Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Babu mutane acikinta daga cikin gidan har su kansu masu gidan.





07066508376________
'Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD







*<9 HUYAAM <9*



(The love e& story)



*Paid book=*


*Free pages*



*NA*



*___NAJA'ATU UMAR FAROOQ ___*




*___(MRS SARAKIES =؋)=1___*



*Bismillahirrahmanirrahim*




Page 3


___________&


Washe gari da safe har k'arfe bakwai Saura gimbiya Aysha Bata farka daga doguwar Sumar da tai ba, gabad'aya hankalin su goggo ya gama tashi dashi kansa Mai martaba,iya da bugun zuciyarta ne kawai doctors d'in suka Gane cewa tana a yare .da k'yar da k'yar dai likitocin suka samu nasarar dai dai tuwar numfashinta kafin su d'auki mataki ja gaba .ganin numfashin nata ya dawo normal tana kuma buk'atar hutu yasa sukai mata allurar bacci kafin su fito suna sharce gumin wahala.


Gabad'aya daga kan gimbiya Bilkisu zuwa kan su goggoninsu suna nan Cikin asibitin suna zaune a k'ofar d'akin da aka kai gimbiya Aysha kafin daga baya akaisu Wani d'aki Dake cikin asibitin na musamman Dan su huta dan har K'arfe ukun dare a tsaye suke sun kasa sama saboda tashin hankali Dan Suma dai basuyi baccin ba yadda sukaga dare haka sukaga rana a wannan dare.


Wajen k'arfe takwas da Rabi Mai martaba yazo asibitin direct d'akin da gimbiya Aysha take ciki akai mishi rakiya .Yana zuwa Yana Bud'e k'ofar d'akin bak'insa d'auke da sallama zuciyarsa na bugawa da halin da zaizo ya tadda matarsa aciki idonsa ya sauka akan gadon adai dai lokacin da gimbiya Aysha ta Bud'e idonta Dan da kuka ma ta farka tana daga kwancen da take.k'arar Bud'e k'ofar da kamashin turaran da taji yasata juyo tana kallon Bakin k'ofar Dak'yar ,ido hud'un da sukai da Mai martaba yasa Bata d'auke idonta akansaba Dan gani take kamar zata ga babyn ta a hannunsa ya kawo mata ita ,tana kallansa harya k'araso cikin d'akin ya zauna nan kan kujerar Dake gaban gadon Yana kallan gimbiya Aysha har lokacin.


Gimbiya Aysha ta motsa lips d'inta kad'an tana k'ok'arin dai dai ta kanta tace.


"Rankai Dad'e ba'a ga baby naba ko?,ta fad'a tana kallansa .Mai martaba yay jimmm yana kauda kansa daga kallanta Dan Wani Irin rauni yakeji idan yaga matar sa Abar alfaharinsa tana wannan kukan ya Dake ya juyo Yana kallan ta yace cikin nutsuwarsa.


"Kiyi hak'uri da abinda zan fad'a Maki fulani!, hak'ik'a wannan abun daya faru muk'addarine daga ubangijinmu ,kiyi hak'urin sanar mikin da Zanyi cewar har yanzu ba'a ga Mai sunan Daada ba , Amma Kuma muna nan muna binciken yadda za'a sameta, yanzu haka kafin na taho saida natara zama na gaggawa a cikin masarautar nan tundaga kan ma'aikata har masu sarauta Dake cikin gidan nan ,nai tambaya ga duk Wanda yasan yaga zuwan matar da akace ta d'auki Mai sunan Daada da kuma fitar da ita daga cikin masarautar nan, Amma kowa yace shi bai ganta ba, sannan nasa a ciki tamin duk Wanda yazo taron sunan nan tun daga kan 'yan gidan nan Wanda suke AURE a waje har Wad'anda ke wajen masarautar nan duk nasa ayi bin cike yanzu haka ana kan binciken so Dan Allah Ina rok'anki da kiyi hak'uri Dan Allah Fulani"ya fad'a cikin lallashi.


Tunda ya fara magana gimbiya Aysha take kuka marar sauti tana kallan Mai martaba cikin rawar murya tace.


"Yanzu shikenan rankai Dad'e na na rasa baby nah jaririyace fa yaushe aka haifeta yaufa satin ta D'aya a duniya meyasa za'a rabani da ita? Metai musu ko kuma ni Mai nai musu Dana can cancin wannan sakayyar daga wajen su ,Ni Yanzu babbar damuwata shine bansan a Wani Hali take ciki ba zuciyata zafi take mun kamar ta fashe haka nakeji rankai Dad'e"ta fad'a cikin gunjin kuka .


