Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fad'awa su Huyaam akan tana gayyatar su zo.to jin Huyaam tai shiru batai magana ba yasa Huda ta kalleta ta cikin mirror taga hankalin Huyaam ma bama ya kanta Yana Wani wajen daban Hakan yasa ta juya tana kallonta kafin ta k'arasa kusa da ita tace.


"Sis". HUYAAM ta juyo tana kallon Huda Wacce ke sanye cikin shigar less d'inkin doguwar riga fitted gown Ash color da ratsin golding mayafin shima kalar kayan tasha uban d'auri tayi kyau sosai ba kad'an ba shigar su iri D'aya sukai da Huyaam. Huyaam ta kalleta Amma Batai magana ba.Huda tace.

"Ke tunanin me kike tun d'azu Ina tai Miki magana kinyi Shiru?..."ta fad'a tana kallan Huyaam bayan ta zauna a gefenta Huyaam.


Huyaam ta ya Mutsa fuska tace .


"Wallahi sis ji nake kamar banda lafiya".ta fad'a tana dafe kanta.


Jikin Huda yay sanyi ganin Huyaam ta dafe kanta tana tsoron ace ciwon tane zai tashi.sai kuma tai saurin cewa.


"A'a sis in Sha Allah ma Babu abinda zai sameki ".ta fad'a cikin tausayawa.huyaam ta d'ago ta kalleta tace .


"Sis kawai Kije ni bazan jeba". Ta fad'a tana k'ok'arin yaye mayafin jikinta.huda tai saurin rik'e mayafin HUYAAM ta marai raice tace.


"Please sis Dan Allah karki ce baza kije ba kinga Hakan Babu Dad'i fa,kawai ki daure muje in Sha Allah babu abinda zai sameki,Abinda yasa ma kike Jin jikin naki haka Babu Dad'i baccin da kikayi ne yasa kike jin Wani Iri amma muna fita in Sha Allah zakiji kin ware, karki ce kin fasa zuwa Dan Allah Dan nima idan baza kije ba nima Babu inda zani". Huda Ta fad'a itama tana k'ok'arin cire mayafin jikin nata .


Huyaam tai murmushi ta rik'e mayafin Dan tasan indai baza taba to itama Huda ba zuwan zatai ba Hakan yasa tace.


"Shikenan zani muje". Ta fad'a tana murmushi. Huda ta sauke ajiyar zuciya tai murmushi tace.


"Ko kefa ki kwantar da hankalinki in Sha Allah Babu abinda zai sameki itadai Huyaam murmushi kawai take.huda ta mik'e ta tafi inda suke ajiye takalmansu da hand bag d'insu ta d'auko musu iri D'aya sannan ta dawo ta ajiye ma Huyaam nata a gabanta tana kallan ta tace.


"Kisa mu tafi ko bashi kike so ba?.."ta fad'a tana kallanta .Huyaam ta Bud'e ido tace.


"A'a yayi mana tunda kema irinsa kika sa".Huda ta kamo hannun Huyaam bayan sun d'auki hands bag d'insu sannan suka fita daga d'akin.


Saida sukaje har d'akin Ammie sukai mata sallama sannan suka fito daga b'angaren gabad'aya . Abakin gate d'in bangaren su suka had'u dasu ikleema da suka biyo musu.safna ta saki murmushi tana kallan su tace .


"Ikleema ai gasu ma sun fito ba sai mun shiga ba"Huda tace.

"to kuzo mu koma ciki mana". Ikleema tace.

"A'a tunda kuka fito mu tafi kawai idan muka dawo ma shigo ko safnah?..."ta fad'a tana kallan safnah.

Safnah tai murmushi tace.

"Eh" sai kuma ta Kalli HUYAAM tace .

"Irin haka wannan kyau lallai kunsha kyau ba kad'an ba".Huda tace.

"zaki fara ko safnah?...dalla wuce mu tafi Keda bakya gajiya".safna tai murmushi tace .


"Ai gaskiya na fad'a ko ikleema?..." ta fad'a tana kallan ikleema. Huda tace.

"sai kiyi tayi nidai Kunga tafiya ta". tai gaba suka bi bayanta suna Murmushi.

