


"Kiyi hak'uri Ammie bazan K'ara ba"ta fad'a tana K'ara shigewa jikin Ammie.


Ammie tai murmushi tana shafa kan Huyaam Dan itama dolene take sawa taiwa Huyaam fad'a badan komai ba sai Dan ta gyara abinda take tunda ita macece duk mun daran dad'ewa ba'a gidan zata dauwama ba gidan Wani zata.Ammie ta sauke numfashi tace.


"Naji na hak'ura. but dear kinsan banason duk abinda zai B'ata Miki Rai ko? So please ki kiyaye, ni tsorona kada ki dinga zama da yunwa har Wata cutar ta kama ki". Ta fad'a tana Shafa kan Huyaam.


HUYAAM ta gyad'a mata kai tace a shagwab'e.


"In Sha Allah Ammie kema kin hak'ura ko?.."Ammie ta d'agota tana kallan fuskar ta da Murmushi tace .


"Na hak'ura dear dama bakimun Komai ba karki damu kinji?..." Huyaam tace "Thank u lovely mother".ta fad'a tana murmushi.


Ammie itama murmushin tai ta rik'e fuskar HUYAAM da tafukan Hannunta tana kallanta tace .


"Nevermind lovely daughter"ta fad'a tana fad'ad'a murmushinta .Huyaam tai murmushi tai kissing Ammie a Kumatu.


Ammie ta shafa fuskarta tace.

"Thanks dear fatan kinci abincin dai koh?..."


Huyaam ta girgiza mata kai tace cikin k'asa da murya.


"Yanzu zanje naci".


Ammie ta kalli Wani Dan k'areren agogon bangon Dake d'akinta sai Kuma ta juya tana kallon Huyaam tace.


" past 12 fa Huyaam, Amma kike zaune Bakije kinci abinci ba? oya wuce kije kici".ta fad'a tana nuna mata hanyar k'ofa.Babu musu HUYAAM ta juya ta fita daga d'akin bayan ta kullowa Ammie k'ofar.


" LAmmie ta sauke numfashi tana girgiza kai tare da cigaba da abinda takeyi.


Huyaam tana sauka k'asa tun kafin ta k'araso sukai ido hud'u da Huda wacce take Harararta. Ganin haka yasa Huyaam ta sauko downstairs d'in a hankali tana Murmushi ta had'a hannayenta biyu alamar roko tace.


"Dan Allah kiyi hakuri lovely twin". Ta fad'a tana murmushi.

Huda ta d'auke kai kafin tace .


"Sorry for your self Yarinya ,Dan bazan tab'a hak'ura ba sai na rama ,Kuma karkiyi tunanin ma yanzu zan rama,Dan idan zan rama ma ai ba yanza ba sai kin sakan kance kamar yadda Nima kikai min". tana fad'ar haka ta Maida hankalinta kan TV ta cigaba da kallonta.


Huyaam tai murmushi ta k'arasa dining d'in cikin sand'a ta zauna kan kujera har lokacin a tsorace take da Huda Dan Gani take a kowani lokaci Huda zata iya tasowa kanta .ta bubbud'e warmers d'in tana k'ok'arin d'ibar Abinda zata iya ci...



_____________&



Washe gari Monday Huyaam basuda paper sai washe gari wato Ranar Tuesday. Aranar kan suna da paper zasuyi second to the last paper itama ta safe ce Danma yau D'aya zasuyi ba biyu ba,Dan haka da wuri suka Tashi sukai shiri suka tafi makaranta.basu suka dawo ba sai wajen k'arfe biyu da Rabi na Rana Shima suna dawowa sukai shirin islamiya k'arfe uku da 'yan mintuna Kuma suka tafi..... Ranar Wednesday Basu da paper sai ranar Friday itace last paper kenan aranar kuma zasuyi candy.da yamman Ranar su Huda suka shirya ya haidar zai kaisu suyi siyayyar kayan graduation d'in da zasuyi Mai martaba ne da kansa yace akaisu kowa ya zab'i abinda yake so duka su biyar d'in harsu ikleema tunda dama sune zasuyi graduation d'in a duka gidan ,Shine a matsayin gift d'in Da Mai martaba zai Basu . kuma ko Wacce dama uwarta tayi mata gift na graduation . itama Ammie tayiwa su Huyaam d'in Kuna musu bala'in tsada kala hur hud'u less da atamfa.dama tun jiya su Huda suka fad'awa su ikleema akan cewa yau za'a kaisu shopping....yanzu haka k'arfe biyar ne Saura na yamman ranar su ikleema already sun fito daga part d'insu suna tsaye nan harabar gidan itada safna ko Wacce cikin shiri sunyi kyau ba kad'an ba suna tsaye suna k'ok'arin zuwa part d'in su Huyaam Aziza ta fito daga part d'insu ta k'araso har wurinsu tana kallansu tace.