Mai martaba ya mik'e daga zaunan da yake cikin nutsuwa ya Tako har zuwa gaban gadon ya d'ago gimbiya Aysha zuwa jikinsa Ya zauna nan akusa da ita tana jikinsa har lokacin.


Yay k'asa da murya yace.


"Na sani Fulani Amma kiyi hak'uri Wallahi Nima Ina cikin damuwa Amma in Sha Allah za'a ganta"ya fad'a cikin damuwa.


Gimbiya Aysha ta d'ago tana kallansa kafin tace cikin Damuwa.


"Yanzu Ina sultan yake?Dan Allah ka kula min dashi shima karsu rabani dashi".ta fad'a fuskarta na bayyanar da tsoro.


Mai martaba ya shafa kanta yace ..

Babu Wanda zai rabaki da sultan Yana tare dasu goggo, please ummu sultan kiyi hak'uri"ya fad'a shima cikin rauni.


Gimbiya Aysha kasa shiru tai Dan gabad'aya jinta take kamar ba itaba yanzu Shikenan anrabata da 'yarta wacce take mutuwar so da k'auna, tunda tai ido hud'u da babyn bayan haihuwar ta datai lokaci D'aya taji babyn gama tashiga ranta ashe bama zata rayu da itaba yanzu ko a wani Hali take oho. idan ta tuno da wannan Abu shike sawa taji Wani kunci ya mamaye mata zuciya.knocking k'ofar d'akin da akai yasa Mai martaba matsawa daga kusa da gimbiya Aysha ya koma kan kujerar ya zauna kafin ya Bada iznin shigowa.daya daga cikin doc din suke kula da gimbiya Aysha ce tashigo da sallama abakinta ta gaida Mai martaba cikin ladabi ,Mai martaba ya ansa mata Batare da ya kalleta ba ta sanar dashi tazo duba Jikin gimbiya Aysha ne, take mai marataba ya Bata iznin ,ta tafi ta k'arasa gaban gadon gimbiya Aysha ke zaune akai har lokacin tana sunkuye da kanta k'asa tana share hawayen dayak'i tsaya mata doc tai mata magana cikin ladabi akan tazo duba tane,Da ka gimbiya Aysha ta ansa mata nan doc ta fara duba gimbiya Aysha cikin nutsuwa ganin jinin natama ya sauka yasa ta rubutu Mata sallama tareda prescription d'in da zata siya bayan ta gama ta Kalli Mai martaba da Ladabi tace.


"Rankai Dad'e za'a iya sallamarta, yanzu haka ma na rubuta sallamar".ta fad'a tana sunkuyar da kanta k'asa.


Mai martaba ya jinjina kai kafin yace cikin nutsuwa.

"Ok doc bari naje yanzu sai su Bilkisu su shigo su taimaka mata" Yana fadar haka ya Maida dubansa kan gimbiya Aysha, tuni doc d'in ta fice daga d'akinta


Mai martaba Yana kallan gimbiya Aysha yace .



"Allah ya K'ara lafiya Fulani Dan Allah kada ki k'ara sawa kanki Wata Damuwar please kinsan bazan iya d'auka ba koh?...."ya fad'a Yana mata Wani Irin kallo.


Gimbiya Aysha ta sunkuyar da kanta k'asa tana gyad'a masa kai hawaye na zirarowa a saman fuskarta tuni Mai martaba ya kau da kansa Yana barin d'akin gimbiya Aysha ta d'ago ta bishi da kallo .