_____________&


A b'angaren fulani Salamatu kuwa Aziza ce zaune kan kujera gaban mirror ga me make up d'in da fulani Salamatu ta k'ira for home service tazo tana yiwa Aziza kwalliya ga k'awayen Aziza nan suna zaune a d'akin suna jiranta Mai make up d'in ta Kalli Aziza bayan ta gama mata d'auri tace.


"Wow Masha Allah gimbiya kinyi kyau sosai" ta fad'a tana murmushi.Aziza da take cikin shigar Wani D'an k'areren yadi Wanda idan kikaji kud'insu saikinyi mamaki saboda tsadar sa sai Wani fidda hasken stone yake ta ko Ina different colors tai murmushi tace.

"Thanks", Mai make up d'in ta fara mata pictures da videos a wayar Hannunta bayan ta gama ta nunawa Aziza adai dai lokacin da hadimar fulani Salamatu ta shigo d'akin bakinta d'auke da sallama ta k'araso ta zube gaban Aziza kanta a k'asa tace .


"Ranki Dad'e fulani tace idan angama miki kije tana san Ganin". Aziza ta ya Mutsa fuska tace .


"Kije kice mata Ina zuwa".ta fad'a tana juyar da kanta gefe.hadimar Fulani Salamatu Mai suna Karima ta sunkuyar da kanta k'asa cikin girmamawa tace.


"To ranki Dad'e afito lafiya".tana fad'ar haka ta Mik'e tabar d'akin.


Babu dad'ewa Aziza ta fito zuwa d'akin ta shiga na fulani Fulani Salamatu ta sameta itama taci kwalliya tana zaune bakin gado ta k'arasa tace.


"Mummy Gani".


Fulani Salamatu tace .

"Dama tambayar ki Zanyi zaku fita da kayan naki yanzu ne ko sai Kun gun gama parting?.."ta fad'a tana kallan Aziza....Aziza ta yamutsa fuska tace.


"Mummy sai za'ayi pictures tukunna". Fulani Salamatu tace .


"A to shikenan kije"Aziza ta juya ta fita daga d'akin ta sauko downstairs Dan k'awayen nata tuni sun fita compound Dan anan za'ayi partyn.


Lokacin da Aziza ta fita compound ya Allah.wow haka ta Ambata ganin Yadda akai decorations d'in wajen, Dan anan compound daga jikin bango akai decorations d'in da balooms da flowers haka aka mam manna awurin, wurin yayi kyau ba kad'an ba . tsakiyar wurin kuma aka shim fid'a Wani k'aton carpet akai sai table a tsakiyar sa Wanda akai masa decorations Shima da Wani farin yadi da kuma flowers sai tun tun sarauta da aka zagaye table d'in dashi inda k'awayen Aziza zasu zauna a gaban kowa kuma and'ora masa plate na snacks wanda k'awayen zasu ci .Wuri dai yayi kyau sosai sai kace wadda zatai parting graduation na university ba SSCE ba .



Aziza ta k'arasa wajen friends d'in ta Wanda suka mik'e sai zuzuta kyan da tai suke Dan yawan cin suma 'ya'yan k'awayen Fulani Salamatu masu kud'i suma sai wasu class mate d'inta su biyu.aziza sai murmushi take ganin yadda ake ta cewa tayi kyau.Adai dai lokacin da Aziza ke tare da k'awayen ta su Huyaam suka shigo gidan bayan sun k'araso Aziza ta juyo tana kallansu take annurin fuskarta ya canza daga fara'a zuwa B'acin Rai ganin yadda HUYAAM tai kyau sai taji gabad'aya kamar Huyaam ta fita kyau duk da kwalliyar da tasha itama.amma saboda Aziza ta riga da sawa kanta cewa duk lokacin da HUYAAM tayi kwalliya to Gani take sai ta fita kyau . wannan abun data sawa kanta yasa ko tayi kyau take ganin kamar batai ba Koda ko Wani ne ya fad'a mata Gani take dole sai su Huyaam sun fita.take kuma ta kauda tunaninta ta k'araso wajensu tana murmushin yak'e tace...

