Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Karan farko ya ɗan ɗago ya kalla Hayatun, sai kuma ya maida kansa ga wayar batare da yace komai ba. Tsahon mintuna biyu kamar yama manta da shi sai kuma ya ajiye wayar a gefensa. Hannunsa ya ɗan matsa tare da ɗagowa ya zubama Hayatun idanunsa. Dole Hayatu yay ƙasa da nasa kan dan baya iya jure irin kallon nan na ogansa mai kama da na abokin yaƙi a filin daga..
Cikin silent voice ɗin nan nasa da janye idanunsa daga kansa ya furta, “A sanarma Hameed ya shirya zuwa 9 zamu wuce Abuja. Sai kai magana da Faisal zamu iso masa da mara lafiya ya taremu a airport”.
Sosai Hayatu ya zaro idanu waje. Duk yanda yaso haɗiye abinda ke masa kai kawo ya kasa hakan. Bai ma san sanda ya furta, “Amma Sir baka ganin tafiya da ita zai iya ɗarsama family ɗinta wani abu a rai kuwa? Jiya ne fa suka kawota nan a matsayin amarya. Kasan fa sunan arewa komai nasu na tafiya da addini da al'ada”.
Ko motsi Maash daya kwantar da kansa jikin kujera ya lumshe idanu baiyi ba balle Hayatu yay tunanin samun amsa. Ya kuma san shirun nasa na nufin bazai tanka ɗin ba, ya kuma gama zartar da hukunci kenan. Jiki a sanyaye Hayatu ya juya zai fita. Yayinda yake ta sake-saƙen mai fishshesa a zuciya. Dan dolene fa suyi wani abu da zai gamsar da family ɗin ta. In ba hakaba akwai babbar damuwa fa, kwaɓarsu zata iya yin ruwa batare da sun farga ba, shi komai ma sake ruɗar da shi yake. Dan yarasa dalilin ogan nasa na ƙulla igiyar aure tsakaninsa da ƴar bala'in yarinyar nan. Tunda yasan idan amsar video ɗin nan yay niyya da tuni ya amsa tako wace hanya ai, duk da dai ya fahimci itama yarinyar akwai taurin kai, sannan tana da power a cikin al'umma game da aikinta, maybe shiyyasa ogan nasa yaƙi yin komai kai tsaye a kanta ya biyo ta wannan sigar.
Gashi bai sanar masa komai akan shirin nasa ba. Hasalima sai a jiya shima ya san da batun auren bayan sun baro Lagos a jirgi yake sanar masa. Ya shiga shock matuƙa, sai dai bashi da hurumin iya cewa komai tunda ya riga ya zartar da hukunci, amma ya yini ya kwana al'amarin nan na juya masa a rai. Dan duk duniya shine kaɗai kuma yasan Maash ɗin yayi wannan auren, ko su dangin yarinyar basu san shine ba, saboda baije musu a Maash ɗin ba. To koma dai miye, shi kam zaiga yaya wasan zai kaya, dan shi ɗin shaida ne, ogansa mutum ne mai tsananin taurin kai da aljananci na gaske. Ga hatsabibancin masifa da dagiya akan abu, ya tabbatar ba son yarinyar nan yake ba, dan inda hakane kai tsaye zaije yace yana sontan saboda shi bai iya ɓoye-boye ba tamkar bature yake komai nasa kai tsaye yake yinsa. Ko minene a ransa kai tsaye yake fiddashi koda bazai ma kowa daɗi ba shi babu ruwansa idan yayi dai-dai da ra'ayinsa kansa kawai yake kallo..
Kai tsaye anguwar su Samraah ya nufa, dan dolene yaje ya tsara abinda ya dace gudun samun akasi..