"Ina su ishashshu mulkakku Daman suke basu fito ba koh?..."Ta fad'a tana kallon hanyar part d'in su Huyaam.


ikleema ta Kalli Aziza wacce ta Wani had'e Rai tace .


"Haba Aziza Dan Allah ki daina abinda kikeyi Babu Dad'i,yanzu me zaisa ki Fad'i Irin wannan maganar yanzu idan agabansu kikayi fa? Ai kema kinsan fad'a kika takalo ko?..."Aziza zatai magana ya Haidar ya fito daga part d'insu sanye yake cikin shigar k'ana nun kaya Wanda sukai masa bala'in kyau sai baza k'amshi yake hannunsa Kuma rik'e da key d'in motarsa su Huyaam Kuma suna bayansa .tun daga nesa Aziza take kallansu Huyaam Ganin yadda sukai bala'in kyau ba kad'an .gabad'ayansu sanye suke cikin shigar doguwar rigar abaya maroon color wacce ta fito da ainihin kyansu sai Wani d'aukar ido kayan suke saboda duwatsun da akai adon rigunan dasu sai kawo haske suke ta ko Ina.Ai take Aziza ta d'auke kanta tare da tsuke fuska ta Maida gefe ganin yadda kallo ya koma kansu HUYAAM Dan hadiman gidan nan sai kallansu suke suna musu kirari,har suka k'araso wajen motar. ya haidar ya danna remote d'in Dake jikin key d'in motar take motar ta Bud'e da Kanta ganin haka yasa Aziza tai saurin shiga can bayan motar Dan Bata so ma su hadu dasu HUYAAM bare tai musu magana, ikleema da safna suka shiga suma suka zauna kan seat d'in Dake gaban Aziza su Huyaam ne suka karaso Suma suka shiga inda su ikleema ke zaune HUYAAM ce k'arshen shiga tana Zaune daga bakin murfin motar.


Ya haidar ya juyo Yana kallansu fuska d'aure yace.


"Nine driver ku da duk zaku shige baya?wa kuka barwa front seat d'in?...". Sukai shiru basuyi magana ba suna sunkuyar da kai k'asa.yace.


"ba magana nake muku ba?..."ya fad'a a D'an tsawace.


Huda ce tai k'arfin halin kallan Huyaam Wacce ta tura Baki gaba tai k'asa da murya tace.


"Kije tunda kece a farko HUYAAM"...HUYAAM ta d'ago zata harari Huda sukai ido hud'u da ya haidar Wanda shima kallanta yake yay mata Wani kallo take ta Bud'e Murfin motar ta fito daga wajen ta koma gaba ta zauna tana K'ara tura Baki gaba .ya haidar ya juya ya ta-da motar suka fice daga gidan bayan an wangale musu gate fadawan nan sai kirari suke musu.


Awani K'aton mall Wanda ake ji dashi a garin kano ya haidar yay parking motar ya fito Suma suka fito ya rufe motarsa yay gaba suka bishi a Baya Huda da ikleema sune a gaba sun jera suna tafiya Huyaam kuma da safna wacce ke ke tai mata surutu itadai sai dai ta bita da uhmm ko a'a sai Aziza wacce ta ware kanta ita kad'ai tana tafiya cikin Isa da tak'ama sai Wani Shan k'amshi take .tun kafin su shiga cikin Mall d'in nan kallo ya koma kansu saboda Babu k'arya ko Wacce tayi kyau Kuma keda kin gansu kinsan hutu Had'i da Jin Dad'i sun samu muhalli ajikinsu.Ahaka suka shiga cikin Mall d'in ya haidar ya Kallesu bayan sun shiga yace.

"kuje ku zab'i duk abinda kuke so".yana fad'ar haka samu waje ya zauna ya zaro wayarsa. ikleema da Huda suka tafi wajen trollories d'in Dan d'aukar musu.D'aya ikleema da safnah Huda Kuma ta d'aukar musu itada HUYAAM Aziza kuwa dama sun San halinta itama haka ta K'arasa ta d'auki nata trolling tai nata wurin HUYAAM ta k'araso kusa da ya haidar tai k'asa da murya tace.

"Yaya! ya ka zauna Kuma?..." Ta fad'a tana tura Baki gaba.


Batare da ya haidar ya d'ago ba Yana duba wayarsa yace.

"Da kukai Sa'a ma na rakoku shine kike tambayar ya na zauna ko? to ki zauna tambayata Karki bisu kuyi abinda zakuyi nidai ina gajiya tafiya ta Zanyi "ya fad'a Yana cigaba da kallan wayarsa.


