Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da sauke idanunsa akan ogansu ya furta, “Wace doka ce ta baku damar shigowa cikin gidana kuyi harbi batare da kun samu wani dalilin yin hakan ba? Wace doka ce ta baku damar shigowa har cikin gidana kuci zarafin ahalina? Bayan ba'a turoku domin su ba an turoku ne gareni ni ɗaya”.
Rasa wace amsa ya kamata su bashi sukayi, sai ƴar kallan kallo suke. Sai da ogan nasu yaga zasu muzanta cikin aro jarumtar dole ya matso inda Maash ɗin ya ke ya miƙa masa takardar hannunsa. “Munada cikakken lasisin shigowa gidanka Mr Awwab El-Mu'azz Adams”.
Da ga shi har takardar Maash yabi da kallon wulaƙanci batare da ya amsa ba. “Baka amsa min tambaya ta ba ai”. Ya faɗa a daƙile.
Kame-kame jami'in ya fara cikin son aro jarumtar dole. Sai kawai Maash ya zare takardar daga hannunsa yana faɗin, “Okay bama sai ka amsa ba anan. Next time kawai”. Ya ƙare maganar cike da rainin wayo yana kallon takardar. Yana gama karantawa ya saki wani shegen murmushi, a saman lips ɗinsa ya furta “Mr Paul” dan ya fahimci kai tsaye daga inda saƙon yake. Nuni yay ma Hayatu da ya tashi. Babu musu kuwa ya miƙe ya nufosa. Hannu yasa a aljihu ya ciro wayar TJ daya amsa da key ɗin bedroom ɗinsa ya miƙa masa. “Ka bama Mama ta dubata. Idan akwai matsala kuje da ita asibiti zan sameku acan. Juliet taje ta ƙarasa meeting ɗin jiya”.
“Amma sir...”
Ɗauke kansa yay alamar baya buƙatar jin komai da ga Hayatun. Tj ya kalla tare da faɗin, “Bani key ɗin mota”. Cikin sauri TJ ya zaro ya miƙa masa. Batare da ya kalla ko inda su Hajiya Mammah suke ba ya matsa ga jami'an tsaron. Wani ne ya yunƙuro da Handcuffs a hannunsa da sauri. Wani banzan kallo da Maash ɗin ya masa bai ma san ya taka burki ba harda cin tuntuɓe. Wucewarsa yay ga motarsa ya buɗe ya shiga mazaunin driver. Sai da yazo saitin ogan nasu ya tsaya, batare da ya kallesa ba ya furta, “Zan iya wucewa ni kaɗai?”.
Kallonsa kawai shugaban jami'an yake. Dan shi kam yanzu yake sake tabbatar da rashin mutuncin Maash ɗin da ake faɗa ya zarta duk yanda aka gaya masa ashe. Ga yaron da shegen kwarjini. Duk da kasancewarsa jami'in tsaro, a shekaru kuma zai iya haifar Maash ɗin, wata irin shakkarsa yake ji har ƙarƙashin zuciyarsa. Har takai ya fara jin nadamar amsar wannan aikin da yay. Yaransa biyu ya bama umarnin shiga bayan motar, shi kuma ya shiga gaba kusa da Maash ɗin. Sauran kuma suka fita da sauri wajen gate inda motocinsu da sauran ƴan uwansu suke.
Shi Maash ma sai abin yaso bashi dariya ganin yanda aka cika kusan rabin street ɗin da jami'an tsaron kai kace sunzo kamo wani ƙasurgumin ɗan ta'adda ne daya addabi duniya. Lalataccen Murmushi ne ya suɓuce masa kaɗan. Dan in ba kallonsa kake ba bama zaka taɓa fahimtar yayisa ba. A nutsensa yake jan motar tamkar wanda baya so, har suka iso babban headquters ɗin DSS ɗin dake a garin na Lagos babu wanda yay ko tari a motar.....

