Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Fahad ya fasa yana rungumeta gaba ɗayanta sai kuma ya fashe da kuka.
A hankali Maash ya kauda kansa gafe na tsawon minti ɗaya kafin ya maidosa kansu. Hayatu ya miƙama Babyn sannan ya kai duƙe a slowly tamkar wanda baya so ya ɗago Fahad daga jikin Ummie. Miƙar da su yay tsaye su duka ya kama fuskar Fahad da hannu biyu ya fara share masa hawayen da yatsunsa manya yana wani ɗan jujjuya masa kansa”.
Jikinsa kawai Fahad ya faɗa suka wani ƙanƙame juna da iyakar ƙarfin ƙwanji. Cikin kuka Fahad ya ce, “Yaya dan ALLAH da gaske UMMIE ta samu lafiya? Da gaske ba mafarki nake ba kamar yanda na saba?”.
Ɗagoshi Maash ɗin yayi ya tsurama fuskarsa ido. Sai kuma ya sakar masa wani shegen murmushi daya kusan ɓaro zukatan wasu tare da motsa lips ɗinsa kaɗan, cikin silent voice ɗin nan tashi ya furta, “Ba barci kake ba Kiddo. Ummien ce a gabanka da lafiyarta. Dan haka ga saƙo ka faɗama MAƘIYA GASKIYA!!!” ya ɗan ɗaga sautinsa anan ta yanda kowa sai da ya jisa. “Su fara gudu, gudu na ceton rayukansu. Gudu na cigaba da bizne abinda suka shuka. Idan ba haka ba. Bayan ka musu zanen Yarabawa. Ni Muhammad Awwab El-Mu'azz nayi musu alƙawarin sai nayi gunduwa-gunduwa da kowanne gaɓa ta jikinsu ta yanda ba za'a iya iya banbance kowanne ɓangare na halittar su ba!!!”.
Tamkar wani abun shirin Film kawai Fahad ya bushe da wani ɗan iskan dariya. Sai da yay mai isarsa kafin ya kalla yayan nasa. Cike da jin sabuwar izza ya ce, “My sweetheart yayana. Idan ka fatattaka namansu. Na maka alƙawarin siyo ƙatuwar tukunya da ƙatin iccen nan na dahuwan naman raƙumi, na bama Aunty Samraah ta mana DABGENSU mu baje a ƙaton tray UMMIE da MAMA su dinga bamu a baki muna taunawa da korawa da ruwan kamfanin MAASHHHHHHH”.
Dariya abin ya bama Falaq. Tako kasa haɗiyewa ta fara ƙyalkyatawa. Sai kawai Hajiya Mama da itama abin ya birgeta ta shiga yin dariyar. Ai kawai sai su Mama da Hayatu da Maman Malika suka hau tayasu. Gogan kan sai ya wani lumshe idanu kawai yana mai tura hannayensa duk biyu a cikin aljihu. Da wannan damar Hajiya Mama da Maman Malika suka sami damar tahowa rungume Ummie. Tsabar makirci sai itama Hajiya ƙarama ta taho da gudu tana kuka zata rungume Ummien wai. Ajiyar zuciya Hajiya Mammah ma ta saki tana sakkowa. Ganin hakan yasa su Azizat fara sakkowa daga upstairs da suka maƙale a guje suma duk da bawani saninsu Ummie ɗin tayi ba duk suna ƙananu sosai, sai ɗan sanda ta samu lafiyar nan lokacin kuma ba'a tare suke ba. Suma duk nufar rungumetan sukayi. Amma mi duk kafin su isa gareta sai kawai Fahad yasha gaban kowa ya tare ta. Cak duk suka tsaya suna kallonsa kamar yanda shima yake kallonsu cikin wani irin ɗage kan rainin waye da girgiza hannu ya ce, “Inaa ai babu mai taɓa Ummie a gidan har sai anyi searching”. Yana gama faɗa yaja hannun Ummie yay hanyar sashen Maash da ita dake ta cikin falo yana wani kalar takun buɗewa daka gani kaga tsageran matashin zamani mai shirin a mutu ko ai rai🤣😂.
Shi kansa Maash a wannan gaɓar sai da yay gajeren murmushin da kowa zai iya gani a kan fuskarsa yana mai ɗan girgiza kan kaɗan. Batare da yace ma kowa komai ba yay ma Falaq nuni da hanya ita da mama Balki. Gaba kuwa sukayi ya bisu a baya bayan ya juya ya kalla Baba prof cikin ido ya sakar masa murmushi, ya sake juyawa ga Hajiya ƙarama ita kuma ya mata wani shegen kallon da su duka sai da suka nema zubewa ƙasa. Cikin nashi takun bajintar shima yay gaba. Yayinda falo yake tsitt har yanzu tamkar an jera gunkunaye. Kowa da abinda yake rayama zuciyarsa.
Rawar da ƙafafun Baba prof keyi yana shirin zubewa a ƙasa ya maidosa hayyacinsa daga sumar tsaye da yayi sakamakon kallo da murmushin da Maash ya masa. Yay taga-taga zai faɗi sai da Hayatu ya taroshi yana faɗin faɗin, “Subahanallahi Baba”.
Cikin wani irin jan numfashi dake shirin ƙwace masa a hankali ya ce, “Kaini na zauna Hayatu zaunar da ni.”
Babu musu Hayatu ya kamashi har kan kujerar dake kallon ta Hajiya ƙarama da itama ta kai zaune sakamakon jirin dake neman yarda ita ya zaunar. Sai kawai ya ƙara yin shakaff a kujerar dan kaɗan ya rage zawayin dake ƙoƙarin ɓarke mas ya samu ƙofar fara tsirarowa.........✍️

