Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sannan ya ɗauke kansa tare da gaisheta a fisge. Dan wannan ɗabi'ar Tata ta shigama mutane ba sallama na ƙona masa zuciya. Ya tabbatar idan bata fasa ba wataran sai taga abinda zai dameta wlhy. Yanda yay mata ɗin yasa ranta sake ɓaci, a take ta balbalesa da masifa akan laifin Maash kamar wani ɗanta ba ƙani ba. Ƙanin ma fa sako bawai na can-can nesa ba. Banda ma ta raina masa wayo a yanzu duk wanda ya kalleta ta kallesa baza'a taɓa cewa ta girmesan ba saboda shi namiji ne. Amma bai sani ba ko wannan linda-lindar jikin nata ne ke kwasarta tana ganinta shirum kamar matar sarkin yarabawa. Karan farko da ya fara manna mata hauka har taci jarabarta ta tsire bai tanka mata ba. Sai Hajiya ƙarama ce data fito da shirin fita asibiti ta ke bata baki. Bata kulata ba, hakan kuma ba sabon abu bane ba. Dan tun tana ma amarya basa shiri, duk da kuwa da farko farkon auren babu wata matsala saboda Hajiya Mammah na murna amma Ummie kishiya, kasancewar a lokacin akoda yaushe cikin saka ran zata warke suke. Sai dai a dalilin wani abu da su suka san tsakaninsu ya saka su ƴar walle-walle. Duk da kuwa ita Hajiya ƙarama taƙi nuna akwai matsala kowa laifin Hajiya Mammah kawai take gani da tunanin itace tama Hajiya Ƙaramar koma minene.
Rai ɓace Paah ya tashi ya bar mata falon. Ai ko sai ta hayayyaƙo masa harda shan gabansa tana daka masa tsawa. Ai ko shima ya daka matan cikin matuƙar fusata da hargagin da bai taɓa koda kwatanta mata ba ya nunata da yatsa tare da faɗin, “Addah! Leave me alone!. Get out of my side kafin na nuna miki ainahin true color ɗina wlhy. Kin isheni! Kin isheni!!. Haba wai ƴaƴana sune kaɗai ƴaƴa a family ɗin nan da kullum dai sai ance sunyi-sunyi. Musamman Muhammad bashi da wani filin shaƙar iska mai daɗi a gidan nan. Kullum cikin wahalar nema da kai kawo yake na ganin ya ƙyautata rayuwarmu da ingantata amma bazamu masa addu'a ba mu gode masa sai zaman lissafa kurakuransa. Kuskuren ma daba kuskure ba dai Muhammad. Yanzu ki duba Fahad tunda ya iso gidan nan wlhy ko kallo ban ishesa ba. Yama nuna gaba ɗaya bai san dani a cikin gidan nan ba. Shekara nawa ban gansa ba, ko naje ƙasar da yake guduwa yake baya barin ma mu haɗu sam. Shi kansa Muhammad idan bai so ba sai ya shafe wata biyu ban gansa ba kuma yana cikin ƙasar koma cikin gidan. Miyyasa wai bazaku tausaya min bane ku barni da damuwata. Shin da halin da uwar ƴaƴana data zama sanadin rufin asirina da ku zan ji ko da fitinarki Addah?!!. Ke wane kalar iskanci ne yaranki basayi kin ma taɓa nuna kin san suna yi ɗin. Please! Mind your business and leave me alone!!!!”.
Ya wuce abinsa fuuu cikin bedroom. Ba Hajiya Mammah da Paah yayima ihun ba. Hatta da Hajiya ƙarama sumar tsaye tayi. Dan abune da bai taɓa kwatanta faruwa ba a gidan koda a mafarki. Mu'azz na ɗaga murya ma wani. Kai kai koda ƴan aiki bata taɓa ji ba. Shi mutum ne mai shiru-shiru, dan zata iya cewa ma rashin magana kamar a wajensa Awwab ya gado shi. Sannan shima wani lokacin akwai miskilanci, dan in bai gadama ba sukan iya gaɓar sati biyar ita da shi wlhy bata ishesa koda kwallo ba. Sai dai ita ta gaji ta sauka. Amma jiba yau ya koma kamar wani mafaraucin zaki..
