Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tashi ina kallon Mama Balki da barci ya ɗan fara figa. Sai kuma na miƙe cikin sanɗa na nufi ƙofar fita.
“Samraah ina zaki je?”.
Muryar Mama Balki a bazata ta daki cikin kunnena. Cak na tsaya tare da runtse idanuna. Sai kuma na juyo a hankali cikin son wayancewa zanyi magana ta dakatar da ni.
“Baki iya ƙarya ba Samraah, kada ki farata yanzu”.
Sosai furucin nata ya dakeni, dan haka na sauke ajiyar zuciya tare da dawowa a hankali na koma saman gadon na zauna. Kaina a ƙasa ina wasa da yatsun hanuna nace, “Kiyi haƙuri Mama. Ba wani abu zanyi ba. Reception zanje na samo pen da takarda zanyi amfani da su”.
“Amma a daren nan Samraah. Na kula tunda Alhaji ƙarami ya tafi baki da nutsuwa. Bana fatan ace kina son samo takarda da biron ne dan kiyi rubutun da zaki bar masa ki gudu”.
A karo na farko nayi murmushi tare da girgiza mata kaina. “Haba Mama, ai a yanzu wlhy koda shine da kansa yace na tafi gidanmu bazan je ba. Dan insha ALLAHU sai na sauke alkawarin dana ɗauka akan Ummie. Kawai zanyi amfani da sune dan ina son yin lissafi dalla-dalla. Ba kuma zai yiwu a cikin ƙwaƙwalwa ba dole sai da taswira a rubuce”.
Ajiyar zuciya Mama ta sauke. Batare da tambayata abinda zanyin ba ta miƙe. “Shike nan ki zauna ni bari na fita na samo miki. Kin san dai ba'a son ki yawaita motse-motse mai ƙarfi saboda ɗinkin jikinki”.
Bance mata komai ba sai duƙar da kaina dana sake yi. Itama sai ta fice abinta bayan ta zumbula Hijjab ɗin ta..........✍️


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒆𝒆𝒏_


......Mintuna basu fi biyar ba kuwa sai gata ta dawo. Cike da farin ciki ta miƙa min takarda da biron tana faɗin “Kinga Alhamdullah na samu ƴar arziƙi a reception ɗin ma. Ina tambaya babu musu ta ciro ta bani har shida, gasu kuma manya nasan dai zasu isheki ai ko?”.
Nima fuskata a washe da murmushi na amsa ina faɗin, “Yauma Mama Nagode sosai. In sha ALLAHU zasuyi harma ƙila suyi yawa.”
File ɗina na ɗauka na ɗaura a samansu tare da gyara pen ɗin. Gaba ɗaya ahalin Maash Mansion na shiga lissafowa a jere. Wanda na manta ina tambayarta. Hatta da adadin masu aiki maza da mata da aikin kowa sai da na rubuta su. Kafin nabi duk manyan gidan na zana halin kowa dana fahimta agaban sunansa. Hatta shi kansa Maash ɗin harda shi. Daga haka nai shiru ina nazari tsahon lokaci, kafin na ɗaga katifar na saka takardar. Toilet na nufa na ɗauro alwala. Duk da yanda nake jin jikina haka na nutsu na kabbara salla domin miƙama UBANGIJINA kukana tare da kai ƙarar wasu mutane garesa dan ya shigemin gaba wajen gano ainahinsu kozan san inda zan kama a wannan tafiyar dana shirya yi....