HUYAAM ta tab'e Baki tabi bayan su Huda. B'angaren dogayen riguna suka fara zuwa nan suka fara zab'a kowa biyu biyu kafin su d'auki Wasu iri D'aya Guda biyar suka ce anko zasuyi gabad'ayansu .duka su biyar d'in harda Aziza suka d'aukawa da tai nata wurin,daga wajen dogayen riguna Kuma wajen hands bag da takalma suka nufa nanma kowa ya d'auki biyu biyu sai Kuma sukai wajen cosmetics suka d'auki turaruka masu bala'in kyau da tsada da kayan kwalliya,bayan sun gama da nan Kuma sai sukai wajen kayan graduation d'in da zasu d'auka nan ma dai sun d'auki abubuwa sosai daga nan Kuma sukai wajen payments. A cikin Mall d'in nan inbanda Kallansu Babu abinda akeyi ganin sun gama yasa ya haidar ya mik'e ya karasa wajen payments d'in shima bayan anyi counting kud'in ya Mik'a musu card d'insa suka cire kud'in sannan aka zuba musu cikin Manyan bags ma'aikatan wajen suka rakosu dashi har boots ya haidar ya Bud'e musu suka sa kayan ya zaga driver seat ya shiga ganin su Huda har sun shiga ya ta-da motar suka nufi palace.


K'arfe shida Saura suka shiga palace bayan ya haidar yay parking motar nan harabar gidan ya Bud'e musu boots kowa ya d'auki ledarsa Dan dama tun a wajen payments aka sawa kowa nata unlike su Huyaam da nasu ke had'e sai bayan kowa ya d'auki ledarsa Sukai wa ya Haidar godiya kowa ya nufi part d'insu bayan sunyiwa juna sallama.Amma Banda Aziza data Saka kayan a gaba tana K'iran Wani dogari Mai suna bala akan yazo ya kai mata nata kayan b'angarensu.


Gabad'aya su ikleema sai da suka juya suna kallan Aziza saboda mamakin abinda tai, Amma sai basuyi magana ba Suka juya suka cigaba da tafiya ganin ya haidar ya juya Yana kallanta alamar zai mata magana suko su Huyaam tuni sun shige part d'insu.


Ya haidar Yana kallan Aziza da bala yazo ya zube agabanta cikin rawar jiki Yana cewa.


"Gani ranki Dad'e" ya fad'a cikin girmamawa.

Aziza ta juya masa ido tace.

"Kayan nan zaka biyoni dasu". tana fad'ar haka ta juya zatai gaba ya haidar ya k'ira sunan bala da k'arfi wanda ya juyo da sauri Yana zare ido ya haidar yace.


"Kai bala karka sake ka d'auki kayannan idan ba zata iya d'auka ba ta barshi " ya fad'a Yana kallan Aziza data juyo da sauri tana kallansa Jin abinda ya fad'a.


Aziza ta Marai raice tace.

"Yaya haidar da nauyi fa kayan,Dan Allah ka barshi ya tayani d'auka mana".ta fad'a kamar zatai kuka.


Ya haidar yay mata Wani kallo yace.


"Su sauran 'yan uwanki da suka d'auki nasu kayan kin fisu ne? ba Kai D'aya kuka Siyo ba nawa kayan yake da Dan Rashin tausayi zakisa mutumin Daya kusan haifarki d'aukar miki kaya?..." ya fad'a atsawa ce.sai Kuma ya juya Yana kallan bala Daya k'asa tafiya yace.


"Bala ko baza ka tafi bane?..." Bala ya mik'e da sauri yace.


"A'a rankai Dad'e wane ni,Allah ya huci Zuciyarka".Yana fad'ar haka ya tashi ya bar wajen.Aziza ta fashe da Kuka ta d'auki kayan tai part d'insu tana rusa uban kuka kamar wacce akayiwa Wani mugun abu.ya haidar yay tsaki yabi bayan su HUYAAM......






07066508376________
'Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD


*<9 HUYAAM <9*



*NA*



*__NAJA'ATU UMAR FAROOQ__*


*__(MRS SARAKIES =؋)__*



*PAID BOOK =*



*FREE PAGES*





*Tallah! Tallah!! Tallah!!!*


*Ina kuke hajiyoyin gidan nan,nace Ina kuke hajiyoyin gidan nan?to maza ku matso ga wata garab'asa ta zo muku har inda kuke=؃=؃?.*


*Hajiya kaya Kikeso na fita kunya cikin taro ku Kuma so kike kallo ya koma akanki acikin Taron mata idan kika shiga biki ko suna ko Kuma Wani taro na musamman.to maza idan kina so ki kankarowa kanki mutunci kizo UK collection and gallery mu gwan gwajeki da kayanmu masu quality Wanda zaki gaji ki ajiye Dan kanki Amma badai ya mutuba Muna sai da kaya kamar haka=G*


*Atamfofi da lesses*
*Abaya*
*Shadda*
*Hand bag*
*Shoe*
*Veil na manya Dana Yara*

*Socks rin hands made d'in nan masu net*.