(😂😂😂😂Baba prof sannu kaji, abin tausayi wlhy🥱🥱🥱).



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒊𝒙𝒕𝒚-𝒇𝒐𝒖𝒓_


.......Shigowar Uncle Abdullahi gidan da labari ya kaimawane ta dawo da kowa a hayyacinsa. Sai tarin da ya sarƙe Baba prof. Su duka su kansa sukayi, banda Hajiya ƙarama data samu hanyar hayewa sama. Kallon kallo sukaima juna ita da Hajiya Rubayya da har yanzu ke tsaye tana kallon komai. Sai kawai suka sakima juna murmushi. Cikin rawar murya Hajiya ƙarama dan ita kaɗai tasan halin da take ciki itama ta ce, “Ki tattara su Falilah subar gidan nan zuwa gobe bayan kowa yasan wacece Nafisa”.
“An gama ranki ya daɗe”.
Hajiya Rubayya ta faɗa cikin kashe ido tana sakin wani makirin murmushi. Gaba Hajiya ƙarama tayi zuwa sashensu. Sai da ta tabbatar ta dannama ƙofar key kafin ta wurgar da bag ɗinta bayan ta ciro wayarta. Kira ta dannama Commando, yana ɗagawa bata jira cewarsa ba cikin bushewar zuciya ta furta, “Wasa ya canja gaba ɗaya. Dole ne a mutu har liman. Uwar tafiya ta dawo hayyacinta, yanzu kam kan mai uwa da wabi kawai. Ka canjama Mu'azz wajen zama a daren nan. Shi kaɗai ne makamin mu a yanzu”.
Tana gama faɗa ta yanke wayar. Jannifer ta kira, itama tana ɗagawa tace, “Bana son kuskure. Idan har naga kiranki ya zama Mu'azz da Commondo na a hannunki ne”. Wayar ta wani irin jefa saman gado. Sai kuma ta ƙyalƙyale da dariya ta kuma fashe da kuka duk a lokaci ɗaya, tamkar itama dai kan nata ya fara taɓuwa.

Hajiya Lawisa sorry woohoo😂😂🤣🥱.