"Sannunku da zuwa ku k'araso mana". Ta fad'a tana murmushin yak'e suka ansa mata suka bi bayanta ta k'arasa inda k'awayenta ke Zaune kan tun tun nan suma duk suka samu waje suka zauna k'awayen Aziza sai kallan Huyaam suke suna Yaba kyau da nutsuwarta. Aziza ko sai cika take tana batsewa kamar Wani ne yasa tai parting.Babu Bat'a lokaci aka fara gabatar da partyn bayan sunci sun sa sai kuma akazo za'ayi pictures Karima ta kawowa Aziza gifts d'in nata Aziza ta karb'a ta nuwa k'awayenta da cewa a school aka Bata suka Karb'a suna tayata murna ko kunya Bata jiba .bayan sun gama Gani akai musu pictures d'in tare da Aziza sai da aka gama mata da friends d'in ta Sannan ta tafi wajensu Huyaam ta nuna musu gifts d'in tace ..


"Kunga d'azu uncle Samuel Jackson ya kawo min wai mantawa akayi shiyasa alokacin da za'a Baku ni ba'a bani ba".ta fad'a ko kunyar k'aryar da tai bataji jiba Mamaki ya kamasu ikleema Amma basuyi magana ba tunda sun San halin Aziza zatai yafi hakama.suka karb'a duk suka Gani Suna tayata murna ta k'ira photographer da suka d'auko na musamman yazo yay musu pictures aka had'u harda k'awayen Wannan Karan ma akai musu su sai Kuma Aziza tace photographer yazo yay musu na iya su 'Yan Cikin palace d'in suka had'u su su biyar suka tsaya safna ta tsaya kusa da Aziza Amma sai Aziza ta tureta ta jawo Huyaam kusa da ita kamar abin arzik'i Hakan sai ya bawa safnah mamaki Amma batai Magana ba ta tsaya akusa da Huyaam ita aka fara d'aukar su pictures Aziza data lura hankalin kowa Baya kanta Yana wajen photographer nan kawai tasa k'afarta wacce ke d'auke da highheel shoe ta take k'afar Huyaam da shi Babu shiri Huyaam tasa Wani ihu tana k'ok'arin janye k'afar ta jin Wani azaba ya ratsa ta har tsakiyar kanta Huyaam zata Fad'i safnah Dake gefenta ta rik'ota cikin tashin hankali.take su Huda ta iyo kan Huyaam tana tambayar ta da lafiya Maiya sameta Amma Ina Huyaam sai kuka take tana rik'e da k'afar ta wacce sai zubar da jini take sosai tana K'iran sunan Ammie k'awayen Aziza duk suma hankalinsu ya tashi Ganin wannan jini safna ta Kalli Aziza Ganin yadda ta saki wani murmushi d'aukarta Babu Wanda ya lura da ita take safnah ta gane me yake faruwa wato Aziza ita ta take k'afar Huyaam kuma tana sane tunda gashi ko ajikinta bare tazo wajen da HUYAAM take tai mata sannu Babu Bat'a lokaci su Huda suka fita da Huyaam daga b'angaren su Aziza gabad'aya sukai b'angaren su da ita tana ta ihun K'iran sunan Ammie.


Ganin amfita da Huyaam ga lokacin sallahn magrib yayi tunda gashi ana k'ok'arin shiga sallahn magrib a masallaci cikin masarauta yasa duk da k'awayen Aziza sukai Mata sallama suka tafi Aziza tai musu godiya nan suka tafi shima photographer da yake dama an sallame shi shima ya tafi itama Aziza ta shige cikin gidan tunda an gama mata pictures d'in tana kuma tsaron kada Mai martaba yazo ya samesu ba'a gama ba yasa a Zane ta gefe D'aya Kuma tana farin cikin abinda taiwa Huyaam......



Alokacin da aka shiga da HUYAAM b'angarensu tana tana ta ihun kuka saukowar ya Zarah kenan downstairs bayan ta idar da sallahn magrib a a d'akinta already Dama muneefa tana zaune itama afalon tai nata sallahn cikin tashin hankali ya Zarah ta k'araso cikin falon Tana kallan Huyaam Dake zunduma ihu tana K'iran sunan Ammie da tashiga uku ga hannun ta rik'e da k'afarta .idan ya Zarah ya sauka a kan k'afar Huyaam Dake zubar da jini har lokacin take hankalinta ya K'ara tashi ta k'arasa ta karb'e Huyaam daga rik'on da su Huda sukai mata ta rungumota zuwa jikinta ta Kalli Huda da damuwa tace.


"Ayina taji wannan raunin". Safna tai saurin cewa.

"Ya zarah Aziza ce ta taka ta kuma tana sane wallahi ". Cikin confused ya zarah tace.