Ido suka haɗa da Hajiya Mammah data suma a tsayen itama. Sai kawai ta wani balla mata uwar harara tai gaba abinta.. sai kawai murmushi ya suɓucema Hajiya ƙaramar batare data shirya ba. Wayar dake hannunta ta kalla, sai kuma ta kwashe da dariya, tare da shiga WhatsApp ta turama Baba prof recoding ɗin da tayi na duk abinda ya faru. Tana turawa ta kashe wayar gaba ɗaya ta koma cikin ɗaki dan ga fasa fita aiki kuma. Sai taga ƙarshen wasan........✍️


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚-𝒇𝒊𝒗𝒆_


.......Koda kiran salla ya farkar da mu da asuba nayi mamaki. Sai daga baya na fahimci daga wayarsa ne ya saita hakan. Tashi yay ya shiga bayi. Bayan ya fito ya kabbara salla nima sai na shiga domin gyara jikina na kuma yo wanka. Sai dai ƙasan raina ina cikin damuwar kayan sakawa. Koda na fito sai da na gyara gadon sannan na zauna. Wayarsa na ɗauka na duba naga ko akwai app na Alkur'ani. Nayi sa'ar samu kuwa, dan haka nayi zaman yin karatu, shi kuma da alama azkar yake yi dan yana dai zaune a inda yay sallar idanunsa a lumshe ya jingina bayansa da kujerar wajen. Mun jima a hakan har sai da gari yay haske sosai ya miƙe, nima sai na ajiye wayar batare dana kallesa ba kaina a ƙasa na gaishesa.
“Kin tashi lafiya?”.
Ya amsa min a taƙaice. Numfashi na ɗan sauke a hankali ni ma nace masa, “Alhamdullah”. Fita yay, ni kuma na ɗan sauke ajiyar zuciya. Ina a wajen zaune babu jimawa sai gashi ya dawo riƙe da wata ƴar ƙaramar bag mai shegen ƙyau. Kusa da ni ya ajiye batare da yayi magana ba ya wuce bathroom. Da kallo kawai na bisa har sai da ya shiga na ɗauka jakar na buɗe. Abinda ko nayi tunanin ganin ne wato kaya. Har cikin raina naji sanyi, dan haka na miƙe a gurguje na shirya cikin doguwar rigan mai ƙyau sosai. Yana fitowa ɗaure da towel kallo ɗaya na masa na ɗauke kaina, har ya kammala shiryawa ban sake maimaitawa ba. Sai da yazo har inda nake ya kama hannuna sannan na ɗago na kallesa. Da ido yay min nunin na tashi, ban musa ba na miƙe, sai dai a raina ina mamakinsa. Gurin jiya muka fito, ganin da nai masa na yau sai naji ya sake ƙayatar da ni. Gamu a gaɓar ruwa yanzu kam al'amarin zabbirgewa da ƙayatarwa, sai dai bata inda muka baro bane nan ɗin ma babu kowa shiru sai kukan tsuntsaye. Bamma san na saki murmushi ba. Ganin yana kallona nayi ƙoƙarin ɗauke kaina ina gimtse abina. Nima gwara ai na koya irin halin nashi Aita zaman kuramen kawai. Ƙayataccen breakfast ɗin da aka shirya mana mukai zaman ci. Koma nace naci, dan shikam ma tsakurar komai yake kamar abin dole. Na fahimci sam baya son abinci, ya dai fi ganewa kayan ƙwalam ɗin nan da maƙulashe...
Ana kiran wayarsa ya tashi a wajen, can ya koma ya tsaya. Ban tsaya jiransa ba na ƙarasa cin abincin na tashi. Ciki na koma ban jima ba na dawo. Na samu ya gama wayar, ma'aikatan jirgin ma na tattare kwanikan da mukaci abincin. Kallona naga yayi kamar mai nazari, sai kuma ya ɗauke kansa da maidawa kan wayarsa dage vibration dan shi sam baka jin ƙara a duk wayoyinsa.
“A ƙaraso da su”.