✨✨✨✨

Commondo ya jima zaune da waya a hannu shi bai ajiye ba shi bai motsa ba. Dan shi kansa ba ƙaramin dukan zuciyarsa zancen Hajiya Ƙarama ɗin yay ba. Yanzun nan fa yake ganin text message ɗin wani yaronsa da tun ɗazun ya turo masa kasancewarsa da Hajiya ƙarama yasa bai lura ba. A saƙon yana sanar masa cewar ya gano inda Mahaifiyar Maash take. Har ya tura masa address yanzu haka shirin da yake kenan na zuwa su ƙwamusota ransa fari ƙal zai fara aiwatar da nasa plans shima. Kansa ya girgiza, dan haka kawai yaji kamar bai yarda da batun Hajiya ƙarama ɗin ba. Wayar ya fara daddanawa, yana zuwa kan sunan da yake nema ya danna mata kira.
Siyama da tun ɗazun take a bayan window laɓe ita da wasu ma'aikatan gidan mabanbanta suna kallon komai dake faruwa dan tun isowar su Maash duk wanda idonsa ya gansu bai zauna ba ya biyo saboda son tabbatar da Hajiya Babba ɗin ce ko watace ke musu gizo wayarta ta hau tsuwwa. Da sauri tabar wajen ganin Commondo ne. Sai da ta shige cikin garden sosai sannan ta ɗaga tana mai maida muryarta can ƙasa ta ce “Boss”.
“Siyama mike faruwa a gidan nan?”.
“Hummm! Boss ai komai ma ya faru ko nace yana kan faruwa. Jira nake kawai akai ƙarshen Film ɗin na kiraka na baka bayani.....” tsaf ta zayyane masa komai fiye da yanda Hajiya Ƙarama ta sanar masa. Sannan ta ɗora da faɗin, “Mutuniyarka ta haye sama kamar zata zube. Dan numfashinta ma kamar siezing yake. Kakansu ɗin nan da yau na ɗaura alamar tambaya a kansa gashi nan za'a wuce da shi gida naji suna kiran likitansa”.
Murmushi Commondo yayi, dan yasan Siyama bata san komai akan Baba prof ba. Ya turata jikin Paah ne domin ɗaukar fansa da sanya masa ido akan duk wani motsin Hajiya ƙarama. Tunaninsa ya katse tare da yin gyaran murya. Sannan ya ce, “Zamanki ya kusa ƙarewa a gidan nan. Sai dai ki saka min ido akan Lawisa sosai-sosai a tsakanin nan. Koda tari tayi na sani”.
“An gama Boss”. Ta faɗa cike da girmamawa. Dan commondo ya cancanci fiye da komai a wajenta. Ya taimaketa a lokacin da kowa ya ƙyamacesu akaƙi taimakonsu ita da mahaifiyarta. Ita kaɗai ta tashi gaban uwarta batare da sanin kowa a danginta ba da mahaifinta. Tunda tai girma tayi wayo takan tambayi mamanta ina babanta saboda ganin sauran yaran da iyayensu ke haya a gidan da suke duk suna da Baba. Maman tata bata bata amsa. Sannu-sannu idan faɗa ya haɗata da yara sai a dinga zaginta da kiran mamarta karuwa ita kuma ƴar shege. Tun abin baya mata zafi harya fara. Ta dinga tsare mamarta tana kuka amma bata cewa da ita uffan. Daga ƙarshe ma suka bar gidan. A anguwar da suka koma ɗin ma komai bai canja ba, dan nan ɗin ma dai Hausawa ne. Tasha kama mata a lokuta da dama na gulmar mamanta akan ita munafukar karuwa ce. Kullum tana nuna ita ta ALLAH ce sai dare yayi ta fita aikata aikin ta. Tun abin baya mata tasiri har itama ta fara tsarguwa da fara sakama Maman nata ido. Sai dai hakan ya gagara dan barci na hanata rawar gaban hantsi. Tunda tai wayo bata iya wuce takwas na dare batai barci ba, takan kuma rasa dalilin hakan. Sai daga bayan nan data duƙufa bincike ta gano Maman nata ce ke bata abinda ke sakata barci ashe a cikin wata FURAR ƙaddara data sabar mata sha tun tana yarinya. Dan haka tafa canja taku itama. Furar ta fara sayowa tana ɓoyewa a duk sanda Mamanta ta bata wadda keda maganin sai ta ƙi sha ta canja da wadda ta sayo ta ɓoye waccan. Haka zatai likimo har Maman tata ta gama shirinta cikin ƙazamar shiga irin ta karuwan dare ta zabga hijjab har ƙasa sannan ta fita. Randa ta fara gani tayi kuka sosai, daga baya ma sai ta sha furar nan barci dole ya ɗauketa. Sai da sukai haka da mamanta fin sati sannan a cikon kwana na takwas tabi bayanta. Hankalinta yay mummunan tashi da abinda ta gani, dan tabbas Mamanta Karuwa ce. Karuwarma ƙazamar karuwa da ake nema ta gaba da baya. Kaɗan ya rage a ranar Siyama bata bar duniya ba. Dan har jiyya ta kwanta na wasu kwanaki. Bata da aiki sai kuka. Ko kallon Mamanta bata ƙaunar yi. Kwatsam a washe garin da aka sallameta asibiti sai ga Mamanta an kawo jage-jage da jini wai wata ta soketa da kwalba a club. Duk yanda taso barinta zuciyarta bata yarje mata hakan ba. Haka ta rungumeta tana kuka da roƙon a taimaka mata. Amma mi kaf anguwar babu wanda ya taimaketan sai Commondo. Shi ya saka yaransa suka ɗauki Mamanta aka