Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi tanaso ne anjima ko Kuma gobe idan Allah ya kaimu zatai mata kalba.Anam ta k'arasa har gaban mirror ta d'auko turare ta fesa mata tana kallanta tana murmushi tace. "Mami kinyi kyau". ta fad'a tana kallanta". Gimbiya Aysha na kallan Anam ta lumshe idonta alamar taji Dad'i Amma Batai magana ba.anty Amina ta kwantar ta saman gadon bayanta ta D'ora kanta saman filon ta d'auko sabon blanket da Anam ta d'auko mata ta rufa mata dai dai k'ugunta. Anty Amina Tana kallan Anam tace.

"bari naje gun sultan d'azu da kika lek'a ayaya kika sameshi?..." Ta fad'a da sigar tambaya.Anam tace. "Eh! na sameshi ya fito daga wanka Yana karanta Wani littafi". Anty Amina ta Sauke numfashi ta rik'e hab'a tace. "iKon Allah jiya fa haka muka kwana Yana ta ihu d'azu bayan ASuba Kuma Dana lek'a na samu Yana bacci ,gashi yanzu Kuma da kikaje kince wanka yayi harma Yana karatu". Anam na murmushi tace. "Wallahi Anty harda hira mukayi wai ranar Monday zai koma school". Anty Amina tai murmushi tace. "To Allah ya K'ara musu lafiya Baki D'aya". Anam tail ansa da Ameen jiki a Sanyaye........


Anty Amina ta fita daga d'akin Zuwa d'akin sultan.Anam Kuma ta koma saman gadon ta zauna kusa da maman nata tana tofa mata addu'o'in da duk ta iya kamar yadda Wani malamin islamiyarsu ya koyar da su indai suna tare da Marar lafiya .gefe D'aya Kuma ta tsura mata ido tana Kallanta haka take kullum inta zauna tare da ita tayi ta kallan mamar tata kenan kamar ta samu TV...

Anty Amina tana shiga d'akin sultan ta tarar dashi Zaune saman gadon sa wanda yake a gyare tsaf dashi har ga hand out rik'e a hannunsa har lokacin Yana karatun kamar yadda Anam ta fad'a.d'ago da kansa yayi jin anbud'e k'ofar Yana kallan anty Amina harta k'arasa shigowa cikin d'akin, sauke idonsa yayi Daga kallanta da yake Yi Yana ansa mata sallamar tata .anty Amina na murmushi ta zauna gefen gadon da yake kai tana kallansa har lokacin tai k'asa da murya tace. "karatu kake sultan?.."Batare da ya dag'o ba ya gyad'a mata kai .anty Amina tai murmushi tace. "To ya jikin?..."nan ma da ka ya ansa mata. Tace. "Kai min magana mana sultan?..." Ta fad'a tana Marai raicewa.ya dago ya kalleta ya D'an ware mata ido Yana murmushi Amma baiyi magana ba .anty Amina tana k'ok'arin mik'ewa tace. "Tunda baza kai min magana ba sai anjima". Tana fad'ar haka ta Mik'e.sultan ya rik'o hannunta Yana d'an murmushi yad'an Motsa bakinsa kad'an yace. "Me kike so nace". Anty amina tace. "Dama so nake kai magana kuma gashi kayi,nifa nafison duk lokacin da nake maka magana ka dinga ansa min bawai kadinga ansa min da ka ba". Yana rik'e da Hannun ta har lokacin yace. "In Sha Allah" sannan ya saki hannun nata .anty Amina tace. "me kake so ai Maka for lunch?..'ya Dan d'age kafad'a yace. "Koma meye zanci". Tace. "Ok, Amma kafin nan ka kunna Karatun Al'qur'ani da Kuma addu'o'in yanzu kaga Rana tayi ?.."yace.
"Ok" anty Amina tace. " To na tafi sai anjima". Yace. "good bye" daga haka ya d'auke hand out d'insa ya cigaba da karatun. anty Amina ta fita daga d'akin cikin farin cikin halin da tarar da sultan aciki tana yiwa Allah godiya da Kuma tasbihin ganin sauk'i ya fara samuwa a wajen sultan......