★★★

A gidan Abba kam sai a safiyar yau ƙananun magana suka fito sosai. Dan kuwa Mom ta titsiye Abba taji komai daya faru a wajen ɗaurin aure dama kafin ɗaurin auren. Dan haka ta shiga bazama na kusa da ita su kuma suka ɗauki zance ƙus-ƙus. Tun anayin abin a gwargwaɗe har dai komai ya fito cewar bada Mansoor aka ɗaurama Samraah aure ba da wani ne daban. Dan mahaifiyarsa ta shata layi akan auren nasu, duk da dai shi Mansoor ɗin yaso bijirewa amma su Kawu Musa suka ce bazasu bashi ba saboda abinda mahaifiyar tasa tazo tayi a jiyan har gida batare da matan cikin gida sun sani ba sai su Gwaggo Gudidi kawai. Tun dai zance na iya cikin gida har maƙwafta suka fara shigowa jin gulma da kawo wadda suka jiyo a waje. Yanda Mom ta nuna farin cikinta a fili akan abinda ya farun ya ƙona zukatan su Gwaggo Gudidi da ƴan Gwarzo. Sai ga faɗa ya kaure tsakaninta da Aunty Jimmai babbar ɗiyar Kawu Musa. Kafin kace mi gida hargitse. Suka haɗu sukama Mom tatas, dan babu abinda suka manta basu faɗa mata ba har sai da tai kuka. Kuma Gwaggo Gudidi ta tabbatar mata indai tana raye sai Abba ya ƙara aure. Da ƙyar da ƙyar dai Musaddiq ya kwantar da wannan tarzoma. A kusan kuma dai-dai lokacin Hayatu ya iso gidan. Inda ma ALLAH ya taimaka Musaddiq da Abba da su Kawu Musa na ƙofar gida a lokacin da ya iso ɗin, dan haka ya samu tarba ta mutunci. Cikin ɗar-ɗar da addu'a a ƙasan ransa bayan sun gaisa ya sanar da su abinda ke tafe da shi kamar yanda ya tsara domin bama ogansa kariya. Hankalinsu ya tashi da jin Samraah babu lafiya. A take babu ɓata lokaci suka muƙe domin binsa asibiti dubata. Bai hanasu ba, dan bashi da wani zaɓi, sannan hakanne ma zai taimaka masa tsarin nasa ya tafi dai-dai yanda yake buƙata batare da Maash ya rufta ba ko shi dake ɗan kore ba.........✍️


Hummmm🥱

_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒐_


.......Hankalinsu ya tashi matuƙa da ganin yanayin Samraah a asibiti. Yayinda Dr Su'adah ta sake ruɗar da su da bayanin haɗarin da Samraah ke ciki. Tare da tabbatar musu idan ba'a sadata da ƙwararren likitansu dake birnin tarayya Abuja da zama ba za'a iya rasata, dan zuciyarta na gab da bugawa saboda yanda jininta yay tsananin hawa sama. Sam babu wanda yay musu akan yarda da hakan. Sai dai sun nema alfarmar Hayatu akan Musaddiq zai bisu zuwa Abuja ɗin. Rasa abincewa Hayatu yayi, dan ya tabbatar tafiya da Musaddiq bazai yiwu ba. Amma rashin mafita sai ya amsa musu da to su jira suji daga likitar yaya za'ai tafiyar. Sun gamsu da hakan, dan haka ya lallaɓa ya koma gefe ya sake samun Dr Su'adah akan ta taimakesa ya fita a tarkon mutanen nan, dan yana da dalilin da yasa baya so kowa ya bisu. Ita dai Dr Su'adah bata san ainahin mike faruwa ba, dan Hayatu ɗan uwanta ne na jini, abinda ya gaya mata kuma bashi ne ainahin alaƙar dake tsakanin Samraah da Maash ba. Dan haka babu musu ta taimaka masan. Ita ce ta tsara su Kawu Musa ta hanyar da dole suka gamsu akan za'a fara tafiya da Samraah ta jirgi ne, masu son bin bayanta sai suyi hakuri subi a baya ta mota nan da kwana biyu haka. Haka kawai sai hankalin Musaddiq ya kasa kwanciya, sai dai babu yanda zai yi tunda su Kawu Musa sun yarda. Haka dai yana ji yana gani aka shiga yima Samraah shirye-shirye dan wai za'a wuce da ita ne a jirgin ƙarfe takwas na dare...