🌿💞🌿💞🌿

Sosai biki ya kankama a gidan Abba Imamu. Sai dai gaba ɗaya bai zoma Mom a yanda ta shirya shi ba. Dan har yanzu Abba yaƙi maidata ɗakinta. Babu irin haƙurin da bata bashi ba, hakama Ummanta tazo ta saka wanda yake jin kunya amma yaƙi sauraren kowa. Kasancewar tana a cikin gidan har yanzu yasa mutane da yawa basu san abinda ke faruwa ba. Abun zai baku mamaki idan nace muku tunda Halime ta fuskanci abinda ya faru tsakanin Mom da Abban itama ya kasa gane kanta. Kuka ta dinga masa da magiya da roƙon ya maida matarsa, idan ba hakaba itama gaskiya sai dai ya saketa. Ita haka kawai yaja mutane su tsaneta a dinga cewa dan ya aurota ne ya saki uwar ƴaƴansa. Duk yanda ya nuna mata babu ruwanta a ciki taƙi haƙura ta barsa. Kullum cikin masa nagiya take da kuka gashi bata da lafiya sosai. Dan ta kai ma a yau sai da suka je asibiti saboda yanda take amai gaba ɗaya ta galabaita. An tabbatar musu tana da shigar ciki. Zo kuga murna wajen Abba. Yayinda Halime ido yay gwalo-gwalo. Tabbas tana son yara sosai, kodan yanayin rayuwar data gashi ta tsangwama da rashin sakewa. Bata da wani wanda zatace yau ya zame mata amini tunda ƙaninta ya rasu. Ba kunya Abba na dawowa gida ya barbaɗama Auta. Murna da tsalle Auta ya dinga yi da ga ƙarshe ya kwasa da gudu yaje ya barbaɗama Mom dake tare da ƙanwarta da Ummanta da suketa tsare-tsaren biki da za'a fara nan da kwanaki biyu. Neman ɗaukewa numfashin Mom ya yi, har sai da takai hannu ta dafe goshinta dan wani irin sara mata kanta yayi na masifa. Ganin tana neman ɗagama kanta hankali Ummanta da ƙanwarta suka shiga lallashinta da mata nasiha akan tafa kwantar da hankalinta. Wata fitina ko nuna wani abu a yanzu ba nata bane. Ita da ake lallaɓawa ya maidata ɗakinta ya kamata ace ta nutsu, kai kodan bikin nan da za'a tara mutane ta rufama kanta asiri karta bari ƴan uwansa su samu lagonta. Dan yanda bata riƙesu hannu biyu ba sumafa a yanzu dole su ringa nuna mata cewar amarya ta fita a wajensu. Sannan duk hanyar da zasu ƙuntata mata a shirye suke da nemota komai ƙanƙantarta. Shi kansa Abban yanda yake jin kansa on top akan yarinyar nan yanzu idan fa ta cigaba da matsawa sauran igiya biyun ya tsinketa ba abinda zai damesa bane.
Wannan nasiha da ƙanwarta ta mata ne ya sakata kama kanta badan taso ba. A haka aka shiga shagalin bikin Baby. Danginta da ƴan gwarzo sun cika gida tako ina. Tun ranar alhamis aka fara event, dan wasu irin mahaukatan kuɗaɗe mijin Babyn ke kashewa tamkar baisan ciwonsu ba. Duk da kuwa bikin Abba ya dawo dashi baya ne akan yanda aka sanyashi an zaftare har sati biyu a ciki. Ranar juma'a aka kawo lefe na nunama tsara harda key ɗin motar da aka zubo kayan. Wannan bajinta ta ragema Mom raɗaɗin dake damunta a cikin zuciya game da cikin Halime. Ta dinga yanka ƙananun habaici da ɗagawa ma mutanen Gwarzo. Faɗa take yanzu ne akai biki na ƴar gata ba irin na Samraah da har yanzu basu san ina ya dosa ba. Maybe ma Abba da Musaddiq sun saidata ne ko turata karuwanci. Yo inba haka ba wane irin aurene wata kusan takwas basu taɓa sanin miji ba itama bata taɓa zuwa gida ba. Ai dole ne akwai abin ashshar da ake ɓoye wa. Duk da kalamanta sun tada hankulan su Gwaggo Gudidi duk da zuwa yanzu suna waya da Samraah dan hatta su Kawu Musa tana ɗan kira sai suma suka ji kamar basu ƙyautama Samraah ɗin ba. Amma dai sun shanye a fuskokinsu babu wanda ya tanka Mom da haukarta. Washe gari asabar aka ɗaura aure. Abu na farko daya fara bama mutane mamaki shine ango daga shi sai abokansa guda uku yazo wajen ɗaurin auren. Sune suka amsa masa auren a matsayin waliyyay. Kowa yayi zato da tsammanin yanda yake faman ɓarin kuɗi kamar babu gobe sai ƙofar gidan Abba an rasa wajen faka motocin gayyarsa data ango. Amma sai gasu su huɗu a mota ɗaya rak kamar dangin mayu. Jikin Abba shi kansa ya fara sanyi, sai dai bai iya yace komai ba har aka kammala. Zuwa dare maimakon an shirya amarya a miƙata ɗakinta sai akacema Abba