Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nayi sai da na kallesa. Sai kuma na shiga ƙyaƙyƙyafta idanu. Muryata na ɗan rawa na sake ɗagowa zanyi magana yay mun alamar zipping akan bakinsa tare da sake nuna min hanya. Kamar zan fasa kuka na shiga tafiya a hankali yana biye da ni har cikin bedroom. Koda muka shigan ma sake nuni yay min ba bathroom. Nan ma sum-sum na wuce dan babu alamar wasa a tattare da shi. Gaba ɗaya a tsorace nake, idan yace abinda ya aikata zai maimaita nama san mutuwa zanyi kawai.. Wankan nayi tare da ɗauro alwala amma sai na kasa fitowa duk da bathrobe na saka. Ina tsayen ina faman ƙullawa da kwancewa kawai ya shigo shikin bayin, idanu na waro sosai na mamaki, sai ya wani lumshe min idanunsa yana nufoni, da sauri naja da baya na manne da bango, na gama sadaƙarwa kaina zai zo sai kawai ya wuce ni. Ajiyar zuciya na sauke mai nauyi tare da fita a hanzarce cike da sassarfa. Na ji daɗin ganin kayan barci daya ajiye min wando da riga masu kauri, ɗauka nayi na saka a gurguje, tare da ɗaukar mayafina na yafa. Har na kammala abinda zanyi dan ya ɗan jima a cikin bayin sai kuma gashi ya fito sanye da bathrobe fara tas shima. Idanu muka haɗa, nai saurin ɗauke kaina ina sake ɓata fuska. Shima sai yay wucewarsa kamar bai ganni ba.

Ya jima a cikin closet kafin ya fito nan ma, ina kwance kan sofa ina game da wayarsa daya ajiye a Centre table sai gashi ya fito shima cikin kayan barci sky blue da suka masa ƙyau sosai. Batare da ya kallan ba yace, “Muje”. Wani ɗan karan daɗi ne ya kamani, cike da zumuɗi na bisa dan a zatona ya barni naje can ɗin na kwana. Bare ma dana ganni a sashen Ummie ta hanyar da ban taɓa sanin yana da ita ba. Mun sami Ummie har tayi barci. Zama yay yana mata addu'a, ganin haka nima sai na zauna ina mata addu'ar. Tsahon mintuna goma sha muna a ɗakin ya fara riƙe kansa. Muƙewa yay a hankali tare da riƙo hannuna ya ce, “Lets go”. Tsoro naji yanda naga ya riƙe kan, dan haka banyi musu ba na bisa. Sai da naga zamu koma sashensa nai ƙoƙarin yin magana amma ya hanani hakan. Muna shigowa a bakin gado ya kai zaune, yana sake dafe kan nasa da hannu bibbiyu.

Tsoro ne ya kamani da tausayinsa, har bamma san naje gabansa na durƙusa ba ta tsakanin ƙafafunsa na dafa gwiwarsa ɗaya, ɗayan hannun kuma na kaisa saman nasa hannun daya dafe kai. A hankali na janye nasan muryata a raunane na ce, “Ya Awwab miya faru? Baka da lafiya ne?”.

Shiru kamar bazai kulani ba, sai kuma ya ɗago shanyayun idanunsa da launinsu ya sauya zuwa golden yana kallona. Cikin motsa lips ɗinsa kamar baya so ya furta, “My head”.

“Ciwo yake?”.

Idanunsa ya lunshe min alamar eh. Cikin damuwa nace, “Na maka kamu?”. Nan ma kan kawai ya jinjina min yana maida idanunsa ya rufe. Miƙewa nayi sosai dan na fara gajiya da durƙuson, hannunsa na janye, na ɗaura nawa a wajen na fara masa addu'a. Inayi ina kamun da tofa masa addu'ar. Har na kammala ina faɗin, “ALLAH ya ƙara lafiya”. Ya amsa min da amin akan lips ɗinsa, ƙoƙarin barin gaban nasa nake naji saukar hannunsa a saman ƙuguna. Da sauri na kallesa tsigar jikina na tashi.