★★★

Motocin na gama fita a harabar gidan Hayatu yay wani irin sauke numfashin damuwa. Sai kuma ya maida kallonsa gasu Paah dake ƙoƙarin nufar motoci alamar zasubi bayansu. Nufarsu shima yayi, cikin girmamawa ya dakatar da su. Bayani yay musu akan suyi haƙuri kar suyi gaggawar binsu har sai ya sanar da lawyers ɗinsu yanzu.
Duk sun nuna gamsuwarsu akan hakan, shima sai yay ƙoƙarin ciro wayarsa a aljihu ya shiga kiran lawyers ɗin nasu har su uku. Yayinda shi kuma Paah ke ƙoƙarin neman Baba prof.. da baya ma ƙasar kusan sati uku kenan. Hayatu na gama kiran lawyers ɗinsu ya isa ga Mama Balki dake ta faman share hawaye ita da su Bahijja. Key ɗin da Maash ɗin ya bashi ya bata, tare da mata bayani. Wani irin ajiyar zuciya ta sauke a karo na farko, dan dama hankalinsu a matuƙar tashe yake tun sabe na rashin ganin Samraah ɗin, ita a zatonta ma ko guduwa tayi. Dan ko'ina na gidan babu inda ba'a duba ba har sashen Hajiya Babba daya zama na farko amma babu ita. Batare da kowa ya farga ba Mama Balki ta zare jikinta sashen Maash. Dan su Hajiya Mammah sunata bige-bigen waya ne...

Matuƙar tausayin Samraah ne ya cika Mama Balki har sai da tayi hawaye. Bata kawo a ranta wani dalili ne ya saka Maash yin wannan ɗanyen aikin ba, sai ƙila gardama Samraah ɗin ta masa. Amma yanda tasan Maash da tausayi da ƙoƙarin tsare hakkin kowa a rayuwa da mamaki wannan al'amari. Dan gaba ɗaya al'amarin babu tausayi a ciki. (Koda yake ƙila shima ya kasa riƙe kansa ne) zuciyarta ta ayyana mata tana mai ƙoƙarin ganin bataji zafin Maash ɗin ba a ranta. Ruwa ta shafa ma Samraah ta kawo numfashi, kukan data fashe da shi cikin zabura ya saka Mama Balki riƙota jikinta ta rungume. Sai kawai itama ta fara hawayen tana lallashinta.
Jin muryar Mama Balki yanzu ba shi ba ya sakani jin nutsuwa. Sake ƙankameta nai cikin kuka ina mata magiyar dan ALLAH ta fita dani a ɗakin, idan ta barni kasheni zaiyi bashi da imani. Lallashina ta shiga yi da kalamai masu sanyi, sai da taga na sake nitsuwa sannan ta kwantar dani tana faɗin na jirata. Hawayena na cigaba dayi harta dawo bayan wasu mintina. Babu abinda ke mun kai kawo sai abinda ya farun. Sam hawaye sun gagara ƙafe min, koda Mama Balki ta kamani domin tashi sam na kasa. Sai ma kukan fitar hankali dana sakar mata dan wata irin azaba ce ta ratsani tun daga yatsun ƙafata har tsakkiyar ƙwalwata. Itama ganin bafa zan iya tashin ba ya sakata sake jin matsanancin tausayina. Rigar wankansa data ɗakko daga bathroom ɗinsa ta saka min ta sake gyarawa, sai kuma ta kamani cike da jarumta ta ɗaga gaba ɗaya na. Haka tana nishi baiwar ALLAH ta kaini har Bathroom ɗin. Sai da tamun gajeriyar nasiha da lallashi sannan ta taimaka min na shiga ruwan data haɗa. Bakina na dumtse ina mai fashewa da kuka jikina na rawa. Haka ta rirriƙeni tana cigaba da mun nasihar duk zaburar da nake bata yarda nabar cikin ruwan ba sai da ya huce. Wani ta sake haɗawa, sai da tamun haka sai uku abinka da dattiwar data san takan duniya sannan ta baroni nayi wanka.
Kuka naci sosai har sai da tamun knocking ƙofar sannan nayi wankan. Cikin jarumta da son daurewa na ɗauka wata rigar wankan na saka dan wancan ta jiƙe saboda bata cireta a jikina ba ta sakani a ruwan da ita. Duk yanda naso taka ƙafafuna na fita da kaina hakan ya gagara. Kuka na sake sanyawa mai sautin da har sai da Mama Balki taji ta shigo. Kallona ta tsaya yi, kafin cike da tausayi ta furta, “Samraah bazaki iya tafiya ba yanzu ma?”.
Kaina na jinjina mata ina sharce hawaye. A sanyaye tace, “Kiyi haƙuri kinji, in sha ALLAHU zaki ci riba a rayuwarki tunda bata hanyar banza kika tsinta kanki a wannan halin ba. Amma lallai dole zamuje asibiti kenan”.
Kuka na sake fashe mata da shi batare dana iya cewa komai ba. Yanzun ma itace ta fiddoni. A saman kujera ta ajiye ni. Ta gyara ɗakin fes kamar bashi ba. Dan hatta da bedsheet ɗin ma ta canja wani. Kayana da ban san waya kawo mata ba ta bani tace na saka. Ita kuma ta koma bathroom ɗin bayan ta shinfiɗa min abin salla. Kayan na saka ina hawaye na sakko domin yin sallar, da ƙyar na iya yinta a tsaye, inayi ina kuka. Ina idarwar na zame a wajen na kwanta, kafin mama Balki ta fito zazzaɓi mai azabar zafi ya rufeni.
Barci ya ɗan fara figata mama Balki ta tasheni nasha tea, kasa sha nayi, sai kuka nake mata kawai. Baiwar ALLAH duk ta shiga damuwa sai lallashina take yi. Wani barcin ne ya sake figata, gigitaccen bugun ƙofar da ake ya farkar dani. Buɗe ƙofar Mama Balki taje tayi, ɗauuuu kake jin saukar mari a fuskarta. Kafin Hajiya Mammah ta hankaɗota ciki. Taga-taga tayi zata faɗi ALLAH ya taimaketa ta rike ƙarfe net ɗin gado. Har cikin rai naji zafin marin nan da taima Mama Balki yau. Cikin matuƙar masifa ta shiga surfama Mama Balki zagi wai itace kawaliyarsa dake kawo masa yara ashe yana musu fyaɗe, to yau kam sai sunci ubanta a gidan nan. Duk yanda take son musu bayani kowa yaƙi yarda da ita, sai tambayoyi suke jefe mata kuma sunƙi bari ta basu amsa.
Shiɗewa numfashina ya farayi saboda yanda hayaniyar Hajiya Mammah ke shiga har cikin tsakkiyar kaina dake ciwo. Sama-sama nake jiyo muryar Hajiya ƙarama na bada shawarar kaini asibiti. Daga haka ban sake gane komai ba........✍️