★✓★✓★✓★✓

*_ABUJA AIRPORT_*

Ƙarfe tara dai-dai jirgin daya taso daga Kano zuwa Abuja ya sauka a filin jirgin na birnin tarayya. Maash da tawagarsa na ɗaya daga cikin passinges ɗin wannan jirgi. Hakama Samraah da likitan da take tare da ita suna a jirgin. Sai dai a tsarin tafiyar sam babu abinda ya alaƙantasu da Maash. Hasalima shi yana a private section ne. Yayinda ita da likita suke a sashen kowa da kowa, koda yake ita bama ta a hayyacinta balle ta fahimta. Dan an shigo da ita ne a yanayin wadda take bisa umarnin likita da zataje gani a Anuja. Ko'a airport ɗin ma tuni Maash ya shige ɗaya daga cikin tawagar jerin motocin da suka zo ɗaukarsu. Yayinda ita kuma ambulance ta ɗauketa ta wani babban private asibiti da ake matuƙar ji da shi anan birnin Abuja ɗin..

*_KANO_*

Anan Kano an wuce da Samraah an bar danginta da jimamami. Musamman ma Musaddiq da sam zuciyarsa ta kasa zama waje ɗaya. Kai shi tunma jiya hankalinsa a tashe yake da wannan aure. Sai dai babu yanda ya iya tunda su Kawu Musa sun bama mijin da suka aura matan yarda ɗari bisa ɗari. An ƙarasa dai wannan dare cike da jajantama juna bisa ga halin da Samraah ɗin ke a ciki. Daga ƙarshe dai a washe gari kowa ya shirya ya kama gabansa saboda wayar da akai da mijin na Samraah akan jikin da sauƙi suka ganta ta hanyar video call. Taro dai ya tashi an bar Mom da mijinta sai auta da Musaddiq da Hafizzullah kawai a gidan dan su Baby basa nan. Sai a washe gari suka dawo gidan. Hafizzullah ma dai shirin komawa makaranta yayi, duk da yaso zuwa wajen Samraah Musaddiq ya lallashesa akan yayi haƙuri tunda an kusa musu hutu, yanzu zuwa Abuja dubata ba nashi bane, shima ɗin da akace zai je su Kawu since ya dakata kada mijin yaga kamar ana nuna ya gaza ne. Badan yaso ba ya shirya ya wuce zuciyarsa duk babu daɗi. Dan duk wani masoyin Samraah ɗin zuciyarsa a ƙuntace take da abinda ya faru akan wannan aure da kuma halin ciwo da take a ciki yanzu. Dan idan ta shine ma baza'a ɗaura mata aure da wani da bata sani ba tun farko. Amma dai su Kawu Musa sun bada goyon baya babu abinda su zasu iya musamman ma shi dake amsa sunan ƙani a wajenta. Amma zai cigaba da binta da addu'a kamar yanda Yaya Musaddiq yace yayi. Musaddiq ɗin ne ya kaisa har Katsina da kansa. Ya sake masa nasiha sosai sannan ya juyo gida.....

*_MANSOOR_*

Kowa ka kalla a ahalin gidan hankalinsa a tashe yake. Dan kusan duk manyan suna a sashen su Mansoor da aketa ƙoƙarin gaggaɓe ƙofar ɗakinsa. Yau kwanaki uku kenan yana a kulle a ciki yaƙi ya fito. Lallashin duniya da roƙo yay biris da kowa. Tun ana ɗaukar abin nasa a fushi na ɗan lokaci har abin ya wuce makaɗi da rawa, dan zuwa yau ko motsinsa an bar ji a ɗakin, dole fa aka nemo mai gyara domin gaggaɓe ƙofar. Kuka sosai Mamynsu keyi tun jiya, dan ita kanta har sai da hawan jininta ya motsa. A yanzu haka a nane take da ƙofar ji take mai aikin ma kamar baya sauri ne.
Ana ɓalle ƙofar mafi yawansu duk suka afka ciki, tsakanin Attahir da Mamy har turereniyar rige-rigen isa ake kan Mansoor dake kwance samɓal a ƙasa babu alamar rai a tare da shi. A tare suka ɗagosa, sai dai me yaraf ya koma alamar babu rai. Wani mahaukacin ƙara Mamy ta fasa mai firgitarwa, tamkar ƙiftawar ido sai gata ƙasa wanwar itama ta sume musu. Sake harmutsewa ɗakin yayi, dole aka kwashesu zuwa asibiti kamar yanda wasu suka bada shawara.....


