Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

har Auta da su Yaya Abbas da Nabel da shi banama zaton yazo gidan yana makaranta. Gara ma ita Mum ɗin bayan ɗaura aure sanda Yaya Musaddiq yazo ya fita dani ɗin nan zuwa falon baƙi na ganta ita da wasu ƙawayenta a tsaye sunata faman dariya da alama akwai abinda suke tattaunawa a tsakaninsu.

★★Bayan nayi sallar magrib kamar yanda Gwaggo ta faɗa aka haɗamin ruwa mai zafi da kayan turaren ƙamshi a ciki nayi, koda na fito da taimakon Gwaggo na kimtsa jikina. Ta kuma tsareni sai da naci abinci da wani nama na musamman mai romo a cikin kula. Naman yayi daɗi dan haka na saki jiki naci sosai, koda tace sai na cinyesa ma ban musaba na dage na cinye nasha romon. Hakan yasa cin abincin bai armashi ba garan sosai. Tun ina kallon agogo harna daina. Sai dai a raina inata mamaki, dan tara dai-dai ya kamata ace muna a wajen dinner. Amma gashi anan har taran yama wuce ba'a kaini gidan su Mansoor ba balle ai batun zuwa dinner. Bily kar kiga kamar na cika zumuɗi ne fa. Kawai dai bana son naga an saɓama Mansoor alƙawari ne, to amma yaya zanyi, sai sanda aka kaini. Matsalata kawai da babu waya a hannuna.
Muna nan zaune Gwaggo na ƙaramin nasiha kusan goma saura akace su Yaya Musaddiq sun dawo sai a fito da amarya ga motoci sun zo. Sai a lokacin kuma naji duk na rikice. Nanfa na saki musu kuka. Duk yanda akaso na miƙe naƙi nai hakan har sai da Kawu Musa da kansa ya shigo yana faɗa sannan. Kuka nake sosai har numfashina na shiɗewa. Amma babu wanda ya saurareni, sai ma gaban Mum da aka kaini na roƙi yafiyarta. Cikin taɓe baki tana wani fisge-fisge ta ce, “ALLAH ya yafe mana baki ɗaya sai aje aita haƙuri, dama ita rayuwa ai haka take babu tabbas...” ganin tana neman sakin layi Gwaggo ta kamani muka fito. Abba ma an sake kaini na masa sallama. Yaya Musaddiq kam ya rufe kansa a ɗaki yaƙi yarda. Nasan kuka yake, dan haka nima na ƙara ƙarfin nawa kukan ina tutturjewa, amma babu wanda ya saurareni sai dai wasu nata bani haƙuri wasu na tayani matsalar ƙwallar aka fita dani. A rikicen da nake yasa bamma san kala ko adadin motocin da suka zo ɗaukata ba. Ni dai kawai an sakani a motar da ƙamshin da take yaso sakamin razani a zuciya, sai dai kuma rashin ƙarfinsa sosai da ruɗanin da nake a ciki na rabuwa da ƴan uwana ya hanani bama abin muhimmanci. Gwaggo Gudidi da Inna Magajiya ne tare da ni, sai gaba Ruƙayya ce ta office ɗin mu data zame min kamar babbar ƙawa ita da ƙanwar mijin Aunty Zakiyya........✍️


_🤭Uhummm inji mai ciwon haƙori._



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒚_

_______________

_Koda kuɗinka sai da rabonka. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge mai kallonka. Albishirin ku ƴan kasuwa da masoya. Kuna ina? Ina kuka shiga? Maza ku garzayo kantin sauƙi da rahusar ingantattun kaya na kasarku dama ketarenta. Bari na kaiku, *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* ke muku sallama irin ta addinin musulunci da babban albishirin shiryawa tsaff domin kawo muku kayayyakin buƙatunku na yau da kullum. Tun daga kan irinsu, atamfa, lasses, shaddoji, materials, abayas, takalma, handbags na zamani, vails ƴan yayi. Hijjabai. Sarkoki da dangoginsu. Kayan shafe-shafen dana kwalliye fuska. Agoguna harma dasu eyeglasses na manyan mata. Kai kai Karfa na cikaku da zance, dan zaku iya ganin komai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* domin farin cikinku. Kayan yara harma dana maza ba mata kawai ba. Ba'a sayen ɗai-ɗai zamu tsaya ba harda sari ga mai buƙata zamu bada in sha ALLAHU kuma akan RAHUSA mai sauƙi da kaima zaka samu naka rabon. Zakuma mukai maka kaya a duk inda kake a *NIGERIA* in sha ALLAHU. Ƴan kasuwa masu sari da masu sayen ɗai-ɗai ku garzayo nan domin gani da ido in sha ALLAHU. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge masu kallonka sai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING*👇_