___________¡&

3:45pm


A Wani tsauni Dake can Wani k'auye Wanda yake lungu acikin wani k'auye Dake cikin garin ZARI'A.tsauni ne Wanda girmansa da Nisan gun zaiyi kilo meter 8, Dan kafin ma aje inda akesan zuwan ma wata uwar tafiyar ce. Cikin Wani tsohon Gini Wanda akai wata bukka ta Kara Irin Mai k'arfin nan a tsakiyar wurin ce Mai girman Gaske, na hango Wani Bak'in mutum kakkura Wanda duk jikinsa Zane ne gashi Babu wata sitirara kirki a jikinsa Dan jikin sama babu riga daga shi sai D'an kamfai.ke da inganshi dama zaki Gane ba bahaushe bane yare ne saboda yadda kaman ninsa suke, Amma idan kikaji Hausa a bakinsa kamar jakin kano.sanye yake da kaya irin na bokaye ya d'aura Wani Bak'in k'yalle a k'ugunsa sai Wani Abu Mai kama da fata daya d'aura a saman k'ugun nasa sai wasu layu Daya d'aura a duka dantsan hannunsa, gabansa kuma wasu k'warayene Wanda ke d'auke da kayan sidda barunsa aciki ,wasunsu ruwane aciki wasu Kuma wasu Irin ganyayyakine da garin magun gunan Iri daban daban na k'asa she daban daban. Gaban sa kad'an wata matace zaune tana kallansa Yana wasu Irin sum batu Amma sai naga idonta yana kansa da dukan alamu tasaba da zuwa wurin Dan naga ko tsoro Babu a tare da ita.sai da ya gama Sumbatunsa sannan ya kalleta da jaja jayen idanuwansa yace cikin wata iriyar murya wacce babu dad'in sauraro. "Wannan Karan mafa sai dai ke kiyi aikin da kanki ,Dan bazai yu Wani yay miki ba dole sai dai kije da kanki kisa mata maganin kamar yadda kika Saka mata a nafarko ,Wanda ta daina magana sannan kuma ta daina moruwa kwata kwata, to yanzunma idan kinaso aikin ya K'ara shigarta saidai kije da kanki Amma bazai yu mu tura aljanin muba aje a sake K'ona su a Banza kamar yadda akai waccen lokacin sukazo suka Sha jinya kamar bazasu tashi ba". Ya fad'a Yana zarewa gimbiya Hajara ido. Sha kudum ta gyara zamanta kamar zatai kuka Gaban ta na fad'uwa dum dum kamar zai tsage biyu tace. "Yanzu boka barzuk Babu yadda za'a Yi atura wani hatsabibi a cikin aljannun yaje yayi? wallahi wancan Karan ma daka sani nai da kaina nafi wata biyu kafin nasamu nai narasa akanta". Ta fad'a kamar zatai kuka.boka barzuk ya sheke da wata iriyar dariya har saidai wannan bukkar da suke ciki ta ansa dama ilahirin zagayen wajen gabad'aya, boka barzuk Yana kashe leb'e yace. "Yanzun ma zaki iya ai yadda kikai waccen aikin haka Zakiyi wannan ma". Shakundum tai shiru tana kallansa Gabanta har lokacin Bai daina fad'uwa ba, Dan Bata manta da waccan Karan bama Dan ba k'aramin wahala Tasha ba kafin tai nasarsa a kan gimbiya Aysha ba, Dan Saura kad'an ma a kamata Allah dai ya taimaketa..boka barzuk yace. "Ai yanzu aljannu baza su iya tun karar gimbiya Aysha ba, saboda addu'o'in da ake mata ana shafe mata duka jikinta dasu sannan ai mata rubutu Tasha Banda Karatun Al'qur'ani da Azkar da ake kunna mata kullum ta kwana Dashi tana sauraro.kinga ko ai babu Wani aljani duk mun hatsabibancinsa da zai iya zuwa yace zai tun kareta ta ko Kuma kusantarta,wancan lokacin ma Dan ke kikai aikin da kanki shiyasa komai ya faru.sannan ga can gidan iyayennta Suma Basu zauna ba kullum cikin addu'a suke mata da saukar Al'qur'ani sannan ga itama surukarku yadda Bata bacci Babu dare babu Rana tana tsaye Gaban ubangiji tana Kai masa kukanta Kuma duk akan matar d'anta da Kuma jikanta mafi soyuwa agunta". Ya k'arasa fad'a Yana Wani Irin murmushi.shakundum