wai ai wajen dinner za'aje sai zuwa gobe ango zai ɗauki amaryarsa daga gidansu sai airport zasuje honeymoon ne. Sai bayan sun dawo zai wuce da ita gidanta. Tofa anan ne fa ƙananun magana suka ɗan fara tashi, haka aka shirya tafiya dinner kowa bakinsa da abin faɗa. A wajen dinner an ɗan ga wasu mata a matsayin danginsa. Sai abokansa da suka ɗan zazzo da matansu. Dan ko wajen bada tarihinsa ƙanwarsa ce ta bada. Dinner kam tayi dinner, dan anci kaji ansha lemon roba gwargwadon iko. Ga bag da aka raba cike da kayan rabo a ciki. Amarya baby da ƙawayenta sai feleƙe ake abin nema ya samu. Haka Mom dan tare da ita akaje dinner sai nuna isa ake. Hatta da Umma sai da taje abinta ko kunya. Ƙarfe ɗaya da wani abu na dare aka tashi, su dai ƴan Gwarzo ma tun kusan goma da wani abu suka saka Musaddiq ya dinga fito da su yana sakawa a napep ana maidosu gida dan sun gaji. Lokacin da su Mom suka dawo su tuni sunyi nisa a barci. Ita kam Halime dama bata da wani sakewa a bikin saboda laulayinta mai addaba ne. Koda yaushe tana ɗaki kwance. Da ƙyar take ɗan yin dauriyar fitowa ta gaida ƴan gwarzo. Dan hakama dinner ɗin bataje ba sukai zamansu ita da Abba a gida yana tattalin kayarsa da lallashi itako tana zuba masa taɓara..
Washe gari lahadi da aka tashi da shirin wucewar baby da mijinta shi kuma Musaddiq ya shirya wutowa Lagos. Sunyi waya da mijin Samraah zai je wajenta ya kwana washe gari litinin zai haɗu da wanda zai masa jagorar wucewa ƙasar Chaina kamar yanda MD ɗin sa ya bashi a rubuce. Dan haka ya shiga sallama da ƴan uwa anata koke-koke. Abinka da tsoffi gani suke tafiya Chaina ɗin nan kamar tafiya lahira ne. Dan wasu ma da farko da ca sukai basu yarda Musaddiq ɗin yaje ba. Sai da Abba ya dinga basu haƙuri da nuna musu muhimmanci da cigaban da Musaddiq ɗin ya samu har suna wataran zai shafesu sannan suka haƙura badan sun so ba. Sai dai sunyi farin ciki da jin shi da Hafizzullah zasu je wajen Samraah ne a yau kafin shi ya wuce gobe. Dan rigima da Hafizzullah ya saka masa akan son zuwa shima yaga Samraah ɗin ne yasa shi fidda yan kudaɗensa ya saya masa ticket ɗin jirgi saboda shi ta sama zaibi zuwa Lagos ɗin sai ya saima Hafizzullah ɗin shima zasu wuce tare. Kafin ma mijin Baby ya iso su sun fito, dan motar company ce zata kai Musaddiq ɗin airport. Haka suka wuce ƴan uwa da abokan arziƙi na musu fatan alheri. Tare da saƙon gaisuwa ga Samraah buhu-buhu aunty Zakiyya harda saƙo a cikin kwali datai nannaɗe da su Musaddiq basu sani ba. Hakama Gwaggo Gudidi ta haɗa kayan maƙulashe irinsu tuwon madara, carbin malam, gullisuwa, aya, gyaɗa, riɗi, cike da leda viva tace a kaima ɗiyarta. Wai maybe tanada ciki kunya ta hanata faɗa, ba kuma a raba masu ciki da son kaya kwaɗayi irin waɗan nan. ALLAH sarki Halime itama sai da ta bada zuma mai yawa a gora da uban aya da take saidawa a kaima Samraahn duk da a hoto kawai ta santa. Ta kuma saka Abba dole ya bada naira dubu hamsin a kaima Samraah ɗin. Sosai Musaddiq yayi mamaki bada waɗan nan kuɗi, amma haka kawai sai yaji a ransa aikin aunty amarya ne. Sosai yaji kima da darajar yarinyar na ƙaruwar masa a rai, har sai da ya share ƙwalla. Dan tunda tazo gidan nan abubuwa da yawa suka sauya. Abincinsa, tsaftar ɗakinsa bata ƙyashin shiga ta gyara, komai kuma tana yimasa a mutunce da girmamawa. Yana kiranta aunty tana kiransa Yaya. Da yay magana sai tace ai ita ɗan uwa take kallonsa kuma babban yaya bawai ɗan mijinta ba. A bata da lafiyar nan duk rintsi bata bari ya fita da safe bai karya ba koda ba ranar girkinta bane. Haka tunda Hafizzullah yazo take hidima da shi da jansa a jiki shima kai kace ƙaninta ne uwa ɗaya uba ɗaya. Duk yanda Hafizzullah keda ƙin sakin jiki da mutane sai gashi dandanan ya saki jiki da ita. Hatta da jakar kayansa yanzu haka a ɗakinta ya bari dan ɗakin Musaddiq ɗin akwai baƙi maza yan gwarzo da basu kai ga wucewa ba.........✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒆𝒆𝒏_