_Huuuum tofa masu karatu ƙaƙa raƙa ƙaƙa.._

*_Yaya zata kaya kenan? Maash zai sanarma ahalinsa wacece Samraah a yanzu ko zai cigaba da ɓoyewa?._*

*_Shin waye Mr Paul daya saka a aka kama Maash? Mi kuma kuke tunanin zai faru?_*

_Samraah!! Samraah!! Wane hukunci kuke tunanin zata iya ɗauka akan Maash kan abinda ya faru, da labarin da taji na al'ummar wannan gida?._

*Hajiya Mammah?*
*Hajiya ƙarama?*
*Paah?*
*Uncle Abdullahi da matarsa?*

_Shi kansa Maash bakwa tunanin akwai abinda yeke binnewa kuwa?._

_Gidan Abba, gidan su Mansoor, nan ma fa duk akwai sabuwar cakwakiya._

*_Hummm kar dai na cikaku da surutu, mu tara ranar Monday in sha ALLAHU. Banda pages dole zanyi hutun weekend ɗin nan insha ALLAHU. Dan munzo gaɓar da komai yake buƙatar fita da fitarsa. Ku muje zuwa TSUTSAR NAMA BOOK 3 Guys._*


_Bana son naga numbers ɗin na tsaho ganda rubutun nake ji wlhy, dan haka zamu tafi part 3 yanda zamuyi maza kafin salla mu kammala in sha ALLAH 😘😘😘_