https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5

_______________

.......Har muka iso kuka nake sosai, haka dai aka fita dani kaina a lulluɓe. Ina jin mutane nata yaba gidan. Hakan baisa naji wani abu daban ba saboda nasan gidan Mansoor kam tabbas yayi ƙyau da tsari. Sannan babu laifi babbane. Da addu'a na shiga kamar yadda Gwaggo ta bani umarni. Dan motar da aka ɗakkoni ce kawai dama ta shigo har cikin gidan. Sauran duk a waje suka tsaya. A falo aka ajiyeni kamar yanda Inna Magajiya tace. Mutane suka ɗan shishshiga kitchen da inda ba'a rasa ba. Bedrooms dai a rufe suke duka biyu dake a gidan kamar yanda naji suna faɗa. A karan farko na ɗan ji mamaki, dan nasan bedrooms huɗu ne a gidan Mansoor. Amma dai banda tacewa, bayan mutane sun gama zazzagawa suka fita dan dare ya farayi za'a maidasu gida. Sai da kowa ya fita sannan Gwaggo ta kama hannuna ta kaini bedroom da naji tana faɗa bayan ta buɗe da makulli, anan ne na gane ashe keys ɗin na hannunta sune dai suka hana mutane shiga wai dan kar a ɓata tunda dare yayi babu damar zama a gyara min. A bakin gado ta zaunar dani, tana sake jaddada min kalmar haƙuri, haƙuri dai da duk abinda zan gani, dan shi aure ibada ne bawai wasan yara ko nanaye kamar yanda mu yaran yanzu muke tunani ba. Ni dai kuka kawai nake zabga mata. Tadai samu ta zame jikinta ta gudu ta barni. Kuka na sake fashewa da shi irin mai cin rai da zuciya ɗin nan, harna zame na kwanta a gadon batare dana sani ba na cigaba da kukana.
Tun ina darzar kuka da tunanin Mansoor zai iya shigowa har al'amarin ya fara bani tsoro. Dan gari yay wani irin shiru sai kukan karnuna amma babu Mansoor babu labarinsa. Kai komai ya fara canja min daga yanda nake tunani da hasashensa. Dan daga jiya zuwa yau komai da nake gani ba irin tsare-tsaren Mansoor ɗina bane. Komai yana zuwa min a banbancin abinda muka tsara. Mi hakan ke nufi, Mansoor ne ya canja komai a yanda na sanshi ko yaya al'amarin yake ne?. Banda mai bani amsar ko ɗaya daga cikin tambayoyi na. Dan haka na cigaba da kwanciya a wajen ga ciwon kai mai tsanani na ratsani, kafin ma wani dogon lokaci na fara rawar sanyi. Ina jin yanda wata iskar hadari ke tasowa da ƙarfin tsiya amma na kasa ko motsi. Haka na cigaba da kasancewa a wajen na tsawon lokacin da ban san adadi ba har barci yay awon gaba dani batare dana farga ba....

