Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata kaɗan-kaɗan daga ƙauye mu, sai kuma yazo da buƙatar neman ƙoda. A tsakanin ne babanki yay accident, zan ma iya cewa da ƙodarsa muka fara a wajen treatment. Bayan mutuwarsa dil ɗina da Adams ya ƙare dan haka na buƙaci shere ɗina dan lokacin idanuna sun fara buɗewa da kuɗi. Amma sai ya sake kwaɗaita min batunki da kuma yanda kukayi da shi. Banyi mamaki ba dan ni nasan kina da taurin kai, zama ki iya faɗa masa abinda yafi hakan. Ko musu banyi ba da wannan sabon dil na amsa kuwa, mukai cinikin Shere ɗina akan zamuyi 60-40 muka fara aiki. Sai dai a tsakanin anyi aurena da Sabilu, mukai zaman shekara biyu da shi ya rasu. A randa kikai sumar farko na shock ɗin da kika shiga kan batun Mu'azz da budurwarsa ni na fara miki allura. Shi kuma ya bizne asirin daya amso akan ki tun daga ƙasar Togo. Daga baya kulawar da ɗanki ke baki ya nema wargaza mana aiki, dan duk wanda yasan Awwab tun yana yaro hatsabibin kansa ne. Shi kansa Adams ɗin wlhy yana jin shakkarsa da wasi-wasin karfa wataran ya zame maka ƙayar kifi. Dan akwai lokacin da yay niyyar ya kashesa na dai lallaɓashi akan koba komai zai mana amfani, dan yafi Fahad ƙarfin zuciya. Haka dai ya barshi badan yaso ba. Sai dai mun sake hanyar maidosa tafin hannunmu shima, muka saka ƙiyayya tsakaninku, hakama tsakaninsa da ɗan uwansa. Ni kuma na zama matar Mu'azz saboda aikinmu ya tafi yanda ya kamata, tunda mijina ya mutu na gama takaba. Sannu a hankali abubuwa suka kankama, maganar Adams ta fara tabbata, dan kuwa Awwab ya koma juya dukiyar, duk inda zai shiga ya fita ya sani akan kasuwanci. Har yama fi mahaifinki da ke zafin nama, ga shi da nasibi komai ya taɓa kafin wani lokaci ya zama kuɗaɗe. Tun muna ɗaukar abun ƙarami sai muka fahimci babbane fa, dan dukiya nata hanƙoro da bunƙasa. A tsakanin mukai tunanin warware asirin kanki domin gwadaki ko kin saduda ne, Adamu yazo da malaminsa na Togo, wanda shine yay ainahin asirin dama matsayin mai magani. Ya warware asiri a zuwan magani ya baki, kowa nata farin ciki lafiya ta samu gareki, yayinda mu kuma muke ta shirin kammala dil ɗin mu. Abin mamaki abin tsoro, koda bayan samun lafiyarki Adamu ya tunkareki sai gadararki tafi ta farko, kamar ma an ƙaro miki izza ne. Dan maimakon ki risina ƙaimi aka ƙara kunna miki. Kin saka ɗanki yin katafaren company a garin kano. Kin kuma fara wannan katafaren gidan dake a jerin gidaje na farko da ake alfahari da su a garin Lagos. A babbar anguwa irin wannan. Hakan ya sake haukatamu, dan mun sake tabbatar ba ƙananun kuɗi kika mallaka ba. Hankalinmu ya tashi, mun kuma fahimci idan fa har lafiyarki ta ɗore tofa mu wankin hula ne zai kaimu dare ne. Dan mun gano shirye-shiryen da kike akan