“Ina zaki?”.

A raunane na ce, “Saman sofa”.

“Gadon fa?”.

“Amma....”.

“Shiiiiii!!!”.

Ya katseni tun kafin na ƙarasa faɗa. Tare da nuna min saman gadon babu wasa sam akan fuskarsa. Duk da shi dai ba banbance farin cikinsa ko damuwarsa kake dama a saman fuskar ba. Tunda akoda yaushe babu alamar fara'a a tare da shi. Sai idan shine ya so ya saki wannan munafukin murmushin nasa iya lips. Jikina har rawa yake wajen hawa gado. Idanuna kam tuni sun tara ƙwalla. Haka na kwanta ƙarshe gadon na wani naɗe jikina tamkar ƴar mage. Shiru banji ya hawo ba bai kuma tashi ba. Kaɗan na ɗan buɗe ido na kallesa. Yana zaunen har yanzu dafe da kan nasa alamar bai gama sauka ba. Jinai tausayinsa ya ƙara kamani, bamma san cikin raunin murya na furta, “Ko dai yunwa ce? Nifa duk yau banga kaci abinci ba”. Shiru baida alamar amsa min. Baima motsa a yanda yake ba har na gaji na maida idanuna na rufe. Mintuna baifi biyu ba ya hauro saman gadon, tuni zuciyata ya fara mutsu-mutsu, barema da ya kashe wutar ɗakin ya bar lamp ɗin side ɗinsa kawai itama ya maidata can ƙasa ba wani hasken kirki kasancewar muna a cikin net ne da yayma gadon rumfa gaba ɗaya. Jira kawai nake naji yamin irin na waccan ranar amma sai naji shiru baima ko matso inda nake ba. A hankali a hankali na fara samun nutsuwa har barci ya ɗan fara figata. Sai can na saki jikina sosai sannan na jisa a bayana. A ɗan firgice na farka, sai da ya riga har ya birkitoni na koma jikinsa gaba ɗayana ya rungumeni. Kasa daurewa nayi, sai da nayi magana cikin rawar murya irin ta wanda ke cikin tsoro.

“Yaya wlhy akwai ciwo”.

“Nace zanyi wani abu ne”.

Ya faɗa cikin kunnena da wata irin muryar da sai da tsigar jikina ta tashi. Ƙam na runtse idanuna ban sake cewa komai ba. Shiru har kusan mintuna biyu muna a haka kafin a hankali ya dai-daita fuskata da tashi, goshinsa a saman nawa hakama hancinsa sai lips ɗinmu sai dai su ba'a haɗe ba. Duk da a cikin duhu-duhu muke yanda idanuna ke a rufe shima nasa a rufen suke. Cikin wani irin soft and low voice ya furta, “Yanzu dai so kike ayi wani abu ko?”.

Da sauri na shiga girgiza masa kaina hawayen da nake riƙewa na zubowa da gudu.

“To mi kike so?”.

“Barci”.

Na bashi amsa har ina taune lips ɗina jikina na tsuma.

“Ni kuma bana jin barci ya za'ayi?”.

A marairaice na ce, “Ka tashi kayi salla to ko karatun Alkur'ani”.

“Uhum-uhum. Ni matata nake buƙata”.

Har cikin tsakkiyar brain sai da naji saukar furucin. Muryata na matuƙar rawa na ce, “Ya Awwab wlhy akwai ciwo. Kuma doctor tace ba...bai...war...ke...b.....” Nama kasa ƙarasawa.

“Yanzu mi kike so ayi to?”.

Da sauri na sake maimaita, “Barci”.

“Kin tabbatar?”.

Kaina na shiga jinjina masa. Da sauri-sauri.

“Tom bari na saki barcin”.