Hasken rana irin mai kashe idon nan ne ya addabi fuskata. Dole na buɗe idanuna da sukai min wani masifar nauyi saboda kukan da nasha. Ganin a inda nake nada banbanci da inda na saba ya tuna min da mike faruwa. Zumbur na miƙe zaune ƙirjina na luguden daka. Ɗakin na shiga bi da kallo, madaidaici ne ba wani ƙato ba can. Sai dai kayan sun masa ƙyau cas. Abu na farko dana fara lura da shi sam ba irin fentin gidan Mansoor bane ba, kuma bedroom da Mansoor ya nunan a matsayin nawa randa mukazo ƙatone sosai. Ƙirjina yay wata irin girgiza. Sai dai tunawa da banyi sallar asuba ba yasa na tattare komai zuwa gefe na miƙe. Ƙofar da na gani da nakema zaton bayi ne na nufa. Nan ma dai ba irin toilet ɗin gidan Mansoor bane. Kai ƙwalwar kaina fa na neman juyewa. Amma dai na sake ƙoƙarin dakewa nayi alwala na fito. Akwatin dana gani saman bed side drawer na buɗe, na samu hijjab kamar yanda nai fata, dan haka na nutsu domin gabatar da salla..
Ina idar da sallar na miƙe kamar zararriya, dan kaina gaba ɗaya a juye yake da komai. Fitowa nai gaba ɗaya daga bedroom ɗin. Ganin wani dake a kusa da shi yasa na buɗe na shiga nan. Gabana ya faɗi. Dan babu komai a ciki sai ƙatuwar katifa irin wadda ba'a sanyawa a gadon nan. Sai wani ɗan ƙaramin akwati mai shegen ƙyau. sai takalma haif cover suma dai masu ƙyau sosai, a saman katifar da agogo da waya kusa da shi, sai can gefe kaya ne da aka cire shadda honey color data ciza sosai. Ga wani ƙamshi na musamman dake tashi har ina jin kamar nasan ƙamshin, amma dai na hana zuciyata hasasowa. Fitowa nai ƙwaƙwalwata na sake birkicewa. Falo ne dake tsaka tsaki, shima dai yayi ƙyau da kayan da aka jera masa, saukar idanuna akan wanda ke zaune daga can cikin ɗaya a kujerun dining ya saka zuciyata wata irin girgizar da ya rage kaɗan ta biyo ta bakina ta fito. Karkarwa jikina ya shiga yi, irin wadda bamma san na cigaba da tafiya ba cikin matuƙar sassarfa. Har na iso gaban dining ɗin bai ɗago ba. Yanata danne-dannesa a laptop hankali kwance. Ga mug dake ta turiri alamar shayi ko coffee a ciki.
“Wanene kai? Miya kawoka nan? Ina ka kaimin mijina?”.
Tambayoyi uku a jere suka fito a bakina dake rawa. Kamar baima jini ba, ko nace bai san da zuwana wajen ba. Dan ko motsi baiyi ba balle ya ɗago ya kallan, aikinsa kawai yake hankali kwance cike da ƙwarewa.
A matuƙar harzuƙe hawaye masu zafi na rige-rigen sakko mini cikin daka tsawa na ce, “Da kai nake magana malam!!”.
Cak ya tsaya daga danna keyboard ɗin laptop ɗin da yake yi. Nasan kuma yanda nai tsawar ne da matuƙar ƙarfi ga jikina na girgizar tashin hankali da ɓacin rai. Na sake zabura zan masa wata tsawar ganin nan ma bai amsa min ba yay wata irin juyowar da ta saka ni yin tsalle a lokaci guda da zuciyata saboda tsabar kiɗima. Sai gani rijif a ƙasa wanwar.
“Ba'a min tsawa”.
Ya faɗa a dakensa cikin silent voice ɗin nan nasa na gadara babu alamar damuwa da halin da yaga na shiga kuma. Sai ma ɗauke kansa da yay ya sake maidawa ga screen ɗin laptop ɗin. Yaraf kake jina na ƙarasa zubewa ƙasa gaba ɗaya. A hankali sai kaina ya fara juyawa, yayinda lips ɗina ke wata masifaffen rawa ina nunasa da yatsana da shima ke rawar. Tun ma ina banbance tsakanin haske da duhu har hakan ya fara neman gagarata. Tuni na tafi luuu ƙasa gaba ɗaya alamar ina neman suma. Daga haka ban sake sanin mike faruwa ba sai farkawa nai na sake gani na a inda na faɗin yashe. Da ƙyar na iya miƙewa hannuna dafe da kaina dake faman juya min. Kai tsaye inda nasan yana zaune na kai idona. Wayam babu kowa daga shi har laptop ɗin nasa. Sai mug ɗin nan na shayi kawai ajiye. Falon na juya ina sake ƙarema kallo. Yanzu kam ni kaɗaice a cikinsa da alama, sai zuciyata ke ayyana min kodai mafarki ma nake yi ne? A gaskiya sai dai mafarkin kuwa, dan wanda idona ya ganarmin a gidan nan nafi fatan ya kasance a mafarkin ne. Kasa daurewa nai, cikin layin juyewar kai tamkar wata ƴar maye na nufi ƙofar da nake ƙyautata zaton hanyar fita ce. Da ƙyar na iya lalubar handle ɗinta na buɗe, cikin yanayin dishi-dishi na dinga bin harabar gidan da kallo, ba wata babba bace dan bata wuce ɗaukar motoci uku ba suma a ɗan takure. Motar da nake ƙyautata zaton an ɗakkoni a ciki jiya kawai ce a ajiye. Saukar idanuna akan buzun dake zaune a gate yana fifita wuta alamar shayi yake dafawa yasa ni jin ƙarin gwiwar nufar can. Sai dai ina kai rabin harabar wani mahaukacin farin kare mai kama da tumakin turawa a gashi ko nace zaki a ƙarfi da girma ya wani irin zaburowa kaina daga inda yake kwance a saman motar yana haushi na hauka ga harshensa waje. Daburcewa nai na rikice dan na tsani kare. Balle irin wannan mara ƙyan gani da suffa, sauƙinsa ɗaya daya kasance fari. Ganin yana gab da iskoni na ƙwalla ƙara ina durƙushewa a wajen na ƙanƙame jikina dake rawar mazari.
“Laalah!”.
Aka faɗa a ɗan tsawace, sai dai hakan bai hana fitar muryar tasa acan ƙasan maƙoshi ba. Sannan karen ya tsaya cak bai ƙaraso inda nake ba. Sai kallonsa da yay yayi haushi sau biyu yana kallona kamar mai son masa ishara dani. Da alama ya fahimci mi karen ke nufi, dan a daƙile ya sake faɗi, “leave here”.
Abin mamaki tinƙas-tinƙas karen nan yabar inda nake ya koma saman motar daya taso yay kwanciyarsa kamar bashi ba. Sai lokacin na samu damar sake fashewa da kuma. Ganin ya juya abinsa zai koma inda ya fito na miƙe a zabure nima. Kusan atare muka shigo falon. Batare dama nasan mi nakeyi ba a tsawace na furta, “Ina ka kaimin mijina? Mi kayima Mansoor ɗina? Miya kawoka gidan aurena? Yanzun ma kidnapping ɗina kayi?”.
Bai ko kallan ba ya cigaba da tafiyarsa zuwa bedroom ɗin nan mai katifa. Ai bamma san lokacin dana daka wani uban tsalle ba nabi bayansa nima. Dan amsoshin tambayoyina kawai nake buƙata. Dole kuma ya bani, inba haka ba kuwa zaiga tsagwaron tashin hankali, kuma a wannan karon saina tabbatar masa da kaidin mace, dan ko dare bazan sake kaiwa a gidan nan ba. Ina isa ƙofar ɗakin yana rufota bamm, handle ɗin na kama da rawar jiki na fara murɗawa da jijjiga ƙofar amma ko motsi batai ba alamar ya kulle ta ciki. Wani irin kuka mai tsuma zuciya na sake fashewa da shi ina cigaba da jijjiga ƙofar da bugata a haukace amma mutumin nan ko tari baiyi ba. Galabaita ta sakani silalewa jikin ƙofar zuwa ƙasa wasu zafafan hawaye na rige-rigen sakkomin da masifar gudu. Cikin jin karaya da sarewa na shiga furta, “Awwab why? Why Maash? Why zakamun haka a ranar da tafi kowacce rana muhimmanci a garemu. Mike shirin faruwa? Ina mijina Mansoor?!! Miyyasa ka sake satoni zuwa nan a ranar auren...” kuka ya sarƙeni na kasa cigaba da maganar✍️