___________&


Alokacin da su safara suka jefar da baby Zainab Basu dawo gidan ba Dan wanna umarnin shakundum ne saboda tace Dan kada a zargesu karsu sake su shigo masarautar a wannan lokacin har sai anshiga masallaci Dan yin sallahn ASuba, alokacin ne idon mutane baya kan kowa saboda a wannan lokacin da kowa yana masallaci ne Dan yin ibadah,Aiko haka akayi Dan awannan lokacin suka samu damar dawowa masarautar kuma da sukai Sa'a babu Wanda ya gansu Daga nan suka cigaba da aikinsu. Awannan dare haka shakundum tai bacci Irin Wanda ta Dad'e batai irin Saba ,Dan Yanzu kan ta k'udiri aniyar idan har Sau Dubu gimbiya Aysha zata haihu to itama sau dubu saita salwantar mata da abinda ta haifa Dan bazata fasa ba .Ai Allah nema yasa wannan cikin zaizo duniya Amma tun ranar da ta San gimbiya Aysha tana da ciki tai ta D'ana mata tarkon mugunta tana tsallakewa Allah ne kad'ai yasa zata haihun sai gashi yanzu bayan ta haihun asannan burin nata ya cika.yanzu sultan ne kawai ya rage Shine matsalarta ta rasa yadda akai har haryau sultan yak'i mutuwa duk da abubuwan da tasa akai tai masa Amma sultan yak'i mutuwa Kuma tabi duk wata hanya da sata sa a b'atar dashi abinci yaci tura, to shiyasa Yanzu tunda hak'arta ta kasa cinma ruwa akan sultan yasa tasa masa ciwo kullum acikin ciwo sultan yake baida ishashshiyar lafiya baya zuwa ko Ina acikin gidan sarautan nan ada ko school baya zuwa sai dai ai masa lesson Amma taga yanzu ya fara zuwa school d'in dole kuma ta k'ara dak'ile wannann hanyar sultan kusan 10years yake a Shekaru Amma Yanzu idan kika ganshi kamar D'an shekara 5 saboda yadda ya koma baya shiga cikin mutane kullum Yana part d'insu, part d'in nasuma sai dai d'akin uwarsa ko kuma Wanda ake kula dashi.yanzu haka tana zaune bakin gado tashinta daga bacci kenan ta zauna take wannan tunanin farin ciki ne fall zaciyarta tai Wani murmushi kafin Tace a fili .


"wallahi Aysha ni sarauniya Hajara Kuma shakundum indai Ina numfashi a duniya baki isa kin haihu da Mai martaba agidan nan ba matuk'ar ni ban haihuba". tana fad'ar haka ta Mik'e Dan shiga toilet danyin wanka bayan ta fito a gurguje ta shirya tunda taji labarin cewa an sallamo gimbiya Aysha tun d'azu daga asibitin Hakan yasa zataje tai mata jaje Dan kada a zargeta..haka ta fito hadimanta sukai mata rakiya har part d'in gimbiya Aysha Wanda alokacin suma 'yan cikin masa rautar suna ta zuwa dan Yi mata jaje.


__________&


Goggo hauwa ta dubi gimbiya Aysha wacce ke kwance saman gadon d'akin nata zazzab'i ya gama rufeta ruf tace cikin kwantar da murya.


"Dan Allah gimbiya Aysha kiyi hak'uri idan Mai sunan Mai babban d'aki (sunan Daada kenan mahaifiyar Mai martaba Ina fatan kun Gane shi akasawa jaririyar)rabo ce Za'a ganta Dan Allah kiyi hakuri kinji"ta fad'a cikin sigar rarrashi.dan tunda suka dawo daga asibitin nan gimbiya Aysha take kwance Bata tashi ba .


gimbiya Aysha batai magana ba Dan ita kad'ai tasan halin da take ciki ayanzu.


Gimbiya Bilkisu ce dake zaune kan kujera dake d'akin ta haday Kanta da gwiwa damuwa fal ranta idonta ya kumbura yay suntum saboda Kukan da Tasha tace cikin rawar murya wacce k'iris ya rage ta saki Kukan da take rik'ewa.


"Dan Allah Yaya gimbiya kiyi hak'uri nasan nice silar faruwar komai Dan Allah ki yafemin wallahi idan na tuno da cewa nice silar faruwar komai sai naji kamar zan Mutu saboda Damuwa,Dan Allah Yaya gimbiya ki yafemin".ta fad'a tana Wani Irin kuka Mai ratsa zuciya.


Jin Muryar k'anwar tata yasa Gimbiya Aysha ta Bud'e idanta kad'an da suka kumbura saboda Kuka tana kallan gimbiya Bilkisu tace cikin dashashshiyar Murya.


"Ko kad'an Bakimun Komai ba Bilkisu dama can Allah ya tsara koba ta silar kiba sai an rasa babyn mu ki daina fad'ar Irin wannan nidai banga laifin kiba "ta fad'a cikin rawar murya.


Gimbiya Bilkisu ta Kalli gimbiya Aysha tace.