*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._

*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram_*

I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_WhatsApp_*
https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG


https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5

____________

......Lokacin da suka iso airport ɗin su duka sai da ƙwalla ya cika musu idanu. Dan abune da basu taɓa zato ko tsammani ba a rayuwarsu. Sune yau da hawa jirgi daga Kano zuwa Lagos. UBANGIJI al-musawirru mai sassauya al'amura a sanda yaso ga kuma wanda yaso. Da suka shiga jirgin sai Hafizzullah ya rungume yayan nasa yana hawaye. Dole shi ya haɗiye nasa ya dinga lallashinsa. Bayan yayi shiru kuma ya dinga musu video wai dolene ya nunama Aunty Samraah yau sun hau jirgi. Dariya Musaddiq ya dinga masa har ALLAH ya saukesu lafiya garin Lagos. Sunyi mamakin ganin zuƙeƙiyar motar da tazo ɗaukarsu. Amma sai Musaddiq bai kawo komai a ransa ba tuna cewa dafa companyn Maash yake aiki, mai lamba ta ɗaya a Africa, na uku a duniya a matasa. Ai hakan ba komai bane ba. Sunyi da MD dama motar company zata daukesu daga airport ta kaisu duk inda zai je, sannan idan ya kammala gobe idan ALLAH ya kaimu zai kira aje can gidan ƴar uwar tasa a ɗaukesa zuwa wajen GM, daga nan zai wuce kuma....