Adams saboda shi kaɗai kika sani. Bamuyi ƙasa a gwiwa ba kuwa muka garzaya Togo, muka sake sabunta aiki, muka kuma canama mai maganin wajen zama dan mun san zaku nemeshi. Hakan kuwa akayi, kun nemeshin kamar yanda mukai zairgi, rashin samunsa kuma ya ɗaga muku hankali matuƙa. Ko'a kwalar rigarmu mukam. Bayan kun gama bige-bigen neman maganin asibiti da mutumin, dan babu kalar kai-kawon da baku sha ba daga baya dai kuka haƙora da tunanin mutumin ya mutu ne ma. Bayan shuɗewar watanni Awwab ya ƙarasa gina gidan nan, ɗakkoki ku dawo nan yasa abubuwa suka ɗan fara mana nisa. Dan sai dai kawai nazo sau ɗaya a rana da doctors ɗin ta damu sukema aiki kawai mu dubaki. Dan haka dole muka sake sabon lale musamman daya zama zuwa lokacin shi Awwab ya gama yarda da sakin jiki da ni, ta ɓangaren kakansa ma babu matsala. Shine ya masa magana da nuna masa muhimmancin dawowarmu kusa da su saboda al'amarinki. Da farko yaso ɗan tirjewa, sai daga baya kuma miya gani oho masa ya dai amince. Mun dawo Mansion, Nafisa ta dawo, Mama ma ta dawo, hakama Abdullahi da iyalansa, wannan duk cikin burin kakanku ne daman. Dan haka bai taɓa damuwa ba game da hakan duk da bashine yace duk sauran su dawo ba, saboda ya miki alƙawarin dama sai zuri'arsa sun zama suna kwance ya bautar da ɗanki wajen nemo musu suci su hutama ransu. Shi kansa baida aiki sai yawon bin ƙasashe yana hutawarsa duk da tsufar nan nashi da kike gani matsiyacin. Da kike maganar na auri Mu'azz ban taɓa sonshi ba. Ina zaune da shine kawai dan cika manufa..
Duk da a farko-farkon aure zuciyata ta fara karaya, amma bawai na miƙa wuya bane, soyayya ta gaskiya har yau har gobe mahaifinki kawai nake ma ita Ummu-Hidaya. Tabbas tako ina Mu'azz baida daɗin zama. Dan ko matan da yake bi a waje bawai suna jin daɗin mu'amula da shi bane saboda bai ɗauki mace da wata daraja ba. Kawai dai idan akace kuɗi to ƙarshen zance kenan. Suma kuɗin sukema biyayya. Shiko bin matansa mujarrabu ne a garesa ko nace hakkinki, dan akwai lokutan da sam baya so saboda tsoron Awwab da yake ji. Dan zan iya ce miki wannan ma shine dalilin fara shirina da Awwab, tun da ya gano halayyar sa sai ya fara tausaya min, dan ya fahimci nima bawai zaman daɗi nake da shi ba. Sosai shirinmu na tafiya yanda ya kamata, sai dai maganar buɗe Companyn Kano ne ya fara hargitsa mana lissafi. Dan na kula Adamu sam baya ƙaunar hakan a ransa da gaba ɗayan rayuwarsa. Ga kuma Awwab ɗin ya nuna masa taurin kai a bisa umarninki. Ban fahimci abinda yake jima tsoron ba sai da matashiyar budurwa ƴar jarida mara tsoro ta saka Awwab magana a karo na farko na rayuwarsa.........✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕𝒚-𝒏𝒊𝒏𝒆_


*_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*.