🤔🤔🤔😞

Alhamdullah 🙏. Anan zamu dakata a book one na wannan littafi mai suna TSUTSAR NAMA. sai kuma ALLAH yasa muna da rabon kaiwa bayan salla.

★Tofa masu karatu yaya take ne?.

★Mike shirin faruwa?.

★Ina Mansoor ango?.

★Miya kawo Maash a madadinsa?

★Kidnapping Sam-G ya sake yi kamar yanda take tunani itama kokuwa yaya al'amarin yake?

★Waye yay kidnapping Sam-G a farko tunda Maash ya tabbatar mana bashi bane?.

★Waye Maash ya kashe ma wai?

★Wake amfani da sunan Samraah wajen amsar kuɗi maƙudai haka a wajen Maash? Tunda tace ba ita bace.

★Maash zai samu nasarar amsar videon a wajen Sam-G kuwa?

★Magana fa ake ta an kawo amarya gidan mijinta amma ango ya rikiɗa zuwa wani daban.

★Hhhhh masu karatu akwaifa gurmi. Gurmi gagarumi ma kuwa na musamman. Dan littafin nan ɗauke yake da nasa salon shima. Hargitsi da cakwakiyar dake cikinsa kuwa. Hhhhumm ba'a magana, dan bama mu fara komai ba sai a book 2 da zai zo bayan salla, kuma komai da kuke buƙata yana a cikinsa ne.