🩸🩸🩸🩸🩸

Kamar kullum alarm ɗinsa ne ya tashesa. Hannu ya kai idanunsa a rufe ya lalubosa a saman side drawer ya danne wajen kashewar dan shifa ko yaya ƙara take damun rayuwarsa take. Shiyyasa bazaka taɓa ganin wayarsa da ringing ton ba. Kullum cikin vibration phones ɗinsa suke. Hakama television da wahala kiji ya buɗeta caaa tana surutu. Cikin mayen barcin da bai gama isarsa ba ya nufi toilet. Sai da yay wanka kamar yanda abun ke neman zame masa sabo saboda mafarki duk da ba kullum yake tashi a irin yanayin ba sannan ya ɗauro alwala ya fito. A ɗan gurguje ya busar da kansa ya shimfida sallaya yay raka'atainul fijir sannan ya fice masallaci. Ana idar da salla bai yarda sun haɗu da Paah ko Uncle Abdullahi ba ya dawo gidan. Jallabiyarsa ya zare ya ɗauka sports wear ya saka masu kalar blue da rashin white. Sosai kayan sukai masa ƙyau duk da baya sakasu ne domin kwalliya ba. Ya kama gashinsa ya haɗe a tsakkiya tare da ɗauresa da siririn baƙin band. Duk da gudu zai fita sai da ya sakama jikinsa turare ya maƙala bluetooth a kunensa sannan yay zaman saka takalma spots na companyn nike. Yana fitowa falo Laalah dake kwance ya miƙe ya nufosa. Kansa ya shafa cikin lumshe idanu da silent voice ɗin nan tasa ya furta, “Let's go my friend”. Cikin kaɗa bindi kuwa ya bisa abin cike da mamaki. Daka gansu kasan karen ya gama samun training na musamman a hannun uban gidan nashi. Gashi fari tass babu alamar wani dattin ƙazanta a tare da shi. Wanda ma bai sani ba sai ya ɗauka ba kare bane saboda yanda jikinsa ke duguzum da gashi. Yana nufar gate da ɗan gudu Laalah biye da shi ƙafa da ƙafa dan a jere suke tafiya su Sha'aibu dake zaman jiran fitowarsa na take musu baya suka fice yana ɗagama ma'aikatan daketa faman gaishesa hannu. Gudun ya fara tun daga wajen gate ɗin a hankali Laalah a gefensa guards ɗinsa biye da su. Haka suka miƙe street ɗin nan. Sosai sukayi nisa bana wasa ba. Jefi-jefi suna gamuwa da mutane da suma suka fito jogging ɗin. Hannu kawai suke ɗagama juna kowa ya wuce. Sai wasu ƴammata ne da suka dai-daita gudun kusan da shi dan suna a ɗan gabansa kaɗan amma ko kallo basu ishesa ba. Sunyi nisa sosai ya jiƙe sharkaf da zufa har yana ɗiga sannan suka sake juyowa bayan ya kalla agogon dake a tsintsiyar hannunsa. Suna isowa kwanar da zata sadasu da gida ya tsaya cak. Nuni yayima Shu'aibu daya bashi ruwa cikin sauke numfashi da sauri-sauri. Da sauri ya nufesa tare da ajiye ƴar jakar da abubuwan da zai buƙata ke'a ciki. Kamar su bottle water, towel da abinda ba'a rasa ba. Ruwan ya amsa ya buɗe murfin haɗaɗɗiyar bottle water ɗin ya kai bakinsa. Kansa ya ɗaga sama ya shiga kwararawa. Wani irin kaiwa da komawa maƙoshinsa ya shiga yi, illahirin ƙofifin gashin jikinsa na buɗewa zufa na fitowa da gudu. Sai da ya sha fin rabi sannan ya sauke gorar yana sauke numfarfashi. Laalah ya zubama kaɗan a jiki, shiko yay wani irin matsawa yana girgiza jiki. Yanda yay ɗin ne ya saka Maash ɗin sakin wani ɗan guntun murmushi yana sake kai goran bakinsa ya ɗan kurɓa sannan ya rufe ta ya miƙama Shu'aibu da suma duk suke shan nasu ruwan tare da masa alamar ya bashi towel. Da sauri ya miƙa masa fari tass ɗin towel ɗin hannunsa dake a linke. Sai da ya fara gogo wuyarsa zuwa gashi dake kwance a kumatunsa sannan yay magana batare da ya kalli su Shu'aibu ba.
“Kira Tijjani ya samemu anan da mota”.
Duk da a hankali yay maganar sarai Shu'aibu ya jisan. Sai dai yayi mamakin jin abinda yace ɗin. Amma bashi da hurumin musawa. Sai ma waya daya zaro yay kiran TJ ɗin. Cikin ƙanƙanin lokaci motocin biyu suka iso. Ta farkon aka buɗe masa ya shiga shi da Laalah. Ta bayan guards ɗinsa ne. Sai TJ da Shu'aibu a gaba tunda ba Hayatu. A ɗan ɗarare TJ ya ce, “Sir ina zamu je?”.
Shiru kamar bazai ce komai ba. Sai kuma can a ƙasan maƙoshi ya furta, “Hospital”.
Da girmamawa TJ ya amsa da, “An gama ranka ya daɗe” yana tada motar. Kansa kawai ya kwantar jikin kujera ya kumshe ido. Har lokacin zufa na faman tsatstsafo masa. Bai ɗago ba har sai da suka isa asibitin. Shu'aibu ya buɗe masa da sauri ya fito. Sai dai banda Laalah shi an barsa a motar. Cikin takun nan nasa ya nufi cikin asibitin Shu'aibu da TJ biye da shi. Tako ina tsirarun ma'aikatan cleaners da ma Nurses da sauransu sai kalonsu suke. Koda suka shiga reception tuni yammatan dake a kan katan sun miƙe bakunansu a washe suna masu Barka da zuwa idanunsu a kansu kamar tsoffin mayu. Ko kallo basu ishesa ba sai su TJ suka amsa musu...