Kawai yace yana mai yanke wayar. Mamaki ne ya kamani, na kalla gabas da yamma kudu da arewa naga dai a tsakiyar jajeji muke sai ruwa. To ta'ina ma wani zai samu damar zuwa nan ya same mu. Bari dai naga ikon ALLAH. Aiko na gani, dan ba'a cika minti biyu ba sai ga ma'aikacin jirgin ya shigo bayansa da mutane guda uku. Ɗaya babban mutum ne mai cikar kamala da mutumtaka. Ni sai ma naga kamar nasan fuskar. Sai matashin saurayi da bazai wuce sa'an Hayat ba, shi kansa saurayin kamanninsa da Bahijja sosai ya mugun jan hankakina. Sai dai na cije kawai na kame kaina, sai Hayatu dake biye da su. Araina nace (bindin Maash kenan). Ganin Maash ɗin ya miƙe cike da girmamawa yana ma dattijon barka da zuwa da kiransa da Abbah yasa nima suna zama na gaishesa cikin girmamawa kaina a ƙasa. Sosai yake murmushi, kafin cikin jinjina kai ya ce, “Masha ALLAH, abu yayi ƙyau Muhammad Awwab. ALLAH kaine abin godiya, ALLAH ya ƙarama wannan aure albarka”.
A mamakina murmushi naga yayi yana ɗan rissinar da kai alamar jin nauyi, nace (tofa, dama akwai wanda Maash kejin kunya a duniya ashe). Gaisuwar da saurayin nan ya mun cike da girmamawa ta katse min tunani na. Na amsa masa shima ina ɗan murmushi. Muka kuma gaisa da Hayatu na tambayesa aunty Falaq yace tana lafiya.
“Samrh!”.
“Na'am”.
Na ɗago ina amsawa da ɗan kallonsa. Inda dattijon nan yake ya ɗan kalla, tare da sake maido idanunsa a kaina ya ce, “Wannan shine Malamina kuma kamar Abbana. Shiyya fara koyar da ni ilimin addini kamar yanda ya koyar da kakana mahaifin Ummie kenan da ALLAH yayma rasuwa tare da Baba. Shine kuma ya amsar min walliccin aurenki. Nasan dan da wahala ace baki san wannan fuskar ba. Dan Sheikh Muhammad bin Khalipha Al-Hussain ba Nigeria ba a Africa ma sananne ne”.
(Haba no wander nifa nace nasan fuskar nan) a zahiri kuma sai na jin jina kaina da sake rissinawa na ce, “Sannu da zuwa Abba. ALLAH ya ƙara lafiya da nisan kwana masu albarka”.
“Amin ya rabbi ɗiyata. ALLAH yay miki albarka. ALLAH kuma ya jiƙan mahaifinki Abdul-wahab da rahama. Mutumin kirki mai gaskiya da riƙon amana. Mai sadaukarwa. Ina fata da addu'ar ALLAH ya gadar da ƙyawawan halayensa ga ku zuri'arsa. Dan masu iya magana kance TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE. Nayima mahaifinki ƙyaƙyƙyawan sani gaskiya. Har takai ina jin kunyarku matsayin zuri'ar daya tafi ya bari da ya kasance bamu taɓa bibiya ba har sai a gaɓar da UBANGIJI ya zartar da ikonsa. Amma tabbas nasha yin hasashe a kanki a duk lokacin dana ganki a tv. Saboda iyalan gidana na bin program ɗin da kike gabatarwa. Tun ina faɗa da yawan kallon tashar har dai na nutsu nima naga abinda suke kallon a wata rana. Amfanin shirin da hikimar iya zance da ALLAH ya baki yaja hankalina matuƙa. Sai kuma a raina nake jin kamar na taɓa saninki amma a ina shine na manta. Har dai randa Muhammad ya kirani da bayani akan rikicin aurenki da hukuncin kawunki. Kasancewar yana faɗin min wadda yay hira da ita a Alheri tv yasa na gano kece. Abinda yay matuƙar sake ɗaukar hankalina kuma hoton da ya tura min na ɗan uwanki dake tsananin kama da mahaifinku, kema ashe jininsa nake gani a jikinki shiyyasa nake ganin kamar na sanki. Dan haka na buƙaci yazo ya sameni. Mun tattauna sosai akan abinda bamu tabbatar ba, a take nan ya saka aka masa bincike aka kuma tabbatar mana ke ɗin jinin Abdul-wahab ce. Madalla da ƙyaƙyƙyawan tsiron alkairi. ALLAH ya gafartama Abdul-wahab Gwarzo”.