★Dan shi kansa Maash fa akwai wani ƙunsashen al'amari a tashi duniyar dako fara taɓota bamuyi ba.

★Kai kar dai na cikaku da surutu, ku shirya kawai tsaff zuwa bayan salla idan ALLAH ya kaimu da rai da lafiya domin samun duka wannan amsoshin a TSUTSAR NAMA BOOK 2 har ma da wanda baku sani ba.

★Ya rabbi ka karɓi ibadunmu, ka gafarta mana ka yafe mana kurakuran mu. Ƴar uwa! Ɗan uwa! Duk wanda naima ba dai-daiba ya gafarceni. Nima na yafema kowa. Kada ka bari ko ki bari ku zama cikin jerin mutanen da zan iya kaima UBANGIJINA kuka a kansu a acikin wannan watan mai tunkaromu. Wannan shawara ce. Dan nima bazanyi fatan nazama cikin wanda kuma zaku kai ƙarata wajen UBANGIJINA ba. Fatana kumin addu'ar fatan alkairi nima na muku tare da iyayenmu baki ɗaya.


Taku har kullum👎
BILKISU IBRAHIM MUSA
(Bilyn Abdull 💞)


(C)2024.


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒐𝒏𝒆_

_Assalamu alaikum masoya. Fatan alkairi a gareku tare da barka da salla. Ya rabbi ka amshi ibadunmu ka yafe mana kurakuran mu. Ka gafartama iyayenmu. Kafin komai dole na fara da tarin godiya a gareku musamman wanda suka sayi kayan salla a wajena. ALLAH yabar zuminci. Nagode sosai da yanda kuka nuna ƙarfafawa a gareni akan wannan kasuwanci. Ina sake albishir a gareku da in sha ALLAHU wasu kayanmu na gab da sauka musamman abayoyi da handbags na yara dana manya. Sai kowa ya ƙara zuba kuɗi a asusu 😂. Gamu mun dawo filin daga. ALLAH ya bamu ikon sauke nauyin juna mu daku, ALLAH ya haneku cin hakkinmu, muma ALLAH ya hanemu tauye hakkinku 🙏. Godiya ta musamman gareku baki ɗaya 😘😘😘🙏_.



.......Kuka nayi sosai a wajen. Dan har sai da kaina ya dinga sara min tamkar zai rabe gida biyu sannan na miƙe. Cikin layi irin na rashin ƙarfin jiki na koma ɗakin dana kwana. Handbag ɗina na ɗauka tare da hijjabin danai sallar asuba. Gudun haɗuwa da shegen karensa ya sakani bi ta kitchen duk da ban san takan gidan ba. Ta bayan na bi, hakan yasa har na zagayo inda gate yake banga karen ba. Zaram maigadi dake zaune yana jin waƙa ya miƙe. Bakinsa har rawa yake wajen gaidani. Ban amsa masa ba. Face cemasa “Buɗe min!” cikin kakkausar murya da tsawa.
Cikin daburcewa da wuru-wuru ya ce, “Amma Hajiya oga baice....”
“Wlhy idan baka buɗe min ba zan haɗa kai da ogan na danna muku zagi.” nai maganar ina fisgo sandarsa dake ajiye saman bench. “Zaka buɗe min ko sai na ɗora maka ita a saman kanka”.
“ALLAH ya huci zuciyarki Hajiya bara na buɗe”. Ya faɗa cikin rawar jiki yana nufar ƙaramar ƙofar. Key yasa ya buɗe, na watsa masa harara sannan na fice. Sai da na tabbatar na fita sannan na jefa masa sandarsa nai gaba. Dogon street ɗin nabi da kallo, mai ɗauke da lafiyayyen titi. Sam ban gane a wace anguwa bane ba. Dan haka hankalina ya tashi. Amma sam banji na sare ba na cigaba da tafiya sauri-sauri duk da rashin ƙarfin jiki da nake ji. Addu'a kawai nake ALLAH ya kawo mai napep. Kai koda mota ce zan nema taimako. Na ɗan yi nisa a tafiyar inayi ina waigen bayana dan ji nake kamar makirin zai iya biyoni. Jiri ne ke ɗibata sosai, dan kaina har yafara harmutsawa. Na ɗan tsaya ina mai dafe shi da ambaton sunan UBANGIJI. Dai-dai nan wata farar mota da har ta gittani ta dawo da baya.
“Baiwar ALLAH lafiya kuwa?”.
Muryar matashiyar mace ta daki kunnuwana. Hannuna na janye daga saman kaina. Cikin kallonta dishi-dishi a wahalce na furta, “Bakomai hajiya.”
“A ya zakice ba komai. Gashi kinayi kamar ma zaki faɗi”. Tai maganar tana fitowa a motar. Riƙoni tai dan jirin ne ya ɗeban zai zubar. Muryarta da damuwa sosai ta ce, “Kinga bara na sakaki a mota. Sai ki faɗamin ina zaki na kaiki”.
Ganin mace ce, kuma dama abinda nake buƙata kenan sai banyi musu ba. Da taimakonta na shiga motar. Ina zama na lumshe idanuna kaina na ƙara ƙarfin sarawa matuƙa. Koda ta shigo ta zauna tana tambayata ina zata kaini kasa bata amsa nayi, hakan yasa tai shiru ta bani ɗan lokaci da take tunanin na samu nutsuwa sannan ta sake tambayata. Da ƙyar na iya furta mata. “Yakasai”.
“Okay ba damuwa. Amma ina ganin mu fara zuwa clinic sannan. Dan kina cikin halin buƙatar taimako. Ni likitace”.
“Karki damu ki kaini gida kawai na gode”. Na faɗa a matuƙar wahale.
“Bazai yiwu ba, kiyi haƙuri na taimakeki dan ALLAH”.
(Dan ALLAH) data ambata yasa ban iya sake cemata komai ba. Daga haka ma na sulale ban sake fahimtar komai ba.