"Nagode da kika fahimceni Yaya gimbiya in Sha Allah za'a ga babyn duk Wanda ya d'auketa ma Allah bazai tab'a Basu damar cutar mana da ita ba"ta fad'a tana share hawayen ta.goggoninsu duk suka ansa da in Sha Allah.itadai gimbiya Aysha kukun zuci kawai take .aranar haka akai ta zuwa yiwa gimbiya Aysha jaje wasu basa samun damar ganinta saboda halin da take ciki.hajiyarsu data ji wannan Abu haka tai ta K'iran gimbiya Aysha tana Bata Baki ita ko Daada mahaifiyar Mai martaba tana can india ganin likita shiyasa Bata san halin da ake ciki ba ,kuma Mai martaba da kansa ya hana a fad'a mata saboda karsu ta-da mata da hankali Dan batanan akai haihuwar tana can, aikuwa tunda taji labarin haihuwar da Kuma takwarar da akai mata take ta murna da muradun dawowa taga takwararta.


Wasa wasa har baby Zainab tai sati D'aya da Bat'a ba'a ganta ba Babu labarinta babu dalilinta nan dai gimbiya Aysha ta sare da samun 'yarta Dan tasan tunda har aka kai wannan lokacin ba'a gantaba tofa samunta sai dai tsananin rabo .Ahaka dai ta fawwalawa Allah lamuranta tana addu'a babu dare babu Rana akan idan 'yarta tana raye Allah yasa ta tafad'a Hannu nagari idan kuma Bata raye Allah yay Mata Rahma Dan ita yanzu tama daina kukan filin sai dai na zuci ta Mik'awa Allah duka Al'amuranta.A Ranar da baby Zainab ta cika sati biyu da Bat'a a Kuma ranar su goggo hauwa suka tafi bayan sunyiwa gimbiya Aysha nasiha sosai tunda dama sun D'an K'ara zamane dan kwantar wa da gimbiya Aysha hankali Ba Dan komai ba, itadai ta nuna musu ta karb'i k'addara ahaka har akai wata D'aya ba'a ga baby Zainab ba zuwa lokacin Kuma gimbiya Aysha harta gama fiddarai daga samun baby Zainab wacce ko nickname ba'a sa mata ba Mai martaba da hajiyar su kullum cikin kwantar mata da hankali da nasiha suka mata kuma har lokacin Daada Bata dawo k'asar ba bare ta sani .ahaka dai har gimbiya Aysha ta fitar da Rai Daga samun baby Zainab Amma fa ciwon nan Yana nan Acikin zuciyarta Bai warke ba Bata kuma tunanin akwai ranar da zai warke tunda har ta rasa 'yarta a haka ta cigaba da safgoginta Amma fa abun Yana nan a ranta .



A wannan lokacin kuwa shakundum Wani Irin farin ciki take ciki tareda walwala ganin yadda gimbiya Aysha ke cikin k'unci wannan shine babban burinta a rayuwa kullum taga gimbiya Aysha cikin k'unci gefe D'aya Kuma tana nan tana shirin yadda zata K'ara Sako sultan agaba dasa masa ciwuwuka iri iri ahaka har ya mutu shima shikenan idan tai haka burin ta ya gama cika sannan Bata da wata sauran far gaba.wannan kenan.




*Tofa masu karatu meke shirin furuwa ne haka>? Wannan Karan Kuma ga inda Alk'alamin
' MRS SARAKIES =؋ ya kawo mu ,shin Ina baby Zainab take Shin tana raye ko Bata raye?idan tana raye tana Ina?su waye suka d'auketa?kudai ku kasance Dani Dan jin yadda labarin zai kasance dan war ware muku shi bit by bit Dan wannan tafiyar ta banbanta da sauran*




& Present &


4 April,2025



Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD






*<9 HUYAAM <9*



(The love e& story)





*NA*



*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*



*___(MRS SARAKIES =؋)=1___*




*Bismillahirrahmanirrahim*




Page4


__________&


*Present*

4 April,2025


*Emir palace kano state*



Wajen k'arfe shida dai dai na yamman Ranar, Wata k'atuwar mota ce nagani ta tunkaro Wani babban gate Irin na gidan sarauta motar k'irar family car ce sabuwa dal da ita . tun kafin motar ta k'araso naga wasu dogaraye Wanda suke Zaune abakin gate d'in gidan daga waje Wanda ak'allah zasu kai kusan su shida sai police guda hud'u Wanda da dukan alamu sune suke tsaron gate d'in.mutane biyu daga cikinsu naga sun mik'e cikin sauri suka wangale k'aton gate d'in gidan, adai dai lokacin motar ta iso bakin gate d'in gidan direct ta kutsa kai ta shiga har cikin gidan yayin da fadawan nan suka cika wad'anda ke cikin motar da kirari tare da saukowar su lafiya.