Ya faɗa acan ƙasan maƙoshi. Kafinma nace wani abu naji saukar small lips ɗinsa kan nawa. Tun ina mutsu-mutsun ruɗewa da firgici har na nutsu luff, dan wani irin salo yake min mai shagaltar da gangar jiki, cikin ƙanƙanin lokaci na gama sallamawa gaba ɗaya na batare da ni kaina nama san minake ba. Ban tashi fahimtar kuskure na ba sai da aka ɗauki wani layi daban. Duk da a yanda yau yake bina a mugun nutse, cike da tattali da kulawa bamma san sanda na sakar masa kukan azaba ba jikina na matuƙar rawa.....

❤️★❤️★❤️

Tun a balcony ɗin take faman jera manya-manyan ashariya wa Maash. Koda ta afka bedroom ɗinta gaba ɗaya ta kasa haƙuri saboda yanda zuciyarta ke mata hanƙoro. Wai mi yaron nan ke shirin maidasu? Ƴan iska ko mi? Yanzu har Ummu-Hidaya ta haifi abinda zaifi ƙarfinsu kenan. Yarinyar da aka haifa a gabansu, balle shi karan kaɗa miya. Kai wlhy bazai yiwu ba. Dole ne ta ɓaro aikin da dolema ayita ta ƙare a gobe. Ina dalili Rubayya ta sakata aikata abinda ke neman juyewa da ita. Banda yaron nan ƙwallon ɗan iska ne ka haikema yarinya amma ka koma kana wani abubuwa irin ga matarka ɗin nan kayi first night ko. To wlhy daga daren yau zuwa gobe sai ta tada hankalin kowa na gidan nan sai dai anyita ta ƙare. Munafukai kowa yayi shiru da bakinsa irin komai ma bai faru ɗin nan ba. Waya ta jawo, ta shiga daddanawa. Number baba prof ta kira. Sai da ta kusa tsinkewa ya ɗauka cikin alamun wanda ya fara barci. Kuka ta fashe masa da shi a maimakon sallama. Cikin tashin hankali ya shiga tambayarta abinda ke faruwa?. Amma taƙi magana sai kuka. Sai da ya mata tsawa cikin tashin hankali kafin ta fara magana tana jan sheshsheka.

“Baba wace irin ƙazamar rayuwa kuma ke neman zuwa mana gidan nan. Mun shiga uku Awwab ya ɓalle. Baba kaga kuwa abinda na gani yanzun nan. Ya gama lalata wata gata can kwance a asibiti gashi can kuma yaja wata sashensa zai ƙara. Kuka yarinyar take tana roƙonsa amma bai barta ba. Har magana nayi masa amma ya hauni da zagi, wai bamun damesa yay aure ba, to haka zaita haye ƴaƴan mutane har ƴaƴanmu ma su jira zuwansa. Mu kammu idan bamu kama kammu a gidan nan ba sai layi ya biyo ta kanmu. Baba wlhy Awwab ya gama iskancewa, yaro ya tambaɗe ya lalace, kai ko jinin turawa na yawo a jikinsa. In baiyi bama ai bai cika jikan sifanawa ba (Spain 😂). Wayyo Baba mun shiga ashirin watan zubewar mutuncinmu yazo a duniya. Ƙilama a wannan karon har bbc saita bugamu...”

A rikice Baba yay mata tsawa, dan gaba ɗaya ta gama ruɗar da shi yama kasa yin tunanin daya dace. Ƙitt ta yanke kiran tare da kashe wayar gaba ɗaya. Dariya ta sanya cikin yanayin basanci ta ce, “A'a badai nice ba. Ai sai kaci baban uwarka Alonso Awwab. Gobe-gobe sai ka zama mijin Azizat ɗina. Kwantar da hankalinki ƴar albarka kukanki na kusa sharesa, nima kuma burina ya kusa cika.” ta sake ƙyalƙyalewa da dariya.......✍️

Hummm munsha yajin aikin dole ko🥱😂

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 twenty six


.......Fita tayi a sashenta, kanta tsaye tai sashen Paah shima. Wani irin mahaukacin bugu ta dingama ƙofar tana kuka da ihun da sai da kusan kowa ya tashi. A masifar firgice Paah da Hajiya ƙarama suka fito. Ko bari su tambayi ma abinda ke faruwa batai ba ta hau rusar kuka da sanar musu kamar yanda ta sanar da Baba prof ta waya. Hankalin Paah da Hajiya ƙarama duk tashi yayi. Suka shiga salati da sallalami. Dai-dai nan sai ga kiran Baba prof ta wayar Uncle Abdullahi da suma bugun Hajiya Mammah ɗinne ya tashesu. Kururuwar da Hajiya Mammah keyi har yanzu ya sashi tsawatar musu kasancewar a hansfree Uncle Abdullahi ya saka wayar.