"Garin Yaya?..." nan safnah ta bawa a ya Zarah labarin abinda ta sani .tuni ran ya Zarah ya gama B'aci tace .


"Yanzu Azizan ce taiwa Huyaam haka? Mai tai mata daza tai mata irin wanna zalincin haka ai".ta fad'a ranta a b'ace.jin haka yasa tuni muneefa ta haura Sama da gudu wajen Ammie zata fad'a mata.



Ammie tana zaune kan sallayan idar da sallahn ta kenan taji kamar kukan Huyaam da Kuma K'iran sunanta da taji Huyaam nayi tana k'ok'arin tashi ta fita ta gano meke furuwa kenan Kuma saiga muneefa ta shigo d'akin tana haki tace cikin rawar murya kamar zatai kuka.


"Ammie kizo ya Huyaam ta karye a k'afa k'afar sai zubar da jini take sosai"ta fad'a tana rushewa da gunjin kuka.

Jin haka yasa Take gaban Ammie ya Fad'i Jin abinda muneefa ta fad'a tace .


"Muje" ta fad'a cikin far gaba.muneefa ta juya ta fita daga d'akin Ammie ta biyo bayanta hankali a Tashe. Koda Ammie ta sauka ta tarar Huyaam na Jikin ya Zarah sai kuka take tana rik'e da k'afarta wacce jini ya gama wanke ta tass gashi har lokacin jinin Bai daina zuba ba ga su safnah sun zagaye ta sai sannu suke mata.cikin Tashin hankali Ammie ta k'arasa wurin da suke ta karb'i HUYAAM daga hannun ya zarah ta rik'o ta zuwa jikin kamar zatai kuka tace.


"Meyasa sameta hakane?...".ta fad'a tana duba K'afar HUYAAM .


Kafin kowa yay magana ya Zarah tai saurin fad'awa Ammie kamar yadda safnah ta fad'a mata.Ammie ta Kalli ya Zarah da mamakin abinda ta fad'a.muneeb ne ya shigo falon bakinsa d'auke da sallama dawowar sa Kenan daga masallaci da sauri ya k'araso har cikin falon Dan Ganin abinda ke faruwa Ammie ta kalleshi tace.


" Yauwa muneeb ina haidar?..."muneeb yace. "Yana masallaci".


Ammie tace .


"Yi masa ka k'ira min shi yazo mu kai HUYAAM asibiti yanzu kai sauri".ta fad'a cikin damuwa.babu musu muneeb ya fita daga falon cikin sauri Dan K'iran ya haidar.babu Dad'ewa muneeb ya shigo falon sai Mai martaba Dake biye dashi sai Kuma ya haidar Yana takewa Mai martaba Baya Dan lockan da muneeb yaje zai fad'awa ya haidar alokacin Yana tare da Mai martaba kuma agaban Mai martaba muneeb ya fad'awa ya Haidar sak'on Ammie shine Mai martaba yace suzo su Gani tare.


Gabad'aya su safnah sukai baya Ganin Mai martaba ya shigo falon suna ansa Musu sallamar da Sujay kafin su tsugunna har k'asa suka shiga gaida shi,Mai martaba ya ansa musu da kulawa ya tsaya akusa da Ammie Yana kallan ta yace cikin nutsuwa.


"Meya sameta?... Kafin Ammie ta bashi ansa ya Zarah tai sauri cewa .


"Abba Aziza ce ta takewa Huyaam k'afa da takalminta Kuma da sanin". ta fad'a cikin Jin haushin Abinda Aziza tai.Mai martaba ya juya Yana kallan ya Zarah yace.


"Wani Irin takalmine haka da zai iya Huda mata k'afa"ya Zarah tace.


"highheel ne Abba".Mai martaba yace .


"Garin Yaya? Nan ya Zarah ta bashi labarin kamar yadda safnah ta Bata,ran Mai martaba ya gama B'aci tuni dama su ikleema sun bar falon ganin Mai martaba ya shigo ya kalli HUYAAM yace.


"sannu mamana". sai Kuma ya kalli Ammie yace.

"Kiyi hak'uri fulani zan d'auki mataki in Sha Allah". Ammie dai batai magana gyad'a masa kai kawai tai .Mai martaba ya Kalli ya haidar Wanda shima jikinsa yay sanyi yace.


"Haidar ku kaita asibiti bari na koma masallaci".Yana fad'ar haka ya fita daga falon gabad'aya.yana fita Ammie ta Kalli ya Zarah tace cikin Damuwa.