da duk ta jik'e da gumi Jin abinda boka barzuk ya fad'a tace cikin sanyin jiki. "Shikenan naji Zanyi da kaina boka". Boka barzuk Yay Wata iriyar dariya yace. "Yauwa 'yar gari ai dama nasan zaki iya" Sai Kuma yace. "yanzu me kike buk'ata ai miki Kuma ?... Ya fad'a Yana kallanta. shakundumTace. "so nake a kashe min ita kowa ma ya huta". Ta fad'a cikin b'acin Rai.boka barzuk yace. "kisa Kuma ? To bazai yuba domin tun ba yau kike so akashe taba Kuma Nasha fad'a miki gimbiya Aysha tana da tsawan Rai sosai Anan gaba shiyasa ma tun farko da Kika zo da wannan batun na ce Miki bazai yuba". Ya fad'a Yana kallan shakundum. Shakundum ta sauke numfashi tace. "to tunda kisan bazai yuba inaso ahauka tata tabi duniya ta yadda babu Wanda zai K'ara ganin ta bare Kuma aji labarin ta,dan so nake a Nisan tata da masarautar zazzau gabad'aya da shi kansa Mai martaba ko zai daina abinda yake min ya dawo da hankalinsa kaina kaga idan ta tafi daga can ta had'u da ajalin nata Idan ma ni ban kashe tanba ." Ta fad'a har cikin zuciyarta wacce Babu ko d'igon imani acikin ta.boka barzuk yace. "an gama".daga haka Kuma ya fara wasu Irin abubuwan sihiri ya d'auki tsawan mintuna Talatin yanayi sai kuma ya d'ogo ya kalli shakundum yace."Baganta ba Duhu kawai nake Gani". Shakundum ta zaro ido waje tana kallan boka barzuk tace. "Duhu Kuma barzuk.boka barzuk yace. "Tabbas duhu nake Gani dama fa na Sha faday Miki tana tare da Kariyar addu'o'in ubangiji shiyasa bazan iya ganin taba amma akwai mafita zan Baki duk abubuwan da zaki bi wajen hauka tatan akwai mata kai dayawa Wanda duk sai Kin bisu kafin aje ga wannan matakin shima idan akai ba wai take zata haukace ba ko Kuma tabar masarautar ba, dole sai Kin dawo nan kin karb'i Wani maganin da layu Shima Kuma sai tayi watanni kamar biyu tana hauka anan cikin masarautar sannan zamu mata kurciya tabar masarautar zazzau na har abada". Ya fad'a Yana Wani shek'ewa da wata iriyar dariya. Sai alokacin shakundum ta sauke ajiyar zuciyar salama duk da za'a d'au lokaci kafin komai ya kammala Amma Kuma hakanma sai taji taji Dad'i sosai jin za'a haukata gimbiya Aysha. Ta Kalli boka barzuk tace. Amma barzuk Babu yadda za'ayi ayi aikin a kusa". Boka barzuk yay mata wata tsawa yace. "Bafa ke kad'ai zaki aikin ba muma nan akwai abinda zamu tai Maka miki dashi sannan shi kansa aikin yana da matuk'ar Wahala dole sai anbi komai a sannu tukunna zamu kai inda muke San kai war". Gimbiya Hajara tace.."ayi hak'uri boka Mai zamani tuba nake".boka barzuk Yay k'wafa yace.. "sai Kuma me kike buk'ata?...". Ta k'ara gyara zamanta tace. "Sai Kuma sultan" boka yay shiru Yana sauraran ta tace. "Inaso ne a K'ara sa masa wani ciwon akan nada Dan so nake kullum ace Yana kwance Yana hauka shima baya moruwa ko kad'an kamar yadda uwarsa take sannan a K'ara nesanta sarki dashi yadda ko tausayin sa karya K'ara ji, bare Kuma ya dinga d'aukar sa a matsayin wata Rana zai masa amfani Dan naga fa yanzu har wai school yake zuwa ni Kuma abinda bana so kenan naganshi Yana rayuwa lafiya lafiya" .Ta fad'a tana kallansa. Boka barzuk yace . "Hakan bazai yuba Dan soyayyar sarki da sultan ginan Niyace ta har abada saidai A K'ara masa Wani ciwon, Kuma Shima sai lokacin da muka samu dama Dan Yanzu yana cikin tsarin addu'a na fad'a miki dukansu addu'a ake musu babu dare babu Rana". Shakundum ta had'e Rai azuciyarta tace.