Sosai nake kuka. Yayinda Malam ya cigaba da zabgama Baba addu'a har ma da kakan Maash ɗin. Maash na amsawa da Amin, dan Hayatu da saurayin nan suna can gefe sun bamu wuri. Nima dai ina amsawar sai dai kuka yaci ƙarfina. A hankali naji saukar hannunsa saman nawa kasancewar muna zaune ne a kusa da juna. Na kuma ɗan dafe kujera da hannun, ina sharar hawaye da ɗayan. Sosai ya runtse hannun cikin nashi tare da ɗan murzawa alamar lallashi. Sai kuma ya zato tissue a cikin kwalinsa dake saman Centre table ɗin kujerun wajen ya miƙa min. Ban musa masa ba na amsa. Hawayen na share, sai kuma ya miƙa min ruwa. Nan ɗin ma amsa nayi na sha kaɗan na ajiye. Sai da na ɗan samu nutsuwa kafin Malam ya cigaba da faɗin, “Samraah kinyi ƙoƙarin, ALLAH ya saka miki da alkairinsa. Mijinki yana min duk bayani akan kula da mahaifiyarsa. Tare da cigaban da ake samu yanzu sosai. Waɗan nan halayyar sune halayen mace ta gari. Sune irin halayen da kowane namiji zai so samu ga matarsa koda kuwa akwai wani special abu da yafi so ga mace. Ki cigaba da yanda kika fara kar ki canja kinji. Kema in sha ALLAHU ALLAH zai kula dake. Ba kuma zai taɓa taɓar dake a ƙarƙashin ƙafafuwan ƙasƙantattu ba masu bijirema gaskiya”.
“In sha ALLAHU Abba Nagode sosai. ALLAH ya ƙara rahama da jin ƙai a gareka.”.
“Amin ya rabbi ɗiyata, tare dake da zuri'armu baki ɗaya. Akwai magunguna da nazo da shi da ruwan addu'a duk suna a motarku. Idan kun koma gida sai a cigaba da yimata amfani da su. Hatta kuma zaku iya sha da amfani da su ɗin ba komai bane, har a girki kina saka muku musamman ruwan addu'ar zaki iya abinci da shi. Sai kuma a ƙara dagewa da addu'a da sadaƙa. Kiyaye dokin ALLAH, kiyaye hakkokin mutane. Azkar, karatun Alkur'ani. In sha ALLAHU muna fatan nasara a wannan gaɓar. Sannan Bahijja ta sanar min dukkan abinda ya faru a ɗazun akan Fahad, shima kar ai wasa dan abinda ke jikinsa a yanzu yafi na ɗan uwansa ƙarfi sosai gaskiya, dolene zai fishi zafi da son ayima duk wacce za'ai. Jarabawa ce ALLAH ya bamu ikon cinye wa baki ɗaya”.
Sosai nayi mamakin jin sunan Bahijja a bakinsa. Amma dai na daure na amsa da “Amin ya rabbi. ALLAH ya tabbatar Abba. In sha ALLAHU shima komai zai tafi dai-dai”. Na faɗa fuskata cike da murmushi. Shima murmushin ya min tare da faɗin, “Kina mamakin nace Bahijja ko?”.
Kaina dake a ƙasa na jinjina ina murmushi. Shima sai ya sake murmusawa. Tare da nuna saurayin da suke tare da Hayatu. “Wancan yarona ne shima. Sunansa Hameed. Yayane ga Bahijja mamansu ɗaya. Mijinki shine ya kawo Bahijja gidan nan domin yimana wani aiki, kuma Alhamdullah ana cin nasara. Sai dai itama ban sanar mata ke ɗin matar Yayan nasu bace ba.”
Kasa daurewa nayi sai da na ɗago na kalla Maash da hankalinsa gaba ɗaya ke a kan wayarsa yana daƙila. Mamakin duniya ya kasheni, amma sai bance komai ba na sake maida hankalina kan malam da fuskarsa ke a ƙawance da Murmushi. Ya ce, “Karki damu, a hankali zaki fahimci komai. Dan gidan nan naku sai mijin naki ne ya iya musu ai. ALLAH dai ya shiryar camu”.
“Amin” na amsa masa a hankali, ina sake mamakin mutumin nan. Tabbas na yarda shi ɗin yafi Aljani taƙadaranci kamar yanda Hayatu ya taɓa faɗa min...