kai asibiti, ya biya kuɗin komai harna gado. Tsahon sati uku da tai a asibitin nan har nauyin abincinsu shiya ɗauka. Sai dai me tunda suka dawo gida sai sabon ciwo ya tashi ma Maman tata. Bata ɗauki hakan komai ba sai tunanin wajen yankan ne bai gama warkewa ba. Sannu-sannu suna zuwa asibiti ganin likita kwatsam randa jiki ya rikice sai aka tabbatar mata Mamanta fa nada ƙanjamau. Ga tsutsa na fita mata ta baya Sakamakon abin da take aikatawa dan bata amfani da maganin da masu wannan ɓarna ke sha. Hankalinta ya tashi, taje domin sanarma Commondo ya sake taimaka musu ta samu baya nan yayi tafiya wai. Hankalinta ya tashi, dan asibitin basu riƙesu ba dole suka dawo gida. Wata sabuwar ƙyama da tsangwamace aka fara musu, bataga laifin mutane ba dan ko ita dauriya take saboda warin da mahaifiyarta ke fitarwa ta bayanta daya zazzago. Takai ko zama bata iyayi ma sannan toilet baya iya riƙuwa gareta. Babu kalar kukan da batai ba da magiya amma ina abinci da zasu ci ma ya gagaresu balle omon da zata tsaftacema Mamanta jiki. A haka suka kwashi watanni uku. Kwatsam wata rana zuciyarta ta ayyana mata zuwa wani company neman taimako anan bayansu. Dan haka ta shirya taje. Securitys basu barta ta shiga ba duk da magiya da kukan data dinga musu. Dole ta tsugunna a bakin gate ɗin ta cigaba da kukanta. Tafi minti talatin a haka sai ga wata dalleliyar mota mai azabar ƙyau. Harta gotata aka dawo baya. Magana driven ya mata, hakan yasata miƙewa zaram jikinta na rawa ta nufoshi. Cikin tsawa-tsawa ya tambayeta mi take yi a wajen?.
Jikinta har rawa yake dan tsoro ta sanar masa taimako take nema. Sai da ya gama saurarenta yay mata tsawa tabar wajen. Har ta juya zata tafi tana kuka sai kuma ya dakatar da ita. Hotonta ya ɗauka yay danne-danne a waya. Babu jimawa taga ya ɗago ya kalleta da murmushi. “Yarinya kakarki ta yanke saƙa shiga mota oga yace zai taimakeki a kaiki”. Cike da farin ciki ta shiga motar, shi kuma yay reverse ya koma batare da ya shiga companyn ba. Wannan shine mafarin haɗuwarta da Paah. Dan an kaita garesa wani gida, Maimakon ya taimaka mata bayan ta gama zayyane masa damuwarta kamar yanda ya buƙata sai ya nuna mata sai idan ta biya masa buƙatarsa. Da farko taƙi har tai fushi ta tashi zata fita. Sai dai tuna halin da mahaifiyarta ke'a ciki ya sakata komawa garesa. Babu ko tausayi kuwa ya keta mata haddi, a kuma ranar ta fara sanin namiji. Bayan ya gama abinda yaso ya bata kuɗi har naira dubu ɗari biyu. Haka ta tafi tana kukan baƙin ciki da na farin cikin samun kuɗin da zata kai mahaifiyarta asibiti. Sai dai me tana zuwa ta samu mahaifiyarta ta mutu an jehota ma bakin bola mutane yayyaɓe da ita suna kallo da zagin gawarta. Wannan al'amari ya ɗimautata. Ɗimautawar data yanke jiki ta faɗi bata tashi farkawa ba sai a gadon asibiti. Bayan ta farfaɗo ta fahimci commondo ne ya kawota asibitin... Wannan shine sanadin komawarta hannunsa. Ta bashi labarin komai daya faru, ya nuna ɓacin ransa tare da tabbatar mata ita da kanta sai ta ɗauki fansa dan yasan wanda yay mata wannan aikin saboda sunan companyn data faɗa. Commondo ne ya kawota Maash Mansion a sanadin Jannifer da ya jima da sani ta sanadin Hajiya ƙarama. Da farko Paah ta firgita da ganinta, dan ta tabbatar masa saita tona masa asiri a wajen ɗansa da abinda yay mata. Aiko fa ya rikice yace ta faɗi duk abinda take so. Sai da ta gama ja masa rai sannan tace zata cigaba da zama a gidan, duk wata kuma zai yanka mata albashin naira miliyan ɗaya. Hankalinsa ya tashi ya nema ta sassauta masa dan miliyan ɗaya duk wata tayi yawa ai. Badan baida kuɗin bane ko hanyar samunsu. Sai dai gudun kar Awwab ya gano shi ne. Dan dole de kuɗin zai dinga fiddasu ne daga asusun company. Da ƙyar ta yarda da 200k duk wata. Dole kuma hakan yake biyanta. A hankali kuma ya fara jan ra'ayinta suka cigaba da mu'amala. Koda ta sanarma Commondo sai yace ta cigaba da biye masa ta hakane ai zata cimma burinta itama.. ta cigaba da biye masa, tare da cigaba da ɗibama Commondo bayanan duk da yake so a gidan musamman akan Hajiya Ƙarama da zuwa yanzu ita kanta ta gama gane alaƙarsu, ta kuma san Arwa ƴarsa ce. Sai dai bata taɓa tunanin bama wani bayanan nan ba dan da iya gaskiyar zuciyarta take ƙaunar Commondo matsayin Yaya daya taimaketa a lokacin da kowa ya gujeta.........✍️