*_ABUJA_*

Kaifin hasken rana da nake ji mai ƙarfi a saman fatar idanuna ya sani motsasu a hankali. Sosai sun min nauyi, dan illahirin jijiyoyinsu a takure suke waje guda. Hannuna da nake ji kamar an ɗaure nai ƙoƙarin motsawa domin kaiwa saman idanun, sai naji an sake damƙesa da ƙyau, tare da jin saukar wata murya cikin kunnena. “Bi a hankali akwai abu a hannunki. Sannu kin farka bari nai kiran likita”.
Sosai naji gabana ta faɗi. A can ƙasan zuciyata na ayyana (likita) a fili kam babu abinda nake iya motsawa a jikina saboda illahirinsa yay min nauyi. Amma sai na shiga ƙoƙarin buɗe idanuna. Dishi-dishi nake gani, sai dai hakan bai hanasu sauka akan mutumin daya shigo bayansa da wasu mata guda biyu ba saboda yanda hayaniyar maganar da suke taja hankalina. Duk da ba ihu suke ba ko fidda sautin maganar tasu da ƙarfi. Ƙarasa buɗe idanun nayi da ƙyar sakamakon jin inuwar mutum a kaina. Wani irin faɗuwar gaba naji ta sake riskata, dan kuwa tabbas a asibiti nake, dan shigar wanda ke kaina tsaye kawai ta tabbatar min da shi ɗin likita ne. Sannu suka shiga jeramin, sai dai na gagara amsawa kowa a cikinsu, na dai zuba musu ido ne kawai ina binsu da kallon ƙurilla. Ko tambayoyin da likitan ke jeromin game da jikina na gagara amsa masa ko ɗaya. Fahimtar kamar a rikice nake da yanda nake bin ɗakin da kallo ya sakashi ƙyaleni shima. Sai cikin matan da ya shigo da su ne ke ƙoƙarin cire min allurar drip dake a hannuna. Kusan mintuna biyar muna a haka kafin ya sake juyowa ya fuskanceni. Cikin harshen turanci ya furta. “I understand that you are confused. This is a hospital, you are under the care of a doctor. Alhamdulillah, your body is very easy.”
A hankali na kai hannuna saman kaina da har yanzu nake jinsa da nauyi, kafin na sake ɗagowa na dubesu murya a karye na ce, “Who brought me? Which hospital is this? Since when have I been?”.
Da alama yanda na jera tambayoyin sun bashi mamaki, dan sai da ya ɗan waro idanunsa, sai kuma yay murmushi da faɗin, "Oh relax! You will all know. Now they will help you to fix your body, eat something and I will come back and answer your questions". Ya ƙare maganar yana nuna min Nurses ɗin. Fuska na ɗan ɓata, sai dai bance komai ba. Shi kuma ya juya ya fita da Nurse ɗaya ya barni da biyu. Da farko naso naƙi yarda, dan nafi son na fara sanin a ina nake. Sai dai yanda suka nuna damuwarsu da tabbatar min ƙin yardata zai iya taɓa aikinsu yasa na amince. Amma zuciyata taƙi gajiya da daina kai-kawon ganin ɗakin da naken matsayin wai asibiti. Saboda sam bai kama da asibiti ba fa, duk da gado da tarkacen ɗakin duk irin na asibitin ne, sai dai da gani na musamman ne su. Ga television ga freight, sannan toilet da suka kamani suka kaini a cikin ɗakin dai yake shima sam bai kama da asibi ba. Ciwon da jikina kemin ya sakani bin umarninsu nayi wanka da ruwan da suka tara min mai ɗumi. Nako ji daɗin wankan, na saka doguwar riga irin wadda na cire pitch color da alama ta asibitin ce. Bata sauka min har ƙasa can ba sosai, amma dai banyi tsirara ba. Gashi tana da faɗi babu wani takura. Alwala na ɗauro na daddafa bango na fito. Da sauri suka iso gareni suka taimaka min muka ƙarasa, a saman lallausar sofa ɗin ɗakin nace su zaunar dani, sannan na buƙaci hijjab na salla da sallaya. Sai dai da alama babu, sai ɗaya ce tace bari ta sanarma doctor a kawo min. Komai bance ba, na jingina kaina da kujerar na lumshe idanuna.
Bata fi mintuna biyar ba sai gata ta dawo da sallaya da sabon hijjab a ledarsa. Ita ta ciromin shi, sannan ta shinfiɗa min sallayar. Har ƙasa hijjab ɗin ya sauka min sosai dan ko ƙafafuna ba'a gani, hakan yasa naji nutsuwa dan dama rigar bai gama sauka ba. Juyawa nai na tambayesa "What day is today?". A tare suka amsa min da, “Today is Monday”.
(Litinin) na maimaita a zuciyata. A zahiri kam sai na sake tambayarsu alƙibla. Ɗayarce mai kama da musulma duk da shigarta zata iya saka kace ba musulmar bace amma akwai ƙaton tabon salla a goshinta ta nuna min tare da bayani, bance komai ba na kabbara sallata. Tun inayi a tsaye har hakan ya nema gagara. Dan dole na koma a zaune kasancewar duk sallolin da nasan suna kaina sai da na ramasu na kwanaki biyun nan da bana a hayyacina.........✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_