*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._

*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram_*

I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

_Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._


......Koni na tsorita, dan duk wanda yasan Awwab yasan baya yarda yay hira da ƴan jarida. Hakan kuma nada nasaba da al'amarin ki, idan har kikaga yayi magana da yan jarida akan abinda ya shafi Bussines ne a kuma filin bussines ɗin kawai. Amma a wannan gaɓar bayan wani kallo da yama yarinyar irin wanda mu kammu shaida ne bayama mace irinsa koma ace bai yaɓa ba kai tsaye ya amshi gayyatarta. Hankali tashe nai kiran Adamu na tura masa faifan video ɗin dan yanata yawo, shine ma latest topic a wannan satin gaba ɗaya. Shima hankalin nashi tashi yayi, dan a ranar ya baro India zuwa Nigeria. Ko gida bai shigo ba daga airport yay Kano. Ba wannan bane kaɗai ya ɗaga mana hankali, akwai yaron Adamu mai suna Commondo dake masa dukkan ayyuka na sharri, kasancewar a gidan nan munada masu naɗar mana bayanai tako ina hatta Fahad dake ƙasar waje sai muka haɗa Awwab da wani yaron Commondo ɗin mai suna Jaga, Jaga irin mutanen nan ne masu wayo matuƙa. Ta duk yanda zasu shiga jikinka ka amince da su ya sani, dan haka duk rashin yarda irin ta Awwab sai da Jaga ya zama makusancinsa, muna murnar zamu samu nasara akan Awwab ta dalilin Jaga na jikinsa sai wasan ya canja, wasu halaye na Awwab suka rinjayi Jaga ya fara daina kawo mana bayanan komai akan duk motsin Awwab, idan ma muka takura sai ya dage mana akan shi bai samo komai ba. Dan haka muka fara sanya masa alamar tambaya. Commondo ya saka aka masa bincike akan al'amarinsa. Sai ko gashi an gano masa Jaga ya koma tsagin Awwab ne. Ya saka ko aka sato masa shi, dan kawai mun yanke shawarar a kashesa. Haka ɗin kuwa akayi, Ni da Commondo mukaje da Jaga har Kano a halin suma cikin companyn da Awwab zai buɗe a ranar buɗe Companyn, zan iya cewa ma har aka fara taron muna a cikin companyn a gabana da kansa ya caka ma Jaga wuƙa. Motsi da mukaji yasa muka shiga maɓoyarmu cikin ɗakin tarkacen machines da suka ajiye. Tacan muka fice dama mun tanadama kammu hanya ta dalilin sabon informer ɗin mu. Muka bar Jaga na shire-shiren mutuwa, mun kuma tabbatar kafin asan da shi ya mutu, idan aka ga gawar kuma a cikin companyn aiki ya tashi, dan dole ne Awwab ya shiga bala'i maganar fara aikin company ya tsaya, a shiga kai-kawon bincike mukuma muyi amfani da wannan damar mu cika burinmu dan mun fahimci abinda muke bibiyarfa sun nuna saura tsinka. Sai dai kuma me, har dare babu wani labari akan al'amarin, har jami'an tsaro mukai ma shune sukazo mana da batun babu wani abu daya faru makamancin wanda muke zargi, sai ma neman ɗora mana wani abu suke daban muka dai sha da ƙyar, ga kuma batun yarinyar nan dole Adamu ya shigo Nigeria. Koda ya isa Kano a can ya samemu, sai dai iya bincike bamu gane komai ba akan al'amarin yarinyar, hakama Jaga bincikenmu ya tabbatar mana ya mutu, Awwab ya saka an fidda gawa ta yanda babu wanda zai iya samun kafar zarginsa. Bamu so haka ba, amma ba komai ai akwai wata damar, koba komai kuma mun kawar da Jaga ɗin dake neman tona mana asiri. Mun cigaba da harkar gabanmu hankali kwance. Sai kuma shigowar yarinyar nan matsayin ƴar aiki ya sake wargaje lissafinmu. Kada kuyi mamakin da ban gane ta ba, saboda a wancan karon bawani kallo na mata sosai ba, akwai kuma facemask a fuskarta eyeglasses, hakama lokacin da tayi hira da Adamu da shi kansa Awwab ɗin ni ban wani maida hankali a kammaninta ba saboda zuciyata ba'anan take ba kuma lokacin ma dai da gilashi. Tabbas Samraah ta wargaza mana komai. Dan yarinyar nan kamar an karanta mata daki-daki ta dinga tafiyar da al'amuran har zuwa wannan gaɓar. Tabbas you are smart, I love you”. Taƙare maganar tana wani kashewa Samraah ido cike da salo...