“Miyasa bazaku nutsu ba ne wai. Baku da hankali ne sai kowa ya fahimci abinda ke faruwa. Darene fa? Gida cike da ma'aikata. Idan abinda ke faruwa bai zama tonon sililin ba wannan shirmen naku da tatarako ai zai zama. Kowa ya wuce ya kwanta. In sha ALLAHU da safe zan shigo gidan zai ci ubansa ne ai”.

Kowa ya gamsu da bayaninsa, yayinda Hajiya Mammah ke kwasar dariya a zuciya. Paah kuwa jiri ma yake jin yana neman ɗibarsa. Sai da ya dafe bango dan tashin hankali. Ita kanta Hajiya Ƙarama zuciyarta sai mutsu-mutsu take a ƙirji. Ji take kamar tayi tsuntsuwa a sashen masu aiki dan ta tabbatar ita dai ba Samraah ɗinta yaron nan ya sake haikemawa ba. Sai dai babu damar yin hakan. Dole ma sai itace ta kama Paah suka koma ciki. Uncle Abdullahi da matarsa ma suka koma nasu sashe. Itama Hajiya Mammah ta juya tana dariyar ƙeta. Ranta fes wlhy dan gwara ayita ta ƙare.....

😂😂Hegiya Hajiya Mammah kin iya haɗa guri ko, to bari muga yaya wasan zai kaya🚴.

🌿❤️🌿❤️🌿

Ni a karan kaina ban san iya adadin kukan da naci ba. Dan gwara waccan ranar daga ƙarshe suma nayi, yau kuwa har ma fata nake ko zan suman na samu sassauci amma sumar taƙi zuwa. Azaba iya azaba da kwantata badai baki ba. Ban sani ba, ko hakan ya faru ne dalilin ina cikin tsoro da kuma ban gama farfaɗowa a waccan baƙar wahalarba oho. Duk da a yau komai yana yinsa gently ne ni banga wannan gentle ɗin ba sam. Kuka na gidan duniya na shashi har ina jin idanuna kansu sun min wani uban nauyi. Roƙo magiya harda cizonsa nayi amma bawan ALLAHn nan sai da ya kai inda yake buƙata. A Bathroom ma wani sabon kukan na sha, amma sam baiji tausayina ba sai da ya tabbatar ruwan zafin ya ratsani sosai yanda ya kamata sannan ya taimaka min na tsaftace jikina. Yanda ya ɗaukeni da kansa ya kai haka ya sake ɗakkoni ya maido saman gadon. Da ƙyar na amshi magani daya bani, ina gama sha ya kwantar dani, bamma san barcin wahala yay awan gaba dani ba. Dan tun ina jinsa sama-sama yana salla har nayi barcin ban san ya dawo saman gadon ya kwanta ba sai asuba....