A babban compound d'in gidan motar tai parking .Wani dogari na gani ya fito daga gaban motar cikin sauri inda yay saurin zuwa ya Bud'e bayan motar Wanda naga yaran gidan ne gabad'ayansu sanye da uniform na islamiya a jikinsu Wanda da dukan alamu daga islamiyar aka d'aukosu.


yara mazan ne wad'anda ke seat d'in farko suka fara fitowa daga cikin motar cikin shigar uniform na islamiya kusan su hud'u Wanda a shekaru a k'alla zasuyi 12 years haka,sai da suka gama fitowa sannan naga Yara matan suma sun fara fitowa , Wad'anda sune k'ana nun cikinsu,su su hud'u ne suma Wanda a shekaru a k'alla zasuyi 8 years haka D'aya ce kawai take 12 years Acikinsu.bayan sun gama fitowa sai yayunsu 'yan mata Suma su hud'u Wanda duk Sa'an nun juna a shekaru zasuyi 17 years haka , bayan sun gama fitowa sai yayansu suma su hud'u biyune manyan cikinsu wadda suka fisu dan sune manya Wanda a shekaru zasuyi 24 haka sai sauran biyun Wanda su Kuma ashekaru zasu 22 haka , gabad'ayansu sun gama fitowa wasu sun cikin gajiya Dan naga sai Wani ya Mutsa fuska suke alamar gajiyawa atare dasu .bayan sun gama firfitowa kowa ya nufi part d'insu dayake gidan Irin K'aton gidan nan ne Mai d'auke da sashe daban daban Wanda a k'alla zasuyi guda biyar agidan, sashe biyu suna b'angaren dama sai sauran sashe ukun Dake nan b'angaren hagu.


Wanda ke b'angaren Daman part na farko naga wasu daga cikinsu sun nufa su_su biyar suka nufi part d'in Wanda su Hud'un mata ne sai namiji guda D'aya,yaran sune agaba macen da namijin kenan, namijin Yana rik'e da Hannun k'anwar tasu Mai suna muneefa wacce itace autar su sai shi Mai suna muneeb.


Daga bayansu kuma yayar suce Wadda itace Babbar cikinsu Mai suna zarah sai K'annanta Wanda suke bi mata suna bayanta D'aya na rik'e da D'aya ajikinta da dukan alamu d'ayar Babu lafiya ne Wanda Sa'an nun juna ne .


Ta juya Ganin da tana bayansu,ganin basa sauri yasa tai gaba.ta tsaya tana kallan wacce ke rik'e da d'ayar tace cikin fad'uwar gaba .


"Huda! meya samu HUYAAM d'in naga kin rik'ota?...."ta fad'a tana kallan HUYAAM wacce idonta ke lumshe.


Wacce aka k'ira da Huda ta d'ogo tana kallan wacce tai maganar tace cikin Damuwa.


"Wallahi ya Zarah tun muna class tace min kanta na ciwo,to sai yanzu Kuma da muka dawo gida muna sauka sai naga tana k'ok'arin fad'uwa shiyasa na rik'ota".ta fad'a cikin damuwa.


Wacce aka k'ira da Ya zarah ta k'araso da sauri cikin fad'uwar gaba Dan tana tsoron ace ciwon k'anwar tasu ne zai tashi ta Mik'awa Huda Jakar Hannunta tace.


" rik'e min bari na kamata". ta fad'a tana k'ok'arin rik'o HUYAAM daga jikin Huda..Babu musu Huda ta karb'a ta had'a ta rik'e musu jakan kunan duka ukun.ya Zarah tai gaba tana rik'e da HUYAAM Huda Kuma tana binsu abaya.