Hankali tashe maigadi ya nufi cikin gidan. A dai-dai ƙofar shiga falo ya samu Maash tsaye. Rikicewa yay, musamman da yay ma fuskarsa kallo ɗaya ya ganta a tsuke kamar hadarin gabas. Cike da tashin hankali ya zube ƙasa saman gwiyawunsa yana kwaso rantsuwa. “Wlhy tallahi ranka ya daɗe ba laifina bane ba. Tace idan ban buɗe mata ba zata fasamin kai ne.”
Shiru baice masa komai ba. Maigadi ya sake rikicewa yana jera rantsuwa da magiya duk a gurbi ɗaya. Sai da ya mula dan kansa a hankali ya furta, “Jeka kan aikinka”.
Duk da a sauƙaƙe yay furucin hankalin maigadi bai kwanta ba sam. Dan gani yake akwai abinda zai iya biyo baya. So yake ya cigaba da bada haƙuri har sai yasan ainahin gaskiyar abinda ke zuciyar mai-gidan nasa, sai dai kuma baiga muhallin yin hakan ba. Dan haka sum-sum ya juya bakin gate zuciyarsa na rawa matuƙa. Cikin taraddadi da ƙaulani ya koma, kusan mintuna goma da komawarsa yana zaune ya zabga tagumi akai horn. Firgigit ya tashi domin dubawa. Sai da ya buɗe ƙaramar ƙofa yaga mai horn ɗin sannan ya buɗe gate ɗin gaba ɗaya. Cikin girmamawa ya gaisar da Hayatu dake shigowa. Shi kuma ya ɗaga masa hannu yana ƙarasa shigewa cikin gidan. Yana fitowa a motar Laalah ya zaburo, inda yake yazo shi adole ya sanshi, hakan ya sakashi sakin murmushi da kai hannu ya shafa kansa yana faɗin, “Laalah how are you?”. Daga haka ya wuce zuwa cikin gidan.
Koda yay sallama a ƙofar sai da aka kwashe kusan minti ɗaya kafin a amsa masa, tare da bashi izinin shiga. Sarakin na zaune tamkar babu abinda ke damunsa. Hasalima dukan hankalinsa naga wayar hannunsa ne. Koda Hayatun ya shigo ma bai ɗago ba. A haka ya amsa masa gaisuwar da yay masa. Sanin hali yasa Hayatu bai damu ba ya cigaba da maganarsa. “Sir Alhamdullah yanzu haka tana tare da ita. Sai dai tace akwai matsala. Dan tana shiga motar ta sume mata, a yanzu haka ma suna clinic, sun kuma tabbatar da jininta yayi matsanancin hawa da take buƙatar taimakon gaggawa saboda gudun samun matsala a zuciyarta. Amma nadai basu damar yimata dukan abinda ya dace”.


Please Login or Register in order to submit comment