★★

Yanda Maash bai bari sunyi wani barcin kirki ba a wannan daren haka mafi yawan iyayensa basu runtsa ba. Hajiya Mammah dai na sake ƙulla abinda zata zo da shi gobe idan ALLAH ya kaimu. Paah na cikin tashin hankali da damuwa tare da nadamar abinda yake aikatawa. Dan shi kawai zuciyarsa na bashi TSUTSAR NAMA CE TA ZAMA NAMA. Ɓarnar da yake aikatawa ce tai naso wa gudan jininsa. Shiyyasa masu iya magana ke cewa ƊAN GADO HAR YA ZARTA. A wannan gaɓar kam ya yarda. Dama ance zina na bibiyar jini, idan kayi da ƴar wani sai anyi da taka. To shi bashi da ɗiya mace, shine ALLAH ya jarabci ɗansa babba da wannan ta'asar da ƙila zata zama sanadin tashi fallasar shima. Harga ALLAH bai taɓa fyaɗe ma kowa ba, amma fa tun yana secondary school ya fara neman mata. Saboda irin rayuwar da suka tashi, rayuwar turai. Uwa babu kwaɓa uba ba tsanani. Dan Ummansu nada faɗa, amma gasu ƴaƴanta soyayyace ziryan take musu. Garama mahaifinsu, yakan ɗan yi faɗan idan yaga abubuwan sunyi yawa. Shi kansa bai san adadin matan dayay mu'amala da su ba a rayuwarsa. Tun ma yanayin mai aji har gashi ya koma mu'amala da mai aiki. Dan da Siyama kawai yake mu'amala a gidan, hasalima ya santa ne tun kan ta fara aikin, koma yace saboda shi ta dawo aiki gidan, dan tace suyi aure yace a'a, shine ta zagaya ta samu aiki a gidan sai kawai ganinta yayi. Ya shiga matuƙar shock a lokacin, amma da yake ƴar duniya ce sai da ta maida shi ruwa a kanta duk da kuwa shi in har ya mu'amulanci mace ya rabu da ita da wahala ya koma. Amma akan Siyama sai tarihin ya canja, dan ta rantse masa in har yay sanadin data bar gidan sai ta tona masa asiri, shiyyasa ma ya barta saboda ya fahimci yarinyar hatsabibiya ce kwarai da gaske. Amma yau sai gashi ɗansa nayin yanda yaso a cikin gida batare da kunya ko shakkar wani ba.

Ita ko Hajiya ƙarama tashin hankalinta kada ace Maash ya sake haikema ƴar gaban goshinta Samraah ne. Har bayi ta shiga ta gwada kiran Mama Balki sai kuma ta fasa, saboda tunawa da Mama Balki nada miji fa. Ita dai damuwarta kawai kada Maash ya sake taɓa mata yarinya.

Acan Uncle Abdullahi da matarsa sun shiga wasi-wasi. Dan su zukatansu sun fara nusar da su anya kuwa ba magauta bane suka asirce Maash ɗin ke wannan irin ta'asar babu kunya babu tsoron ALLAH a cikin gida kamar wata rayuwar kafurci. Kai da sakal fa. Yaron nan na buƙatar manyan malaman ruƙuya a kansa. Ita dai Maman Malika ma harta fara batun maida Malika Niger sai abubuwa sun dai-daita. Idan har abinda Hajiya Mammah ta faɗa Awwab ɗin ya faɗa to lallai basuga ta zama ba kuwa. Dole abar gidan da ƴammatan yaran nan guda huɗu zankaɗa-zankaɗa. (😂Yayanmu kaga idi. Kowa zai fara killace ɗansa saboda kai🌚, wannan aiki yayi tsamari🤣).

A ɓangaren Baba prof shima ba barcin daɗin ran yayi ba. Dan ya jima ma bai runtsa ba bayan ajiye wayar da yayi. Har gwada kiran wayar Maash yay amma ba'a ɗauka ba (😂ina zai ɗauka kuwa kandala ta kanainayesa, danginta na murna an kwace mana Yayanmu🥶). Haka ya dinga kai-kawo kamar mai Safa da marwa, sai da yaji ƙafafunsa na neman sagewa ya haƙura ya kwanta. Aiko asubar fari ya miƙe dan ko'a barcin nasa mafarkin Maash ɗin kawai yake yi ya haikema yarinyar mutane (kuji masifa🥱. Yo banda sa kai a uku kai tsoho ina ruwanka😝).