Da suka shiga falon babu kowa sai k'arar AC data fan sai k'arar TV dake tashi da sautin karatun Al'qur'ani Mai girma daga bakin Wani babban malami a k'asar nan.direct sama Huda ta haura zuwa d'akinsu rik'e da bags d'in nasu Dan ta ajiye musu .ita Kuma ya Zarah d'akin Dake nan downstairs Wanda shima yake a mazaunin nasu Duk da Basu fiye zama acikinsa ba sai lokaci zuwa lokaci yasa ta nufi Dan takai HUYAAM tunda tasan ba lallai ta iya haurawa sama A wannan yanayin da take ba.tana shiga d'akin ta k'arasa har gaban gadon ta zaunar da HUYAAM akai wacce idonta har sun kad'a sun koma JAA daga farin da suke ada. ya Zarah ta kalleta ganin kwanciya take son Yi tai k'asa da murya tace cikin Damuwa da lallashi.


"Sannu HUYAAM! bari na Baki magani in yaso sai ki kwanta d'in".ta fad'a tana kallanta da tausayawa.


Huyaam ta k'ara lumshe idonta Amma Batai magana ba.hakan yasa ya Zarah ta fita daga d'akin ta tafi kitchen Dan d'auko mata ruwa. Tana fita Huda ta shigo d'akin ta k'arasa har saman gadon wajen HUYAAM Dake kwance ganin kamar bacci take yasa ta juya ta tashiga toilet d'in d'akin Dan d'auro alwala tunda K'iran sallahn magrib akeyi .Babu dad'ewa ya Zarah ta dawo d'akin da gorar ruwa a hannunta ta tafi gaban lockan Dake gaban mirror ta jawo na tsakiyar ta d'auko Wani k'aramin box ta Bud'e ta d'auko park d'in PCM ta b'alli guda biyu sannan ta Maida ta rufe ta dawo gaban gadon inda har Huyaam ta kwanta ta zauna tana k'ok'arin d'ago Huyaam zuwa jikinta tace .


"Tashi Huyaam kisha maganin".ta fad'a tana kallan Huyaam bayan ta d'ago da ita.da k'yar Huyaam ta yadda tasha maganin nan . Saida Zarah ta tabbatar da ya maganin ya D'an tsirga mata sannan ta taimaka mata ta kwanta. tana k'ok'arin Tashi Daga saman gadon kenan aka Bud'e k'ofar toilet d'in d'akin Huda ce ta fito daga cikin toilet d'in tana d'igar ruwa alamar ta d'auro alwala ya Zarah tana kallanta tace .


"Yauwa Huda ki zauna da ita bari naje Nima nai alwalan" ta fad'a tana kallan Huda.


Huda data d'auko darduma a inda suke anyiwa tana k'ok'arin shimfid'a darduma Dan yin sallahn tace.


"To ya Zarah!, da sauk'i ai jikin nata ko?.ta fad'a tana kallan HUYAAM wacce ke sauke numfashi.


Ya zarah juya itama tana kallon Huyaam d'in kafin tace .


"Eh nadai Bata maganin Tasha"Huda ta gyad'a kai daga haka ya Zarah tabar d'akin.



Ya zarah tana yin sallahn magrib ta dawo d'akin Dan K'ara duba jikin Huyaam d'in ta Tarar da Huda ta fito daga toilet rik'e da HUYAAM wacce da dukan alamu ta tai maka matane tayo alwala itama, Huda ta zaunar kan daddumar dake shimemfid'e nan tsakiyar d'akin.


Ya zarah ta k'araso cikin d'akin tana kallan Huyaam tace .


"Sannu HUYAAM jikin da sauki kenan",sai kuma ta Kalli Huda tace." sallah zatayi ne?..."Huda tana k'ok'arin sakawa HUYAAM hijab Ajikinta tace.


"Gatanan dai cewa tai nakaita toilet zatai alwala"ta fad'a tana matsawa daga gaban HUYAAM bayan tasa mata hijab d'in Dan Bata dama tai sallahn.


Ya zarah ta sauke ajiyar kafin tace.


"Allah ya sawake tunda kina tare da ita bari naje".Huda tace.


" Shikenan".daga haka ya Zarah tabar d'akin.


Bayan sallahn isha'i gabad'ayansu suna zaune a dining gabad'ayansu tun daga kan ya haidar har zuwa kan muneefa suna dining suna yin dinner muneefa Dake kusa da Ammie ta Kalli ya Zarah tace .


"Ya zarah Inasu ya HUYAAM naga bangansuba?..."ta fad'a tana kallan ya Zarah . Ammie itama kallab ya Zarah tai tana jiran ansar da zata bawa muneefa Dan itama Ammien tambayar Dake ranta kenan tun d'azu muneefa ta rigata,ganin Bataga yaran nata ba bayan kuma ba haka suka sababa indai suka dawo daga islamiya ko boko tofa sai sunje har Inda take sunce sun dawo bayama HUYAAM itakan tana da k'ok'arin wannan .