Kuka na gama zabgama mama Balki akan nifa yau ko su sallamen daga asibitin nan kona gudu gida. Dan bazan sake kwana banje naga halin da Ummie ke a ciki ba. Lallashina taitayi akan nayi haƙuri jikina ya ƙara ƙyau tunda doctor tace sai nan da kwana biyu, jikin Ummie kuma da sauƙi sosai. Tirjewa nayi akan nifa sai na tafi. Ganin yanda nake zabga uban kuka yasa Maman cewa shike nan naje nayi wanka idan Alhaji Ƙarami yazo anjima itama zata sake masa magana da kanta. Badan naso ba nabi umarninta. Kamar kullum sai da ta fara taimaka min na shiga ruwan zafi na mintuna goma sha biyar zuwa ashirin da nake yi sau uku a rana. Sannan ta fito akan nayi wankan bara taje ta dawo.
Wankan na ƙarasa batare da tunanin kowa zai iya shigowa ba na fito ɗaure da towel kawai. Dan masu shara tun sanda zan shiga cikin ruwa Mama Balki ke cemin sun shigo aikinsu. Haka dama sukeyi, kullum tunda sassafe zaki gansu, wani lokacin ma ana idar da sallar asuba. Daga nan kuma sai da rana, sai kuma yamma. Fes kuwa na samu ɗakin harda turaren wuta sun kunna. Jikina na goge da ɗan hanzari. Bana son Mama Balki ta shigo ban saka kaya ba duk da nasan ko tazo ɗin tsayawa take bakin ƙofa sai ta tambayi na shirya sannan ta shigo, dan kunyarta nake ji matuƙa. Ƴar jakar kayanmu na buɗe na ciro b&p da zan saka dan ni ina amfani da kayan asibitin ne. Bra ɗin na fara ƙoƙarin sakawa da sauri-sauri, na saka hannu ɗaya ina ƙoƙarin saka ɗayan kawai ya zaro ta baya. Fuska na ɓata kamar zan fasa kuka, abinda dai nake gudun sai ya faru, tunda dole na jira Mama Balki tazo ta maƙala min ko kuma na cire na sake sakawa tazo ta sameni, amma bari muga na gwada dai kozan iya nawa ƙoƙarin. Kicin-kicin maidawa na fara ina famar cizar lips, sai kawai naji saukar lallausan hannu mai bala'in sanyi akan nawa dake riƙe da hannun bra ɗin. Tabbas wannan ba mama Balki bace, dan wani irin mayataccen ƙamshi ne ya shiga ratsa ƙofofin hancina. A birkice na juyo gaba ɗaya na nama manta da wani batun saurin da nakeyi. Saukar idanuna cikin lulu cat ɗin nashi ya sani ja baya jikina har tsuma yake. Shiko ko gezau, sai ma wani irin kallon ƙurilla yake bina da shi idanunsa a shanye. Inda naga ya kafama idanun nima na kalla da sauri, ai da sauri na naɗe hannayena a wajen ina tura baki kamar zan fasa kuka. Kafaɗa ya ɗan ɗage tare da taɓe baki irin shi baiga abin kallo ba, ina ƙoƙarin sake juya masa baya sai kawai ya shiga takowa a hankali. Baya na sake jan jikina yana cigaba da biyoni duk na ruɗe. Jin na dangane da abu yasa na juya da sauri na kalla, sai naga bangone, tashin hankali anzo the end kenan inji bature. Banda zaɓin daya wuce kawai na juya masa baya na kalla bangon. Idanuna a runtse murya na rawa na ce, “Wai da ALLAH minene haka kake yi? Ni dai ka fita kayafa zan saka, sai Mama ta shigo ta ganka”.
Maimakon amsa min ko ya fitan sai kawai naji ya saukar hannunsa akan kafaɗata, da ƙarfi na sake matse idanun nawa jin yanda yake wani irin tafiya da yatsun kamar mai yi da gayya........✍️




_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*


Please Login or Register in order to submit comment