"Zarah Mai yasa zaki fad'a masa salon ki K'ara jawomin wani bakin Jini a wajen funali".ya Zarah tace.


"Ammie idan ma Ba'a fad'a masa ba dole fa sai ya sani to gani nai gara kawai a fad'a masan shi zaifi sauk'i, Kuma kawai Ammie sai a b'oye masa saboda kar ai mata fad'a ko yaya?kina fa kallo yadda Aziza take cutar Huyaam agidan nan ba Dole Abba ya sani ba danya d'auki mataki".Ammie ta d'auke kanta tace .


"Nidai karki K'ara yimin Irin wannan". Sai Kuma ta Kalli ya haidar tace.


"Kaje ka fito da motar mu tafi".Babu musu ya haidar ya fita daga falon. Ammie ta kalli Huda wacce sai zubar da hawaye take tana mak'ale da Huyaam itama tace. "Huda jeki d'auko mata hijab d'inta a daki yanzu". babu musu Huda ta tafi....har bakin part d'in ya Haidar ya kawo motar ya Zarah da baba magajiya suka kama Huyaam suka shigarta bayan motar inda Ammie ta shiga ya Haidar ya rufe musu murfin motar sannan ya zaga driver seat yaja motar suka tafi asibitin........



Mai martaba Yana dawowa daga masallaci direct b'angaren fulani Salamatu ya nufa.yana Isa b'angaren falon ya shiga bakinsa d'auke da sallama . Ramlat Dake Zaune falon suna kallo suka ansawa Mai martaba sallamar sa sannan kuma suka shiga gaida shi lokaci D'aya.Aziza Dake kusa da fulani Salamatu tana Bata labarin yadda taiwa Huyaam d'azu a wurin parting ta, tai shiru ganin Mai martaba ya shigo Dan basu tab'a tunanin zai shigo a wannan lokacin ba .bakinta na rawa itama ta ansa masa sallamar sa tana gaida shi.


Mai martaba ya k'araso har tsakiyar falon sai a lokacin Fulani Salamatu ta mik'e tana kallan Mai martaba tace cikin girmamawa.


"Barka da shigowa rankai Dad'e"ta fad'a tana sunkuyar da kanta k'asa alamar girmamawa.


Da hannu Mai martaba ya ansa mata fuska d'aure ya kalli Aziza data sunkuyar da kanta gabanta na fad'uwa Dan ta tabba kenan yanzu Mai martaba yasan abinda ta aikata.


Mai martaba ya kalli Aziza yace cikin b'acin Rai.


"Aziza meya had'a ki da HUYAAM da kika Huda mata k'afa da takalminki?.."Mai martaba ya fad'a Yana lura da yanayin Aziza.

Aziza ta k'ara sunkuyar da kanta k'asa batai magana ba.mai martaba yace.


"Badake nake ba?..".

Da k'yar Aziza tace.

"Abba Bada sani na bane bafa".Mai martaba ya mata Wani kallo yace.


"Baki sani ba kamar Yaya? wad'an akai abin a gaban nasu sune zasu miki K'arya ko yaya? Nan ma Aziza shiru tai batai magana ba .Mai martaba yace.


"To Kinga wannan shirun da Kikayi ya tabbatar min da cewa k'arya kike kenan kina sane kika takatan".ya cigaba yace. "Aziza na riga da nasan halin kowa acikinku sau nawa kina yiwa HUYAAM Irin wannan d'in ko kun d'auka ban sani bane ba? To na sani Wani abun kau da kai kawai nake Dalili kuwa shine saboda uwarta Batasan Hayaniya ko kad'an shiyasa ko nace Zanyi magana take hanawa da tunanin zaki gyara watarana. Amma duk na lura keda uwarki duk Baku San haka ba, sannan Baku San kawai cin da take muku ba har yanzu ko? Ko nace Bakwa Gani tunda gashi Baki fasa ba Shine yau ma kika K'ara ji mata Wani ciwon ko?.


Aziza tai shiru tana k'ok'arin fashewa da Kuka Amma ta kasa yin hakan.


Mai ya ya cigaba yace.