🩸🌟🩸🌟🩸

Saukar iska mai sanyi akan idanuna ya sani buɗesu a hankali dan sun min nauyi jingim saboda kukan dana sha. Ga barci da nake ji matuƙa dan sam ɗan wanda nayi bai wadaceni ba. Dishi-dishi nake ganin abinda ke gab da ni, cigaba da huramin iskar ya sani ƙarasa buɗe idanun sosai. Fes suka shige cikin nasa da sukai wani irin fitowa blue sosai, hakama golden ɗin daya ratsasu ya sake yin garai-garai tamkar zinare na ƙyalli a cikin glass. A hankali na ƙoƙarin sake maida nawa zan kulle saboda wani irin kunya ne ya baibayeni.

Cike da karsashi ya ɗaura soft hannunsa saman fuskata yana sake matso da tasa fuskar gab da tawa, har hancinmu na gogar juna. Da silent muryar nan tashi mai fita acan ƙasan maƙoshi kamar abin dole ya furta, “No! Baby. Open your eyes”.

Baki na taɓe kamar zanyi kuka. Cikin shagwaɓa da ban san ni kaina nayi ba na ce, “I'm not baby”.

Sake manne fuskarsa da tawa yayi, tare da sake maida muryarsa can ƙasa ya ce, “Yes you are not ni shaida ne”. Yanda yay maganar yana kai hannunsa saman jikina da sauri na saka nawa na ɗan buge nasan ina sake ɓata fuska zan saki kukan. Na kuma janye fuskata da ga jikin tasa na juya baya. Zafin da naji ya sani sakin ƴar ƙaramar ƙara. A hankali ya kwanto ta bayana duk da ma ya rufeni gaba ɗaya ƴar tsitt dani a jikin nasa. A cikin kunnena ya furta, “Still Pain?”.

Maimakon amsa kuka na sakar masa. Sautin murmushinsa naji a cikin kunnena, sai kuma ya saka hannunsa a saman fuskar tawa ya shafo hawayen. Hannuna nasa na ture nashin in ƙara ƙarfin kukan. Baice komai ba ya miƙe, har nayi tunanin ya barni ne sai naga ya zagayo ta gabana. Duvet ɗin da nake ciki ya yaye, tare da duƙowa ya ɗagani gaba ɗaya. Luff na kwanta a jikinsa tare da lumshe idanuna. Sai da muka shiga bayin na buɗe ganin yana ƙoƙarin cewa zai min wankan ma. Da sauri cikin shagwaɓa na ce, “Ni ka fita zan iya”.

“Kin tabbatar?”.

Ya faɗa cikin tsatstsareni da idanu. Kaina kawai na jinjina masa. Shima sai baice komai ba ya juya ya fita, yana gab da ƙarasa ficewar ya ce, “Ki tabbatar kin shiga ruwan nan”. Daga haka ya ficewarsa. Ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi, ni ba haushinsa nake ji ba. Tausayin kaina kawai nake ji, in dai haka zata cigaba da faruwa wlhy na kaɗe har ganye na. Dan al'amarin sam bashi da sauƙi. Ban cuci kaina ba na nutsu na gyara jikina yanda ya kamata, kamar kuma yanda Mama Balki ta koya min hakama Doctor. Sai kuma naji na ƙara jin nutsuwa. Wanka nayi na ɗauro alwala. Cikin sanɗa da jan ƙafa na fito. Naji daɗin ganin babu kowa a ɗakin, sai doguwar riga mara nauyi da hijjab dana samu a saman sofa. Ɗauka nayi cikin sauke ajiyar zuciya na saka dan har shida da wasu mintuna. Sallar asuba nayi, koda na idar duk yanda naso yin karatun Alqur'ani kasawa nai, anan inda nai sallar na ɓingire barci. Bamma san ya shigo ya ɗagani ya maida a saman gadon ba..........✍️

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
𝑷𝒂𝒈𝒆twenty- seven


.......Kamar yanda Baba prof yay alƙawari ƙarfe shida da kusan rabi a Maash Mansion ta masa. Sosai ma'aikatan gidan sukayi mamakin ganinsa da wannan uban safiya. A ƙasan rai kuma kowa na tunanin ko jikin Hajiya Babba ne ya sake motsawa. Dan in har ba ciwon Hajiya Babba ba baka ganin Baba prof ɗin a gidan sai dai wani babban dalili. Fitowarsa a mota dai-dai da fitowar Maash daga sashensa sanye cikin farare ɗin tas sports wear. Gefensa Laalah ne sai baƙin bluetooth daya manna a kunnesa ƙafarsa da sport shoes na kamfanin adidas. Kallon kallo aka tsaya tsakanin shi da Baba. Kafin shi Maash ɗin ya fara rissinar da nasa idon a yanayin nan nasa mai ban haushi. Inda Baban yake ya ƙarasa, ƙasa-ƙasa ya ce, “Good morning grandpa”.