*Hula ta 'yan Gayu*

*Siyan D'aya ko sari*

*Duk zaki samu kan Farashi Mai sauki kedai ki garzayo UK collection & gallery Kisha Mamaki*

*Domin ganawa damu ko magana damu kai tsaye ku tun tub'emu kai tsaye ta wannan number kamar haka*=I08135305790

*Sai mun jiku =؃=؃=؃*


<9<9<9<9<9<9



*Bismillahirrahmanirrahim*




PAGE 1 0



__________&


Da kuka Aziza ta k'arasa b'angaren su.Ramla da walida ta rara a falon suna Zauna suna kallo Baki Bud'e suka bi Aziza da kallo ganin yadda ta shigo cikin falon tana zunduma uban kuka kamar wacce akayiwa Wani mugun abu.tun daga sama Fulani Salamatu Dake cikin d'akinta ta d'auro alwala ta fito daga toilet kenan zata ta-da sallah tajiyo kamar kuka d'aukarta ma ko walida ce yasa babu shiri ta fito daga d'akinta cikin tashin hankali ta sauko downstairs.


Mamaki ne ya kamata ganin yadda Aziza take kuka ta k'araso Gaban Aziza tana kallanta tai k'asa da murya tace.


"Aziza meyasa meki kike wannan uban kukan haka? Ina daga shopping kuke?...."ta fad'a Tana kallan Aziza tare da k'arewa falon kallo da mamaki.


Aziza da tun shigowarta ta dire kayan nan kan tiles tana kallan Fulani Salamatu tace tana sheshshek'ar kuka.


"Mummy ba ya haidar bane Dan nasa bala dogari ya d'aukar min kayan nan ya tayani shigowa dasu ciki Shine ya Haidar ya hanashi wai bazai kawo ba idan hazan d'auka ba na barshi. kuma Bai tsaya nan ba Saida ya wulak'anta ni a gaban gabad'aya bayin gidannan sai kallo na suke Dan dai kawai su Raina ni".ta k'arasa fad'a tana K'ara sautin Kukanta.


Fulani Salamatu da tunda Aziza ta fara magana take kallanta da mamakin abinda haidar yay mata . gabad'aya ranta ya gama B'aci tace cikin D'aga murya da b'acin Rai.


"Shi Haidar d'inne ya hana Wani bawa Irin dogari ya d'aukar miki kaya sannan Bai tsaya iya nan ba ya wulak'antaki agaban su saboda shi ya isa yake nufi kome?...." Ta fad'a da k'arfi har Saida hadimanta biyu Dake kitchen suna mata girki suka lek'o suna kallan iKon Allah.


Aziza ta gyad'a mata kai tana cigaba da murza idonta tana Kuma sheshshek'ar kuka.Fulani Salamatu ta gyad'a kai kafin cigaban tace .


"Wato tunda yayansa baya nan shine shi Kuma zai D'ora daga inda ya tsaya ko me yake nufi? To wallahi Bai isa ba bazai yuba yace sai takurawa Yara na agidan nan ba, ko yayansa alokacin da yake kan ganinyar Rashin mutuncinsa Baya min haka bare Kuma shi ki K'yaleni dashi Dan wallahi bazan zuba ido ana tsangwamarku ana wulak'anta Kuba kuda gidan ubanku bari Mai martaba ya shigo zan fad'a masa idan zai d'auki mataki gara ya d'auka idan kuma bazai iya d'auka ba toni zan d'auka da kaina sai dai ayi duk wacce za'ayi agidan nan Dan bazan d'auka ba". ta k'arasa fad'a tana huci Aziza dai sai share hawayen idonta take Yi Ramla koh da walida sun nan Zaune kan kujera sun zuba musu ido kawai suna kallansu .


Fulani Salamatu ta kalli Aziza tace. " ki wuce ciki ki wanke fuskarki ki barni dashi ai zai K'ara idan halin sane dama can shima ba mutunci ne dashi ba,ki dai na kukan nan haka Aziza". ta fad'a tana kamo hannun Aziza ta kaita har d'akinta ta cigaba da lallashinta kafin tace tai alwala tai sallah . Aziza ta gyad'a mata kai bayan ta goge hawayen fuskarta Fulani Salamatu ta fita daga d'akin ta koma nata danyin

Please Login or Register in order to submit comment