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒐𝒏𝒆_

_______

*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._

*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram_*

I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_WhatsApp_*
https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG


https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5

__________


.......Suna shiga cikin headquter ɗin Lawyers nashi na isowa shima. Sai dai kafin su ƙarasa gareshi an shige dashi wani ɗakin bincike. Table ne kawai da kujeru biyu masu facing juna. Sai da ya gama ƙarema ɗakin kallo fuskarsa a yamutse kafin yaja kujerar ya zauna. Yana zama cikin jami'an wani shigo, da girmamawa yake tambayarsa ko yana buƙatar wani abu kamar su tea haka. Ɗan jimm yay yana kallon ma'aikacin, sai kuma ya murmusa kaɗan alamar a'a. Fita Jam'i yayi, shi kuma ya jingina bayansa da kujerar sosai ya lumshe idanunsa kawai. Kusan mintuna fin ashirin sannan aka sake buɗe ƙofar. Bai motsa ba bai kuma buɗe idanunsa ba har jami'in ya kai zaune. Kaɗan ya ɗan buga table ɗin, sai dai a hakan ma Maash ɗin ƙin motsawa yayi. Sai da ya mula dan kansa sannan ya buɗe idanunsa ya zubama jami'in batare daya tashi ba. Ji Jami'in yay bazai iya jure kallon ba, sai ya kauda idanunsa cike da basarwa yana furta, “Sir bamu da isashen lokaci. Idan ba damuwa ka amsa mana wasu ƴan tambayoyi mana”.
“Jeka maganarka kai tsaye” Maash ya faɗa a daƙile.
Ran jami'in ne ya sosu, sai dai baice komai ba ya cigaba da faɗin, “Akwai containers ɗinka da suka tashi daga Lagos a shekaran jiya da dare zuwa ƙasar Ghana. An samu yara ƴammata a cikin ɗaya da muke da tabbacin safararsu aka shirya yi. Still dai a cikin container ɗin anyima yaran makwanci, a ƙasan shi mun samu kayan laifi”.
“Kamar......?”
Maash ya faɗa cike da rainin hankali. Yanzu kam a fusace jami'in ya kallesa. Sai dai kuma bai iya cewa komai ba ya cigaba da faɗin, “Drivers ɗin sun tabbatar mana da cewar sun fito daga companyn ka ne”. Ya ƙare maganar da tura masa hotuna gabansa. Batare da Maash ya ɗauki hotunan ba ya zuba musu ido kawai. Kansa ya ɗan girgiza cike da rashin damuwa ya furta, “A staff ɗina bana tunanin nasan waɗan nan fuskokin”.
“Ba zamu tabbatar da hakan ba, dan zaka iya hiding nasu. Sai dai kuma su containers ɗin ai bazai yiwu kace ba naka bane ba”.
Shiru babu alamar Maash ɗin zai tanka, sai da ya mula dan kansa sannan ya saki ɗan gajeren murmushi da kai hannu ya shafi kwantaccen gashin fuskarsa. Zamansa ya gyara da ƙyau gaba ɗaya hannayensa akan table ɗin ya zubama jami'in ido. “Mr Man kamar ya dace ka tuna kai jam'i ne ba alƙali ba. Damar samuwar amsar tambayoyinka kuwa zaka same su ne kaɗai a bakin lawyers ɗina”. Daga haka ya gyara zamansa ya sake lumshe idanunsa duka hannuwansa harɗe a ƙirjinsa.
Iya ɓacin rai Jam'in nan ya shiga. Dan haka ya miƙe a fusace ya fice abinsa. Murmushi Maash ya saki mai ɗan sauti batare da ya buɗe idanunsa ba.