Danne komai Baba prof yayi, cike da kulawa ya amsa masa da, “Morning dear, how was your night?”.

A takaice ya ce masa, “So good”.

“Hummm Masha ALLAH haka ake so ai. Amma inaga zaka bar fita Jogging ɗin nan kamar?”.

Cikin wani irin tsare kakan nasa da ido ya furta, “But why?”.

Haɗe fuska Baba prof yay dan karma ya masa gardama. Kai tsaye ya amsa masa da, “Nazo ne muyi magana mai muhimmanci”.

Shima fuska Maash ɗin ya ƙara tsukewa, tare da kallon agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa baƙi mai ƙyau. Kansa ya ɗan girgiza fuskar na sake komawa tamau. “No grandpa am sorry. Ka shiga ciki, jus 30minutes am come back”. Baima jira mi Baba prof ɗin zai ce ba ya raɓashi ya wuce. Matuƙar sosuwa ran Baba prof yayi, dan ko iya cewa komai baiyi ba ya bisa da kallo kawai shi da karen nasa. Sai guards ɗinsa da suka take masa baya. Gefen lips ɗinsa ya ɗan cija kawai yana nufar hanyar babban sashen. Duk ta inda ya gitta masu aiki zubewa suke suna gaishesa. Ɗaya bayan ɗaya masu gidan suka fara fitowa suna gaishesa suma tunda duk sun san da zuwansa. Su dai yaran basu san mike faruwa ba dan ko barci ba tashi sukai ba balle ai batun yin sallar asuba. Hajiya Mammah tayi zaram zata wuce kiran Maash Baba ya dakatar da ita. Sanar musu Maash ɗin ya fita yayi, amma yanzu zai dawo. Sai a lokacin Paah ya ɗan sauke ajiyar zuciya. Tashi yay ya haura sama ya duba Ummie. Barcinta ma take hankali kwance. Sai mama Balki dake ɗan siɗaɗowa da tayi sallar asuba ta gyara sashen ta mata wanka ta bata abinci. Cikin girmamawa ta gaida Baban. Shiko yanata faman saka mata albarka da wannan ƙoƙarin nata. Murmushi dai ta dinga yi ita dai kawai.

Bayan ya dawo ƙasan suka ɗan fara tattaunawa akan al'amarin Maash ɗin. Hajiya Mammah nata sakko batun Azizat, acewarta hakan shine kawai maganin wannan matsala data kunno musu kai. Uncle Abdullahi ya bata goyon baya, shi dai Paah da farko shiru yayi, sai da Hajiya Mammah ta balbalesa da masifa ne ya ce shifa bawai baya so bane. Kawai yana tunanin ta yanda za'a sake tadawa Awwab ɗin maganar ne baya kuma anyita a watannin baya sai dai rai ya ɓaci kawai a banza. Kowa ya fahimci uzirin Paah ɗin, dan taurin kan Maash a bayyane yake ga kowa na gidan. Dan in fa har bashi yace zai yi abuba babu ubanda ya isa ya sanya shi ya yisa. Hajiya Mammah dai ta nuna musu wannan karon za'a masa zagir-zagir ne, dolene su nuna masa su suka haifesa ba shine ya haifesu ba. Domin kafa hujja aka aika Maman Malika wai taje sashen Maash ɗin ta duba wace yarinya ce ya kai. Taso noƙewa, amma girman suruki ya hanata dole ta miƙe ta tafi, babu jimawa

Please Login or Register in order to submit comment