.......Tun ina sallan shigowar doctor biyu. Sai dai ganin ban idar ba yana komawa. A na ƙarshe suka shigo su biyu dai-dai na idar ina zaune kawai nayi tagumi cikin dogon nazari da son sanin a ina nake wai. Jin muryar da banyi zato ba kasancewar nasan na kuɓuta daga garesu yasa na ɗago da sauri. Shi ɗinne kuwa. Wato yaron mugun nan Maash. Ganin yanda ina ɗagowa ya duƙar da nasa kan ƙasa kamar wani munafuki ya sani cigaba da kallon nasa kawai. Doctor ne ya katseni da tambayar yaya nake jin jikina yanzu. Cikin janye idanuna na amsa masa da Alhamdullah. Ya nuna jin daɗinsa kafin yay min nuna da mutumin nan. “Now you will get all the answers to your questions from him. I will send a nurse with your medicine. If you eat, she will give you.” daga haka ya juya ya fita. Shiru ɗakin ya ɗauka kusan na minti ɗaya, kafin a ƙufule cikin dasashjiyar muryata mai nuni da banda lafiya na furta, “Ya akayi na dawo gareku? Ina ne nan kuka kawoni?”.
Sake duƙar da kai yayi kamar mai tsoron bani amsa, sai kuma a hankali ya furta, “Kiyi haƙuri nan asibiti ne. Yaya jiki?”.
Wani irin takaici ne ya ƙuleni, dan haka cikin sake zafafa harshe na amsa shi da, “Ba ruwanka da jikina. Kaje ka sanar ma wanda ya aikoka yasa likitan nan ya sallaman. Sannan ku fita a sabgata. Idan ba haka ba zan sakaku nadama da dana sanin sani na. In ba hakaba zan tabbatar muku TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE”. Daga haka na yunƙura a hankali na miƙe, ko inda yake ban sake kallo ba na koma saman gadon. Dai-dai nan Nurse ɗin nan ta dawo...

*_KANO_*.