"To bari Kiji zan Miki worning na k'arshe Aziza.kinyi na farko kinyi na k'arshe Kuma kinsan halina duk ranar da kika sake jiwa Huyaam Wani ciwo ko kikai mata kallan Banza ma agidan nan ke ba ita ba ko waye kika sake naji labari to aranar sai Kinga true color d'ina kinji ko bakiji ba?..."ya fad'a cikin b'acin Rai.


Aziza na sheshshek'ar kuka da Bata tab'a ganin b'acin Ran Mai martaba ba kamar na yau ba tace.


"Naji Abba".


fulani Salamatu da ranta ya gama B'aci jin abinda Mai martaba ya fad'a Amma sai Bata nuna ba ta Kalli Mai martaba takwantar da murya tace.


"A gafarceni Rankai Dad'e da abinda zan fad'a Allah ya taimakeka. Amma da ba haka ya kamata kace ba, kamata yay ka had'a su duka su biyun kai musu fad'a,idan ma Hakan bazai yuba to gara kawai kace kar Wanda ya K'ara yiwa Wani magana acikinsu nake Ganin Hakan zaifi".ta fad'a tana d'auke kanta daga kallan Mai martaba ganin tunda ta fara magana taga yadda yake mata Wani Irin kallo.


Mai martaba ya Jin Jina kai Kafin yace.


"da dukan alamu dai Fulani bakisan Irin raunin da Aziza taiwa Huyaam ba koh, Shiyasa zaki fad'i haka
?To bari Kiji na fad'a miki idan Baki sani ba Aziza ta kusan nakasta Huyaam tai a k'afarta tunda gashi har suka tafi asibiti jini Bai daina zuba a k'afar taba Allah ne ya tak'aita da ba wannan labarin ake ba yanzu.kuma da ace ta nakasta tatan me zaki cewa uwarta Fulani?". ya fad'a cikin b'acin Rai.fulani salamatu tai shiru kanta a k'asa Mai martaba ya cigaba yace."sannan Abinda na fahimta Dake wato fulani kome Aziza tai na laifi to ke awurinki ba laifi bane ke bama iya Aziza duka yaranki basa laifi idan ma sunyi sai kinyi yadda kikai ba'a ga laifinsu ba.to bari Kiji ni bazan d'auki wannan ba Aziza dai 'ya tace Kuma na Isa da ita bama ita kad'ai ba har ke Saboda haka idan Ina mata fad'a karki K'ara samun Baki kinji na fad'a miki,sannan Abu na gaba shine ni bazan yadda a rabamin kan 'ya'yana ba Kuma duk Wanda ya Sab'a umarnina bazai ji Dad'i ba nasan kema kinsan da wannan sai dai ki bawa Wani labari Ina fatan kinji?". ya fad'a Yana kallan Fulani Salamatu...da k'yar fulani Salamatu ta gyad'a masa kai tana Wani cin magani.mai Martaba ya cigaba Yace .


"Sai Abu na gaba yanzu basa nan sun tafi asibiti Ina umar tarku da idan sun dawo zuwa gobe da safe inaso daga ke har Aziza kuje har b'angarensu ku duba HUYAAM sannan ku bawa uwarta hak'uri kinji na fad'a muku, kuma wallahi idan Baku jeba wallahi sainayi mumman Sab'a muku". Yana fad'ar haka ya nufi kofa ya fita daga falon gabad'aya.


Yana fita Fulani Salamatu tace.


"Tab' d'ijan lallai ma wato an tab'o 'ya'yan mowa ko? To wallahi babu inda zani".kawai Babu tambayar Mai ya had'asu saboda kaje an zugo ka shine zaka zo nan mu ka sauke mana ta wallahi wannan Karan sai dai ayi duk wacce za'ayi Amma babu inda zani".ta fad'a tana huci Ramla ta kalli Fulani Salamatu tace cikin sanyin murya.

"Mummy Abba fa gaskiya ya fad'a Yaya Aziza ce Bata da gaskiya fa". Fulani Salamatu tace cikin b'acin Rai.

"Dalla rufe min Baki marar zuciya kawai,keda bakya k'aunar naki bare kiyi kishinsu sai bare a gaban ki akayi da har zaki Yi Shardai zirr?..."


Ramla tace .


"Wallahi mummy agabana akayi" .


Fulani Salamatu tace.


"Dalla rufe min Baki idan na K'ara jin bakin ki a wurin nan saina fasa wallahi Sha Sha kawai marar hankali wacce Batasan masu k'aunar taba". Ramla taja bakinta tai shiru tana sauraran mummyn nasu. fulani Salamatu taja tsaki ta k'arasa wajen Aziza Dake kuka tace.