Ya zarah Dake juya abincin gabanta Wanda Bata kai ga ciba tace cikin Damuwa .


"Suna nan,HUYAAM ce Bata da lafiya kanta ke mata ciwo Shiyasa Basu fito ba". ta fad'a tana k'in kallan Ammie wacce ta zuba mata ido.


Take gaban Ammie ya Fad'i Jin abinda Zarah ta fad'a sai kuma ta Dake tace.


"Amma shine babu Wanda yazo ya fad'amin acikinku?,bayan kunsan cewa bana wasa da duka jinyanku musamman ma HUYAAM kinsan Bata da lafiyar Amma shine kika kasa fad'a min Zarah"ta fad'a cikin b'acin Rai.


Ya zarah ta marai raice tana kallan Ammie tace."ai Ammie na Bata magani fa"ta fad'a tana kallan Ammie.

Ammi tace.

"Rufe min Baki babbar kawai kinsan Bata da lafiyar Amma kika kasa fad'a min".ya Zarah tai shiru ta sunkuyar da kanta k'asa .
Muryar Ammie taji tace.


"Tun yaushe ne kan nata ya fara ciwon?...."sai a sannan ya Zarah ta d'ago tace.


"Huda tace tun suna aji har muka dawo". Ammie tace.


"Yanzu tana Ina?.."


Ya zarah tace.


" Suna nan d'akin downstairs tare da Huda"tun kafin takai k'arshe Ammie ta mik'e ta nufi hanyar d'akin jikinta a Sanyaye gabad'aya sai Suma suka Mik'e suka bi bayan Ammie.


Ammie tana tura k'ofar d'akin ta Tarar da Huda suna kokawa ita da HUYAAM a Saman gadon bil hakk'i da gaskiya sun Zubo da pillows d'in Dake saman gadon k'asa gabad'aya sun jik'e sharkaf da zufa sai kace Wanda sukai gudun tsere fuskar Huda tayi jaga jaga da hawaye da sauri Ammie ta k'araso ta rik'o HUYAAM wacce gashin kanta ya bar baje saman kanta ta kamota kamar wata mahaukaciya tana cewa .


"Subhanallah Meya faru Huda?..."ta fad'a tana k'ok'arin rik'o HUYAAM Dake San k'wacewa daga rik'on da tai mata. Huda tace tana huci.


"Ammie wai dole saita fita kuma fa Bata da lafiya"ta fad'a kamar zatai kuka.


Ammie ta kalli HUYAAM wacce har lokacin idonta Yana rufe tana k'ok'arin k'wacewa daga rik'on da Ammie tai mata tace cikin sanyin murya.


"HUYAAM! Ina zaki?..

HUYAAM tai shiru batai magana ba Kuma Bata fasa k'ok'arin k'wace kanta daga rik'on da Ammie tai mata ba.Nan Ammie ta Gane ba ita bace ba, take ta fara Yi mata addu'o'i HUYAAM ta k'ank'ame Ammie tana cewa.


"Ammie kaina , Ammie kaina ki rik'emin zai fashe , Ammie zan Mutu"ta fad'a tana rusa da Wani Irin ihu.


Take Ammie tai Saurin rufe mata Baki tana K'ara mannata da jikinta tace Cikin damuwa.


"Innalillahi wainna ilaihi rajiun Baza ki mutuba HUYAAM in Sha Allah sannu" ,ta fad'a tana tufa mata addu'o'i har lokacin.itadai Huyaam sai jujjuya kanta take tana kuka ganin haka yasa Ammie ta dubi Huda tace cikin Damuwa .


"jeki d'akina ki Bud'e drower ki d'auko min maganinta yanzu sannan ki taho min da wayata akan mirror".ta fad'a tana tana rik'o HUYAAM.babu Bat'a lokaci Huda ta fita daga d'akin cikin sauri tai d'akin Ammie. babu dad'ewa ta dawo Hannunta rik'e da wata gora wacce ke d'auke da Wani magani aciki.ta Mik'awa Ammie gorar maganin da wayar. Ammie ta karb'a ta ajiye wayar nan gefenta ta Bud'e gorar ta tsiyaya a hannunta sannan ta shafa a fuskar HUYAAM wacce ta

Please Login or Register in order to submit comment