Harara na watsa mata cikin takaici na ce, “Ni kuma Kinga na tsaneki. Tsana mafi munin tsana da nake jin zan iya ɗaukar makami akanki wlhy. Jaka jahila butulu kawai. In sha ALLAHU ƙarshenku bazaiyi ƙyau ba. Ummie kuma ta muku nisa mai tazarar zango da har gaban abada bazaku taɓa iya kamota ba. Jinin iyayenmu kuwa daya rataya a kanku in sha ALLAHU bazai barku sake zaman lafiya ba a rayuwarku daga nan har ranar mutuwarku. Dan yana da nasaba da rashin nasarar ku kuketa wahala na shekara da shekaru har zuwa yanzu kun gagara cimma abu guda. Ciwon da Ummie tayi kuwa ƙaddararta ce wawaye, hakama rabata da ƴaƴanta ƙaddararsu ce. Yanzu da UBANGIJI yaso yaye musu ba gasu ba kukuma har yanzu kuna a ƙasan ƙafafunsu. Kai a tunaninka ka bautar da Ya Awwab yana nema muku duniya kuci kai da zuri'arka ko. Hhhhh baka fahimci ƙarshen labarin naka ba yanzu? Shi da kake tunanin ka bautar, da ku ƴan kwanciya a kawo muku kuci matsayin iyayen gida waye ta ƙaremawa? Waye ya faɗi ƙasa wanwar? Dawa ta ɓare? Da ku, ku ɗin nan marasa tawakkali ga UBANGIJI, marasa tauhidi da yarda da ALLAH ba abin wasan wani banza bane. Idan dai har ƙyautatawa zata iya zama wa irinku mutum bazai taɓa fatan ƙyautatama kowa ba. Dan kune kesa bayin ALLAH tsoron ƙyautata ma mutane a wannan ƙarni, kuke saka a gagara banbance na ƙwarai da butulallu irinku. Kaicon bawan da za'a ƙyautatama da tarin alkairi ya maida da sharri. Kaicon bawan da zai dinga kallon hidimarsa ga wani kamar ta fi ƙarfin ƙyautatawar da yake masa koda ya fitar da hakkinsa. Kai kana ganin kun tallafa ma Abie ya tashi saboda ya shigo ƙasarku matsayin baƙo. Ka hidimta masa, ka masa miye, ka masa miye, miye, ko. To amma malam mai hidima idan har da kunya a tare da kai kuwa ya dace ka zauna bamu wannan labarin ma?. A wannan hidimar da kai masa fa, shima shine ya ɗauki nauyin karatunka har zuwa wata ƙasa. Ya baro iyalanka daga ƙauye suma ya ƙyautata rayuwarsu, ya ɗauke su ya kai su ƙasar da kake ya inganta musu rayuwa da ilimi....”
“Ilimi kodai ya lalata musu rayuwa, ta sanadin hakan ɗana ya lalace da neman mata....”
A fusace na ce, “Ban gama magabata ba kada ka sake katseni!!!!”. Babu wanda bai kallan ba a falon, dan nayi magana ne fa like wata boss lady, ni kaina naga ƙarfin hali na. Fahad ya kwashe da dariya tare da faɗin, “Duk wanda ya ƙara katseki Aunty Sam ALLAH sai na kwashe miki ƙafafunsa. Cigaba da basu bayani.”
Jinjina nai masa da satar kallon Maash, zaune kawai yake kansa a ƙasa ya dafe shi da duka hannayensa. Ummie kam kallona take tana murmushi. Murmushin na mata nima da cigaba da faɗin, “Abie bai lalata maka ɗa ko ɗaya ba. Baƙin halayyarka ce ta lalata su. Ko baka san masu iya magana kance TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE ba. To ka binciki kanka da kanka kaine amsar tambayar abinda ke zagaye da zuri'arka. Abie ya baka gida bayan dawowarka, ya baka motar hawa. Ya ɗauki company guda sukutum ya baka tare da kuɗaɗen da zaka kafa Bussines. Ya ɗauki ƴarsa ɗaya tilo ya bama ɗanka aurenta. Duk da wahalar da take sha bata taɓa iya gaya masa ba ta shanye tai haƙuri, har ma tana tattali da fatan haihuwa da shi, a hakan da yake sonshi take. Duk da halin daka nunama mahaifinta na banza, ka kuma fiddo masa da ainahinka a sanda yake gadon asibiti bai gaya mata