"wai maiyasa ake musu addu'a ne ba'a tab'a Bata dama tai nasara akansu lokaci D'aya dole sai an d'auki lokaci kafin asirin ya kamasu to kodai sun fara ganowa cewa asirin ake musu ba ciwon Allah da Annabi bane ba, Amma Kuma babu komai tunda zai Yuwu ba wai bazai yuba ai da sauk'i,Kuma dole sai tabi duk yadda zatai Dan adaina musu wannan addu'ar.maganar da boka barzuk yay ne yadawo da ita daga duniyar tunanin Data tafi.yace. "sai Kuma me?.." tace. "sai Kuma Anam". Tun kafin ta k'arasa fad'a boka barzuk ya daka mata uwar tsawa yace. "Kul karki sake fad'ar haka Zainab Anam tafi k'arfin mu yarinyar da tun tana ciki take tsare cikin addu'o'i da Kariyar ubangiji ko kin manta attabun da muka shayi akanta Wanda har Hakan ya kusan zama silar rayuwarmu". Shakundum tace jiki na rawa Dan har lokacin batai recovering daga tsawar da boka barzuk yay mata ba tace Baki na rawa . "Ban manta ba". Boka barzuk yace. " Tom sai a kiyaye nan gaba". Shakundum tace. "Na d'auka".ya K'ara cewa ".Sai Kuma me?..." Tace. "Shikenan", nan ya had'o mata duk magun da ganyayyakin da zatai amfani dasu cikin wasu takaddu sai layu kusan guda biyar ya zube a gabanta Yana kallanta yace. "gasunan, wannan maganin k'ulli shida ne ko wanne akwai number ajiki daga number 1 har 6 Kuma duk ta number zamu bi muyi aikin tun daga number ta farko harta k'arshe Ina fatan kinji?.. shakundum ta gyad'a masa kai yace. "Yauwa to kije dasu zamuyi waya idan har kin shirya".cikin farin ciki shakundum ta d'auka tasa acikin jakarta sannan ta ciro kud'i naira million goma ta ajiye agabansa sannan tai Mai sallama ta fita daga cikin bukkar ta baya ..


Bak'aramar tafiya tai ba kafin ta fito daga kan wannan tsauni kafin ta k'arasa inda amintaccen dogarin gidan Wanda yake mata aiki wato haladu,inda yay parking motar,Yana ganin ta yay sauri ya fito daga cikin motar ya Bud'e mata bayan motar yana mata kirari har ya rufe sannan ya zaga driver seat da sauri ya shiga ya ta-da motar suka bar wajen da gudu sai palace.......




#<Ø9ßHUYAAM
#<Ø9ßLAMID'O
#<Ø9ßAZIZ CHIROMA
#<Ø9ßAFEEF




*Muje zuwa mutanan MRS SARAKIES =Ø‹Ü.ke daga Jin salon labarin kinsan zai k'ayatar ya Kuma fad'akar.akwai chakwakiya sosai anan gaba Dan labarin ma yanzu muka fara shi*.


*ga masu buk'atar fara payments zaku iya sa kud'inku a yanzu before mu gama free pages Regular group akan naira 500 kacal idan kuma muka gama Free pages zai koma 700 ne.ga masu buk'atar Vip Kuma 2 pages a Rana zaku iya biyan nai 1000 kacal. ku hanzarta ku fara biya tun kafin mu gama free pages.zaku iya tura kud'in ta wannan account d'in =ØGÜ*


2270127432 Naja'atu umar
Zenith bank

Evidence of payment (shaidar biya )via
07066508376

Da zarar mungama free pages Kuma zamu sa duk Wanda ya biya kud'in sa a paid group, karku bari ayi wannan tafiyar Babu ku =؃Ü=ØƒÜ mutanan arziki.