Har yamma Lawyers na Maash na fafatawa a station ɗin, shi dai yana a inda aka kaisa har yanzu. Sai da lokacin Sallah yayi ya buƙaci yin alwala. Basu da damar hanashi. Abincin da Hayatu ya kawo masa kuwa ko kallonsa baiyi ba. Dan shi fa sam bawai cakwakiyar station ɗin ma bace damuwarsa. Hankalinsa ma gaba ɗaya baya a wajen.
Gab da magrib Baba prof... Ya iso, da ga airport kai tsaye shima station ɗin yayo, anan ya samu kusan duk ahalin gidan. Paah, Uncle Abdullahi, Hajiya Mammah, Maman Maleeka (Matar Uncle Abdullahi) sai Hayatu dake kai kawo tsakanin asibiti da aka kwantar da Samraah zuwa nan. Ko bayan isowar Baba prof.. ɗin shima ya kai awanni uku a station ɗin kafin su samu bell ɗin Maash ɗin bisa wasu sharuɗɗa masu tsauri.
Ƙarfe tara da wasu mintuna aka fiddo Maash da ga ɗakin nan. Kallo ɗaya yay ma ahalin nasa ya ɗan kauda idanunsa. Sai kuma ya cigaba da takowa a nutsensa har inda suke. Baba prof.. ne ya riƙosa ya rungume yana faman ambaton Alhamdullah. Shi dai Maash baice komai ba. Bayan ya sakesa kuma ya koma tattaɓashi da jera masa tambayoyi. “Kana jin yunwa? Akwai inda ke maka ciwo? Sun maka wani abu ne?.....”
“Grandpa! I'm not small boy now”.
Ya katse Baba prof.. ɗin cikin wata irin murya mai cike da rashin damuwa. Murmushi Baba prof.. yayi da kai hannu ya yamutsa masa sumar kansa kamar yanda yake masa a duk sanda suka haɗu. “Oh na manta Muhammad Awwab ɗina dutse na rimi ne baka fargaba sai ta ruwa.”
Dariya su Paah suka ɗan yi, kafin shima ya matso ya rungume Maash ɗin, hakama Uncle Abdullahi. Maman Malika ma tai masa barka. Ganin haka itama Hajiya Mammah ta bashi side hug. Shi dai komai bai cema kowa ba. Sai hankalinsa da ya ɗan maida ga lawyers ɗinsa da Hayatu dake fitowa. Cike da girmamawa suka shiga gaisheshi. Tare da jajanta abinda ya faru suma. Idanunsa ya lumshe kaɗan da sake buɗewa, suma ɗin dai batare da yace ma kowa komai ba ya motsa a hankali ya fara tafiya.
Suma duk ƙoƙarin ficewar sukayi, kowa da abinda ke a zuciyarsa. A motar da yazo da ita da safe ya shiga. Sai dai yanzu Hayatu ne a mazaunin driver. Har sun ɗauki hanyar gida a kasalance Maash da idanunsa ke rufe har a lokacin a hankali ya furta, “Hospital”.
Cikin girmamawa Hayatu ya amsa masa, tare da fita a cikin sauran motocin ya ɗauki hanyar asibiti. Sauran abokan tafiyar basu farga ba sai da akaje sauke Baba prof a gidansa. Da farko sun ɗauka ko gida su suka wuce saboda Maash ɗin ya huta, sai da drivern Baba prof ɗin ya sanar da inda yaga sunyi sannan ne a fusace Hajiya Mammah ta ce, “Eh lallai, al'amarin Awwab kullum sake gawurta yake wlhy. To amma kuma anya ba wani abun yaje aikatama yarinyar nan ko hana likitocin faɗa ba saboda ya rufe sirrinsa.”
Har cikin rai zancenta ya soki zuciyar Paah, sai dai baice komai ba. Baba Prof ne ya tambayi abinda ke faruwa? Har zagwaɗi Hajiya Mammah keyi wajen zayyane komai daya faru da safe har neman yarinyar da suka dinga yi da daddare. Wani yawu mai kauri Baba prof ya haɗiya idanunsa akan Paah da Uncle Abdullahi. Kamar zai yi magana sai kuma ya fasa. Wayarsa ya amsa a hannun drivern sa daya kwaso kaya zai kai ciki, dan duk abinda Hajiya Mammah ta faɗa ya laɓe yana jinta. Kai tsaye Baba prof ɗin wayar Hayatu yay kira, bugu ɗaya kuwa ya ɗaga.
“Kuna ina?”.
Da ƴar in ina Hayatu ya ɗan kalla Maash dake ƙoƙarin fita a mota daya buɗe masa dan isowarsu ke nan. “Bab ba baba muna CLINIC”.
“Clinic! Yin me?”.
“Zamu duba mara lafiya ne”.
Ƙittt Baba prof ya yanke kiran batare daya sake cewa komai ba. Cikin damuwa Hayatu ya dubi Maash ɗinya ce, “Baba Prof”.
Komai baice masa ba, sai ma ƙoƙarin raɓasa da yake yi zai wuce abinsa. Dole shima ya haɗiye abinda ke bakin nasa ya bisa.