wanene kai ba saboda halin dattako. Bai ce ta rabu da ɗan ka ba. Bai ce ta tuhumeka da abinda ka aikata masa ba, sai ma cewa yay duk rintsi ta kasance da shi, duk rintsi ta maka biyayya a matsayin ƙaninsa na jini. Kaji halin manyan ƙwarai masu tauhidi. Dan ALLAH abin bai birgeka ba?. A lokacin da kazoma da Ummie baƙin halinka ɗanta nada wayon da zata sanar masa. Ya ƙullaceka a zuciya har kawo yau. Amma ka duba batace ma kowa komai ba har ka aikata abinda kake ganin damace ta baka ka aikata. Har warkewa tai a lokacin da shekarunsa suka kai yasan komai amma ta shanye bata faɗa masa ba. A hakan bata faɗa masa ba da ilimin da UBANGIJI ya bashi ya gano kai ɗin wanene? Amma duk da haka bai tunkareka ba ya barka da halinka shima. Baka tunanin talala suka maka na barinka da ƙarfin ikon ALLAH har azo irin wannan gaɓar da zaka fallasa kanka da kanka?. Ke ko baƙar tsinanna ai bani ma da abin faɗa a kanki. Dan ke baki da banbanci da dabbobin aladu masu cin kashi matsayin abincinsu. Kuma a cikinku duk ma wanda ya ɗauka min ƴan uwa ya dawo min da su. Idan ba haka ba ni ba Ummie bace da zata iya barinku da halinku, take a yanzu zan sakaku kuyi nadama wlhy, dan kunga wayar nan, komai da kuka faɗa ta kwashe a ciki, yanzu kuma zan tabbatar muku da sunana ƴar jarida ne. Bara kuma ku gani”.
Kaf falon babu wanda bai waro idanu a kallona ba. Yayinda prof ya zaburo kaina jikinsa na rawa. Babu zato kawai mukaga Maash a tsakkiyar mu. Kallonsa yake kamar zai cinyesa da idanu. Cikin matuƙar fusata ya ce, “Mi zakayi”.
A fusace shima prof ɗin ya furta, “Duk abinda zuciyarka take tunanin zan iya. Har yaushe aka haifi ubanta ma balle ita da take tunanin wani abu”.........✍️




_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑵𝒊𝒏𝒆𝒕𝒚_


.......“Ai ko da kayi mafi girman kuskuren data faɗa zakayi, dan daka taɓa koda kayan jikin wannan wlhy Gara kaje ka ringume transformer kasan dama tsautsayi ya kaika. Oh kai da tunaninka zakayi duk wannan surutun naka ya tafi a banza yaranka su kashe mu ka fice salin alin zuwa airport ka hau jirgin zuwa Saudia daka gama shiri ko, daga can ka wuce ƙasar da kake so. To ai ka makaro. Dan wannan TSUTSAR NAMAN ITAMA NAMA CE. Idan taƙadaranci kakeji ka iya kada ka manta jininka ne ni, na ɗebo daga wasu ɗabi'unka, sai dai ina bi dasu ta hanya mai ƙyau domin maganin irinka. Idan kuma dattako ne, jinin Ibrahim nake, kaga ko gidan ka taras. Bari na faɗa maka abinda baka sani ba. Tun daga randa na gane kai wanene duk wani motsinka a tafin hannuna kake yinsa. Kaf ma'aikatan gidanka da kake gani aikina suke yi.” ya ƙare maganar da kallon ƙofa ya ce, “Bismillah”.
Ba prof ba mu kammu sai da zukatanmu suka girgiza. Duk da ni Bama sanin ma'aikatan nai ba tunda ba taɓa zuwa gidansa nayi ba. Isma'il Kuku ne farkon shigowa. Sai maigadi, amintaccensa, drivernsa daya taɓa karyawa, bai san sanda ya bar hannun Commondo ba sai dai har yanzu akwai ɗaurin karaya a hannunsa. Amintaccensa, mai bayin filawa, masu share-share da goge etc. Taga-taga prof yay zai zube ƙasa sai da Hayatu ya taresa yana faɗin, “Hankali dai Baba hankali”. A yanda yay maganar kowa yasan akwai shaƙiyanci a ciki. Aiko Fahad ta bushe da dariya da faɗin, “ALLAH Yaya Hayat dama ka barsa ya ɗan sha ƙasa”. Mangare kan Fahad Ummie tayi kaɗan.