_(Hummm ALLAH ya rabamu da mummunar ƙaddara. Da yawan yaranmu idan mummunar ƙaddara ta gitta ma rayuwarsu nakasassun zukatanmu suka gagara taimakonsu a matsayinmu na al'ummarsu, sheɗancin mutane irin su Paah yay tasiri a kansu ko muka dinga musu hisabi da laifin iyayensu ko wasu ahalinsu sai irin su Commondo da akema kallon gurɓatattu su rungumesu, su tallafesu, komi tsarkin zukatansu sai su koma irinsu suma. Kamar dai Siyama. A yanzu zuciyarta ta gama bushewa. Ko kisa Commondo yace tayi wlhy zata aikata saboda shi kaɗai takema kallon girmamawa. Dan ALLAH mutane mu gyara, mu kiyayi hukunta wasu da laifin wasunsu. Hakan na maidamu bayane da sake raunana al'ummar mu da fiddo gazawarmu a fili. ALLAH ka yafe mana kurakuranmu baki ɗaya. Ka shiryemu ka shirya mana zuri'a. ALLAH ka rabamu da mummunar ƙaddara. Ka kiyaye mana mutuncin mazajenmu karsu jawo ma ƴaƴanmu da mu abin kunya ta hanyar aikata mummunan aiki😭🙏. Yanzu idan Awwab yasan gaskiyar irin waɗan nan abubuwan da Paah ya aikata dan akwai ire-iren hakan da yawa da wace kalma zai iya kare kansa. Ummie Ummie Hummm ya rabba🙏😭)_