07066598376________
'þFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD


*<Ø9ßHUYAAM<Ø9ß*



*NA*


*__NAJA'ATU UMAR FAROOQ__*



*___(MRS SARAKIES =Ø‹Ü)__*



PAGE 2þã 4þã



*Tallah! Tallah!! Tallah!!!*


*Ina kuke hajiyoyin gidan nan,nace Ina kuke hajiyoyin gidan nan?to maza ku matso ga wata garab'asa ta zomu har inda kuke=؃Ü=؃Ü?.*


*Hajiya kaya Kikeso na fita kunya cikin taro ku Kuma so kike kallo ya koma kanki acikin Taron mata idan kika shiga biki ko suna ko Kuma Wani taro na musamman.to maza idan kina so ki kankarowa kanki mutunci kizo UK collection and gallery mu gwan gwajeki da kayanmu masu quality Wanda zaki gaji ki ajiye Dan kanki Amma badai ya mutuba Muna sai da kaya kamar haka=ØGÜ*


*Atamfofi da lesses*
*Abaya*
*Shadda*
*Hand bag*
*Shoe*
*Veil na manya Dana Yara*

*Socks rin hands made d'in nan masu net*.

*Hula ta 'yan Gayu*

*Siyan D'aya ko sari*

*Duk zaki samu kan Farashi Mai sauki kedai ki garzayo UK collection & gallery Kisha Mamaki*

*Domin ganawa damu ko magana damu kai tsaye ku tun tub'emu kai tsaye ta wannan number kamar haka*=ØIÜ08135305790

*Sai mun jiku =؃Ü=؃Ü=؃Ü*


<Ø9ß<Ø9ß<Ø9ß<Ø9ß<Ø9ß<Ø9ß


*Bismillahirrahmanirrahim*

____________¡&


Su Shakudum Basu dawo gidan nan ba sai wajen k'arfe shida Saura na yamma,saboda uwar tafiyar da sukayi Dan ba k'aramin tafiya suka Sha ba wai ahakanma Dan tasa haladu yay gudu a hanya ne.Agajiye ta fito daga cikin motar bayan haladu yayi parking ya fito daga driver seat da sauri ya Bud'e mata bayan motar,sai faman zab ga mata uban kirari kawai yake Wanda yasan wannan shine favorite d'inta akan sarauta.d'auke kanta tai bata ansa masa ba illah kallan b'angaren gimbiya Aysha kawai da tai kafin ta Wani cije leb'enta da karb'i tana Wani sakin murmushin da Babu Wanda ya isa ya Gane Hakan har sai idan mutum ya kula. D'aga k'afar ta tai D'aya ta fara tafiya a hankali cikin nutsuwa da izzah Dan kuwa cikin shiga take Irin ta sarauta Hakan yasa ta fito sak a matar sarki Dan a yadda ta fita ahaka ta dawo. Kallo ne kawai ya koma kanta Dan duka bayin gidan ita suke kallo Kuma duk inda ta gifta kuwa sai bayin gidannan sun duk'a har k'asa sun gaidata kawunansu a k'asa Cikin girmamawa. idan kuwa tabiyo hanya Koda wasa Baka Isa ka biyo hanyar ba har sai bayan ta bar wajen. Ahaka har ta Isa b'angarenta Wanda ke a can gefe. Tun daga bakin k'ofar shiga falon dogarayen da Suke b'angaren duk suka zube ak'asa suka shiga Yi mata barka da zuwa cikin girmamawa,da k'yar take iya ansa musu harta k'arasa shiga tangameman falon nata Wanda ya gaji da kayan more rayuwa .hadimanta ne kawai suke kai kawo a falon nata wajen ganin sun kimtsa komai yadda ya kamata kamar yadda sukeyi kullum.sud'in ma zubewar sukai a k'asa suka shiga kwasar gaisuwa, amintacciyar hadimar safara ta taso zata karb'i hand bag d'in hannun nata Amma ta da katar da ita ta hanyar d'aga mata hannu alamar Bata buk'atar Hakan .nan safara Taja burki ta tsaya tana sunkuyar da kanta k'asa. Shakundum ta Kalli Sauran hadiman nata Dake ta faman Yi mata sannu da zuwa nan ma dai da k'yar ta iya ansa musun harta haye stairs d'in b'angaren nata. tura k'ofar bedroom d'in nata tai bayan ta Bud'e ta juya ta k'ullo k'ofar da key . sannan ta k'arasa shiga cikin d'akin Bata zarce ko Ina ba sai inda zata b'oye hand bag d'in nata da tazo da ita Dan kada ta barta afili tsau tsayi yasa Wani ya shigo ya Gani.bayan ta b'oye ta dawo gaban gadon ta fara cire alkyabbar jikinta sannan ta k'arasa rage duka kayan jikinta Daga nan kuma ta shiga toilet danyin wanka Dan Wani Irin zafi take ji , Amma Kuma acan k'asan ranta Wani Irin farin ciki takeji zuciyarta fes Dan Gani take kamar komai yazo k'arshe ne akan abinda ya to Kate mata farin cikin ta na Wanda take fama dashi na shekara da shekaru....