Daga haka suka cigaba da tattaunawa da Maash, a tattaunawar tasu ne na fahimci shima Hameed ɗin an kawosa ne yin wani aiki a asibitin da Hajiya ƙarama ke aiki. Abin ya bani mamaki, sai dai ban iya saka musu baki ba tunda zancensu ne. Amma wai abu dana taɓa ji a asibitin nan sanda nake jiyya sai Sosai wannan zama ya jamu lokaci mai tsayi, dan sallar Azhar ce ta tashemu........✍️


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚-𝒔𝒊𝒙_


*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._

*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram_*

I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_WhatsApp_*
https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG


https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5


......Malam shine ya ja musu sallar azhar a cikin jirgin. Maash da malam ɗin sun sake sabon zama da ga shi sai malam ɗin daya jasu har zuwa la'asar, kai da kaga zaman zaka san abu mai muhimmanci suke tattaunawa, nan ma ya jagorancesu sallar la'asar sannan suka tafi. Ni lokacin ma ina ɗaki kwance ya kirani mukai sallama. Bayan tafiyarsu na zata muma zamu wuce sai naga wasa farin girki. Dan kuwa zama daram mai naƙuda ta samu katifa. Haka ina ji ina gani muka sake kwana a cikin jirgin nan dake ta faman shawagi kawai a cikin ruwa. Daren ranar ɗin ma dai bai ƙyaleni ba nasha jagwalgwala har sai da nayi laushi a hannunsa. Kai jama'a mutum ina ma prioud ɗin ban tsira ba. Kamar yanda ya faɗa kuwa washe garin cikarmu kwana biyun gabanin magrib muka bar cikin jirgin. Sai kuma naji du kamar kar mu wuce. Dan rayuwa a cikin jirgin nan rayuwace mai tsayawa a zuciya da bazamu taɓa mantawa da ita ba da ga ni har shi. Ga wata shaƙuwa ta musamman data shiga tsakanina da shi. Duk da kuwa yana nan da halinsa da kuka sani na rashin son magana babu abinda ya canja. Wani lokacin ma idan na gaji da shirun nasa sai na ɗauka wayarsa naita game abina. Dan zuwa nai na dinga ɗakkosu a play store iri-iri. Wani lokacin ma ina a jikinsa zanta abina yana kallona. Kokuma yana aikinsa a computer ni kuma ina game ɗina ko kallon films tunda ga datan banza. Yo ta banza mana tunda shi koyaushe data ɗinsa a buɗe yake.
A motar da mukazo dai muka koma. Sai dai maimakon gida ma wani wajen yay dani. Ganin ƙaton companyn da muka zo ya sani tambayarsa ina ne nan. Bai bani amsa ba sai da ya gama shan ƙamshinsa ya ce, “Na Ummie ne. Shine ta fara ginawa”.
“Woow Masha ALLAH”. Na faɗa tare da cigaba da yaba haɗuwar companyn da girmansa. Har ciki muka shiga a office ɗin dana fahimci nashi ne. Dan babu kowa sai masu gadi a ciki da waje. Kujera ya nuna min shi kuma ya shiga bayi, koda ya fito ficewa yay da alama zaije massalaci. Ina jin ya kulleni ta baya. Ban damu ba na miƙe ina bin hotunan saman desk ɗinsa da kallo. Kusan biyar duk shi da Ummie ne da Paah da wani da aka rufema fuska da wani emoji kwalliya. Mamaki ya kamani na ɗan kware ɗaya sai naga fuskar Fahad. Murmushi kawai nayi tare da jin tausayinsu. Dan masifa ma ace a hoto ma basa son ganin juna. Duk inda fuskar Fahad take ya rufeta. Da ga shi sai Paah da Ummie sai wani ƙyaƙyƙyawan baturen dattijo dake tsananin kammani da Ummie da shi kansa Maash ɗin daya ɗan ɗebe wasu abubuwan da ƙyaƙyƙyawar mace baka. Tabbas wannan shine Ibrahim (Alonso) kenan, ita kuma macen Rabi'ah. A take naji ƙaunar dattijon ya shiga raina yayinda na shagala a kallon Rabi'ah, wlhy ji nake kamar na san fuskar nan. Addu'ar samun rahama na musu tare da mahaifina sannan na maida hotunan a yanda suke na koma na zauna inata son tuno a inda na san fuskar Mama Rabi'ah. Zamana baifi minti biyu ba ya dawo. Zama yay tare da ɗaukar wayarsa dake vibration tun ɗazun ya kai kunne.
“Office”.