"Tashi Muje kibar kukan nan ya isa haka aziza, ni wallahi kin mun dai dai dama kin karya k'afar tata sai muga ya za'ayi" Aziza Bata ce komai ba ta mik'e ta bar falon gabad'aya ta haura sama da sauri tana goge hawayen fuskarta. Fulani Salamatu tabi bayan ta.Ramla da walida suka bisu da kallo ganin yadda momyn nasu take ta fad'a kamar zata Ari Baki.......








07066508376_______
'Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD



*<9HUYAAM <9*




*PAID BOOK =*


*FREE PAGES*



*NA*



*__(MRS SARAKIES =؋)__*



*Bismillahirrahmanirrahim*




PAGE 1 3


____________ &


*Ingiland =*


*5:40 pm*



Alokacin da su Ammie suka tafi asibiti wajen k'arfe 7:40pm na dare anan ingiland Kuma k'arfe biyar da mintuna Arba'in ne . dawowarsa daga wajen aiki kenan Yana tsaye a tsakiyar d'akinsa bayan ya rage kayan jikinsa k'ugunsa d'aure da towel zai shiga wanka.har ya k'araso Bakin toilet d'in zai shiga kawai sai yaji yana son jin muryar Ammie a wannan lokacin Dan rabonsu da waya da ita tun a daren jiya yaso d'azu yana office ya K'irata to sai aiki ya Hanashi Hakan.ya dawo har Inda ya ajiye wayoyinnasa Dake gaban mirror d'akin ya d'auki wacce yake amfani da ita for important person more especially iyayensa sai siblings d'insa iya contact d'insu ne kawai aciki.bayan ya d'auka ya shiga call logs yay darling number Ammie sai da Yay mata 2 Miss call batai picking ba abun sai ya D'an bashi mamaki kad'an, Dan Bai fiye K'iran Ammie Batai picking ba ,Koda yaushe idan ya K'irata miss call D'aya biyu tai picking idan har Bata kusa kenan Hakan yasa ya K'ara dealing number nata a karo na uku.


A wannan lokacin kuwa da Afeef ke K'iran Ammie wayar tana d'aki Dan tashin hankalin ma da take ciki Bai sa Ammie ta tuna da wayar taba bare ta d'auka ta tafi asibitin da ita ba.


Gabad'aya su kuma su Huda suna falon k'asa azaune tun tafiyar su Ammie Babu Wanda ya shiga ko da d'akine dukansu suna zaune a falon sai ya Zarah da tashiga d'aki yanzu bada dad'ewa ba .baba magiya ma tana zaune a falon tare da su, muneefa na kwance ajikinta ta mik'e da sauri daga jikin baba magajiya.

Baba magajiya ta Kalleta tace..

"A'a muneefa Ina saki Kuma?..."muneefa ta ya Mutsa fuska tace.


"Fitsari nake ji".daga haka ta haura sama da sauri zuwa d'akin Ammie ko kula baba magajiya Dake cewa Kizo ki shiga toilet d'in falon batai ba hankalinta yayi d'akin Ammie tana shiga tai cikin toilet d'in da sauri babu dad'ewa ta fito tana fitowa ta Tarar da wayar Ammie na ringing Hakan ta yasa ta k'arasa inda take Jin ringing d'in ta d'auko ta fita daga d'akin wayar na rik'e a hannunta da sauri ta koma falon ta K'arasa wajen Huda tace.


"Ya Huda ga wayar Ammie ana ta k'ira".ta fad'a tana Mik'a mata wayar..Huda ta karb'a tana kallan Mai K'iran ganin yayansu sune yasa tai picking cikin girmamawa tace.


"Assalamualaikum.barka da dare Yaya Ina wuni".ta fad'a cikin sanyin murya.take gaban Afeef ya Fad'i Jin Huda ce ta d'auki wayar Sannan kuma yaji muryarta Wani Iri amma sai Bai nuna Hakan ba yace cikin deep voice d'insa.


"Lafiya Ina Ammie da kika d'aukar mata waya". ya fad'a cikin kamewa


Huda tace cikin sanyin murya.


"Batanan sun tafi asibiti ne shiyasa". ta

Please Login or Register in order to submit comment