*Washe gari*


K'arfe 7: 30am na safe sarki Abdallah ne ya shigo d'akin gimbiya Aysha bakinsa d'auke da sallama cikin shiga Irin ta sarauta Dan d'azu bayan ASuba yaso yashigo kamar yadda ya saba to Kuma sai Wani uzuri ya hanashi zuwa sai Yanzu ya samu ya fito,Kuma babu inda ya nufa direct nan ya iyo. anty Amina ce Dake gyarawa gimbiya Aysha filon da take kai ta d'ago tana ansa masa sallamar tasa .tana matsawa daga gefen gadon ta koma can site d'in tana sunkuyar da kanta k'asa bayan ta D'an duk'a tanai wa Mai martaba Barka da zuwa cikin girmamawa. kallo D'aya sarkie Abdallah yay mata ya ansa mata Yana K'arasa shigowa cikin d'akin ya zauna nan Bakin gadon anty Amina kuma ta fice daga d'akin Ganin yazo duba iyalin sane.kallan gimbiya Aysha Mai martaba yay data Bud'e idonta kad'an Wanda suke koda yaushe a kumbure tana kallansa dasu Bata ko kiftawa.shima kansa Mai martaba idon nasa Yana cikin nata sai Kuma ya lumshe su Yana bud'ewa lokaci D'aya ya kamo hannunta na dama yay mata murmushinsa Mai kyau cikin k'asa da murya yace. "Amincin Allah ya tabbata a gareki gimbiya nah". Ya fad'a Yana Wani k'an k'ame hannun gimbiya Aysha Wani Irin soyayyarta na k'aruwa a duka sassan jinkinsa.Lumshe ido gimbiya Aysha tai har lokacin idonta Yana kansa.ganin ta ansa masa da idon nata kamar yadda ya zama shine maganar ta a Yanzu tunda Bata iya magana yace cikin Jin dad'in ansa masa da tai. " Ya jiki ? Allah ya k'ara lafiya fulani nah" sai Kuma ya D'an runtse ido Yana bud'ewa lokaci D'aya yace. "kiyi hak'uri Aysha nah, in Sha Allah zaki samu lafiya soon.kiyi hak'uri idan na Gaza ta wannan b'angaren, kiyi hak'uri idan na Gaza ta fannin sama miki Lafiya duk da Babu inda ba'a jeba a fad'in k'asashen nan duk Wani hospitals da muka sani ko Kuma mukaji labari munje Amma kuma results d'in D'aya yake nunawa shine babu abinda yake damunki. sannan duk Inda mukasan akwai Mai maganin gargajiya Shima Babu inda Bakuje da Hajiya inna ba Amma sauk'i na Allah ne Yana sane damu gimbiya nah tunda kullum cikin Miki addu'a muke babu dare babu Rana Allah ubangiji ya Baki lafiya , Allah ya tashi kafad'unki Allah yasa kaffarane Aysha na". Ya fad'a cikin raunin murya.itadai gimbiya Aysha kallansa kawai kafin ta lumshe masa take da ido tana jin Duk abinda yake fad'a Amma Kuma Babu bakin magana. Mai martaba ya d'auke idonsa daga kallanta ganin idonsa na k'ok'arin kawo k'walla wai yau matarsa ce acikin wannan halin, wai yau gimbiya Ayshansa ce akwance babu lafiya shekara da shekaru Babu uhm Babu uhm_uhm saidai akwantar akuma tayar yau itace ta koma haka ya Allah" da ace dukiya na anfani ta b'angaren Samar da lafiya da kuwa ko dukiyar sa zata kare wajen ganin matarsa ta samu lafiya da wallahi ya Bada, sai dai Kash Babu halin yin hakan ubangiji ne kad'ai keda wannan damar kuma yake da Iko "ya Allah"haka ya am Bata kabawa wannan baiwa take tafiya cikin aminci". daga haka ya juyo ya Sumbaci hannunta idonsa Yana kanta har sannan yace cikin Wani yanayi "I love you Aysha nah Allah ya kula min Dake Allah ubangiji ya Baki lafiya". ya fad'a cikin damuwa.Anam ce tai knocking d'in k'ofar bayan wasu seconds Kuma ta turo k'ofar ta Bud'e tashigo bakinta d'auke da sallama cikin shigar uniform da school bag a bayanta da dukan alamu dai school za'a kai ta. Mai martaba ya zuba mata ido harta k'arasa shigowa cikin d'akin Mik'a mata hannu yayi alamar tazo gareshi Yana mata murmushi, itama murmushin ta sakakar masa Kafin ta k'arasa warinsa ta mik'a masa nata hannun ya kama Yana murzawa Yana kallanta yace. "Har anyi shirin za'a tafi school d'in?..." Ya fad'a Yana kallanta. Anam na murmushi ta gyad'a masa kai kafin tace. "Eh Dady". Sarki Abdallah ya gyad'a kai yace. "Masha Allah Ina fatan ana karatu Sosai". Tana murmushi tace. "Eh". Sarki Abdallah yace. " Good girl Allah ya taimaka". Ta ansa masa da Ameen.sakin hannun nata yayi ganin hankalinta na gun mamanta kamar yadda ta zuba musu ido itada baban tana kallansu.Anam ta matsa kusa da maman nata ta haura saman ta rik'o hannun gimbiya Aysha ta sumbata tana murmushi tace. "Na tafi mami saina dawo Allah ya Baki lafiya". Ta fad'a tana kallan gimbiya Aysha.lumshe idonta tai alamar ansa mata. shidai Mai martaba Yana kallansu da tausayawa Anam ta saki maman nata sannan ta sauka daga saman gadon tana kallon Mai martaba tace. "Saina dawo Dady". Ya rik'o hannunta ya jawota jikinsa ya rungume sai Kuma ya d'agota Yana kallanta Yace. "Allah yasa ayi karatu sosai mamana" ya fad'a Yana sakin Hannunta . Anam ta Ansa masa sannan ta juya ta fita daga d'akin. sarkie Abdallah ya bita da kallo hakama gimbiya Aysha Yana K'ara Jin k'aunar 'yar tasa na K'ara shiga ransa har ma da mahaifiyar tata.bayan tafiyar Anam Mai martaba Bai Dad'e a d'akin ba yay ma gimbiya Aysha sallama bayan yayi mata addu'o'i kamar yadda ya saba aduk kwanan duniya ya fita daga d'akin saboda Abincin da anty Amina ta shigo zata Bata.....