Dafe ƙirji Baba prof ɗin yayi. Abin mamaki fuskar Maash da murmushi ya ce, “No no ai lokacin bugawar zuciyar baiyi ba da saura ɗan dakata min.” juyawa yay ya kalla masu bindugun dake zagaye da mu. A take suka sauke bindugun suna murmushi. Sai kuma suka haɗe hanayensu waje guda suka ɗan risina wa Ummie alamar ban haƙuri, nima suka juyo suka rissina min, sukaima Fahad da Hayatu ma haka... A razane Baba prof ya ce, “What?! Ozee. Ni zaku cima amana? Na ɗauki nauyin zuwanku tun daga ƙasarku kuce wani kuke ma aiki ba ni ba?.”
“Dama can bakai mukazo yima aikin ba old man. Dan tun kafin kazo garemu shine ya fara zuwa”. Ozee yay maganar cikin nuna girmamawa ga Maash da harshen turanci. Idanu kawai ya lumshe musu ya buɗe su akan Prof da ya gama diriricewa yana kalle-kalle. Murmushi Maash yay da faɗin, “Oh Mr Paul daya ɗakko maka hayarsu kake nema. Hayat!”. Da sauri Hayatu yay salute ɗin Maash ɗin cike da girmamawa yana fita, sai ko ga Mr Paul bayansa da police biyu ya shigo. Maimakon ya kalla Prof sai ya rissina ya gaishe da Maash.
“Kuturun bala'i, Yaya kana aljanna ina binka da addu'a wlhy, harma Ministar guda a ƙarƙashin komarka yake. Shegiya nera duniya ce”. Fahad ne da wannan maganar yana miƙewa zaram. Ba shi ba mu kammu abin ya matuƙar razana mu. Mr Paul fa da kowa ya sani Minister mai faɗa aji a ƙasar. Eh kam gaskiyar Fahad Naira maganin wata magana. Yanzu kam Baba prof sai da ya kai ƙasa yana nuna Mr Paul da hannu, murya da bakinsa na rawa ya ce, “Kaima munafukina ne dama Mr Paul?”.
Cikin halin ko'in kula Mr Paul ya ce, “Professor magana ce ta kuɗi fa. Sannan magana ta gaskiya Maash yafi ƙarfina, ya wuce da sani na. Bani da zaɓin da ya wuce goya masa baya. Kadai san ni akan kuɗi Mamana ma zan iya badawa”.
“Kutumelacy babarka fa? Shege Ministar yasan takarda hhhhhh!!”. Fahad ne da iskancin nan yanzu ma. Yanzu kam kasa daurewa nayi sai da na murmusa ina mai girgiza kaina. Yayinda Hawaye suka ɓallema Prof a bazata. Nan ma murmushin Maash ya sake saki da faɗin, “Inaa ai lokacin kuka ma baiyi ba. Hayat next level.”
Sake fita Hayatu yayi sai gashi ya shigo da Jaga. Sai wani takun ƙasaita yake ana bubbuɗewa cikin tsadaddun suit Dan yanzu kam Maash ya ɗaure masa ƙugu. Baba prof zai zabura Jaga ya dafesa yana dariya da faɗin, “No tsoho kwantar da hankalinka ba Fatalwa bane JAGUS ne”.
Kalmar JAGUS ɗin nan daya faɗa ita ta sakamu dariya. Dan hatta Maash ɗin sai da yay ɗan girgiza kansa. Cike da izza Jaga ya cigaba da faɗin, “Kun zata na mutu ko? To kwana basu ƙare ba old man. Kasan mu ƴan gidanmu ALLAH ya bamu tsahon rai. Kakana na goma ance shekara ɗari huɗu yayi a duniya, hakama na tara dana takwas dana bakai. Na shidda ne yay ɗari uku da uku, na biyar kuwa ɗari uku da arba'in. Na hudu yay ɗari biyu, na uku kuwa ɗari da hamsin, shine ya fara rage mana mudu. Wanda ya haifi ubanta ɗari da arba'in yayi, babana kuwa har yanzu yana raye ya kusan cika ɗari da hamsin shima. Ya kake tunani akan ni JAGA, ai maybe ma kakana na goma zan gado nayi four hundred inji turawa, larabawa kuma sukace أربعة مئة.
Wani tsugunne gayu yay

Please Login or Register in order to submit comment