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒊𝒙𝒕𝒚-𝒇𝒊𝒗𝒆_


......Kuka sosai Fahad yaci a jikin Ummie itama tana taya shi da sake jin tausayinsa, dan kiyayewar UBANGIJI ce kawai tasa yaronta bai lalace ba. Sai Mama ke lallashinsu. Dan Maash ya fita zuwa asibiti ɗakko Samraah kamar yanda yay ma Ummie alƙawari.

Ina zaune a saman abin salla dana idar da shafa'i da wutri hannayena biyu tallafe da fuskata na afka duniyar tunani. (Ko ina Yaya Awwab ya shiga ne? Ina Fahad da Hafizzullah? Da har yanzu ko mai kama da su ban gani a asibitin ba. Shin Ummie fa? Aunty Falaq kota haihu?) Waɗan nan tambayoyin sune fal zuciyata. Sai kuma zancen ɓatan Paah ɗin nan yana cimun rai da saka tunanina rarrabuwa akan Matarsa da Kakansu. Saukar soft hand mai sanyi akan nawa ya sani ɗago idanuna. Sosai naji shock ɗin ganin wanda banyi zato ba. Dan sam ba ƙamshinsa bane dana sani kamar dai ranar nan. Sai kawai raina ya bani yau ma na sake yin mafarkinsa kenan. Numfashi na ɗan sauke da cigaba da kallonsa dan na gama yarda mafarkin nakeyi ɗin.
Cike da wani irin salo ya ɗan ɗage girarsa duka biyu da mun alamar kallon fa?. Samun kaina nayi kawai da ɗan ɓata fuska. Cikin ɗan ƙunƙunin da nai zaton duk a mafarkine kawai na ce, “Ni ka bar min gizo”.
Idanu ya ɗan lumshe a hankali. Tare da rungumeni a jikinsa. Gaba ɗaya naji jikina ya wani mutu. Musamman da ya ɗaura mitsitsin bakinsa akan kunnina can ƙasan maƙoshi ya furta, “Kona mutu sai na dinga zuwa miki a fatalwa ma”.
Da sauri nayi ƙoƙarin janye jikina zuciyata na harbawa da sauri-sauri. Amma sai ya hana hakan yama sake ƙanƙameni da ƙyau yana sakar min numfashin sa a cikin kunne. Dole na sake ƙanƙamesa muryata na rawa na ce, “Please Ya Awwab mafarki nake ko gaske kai ne?”.
Baiyi magana ba, sai mintsinin da ya sakar min a gefen cinyata babu shiri na ɗan gantsare tare da faɗin, “Ouch!!”. Ina ɗan kai masa duka a bayansa. Ɗagoni yay yana kallona cikin ido, kafin ya motsa lips ɗinsa a hankali ya ce, “Kin yarda ido biyu ne?”.
Murmushi na sakar masa nima tare da faɗawa jikinsa na ƙanƙamesa. Cikin rikicewa nake jera masa tambayoyi. “Yaushe ka dawo? Ina ka shige ne? Ina Ummie na? Aunty Falaq ta haihu ne? Anga Paah? Ina Fahad da Hafizzullah ban gansu ba.......”
“Shiiii!!!. Wanne zan amsa a'a ciki to? Ammien unborn”.
Ya faɗa cikin kunnena da raɗa. Ajiyar zuciya na sauke tare da ɗagowa ina kallonsa. Idanuna cike da ƙwalla na ce, “Please My Lion duka ka amsa min, waye kuma Ammien Unborn ɗin?”.
Nunani yay da yatsa.
Sai naji gabana ya ɗan faɗi, muryata har rawa take na ce, “Ban gane ba ALLAH Yaya”.
Ido sosai ya zuba min kawai yana kallona. A hankali na fara ganin ƙyalli a cikin idanunsa alamar hawaye na taruwa. Sai kuma ya ɗan duƙo ya sumbaci idanuna dake kallonsa da hancina da baki na. Kafin ya riko hannuna shima ya sumbata. Murya can ƙasan maƙoshi lips ɗinsa na motsawa a hankali ya furta, “Samrh! ALLAH ya mana ƙyauta da abinda kuɗi ko ƙarfin mulki basa badawa. Naso yin kuskuren wasa da rayuwar ƙyautar da UBANGIJI yay mana. Am sorr...”
Da sauri na kai hannu na rufe masa bakin ina girgiza masa kai. Hawaye na silalo min na ce, “Baka min laifin komai ba Yaya. Dan ALLAH karka bani wani haƙuri. Komai daka gani a rayuwar bawa ƙaddararsa ce tazo da hakan. Ina tayaka murnar samun ƙaruwa”. Na ƙare maganar da shigewa jikinsa sosai na ɓoye fuskata dan kunyarsa naji tana sake shigata mai tsananin. Ga wani irin farin ciki na matuƙar ratsani wai ni Samraah ke ɗauke da ciki irin na haihuwa. Nima zan zama Mama”.
Sake ƙanƙameni yay sosai a jikinsa shima kamar zai maidamu abu ɗaya cikin kunnena ya furta, “Nima ina tayaki murnar samun ƙaruwa Aljannata”.
Dariyar na sake ƙyaƙylƙyalewa da shi ina sake ɓoye kaina a cikin jikinsa. Sosai naji motsin fitar sautin nashi murmushin shima a cikin ƙirjinsa. Mun jima a haka kafin ya ɗagoni ya sumbaci lips ɗina. Tare da nuna min nashi alamar nima nayi masa. Kafaɗa na maƙe masa alamar naƙi ɗin.
Fuska ya ɗan yamutse yana wani ɓata ta. Hakan ya sani kai yatsana manunuya na ɗalli small pinkish lips ɗinsa ina murguɗa baki da faɗin, “Ɗan kurma kawai”.
Ƙaramin murmushi ya ɗan saki da alamunsa kawai na gani ya ɗauke kansa. Batare da yayi maganar ba dai ya miƙe dani a haka ya nufi ƙofar fita. Mamakine ya kamani, da sauri na ce, “Yaya bafa a sallaman ba. Ina zaka je da ni”.
“Saidawa”.
Ya faɗa a taƙaice yana ficewar dani. Dole sai nice na lumshe idanuna tare da ɓoye

Please Login or Register in order to submit comment