A matuƙar tashin hankali zuciyar Mamyn su Mansoor ta gama shiga. Dan suna isowa asibitin ta farfaɗo ita. Amma Mansoor kusan awani uku kenan likitoci na tare da shi ba kuma su musu bayanin komai ba. Sai dai faman kaiwa da komawa suke a tsakanin ɗakinsa zuwa ofisoshinsu. Tun tana hawaye har ma sun ƙafe ta koma na zuci. Nadama take ji na sake shigarta akan abinda ta aikata. Lallai tayi dana sanin biyema shawarar ƴar uwarta. Inama zata iya maida hannun agogo baya. Data goge komai da yake a yanzu da maida baya data shuɗe. Dan har ga ALLAH Mansoor shine ɗa mafi soyuwa a zuciyarta. Kodan tasha matuƙar wahala ne a yayin haihuwarsa, ko kuwa dan kamanin da yake da mahaifinsa. Sam bazata iya jure rasashi ba. Dan bazata taɓa yafema kanta ba.
“Mamy dan ALLAH ki zauna ki huta, in sha ALLAHU ɗan uwana zai tashi. Kinga kema fa ba lafiyar ne da ke ba”. Attahir ne mai maganar cikin tsantsar damuwa ganin yanda Mamyn tasu ke faman kai kawo ga hannunta dafe da kanta. Yasan komai zai iya faruwa da ita, dan bata gama dawowa dai-dai ba ta fito a ɗakin da aka kwantar da ita. Anyi-anyi kuma taƙi ta koma dole aka haƙura aka barta. Dan Dad ɗin su ma haushin dagiyar tata ya sashi komawa can gefe ya zauna kawai bai sake kulata ba.
“Attahiru bazaka gane ba. Nasan bazaka fahimta ba. Barni kawai kaji. Barni da abinda ya dameni. Ni da kaina na jefa rayuwar yarona a bala'i. Da nasan haka zata kasance da ban aikata ba. Da ban hanashi aurenta ba. Attahiru idan na rasa Mansoor nima zaku rasani ne wlhy”.
“Dan ALLAH Mamy ki daina faɗa. In sha ALLAHU bazamu rasaki ba. Ki kuma daina zargin kanki kowa baya wuce kuskure ai. Mansoor zai samu sauƙi. Ki masa addu'a”.
Kuka mai nauyi ta sakar masa tana ƙoƙarin dafe bango saboda jirin dake neman yaddata taji ya kwasheta. Da sauri yayi kanta ya riƙota. Da taimakonsa suka zauna yana jera mata sannu. Dai-dai nan shima Dad ɗin su ya taso, hakama ƙannensu da suka haɗe kai gefe suna kuka. A ruɗe duk suke tambayar miya faru, sai da ta ɗago ta ce musu ba komai sannan suka shiga sauke ajiyar zuciya. Hakan sai yay dai-dai da fitowar amintaccen likitansu Dr Gana. Kamar waɗanda aka zabura duk suka miƙe garesa har Mamy. Har rige-rigen tambayarsa yaya Mansoor suke yi. Shiko ya ɗan bisu da kallo cikin damuwa. Sai kuma a hankali ya furta, “Alhaji idan babu damuwa na ganka a office mana. Amma Hajiya tai zamanta Please”.
Tsantsar tashin hankali ne ya bayyana a fuskokinsu. Yayinda Mamy ta fashe da kuka sauran ƙanensu na tayata. Shi kansa Dad ji yay ƙafafunsa sun masa matuƙar nauyi. Haka shima Attahir ya gagara tashi har sai da doctor ya sake musu magana sannan. Attahir ne ya fara jarumtar miƙewa, sannan shima Abban ya tashi suka nufi office ɗin su biyu kowanne na jin zuciyarsa na bugawa da sauri-sauri tamkar zata faso ƙirazansu ta fito waje.....

_Ni kaina Bilyn ku zuciyar tawa bugawa take. ALLAH yasa dai ba rasa Mansoor mukai ba😭😭🙆._

*_ABUJA_*

★Sosai na birkicema likitan nan akan nifa sai nasan a inda nake. Hankalinsa ya tashi, dan ya tabbatar min in har ban kwantar da nawa hankalin ba aikinsu zai iya komawa baya. Ganin fa ba saurarensa zanyi ba ya sanar min in a Abuja ne cikin MAASH HOSPITAL.
“Abuja?!”.
Kansa ya jinjina min da sauri. “Yes, yes. You were brought from our branch in Kano. Once you have finished receiving the medicine, you will return. Please calm down”
Rasama mi zance masa nayi, sai kawai nayi shiru ina kallon PA da suka shigo kusan tare. Shi doctor ya zata na fahimcesa ne, dan haka ya sauke ajiyar zuciya da cigaba da kwantar min da hankali. Ko kulashi ban sake yi ba. Har ya gama ɓaɓatunsa ya fita. Ɗauke idanu nai da ga kan PA ina mai cije lips ɗina da ƙarfi. Na fahimci waɗan nan mutanen so suke sai mun kai matakin ƙarshe da su. So suke sai na bijire ma maganar Yaya Musaddiq da Mansoor. So suke sai na musu fallasar da zata ruguza dukkan tanadinsu. Kamar PA ya fahimci mi nake ayyanawa a raina. Takowa yay ya ƙaraso gaban gadon ya ajiye ledar hannunsa. Kafin ya ciro wayarsa a aljihu yay ƴan danne-danne batare da yace komai ba ya ajiye min saman table da akai crossing a tsakiyar gadon da magunguna a kai da dama sune Nurse zata bani na birkice musu. Harara

Please Login or Register in order to submit comment