★★

Mama Balki na zaune a saman abin salla idar da shafa'i da wutirinta kenan akai knocking ɗin ƙofar. Miƙewa tai tana kallon agogo, azatonta ma Nurse ɗin data sakama Samraah ruwa ce ta dawo. Ruwan ta kalla taga ko rabi bai kai ba ma, kamar zatai magana sai kuma ta fasa. Ƙofar ta nufa, sai dai kafin ta buɗe sai da ta tambaya waye?. Hayatu ne ya amsa mata da cewa, “Mama mune”.
Da sauri ta buɗe tana murmushi, tana ƙoƙarin bashi hanya ya shigo idonta ya sauka akan Maash. Wani irin washe baki tayi tana ambaton Alhamdullah. Da jerama UBANGIJI kirari. Ɗan lumshe idanunsa yayi tare da sakin gajeren murmushi ya shiga gaidata. Amsa masa tai tana ƙara godema ALLAH daya sa komai ya zama mai sauƙi.
Nan ma murmushin kawai ya saki baice komai ba, sai Hayatu ne ke tayata murnarta. Ƙarasa takawa yay a hankali zuwa gaban gadon idanunsa a kanta. Tana kwance samɓal idanunta a rufe alamar barci take. Fuskarta ta wani irin yin fayau da ita, sannan har yanzu idanunta a kumbure suke alamar taci kuka mai yawa. Lips ɗinta sun bushe tare da tsukewa waje guda sun ƙara pink sosai. Take wasu abubuwa suka shiga dawo masa game da ita. Cikin sauri ya kauda su tare da janye idanun nasa daga lips dinta, akan hannunta da aka saka ruwa ya sauke. Madaidaitan farcinanta dake da ɗan sauran jan lalle na biki kaɗan da bai gama fitaba yaja kusan mintuna biyu yana kallo, kafin ya maida ga ruwan da ake ƙara matan. Sai kuma ya janye gaba ɗaya ya matsa gaban side drawer dake a gefen gadon ya ɗauki file ɗin da aka ajiye ya fara dubawa. Juyowa yay da nufin yin magana sai ya ga ɗakin wayam, ashe Mama Balki da Hayatu sun fice. Kansa kawai ya girgiza yana ajiye file ɗin, sannan ya zagaya ta ɗayan side ɗin gadon inda hannunta ke free ya zauna kusa da ita jikinsa na gogar nata. Hannun nata ya kamo cikin nasa, ya zubama dan sauran lallen dake jikin faratan nata ido, abubuwa da yawa zuciyarsa ke tunano masa da suka shafi Ummie, mace ce mai tsananin son jan lalle, tunda ya santa kafin lalurarta lalle baya gama fita a hannunta take yin wani. Hakan ya sashi tashi da son lalle shima, lokacin yana ƙarami yakan saka mata rigima shima sai an masa. Takan ce masa maza basa lalli, amma ya tubure ya dinga bori ko yaje ya tsare Mama Balki ko mahaifiyar Hayatu akan dole su sai sun masan, dan a farkon ciwonta kafin komai ya damule har da kansa yake mata lallin a yatsun hannu saboda yasan tana so. Murmushi ne ya suɓuce masa da shi a karan kansa ya mance tsahon shekarun daya ɗauka baiyi irinsa ba. Sai kuma ya kai babban yatsarsa ya ɗauke guntun ƙwallar da suka taru masa a gefen ido kaɗan........✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒐_


*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._

*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram_*

I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_WhatsApp_*
https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG


https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5

_______

.......Ɗan motsi Samraah tayi fuskarta a yamutse baki a taɓe kamar mai shirin sakin kuka. Idanu kawai ya zuba mata yana kallon yanda take laɓe bakin, ƙoƙarin motsa hannunta da tai ya sashi sakin wanda ya riƙe ya riƙe mata wancan gudun karta goce ruwan, sake yamutse fuskar tayi da ƙara tura baki.
“Cry. Cry”.
Ya faɗa a hankali saman lips ɗinsa yana kai ɗayan hannunsa a karo na farko kan fuskarta ya ɗan shafa gefen kumatun kaɗan. Idanunta ta shiga motsawa a hankali, sai kuma ta buɗesu gaba ɗaya. Cikin yanayin wadda barci bai saka ba ta ɗan zuba masa su, shima kallon nata yake...

Tar tar fuskarsa ta fara bayyana cikin idanun nawa sosai. Wani irin harbawa zuciyata tayi babu shiri na zabura. Sai dai jin an riƙeni yasa na kallesa a marairaice, batare dana san hawaye sun ɓalle min ba na fara roƙonsa cikin

Please Login or Register in order to submit comment