K'arfe shad'aya da mintuna Hajiya inna ce zaune saman kujera a nan d'akin gimbiya Aysha ta shigo duba tane kamar yadda ta Saba a kullum kwanan duniya.tana kallan anty Amina Dake gyarawa gimbiya Aysha kayanta Dake cikin press d'in kayanta tai k'asa da murya tace. " Nifa Amina wallahi tun ba yau ba nake cewa wannan Ciwon na Aysha ba iya b'atan 'yarta bane ya ja mata wannan ciwon ba harda sihiri ajikinta Dan haka wannan makamin ya fad'a mana kina fa ganin Abu shekara da shekaru inda ciwon Allah da Annabi ne ayya ci ace yanzu ansamu Wani sauyi sosai Allah na tuba, Kuma kina fa kallo Wani asibitin ne bamu jeba a fad'in k'asashen nan Amma Abu D'aya ake fad'a mana shine su basuga Komai ba inbanda hawan jinin kawai da akace tana da shi shima Kuma ance da sauk'i". Ta fad'a cikin Wani yanayi.Anty Amina tai murmushi ta juyo tana kallon hajiya inna tace. "To koma dai menene Allah ubangiji ya Bata lafiya har yau mudai bazamu gushe ba muna nan mun duk'ufa a kan addu'a da iznin Allah yaya gimbiya zata warke Allah zai tashi kafad'unta Hajiya inna in Sha Allah". Hajiya inna ta rausayar da kai tana tab'e Baki tace. "Ameen Allah yasa Amina ai mu haka mukeso Dan

Please Login or Register in order to submit comment