Kawai ya faɗa yana mai yanke wayar. Ɗan juyowa yay ya kallan, sai kuma ya ɗauke kansa tare da nuna min wani ƙofa ya ce, “Jeki ciki”.
Kamar zanyi magana sai kuma na fasa. Mikewa nai na nufi inda ya nuna ɗin, a cikin raina ina mitar ALLAH ko'a jikin ƙofa ne sai na maƙe naga wanda zai shigo. Ai ko hakan nayi, ina maƙe a jikin ƙofar ina kallo da ido ɗaya ta ɗan wajen nan mai kamar camara. Saurayine matashi ya shigo, sai dai fuskarsa kusan a rufe take da hirami, sai gilashi daya rufe idanunsa tas ba'a iya ganin komai. Idan ka gansa saika ɗauka baida gaskiya. Cike da girmamawa ya rissina ya gaishesa. Ina kallo ya amsa masa da alamun jinjina kai. Sai kuma ya nuna masa kujera. Zama yayi, tare da yaye hiramin ya cire gilashin. Ban sanshi ba, bamma taɓa ganinsa ba. Oho su suka sani wannan kuma. Ganin bazan iya jin abinda zasu faɗa ba na ɗan buɗe ƙofar kaɗan. Dai-dai nan ko saurayin ya miƙa masa wani abu kamar yana faɗin,
“Alhamdullahi Sir, naci nasarar ganin fuskar ɗaya daga cikin masu zuwa gidan da ɓoyayyar fuska. Sai kuma ita Hajiya Nafisa kwana biyun nan tana yawan zuwa gidan gaskiya. Guy ɗin nan mai suna Commondo da muka bibiya kwanaki shima kwana biyu nan yana zuwa akai-akai gidan. Sauran baƙin kuma da suka ɗan zazzo duk akwai sunayensu da fuskokinsu anan zaka gani. A jiya tattaunawasu da commondo ya bada damar a bibiyar masa brothers ɗin wata yarinya da suke zargin tana anan cikin Mansion ɗinka kamar mai something suna Samraah. Wadda naji Hajiya Nafisa ma tazo da batunta. Sai ita mai ɓoyayyar fuska data bayyana itama tazo da batunta. Kamar dai itace ya bada umarnin a kashe a asibiti ranar.”
Shiru Maash ɗin bai ce komai ba. Har kusan mintuna biyar kafin ya buɗe baki da ƙyar ya furta, “Ya akai ka fito kai yanzu?”.
“Baya gida tun around 11am ya fita. Amma dai akwai abinda yake ƙullawa gaskiya, sai dai bai faɗi komai ba akan shirin dan an sanar masa kun fita a gida tun shekaran jiya, lokacin suna tare da ita matar nan yace zai yi wani abu amma itama yaƙi sanar mata, amma a randa kuka fitan aka sanar masa. Jiya ma bai yini a gidan ba, yau ma gashi kusan hakan”.
“Kai mi kake tunanin yana shiryawa?”. Ya faɗa a daƙile.
“Eh gaskiya bazan ce ba kai tsaye. Amma dai ina hasashen koma minene tabbas zai iya shafarka. Dan haka ma na saka abu a jikin driver ɗinsa. Idan har an dace bai farga ba ya cire to zamu iya ganin wani abu koda ba duka ba ta nan. Sai dai gaskiya Sir ya kamata ka ƙara ninka tsaro a mansion. Dan shirin nan na musamman ne kuma daɗaɗɗen shiri kamar yanda Jaga ya faɗa. Sannan har yanzu kowa ba abin yarda bane a gidan nan. Ita kanta yarinyar da suke magana na fahimci a al'amarin nata akwai lauje cikin naɗi, musamman yanda naga al'amarinta na ɗaga musu hankali matuƙa, dan a nasu bincike sun gane tana da aure, amma sun gagara binciko ainahin mijin nata. Shiyyasa nake ga muma kamar ya kamata mu binciko ita ɗin wacece kafin su su binciko”.
“No wannan ba aikinka bane. Yanzu abinda nake so da kai shine. Ka tabbatar Hameed ya samu karɓuwa a wajensa hundred percent ta yanda samun aiki a asibitin bazai masa wahala ba. Akwai yarinya mai suna...” ya ɗan yi shiru alamar tunani. “Oh na manta. Ka kira Bahijja zata faɗa maka. Ina son kama oganka bayani

Please Login or Register in order to submit comment